Showing 132001 words to 135000 words out of 270738 words

Chapter 45 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

Malam na jima ina Wauke da cikinta ba dan tana cin albarkacin mahaifina take aureba da tuni ta gane kuranta. Sabida tana da fitina da yawa fiye da sauran iyayen namu." Nan dai suka Wan taSa hirarsu Ine tai mata sallama ta tafi. Sai wajajen azahar Sai ga Sailuba tazo kiranta.
Wayarta ta Waga ta kira Gwadabe ringing biyu ya Waga.
"Gimbiya lafiya dai ko?"
Murmushi tayi tace
"Lafiya lau. Dama Anty Badi'a ce tace tana son ganina shine nace bari in sanar maka" Sai da yayi murmushi yace.
"Masha Allah kije ba damuwa. Ni bana gidanma muna wajen Malam, an Wan samu kacaniyane a cikin gidan. Sai dai inna dawo zakiji komai"
"To Shikenan saika dawo Win." Wayarta ta kashe suka fito ita da Sailuba. Su Yaya Jazuli da su Nazifi suna Sarayin Yaya jamilu. Suma zancan korar mahaifiyarsu da Malam yayi a gidan suke yi. Karaf a kunnen Hadiza Nazifi yana cewa.
"Dole zamu je mu dawo da uwarmu babu inda zata je, tunda ta haifemu muna da gado a gidan" Hadiza ta kalleshi shima ya kalleta yana muzurai.
"Dena kallona dan ta abu kazan..." Ya danno wani zagi ya dannawa Hadiza tare da Worawa da cewa.
"Ku gaku ?a?an so, yaran mowa shafaffu da mai. To wallahi wannan abun masifa da bala,i kawai zai haifar dam mahaifiyarmu ba zata koru ba" In kun tanka Hadiza ta tanka. Inda sabo ta saba da jin waWannan zagi da waWannan furuci na cewar sune ?a?an so a idanun Malam. Haka zalika dukkan abinda ya faru a wannan gida nasu gani akeyi dasa hannu Baba Fhatsima da Yaya Tasi'u da suke ganin kamar suke juya Malam. Hadiza ta shiga tunanin yanzu haka suma in suka ?i samun zaman lafiya a tsakaninsu yaransu zasu taso a cikin ?iyayyar jininsu?
Wai to wake da Matsala ne mazan dake auro matam su haWe su. Ko kuma matan da aka aurone masu matsalar? Ita dai tasan matsalarta Waya kishine, kuma kishi shine matattakalar data rusa ahalin gidansu da duk gidajen da aka kasa samun daidaito da fahimtar juna kuma ba mace Waya bace a cikin gidan. Duk kishi shine sababin dake sa uba ya tsani ?a?an cikinshi, uwa taji kamar ta kashe Wan da kishiyarta ta haifa, kishiya da kishiya su kasa samun zaman lafiya. Gida ya zama gidan rikici da hayaniya kullum. Wannan lallai babbar matsalace da Hadiza take ganin bai kamata ta bari sheWan yaci galaba a kanta ba. Take zuchiyarta ta sassauto mata dangane da zafin kishin Shafa. Duk da bata da burin yin zaman doya da manja da Shafa. Amman ta Waura Wamarar saita zama tauraruwa sarauniya a birnin zuchiyar Gwadabe ta yanda zata ture har matsayin da Iyabo take dashi. Da wannan tunani ta shiga falon Anty Badi'a. Suna zaune a ?asan kafet an barbaza kayayyakin mata na ado da kwalliya kyawawan gaske Anty Badi'a sai Wagawa take yi. Hadda manyan zannuwan gado ?an kwali irinna saudiyya Winnan masu laushin gaske.
"Kinga yadda kayannan suka amsheki kuwa Hadiza? Ga wasu samfurin masu wando, da gajeren siket an kakkawa zo zauna." Cewar Anty Badi'a.
Zama Hadiza tayi da hanzari suka soma WaWWaga kayayyaki harda wasu rigunan bacci na garari .
"Kinga zaSi kaya Hadiza. Ba'a bori da sanyin jiki. Kinga waWannan dana zaSar mana ni dake, duba kiga kalolin sunyi" Anty Badi'a ta mi?o mata kayayyakin ta soma waresu tana gani, dogayen ruguna, da riga da wandone, sai kuma mai gajeren siket wanda zaka saka daga kai sai mijinka. Kaya dai kusan guda takwas_takwas harda zanin gado na kwali mai Wawisu irin na da. Hadiza rabin kuWin kayannan ta biya, Anty Badi'a ta biya mata kuWin rabin. Ta sake yin mata kwalimar nata ?ananun kaya. Ta bata wasu surruka masu ?arfi tace ta ri?esu tayi amfani dasu zata ci ribar zaman Aure.
"Fatanmu shine mutuwa itace zata rabaki da mijinki. Kinga maza kullum su babban birinsu shine mace ta zama musu tamkar hawainiya wajen caccanja salo_salo na komai nata ta yanda zamanku bazai zama ya gundureku ba. Ki tabbatar a ranar dazai bar Wakinki kin mishi abinda zaiji yana Woki da mararin sake shigowar girkinku.
Ki ri?e talaucinshi kuita mishi adda'a Allah zai buWa mishi Gwadabe yana da zafin nema ba malalaci bane muna mishi fatan nasara. A ido haka Shafa bata da wani matsala kiyi ?o?arin janyo ta a jika, karki bari wasu daga cikin gidan su janye miki ita da hakanne gulme_gulme ke ratsowa. Hadiza ai Baba ya kamata ta zame miki allon kwaikwayo. Dan har gobe kinga yadda ruwa yake maganin dauWa. Anty Badi'a ta jima tana bawa Hadiza surrukan da zasu tallafi zamantakewarsu daga ?arshe sukai sallama Hadiza ta koma Sarayinta. Gaga gaga haka rayuwa taci gaba da matsawa, duk safiya da irin shiga da Hadiza take yi na alfarma, ga ?amshi. Itama fa Shafa bawai a baya aka barta ba itama tana yin nata salon kwalliyar, amman ita tafi ganewa atampa, leshi sai dogayen riguna ?an kanti. Itama suta ri?e a matsayin makaminta. Ko wacce cikinsu rigegeniyar take yi wajen ganin ta zama ta gaban goshi.
Rayuwar gidan babu daWi domin kuwa wasu basa ko ga miciji da wasu. Ko wanne ?an Waki isu_isu da matansu suke mu'amala, gaisuwa wannan bata shiga tsakani. Shi yasa tsakaninsu Hadiza da matan su Auwala ne kawai suke mu'amalarsu a tsakaninsu, sai Yaya Tasi'u daya zame musu garkuwa. Ko wacce in zata fito bata da aiki sai wa?e da habaice_habaice. Sai gasa da hassada ta shigo cikin lamarin. Daga masu suyan kifi, sai masu suyan nama, ko kaza. Ga gasar sutura da kwalliyar safe data yamma dan tarbar miji."
Ta bangaren gidan Malam kuwa rikicine ya Salle ?aramar maganace take son zama babba. Iyayen matanshi daya tura gida sunyi jelen har sun ha?ura. Amsa Waya malam yake faWa musu itace
"Su je su huta a gidajen iyayensu. Nima inaso in huta"
Yaran Baba Suwaiba suka haWe kansu suka samu Malam akan batun gyatumarsu.
Suma Malam ya fatattakesu da zancan.
Bayan kwana uku suka je suka dawo da Babarsu gidan.
Ranar sunga tsiya.
MRS BUKHARI

Message Safmam Palace on WhatsApp. https://wa.me/2348067145801
Hello Maamas..
Shin ko kunsan AMASI'S TREAT from SAFMAMPALACE ta tanadar muku da ingantattun sinadarai na fito da martabar abinci da abin shaa? A AMASI'S TREAT Muna da spices and herbs irin su;Curry powder, Mixed Spices, special Jollof mix, fried rice, Mandi Spice, Garlic powder, Cinnamon, cloves, Tea blend, Yaji, Spiced daddawa.. Gasu nan dai dayawa.
Har ila Yau AMASI'S TREAT bata barku haka ba Seda ta tanadar muku da kayan maqulashe Don gusar da kwadayi=?? Muna da;
Kwakumeti, Ridi, daquwa, Cin Cin da sauran su.
Bafa anan muka tsaya ba Muna da bangaren qayatattun dinke dinke.. SAFMAM CLOTHING zasu fito muku da kyawun dake materials dinku ta hanyar tsantsara muku dinki musamman na yaranku mata=?
?
Muna nan a Zaria Muna aika Kaya ko'ina cikin aminci
08067145801

Assallamu alaikum mutanan kirki Ina Miko gaisuwa daftn alheri=?O??#? samun damar mallakar duk abunda kakyeeda bukata. Cikin sauki ta hanyi Yi muku adashin gata =؃??#? idan matsalarki rashin sabbin plates Akwai
1, zubi duk sati 2k sati 10 kwasar kayan 20k =؃? Akwai zubi duk sati 2k sati 20 kwasar kayan 40k har zuwa duk yanda mutum yakyee bukata zamu turo maka da kayanmu idan lokacin kwasarka yayi da yarda Allah kazabi duk abunda kakyee bukata da yarda Allah to mekakyee kikyee jira ki tintibene domin jin yarda raguwar tsarukan sukyee insha Allah idan Kuma kyee ma,aikaciyace to kyeemafa =؃? Akwai kayan Yara yankanti
Akwai takalman da jakunkuna da mayafai
Da sauran kayan amfani kyeedai maxa ki hanzarta kafin mu Fara zubi
Insha Allah zamu Fara zubi a farkon( sabon watan August ) Allah yadafa mana nagodee sossai zee Musa takuce =؃??p? ga number din da zaa iya damuna =؃??#?=???=??? 08029882667


*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
07082649563 whats app number kira 07036028230
*INA MASU SAN SIYAN KAYAN ?AMSHINA? NESA TAZO KUSA ZAN TURO DA KAYA KANO DAGA KANO ZA'A TURA MIKI DA KAYANKI DUK GARIN DA KIKE, IN A KANO KIKE KAYANKI HAR GIDA ZAI ISO MIKI IN SHA ALLAH. KAYAN ZASU ZAUNA A HANNUN ANTY ZEE MUSA COLLECTION DA IZININ ALLAH KAMAR YADDA AKA SABA. IN KINA BU?ATA KIYI MAGANA A HA?O DA NAKI KAYAN HAJIYA*


*?AN PROMO SUMA SU SOMA TURO DA KU?IN PROMO ?INSU. 10k NE ABU UKUNE A CIKI. IYAKAR NA MUTUM HAMSIN ZAN HA?A MASU SO SUYI MAGANA KARKU BARI WANNAN PROMO YA WUCEKU*
*WA?ANDA SUKA SAN KAYAN PROMO NA NASAN BABU WASA. IYAKAR MASOYANA NE KAWAI PROMO DINNAN BAZAN SIYARMA DA NA WAJEN GROUP BA. KAYAN 20K NE NA BAR MUKU A 10k DOMUN KU DA BAKU TA?A AMFANI DA KAYANA BA KU JARABA*

*WA?ANDA KU?A?ENSU YAKE HANNUNA DUK ZAN SALLAMEKU SANNAN AKWAI KYAUTA DA ZAKU SAMU IN SHA ALLAH.*

*WA?ANDA BASU TA?A SIYAN KAYAN ?AMSHINA BA SUMA AKWAI KYAUTA TA MUSAMMAN DA ZAN BAKU IN SHA ALLAH.*


NAMA YA DAHU..
ROMO ?ANYE
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI


20

"Wallahi Suwaiba ba zata shigarmun gidana ba, tunda ba da kudinku na gina gidan ba. Ki koma gidanku ki huta, kinganni hutu nake bu?ata ni kam" Cikin marairaicewa Baba Suwaiba tace.
"Haba Malam ai in adalcine sai ka sallami matan naka duka, bamu ka waremu ba su ka barsu ba. Sannan Malam wanne irin ha?urine daga gida ban turo an baka ba ne? Sagiru kasa baki" Ta dubi Sagiru halamar agajinshi take nema. Dan dama yafi kowa rashin kunya a cikin gidan.
"Baba muje ki zauna a Sarayinmu, mun riga mun Wakkoki daga gidanku ai ba kya koma ba. Muje kinji ki dena damun kanki"
Ya kinkimi akwatinta ya kaita wajen Amaryarshi yace ta zauna na wani lokacin. Haka kuwa Baba Suwaiba taci gaba da zaman takura tana kwana a falo akan doguwar kujera. Kwananta biyu ?arta ?anwar Sagirun Aisha tazo ta ganta, ta tattageta zuwa nata gidan tunda su suna da estira Wakin da zata zauna ita kaWai.
Amaryar Malam kuwa tana gidansu zaman gidan babu daWi, gashi mahaifinta yace shi ya gaji bazai sake zuwa ba Malam hakuri ba.
Wannan lamarin ya sake farra?a kan gidan Malam. Bayanin da Baba Fhatsima take ta yi mishi kenan babu dare babu rana kan hakan ba Wa mai idanu zai haifar ba. Shi kuma yace ta zuba mishi idanu data matsa sai cewa yayi.
"Fhatsima in kika matsamun akan batun su Suwaiba, to zaki sa in sallamesu gabaki Waya su fice mun a gida. In yaransu zasu bisu duk su haWa dasu. Ina amfanin yaran da basa dajarta ubansu ne?"
Dole haka Baba Fhatsima ta tsuke bakinta tayi shiru. Da Baba Asshi da yaranta sai suka shafama kansu ruwa, dan basa fatan uwarsu ta bar Wakinta azo ana ro?on Malam yana botsarewa.
Wannan kenan"


Yau monday tushen aiki. Ayau Angwaye zasu koma bakin aikinsu kasancewar yau satinsu guda tim da tarewa a Wakunansu. Wanda yayi dai_dai da kwanan Gwadabe huWu a Wakin Shafa.
Tun asubar fari Gwadabe ya hura huta ya Waura ?atuwar tukunyar maganinshi, yana dawowa Sallah ya sauketa. Shafa ta juye mishi ruwan wanka, shi yana shirin fita kasuwa ita kuma ya kwatanta mata yadda zata ?ulla mishi maganin nashi. Tana girkin safe tana ?ullin magani. Gwadabe shi kuma ya shirya tsab cikin kayan nema ya fito ya kama Waurin magani. Ita kuma Shafa ta samu damar kammala haWa kayan karin kumallo a babban tire, ta shiga ban Waki ta watsa ruwa. Cikin kan?anin lokaci ta shirya cikin doguwar rigar shadda mai ruwan ?asa tasha surfana.
Tana fitowa Gwadabe ya kalleta yace.
"Kinyi ma?urar kyau Shafa. Ki kai abincin Wakin Hadiza nima ganinan"
"Godiya nake yi mijina na kaina" Murmushi yayi mata yana son sanyin halin Shafa sosai. Tiran ta Wauka ta shige Wakin Hadiza, bayan matar Sabitu ta ja dogon tsakinta.
"Gwadabe kayi da jiki bakwai harta gota, Mammada fa harya fice yana jiranmu a ?ofar gida, kai kuma naga sai yanzu ma zaka karya" Cewar Auwala daya fito cikin shirin fita kasuwa"
"Bari kawai in musu sallama sai in fito mu tafi. Ko ?ar tsala naci acan in munje."
Mi?ewa Gwadabe yayi tsaye da sauri. Bokitin maganin ya kinkimo ya fito dashi tsakar gidan, ya ajjiye tsumman da yake gammo dashi, ya samesu a Wakin Hadiza.
Itama Hadiza taci ado yau da Atampa riga da zani, jakarta da mayafinta yana gefenta itama hutun da makarantar su ta bata ya ?are yau.
"Barka da Safiya yallaSai, lafiya ka tsaya a kanmu sai binmu da kallo kake yi?" Cewar Hadiza da take magana a Wan shagwaSe. Yana matu?ar jin daWin shwagwaSar Hadiza da yadda take taimakonshi akan shimfiWa wajen tayashi cimma manufa. SaSanin Shafa da take kwanciya kamar ruwa sai inda aka juyata"
"Kunyi kyaune. Nake mamakin ni Gwadabe maha?in gwal, mai saida maganin basir nine da mata fella_fella haka? Allah nagode maka.
Kuyi ha?uri abincinnan bazai ciyu ba. Su Auwala ni suke jira, saina dawo zanci abincin acan.
Hadiza yau zaki koma bakin aikinki kema ko?"
"E hakane. Ni kaina jiranka nake yi dama ka shigo in muku sallama, inna tsaya yin breakfast a gida zanyi latti. To acan nake karyawa ina tafiya da filas Win tea da abinci"
"To Shikenan tunda Hakane. Na soke karyawar safen. In yaso da daddare ma dinga haWuwa, ni na tafi. Shafa ki yi haquri ki koma Wakinki da abincin"
Sam Shafa bata ji daWi ba. Tana lure dama Hadiza bata son cin abincinta, kuma ita ta duba ta hanga bata ga ta inda Hadiza ta fita tsafta ba. Ba dai tasan irin daWin girkinta ba wannan, tana jiran ranar girkintane taci taji"
Tiran abincin ta Wauka.
"To Yaya sai kin dawo"
Tasa kai ta fice. Tana fita Gwadabe ya jawo Hadiza dake tsaye jikinshi, ya cusa kanshi a kirjinta yana ajjiyar zuchiya.
"Uwargida a matse nake dake fa sosai. Ina mararin juyowar girki bazan Soye miki ba"
Idanu ya lumshe yana hasaso daren ?arshe da yayi a Wakin Hadizan.
Murmushi tayi mishi tace.
"Kamar yaune lokaci zai zagayo, harma ya wuce. Haka zakaita zagaye har abada, tunda burinmu mu dauwama tare da kai har abada" Ba shiri dole ya saketa ya fice, ta biyo bayanshi suna dariya.
Gwadabe ya suri bokitin maganinshi ya fita. Auwalane ya Waura mishi aka suka nufi hanya, Allah cikin ikonshi kafin su isa inda zasu hau abun hawa Gwadabe yana taSa ciniki babu laifi. Acan inda ake aikin ha?on zinare kuma tas maganinshi yake ?arewa sakamakon maganinshi yana da kyau, kuma masu saye sun shaida yana musu aiki. Gashi yana gaba_gaba wajen ha?on zinare, Gwadabe namijine mai zafin nema da zafin nema babu wasa a lamarin aikinshi.
Haka rayuwar dai taita garawa yau mun wayi gari Gwadabe ya gama kwananshi na ?arshe a Wakin Shafa, ya fita da safe inya dawo a Wakin Hadiza zai ya da zangonshi. Sannan yana fitowa Yaya Tasi'u ya bashi takaddar samun aikin Shafa, a wani asibiti zata dinga ba da kati. Gwadabe yayi murna sosai kuma ya yaba da ?o?ari da kulawar Yaya Tasi'u gaya.
Mutuniyarku Hadiza yau wayar garin tayi tamkar anyi mata bushara da gidan aljanna dan daWi. Tana cikin farin ciki ta tafi makaranta. Hatta ?awayenta malamai sun gano farin cikin da take ciki.
Sadiya uwar zolaya, bayan Hadiza ta fito daga aji ta dawo ofishin malamai dan tanaso ta karya kafin lokacin komawarta wani ajin yayi tace.
"Waini Hadiza ko Gwadabe yayi muku wata gagarumar kyautace yau Winnan? Hatta kwalliyar da kika caSa naga ta dabance, harfa taku kika canja." Dariya gabaki Waya matan cikin ofishin suka saka. Hadiza saida ta tura wainar ?wai bakinta kana tace.
"Sharri dai da sa ido Chima in ba haka ba wacce canja tafiya nikam zanyi? Kawai dai yau nice da girki shine naketa nishaWi. Kuma inata tunanin wanne irin abinci zan tari Oga dashi, tunda mu kai aure baici abincina ba, in banda farar shinkafa dana dafa muka ci da Miyar da Balaraba ?ar ?anwar Baba ta soya. To Ku bani shawarar abinda zan girka, da irin wankan da zan fella Sadiya kune masu kishiya, bani labarin yadda kike tashin kan abokiyar zamanki ran girkinku?"
Wata dariyar mugunta Sadiya ta shiga yi har tana tuntsurawa.
"Wallahi har kin tuna mun da Safara'u. Ranar girkina sam bata da sukuni, kalar tausayi take zama. Gashi Sanusi shi ?a'idarshi a turakarshi muke zuwa cin abinci. Gaskiya kusan kullum da jan idanu take fita in ranar girkinane" Hadiza tayi shewa tace.
"Shegiya ?awata. Bani sirrin mana nima in ?ara da nawa. Kinsan Allah inason mijina sosai, kuma in na kalli Shafa a kullum sai inji kamar ma in sha?eta uban kowa ya huta. A kallon da nayi mata lokacin biki, banyi tunanin zafin kishina zai iya sauka a kanta ba, danni na raina yanayinta kuma nasan ?ar ?auyece duk da tayi karatu. Ashe wallahi kallon tsoro nayi mata itama akwai kaya. In ta shawo wankannan suka shigo mun ita da Gwadabe kuma naga hankalinshi a kanta. Kinsan Allah kamar in zazzagama kaina fetur in ?one haka nakeji dan kishi."
Dariya suka kwashe dashi. Barira tace.
"Ni uwargidanmu batta da son girma amman bata da damuwa. Amman Nabila itace take neman Wauramun hawan jini a baya. Sai da Sadiya ta bani maganin damuwar da Nabila ta so Wauramun. Shawarwarine nagartattun da dabarun yadda zaki zama wata ta daban a zuchiyar oga, da kissar danne kishi. Kinga da Wan abu kaWan Nabila zata yi,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login