Showing 249001 words to 252000 words out of 270738 words

Chapter 84 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

gaji shine nace bari in kama mata aikin "
Murmushi tayi tace.
"Ikon Allah Luba kinga mun samu suruka mara son jiki. Matan yaran gidannan ko wani Wan taro aka haWa sai dai a siyo abinci a hotel. Ai ko Usman ne zai shigo ?asar a hotel ake sissiyo abinci dan ganda."
Ni dai kaina na ?asa ta gama shi mun albarka ta koma falo. Dani da Luba muka jera komai a babban daining Win gidan Alhaji Baba sai shi mun albarka yake yi tare da yabon abinda nayi.
Tun daga ranar na karSe girkin Alhaji Baba a hannun Luba ni ke mai girkinshi. Yana ci yana jin daWi sosai.
Kwanana Bakwai muka wayi gari yau su Usman zasu shigo ?asar. Tun suna Airport muke waya dashi har zuwa shigansu jirgi kafin yayi mun sallama. Ina zaune kunyar in fita ince zan yi mishi girki nake ta yi. Sai ga Luba ta shigo da sallamarta.
"Anty Iyabo Hajiya tace in sanar dake sun tafi ?auye ita da Alhaji Baba. Mahaifiyar mai wanki da gugan gidannan ce Allah yayi mata rasuwa, wai sai gobe zasu taso daga nan zasu biya wani wajen."
Ai sai naji daWi sosai.
Ayya Allah ya ji?anta nima yanzu nake son in fito ki taya ni girkin tarbar Usman ai"
Dariya Luba tayi tace.
"Tabb su Uncle yau har kitchen za'a shiga ayi mishi girkin tarba? Tabb shi da wata rana sai ya shigo ?asar zai kwashi matan ya kaisu gidan cin abinci ma"
Mamaki sai ya kamani. Muna kitchen ina ferar dankalin turawa, Luba na zuba ma kaza nono da kayan ?amshi tana bani labarin abubbuwa daya kamata ace na sani, da kuma yin taka tsantsan sosai. Ni dai mamaki duk ya bi ya isheni.
Faten dankalin turawa da ni?a??en naman saniya nayi. Sai nayi shinkafa kaza . Nayi mishi zoSo mai kyau yaji abarba da inabi bushasshe. Sai bayan la'asar muka kammala aikinnan na shiga wanka na bar Biyu tare da Luba a falo suna turara falon da turaren wuta. Sai da nayi sallar la,asar kafin na soma shafe_shafen mai da turarukan ?amshi, da humrori harda humrar matan aure. Sai da na gama mulke jikina da Humrar matan aurennan na tuno sister Badiat Ibrahim tayi gargaWi akan sai in zaka turakane zaka shafa ba'aso kowa yaji ?amshin face mijinki, ko kishiyarki ba'aso ki shafa ranar kwananta gudun kar a shiga hakkinta. Dan wannan humra wani key ne na buWe sha,awar Wa namiji, hanyace ta sawa miji ya zamema matarshi Waye manna, tana da tasiri ainun. ( Babu boka babu malam wallahi Allah Waya ne babu wani abu na surkulle a ciki. Sanin aikine da sanin itatuwa masu tasiri ga ma'aurata. An sanmu Kanuri muna gaba_gaba wajen mallakar zuchiya da ruhin Wa namiji ta hanyar ?amshinmu na jikinmu, da ?amshin gidanmu. Me so tayi magana ina Wiba a ?aramar kwalba dan kowa ta mallaki nata) ina cikin rabe Wayan biyu kawai na jiyo muryar Usman yana wasa da biyu.
Gabanane ya yanke ya faWi duk saina dibibice. Sake kayan zanyi ko in fita a haka kawai?
Luba ce naji tana kirana da ?arfi babu shiri na fito ko mayafi babu.
Da matarshi muka soma haWa idanu tana tsaye shi kuma yana zaune ?an biyu na cinyarshi sunata zillo.
Kallon sama da ?asa tayi mun irin kallon tsantsar wula?ancinnan dan a zahiri kyakkyawace ba?a mai dogon hanci da dara daran idanu. Idanuna na mayar kan mijinmu shima ni yake kallo amman kallon burgewa.
A hankali na tattako da fara,ata na wuceta ina karkaWa abun duniyar da ni shi kaWaine kyauna wanda nayi imanin ya girgizata ga ?amshin humrata daya sumar da'ita. Saida naje daf dashi saina juya mishi bayan nawa ita na fuskanceta da dariyata.
"Antyna bari in soma dake barkanku da dawowa da fatan kun dawo lafiya?"
Na ?arashe ina dariya. A zuchiyata kuma duk fa na raina kaina dan harna soma kokonto akan Usman.
"Lafiya lau Amarya ya ba?unta?"
Ta faWa da salon cinye kishi. Kallon Usman tayi tace.
"Gaskiya ka iya zaSe wannan karon lutiya kaji sha'awa kenan. Naga tana da ?iba masha Allah"
Ni nasan magana ta caka mun. Shi ko gogan naka sai ya saki murmushi yana wani jin daWi.
"Sannu da dawowa ango mijin Amarya ya hanya?"
Ai kafin yayi magana sai ta kwashe da uban dariya harda rufe idanu. Shi kuma yayi lub a kujera sai sha?ar ?amshina yake yi idanunshi har sun sauya kala.
"Lafiya Honey meya faru?" Ya tambayeta murya ?asa_?asa
"A_a ba daku bane a waya ne aka turo wani abun dariya shine ya bani nishaWi. Ni kam ina bu?atar watsa ruwa"
Murmusawa nayi na bita da idanu, itama ni take kallo.
Zama nayi abuna ina jiran abinda zaice.
"To ko in kai ki gidane ni sai in dawo? Tun a Airport nace in kai ki gida kin ?i. Gimbiya kaita masaukin ki ta watsa ruwa. Ina Luba taje mota ta dakko miki akwatinki"
Ni dai ina zaune ina kallonsu kar.
"A_a ta barshi kawai. Sai ka tawo dama na zaci Alhaji Baba na gidanne mu gaisa"
Tana gama faWin haka ta yi ficewarta.
"Asma'u!! Asma'u!! "
Ko juyowa batai ba. Kallona na dawo dashi gareshi, ni yake kallo harda ?an?ance idanunshi. Yayi wani kyau na musamman.
"Ya akayi Gimbiya. Duk kin kashe mun jikina da ?amshinki sai wani kasala ke sakkomun. Kinyi kyau fiye da da. Da wanne turare kike amfani haka mai sanyin ?amshi haka?
Murmushi nayi nima na juya da kyau ina kallonshi nace.
Da yaushe kenan yallaSai?"
"Da kafin in aureki mana"
Dariya muka yi tare. Ya kama hannuna da hannunshi masu Wumi ya ri?e. Lumshe idanuna nayi. Kun dai san mutuniyar taku ba daga nan ba, balle an jima ba'a haWu da rijalu ba.( Ummu nabeeha ni Iyabo dake nake) Da ?yar na buWe idanuna na kalleshi. Shima ya shige cikin kujera yana ta aikin kallona ga ?an biyu sai gwarancensu suke yi mana.
Yanzu dai muje kayi wanka sai kaxo kaci abinci nayi maka girki mai daWi"
Kamar rakumi da akala haka ya zamemun. Ko wankan da ?yar na rarrasheshi ya shiga kun gane ai? Hahaha
Kafin ya fito na fita tsakar gidan ina tambayar da wacce motar suka zo. Mai gadi ne yake sanarmun a motar Hajiya Asma'u ta tafi gida.
Ina komawa ciki na sameshi a kwance a gado daga shi sai tawul a jikinshi.
"Ina jakar kayan nawa ko ba ita kika je Wakkowa ba.?
A hankali yake magana kamar bacci yake ji, ko kuma wanda ake yima susa a takashi. ko kuma ya kwaso gajiya ne ?ila daga wajen aiki, tunda jiya ma a asibiti ya kwana.
Hajiya Asma'u ta tafi da motar da kayan ke ciki. ?ila ta manta ne. Kazo muje kaci abincin ko?"
"Ta tafi mun da kaya fa?".
Ya faWa da mamaki. Ni kawar da zancan nayi ta hanyar taimaka mishi yasa kayanshi, bayan na bashi kulaccam Wina ta musamman ya shafe jikinshi dashi, yanata santin ?amshin. Muka wuce daining na zuba mishi abincinshi nima na zuba nawa.
"Ya ba?unta dai. Da fatan Family na sun karSeki hannu bibbiyu ko?"
Sai da na haWiye abincin bakina kana nace.
Sun karSeni fiye da tunani na ma. Gaskiya akwaisu da karamci"
Murmushi yayi yana kallona.
"Kinga Asma'u yau ko? Ita Suhaila ai kun haWu a sha'anin biki ko?"
A_a za dai mu haWu gobe in sha Allah?"
Cokali ya ajjiye yana tauna abinci yana kallona so yake ya gama tauna abincin nasan ya jefo mun tambaya.
Ai kuwa ilay
"Bata zo buWar kai bane ko Yaya. Kina nufin bata zo gidannan ba.?"
Gaskiya ko tazo bamu haWu ba. Babu mamaki abubbuwane sukai mata yawa"
Dariya kawai yayi tare da kurSan zoSo ya girgiza?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? kai kawai.
"Wacce ?asa kika taSa fita shine ko labari baki bani ba har sai da kuka je ofishin yin paspo tukunna. Ko umara kika je ne uhm?"
Ya tambaya yana dariyar zolaya.
Cikinane ya karta mun, sai da na Wan ri?eshi kaWan kafin nace.
Umara na taSa yi. Na mance ne ban sanar maka ba."
"Okay to naji kince gobe Suhaila zata ganki. Ba yau kike son tarewa da angon naki bane, ko baki shirya bane?"
Ya kafeni da idanu take na ?ware. Saida na daWe ina tari kafin ya faWa mun.
"Sannu kiyi a hankali"
Sai da na dawo cikin hayyacina kana nace.
"Sai su Alhaji Baba sun dawo gobe tukunna zamu tafi"
Dariya yayi harda tafi.
"Au so kike yau in kwana a gidannan kenan ko mu yi abun kunya?"
Da dariyata nace.
"Akan me ga matarka can tana jiranka."
Hararar soyayya yayi mun.
A haka dai mu ka ci abincinmu muna hira har akai sallar magriba.
"To zanje masallaci daga can zan wuce can gida in dubo Antynki da yara. Zan dawo mu kwana anan Win tunda dai haka kike so muyi abun kunya"
Kafin ma in yi magana ya fice.
Da sauri na shiga Waki na tura mishi text akan ya zauna tare dasu, nima zanyi zamana anan har zuwa ranar da zamu juya tunda yace kwana uku zaiyi ni na barma Hajiya Suhailat kwanan.
Ina turawa na datse wayata na ta da kabbarar Sallah.



Bin Usman:.

Yana idar da sallah ya Wauki motar Hajiya ya nufi gidanshi dake Abuja kwatas.
Gidan sama ne babban gaske. Motarshi na shiga harabar gidan yaranshi suka fito a guje zuwa tarbarshi.
Da dariya ya tarbesu yana shafa kawunansu tare da tambayar lafiyarsu.
Gaba yayi suna biye dashi a baya har zuwa falon ?asa wanda anan matattakalar hawa benen take. A gefe_da gefe ko wacce mace matattakalar hawa samanta da ban. Shi mai gidan Sarayinshi na cikin babban falon gidan. A gefen nashi ?ofar shiga Sarayin iyabo yake wanda kafin zuwanta ?an uwan Hajiya Suhailat ne maza a ciki suna karatu a garin.
Yanzu sun koma bq da zama wannan ma ya sake dafa Hajiya Suhailat sosai.
A babban falon ya tarar da Mus'ab ?aninshi yana zaune yana kallon labarai dama mayen labaraine.
"Sannu da shigowa Yaya Usman. Na ganka kai kaWai ina Amaryar tamu mu da muke ta dakon zuwanta?"
Zama Usman yayi kusa da Wan uwanshi yara kuma suka wuce sama wajen iyayensu.
"Ka sassauta muryarka kar Suhailat ta hanaka kallo a falonnan ni dai na faWa maka"
Dariya Mus'ab yayi yace.
"Ta kuwa Wauka da zafi itama fa bayan an kawo Amarya. Kasan matar Usman karami shegen surutu ne da'ita tazo gidannan tana ta labarin amaryar.
A ta?aice ma ?annenta sun tattare kayansu sun bar gidan. ?anwarta Naja dai tazo tun ranar bikin. Mu kammu fishi take yi damu fa. Anty Ma'u ma ko gaisuwata data shigo muka haWu a wajen ajjiye mota bata amsa ba sai tsaki da harara dama kasanta bata da daWi."
Shiru Usman yayi yana nazari ranshi ya Saci matu?ar Saci. Menene laifi dan yaga mace ya aureta kamar yadda suma ya auresu? Ya ga dukkansu sun Wauki auren da zafin da bai yi zato ba ma. Ita kanta Asma'un ya daddanne abubbuwan da tayi mishi a india da dama. Gashi cikinsu babu wacce ta sakko da zummar tarbarshi ma.

Kunji irin gidan da Iyabo ta sake faWowa
Ko yaya zaman zai kasance oho"
MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI



ramlex266: Ina mata da suka amsa sunan su ba Muna mata ba....

Ina macen da take so ta zamo tauraruwa a gidan mijinta,itace uwargida itace amarya...
ramlex266: Uwargida ko Amarya shin minene matsalar ki a wajen miji?

Rashin dandano ko ni'ima?
Bushewar farji qayau kamar busashen ciyawa?
Rashin samun gamsuwa a wajen maigida ko rashin sha'awar ce ga baki d'aya?
Budewar farji kamar kofar wambai ko qarni/wari ke damunki
ramlex266: Kina so ki zama tauraura kuma sarauniya a wajen oga a rasa gane sirrin naki? Ki zamo yar gaban goshi sai yanda kika ce wato kin mayar da oga mijin kafin ta ce? Ba boka ba malam gyaran shimfida kawai Hajiya to ki nemi hjy ramlex domin qarin bayani
ramlex266: 07069722234 ko 08064421211


Message Safmam Palace on WhatsApp. https://wa.me/2348067145801
Hello Maamas..
Shin ko kunsan AMASI'S TREAT from SAFMAMPALACE ta tanadar muku da ingantattun sinadarai na fito da martabar abinci da abin shaa? A AMASI'S TREAT Muna da spices and herbs irin su;Curry powder, Mixed Spices, special Jollof mix, fried rice, Mandi Spice, Garlic powder, Cinnamon, cloves, Tea blend, Yaji, Spiced daddawa.. Gasu nan dai dayawa.
Har ila Yau AMASI'S TREAT bata barku haka ba Seda ta tanadar muku da kayan maqulashe Don gusar da kwadayi=?? Muna da;
Kwakumeti, Ridi, daquwa, Cin Cin da sauran su.
Bafa anan muka tsaya ba Muna da bangaren qayatattun dinke dinke.. SAFMAM CLOTHING zasu fito muku da kyawun dake materials dinku ta hanyar tsantsara muku dinki musamman na yaranku mata=?
?
Muna nan a Zaria Muna aika Kaya ko'ina cikin aminci
08067145801


Assallamu alaikum mutanan kirki Ina Miko gaisuwa daftn alheri=?O??#? samun damar mallakar duk abunda kakyeeda bukata. Cikin sauki ta hanyi Yi muku adashin gata =؃??#? idan matsalarki rashin sabbin plates Akwai
1, zubi duk sati 2k sati 10 kwasar kayan 20k =؃? Akwai zubi duk sati 2k sati 20 kwasar kayan 40k har zuwa duk yanda mutum yakyee bukata zamu turo maka da kayanmu idan lokacin kwasarka yayi da yarda Allah kazabi duk abunda kakyee bukata da yarda Allah to mekakyee kikyee jira ki tintibene domin jin yarda raguwar tsarukan sukyee insha Allah idan Kuma kyee ma,aikaciyace to kyeemafa =؃? Akwai kayan Yara yankanti
Akwai takalman da jakunkuna da mayafai
Da sauran kayan amfani kyeedai maxa ki hanzarta kafin mu Fara zubi
Insha Allah zamu Fara zubi a farkon( sabon watan August ) Allah yadafa mana nagodee sossai zee Musa takuce =؃??p? ga number din da zaa iya damuna =؃??#?=???=??? 08029882667


*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
07082649563 whats app number kira 07036028230
NAMA YA DAHU...
ROMO ?A?YE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI
LITTAFI NA HU?U
(12)

GWADABE:.

Da sauri ya juyo sai yaga ashe Bara'u ne a bayanshi.
Bai ga Bara'u a cikin daWi ba, kamar yadda shima ba'a cikin daWin yake ba. Juna suka zuba ma idanu cikinsu ko wanne na son jin damuwar Wan uwanshi.
", Gwadabe ya dai na ganka tsaye kana sharar hawaye? Ai godema Allah ya kamata kayi. Kai da ganin su Babala kasan sunyi nadamar abubbuwa da yawa. Komai fa ya lalace kai Layla har zane Yaya Hambali take yi. Dukiyar ma daya tara ta kusan ?arewa tas in faWa maka."
Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke. Tare da kallon Bara'u da kyau yace.
"Wani al'amari marar daWi na shirin tunkaroni, da ganin fuskarka kaji labari mummuna Bara'u meke faruwa?"
Murmushi Bara'u yayi kawai ya ja hannun Gwadabe har zuwa ?ofar gidanshi, suka zauna a kututture tare da fuskantar juna.
"Na zaunar da kaine dan gudun kar in yi maka bayani daga tsaye a samu matsala babba.
Amman mu musulmaine dole mu yadda da ?addara duk muninta da kaifinta. Asalima rayuwar gabaki Wayanta jarabawane ranar lahira kuma ranar karSar sakamakone. Gwadabe Iyabo ashe Sata tayi an nemeta sama ko ?asa an rasa. Wallahi Gwadabe da ?yar na kawo kaina Takai da naji mummunan labarinnan"
Gwadabe bai gama jiba numfashinshi ya Wauke Bara'u sai ganin Gwadabe yayi lu ya faWi ?asa wanwar.
A guje ya shiga cikin gida, Sakina na bakin bambu tana Wiban ruwa. Bara'u ya warce moWar cike da ruwa ya danna da gudu.
Sakina ta biyoshi a guje dan ganin meke faruwa. Gwadabe ta gani shanshar a ?asa Bara'u na shafa mishi ruwa a maWigarshi.
Da sauri ta fito babu ko mayafi.
"Subhanallaah meke faruwa Bara'u "
Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke ya buWe idanunshi yana kallon Bara'u da Sakina da suka tusashi a gaba.
Hawaye ke bin kumatunshi ?a?as kamar ?aramin yaro mai shan mamma in yi muku hausar ?an Ghana.
"Alhamdulillah. Taso mu shiga daga ciki kaga mutane har sun soma Wan taruwa kasan ?auye da gulma."
Gwadabe dai babu kalma zungui_zungui yabi Bara'u da Sakina zuwa cikin gidan. A jikin garu ya jingina.
"Bara'u kace fa Iyabo ta Sata sai kace wani ?wallo Wan mutum ace ya Sata. Yaushe kuma a ina kaji?"
A mugun ruWe Gwadabe yake magana yana jijjiga Bara'u. Sakina kuma ta saki salati da tattafa hannaye tare da ri?e haSa.
"Bangane Iyabo ta Sata ba. Bara'u kayi mana bayani"
Kai Gwadabe ya dafe tare da Waga kai sama hawaye sai sharara suke yi ta gefe da gefen fuskarshi.
"Ya Allah. Bara'u zuchiyata fashewa zata yi. Bara'u ka kaini asibiti zan mutu"
Tashin hankali gaga _gaga Bara'u da Sakina suka yi asibitin Takai da Gwadabe. Abu kamar wasa ba sai ?aramar magana ta ke son zama babba ba. Kafin wayewar gari Gwadabe ya fice a hayyacinshi sosai.
A kusan tsaye Bara'u ya kwana a kanshi.
Sai da safe gidansu Shafa suka samu labarin halin da Gwadabe yake ciki.
Afujajan Shafa ta ?araso asibitin ta zo ta samu Gwadabe ya samu bacci Bara'u na zaune a gefen gadon ya zuba tagumi.
"Yaya Bara'u wai me ke damunsh ne haka naga lafiyar Allah muka rabu dashi ya saukeni a gida?"
Ajjiyar zuchiya Bara'u yayi ya dubi Shafa yace.
"Wallahi Shafa iyabo ce ta Sata aka nemeta aka rasa ta ma jima da Satan. Yau na shiga Kano kwatsam na haWu da ?aninta shine yake sanar mini halin da ake ciki, anata cigiyarta a gidan rediyo"
Salati Shafa tayi tayi shiru tace.
"Allah sarki duk inda take Allah yasa tana hannu mai kyau. Oh baiwar Allah kenan ko menene silar Satan sai Allah"
"Ana dai zargin wai kishiyarta ce tayi mata kurciya ta bazama abun damuwar da goyo a bayanta ga mijin nasu baya nan bai san ma me ake ciki ba'
Ashe Gwadabe ya farka sai ji suka yi yace.
"Allah zai saka mata koma wanene yayi silar Satanta.
Na kaWune ainun da wannan labarin na bagatatan."
Bara'u yayi saurin duban Gwadabe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login