Showing 72001 words to 75000 words out of 270738 words

Chapter 25 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

amana.
Da yamma lis yau su Gwadabe suka shigo gidan, sun shawo gajiya sosai. Harda ?ar ledar kayan kwalliya a hannun Gwadabe. ?arayinsu suka wuce dai kamar kullum, sai da su kai wanka suka sake kayan jikinsu. Yayi daidai da lokacin Sallah sai suka wuce kofar gida dan gabatar da sallah.
Ta Sangaren Hadiza kuma tayi kwalliyarta me ?ayatarwa sai ?amshi take faman zabgawa, ga abinci ta ajjiye da kwanukan zubawa, shigowar su Gwadabe kawai take jira. Baba Fhatsima kuma tana zaune daga gefe tana jin wani shiri da ake gabatarwa a gidan rediyo hankalinta yana wajen shirin. Amman idanunta na kan Hadiza wacce tun Wazu sai gyare_gyaren gashin kanta data bazoshi ya sauka kafaWarta take yi. Irin wannan ganWoki ko a aurenta na fari ma bata yishi ba, duk da shima wancan auren Malam ne ya haWashi almajirinshi ne mijin.
"Hadiza sai nake ganin kamar kin zafafa soyayyar da kike ma Gwadabe. Kibi a hankali kinsan halin maza da karya ma mace zuchiya. ?ila ma bake kaWai bace a ranshi" ?ur ta zuba mata idanu tana karantar yanayinta, dama ta soko zancanne taji irin amsar da zata bata. Dan tana son auna kishinta da Malam yake ta ikirarin ita ta biyo"
?asa tayi da kanta, lokaci guda sai ta jagule har idanunta ya kawo ruwan hawaye.
"Baba abinda ya faru a baya kuskurene wanda bana mafarkin ya sake faruwa dani a gaba. Nasan an yi mun laifi, amman nima na nuna rashin hakurina ?arara. Wallahi a lokacin da Tsalha ya dinga nuna mun ni ba cikakkiyar mace bace, sai da yayi amarya ya gane kanshi. Banyi tunanin a daren zan rayu ba, wani abune yake dannemun harshena izuwa mo?oshina. Baba ina da kishi mai yawa, anata cewa wai ke na biyo. Ni kuma in sha Allah zanyi koyi da salon kishinki, da dabarun kissarki ta hanyar gina babban matsayi a zuchiyar Gwadabe. Ta yadda ko mata Wari zai auro bai isa ya haWemu a matsayin abu guda ba" Kuka ta fashe dashi mai ciwo.
MRS BUKHARI



Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Jfn7qq4nyMm0prVhnhfVZK

*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Jfn7qq4nyMm0prVhnhfVZK




*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*




NAMA YA DAHU...
ROMO ?ANYE
LITTAFI NA BIYU
4

Baba Fhatsima ta dubeta a tsanake tace.
"Shikenan ni da kaina zan kwatanta miki yada zaki zauna daram ki wuce wula?anci a zuchiyar Wa namiji. Hadiza a lokacin da Malam yace zai ?aro aure sai da na kwanta jinya. Amman sabida kirsa irin tamu ta mata ni na haWa akwatin da Malam ya kaima Asshi. KuWin dana samu a hannun malam bana wasa bane. Zuchiya kullum ciwo da zafi suke yi mun Hadiza. Wallahi inna kalli Malam sai inji kamar in Wura mishi zagi. Amman wallahi ko Sacin rai baya iya ganewa a fuskata. Horon da nayi mishi na ?auracema shinfiWarshine, tunda ya raina iyawata, sai da nasa da kanshi ya gane mahimmancina da kuma banbancina. Duk da ina fishi dashi, saina dukufa shan magunguna ingantattu, musamman tukuWi da gumbar matan Kanuri da tsuminsu, da shayin su na musamman. Na dinga gyaran kaina dan sake kankaro mutuncin kaina. Ni kishina bana ayi zagi ko bankaura bane. Da duk tsufana Malam har gobe yana mararina Hadiza.
Sallamar su Gwadabe ce ta katse wannan tattaunawa wanda nasan ba Hadiza kaWai ke karuwa da'ita ba, harda masu karatu. Saurin share hawayenta tayi, wanda karab a idanun Gwadabe.
"Baba yinwa" Cewar Auwala wanda baya jurar yinwa. Dariya duk aka saka mishi. Baba Fhatsima tace.
"Ai kai wacce zata aureka ba zaka barta ta huta da Waura sanwa ba" Saida ya cusa tuwo loma babba a bakinshi, tun kafin Mammada ya gama zuba musu, kana yace.
"Tabb ai ni tun da jimawa tasan Yaya nake. Kullum naje saita kawo mun shayi da cukui, wataran harda abinci fa." Mammada yace.
"Bayan uban abincin da kake take cikinka dashi kafin ka tafi? Shi yasa cikinka kullum yake ?ara girma. Baba yau daya zarme rijiyar ha?on zinariya da ?yar aka zaroshi tsabar ?iba fa" Duka Auwala ya kai mishi, yai maza ya matsa kusa da Gwadabe wanda shi kuma hankalinshi na kan gimbiya Hadiza da yaga tana cikin rashin walwala. Baba Fhatsima tayi Dariya tace.
"Duk ai ya kusa karewa gini kam gobe za'a soma an kawo bulo da yashi, an yi ginshi?i. Aikin ba wani daWewa zaiyi ba tunda an riga da an tanaji kudin aikin. Duk kuyi aurenku nima na huta" Gwadabe yace.
"Ai Baba kila fa Auwala ya dinga zamowa cin abinci Wakinki, baya zage ya kwashi girki a gaban Amarya haka ba" haka dai sukaita raha a tsakaninsu kamar yadda suka saba a koda yaushe. Ana cikin haka Yaya Tasi'u shima ya shigo akayi hirar dashi. Kiran sallar isha ne ya fasa taron. Da Gwadabe ya tashi fita sai ya ajjiye ledar kayan kwalliyar da ya siyo ma Hadiza a gefen ?afarta ya fita.
"Tashi kiyi Sallah kafin Gwadabe ya kiraki zance, dan zancanku ba Waga ?afa. Yaran zamani kome kuke cewa in kunje wajen zancen oho. Zance ai sai su Ine yanzu dai duk ya ?are." Hadiza tayi murmushi tace.
"Gobe ma mu kayi da Anty Badi'a zamu je gidajensu mu ganosu, tun bayan biki mu ta Sangarenmu babu wanda yaje. Shekaran jiya Sauma'iyya suka je gidan Hafsatu."
"Daga gidan mijinta taje, ke yaya akayi kika san taje? Tsegumi" Dariya Hadiza tayi tace.
"Baba asshi ce naji tana faWama Amaryar Malam. Wai Hafsatu ta aiko mata da kuWi harda soyayyun zabbi" Harara Baba Fhatsima ta doka ma Hadiza ba shiri ta tada kabbarar sallah. Dan babu abinda Baba Fhatsima ta tsana irin gutsiri tsoma" Hadiza tana kan sallayar bata tashi ba Gwadabe ya aiki yaron Amaryar Malam yayi kiranta. Sai da ta kuma gyare_gyaren kwalliyarta kafin ta fita. Baba Fhatsima tana jimantama Hadiza ranar da zata ji labarin bada ita kaWai Gwadabe yake soyayya ba, kuma akwai yiwuwar ba ma ita kaWai zai aura ba. Ko da ba'a hade bikin ba, tasan babu wani nisa a tsakani.
Fitowa tayi tsakar gidan tana busa ?amshi. Amaryar Malam da taci kwalliyarta na zuwa turaka ta bushe da dariya, dama can basa shiri sam da Hadiza. Dan bama su wuce sa'anni ba. Ko kallonsu batayi ba. Harfa ta sha kwanar Sarayin su Gwadabe ta jiyo Baba Asshi na cewa da Suwaiba.
"Sabida tsabar tayi bandarine fa Malam ya tafi ya Wauko Wan ?anwarshi dan ya haWasu. ?anwar tashi ma da bata da mutunci. Ni dai na gode Allah in Fhatsima ta fini da soyayyar miji, da Wa mai arziki. Bata fini a surukai ba. Dan masu arzikin gaske ?a?ana suke aure. Itako Hadiza gidan da za'a sakata ubanta nema ya bayar" karab a kunnen Hadiza, karab kuma a kunnen Baba Fhatsima. Dukkansu kai suka girgiza kawai. Hadiza tayi shigewarta ciki. A bakin dakalin ?ofar Wakinsu yake zaune. Ga hasken lantarki tanwar ya haske ko'ina. Gardawan malam su biyar suna wajen suna wankin suturunsu, sai Sabitu dake tsaye a ?ofar Wakinsu kawai dan babu dai Abinda yake yi. Kwana biyunanne ya tsiri yin hakan a daidai lokacin da Gwadabe zai fito ya zauna domun ganawa da Hadiza. Tun daga nesa Gwadabe yake ?arema Hadiza kallo. Zani daya gani Waure a jikinta sai yake ganin kamar iyabo ce ke tawowa, dan Iyabo ta ?ware wajen iya Waurin zani sosai, takanyi matu?ar kyau da zani, ?ibarta na daga cikin abinda ke sa ruhinshi ke fisgarshi akan son Iyabo. Isowar Hadiza ce tasa ya dawo hayyacinshi. Zama tayi gefenshi sosai.
"Barkanka da wannan lokacin angon Hadiza mujin mace Waya tilo." Murmushi yayi mata kawai, a kullum in ta kirashi da mijin mace Waya tilo sai yaji faWuwar gaba, haka ?anwar tamu take yawan ce mishi.
"Mijina ni ni kaWai. Babu wata mace data isa ta rabeka" Da sunyi mishi irin furucinnan sai yaji hankalinshi ya tashi a madadin ya samu nutsuwar kalaminsu. Anya bai cutar da zukatan ?an matan ba kuwa, lokaci baiyi da zai bayyana musu gaskiya ba kuwa? To wai in ya zayyana musu gaskiya du suka gujeshi ya zaiyi da kunyar waWanda yake ganin darajarsu a jikin ?an matan? In kuma suka ritsashi suka ce sai dai ya zaSi Waya, Yaya wacce aka ce tayi ha?uri zata yi? Ha?i?a yayi kuskure mafi girma da rinjaye, awannan tunanin kamata yayi tun farko zaiyi shi, ba yanzu da wankin hula ya riga ya kaishi dare ba."
"Wai tunanin me kake yi ne Yaya tun Wazu inata magana fa, bakace komai ba" Ya tsinkayi shagwaSaSSiyar Muryar Hadiza, wanda tasa saida tsigar jikinshi ta tashi, dan wannan yana daga cikin sabon salon da take son fitowa dashi dan mallakar zuchiyar Gwadabe.
"Akwai muhimmiyar maganar da nake son mu yi ni dake. Hadiza banaso ki fassarani da ko wacce iriyar mummunar fassara, ina cikin tsaka mai wuyar fita ne, abinda yasa abinda ya faru ya farun kenan." Shiru tayi tana kallonshi da ?ananun idanunta waWanda gashi sukaima rumfa. Bayan ta ja numfashi na da?i?a sai tace.
"Ina saurarenka, zanyi maka shari'ar gaskiya da gaskiya. FaWamun matsalar dan tuni fuskarka ta nuna matsala zaka faWa mun" Shiru yayi yana shafan sumarshi kanshi.
"Hadiza ba da ke kaWai nake soyayya ba. Akwai ?anwar abokina Tamu da ya bani tun kafin in tawo Nijer " Darara dam_dam_dam gabanta yai mummunan tsinkewar daya tunkudo ruwan hawaye nan take suka soma shatata a idanunta. Duk da haka tace.
"Dan Allah kace dani wasane, kar kayi amfani da kishin da akace maka shi yai sanadiyyar mutuwan aurena ya zamema logo. Na ro?eka karka yaudari zuchiyar data saba da rayuwa da sonka." Take hankalin Gwadabe ya kai ?ololuwar tashi, dan bai taSa tunanin Hadiza zata Wauki wannan lamarin a yanda ta Wauka yanzu ba. Da ?yar ya samu kuzarin ce Mata.
"Wallahi da gaske nake yi Hadiza. Kafin in tawo nan na riga dana amshi soyayyarta. To kuma da nazo nan sai Baba Magaji yace in zaSi mace a cikin ?a?anshi in aura, amman sai yace yafi mun sha'awarki"
"Kenan ba sona kake yi ba, Malam kai ma biyayya? Shikenan ni na hakura kaje ka aureta" Tana gama faWar haka ta mike fu ta bar barayin. Yayi yin?urin tareta sai Auwala da shigowarshi barayin kenan ta gefenshi ma Hadiza ta raba ya dakatar da Gwadabe bisa dole ya tsaya."
"Koma me ya haWaku kyaleta ta huce, su mata a cikin irin wannan halin baka iyawa dasu sam." Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke tare da lumshe idanunshi.
"Auwala laifi nayi mata. Tana da dalilin yin fishi dani. Laifinane, dan Allah ka bita ka bata baki a madadina"
"To wannan ma dabarace. Kai jeka bari in shawo maka kanta ka koma ciki ka jirani."
Gwadabe na shiga Waki kiran Shafa na shigowa wayarshi. Jiki a mace ya Waga wayar, itama yayi mata duk bayanin da yaima Hadiza. ?it ta kashe wayarta, ko da ya kuma kira sai yaji a kashe ma wayar baki Waya. Dafe kanshi yayi bakinshi na Waci, damuwa duk ta haWu ta dameshi.

Hadiza.
Da sauri ta shiga Wakinsu har tana cin karo da Ine wacce suke shirin fita ita da mijinta sun kawo ma Baba Fhatsima ziyara irin ta godiya da angwaye suke yi.
Ganin mijin ?anwarta yasa tai saurin share hawayen dake bin gefen fuskarta.
"Ango ka sha ?amshi kune a tafe da daddarennan? Mu da muke shirin kawo muku ziyara"
A ladabce ya gaishe da Hadiza yana yi yana sosa kanshi.
"In kin gama kya same ni a waje ni kam" Yace da Ine wanda hankalinta yake kan Hadiza.
"Yaya Hadiza nifa fishi nake yi wallahi. Tunda kuka kaini ba wanda ya sake le?oni ma" Ta faWa a karaye yayinda Hadiza take kallonta da halamar tuhuma. Ganin hawaye na neman Sallewa a idanun ?anwar tata ne ya tabbbatar mata tana cikin damuwa, ko kuma kewar gida."
"Ki sha kuruminki dama gobe zamu je gidanki ni da Anty Badi'a. Yanzu dai kije ki samu mijinki karki barshi yaita jira" Ine tace.
"Bamu shiga cikin gidanba ma, yanzu dai zamu zazzagaya, amman munje Sarayin su Yaya Tasi'u." Fitarta shigowar Auwala yana kwaWama Hadiza dake shirin zama kira.
Shigowa yayi ranshi a matu?ar Sace.
"Ke meye ya haWaki da Gwadabe, da har yake kiranki kina ?in tsaiwa? Ki sani wanki ne Gwadabe, kuma mahaifiyarshi ?auna take ga Malam." Hadiza najin wannan sababi na Auwala sai ta saki rushin kuka tana faWin
"Ni wallahi na fasa auren. Yaje can ya auri ?anwar abokinshi. Ai ba sona yake yi ba. Malam ne ya cusani wajenshi" Duka Auwala ya kawo mata. Baba Fhatsima dake zaune tana kallonsu tace.
"Bita a hankali Auwala. Zo zauna inji meke faruwa haka uhm?" Zama Auwala yayi a ?asa, yana dokama Hafiza harara.
"Ki buWe baki kiyi mun bayani Hadiza. Menene ya haWaki da yaiyen naki?" Hadiza ta kwashe yanda Gwadabe ya faWa mata ta sanar ma Baba Fhatsima. Tsaki dogo Auwala ya ja yace.
"Ni nama Wauka wani muhimmin abune yanda naga Gwadabe duk ya damu. To sai me dan ba da ke kaWai yake soyayya ba, dama cewa akayi dan ke aka halicci Gwadabe ke ke kaWai?
Baba kinji fa abinda take cewa, wannan ba?in kishin nata ne yasa ta tsallake yaranta ta dawo gida. Tana da aiki ja matsawar irin wannan ?azamin kishin bai fita a ranta ba." Shiru Baba Fhatsima tayi, tana sauraren SaSatun Auwala, da sautin kukan Hadiza. Ajjiyar zuchiya ta sauke kana tace.
"Hadiza kina nufin ba zaki taSa zama da kishiya ba ko me kike nufi? Bar ganin ina goyon bayanki Hadiza, ai in dai wai ke bazaki zauna da kishiya bane, to ya fiye miki sau?i ki ?are rayuwarki a gidan mahaifinki. Dani da Malam mun san bake kaWai Gwadabe yake nema ba, kuma a haka muka ji yafi miki ki aureshi. Dan Gwadabe yarone mai hankali da kunya. Ke dai kiyi fatan kasancewa uwar gida a gidanshi kawai. Kai Auwala tashi yi tafiyarka, ka kuma cema Gwadabe ya kwantar da hankalinshi Hadiza mu muka bashi ita, duk duniya in banda ?addara babu wanda ya isa soke batun aurennan. " Tashi Auwala yayi ya dubi Hadiza yace.
"Yara basu ajjiye komai ba sai sakarci. Ni zan so ma Malam ya soma aura mishi waccan Win kafin ita. Gashi ita ?ar birni wayayya da'ita, kuma hankalinshi take janyewa sosai. Maza ki tsaya kallon ruwa kwaWo yayi miki ?afa" Baba Fhatsima ta daki ?afafun Auwala dake son tunzura Hadiza.
"Ja'irin yaro, fice ka bamu waje" Ta faWa cikin sigar wasa, fita yayi yana sake kambaba yanda budurwar Gwadabe take kulawa dashi a waya. Kuma duk dan ya tunzura zuchiyar Hadiza ne. Ai kuwa yaci nasara dan take zazzaSi me zafi ya luluSeta, sai hawaye idanunta yake fitarwa" Harara Baba Fhatsima ta doka mata tare da cewa.
"Shashasha maza dai ya gane kishi shine logonki kiga in baki faWi ?asa warwas ba. Ba'a ?arin aure ni Malam yayi mun har kishiyoyi uku? Da banyi ha?uri ba ke kina ganin zan kai haka ne? Ai mace a gidan aure da jarumta akeson ganinta Hadiza. Dan Gwadabe ba ke kaWai yake nema ba, ba hujja bace na cewa ke kin fasa aurenshi ba. Ai kina gani a cikin gidannan dama dariya suke yi ta mana. Ko baki ji Abinda suke cewa bane Wazu da zaki je wajen Gwadaben? Ai kinji sarai. Maza dai ki ma kan ki shaidar da babu me iya goge miki ita na zafin kishi. Ni kinga tafiyata Malam na son ganinmu dukka a turakarshi, Allah dai yasa lafiya. Dan malam bai fiye haWe kan matanshi ya tattauna dasu baki Waya ba, yafi gane ya tattauna da kowacce ranar girkinta" Tana gama faWar haka ta sa kai ta fice ta bar Hadiza da jinyar zuchiya. Yayinda maganganun Auwala suka shiga yi mata amsa kuuwa.
"Ni inata wahalar da kaina na son ganin na burgeshi. Sai gashi ashe wata a waya kawai take jaye mai hankalinshi. Ni Hadiza zan iya zaman kishi a karo na biyu kuwa? Wallahi nasan mata ?an uwana da yawa ba zasui mun uziri ba
Wasu ma zagina zasu yi. Amman Ubangijin da yayi ni, ya yiku. Shi ya banbanta zuchiyiyoyinmu. Wata abinda tata zuchiyar ta Wauke, wata in akace sai zuchiyarta ta Wauke wallahi mutuwa za tayi. Ni Hadiza macece mai mugun kishi mai zafi, nifa ko baiwace na fi son ace tawace ni kaWai babu mai irinta. Kishi ni shine raunina nasan ko wacce mace da irin rauninta."


Baba Fhatsima"
Lallai hausawa sun yi gaskiya da suke cewa magaji mafiyi. Ita kanta Baba Fhatsima tana mamakin yanda Hadiza ta xama kwafinta a kishi. Komansu iri Waya ne ta Sangaren kishi babu inda ta barota saima finta da tayi. Ita kanta da ba dan ta kai zuchiyarta nesa ba, da kuma tunanin goben yaranta ba, da a lokacin da malam zai ?aro Aure da tuni ta bar auren kwata_kwata. Har gobe zuchiyata tana azabtuwa ainun da zaman kishin da Malam ya haWata yi da sauran matanshi. Duk da tasan cewar ita da Tasi'u sune fitulun dake haska gidan malam, hakan bai hanata kishi ba. Iya rigima Malam yake kiranta a duk sanda ta murWa kambun kishinta ta juya mishi baya.
Ajjiyar zuchiya ta sauke a daidai shigarta Sarayin da turakar Malam take. A zuchiyarta take ro?ama Hadiza Allah ya bata ha?uri da juriya. ?ayar zuchiyar tata tana cike da tausayin Hadiza a bisa dakon nauyin kishi da zata Wauka na iya tsawon rayuwar duniyarta.
Da sallama ta shiga falon na malam, yana zaune a kujera mai cin mutum uku Amaryar Malam tana gefenshi tana kiciniyar cire mishi babbar rigarshi. Baba Fhatsima ta haWiye wani yawu mai kauri, tare da yin wuf ta yi ?asa da idandunanta. Kunya da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login