Showing 30001 words to 33000 words out of 270738 words

Chapter 11 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

Banza nayi mishi da ?yar ya iya nasarar shawo kaina na faWa mishi abinda ya faru" Shiru yayi kamar ruwa ya cinyeshi yana ri?e da kumatunshi. Amman naga ranshi ya Saci ainun har jijiyoyin goshinshi sun tsaya.
"Yanzu kayan suna ina, ina shi Lekan Win?" Cikin rawar murya nace.
Kayan suna hannun Baban Nazifi, Lekan kuma Yaya Harisu ne ya koreshi." Numfashi ya ja dogo yace.
"Ina zuwa ki goya Kahinde da Taiwo zamu fita."
Gwadabe na kirayi sunanshi da gaggawa, kulawa ma yabawa dan ko juyowa bai ba. Ina zaune a bakin gado da goyo a bayana, sai na soma jiyo maganganu sama sama ina jiyo tashin muryoyi daga tsakar gida. Ni dai ban ko yi yin?urin mi?ewa ba, hayaniyar sai ?ara tsananta take yi, jin kamar ana titirniyar dambe ne yasa na fito da gudu, aikuwa ?afafuna suka harWe na faWi rib cikina da Manana suka daku da ?asa. Take wasu hawayen wahala suka wanke mun fuska. Abunka da mai ?iba sai fa da dabara na mi?e ?afata naji ta nai mun mugun zafi, a haka na daure na fita. Da'u Gwadabe ya dam?a yake ta kai mishi mahangurSa, Yaya Harisu na ri?e da Gwadabe ta baya yana jayeshi, ?an fodiyo na ri?e da Da'u ga Auwal a tsakiya yayi musu iyaka. Baban Nazifi kuwa yana gefe yana sharce hawaye Yaya Haula tana rarrashinshi kamar wanda jaki ya kada shi da ?asa. Su kuma matan gidan suna cure waje guda da yaransu maza da mata.
"Ni zaka duba ka ce matata Sarauniyace, me aka kamata ta sata da za a ci zarafinta ita da Wan uwanta? Kaya kuma ga kuWin rigarki Haula ku bamu kayanmu" Ban san Gwadabe na da zuchiya haka ba sai yau. ?an uwanshi suka rufu a kanshi da zagi da cin zarafina. Baban Nazifi ne ya jefo mana bugun kayan ya sauka a ?irjina tab, ba da ban ina da ?iba ba da sai na faWi. Yaya Haula kuma ta fisge kudin hannun Gwadabe.
"Gobe_gobe ku tattare yanaku _yanaku ku bar mun gidana, tunda ba da uwa da uban Iyabo aka haWa kuWi akasai gidan ba. Ku kuma ko wacce ta koma ciki ta ja ?a?anta"
"Kullo Wakin mu je mu dawo kinji Iyabo?" Ya faWa yana haki. Da Wingishi na koma na kullo Wakin muka fita. Amman fa har muka isa gidanmu babu wanda yace da wani komai. Acanma mun shiga mun samu kab matan gidan da samarin gidan a tsakar gida Iyaa tana ta faman kwakwaso da sababin abinda ya abku. Ai muna shigowa ta dira a wuyan Gwadabe da zagi, har kakan kakanshi sai da ta zaga. Mahaifiyata ta kaWa kanta ta shige ciki, Gwadabe ya mi?o mun buhun kayan na shiga Waki na sameta, na baro Gwadabe na ba iyaa ha?uri amman kamar ?ara ma zigasu yake yi. Ina jiyo sanda Iyaa Kokodeen ta koreshi shima waje. Da ?yar mahaifiyata ta yarda ta karSi kayannan, shima sai ajjiyewa nayi a gefenta. Ina gunjin kuka na nufi hanyar waje. Muryarta na rawa tace.
"Jabu ki yi ma mijinki biyayya. Muddin shi yana ?aunarki kar ki sake wannan rikice_rikicen banbanci ?abila da aketa gwabzawa kice zaki kaso aurenki. Ko beyerabe kika aura ba tsira zaki yi ba. Dan a ?ar?ashin ko wacce igiyar aure akwai ?alubale, in kika ji na wasu naki ba komai bane. Kice ina gaisheshi bamu samu damar gaisawa ba" Kasa amsata nayi na fice ina dingishi, a ?ofar gida na tad da Gwadabe idanunshi sun rine sosai. Haka muka rankaya gida, a daren dai Sarawon baccine ya kwashemu muka wayi gari da labarin Baban Nazifi yace dukkansu zasu tafi Takai akwai meeting da za'a gabatar. Ni dai har Gwadabe yai mun sallama ya fita ina sharar hawaye. Ga ?afata ta aune ta yi him. Tsabar Sacin rai Gwadabe bai ga ?afarba bai san ?afar ta samu rauni ba. Haka na wuni ni dai sukuku ba laka, ?afa fa kafin la'asar ta sake hayewa da ?yar nake takawa. Ina zaune akan kujera ina kirSa sakwara sai ga ?an Takai sun yi sallama. Gwadabe na ?ura ma idanu sai naga har ya faWa. Yana isowa ya cafe taSaryar a ?o?arinshi na ganin ya kore damuwar dake cin ranshi. Ya hau dukan sakwara a turmi, dan da nan ya kammala tsab. Dur?usawar da zaiyi ya taya ni kai filas Win abinci ciki, sai yaga ?afata a kumbure.
"Me ya samu ?afarli ta aune haka, kuma kike zaune kina aiki? A'a taso muje maza_maza" Babu shiri muka fice a gidan.
"?an iska na mamaji" Cewar Baban Nazifi kenan. Ashe targaWe naji a idanun sawuna, mai Wori ya gyara mun muka dawo gida. Bayan sallar isha muna zaune muna cin abinci yke bani labarin yadda akayi a takai.
"Abun babu daWi. Babala dama kinsan sai dai ma ta daWa kwaye mun baya, gashi Goggo Iyatu tana nan mahaifiyar Laila, itama tai ta kunnawa abun wuta. Mun tsaya akan dukkan abinda ya Sace a gidannan kece kika sace kuma ni zan biya. Wallahi nayi iyakar yina dan in fahimtar dasu fur sun?i. Ni dai ro?on da nake yi miki kiyi taka tsantsan kuma ki iya takunki, kisa ma Laila ido sosai, kinsan na faWa miki ?asurgumar Sarauniyace." Kuka na fashe dashi.
Kana nufin a haka zanci gaba da zama tare da kai anai mun kallon Sarauniya, harma duk abinda aka nema aka rasa sai na biya? Gwadabe ha?urina ya ?are ni na...."
"Kul kika bari mala'ilun Allah su yi fishi dake, Allah yayi fishi dake. Iyabo wallahi dukkan wannan abun so akeyi a samu a ukun da da kanmu zamu ji mun ha?ura da junanmu, abinda suke so kenan. Nayi duk iya iyawata in kare ki, abun yafi ?arfinane bazan tsaya ina jayayya da Yaya Hambali ba, domin uba ne, a kafaWunshi muka girma, Balle kuma Babala da goggo Iyatu. Kiyi ha?uri ni zan dinga biyansu duk abinda suka ce an sace musu."
Ya batun korarmu kuma da Baban Nazifi yayi, ba gara mu bar gidan ba, tunda in bana gidan ba mai cewa nayi sata?" Kanshi ya dafe kafin a tausashe yace.
"Babala tace ko bayan rants bata yafe ma duk wanda ya bar gidannan ba. Ashe Yaya Hambali da Yaya Harisu sun sai gidajen su Malam Audi, da gidansu Baturiya, wata mai kamawa ma za'a soma aikin fashe katangun a haWe gidajen. Kinsan bikin Nazifi da Laraba ya ?arato, nima fa duk yau nake jin labari. Nazifi zai zauna a cikin gidannan da matarshi. Itama Laraban a cikin gidannan zata zauna. Ai kinsan Ilum Wakin Goggo mai YaWiya ko? To shi zata aura, Yaya Hambali zai Waukeshi aiki a kasuwa. Ni dai Iyabo abinda nake so dake shine kar ki sake fita tsakar gidannan sai in fita daga gidan zaki yi, ko ban Waki zaki shiga. Su girki, wanke_wanke wanki duk kiyi a Wakinki, kiyi ha?uri damo.."
MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

NAMA YA DAHU...
ROMO ?ANYE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI


Lamba ta tara (9)




"Kinga can wajen tudun?" Gwadabe ya nuna mun da hannunshi. Wani dan tudune karami akayishi a falon kamar wajen cin abici. ( Daining )Amman bashi da girma, a wajen na saka kayan kallona.
"To ki fito da kayan kallon gobe zan siyo miki teburi da dirowar da zaki dinga zuba kayan abinci a ciki. Zaki dinga amfani da risho, ke ko gawayinne in kika kunna a ?ofar Waki daya ruru ki shigo dashi, ki sa labule wajen ya zama miki kicin. Iyabo bana so ki sake fita na kuma na jajjada miki. Kiyi ha?uri wata rana sai labari. Ki daure wallahi ba'a sona haka ke faruwa ba, naso mu bar gidannan muyi nesa da ?an uwa Kuka babu irin wanda banyi ba, washe gari kuwa sai ga Gwadabe da tebur, da durowarshi gajera ta kicin Win ?an gayu. Tare muka jera kayan tukwanena da Wan kayan abinci da nake dasu, har randunana a cikin wajen na jera, Gwadabe ya hau ya kafa mun labele, Laila sai zirga_zirga take yi tsakanin tsakar gida da ciki. Bai fita ba sai da ya ciccika mun randunanan da ruwa tab, kana ya fice kasuwa. Ni kuma na shiga aikace, aikacen gidan. Bani na fita tsakar gida ba sai da na gama komai nawa na fito da ruwa bokiti uku na she?ar a rariya, bokitin dana shake shi da wanki na fita dashi na je ma?ota na shanya. Ina dawowa na yi komawata Wakina.
Haka al'amuran rayuwar su kaci gaba da gudana yau fari gobe tsumma.
A kwana a tashi, gashi yau mun wayi gari jama'ar Takai suna hanyar shigowa Kano. Gidan namu sha?e da matan anguwa suna ta faman taya mu aikace_aikacen biki. Dan Yaya Haula hantsice le?a gidan Kowa, babu gidan da bata shiga, kowa a layinnan ya santa. Gida ya Wau fenti, ga girma da gidan ya ?ara, sakamakon gidaje biyu na jere damu da Yaya Hambali ya siya, aka rushe katangun gidan ya ?ara girman gaske, kuma yasha gyara sosai. ?angaren Amarya Laraba da Ango Nazifi ya sha gyara na musamman. Wajajen la'asar sai ga ?an Takai sun iso Bus biyu su da gayyar yara raSe_raSe, gida ya kacame da hayaniya, amman nifa babu wanda yazo daidai da ?ofar Wakina . Washe gari aka shiga biki ka'in da na'in. Ranar Waurin aure tun duku_ duku muka game jallof Win shinkafa, da tuwon shinkafa, harda masa. Su Gwadabe kuma suka kama hanyar Takai dan acan za'a Waura auren kasancewar duk haWin gidane. Ko akwatin Amaryar Nazifi baa'a kaiba, ance in aka kawota sai kawai a mi?a. Akwatuna masu taya suna nan a Wakin Yaya Haula, ina dai gani matan waje sunata shigowa kallon kaya. Ni ko da nake gidan babu wanda ya neme ni da in zo in ga kaya, nima ban WaWa kaina ba. Bayan azahar maza ?an Waurin aure suka dawo tare da bataliyar maza ?an Takai. Da yamma lis kuma sai ga jerin gwanon tsofaffi da Amarya an tawo da'iya. Harda Sakina aka tawo, suma sun sha ankonsu na Takai. Muma duk mun ci namu ankon na cikin gida, shaddace mai ruwan toka na iyaye, sai wani yaWi haka na ?awayen Amarya dai. A haka taro ya watse, duk da ina kaffa _kaffa sai da Yaya Halima ta ci mun mutunci a cikin mutane, daurewa nayi na shanye dan a ranar ma Takai zasu komai. A dangina babu wanda yai mun kara yazo, Uwani ce dai na matsama bata da yadda zata yi shi yasa tazo.
A kwana a tashi asarar mai rai. Wasa wasa ?an biyu shekararsu guda, har suna dabo, Toye kuma yanata zuwa makaranta. Fitinar gidanmu kuma babu abinda ya ragu sai ?aruwa, dan sau huWu Gwadabe na biyan kayan da aka sata. Na huWun ma har ?ar?ashin kujerata akazo aka saka mun, da suka shigo bincike suka zaro. Nayi imanin Laila ce ta aikata mun hakan ba kowa ba, dan tuggu da munafurci iri iri take haWawa, tsaraicinta da aljanun ?arya fa babu abinda laila ta dena, a wannan shekara guda Win abubbuwa masu dama sun faru. In baku mance ba nace ina yaye ?an biyu zan bar gidan, to maganar tana Wamfare a zuchiyata. Ga zawarawa kullum a cikin sallama da' Laila suke, tare da kawo mata ?walam da ma?ulashe, amman mayyar tana kan bakarta ita sai Gwadabe. Gwadabe ne yaita bani ha?uri nima ganin na kusan yaye in barshi ma baki Waya shi yasa ma ban yi tafiyata ba na ha?ura na zauna, na cire damuwar kowa da komai a raina.
Kamar wasa wata ranar juma'a sai ga Oga Lurwanu shi da karen motar Gwadabe sun ri?o gwadabe ko iya taka ?afarshi bayayi, suka shinfiWe mun shi a doguwar kujera.
"Gashi nan kin ganshi, mota ya shiga, amman wallahi sai zaro shi akayi ?afa ta?i takuwa. Muna kyautata zaton sammu akayi mishi. Dama in dai a raba mutum da kafa ko hannune a harkar tu?i ba kanshi farau ba. Sai ku dage mishi da maganin gargajiya" Hannu na Waura aka ina kuka, shima Gwadabe kukan yake yi yana girgiza mun kai halamar in yi shiru.
"Ki gode ma Allah ma, da ba haWarin mota akasa yayi ba ya ragargaje ba. Dan shima anayi kana tsaka da tu?i sai kaga zaki ko kura, kana Wauke hannunka magana ta ?are. Wasu kuma teku suke gani a gabansu duk sai su dibibice" Ni dai sai mamaki da tsoron sha'anin mutan Duniya duk ya kamani. Nera dubu biyar ya ajjiye mun.
"Mu kam zamu koma Gwadabe Allah ya ?ara sau?i"
Su kai mana sallama suka tafi. Kifewa a jikinshi nayi ina kuka kamar fitar rai.
"Iyabo ki yi ta mun adda'a Allah zai bani lafiya, ta Allah ba dai ta mutum ba. Ni na Wauka wannan jarabawace ubangijina ya jarabceni dashi. Bazan Waura hakkin akan kowa ba Allah yana madakata yana ji da ganin kowa. Ki yi ta mun adda'a. Kafin in amsa shi Yayyen nashi su kayo sallama suka shigo. Baban Nazifi yace.
"Gwadabe haka abun ya faru? Ni ina kasuwa ma shigowata kenan mata suke sanar dani wai an shige da kai a hannu baka tafiya, haWari ne ya afku kome? Koma dai menene Allah ya kyauta gaba. Ke bamu waje ko?"
Ya juyo yana mun kallon tsana, ?an biyu na kwashe dan kar su damu Babansu. Ina daga uwar Waki na kira Iyaa nake sanar mata halin da Gwadabe yake ciki. Halin ko in kula ta nuna, tsaki ma tayi ta kashe wayarta, sai Burodami kokodeen da Burodami Debisi na kira na sanar musu, sai ?awar arziki Uwani. Su Baban Nazifi sun daWe sosai a falon kafin daga bisani suka tafi, ni da yaran muka fito.
"Iyabo inaso zan Waura alwala, gashi ina jin fitsari ma. Zaki iya kuwa?" Murmushi nayi ina hawaye lokaci guda nace.
"Ai ko Waukarkane kacokam zan iya mijina. Nice a ha??u in yi maka duk abinda kake da bu?ata" Mi?ewa nayi na kai yara uwar Waki na kulle, falonma na kulle na tawo da ?aton po mai murfi, cikin dabara na zamo Gwadabe izuwa kan po Winnan. Yayi fitsari na mai tsarki, na sake mayar dashi kan kujera. Daga ni har shi sai muka fashe da kuka na faWa jikinshi.
Allah kenan mai yin yadda yake so da bayinshi. Mutum ya fita da ?afafuwanshi amman yanzu jibeshi a kwance, abunda yafi ?arfi yanzu ya fi ?arfinshi. Su Baban Nazifi daya kamata ace su zasu mai duk wannan amman kowa ya tafi ya barmu.
Gwadabe kayi ha?uri kuka ba namu bane fa. Akwai Allah shi zai yi mana sakayya. Ka rungumi ?addararks sai Allah ya kawo maka Wauki. Zaka warke bi izinillahi rabbi"
"Iyabo ki duba dangina jinina yanda suka nuna halin ko in kula da abunda ya sameni, babu wanda ya tambayeni ko ina jin wata lalura. Yanzu ko Da'u da ba sai ya zauna ya kula dani ba?"...
A'a Gwadabe kar ka Waura musu nauyin da ba nasu ba. Ni ya kamaci da in jinyata maka. Karma ka sake tada wannan zancan. Ga bawo kayi alwala." Shi da kanshi yayi alwala ni kuma na wanke mishi ?afafuwanshi.
Gwadabe ka daure in kai ka kan gado kaji, sai kayi zamanka acan. Yanzu nan anjima kaWan Laila zata tashi kwanciya."
"Ba zaki iya kaini ba Iyabo, ki je ki kira Da'u ko Nazifi Wayansu yazo ya kaini, ko du su biyun." Bana so in mishi musu da To" Na amsa mishi, na fita da po Win da yayi fitsari na zubar, sai da na mayar ?ar?ashin gado sannan na je kiran Nazifi da Da'u tare da sanar dasu sa?on dake tafe dani. Abun mamaki ko da suka kinkimeshi su biyun dukkansu sai mitar yayi nauyi suka dinga yi, ?afarshi Waya ma basu kama ba sai janta su kai kii. Ni ko ina dur?ushe ina hawaye har suka fice ina kuka. A wajen su Yaya Haula suka shigo suka sameni idanuna sun ?i luSu_luSu dasu.
"Ohh ni ?arnan mutum ba a bakin komai yake ba, yau_ yau Winnan Gwadabe ya zama musaki sai an kwantar sai an tayar. Sannu Iyabo kinji sannu" Kalmar musaki data faWa ya dafani sosai.
"Kaimu muje mu yi mishi sannu ko. Laila sai ki kwashe kayanki ki ko Wakin su Halima da ?auwama sai ki koma kinga ?an zuwa dubiya zasuita sunturi kuma dole falo za'a dinga fito dashi" Ni dai gaba nayi suka biyoni. Suka gama gaisheshi suka fita. Ni kuma ina gefenshi ina tofa mishi adda'a a ?afar tashi, shi kuma yana kallon silin yayi wani irin sanyi"
"Iyabo kinga irin ri?on wula?ancin da Da'u su kai mun? Kinga yatsan ?afata ya fashe. Daga kwanciya lalura yau _yau harna soma fuskantar wula?anci, sai kace ba ciki Waya muke ba. Wannan ?iyayyar dame tayi kama, ki duba fa yanda su Yaya Hambali suka zo suka dubani wallahi babu damuwar komai a fuskokinsu, sai cewa su kai nima karambanine yasa na shiga sana'ar da bani da ilimi a kanta. Wai sana'ar hatsari gareta." Hawayene suka gangaro daga idanunshi izuwa fuskarshi. Rarrashinshi na dinga yi, a ?o?arina na ganin na faranta mishi rai, wala Allah ya samu sassauci. Ruwan Wumi na zuba a bawon na tsoma tsumma na Wan gargasa mishi yatsan nashi da yake jini. Ya samu yayi sallah, na bashi abinci a baki da kaina, ina bashi ina sake yi mishi nasihu masu ratsa jiki, akan ya gode Allah ma da ba hatsari yayi yaji raunuka masu yawa ba, da izinin Allah muddin muka dage da adda'a koma sammunne Allah zai bamu nasara, amman zuwa gobe zamu je asibiti.
"Babu ko ficika a jikina Iyabo, kuma kinga asibiti sai da kuWi Iyabo"
Haba Gwadabe, zan siyar da atampopina in samu Wan kuWin da zamu ri?e a hannunmu, mu gode ma Allah muna da abinda zamu Waga mu siyar ma. Ina zuwa da zafi_zafi akan daki ?arfe. A zabure na mi?e na shiga zaro atamopin sunan ?an biyu, kala goma na fitar na zuba a bako.
Gwadabe bari in je shagon me sai da atampopinnan ta bakin titi yarenmun nan, bazan jima ba, ga yara a falo" Ban tsaya jin abinda zaice ba na fice, sai dai kunsan mutane in suka ganka cikin matsuwa ka fitar da abu zaka siyar, sai su dinga yi maka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login