Showing 21001 words to 24000 words out of 270738 words

Chapter 8 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

fitar suna kala biyu, da takalmi da mayafi, sai sar?a, dasu nabkin, da paints na yara, da man shafawa, da sabulu. ?ayar ledar kuma kayan abinci ne a ciki. Ina farkawa Yemisi tace.
" Lo we. ( Je kiyi wanka)"
O dara ( To) Kawai na iya ce mata na Wauki zani na lulluSe jikina dashi na fita. Ina fitowa ma?otanmu suka soma shigowa barka. Matan gida kuwa babu wacce ta le?o, sai aikace_aikacensu suke yi kawai. Bayan jama'a sun ragu sai na fita zuwa Wakin Yaya Haula dan gaishe da Babala. A falon na tarar da Gwadabe da Bara'u gurfane a gabanta. ?an fodiyo yana gefenta yana Sallo mata magungunanta.
Gaisheta nayi da jiki, da ?yar ta kada baki ta amsa mun. ?an fodiyo na gaishar kafin na gaishe da Bara'u da Gwadabe. Ni dai anan na tafi na barsu. Da tuwon masara miyar kuka da bushasshen kifi Uwani ta tare ni, harda tea mai madara, ina bacci Gwadabe ya shigo da kayan tea. Anty Mulka ce ta shigo ciki tace.
"Wai Iyabo su dangiin mijinki basa zuwa taya aikine? Tun sassafe muke ta aiki a tsakar gidanku, amman babu wacce ta taya mu komai. Mun fitar miki da randunanki tsakar gida, wata bushasshiyar mace tazo tana faWar maganganun banza, har tana dangantamu da ?azanta. Mu fa ba zamu Wauki irin wula?ancin da sukai mana lokacin sunan Toye ba. Bga won ( ki ja musu kunne) sai in zaune mace ni yadda nake da ?ibarnan"
Nan Bose da Kauliya suka Wauka suma sai yare suke ta yi mun. Uwani ce tai ta basu ha?uri ni kam kuka na saka musu kawai. Ganin kukan nawa ne yasa su kai ha?uri. Tun ganin da naima Gwadabe a falon Yaya Haula ban kuma saka shi a idanuna ba. Da rana Iyaa Debisi ta aiko mun da farfesun kan akuya cikin kwano shi naci da rana, su kuma suka dafa taliya. Uwani na kira nai mata raWar ta zuba ma Babala ishasshe a kai mata. Amman ko da aka kai sai dawo dashi Uwani tayi Babala tace bata cin abincin Yarbawa, da akayi tuwon dare ma na kuma sa Uwani ta kai mata, amman bata karSa ba. Har magriba babu Gwadabe ba dalilinshi sai wajajen taran dare muna zaune dani da Sakina da Uwani suka shigo shi da Bara'u da ?ar ba?ar ledarsu a hannu. Idanu ya zuba mun tare da lumshe su. Na fahimci akwai gajiya da tarin damuwa dake damun Gwadabe. Ko wanne halin zai shiga in na barshi oho, nasan Gwadabe yana sona so mai tsanini, duk da na fishi zurfi a soyayyar da nake yi mishi, jin Gwadabe nake tamkar shine mahaWin numfashin da nake yi dan in rayu. Amman dole in fita daga rayuwarshi shima ya samu ya nutsa.
"Ayi mun afuwa uwar biyu. Abubbuwanne su ka haWu suka caSe mun. Mun fita da Bara'u fafutukar yanda za'a samu na abincin suna da abun ha?i?a a fita kunyar ?an uwa." Murmushi nayi mishi nace.
Babu komai, sannunku da dawowa ina wuninku?" A tare suka amsa duk aka gaggaisa baki Waya. Sakina ta tafi kawo musu tuwo.
"Tamu ya kirani da magriba madam Winshi tana son tayi miki barka, yace ma ana gobe suna zata zo. Bari in kira ku gaisa" Kiran layin Tamu yayi bayan ya Waga wayar sai ya mi?o mun muka gaisa tare da yi mun barka. Daga ?arshe ya haWa ni da Ayashe itama tayi mun barka tare da faWin.
"Kayan fitar sunan ?an biyu dana Maman ?an biyu yana wuyana in sha Allah. Ana gobe suna zan tawo in zo ayi komai dani." Dariya nayi nace.
Muna godiya Ayashe Allah dai ya bar so da ?auna, mun gode ?warai" Mu kai sallama na mi?a ma Gwadabe, nan Tamu yake sanar mishi ya Wauki nauyin rago Waya. Mun yi farin ciki matu?a gaya.
Sun jima a falo muna hirarmu gwanin ban sha'awa daga ?arshe su kai mana sallama, suna fita muma muka tafi kwanciya.
Haka dai ranaku sukaita tafiya, duk da kauce ma rikici da dangina suke yi sai da akayi rikici a tsakanin Anty Mulka da Yaya Haula. Wai an ji?a tsakar gida da ruwan wanki, shine fa Yaya Haula tai ta zage_zage tun su Anty Mulka basu tanka ba har suka tanka. Akaita gwabza rikici har sai da manyan unguwa suka shigo akaita basu baki tukunna. Ni dai ranar naci kuka sosai sabida Babala har Waki ta shigo ta ?aremun tanadi tas. Har ta gama babu wanda ya tanka mata, sai da tayi mai isarta ta fita. Ana gobe suna da yamma sai ga su Gwadabe da raguna ti?a _ti?a guda biyu sun Waure, da kayan cefanen suna ni?i_ni?i. Daf magriba Ayashe ta ?araso da yaranta biyu. Gaskiya ta gwangwajeni da ?an biyu sosai. Shadda ta Winka mun taji aiki sosai, harda mayafi da takalm. Taiwo kuma bulawus mai tsada ta siyo mata irin mai takalmi da abun kai na yara, Kahinde kuma riga da wandon jins ta kawo mishi. Godiya na dinga yi mata. A ranar Bose, da Kauliya, da Anty Mulka a nan suka kwana.
Washe gari asubar fari aka shiga aikin abinci. Da asubar Burodami Debisi ya kawo mana nama cikin leda mai zane, Burodami kokodeen kuma ya turo masu rumfa suka kafa runfuna biyu da kujeru. Yasa yara suka shigo da koka kola kireti huWu. ?an uwa masu daWi, ?an uwa abun wuya wannan ya kawo nashi wannan ya kawo nashi sai kaga ashiri ya rufu ruf, a gaskiya ba yabon kaiba muna da hadin kai sosai.
A ?ofar gida suka kafa murhun girki, masu Amala nayi, masu yin jallof nayi, ga nama jingin anata yankawa ana soyawa, wasu suna gyaran kayan miya. Tun asussuba ni da ?an biyu muka yi wanka, ina Waki a zaune Bose tanai mun kwalliya ta kece raini. Ba yabon kai ba mu yarbawa mun iya kwalliya da sanin darajar kaya masu tsada. Domin mazan yarenmu basu san siyama mace ?aramin zani ba, ko ashobi zamu fitar muna zaSar mai tsada mu fitar. Domin matan yarbawa har adashe akeyi na musamman domin kece raini, ko wacce mace tana son asan mijinta na kulawa da'ita. Ko ni duk talaucinmu tun cikina na wata Waya nake zubin dashi a shagon Iyaa Beji me shagon atampa da lace ta bakin layinmu. Da kaWan_kaWan na tara kuWin les Waya, sai naci gaba da tarawa, in ?an uwana sun kawo mun ziyara sun ban kuWi a ciki zan zari wani abu in zuba dashi, da haka na sake tara kuWin leshi na karSi lace biyu iri Waya na bayar da Winkin nawa a wajen Yemi, na gwadabe da Toye na bayar a shagon Winkin maza. Lace Winne a jikina tun sassafe nasa aka mi?ama Gwadabe nashi shi da Toye dan tare suke kwana a Wakin zaure. Sar?a Bose ta saka mun a wuyana.
"Wannan karon mai gidanki yayi ?o?ari ba kamar lokacin haihuwar Toye ba. wannan lace Win da sar?ar babu laifi ba sui arha da yawa ba, ba sui tsada can can ba. Ga raguna manya_manya"
Harara na doka mata, ta kwashe da Dariya ta doki kafaWata. Dole nima na murmusa, dan Bose a lokacin da nake cikin matsi a gida sakamakon soyayya da Gwadabe, a wajenta kawai nake samun sauki. Yaya Haula ce ta shigo Wakin da sallama tana wani gatsine, ta sha kwalliyarta da wata shadda mai mai?o tayi kyau sosai, dan Baban Nazifi yana ?o?arin sosai a kan iyalanshi, bama su kaWai ba harda iyalan ?annenshi. Turus tayi data ganni na fito shar dani kamar ba ni ba, ba wata kwalliya bace a fuskar tawa ba, hoda ce sai jan baki, sai kwalli da Bose ta ziraramun, ko ja gira banyi ba sakamakon akwai gashi sosai a girata. ?an kunne da sar?ar da Ayashe ta tawo mun da'ita ta ba da gudunmawa sosai wajen ?awata kwalliyar tawa, sannan dinkin buba Winkine dake fito da kyawun ko wacce irin mace, musamman masu jiki duma_duma irinmu, kwalliya da ado na fito da masu ?iba ainun.
"Iyabo gashi kayan yarinya na Sangaren dangin miji." Ta dangwararmun da leda mai zane_zane. Kafin in yo godiya ta ?ara watso mun mugun kallo tace.
"Na ga anata aiki babu wacce ta bu?aci ganinmu a wajen. Amman ki sani duk tsiya dangin uba sun fi power fiye da dangin uwa. Amman ke kinfi son duk abunki ?an uwanki su tsaya a wajen, dan ku aikinku kenan ?abilanci, tunda kika haihu ake yare a gidannan dan masifa."
Murmushi nayi dan har ga Allah bana son cusa ma zuchiyata ba?in ciki a irin wannan rana mai albarka.
Ai bansan basu neme ku ba Yaya Haula tunda ni bana wajen."
Jijjiga kai tayi tace
"Ai ba zaki sani ba tunda dai Gwadabe shi ya baki ?ofar raina danginshi. Babala tana gidannan a kasa zuwa a kiramu mu kama aiki a matsayinmu na dangin miji, ai shikenan hausawa na cewa sai bango ya tsage ?adangare ke samun mafaka."
Tana gama faWar haka ta fice fuu kamar kububuwa. Ajjiyar zuchiya kawai na sauke na jawo ledar data dire mun. Riga ce ?ar Wari uku uku guda biyu ta mace da na namiji, sai sabulu sanda biyu da omo mudu Waya shikenan abinda ke ciki. Bose ta ri?e baki tace.
"Wannan kayan shine kayan dangin miji ke da kika haifa musu ?an biyu? Lallai Anty Iyabo dangin mijinki basa ?aunarki..
Ya isheni Bose ki barni in ji da abinda ke damuna dan Allah." Ina faWar haka na mi?e zuwa uwar Waki, na tarar da Ayashe tana shirya Taiwo da Kahinde sun fito sun yi kyau sosai. Dubana tayi tana dariya tace.
"Kai masha Allah mai jego kin fito shar dake kamar ba ke ba." Dariya mu ka yi dukkanmu. Simbi ce ta shigo ni?i_ni?i da buhu ta dire a gabana, Sai ga Taufiq shi da Lekan suma sun shigo da ghana most go. Yaran Burodami kokodeen ne Taufiq, Lekan kuma yaron Iyaa Kokodeen ne, Simbi shekararta goma sha takwas haka, wannan shekarar ta game sakandare Winta. Taufiq kuma yarone shekararshi sha biyu, yana jss 2. Lekan kuwa saurayine
Buhun sobeniya ne na robobi, da kofuna, mafificin roba, moWa da sauran kayayyakin roba mai manne da sikitar dake Wauke da sunan Taiwo da Kahinde. Wanda ya Wauki nauyin yi naga an rubuta Burodami Debisi Adebayo. Ghana most go Win kuma sha?e take dam da kayan jinjiraye da atampopi , omo, sabulu da su nabkin. Hawayene ya gangaro a kumatuna mahaifiyata na tuno tana can ?ungurmin daji, babu waata hanyar da za'a iya sanar mata na haihu balle itama tazo ayi komai a gabanta. Duk da bani da maraicin uwa sam balle uba, Iyaa Debisi itace makwafin uwa a gareni, Burodami Debisi kuma shi ya zame mun makwafin uba. Shi yaita Wawainiya da rayuwata har tasowata yanzu ma da nake gidan mijina bai fasa turo mun abun alkhairi ba, kuma yana kawo mun ziyara lokaci zuwa lokaci, duk da matarshi na tsananin tsantsar kishin kulawar da mijinta yake bani, sabida ala?ar data tafa gibtawa a tsakaninmu na soyayyar da Allah bai nufi shine uban ?a?ana ba. Kafin ?arfe takwas na safe tuni an gama girki tsab an zuzzuba a kuloli, An yanka raguna harma an gyara kayan ciki, kayan cikin dabba Waya nace a mi?a ma su Babala su soya da kansu kar suce an musu coge. Abinci ma ni da kaina na tsaya saida aka basu duk abinda ya dace, har sobeniyarsu nasa an cire musu Anty Mulka da Uwani suka kai musu har Wakin Yaya Haula. Takwas da rabi Alfa Abdulsallam Abdulganiyu ya iso, ?ofar gida, zuwa lokacin ?an uwa maza da mata duk suna waje a cikin rumfa a zazzaune. Gwadabe ne ya ratso cikin mata yana saye da leshi da hular ashoke, Kahinde ya ri?e Ni kuma ina ri?e da Taiwo, Ayashe da Sakina ne suka mara mana baya har zuwa ?ogar gida inda Alfa Abdulsallam Abdulganiyu ya soma wa'azi. A gabanshi muka gurfana, ya soma ragargazo ma ?an biyu adda'a tare da ro?a musu alkhairan duniya dana lahira, tare da samun nasara gami da rayuwa mai tsayi, mai albarka. Duk wannan cikin yaren yarbanci yake yi, yanayi da wa?a dukkanmu muna amsawa da.
Ameen" Muma cikin salon rerawa kamar masu wa?a. Yaran muka mi?a mishi ya shafa kansu yai musu adda'a ya mi?o mana su. Sannan ni yai mun adda'ar samun lafiyar shayar dasu cikin lafiya, Gwadabe kuma yayi mishi adda'ar samun tagomashi ta yanda zai ciyar dani lafiyayyen abincin da zan raini yarana cikin ?oshin lafiya. Iyaa Debisi ta fito itama tayi nata addu'o'in, aka mi?a ma Babala abun magana, "Allah ya raya su da imani" Kawai tace shima sabida idon mutanene da taga sun yi yawa a kanta. Iyaa Kokodeen itama ta yi nata, su Burodami kokodeen da Burodami Debisi duk dai kowa yayi nashi.Daga nan kuma akayi adda'a kowa ya shafa. Sai Bose ta Wauki kwano ta dinga bin mutane Waya bayan Waya sunata zuba kuWi, mu kuma muka koma cikin jama'ar suna. Dangina rankatakab Winsu ankon atampa mai ruwan kunun kanwa ce a jikinsu maza da matansu. Abinci aka soma rabawa masu kalangu kuma suka amshe fagen. Haka dai akaci gaba da gudanar da shagalin suna bamu muka tashi ba sai ?arfe biyun rana. Daga nan kowa ya watse, duk wani gudunmawa a wajen aka bani, sai da muka cika bahun biyu da kaya da atampopi, kuWi kuwa na same shi sosai ?an biyu sun yi goshi sosai. Bayan mun koma gida sai na sake wanka na kwalliye da shaddar da Ayashe ta bani na fito shar dani. Sai lokacin na samu nutsuwa naci abinci na ba ?an biyu nasu abincin. Kafin la'asar har an gama soye naman suna tas Anty Mulka ta ?u??ullama duk waWanda suka dace, ni dai da Gwadabe cikin ?aramar samira kawai muka tsira dashi a matsayin rabonmu. Ragon Waya sukutum aka ba su Babala, Wayan kuma ni da ?an uwana duk muka rataya akai, wanda na samun ma Babala ta aiko laraba wai in ?ara mata nama ?awayenta na Takai basu samu ba. Dan haushi samirar duka na mi?a mata na yi kwanciyata dan in Wan huta.
Washe gari Ayashe ta Wau hanyar garinsu, da rana su Sakina suma suka wuce. Uwani dasu Bose ne suka gyara mun ko'ina su kai mun girkin dare kafin magriba duk suka watse Wakin daga ni sai ?a?ana misalin taran dare sai ga Gwadabe ya shigo furkarshi Wauke da fara'a, nima murmushi na sakar mishi.
MRS BUKHARI


3064127935
Buhari Ibrahim Ladan
First bank

Sanya nera 500 Winki kuWin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan.
Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun
Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. ?ar?ashin Amila Foundation gidauniyar da muka buWe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya.

WaWanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ?ANYE)
300 kacal zasu iya kuWin karatu
NAMA YA DAHU....
ROMO ?ANYE
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

INA MI?A SA?ON GAISUWATA A GAREKU.

KHADIJA MAIDOKI
MRS BASH
MAMANMU (HAJARA ALIYU)
MAMAN SAFWAN
ANTY YABI YUNUSA JIBRIN ( AZARE)
MAMAN ANNUR
KHADIJAN MAKAWA
UMMU NABEEHA
MAMAN YASEER
SISTER FARIDA ( ?AWAR UMMU NABEEHA)
MAMAN MUHSEEN
RU?AYYA YAWURI
UMMU AFFAN ABUJA
UMMU AFFAN SADFAT
RAMLEX
MMN LAMIDO
MAMAN ABDULRAHMAN
INNAR BASMA
ANTY ZEE MUSA
A.A NAFA?A
MAMAN INTEESAR

KUNA DA YAWAN DA BAN ISA JEROKU A PEJI ?AYA BA, A BOYONI BASHI DUK ZAN ZANA SUNAYENKU, INA ALFAHARI DA MASOYANA NA FA?IN DUNIYA.


( JIYA WATA BEYERABIYA TA KIRANI A WAYA TAKE CEWA DANI TANA BIBIYAR LITTAFINA, KUMA TANA JIN DA?INSHI SOSAI. SOYAYYAR GWADABE DA IYABO TA BURGETA, KUMA ITAMA HAKA TAKE FUSKANTAR ?ALUBALE A CIKIN AURENTA. ITA KANURI TAKE AURE TANA BEYERABIYA)





Lamba ta bakwai (7)



Saye nake da doguwar rigar leshi, Waya daga cikin kayan da aka bani a gidan aiki. Toye na kwance a kan bargo a ?asa yana bacci. ?an biyu kuma suna kan gado suna baccinsu sun sha overoll farare tas. Yaran ya zuba ma idanu da kyau sai murmushi yake faman yi. Zama yayi a bakin gadon ya Wauki Taiwo dan tafi kusa dashi. Zama nayi ina fuskantarsu yayi kyau da yarinyar a hannunshi.
Rabon yarannan ne yasa iyayenmu suka amince da aurenmu bisa dole, dan wannan rabon ka iya ajalin duk wanda ya kafe ba zamu auri juna ba. Gwadabe ina alfahari da aurenka, ina alfahari da soyayyarka gareni. Hakanne yake sa in mance da kyara, tsangwama, ko ?yamata daga danginka. Domin kai kam ka zame mun komai, ka cike duk guraben dake da giSi a rayuwata madallah da samun miji nagari irinka"
" Ifemi ( masoyiyata) Na g???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ode da soyayyarki, ina jinjina juriya gami da ha?urinki, samun mace irinki abune da sai an tona shi a wannan zamanin, musamman a ?abilarku da matan yarbawa suke da zafin rai da saurin faWa. Mala'ikun Allah ku shaida ni Gwadabe na Waga ?afafuna Iyabo ta shiga aljanna, ku sake shaidawa ita da kishiya sai ta gidan aljanna, a can ma itace shugabar su " Dariya mu ka yi dukkanmu kafin ya ja fasali yace.
"Ina da tarin tulin tambayoyi kin shirya?"
Ahaf ni dama nasan ba zaka barni ma zuwa gobe ba. Tambayeni in baka amsa, amman kafinnan bari in kawo maka abinci, kana ci kana kora koka kola zai fi. Mi?ewa nayi abincin na gefen sib a tiran silver Wauke da duk abun bu?ata. Tuwon shinkafane miyar bushasshen karkashi wacce ta ji kayan cikin rago, iyakar kayan Cikin miyar shine iyakar rabon da muka samu a raguna biyu ti?a_ti?a. Zuba mishi nayi na matsar gabanshi, Ajjiye Taiwo yayi tare da sakkowa ?asa, ya tan?washe ?afarshi yanata kallo ina hidima dashi. Lomar tuwon farko a bakina ya sauke mun, tare da yankan saifa.
"Bani labarin tv da kafet tukunna, dan dasu na soma cin karo" Sai da na saisaita nutsuwata, na sake tausasa muryata kafin nace.
Burodami Debisi ne ya sake ma Yemisi kayan Wakinta, shine ya bibbimu da tsofaffin"
Kafeshi da idanu nayi ina karantar yanayinshi, dan Gwadabe bashi da daWi sam ta wajen kishi. Ya zafafa kishinshi sosai akan Burodami Debisi. Alhalin shi babu ni a zuchiyarshi sam, bana mance lokacin da Iyaa tace zata haWa aurenmu ayi tuwona maina. Har hawaye Burodami Debisi yayi ma iyaa dan ta tausaya mishi ta janye maganar auren. Ba dan ?iyayya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login