Showing 33001 words to 36000 words out of 270738 words

Chapter 12 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

tayin wula?anci. Dubu goma sha biyar ta taya atampopinnan kuma manyan atampopi harda Holland, da ?yar muka ?ar?are a sha bakwai da Wari biyar. A cikin daren yau daga ni har Gwadabe kusan kwana mu kai muna Sallah muna adda'a, wallahi har akai sallar asuba bama ko jin digon bacci sai jarababben ciwon kai daya jarabeni. Ana fitowa Sallah na jiyo sallamar maza a ?ofar Wakinmu. Baban Nazifi ne yake sanar dani dattawan unguwane suka zo duba Gwadabe. Hijabi nasa kafin nace su shigo. Gaggaisawa mu ka yi dasu, tare da yi mun jajen abinda ya faru, daga bisani kuma suka shiga ciki dubo shi. Ni dai jigum nayi a wajen na rasa me ke yi mun daWi, a wajen suka fito suka taddani, su kai mun sallama suka fita. Ruwan wanka na juyo a bokiti na shiga da sallamata. Na samu Gwadabe yayi jigum yanata aikin tunani, na sani ban isa na hanashi tunani ba, domin jiya uwar haka da lafiyarshi ras ya fita.
Gwadabe bari in Wan goggoge maka jikinka da tawul sai ka yi asuwaki mu samu mu je asibitin ko?" Sai da ya sauke nannauyar ajjiyar zuchiya yace.
"Na yi ma Yaya Hambali magana kan batun asibiti da muke son zuwa. Bai goyi bayan hakan ba, yace ciwon yafi kama da sammu, tunda babu inda yake yi mun ciwo, sai nauyi da ?afafuna su ka yi, kuma Oga lurwanu ma yace sammu ne"
Hakane Gwadabe, amman zuwa asibitin ai yana da amfani, in muka je suka auna basu ga komai ba shikenan sai a yi na gargajiyan
"E haka na ce mishi nimaa. Ya dai ce Da'u zai tsaya mu tafi asibitin tare." Goggoge mishi jikinshi nayi tas, na saka shi a po ya rage mararshi, yayi asuwakin zamani, kana na bashi tea da burodi, da ?yar yaci burodi yanka Waya, ni ko iyaka shayin kawai na kurSa, mu ka jiyo sallamar Uwani.
Mi?ewa nayi na fita falon ina sharar hawaye, ita kanta uwanin kuka take ta faman yi. Muna cikin haka Da'u da Nazifi suka shigo, basu kula mu ba, ciki suka wuce abinsu. Ni kuma na sallami Toye ya tafi makaranta. Fitowa dashi suka yi, Da'u sai tsaki yake yi. Mu dai bayansu muka bi, ashe sun kira tasi tana tsaye a ?ofar gida. Asibitin Murtala muka wuce, ganin halin da muke ciki sai wani likita yace bari ya bamu gado ayi duk binciken daya dace a tsanake zaifi. Hakan kuwa akayi aka bamu gado a Ward Win maza, Da'u da Nazifi kuma jin an ri?e mu a asibiti sai suka yi tafiyarsu. Hawaye kawai nake sharewa, likita yace mu zauna daga waje.
"Yanzu tsabaragen ?iyayya yana ciwon ma ba zasu taimaka mishi ba, a lokacin da yafi bu?atar taimakonsu ba. Tafiya fa suka yi Iyabo" Takaici da damuwa duk suka taru su kai mun yawa sosai. Muna zaune aka fito da Gwadabe a keken da ake tu?a guragu zasu tafi ayo mishi hoto.
"Baiwar Allah ya kamata ace akwai wani namiji da zai tsaya tare da marar lafiyan ba ke mace ba, kinga da su zasu sashi a keke, kuma su tu?ashi zuwa Wakin hoto. " Nurse Win daya tu?o Gwadabe ne ke magana. Gwadabe na kalla, shima ni yake kallo ya dafe kanshi da hannun dama, idanuwanshi tamkar garwashin wuta.
To mun gode, suna hanya masu kula dashi Win." Na faWa mishi haka, kafin ya mi?o mun wata takadda.
"Ki je wancan tagar ki biya kuWin hoto, in mun fito sai ki bari in mun dawo ki bani" KarSa nayi jikina na rawa, su kuma suka wuce.
Kuka na fashe dashi babu ?a??autawa, Taiwo da Kahinde suna ganin ina kuka suma sai suka soma kukan.
"Iyabo kije ki dawo, wannan kukan ya isa haka kinga ga yara suma sun soma. Jakata na kinkima na je na biya kuWin hoto na dawo. A ta?aice sai da muka wuni zumbur babu wanda yazo daga dangina ko na Gwadabe, Hafizu mijin Uwani ne ya kawo mana abincin da muka ci, da naga magriba na shirin yi na dubi Gwadabe nace.
"Inaso zanje gida in dafo ruwan zafi, in tawo da tabarma."
A'a su Babala suna hanyar zuwa. ?azu da likita ya kiraki Yaya Hambali ya kira ni a waya" Baima gama bayanin ba sai gasu sun iso dukkansu, harda Yaya Haula tana ri?e da filas na ruwan zafi da kular abinci. Da sauri na tashi a kujera na ba Babala waje ta zauna. Abu na farko daya fito daga bakinta shine.
"Ba ga irinta ba, akan son gwanance mace kaje ka kai kan ka mahallaka. Waya sani ma ko daga danginta ne aka bugo maka wani agumun. Duk da sammu a tsakanin direbobi abune mai dogon tarihin gaske muma munsan tarihin. Gwadabe bazan yi maka baki ba, amman kaji na rantse maka da girman wanda yayi ni yayi ka buwayi gagara misali. Kana tashi zaka sallami wannan matsiyaciyar ka auri Laila, in ba haka ba sai in tsine maka ka bi duniya uban kowa ya rasa ka. Banga riba a aurenta ba sai ci baya da koma baya da rayuwarka tayi.
Ke kuma na dawo kan ki, ki zauna da shirinki, Allah na tasan kafaWarshi ?arshen zamanki kenan dashi, ya'isa haka, inason yarona ya dawo yanda yake. Kin shigo cikin zuriyarmu kin tarwatsa mun kan yara." Da kuka ta?arashe zancen, yaranta na bata baki kan ta dena kuka. Baban Nazifi ya Waura da cewa.
"Ya zame mishi dole ya rabu da'ita matsawar mune danginshi. In kuma zai sake iyaye da ?an uwane sai mu gani. Sabida wannan ba?ar kadarar matar tashi marar asali yasa na kasa tallafama Gwadabe Babala, amman a baya wanne irin so ne banyi mishi ba." Wannan yace wannan, wannan yace wancan kowa sai da ya tofa albarkacin bakinshi. Mu dai mun yi shiru kamar ruwa ya cinyemu.
"Babala kima Allah kar ki zama silar rabani da Iyabo, son gaskiya take yi mun, bazan iya samun macen da zata soni rabin nata ba. Iyakar zamana da'ita babu abunda ta taSa yi mun na assha." Mi?ewa Babala tayi tace.
"To gaka ga Iyabo. Ta maye maka gurbina dana ?an uwanka da baka da tamkarsu. Ta zauna tayi jinyarka, ni kuma babu ni babu kai. A cikinku duk wanda ya tsaya ya kula dashi ban yafe mishi ba, ko ya cire dukiyarshi ya ba Gwadabe. Haula Wauki abincin da kika kawo mu koma dashi.
Da gudu nasha gaban Babala ina haki nace.
Babala kiyi ha?uri ni nayi miki al?awarin Gwadabe na warkewa a ranar zan bar gidanshi rabuwa irinta har abada. Bazan iya tafiya in barshi a wannan halin bane, ko babu komai uban ?a?anane, kuma a zamanmu bai taSa cusgunamun ba. Nima dashi da aurenshi ya fice mun a raina, wallahi ko baki ce ba ya zama dole in rabu da Gwadabe dan ba shi bane autan maza ba, kuma ba mutuwa zanyi ba. Amman fishinki masifa ne, yana bu?atarku yaya Harisu, Babala Gwadabe na bu?atar adda'arki" Duk wannan maganar cikin dimuwa nake yinta. Majinyatan dake kwance, da masu jinyarsu kab hankulansu a kanmu yake. Tsawa Babala ta daka mun.
"Gafara dallah. Ke baki da uwa dama da sai in ce ki je kisa ta mai adda'ar mana. Tunda akan ki wannan ciwon ya same shi, ke zaki yi mishi jinya dan ubanki"
Fuu suka fita suka barni. Bansan sanda na dur?usa a ?asan Wakin ina salati ba, Allah nake ambato a lokacin wani irin duhu ne ke mamaye mun idanuna. Uwani ce ta Waga ni.
"Tashi Iyabo meye haka kike kuka kamar ?aramar yarinya, Wakinnan kab ke suke kallo. Rabuwa da Gwadabe shi ya fiye miki." Jaye ni tayi ta zo ta zaunar dani a kujera. Gwadabe yana kwance idanunshi a buWe suke amman yayi zurfi a cikin tunani hankalinshi baya tare damu.
"Bara in fita bakin asibiti in siyo muku ko da tuwo ne. Zan yi ma Hafizu filashin in ya kirani zan sa ya kawo ruwan zafi." Bani da niyyar bata amsa, itama bata bu?aci amsar tawa ba ta fice. ?an biyu suna ?asa na shinfiWa musu Wankwalina suna bacci. Har Uwani taje ta dawo ni da Gwadabe babu wanda ya tanka Wan uwanshi. Tayi yin duniya muci abinci mun ?i yarda, damuwar da take gabanmu ta wuci a tsaya ana saka lomar tuwo a baki, ni in banda Waci babu abunda bakina yake yi. Mijin Uwani ma yazo yayi ro?on duniya kan mu ci abinci, ni ko magana na kasa, Gwadabe ne ma yake iya cewa a ?oshe yake.
"Iyabo ki taso mu je gidana, in yaso Hafizu zai kwana gobe mu ma dawo"
"Ku barta tare dani, ina bu?atarta a kusa dani, damuwar zata yi mun yawa" Cewar Gwadabe, sai lokacin hawaye suka surnano da idanun Gwadabe wasu sirara. Uwani ta tattare yaran su kai mana sallama suka tafi. Da ?yar ma'aikatan kiwon lafiya suka barni zan yi jinyar Gwadabe kasancewar ward Win na maza ne, akwai wata mata itama ita take ma mijinta jinya, sai muka zama mu biyu.
Shiru wajen ya Wauka na kasa rarrashin Gwadabe shima ya kasa rarrashina. Wannan daren na ba makaranta gari ku hasaso da kawunanku.
Washe gari sassafe aka sake zuwa aka fita da Gwadabe zuwa wani hoton. Kafin a dawo dashi sai ga Yemisi da Burodami Debisi, da Lekan. Hannunsu ri?e da lodoji. Shigowarsu ke da wuya aka shigo da Gwadabe. Da Burodami Debisi aka kinkimeshi zuwa gado.
"Sannu Gwadabe ya jikin, ashe abunda ya faru kenan?" Cewar Burodami Debisi.
"Jiki sai godiyar Allah, Iyabo likita yace yana son ganinki" Tashi nayi na nufi ofishin likita.
"Duk binciken mu ya tabbatar mana komai nashi lafiya suke. Mun yi hoto har sau biyu bamu ga komai ba. Mun sallameku inaga ku nemi na gargajiya zaifi. Ina mai baku shawarar ku sai mishi keken tu?a marasa lafiya, yafi muku sau?i da a dinga kinkimarshi. Ga takaddar sallama, kije ki biya Allah ya ?ara sau?i" Sai da na share hawayena kana na amshi takaddar bance mishi komai ba na fita. KuWin hannuna sai da suka ?are tas ban tsira da ko ficika ba. Burodami Debisi da Lekan su suka taimakeni wajen Waukar Gwadabe muka samu Taxi ta kaimu har ?ofar gida. Baban Nazifi da Yaya Harisu suna tsaye a ?ofar gida su Lekan suka zo suka shige da Gwadabe, na mara musu baya. Tunda muka dawo ma?ota sukaita tururuwar shigowa gaishe da Gwadabe, su Iyaa Debisi ma sun tawo kusan dukka gidan, sun kawo abinci da dubu biyar, haka mu kaita karSar jaje daga mutanen arziki. Babala kuwa a bakin Gude nake jin wai ta koma Takai Laila ma ta je ganin gida. Atampopi na na Wura a buhu kab harda ma Winkakkun bar bari ba, kala huWu na ware kawai, na Wauki buhunnan na fita hankali da nutsuwata basa tare dani sam. Siyan wula?anci sosai akaima kayan, amman biyan bu?ata yafi godon buri, Gwadabe mutum da Sari ne a wajena. Keken Waukar marasa ?afa ko tsofaffi na siyo ta hannu akan nera dubu ashirin da biyar da Wari takwas. Ina shigowa gidan kallo ya dawo gareni, ni dai babu wanda na kalla takaina kawai nake yi. Ko Gwadabe yasha ruwan mamakin ganina da wannan wul ciya sosai. Ni dai bance uffanba na tallafeshi na sashi a kan wul ciya Winnan. Hawaye ya soma sharewa, ni kuma ina mishi murmushi.
"Mala'ikun Allah ku shaida na sama rayuwar Iyabo albarka, kuma na Waga mata ?afafuna domin ta shiga aljanna. Allah yai miki albarka ya kawo mana mafita akan jarabawar da take kanmu"
Ameen Gwadabe, ka dena kuka. In sha Allah tunda ina nan kafi ?arfin zubar da ruwan hawaye."
Daga haka muka shiga suntirin bin masu magungunan gargajiya, mu ke nan kullum a tafe, amman babu canji kullum jiya e yau. Tafe tafe sai da mu ka kwashe tsawon wata uku muna abu Waya. Dangina da suke Wan tallafamun suma suka gaji suka watsar. Babala sau biyu kaWai tazo ta duba Gwadabe, amman ?an Takai kam sun zazzo sosai. Sakina da Bara'u kam mayar da gidanmu su ka yi kamar aje kasuwa a dawo. Duk wata jigilar zuwa nemo maganin makarin sammun da akaima Gwadabe, tare da Bara'u da Sakina muke zuwa. Abincin da zamu ci Bara'u ke kawo mana. Ayashe da Tamu suma sun mana ?o?ari sosai. Babbar damuwata Waya ce tak har yanzu babu wani sau?i da aka samu."
MRS BUKHARI

3064127935
Buhari Ibrahim Ladan
First bank

Sanya nera 500 Winki kuWin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan.
Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun
Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. ?ar?ashin Amila Foundation gidauniyar da muka buWe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya.

WaWanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ?ANYE)
300 kacal zasu iya kuWin karatu

https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm
NAMA YA DAWU
ROMO ?ANYE
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

10
Duk wannan ?ibar tawa da kuka ji labarinta, wallahi ta zuge sosai, na gama ramewa na fice a hayyacina sosai. Shi kanshi Gwadabe yafi tausayina fiye da kanshi. Bara'u kullum a cikin jinjina ma ?o?arina gami da amanaa suke yi. A kullum ro?ona shine Allah ya ba Gwadabe lafiya, ya yanke mishi wannan zaman. In zaman cikin ya isheshi shi da kanshi yake tu?a kekenshi ya fita ?war gida ya sha iska. Mun gama siyar da komai namu kuWin ya ?are a magani, Wakina goduwar kujer da kafet kaWai ya rage, sai tarkacen kwanuka da katifa , itama sabida Gwadabe na barta Wata rana ina zaune ina wankin kayana dana yara sai ga Uwani ta shigo, Gwadabe kuma yana ?ofar gida ya Wan fita shan iska
"Uwar biyu wanki kike yi ne?"
Wallahi kuwa, daga ina haka na ganki afujajan?" Na tambayeta tare da kallonta. Sai da ta cire mayafinta kana tace.
"Hmm wata harkar arziki na samo Iyabo. Kin ganni daga cikin gari nake gidan Hajiya salamatu, wata matace dake kai ?an mata da matan aure ?ashashen larabawa ko ?asashen turawa. Amman kafinnan na samo miki maganin karya sihiri garanti, daga cikin ayayoyin Qur'ani mai girma. Bari in karanto miki, muddin kuka ri?e wannan da izinin Allah kuka yazo ?arshe a cikin kwana na bakwai Gwadabe zai mi?e da ?afafuwanshi." Ina jin haka na zabur na saki wanki. Na juyo na zuba mata idanu.
Dan Allah faWi ina saurarenki Uwani" Dariya tayi tace.
"?akko biro da takadda ina faWa miki kina rubutawa, da izinin Allah waraka ta zo." Da sauri ba shiri na yago takadda, na Wakko fensirin Toye na dawo.
"Da farko zaki samu ruwanki mai tsabta.
Sai ganyen magarya koraye bushewar inuwa guda bakwai.
Sai a karanta suratul fatiha a cikin ruwan da aka zuba magaryan, a dinga karantawa numfashin baki na komawa cikin ruwan
Sai a karanta Ayatul kursiyyu ( aya ta 255 na cikin suratul ba?ara).
Sai a karanta suratul a'afaaf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122.
Sai a karanta yunus daga kan aya ta 79 zuwa kan ta 82.
Suratul kafirun ?afa Waya.
Fala?i da nasi ?afa uku_uku
Sai a karanta wannan adda'ar.
Allahumma rabban nas,azhibil ba'as ashfi wa antash shafila shifa'a illa shifa'uk shafi'un la tugadiru sakaman
?afa uku za'a karanta.
Sannan za'a iya karawa da wannan adda'ar
"Bismillahi urkika min kulli shai'in yu'uziyaks wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urkika
Shima ?afa uku
In sha Allah ta'ala idan aka karanta wadannan kuma mutum ya dinga sha sau biyu a rana safe da yamma, yana kuma wanka dashi a waje mai tsabta, ko kokuma a ji?a tawul a goge jikin marar lafiyan da ruwan maganin. Da izinin Allah cikin sati Waya mutum zai warke in dai sihirine a jikinshi.
( Kuma zaku iya jarabawa. Wasu malaman sun ce yana da kyau wanda yake da lafiyarshi ma yayi, domin hakan ka iya zama rigakafi kafi magani kareshi. Wallahu mista'al)
Wawuyar ajjiyar zuchiya na sauke tare da ya?inin sau?i ya zo ma Gwadabe. Duk da abaya masu magani sun bamu wasu mayuka tare da tofin ayoyin Allah a ciki mun yi amfani dasu da dama. Wasu kuma mu da kanmu muka zubar dasu, dan ganin shirka ta shiga cikin lamarin, amman wannan sai naji na samu nutsuwa dasu ainun.
Nagode sosai ?awata Allah dai ya bar zumunci. Bari ki ga da zafi zafi ake dukan ?arfe bari in wanko ganyen magaryana, ina da ruwan sama cikin robar fenti sai in yi dashi. Sai fa na gama zan samu nutsuwa." Da sauri na je na Webo ganyen magarya adadin na bu?atar na wanko, na kinkimo ruwa da Qur'ani izu shittin.
"Af na mance sai an daddaka ganyan magaryar ake zubawa." Cewar Uwani k???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?enan. Da haanzari na Wauko turmi na daka na zuba a cikin ruwan da bismillahi. Sai da muka kammala na samu nutsuwa har na sauke ajjiyar zuchiya. Daki na kai ruwan maganin na adana kana na fito."
"To bani labarin abinda ya kai ki gidan Hajiya Salamatu, uwar shige_shige Uwani"
"Wallahi Iyabo ?asar zan bari zan tafi nemo kuWi. Amman shekara biyu kawai zan yi in dawo" Zare idanu nayi ina dubanta da mamaki.
?asar fa kika ce, to aurenki da yaranki a hannun wa zaki barsu Uwani?" Ajjiyar zuchiya ta sauke tace.."Hafizu zai lura dasu Iyabo. Wannan talauci namu yayi yawa. Duk abinda Hafizu fa ya soma babu albarka sam a ciki. Kuma shi ba jari ba. Ke yanzu haka maganar da nake yi miki ma ina gidanmu fa da yaran. An koremu a gidn haya ko ince miki an watso mana kayanmu tsakiyar layi da ranar Allah. To Hafizun ma shi ya bani shawarar ko zan nemi aikatau na ?asashe da ake zuwa, ?anwarshi ma yanzu haka tana Canada a gidan aiki, shima in ya samu tare zamu tafi. Ni fa Iyabo wallahi tafiya zanyi. Su Hajiya ma basu san me ake ciki ba. Babbar damuwar shine ita Hajiya Salamatu tace sai dai in ajjiye dubu Hamsin da kuma ni zan yi ma kaina fasfo. In kuma ba haka ba duk zata yi mun amman zan kai wata shida kafin in gama biyan kuWin da duk ta kashe mun. In kuma na yi fasfo na ajjiye dubu hamshin, da zaran na tafi a cikin wata biyu zan gama biyan kuWin girji" Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
To amman babu wani haWari a cikin tafiyar dai ko. Kuma ina fatan bata Sarauniyar hanya za'a tura ku ba Uwani, kuma kin tabbatar Shekara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login