Showing 264001 words to 267000 words out of 270738 words

Chapter 89 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

mafita kunji ko yaran ummu?"
Da wani irin rauni na faWa to Husaini sun riga sun girma tuni suka fahimci akwai matsala , sai dai basu ga fuskar tambayata ba.
A sanyaye muka gaisa da Usman kaina a ?asa. Muryarshi a dashe ya amsa mun suka gaisa dasu uwani da Hajja Mama ma
"Uwani muyi magana dake a falo mana"
Ya faWa yana fita. Mi?ewa Uwani tayi suka fito falo
A falon Uwani ta tarar da yar Usman Win a zaune tana cike da damuwa Anty Sumayya. Gaisawa suka yi da Uwani.
"Dan Allah a ta?aice ki bamu labarin iyabo Uwani. Tunda tun kuna yara kuke tare. Inason sanin wacece ita da musabbabin shigarta wannan matsalar da ?addara ta cillota garemu"
Cewar Anty Sumayya kenan. Uwani nan ta warware musu zare da abawa ta basu labarin duk wata rayuwa ta Iyabo. Kai Usman yake ta kaWawa ya kasa cewa uffan sai tsananin so cakuWe da tausayin rayuwar matarshi. Anty Sumayya ce tace.
"Na tausaya mata matu?a. Uwar mijinta na farko bata da imani. Na jinjinama aurenta na biyu da irin yadda soyayya ta jata. Ta kuma yi kuskure da a saninta ta auri Hamma alhalin tasan wacece Hama. Amman ?addarallah. Yanzu Hajiya uwani tunda Hajiya Iyabo bata da ishasshiyar lafiya ki bamu lambar Hamma, da lambar Debisi mu kirasu sai su zo su samemu. Akwai wani al?ali dake al?alanci a kotun musulunci zamu gayyaceshi yazo ya warware mana wannan ?ullin.
Usman kayi ha?uri dan Allah ka daWa nasan kayi.
Ita ?addara ta rigayi fata. Ka duba da duk irin soyayyar da Iyabo tayi ma Hamma ko zaman shekara Waya cib basui ba. Kai kuwa sai da ka shekara goma sha bakwai da'ita ta haifa maka yara har uku duk kuruciyarta kai ka kwashe ta. Nasan irin son da kake yima Iyabo da irin tasirinta a rayuwarka ka dangana ka karSi duk abinda Shari'a tazo dashi"
Uwani ta Waga waya ta kira Hamma.
"Hajiya Uwani barka da safiya ya Kano da yaran?
"Malam Hamma kowa yana lafiya. Dama na kiraka ne muyi magana da kai. Gani a Gombe kuma cikin amincewar Allah mun haWu da Iyabo yanzu haka muna tare a gida Waya tare da yaranka ma. Kazo ka sameni a Gombe dan Allah in da hali kazo da wani babba domin akwai wani babban ?ulli"
"Allahu Akbar. Allahu Akbar Allahu Akbar ya Allah nagode maka Allah na gode maka ashe zan sake ganin iyabo. Mustafa inane gabas zanyi sujudul sukur" Yake tambayar na kusa dashi.
Hamma duk ya birkice ya saki kukan murna yanata jero addu'o'in godiya ga Allah.
"Uwani nagode gobe zamu tawo yanzu zan kama hanyar Adamawa"
Nan Uwani tana share hawaye ta zare wayar a kunnenta ta kira Debisi nan shima suka ruWe da murna duk aka tsaya akan gobe suma zasu tawo.
Usman yayi shiru sai Allah yake ambato a zuchiyarshi kawai. Yaranne suka zo suka fice daga gidan. Dr kuma ta shigo sake duba jikin Iyabo.
Uwani ta mi?e tabi bayan Dr, Alhaji Usman da Anty Sumayya suka fita
Nan duk wanda ya dace su zauna dasu dangin iyayensu manya sun zauna sun tattauna an fasa matsalar dai. Cikin ?an?anin lokaci aka san halin da ake ciki.
Ga Usman a zaune Suna karbar gaisuwar makoki amman hankalinshi baya tare dashi. ?an biyu dake zaune a jere dashi kawai yake ji a halin yanzu Iyabo kam ya riga da yasan ta kuSuce mishi in ba wani ikon Allahn ba. Amman yana ji a ranshi da iyabo zai ?are rayuwarshi, irin sonda take nuna mishi yafi son da tayi ma Hamma a baya a labarin da Tabalbalin ta bashi. Idanunshi yake lumshewa lokaci zuwa lokaci.

IYABO:.
Tare Uwani da Dr suka shigo. Bayan Dr ta gama dubani ta fita Uwani ta soma bama Hajja Mama labarin matsayar da aka tsaida lamarinnan. Ni dai sai cikina ya zuge zawo duk minti biyar sai na faWa banWaki.
Mijin Uwani da kishiyarta ne suka zo yi mana sallama.
A hankali na fita falon na zauna a waje guda muka gaisa cike da girmamawa a mutunce. Su kai mun barka da dawowata cikin hayyacina tare da adda'ar Allah ya kare gaba.
"To mu Hajiya jirginmu zai Waga ke sai yaushe kenan zamu saka rai dake?"
Uwani tayi dariya tace.
"Ranka shi daWe ni nan ai sai naga abinda ya ture ma buzu naWi, zan zauna da'ita har zuwa a gama komai in sha Allah sai in dawo"
"To ai Shikenan. Amman yaran shago sun kiraki kuwa, ruwa ya shigar miki shago yayi Sarna sosai gaskiya. Amman nace su kai kayan da ruwa ya taSa gida a wanke a shanya dai. Na kuma tura musu masu gyara su gyara inda ruwan ya shiga"
"Assha to Allah yasa da abinda ya tare. Basu ko kirani ba gaskiya"
Ni dai nan nayi musu Allah ya tsare hanya na sa kai na koma ciki.
"Iyabo bari in shiga cikin gidan mu gaggaisa tukunna. Wai ni kam kishiyoyinki me suka Wauki duniya ne sunfa fito lokacin da kika faWi a can tsakar gidan fa. Amman banga sun zo dubaki ba, su Sumayya mun musu uziri su mutuwa akayi musu."
Ohon musu Hajja ai babu komai duniyarma nawa take. Wallahi Allah gabaki Waya komai na cikin duniyarnan ya isheni ya isheni.
Kafin Hajja Mama ta bani amsa Anty Sumayya ta shigo da sallama tare da cewa.
"Imanine yadda da ?addara me kyau ko akasin hakan Iyabo. Na sani al'amarinnan babbane sosai, amman ki godema Allah daya dawo dake cikin nutsuwarki zaki ga danginki, ki ga mahaifanki me yafi wannan daWi ko babu komai yaranki zasu ga mahaifinsu. Ki sani dan suna amfani da sunan Usman duk daren daWewa za'a samu ko a family da wasu zasu tsokata musu cewar Usman ba mahaifinsu bane. Ko ba'a tsokata musu ba ranar da Usman ya faWi ya mutu a ranar zasu yi kuka dan dole a fayyace musu gaskiya da gaskiya. Hakan ma ban yi tunanin zai kai tsawon haka ba, nayi imani da a Gombe kuka zauna tare da kishiyoyinki ko su Abida zasu goranta ma yarannan. In ma ba sui ba iyayensu zasu yi. Kinga sai ki shiga tashin hankali dan ko yankaki za'ayi ba zaki ce ga ubansu ba, mu kuma zuchiyarmu a lokacin zata shiga wasi_wasin shi yarsn ma na sunnah ne. Ke komai kika ga ya faru akwai hikma a tattare da faruwar. Ki yi haquri daga ke har Usman din. Shima yana cikin mummunan halin da tunda nake ban taSa ganinshi a ciki ba."
Nasiha da ban baki kawai ake ta yi mun. Sai nayi kamar na samu nutsuwa dana ga shige da ficen yara sai damuwa ta sake aurena.
Sai zuwa yamma akaita cincirindon zuwa gaisheni tare da gulmace gulmace a madadin su tausaya mana sai abun ya zama wani iri kuma. Suhailat kuwa sai cemun tayi.
"Ashe komai yazo ?arshe kuma, hankalinki ya dawo jikinki an gano kina da aure. ?ila ma kina sane dokiya kika zo ci, to dubu ta cika".
Uwani ta dubeta tace.
"E yadda kika faWa haka Winne baiwar Allah. Sai dai mu gode ma Allah daya nuna mana wannan lokaci kuma. Dukiya kuma ai tari da ta handami iyakar handamarta karfa ki mance Iyabo itace da miji, ko ya baku labarin adadin gidajen da ya sai mata ita da yaranta kuwa?""
Bata dai kula Uwani ba ta fice. A zafafe dan maganar Uwani ta daketa sosai. Duk da bata san Usman akan rashin adalci ba, akan Iyabo sai take ganin zai iya komai ma akace yayi. Yaranshi basu sami damar karatu a waje ba sai ?a?an Iyabo harda agololi.
Uwani har yanzu kina nan da halinki"
"Me kike ganin za'a fasa Iyabo. Ya zata zo tana faWa mana magana. Ke dai kullum a haka zaki ?are ?ar iska.
Dole Uwani sai da tasa na dara.
Wannan daren cike na kwana da zulumi gami da taraddadi har garin Allah ya waye.
Sukuku nak, gabana kuwa dama shi tunda na dawo hayyacina yake faWuwa.
?arfe biyun rana su Debisi suka iso. Amman Alhaji Usman ya ajjiyesu a can cikin gida ana jiran isowar su Hamma. Su kam sai dab magriba Allah yayi musu karasowa bayan an idar da sallah Alhaji Usman ya shigo da sallama. Ina ganinshi na saki kuka.
"Uwani Hajja Mama kuje falo ba?inmu sun hallara. Inaso zan gana da Iyabo"
Nan suka fice suka bamu waje. Zama yayi a kusa dani yayi shiru sai ajjiyar zuchiya yake yi. Cikin wata murya mai kauri yace.
"Wannan ?addarar da girma take. Allah ya bamu dangana baki Wayanmu Iyabo. Amman me yasa kika boye mun halin da kika samu kanki kuka haWa baki da Hajja Mama tace ke ?ar ?anwartace ashe a gari ta tsintoki?"
Muuryata da bakina yana rawa na bashi labarin yadda mu ka yi da Hajja Mama.
Sonka ne ya rufe mun idanuna shi yasa har na amince dan gudun a faWa maka gaskiya ka fasa aurena. Wallahi babu wani nufi mara kyau a tattare dani ka yarda dani wallahi Usman ina sonka so mai tsanani"
Murmushi yayi mun idanunshi cike da hawaye yace.
"Ni ko nasan kina sona,amman ai dawowarki hayyacinki tuni ya ture gwamnatina dan Uwani ta bani labarin soyayyarki da Hamma. Ashe kyakkyawane haka shi yasa ?an biyu suka fito kamar larabawa."
Usman... Na ja sunan nashi yayi maza ya runtse idanunshi.
"A_a Iyabo kar ki mun wata kalmar soyayya. Ina neman alfarmarki dan Allah in aurena dake ya ?are kiji tsoron Allah ki cire ni cak a zuchiyarki kar ki sake ki zauna kiyi tunanina. Sannan zan sake ro?on wata alfarma duk da ba lallai bane in samu ba kuma baki da ikon yanke hukunci ke kaWai Iyabo in na rasaki na rasa su Hassan zan shiga damuwa mai tarin yawa. Duk da a tunanina ke kike da zaSi a kanmu ko ni ko Hamma. Nayi imanin in dai hakanne dole ni zaki Wauka ba Hamma ba, ki rayu tare damu iyabona cinyar sa maganin mai haWama ki zaSeni kar ki ga Hamma ki juya mun baya. Zaki mun illa. Inason su Hassan ina son su wallahi...
Na baka su har abada Usman babu wanda ya isa rabaka dasu. Yanzu Usman aurenmu rabawa za'ayi kenan? In dai zabi aka bani na shiga ukuna ya zanyi da rayuwata wa zan Wauka wa zan ajjiye to"
Na fashe da kuka. Mun daWe a haka sosai har sai da Uwani ta shigo ganin halin da muke ciki sai hankalinta ya tashi.
"Kuyi ha?uri dan Allah. Usman ku fito muje"
Ficewa yayi fuu. Uwani tazo ta Wagani muka fito falon
Tsarki ya tabbata ga Allah mai kowa mai komai
Da Yaya Hamma na soma haWa idanu, na ganshi ya goge sosai ya zama Wan birni sai dai ramarshi data ?aru da Wan duhu da yayi. Ga BaWWo, ga Amaduyal, ga Yafendo A'i. Ta Sangarensu Burodami Debisi kuwa. anty Ramata, Burodami Kokodeen, Burodami Debisi, da Iyaa Beji ne suka tawo. In taka in isa gabansu ni dai na kasa. Hamma ne kaWai ya mi?e ya iso gareni ya tsaya a gabana.
Usman ya hadiye yawu tare da yin gyaran murya.
BaWWo ce ta ?araso muka rungume junanmu sai kuka, Wakin ya cika da koke koken mata a haka su Hassan Anty Sumayya ta shigo dasu.
Nan kallo ya koma garesu tsugunnawa Hamma yayi yasa goshinshi a ?asa yayi sujjadar godiya ga Allah daya nuna mishi wannan rana.

Zan barku anan kuka yaci ?arfina

A tunanin ku auren waye dahir a kan Iyabo ne?
Shin zaSin za'a bata kamar yadda Usman yake fara da buri?
To wa Iyabo zata zaSa a tsakanin Usman da Hamma. Yaranta uku da Usman, yaranta biyu da Hamma.
Usman yayi mata so zallah, ya inganta rayuwarta da rayuwar yaranta, tayi rayuwar farin ciki tare dashi.
Hamma ya sota a baya ya sai da shanu har biyu domin farin cikin Iyabo, wanda a wajen bafullace babu abinda ya kai shanu daraja, kuma shekara sha bakwai yana zaune ya?i aure sabida Alaja Iyabo, bugu da ?ari gashi Wan uwanta na jini.
Shin wa zata Wauka wa zata bari?
MRS BUKHARI


**Anty Ramlex Me kayan Da'a,ingantattu,fitattu,kuma shahararru*
Na zo muku da albishir na Promo Promo Promo=؃?
Abun da kuka Dade Kuna nema....,hakika dogon Jira ya kare.....Ga abunda kuke bege gaba gare ku=؃??+?=? ?

Ina Uwargida me son sabunta martabarta a wurin Oga,Ina amaren bana masu son su mallaki zuciyar ango,Ina zawarawa da suka shirya gyaran abun cikin buje,domin farfado da mutuntakarsu........ku matso kusa......

Hajiya ta sauke farashi,me kike jira........

Babban set na promo
~#20k~#15k=?L? <د? _dambun zabuwa
<د?tsumin bugenta shakaf
<د?Gumbar Madara me Sanya megida Santi da dalalar yawu
<د?Hadin dabino da cukwui hadin basarakiya
<د?Tsugunno me sirri_

*Karamin set*~#15k~#10k=؃? =???Herbal for vaginal infection
=???Tsimin bujenta shakaf
=???Gumbar Madara da hadin dabino.
=???Hadin dabino da cukwui (manta uwa)
=???Tsugunno me sirri


=ؚ?Muna aika kaya ko Ina a fadin Nigeria da kewaye.
=???Ku tuntubeni a wnn numbern 07069722234
Anty Ramlex taku ce>?p?
NAMA YA DAHU....
ROMO ?A?YE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI
LITTAFI NA HU?U

19


DA SADAUKAR DA WANNAN SHAFIN GAREKA MIJINA ABIN ALFAHARI MASOYI MAI KAMA DA ZUMA. BUKHARI IBRAHIM LADAN.

"Am ina ganin kuka duk ba naku bane face ku nuna godiyarku ga Allah. Ku zo ku zazzauna muyi abinda ya taramu a sallami kowa.
Cewar Anty Sumayya kenan. Hannuna BaWWo ta kama ta zaunar dani a ?asa gefen ?afar Yafendo A'i kaina a ?asa falon ya Wauki shiru. Alhaji Usman ne yayi gyaran murya ya soma jawabi a hankali kuma a sanyaye tun daga haWuwarmu har zuwa yau Winnan. Yana gamawa falon ya Wauki salati da tafa hannaye. Idanuna na Wago na dubi Yaya Hamma idanunshi sun koma jawur farin cikinshi ya koma ba?in ciki jikinshi har rawa yake yi ?irjinshi yana ta hawa da sauka, hawayene naga suna bin kumatunshi kawai, kunsan fa Yaya Hamma akwaishi da kishi. Idanuna na lumshe kawai wasu hawaye masu zafi suka zubo mun.
Alhaji Usman yace.
"Hassan Husaini wannan shine mahaifinku, waWannan dangin mahaifiyarku ne. Kuje ga mahaifinku yasa muku albarka"
A sanyaye yaran suka isa ga Hamma yayi musu wata iriyar runguma kukan kishin da yake dannewa ya saki kawai. Niko tsabar hawaye ko gani bana yi ma.
Yaran sun daWe sosai a jikin Hamma kafin al?ali yace yaran su Wanje daga waje tukunna, a samu a yi abinda ya dace.
Al?ali yace.
"Wanan shine mijin ita wannan baiwar Allah?"
Yaya Hamma ya Wago kanshi yace.
"E nine ranka shi daWe"
"Ko zamu iya jin labari daga naku Sangaren dangane da Satan ita Iyabo?"
Uwani ce tayi gyaran murya ta basu labarin komai. Falonnan ya Wauki shiru, can al?alin yace.
"Tsawon tafiyarka shin Iyabo ita ke ciyar da kanta, ko kuma kai kake ciyar da'ita, duba da yadda ka daWe a wajen kiwo, duk da wannan daWaWWiyar al'adace da akasan fulani da'ita tun zamanin baya."
"Ranka shi daWe mahaifiyata na kula dasu, sannan ?annena maza na kulawa dasu su suke ajjiye hatsi, Wan kuWin cefanene suke nema da kansu"
"To Alhamdulillah naji bayaninka Alhaji Usman, suma Sangaren Hamma naji nasu bayanin. Da kai da Iyabo, da Hajja Mama baku da laifi ko kaWan ita Iyabo hankalinta aka gusar mata rayuwarta ta baya ta mance. Ita Hajja Mama bata san bayan Iyabo ba, kai baka san tana da aure ba wannan abun an yishi ne a bisa rashin sani, baku da laifi har a wajen Allah.
Ina fata bayan bayyanar wannan lamarin babu wata mu'amular auratayya data shiga tsakanin ku?"
Alhaji Usman ya ja ajjiyar zuchiya ya sauke kana yace.
"Babu ranka shi daWe"
"To Alhamdulillah. A zahirin gaskiya dawowar iyabo hayyacinta shi yake nufin aurenku babu shi ya ?are ya zama tarihi, har gobe tana a matsayin matar Hamma tunda yana da ranshi gashi a gabanmu, babu makawa aurenku da kanshi ya warware kanshi ba'a bu?atar sai ka rubuta takadda. Sai dai ku Wauki dangana kawai. ?a?a da kuka haifa yarane na sunnah tunda ta hanyar aure aka samesu kuma suna da gado kamar sauran yara.
Tare dukkanmu ukun muka Wago muna kallon al?ali illahirin jikina rawa yake yi, Alhaji Usman yace.
"Allah shi gafarta ina bayani akan za'a iya bata zaSi ta zaSi da wanda zata yi rayuwa? Naji kace aurena dake kanta ya mutu"
A raunace yayi maganar, al?ali ya gyara zamanshi yace.
"Ba irin wannan case Win bane yake Wauke da irin wannan hukuncin ba Alhaji Usman. Ita wannan baiwar Allah hankalinta ne ya gushe ta baro bayanta, ta manta komanta, kai kuma ka aureta, sabida haka bata da zaSi dole aurenta na farko yananan daram. Shi wancan da kake maganar zaSi shine in shi mijinne ya tafi ya barta shekara da shekaru babu waiwaye babu aike, babu ciyarwa har an cire rai da dawowarshi to sai taje kotu al?ali ya saketa tayi wani auren, to bayan tayi wani auren in shi wannan mijin ya dawo shine al?ali zai bata zaSin zaSar Waya a cikin mazajen nata. Kaga kuwa ai naku case Win ba haka bane, da fatan kun gamsu?"
Idanuna na runtse ina ambaton Allah. Alhaji Usman ma inaji yana ambaton Allah a fili, ya kasa mallakar kanshi"
"Yanzu abu na ?arshe shine Iyabo zata yi idda na wata uku, ko kuma ince jini uku dan wata mace a wata biyu take yin jini ukunta. In kuma ta wuce yin jinin al'ada sai ta ?irga wata uku. Da zaran wannan lokaci ya cika Iyabo zata koma Wakin Hamma a matsayin Matarshi suci gaba da zama, ba sake Waurin aure, ba sabon sadaki, ba akwati. Wannan shine hukuncin. Da fatan zaku bi yadda yazo a musulunci kar abi son zuchiya duk da akwai malaman da suke ba da fatawar macen na da damar zaSan da wanda zata zauna a hakanma. Zance mafi inganci shine dole ta koma hannun mijinta na farko.wannan shine ?arshen maganata."
A hankali sautin kukana ya dinga shiga kunnuwan jama'ar cikin falon hankalina ya tashi sosai da sosai. Bayan an barni nayi kuka ishasshe sai Usman yace.
"Ina neman alfarma Waya a wajen Iyabo da Hamma. Hassan da Hussaini sun riga sun zame mun jinin jikina so nake a barsu a hannuna ko baku barmin su halak malak ba a barsu su ?ar?are digree da mastas Winsu dan Allah ni wannan alfarmar nake nema musu a dubeni. Nasan Hamma shima zai so a yanzu ya tattare kan iyalinshi waje guda, ku dubeni kuimun adalci dukan zai yi mun yawa zai yi mun yawa Hamma"
Anty Sumayya sai ta fashe da kuka.
"Nima damuwata yaranne wallahi Allah, mun yi sha?uwa dasu sosai ya zamu yi Hamma ka tausaya"
Gyaran murya Hamma yayi nayi saurin Wagowa na dubeshi, ashe Usman yana ankare dani, ina sake Wagawa muka haWa idanu
Ba shiri


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login