Showing 69001 words to 72000 words out of 270738 words

Chapter 24 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

Cikin raha dai mu kaita hirarmu har ya kammala cin abincin nashi. Kana nayi mishi sallama na tafi.
Sai zuwa washe gari na haWu da su Burodami kokodeen da su Burodami Debisi. Kuma na zagaya gidajen nasu naga yaransu, na gaisa da matansu. Yemisi dai babu yabo ba fallasa, dama ya lafiyar kura ballantana tayi hauka. Haka dai akaita mana shirin tafiya, dan har munje anyi mana gwaje_gwaje iri da kala a asibiti. Ana washe gari zamu tafi ko bacci na kasa yi dan dadi, da kuma wata fargaba data lulluSeni. Burodami Debisi, da Yaya Hamma, da Hafizu sune abokan rakiyar tamu har zuwa filin jirgi, ko ince Wakin jira. Gefe guda muka keSe da Yaya Hamma da jikinshi naga har rawa yake yi, idanuna a cike da ruwan hawaye. Naso Yaya Hamma ya furta mun kalmar so kafin in tafi ya jaddadamun matsayina a zuchiyarshi. Amman kunya da ?auyanci ya danneshi. Haka dole mu kai sallama ba tare da naji inda soyayyarmu ta kwana ba. Ko da muka shiga cikin Bus Win da zata kaimu gaban jirgi ai sai na sake fashewa da kuka, ina tunano fuskar Yaya Hamma, da yanda yake ta aukin jaddadamun al?awarinmu. Burodami Debisi kuwa kamar ya sha?o Yaya Hamma ya rufeshi da duka haka yake ji. Gurin dake Waure a shintsiyar hannunshi daya bani na sake dam?ewa a hannuna.
Yau ni Iyabo gani a cikin jirgin sama zai tashi damu zuwa ?asa mai tsarki. . Hukunci sai mai tsaga idanu. Allah sarkin girma in ji kishiyar mai duwawu.


MaraWi

Gwadabe:.
Auwala bai dire Sabitu a ko ina ba sai a gaban malam, ga almjirai cike da wajen. Tun kafin Malam yayi magana. Baba Asshi ta fito babu ko mayafi a jikinta. Kallon da taga gardawan Malam Magaji na yi mata ne yasa ta koma daga zaure.
"Auwala wannan wanne irin ri?o kayi mishi kamar ka kamo barawo" Malam ya girgiza kanshi yana bin ?ofar zauren da kallon ba?in ciki. Baba Fhatsima ce ta fito saye da katon mayafinta ta jaye Hadiza tare da cewa.
"Koma me ya faru a barshi a tattauna a cikin gida. Auwala cikashi, kai kuma Sabitu jeka abinka. Allah yayi muku albarka baki Waya. Hadiza ta jawo suka shigo zauren Baba Asshi ta harareta sama da ?asa tace.
"Ni nawa yaran sai ki tsine musu ai, tunda naki kika sama albarka. Ni na ji jaraba fa, kun bi kun sani a gaba Fhatsima kin hana mun jin daWin aure" Baba Fhatsima Taso tsaiwa ko wacce zata hanata bacci ta feso mata. Auwala sai ya kama hannunta suka shige. Su kuma su Gwadabe suka wuce barayinsu dan watsa ruwa su ji daWin jukkunan nasu. Gwadabe yana wankannan yana tunanin me yasa gida in da mace sama da Waya ake yawan samun rabewar kai ne. Ta ina kuma matsalar tafi rinjaye tsakanin matan, ko uba da yake zama majingina a wajen mata da yaran gida.?
Da wannan tunanin ya fito. Fitowarshi ke da wuya Ine tazo ta yi kiransu gabaki Waya harda Gwadabe izuwa turakar Malam. A babban falonshi duk suka gurfana Malam ya soma magana da cewa.
"A wannan karon duk macen data nuna zata kawo mun rabewar kan ?a?a ni zan iya sallamarta ta tafi gidansu. Allah yana gani daidayya ina bakin ?o?arina dan ganin nayi adalci a tsakanin matana harma da su yaran nawa. Ke Fhatsima kece Babba a gidannan na faWa ba tun yanzu ba zan haWe kan yarana da matansu dukka a gida Waya dan su rayu tare yaransu su cuWu da juna ta yadda zasu sha?u da junansu. Wannan magana tamkar a rubuce take ba fashi. Duk da Asshi ta nuna ita bata bukatar a haWe yaranta dana Fhatsima. Harma Jamilu ya goyi bayanta a kan hakan. Rikicin Sabitu da Hadiza ne yasa na dawo da wannan maganar baya. Nasan ko wacce nayi mata bayani ita kaWai Amarya malam uwar kissa ta dubeshi da taushin murya tace.
"Allah shi gafarta malam ni nawa yaran da suka kasance ?ananu ya za'ayi dasu to?" Dariya malam yayi cikin so yace.
"Amarya harda su Rabi'u za'ayi wannan ginin. Su kuma mata _matan da zasu yi aure ko wacce zan bata kadara a matsayin kyauta, kanana marasa aure kuma sai in ajjiye musu zuwa lokacin da Allah zai ?adarta su yi aure. In kuma ta Allah ta kasance a kaina sai a dan?a musu baya cikin gado na basu halak malak, hatta ginin da Shi Tasi'u zai musu baya cikin gado na mallakawa kowa halak malak harda Gwadabe dan gudun kar in kwanta dama tashin tashina ta tashi. Dan kuna ganinane kuke samun damar faWace_faWacen nan da kuke yi. Wallahi duk ranar da za'a wayi gari bana doron ?asa zaku yi dana sani, za kuma kusan mahimmancina. Zaku iya tafiya" A lokacin dai jikkunansu duk ya mutu, amman kowacce tana jaye ?a?anta suka shige ?urya sai labari yasha banban. Wannan kyauta da malam ya furta bata cikin gado itace ta tayar da ?ayar baya, ba?in ciki da hassada ya shigo, musamman ga wadanda basu da damar cin tudu biyu. Haka bikin yaran gidan yaci gaba da matsowa, sai shirye_shirye aketa ta faman yi kowa ta ciki na cikinta. Yaya Tasi'u da matarshi Anty Badi'at ba zama, dan ita ta shiga cikin nijer ta siyo kayan gadajen Amare da kayan kitchen ita da Amaryar Malam. Kwana bakwai da Baba Magaji ya ba Gwadabe ta cika, Baba Magaji baice komai ba, shima Gwadabe ya?i cewa komai, zuchiyarshi kullum cikin taraddadi take kawai, har aka tsunduma sha'anin biki dai Baba Magaji na kallon Gwadabe ya zuba mishi idanu.
To al'adar auren Maradi ya banbanta da al'adar aure a Najeriya ?asar hausa. Su yanda suke bikinsu shine.

*KAN GORO*
Shi yanda ake yinshi shine. Iyayen Ango zasu tawo da goronsu a jarka za'a daddaleshi, yana danganta da yanayin karfin miji. Zasu tawo da balis ( Akwati) wasu suna zuba kaya a ciki, wasu kuma basa zubawa, zasu tawo da kuWin sadaki, da hidimar girke_girke rigi_rigi.
Iyayen Amarya maza su kuma zasu zauna a manyan taburmai domin tarbar iyayen ango da wannan kaya. Iyaye mata a gida kuma zasu yi girki na alfarma a fito dashi. Anan za'a tsayar da lokacin Aure da bai haura wata guda ba, wasu ma sati guda ya danganta. To su dangin Ango zasu tafi da wannan gara ta dafaffen abinci tare da tsayayyen lokacin Aure.

*LIFARAN*
shi kuma lifaran ( Anko) ake nufi. Daga kawo wannan kayan aure da kuWi. Dangin Ango, da dangin Amarya sai su fidda Ankon biki.

*LALLE*
Amarya zasu zauna zaman lalle na kwana biyu ita da ?awayenta.

*KU?IN SIGA*
Shi kuma kuWin siga kuWine da dangin Amarya suke hidima dashi ma dangin ango. Akwai kuWi uwa ko kuma ai mata kaya, da su saitin bahuna, da turmin zani na goyo. Shi wannan setin bahunan da turmin zani ana bayarwane a matsayin an mayarma da uwa zanin goyo da bahunan wankan Ango lokacin da yake jariri, da sontolon tsaba duk na uwar miji.
Sai buhunhuna hatsi na gara bana wasa ba. Hatta facala in amarya na da shi akwai kudinta, kudin abokan ango na zirga_zirgar biki, sai buta da Dadduma, da jikka biyu na kudi na uban miji. Baki ?an nesa kuma da suka tawo biki, ana zuba tsaba a roba da turamen zannuwa a basu. Su kuma sai su ba da jikka goma na uwar Amarya a matsayin tukuicin wannan hidima

?AURIN AURE.
Su kuma da safe akeyin Wauri in dai na budurwane. Sannan ana fitarma da maza ?an Waurin aure abinci waje aci asha a goge wuya.

*WATSI*
Wannan Sangaren gidan ango ke yi.
Bayan isha ko bayan magriba za'a shinfiWa tabarma a zaunar da ango a tsakiya. Ai ta mishi watsin cingom da kudi shima ya danganta da ?arfin dangin ango, amman a wannan watsin ango na samun kudi ainun.

?AUKO AMARYA
Bayan an gama watsi kuma dangin Ango zasu je su Wauko Amarya a kaita Wakin mijinta.
Iyaye suna yin hidimar kayan Waki sosai, gado biyu suke yi, banda kafet_kafet da manyan daddumai.

*YININ BIKI*
Shima bikine rigi_rigi ake yinshi, sannan a yinin bikinnan suke sa anko dangin ango dana Amarya. Ayi yinin biki a watse shikenan biki kuma ya ?are.

Daga cikin wannan sha'ani na biki babu wanda aka raga. A zahirin gaskiya an kashe kuWaWe sosai, duk wata hidima da akayi Tasi'u da matarshi ce suka gudanar da duk wani kashe kuWi.
Gwadabe kuma a lokacin sha'anin bikinne ya karema ragowar ?an matan gidan kallo tsab. A tsahirance sunfi Hadiza kyau ta fuskokinsu, sai dai ita kuma Hadiza ta fisu diri da kiba, dan shi kuma baya sha'awar mata sirara sam. Da wannan dalili nashi ne ya ?udurce a ranshi da zaran an watse biiki zai tunkari Baba Magaji da batun Amincewarshi ga Hadiza. Ga Tamu ko da yaushe su kai waya yakan yi mishi tuni da batun ?anwarshi da take zaman jiran Gwadaben. Harma sun yi waya sau biyu haka. Yanda ya Wan taSa hira da'ita sai yaji babu dai wata matsala a tattare da'ita ko na rashin tarbiyya, ko na fitsara irin ta wasu matan. ?arshen wayarshi da Tamu a cikin hidimar bikinnan yake cewa da Gwadabe.
"Gwadabe duk Wan abinda ka rarumo na kudin moya kazo ayi aurennan kowa ya huta. Bara'u yace ya Wauke maka sadaki. Ni kuma zanyi mata akwati da kaina. Aure kawai zaka zo a Waura, sabida manema sun soma damunta, duk da dai bata ?arashe karatun ba amman ?iris ya rage' Jin wannan batu ne yasa Gwadabe kiran Bara'u yai mishi bayanin halin da yake ciki akan Wiya da Baba Magaji ya bashi harma da kyautar wajen zama. Bara'u shi kuma ya tafi kafa da ?afa har Habuja su kai magana da Tamu. Ya nuna ai wannan ba komai bane, Gwadabe mijin mace huWu ne bama biyu ba. A take suka kirashi suka tsaida magana kan da zaran yarinyar ta gama karatunta za'ayi auren. ?an biyu dake hannun Tamu sai wayau suke yi, suna karatunsu hankali kwance. Ayashe tana ri?e dasu da amana ta game yaran da nata ta maishesu tamkar yaran data tsugunna ta haifa. Haka ma Toye yana zuwa makarantar boko data allo, suna zuwa gona yin noma. Dan Bara'u ya siya musu ?ar ?aramar gona da yaron wajenshi, harma bana sun noma gyaWa na kwano uku, da taimakon Sakina dake rakasu gona tana kuyi wannan ku bar wancan
Amare sun tare a gidajen mazajensu lafiya, hankalin iyaye ya dawo jikinsu kuma kowa ya ci gaba da sha'anin gabanshi. Wata ranar talata da daddare bayan su Gwadabe sun gama karatun dare sai ya nemi ganawa da Baba Magaji kan batun Hadiza. Dan yaga tun bayan da aka yi bikin gidan. Sai zawarawa suka shiga zurubtu akanta, suka shiga hidimar kashe mata kudi. Dan samarin nijar jaruman gaske ne akan matansu.
"Baba Magaji dama akan maganarmu ne da kai. Shine nace na zaSi Hadiza kamar yadda kaima ka zaSa mun tun farko. Sai dai akwai ?anwar abokina Tamu da shi Tamun ya bani tun kafin in tawo nan Win. Shine nake tunanin in ka amince sai a haWa tare ayi bikin lokaci guda. Tunda ita yarinyar kafin lokacin da aka kintata na bikin zata kammala karatun da take yi." ?ur Baba Magaji yayi yana kallonshi ya jima baice komai ba yanata jujjuya maganar Gwadabe a kanshi. Yana kuma hango irin gagarumar matsalar da ka iya bullowa. Wanda ada ita ya guda, sai gashi ta kuma biyoshi.
Bayan dogon nazari da Baba Magaji yayi sai yace.
"To Gwadabe naji duk bayaninka. Kuma na gode da nuna sonka da auren Hadiza. Wani hanzari ba gudu ba Gwadabe. Hadiza macace mai Wan banzan kishi ainun. Kaga kishi? Shi ya hallaka igiyoyin aurenta na baya. Abinda yasa na soka da Hadiza, yarinyace mai biyayya batta da kishi dai. Nayi tunanin kuma ba lallai ka rakito wani auren nan kusa ba, duba da sana'ar taka ma da kake yi har yanzu baka da ido akanta. Kila ko da zaka yi auren sai nan gaba, kila a lokacin Hadiza ta zama babbar mace ka samu sassauci. Kaga mahaifiyarta ko? A lokacin dana auro Asshi sai da muka shafe tsawon shekaru biyu da rabi bata haWa shinfiWa dani ba. Kai ?afarta bata sake taka turakata ba, har sai da santa yaimun lahanin da ya kusan rabani da rayuwata kafin. Gwadabe ina son Fhatsima fiye da yadda kake tunani, kuma ina matukar girmama duk lamarinta. Bata taSa yin hayaniya ko musu dani ba.
Shawarar da zan baka shine. Kaje ka auri ?anwar Tamu Win, ita kuma Hadiza Allah ya fito mata da wani mijin. Gudun kar zumunci ya taSu dukkanku ?a?anane. Tashi kaje Allah yai maka albarka".
Gwadabe yaso Baba Magaji ya bashi dama yace ko da wani abune. Amman sai ya ki bashi wannan damar haka dole ya tashi ya tafi. Kuma tsakani da Allah Hadiza ta kwanta mishi fiye da yanda ?anwar Tamu ta kwanta mishi. Dukkansu a cikinsu baiga na ajjiyewa ba, abu suka haWe mishi goma da ashirin, ga tunanin Iyabo wanda yake Wamfare a zuchiyarshi babu dare bare rana. Da Hadiza yaci karo a zaure zata fita taci kwalliya da bakar lafaya ta zubo gashinta gaba. Murmushi ta sakar mishi da ganinshi. Shima yai mata murmushin tare da cewa.
"Sai ina da wannan kwalliyar kamar zaki gasar sarauniyar kyau?" Dariya kalaminshi suka bata, sai da ta dara kana tace.
"Sallama akeyi dani a waje Yaya. Bansan ma ko waye ba" Sai yaji nan nake kishi ya lulluSeshi dan ai Gwadabe gwanine na ?an kishi mun sani tun a baya. ?in magana yayi da yaga tana shirin wuceshi ne yace.
"Ke daga an aiko ana kiranki sai ki fito harda caSa kwalliya haka? To maza ki koma Baba batai miki bayanin suna son haWamu aure bane, ko ni dinne bakya so talaka?" A zabure ta Wago ta kalleshi cikin maWaukakin mamaki. Shi kuma yai tsai yana karantarta. A madadin yaga damuwa sai yaga akasin hakan. Dan bata san sanda ta kwashe da dariya ba, ta juya ta shige gida da sauri halamar dai itama fa tana ra'ayinshi yayi mata.
Kanshi ya dafe tare da jin haushin kanshi kan furta wannan kalma mai nauyi. Tsoronshi Allah, tsoronshi kar sanadiyyar aurensu zumunci ya taSu. Dan ?asan zuchiyarshi gurbin son iyabo ne, tsakiyar zuchiyarshi kuma na ?a?anta ne. Ko wacce irin macece zata rayu dashi sai dai ta rayu dashi a saman zuchiyarshi. Yana tsoron rashin adalci, yana tsoron fitinar mata biyu da rabe_raben kan ?a?a irin na gidan Baba Magaji. To wacece ta cancanta Gwadabe ya aura a cikin mata biyunnan? Wani shashe na zuchiyarshi yace.
"Ka ba ko wacce daga???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? ciki lokaci ta fayyace maka irin sonta, a ciki sai ka zabi guda, guda kuma ka bata ha?uri. Cikin rashin tunanin abinda hakan ka iya haifarma Waya daga cikin matar da za'a ba hakuri Gwadabe yai na'am da shawarar zuchiyarshi ba tare da yayi hangen nesa ba. Wannan shi ake kira nama ya dahu romo Wanye.
Nan Gwadabe ya raba lokacin shi ta hanyar rabashi a tsakanin Hadiza, da Shafa, Hadiza suna keSewa suyi zance, yayin da Shafa kuma yake kiran wayarta su sha hira. Yana auna kalaman ko wacce a zuchiyarshi, yana nazari dan gano wacce tafi sonshi da nuna tausayinshi. Tun Baba Magaji bai san Gwadabe na zance da Hadiza ba har mata suka tsegunta mishi. Kuma Baba Fhatsima, da yaya Tasi'u, harma da su Auwala sun aminta da wannan haWin kuma sun yi farin ciki sosai. Baba Magaji ranar yaso su tattauna da Baba Fhatsima akan batun Hadizan da Gwadabe, kasancewar ranar ita ke da miji.
"Fhatsima naga kamar Hadiza ta amince da soyayyar Gwadabe ko?" Ya jefo mata tambayar yana daga kwance, ita kuma tana kasa a zaune tana dama mishi furar da duk daren duniya sai ya sha kafin ya kwanta.
" Kwarai ko. Nima kuma na daWa ?arfafarta naga Gwadabe yana da hankali." Kai Baba Magaji ya gyaWa yace.
"Hmm Hadiza kenan. To abinda ta guda a gidan uban yaranta shine ya sake biyota. Kishiya ba? Dan abokin Gwadabe Tamu ya riga ni ba Gwadabe ?aunarshi, kuma ya riga ya karSa tun kafin yazoshi. Ni da naso dakatar dashi neman Hadiza dan harna sanar dashi dalilin mutuwar aurenta na baya. Amman bamu san me Allah yake son nunawa ba akan hakan, ?ila wata ayar zai saukarma mata masu kaso aurensu sabida kishiya. Allah ya daidaita tsakaninsu" Shiru Baba Fhatsima tayi kawai. Furar da take damawa ta dakatar da damata. Lokaci guda ta jagule. Hakan yai sababin sawa Baba Magaji ya mike zaune ya sakko ?asa daf da'ita. Yayi ?asa da muryarshi yace.
"Fhatsima kiyi ha?uri a bisa kalamina. Allah ya sani ba dake nake yi ba, da ita Hadiza nake yi. Amman kiyi ha?uri"
"Hmm Malam kenan. Ashe nuna kishi ga abinda kake so matsalane a wajen maza mu bamu sani ba? Tunda nake kishina a gidannan tsawon shekaru fin talatin ka taSa kamani ina shirka, ko na taSa tayar maka da hankali ne?
Ai ko Hadiza batai kishi na hauka a gidan mijinta ba. Allah yayi ?arewar aurenne dan ku maza in kuka auro wata macen kukan juyama wata baya na wani lokaci kafin ku gama shan romonta. Abunda Hadiza bata da ilimi akai kenan shi yasa aurenta ya mutu a wannan gaSar. Amman Nagode da wannan furuci naka" Ta ?arashe maganar tana shesshe?ar kuka mikewa tsaye tayi tana shirin barin Wakin. Malam yayi carab ya cafe hannunta. Tayi sauri ta runtse idanunta tare da fashewa da wani irin kuka mai Waci. A wannan daren Baba Magaji ya sha rarrashi da ban baki. Dan har kuWi ya debo da baisan iyakarshi ba ya bata da safe kafin ta koma Sarayinta.
A haka soyayyar Gwadabe da ?an matanshi biyu taci gaba da kasancewa. Ko wacce cikinsu na ?o?arin ganin ta nuna bajintarta. Danma ba wacce ta san da zaman ?ar uwarta, iyaye sun bar zancan a tsakaninsu. Domin shi Baba Magaji a ganinshi Gwadabe ai bazai haWe mata biyu a lokacin guda ya aura ba, dole da Waya za'a soma.
Ta Sangaren neman Gwadabe kuwa, Allah yasanya mishi albarka a harkar neman. Dan yana da ido sosai na ganin zinariya. A zuwanshi har ya samu zinariya sau biyu, kuma ba laifi madaidaita ne. Hakanne ya bashi damar yi ma Babala aike, ita da Bara'u abokinshi na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login