Showing 78001 words to 81000 words out of 270738 words

Chapter 27 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

daddare bayan sun gabatar da mu'amalar aure ba.
"Fhatsima samunki nasarane babba a cikin rayuwata. Wallahi Fatsima jina nake yi tamkar wawa soko muddin bana tare dake. A duk lokacin dana kalli ?wayar idanunki su kaWai ka iya sauke mun dukkannin damuwata, duk girman matsalar da nake ciki. ?an siyasar da muke mu'amala dasu da dama sun sha bani Wiyoyinsu in aura. Amman Fhatsima nasan ni naki ne ke kaWai bazan iya haWa soyayyarki da ko wacce mace ba a faWin duniyarnan da muke ciki ba."
Fitowar Malam ita ta katse mata zaren tunaninta ta dawo duniyar mutane. Ido malam ya zuba mata ?ur, jin kaifin idanunshi yasa ta Wago kai suka haWa idanu. Amman me sai malam yaga kwantaccen hawaye a guraben idanun Fhatsima. Zama yayi a kusa da'ita ya kama hannunta dukka biyu, Wumin tafukan hannun juna ya ratsasu sosai. ?unshinta yake bi da kallo yanda aka jera salateb ( suffa,) akayi ado dashi cikin hikima, lallen ya sake fito da kyawu da hasken hannun nata.
"Fhatsima wannan lallen nawa ne akayi mun?" Ya faWa a mugun raunace dan ji yake kamar yayi kuka. Shi kaWai yasan irin gasuwar da ruhinshi da gangar jikinshi take yi. Itama a sanyaye tace.
"In ba kai ba Magaji wa zanyi ma lalle uban ?a?ana?" A sanyaye cike da kunya yace da mamaki ya dubeta dan yasan in tana cikin yarda dashine har take iya kiranshi da Magaji a keSe, amman dama a cikin mutane da cikin fishi Malam duk take kiranshi."
"Fhatsima yau ni kika kira da uban ?a?anki, kuma kikace domina kikai wannan lallen?" Murmushi tayi tace.
"Magaji ai har yau har gobe ruwa na maganin dauWa" Farin cikine marar misaltuwa ya lulluSeshi.
"Fhatsima nayi kewar kasancewa tare dake, nayi kewar rashin samun cikakken lokaci kamar yadda kika sabarmun, nayi kewar kulawarki, nayi kewar tausasamun da kike yi Fhatsima. Na sani ni nayi kuskuren ruguza amincin dake tsakanina dake. Wanda in kin tambayeni dalili bani dashi wallahi. Nayi nadamar komai, ina takaicin faruwar komai Fhatsima. Hawayene tab a guraben idanunshi, yana ta girgiza kai irin na kaico.
"Magaji cutuwa iya cutuwa nayi, tun daga lokacin da abubbuwa sukaita faffaruwa dauriyaa kawai nake yi, da ba a iya hawan jini abun zai tsaya ba, numfashina zai rabani dashi, in Barka a duniya da matan naka na so" ?an murmusawa yayi kawai. Baice komaiba ta Waura da cewar.
"Na fuskanci wula?anci da matsi wanda ni kaina bansan ina da irin wannan ha?urin ba. Soyayyarka data yaranmu ce kaWai tasa naci gaba da rayuwa da matanka. Burina shine ace da kaina naba Wiyoyinmu tarbiyya a bisa doron al?awarin da nayi maka tun kafin aurenmu. To Alhamdulillah na sauke nauyi"
"Gashi ?a?an da suka fito a Wakinki sun kasance sanyi da hasken idaniyata Fhatsima. Sun kasance abun alfahari kuma jagorori. Wannan kaWai wata babbar nasarace a gareki, kuma hakan ya ?ara tabbatar dake a matsayin shugaba kuma uwar gida a gidan Magaji. Ko wacce mace da ?a?anta, dani kaina Magaji a cikin rigar alfarmarki nake Fhatsima " Idanu ta ?ura mishi tana mishi dariya shima dariyar yake yi.
"Magaji kai da kaya mallakar wuya ne. Kuma ba'a hana ma ba da rago fata, tuwo baya canja sunanshi. Yarannan baka ragesu da komai ba tun yarintarsu har zuwa yanzu da nake wannan maganar.
Fatana Allah ya haWe kan iyalin naka baki Waya. Duk da kai da kan ka ka farra?a haular gidanka, kasan....."
"Ya isa Fhatsima kar ki rusamun farin cikin dake ?unshe a raina" Ya katseta da hanzari.
"Inaso ki tsaya mun kuma ki taimaka mun ke da Tasi'u da Jamila mu haWu mu haWa kan iyalinmu. Abinda ya wuce ya wuce, kece zaki taimaka komai ya gudana. Sannan haWe yaran da matansu ni inata jaddadawa kamar zai iya gyara lamarin. In kan yaran ya haWe, dole iyayen su shafa ma kansu ruwa. Asshi ce dai nasan zata ba da wahala. Ammam fa a shirye nake tsab da in rabu da duk matar da zata kawo mun taurin kai. So nake in gyara abinda na Sata tun da rayuwata kar in bar baya da ?ura." Ajjiyar zuchiya Baba Fhatsima ta sauke. Yayin da take hasko abubbuwan da suka zama sune sababin faruwar waWannan matsaltsalu na gidan Malam. Gani take yi kamar yanzu suke faruwa.
"Baki ce uffan ba Fhatsima" Ya jefeta da tambayar.
"Malam a Wayan biyu ne wannan haWe yaran da kai da Tasi'u kuke ganin zai yi tasiri wajen kawo soyayya da sha?uwa a tsakankanin yaranka. Hakan zai iya faruwa, ko kuma hakan ya sake farra?a kan yaran, ko da ta Hanyar matayensu, ko ?a?an da zasu hayayyafa. Malam wannan lamarin babbane. Amman mu dage da ro?on rabbil izzatu. Gamu a ?asa mai tsarki mu dage da adda'a Allah yasa hakan ya zama matattakalar da zamu hau tsanin da zai wanzar da farin ciki a tsakanin Ahalinka. Sannan sai ka sanya dokoki masu tsanani, kayi ?o?arin dogewa akan dokokin. Kar ka faWesu ba tare da ka basu mahimmanci ba, wannan raunin naka yana Waya daga cikin abinda ya soma kawo rarrabuwar kai a tsakankanin Ahalinka."
A ta?aice dai sun jima sunata tattauna yanda za'a Sullo ma lamarin. Sun yi adda'a sosai. Malam da Baba Fhatsima sun sasanta kansu sai Sarzar Amarci ma suke yi abinsu. Sai yanzu ne Malam ya dawo cikin nutsuwa da hayyacinshi. Ya saki ajjihu wajen ganin ya kyautatama Baba Fhatsima, duk da ragowar mata da ?a?anshi ma bai barsu a baya ba.


Gwadabe.
Ana gobe Gwadabe zai kama hanyar Najeriya. Sun sha hira ainun da Hadiza da ?yar ta barshi ya samu ya shiga ciki yaci gaba da shirya kayan tafiya. Kishine Wamfare a ?irjin Hadiza dan ita gabaki Waya a tunaninta Gwadabe baibai kawai ya ninketa amman wajen Shafa yake son zuwa. Shadda dalleliya da ?an kunne Hadiza ta bayar a kaima Babala, ta bada agogo mai kyau tace ya kaima Shafa. Anty Badi'a kuma ta ba da takalmi da mayafi tace akaima Babala. Yaya Tasi'u kuma kuWi ya bayar akai mata, sai ?arin guziri da yaba Gwadabe. Sassafe kuwa Mammada ya rakashi tashar mota. Motarsu ta Waga zuwa Najeriya. A garin Kano ta dabo tumbin giwa Gwadabe ya sauka. Misalin ?arfe tara na dare dake motarsu ta samu matsala a hanya sun daWe a yashe a titi sosai.
Sakkowarshi daga mota ita ta kara mishi damuwar rasa Iyabo da yayi a rayuwarshi. Gashi dare yayi, kuma bazai taSa iya taka kafarshi zuwa gidan Yaya Hambali ba. Bashi da zaSin daya wuce ya nemi gidan kwana a tasha, gobe sassafe yana son ya le?a gidansu Iyabo ko Allah zai yi ko juna su gani, su gaisa kafin ya tafi.
"Malam muna da Wakin saukar ba?i in kana da bu?ata. In kuma a Kano tafiyarka ta ?are akwai tasi da Bus a bakin tasha zata kai ka duk inda kake bu?ata. Cewar wani Wan yuniyon.
"Inada bu?atar Wakin, Takai zan wuce zuwa gobe da safe dan Allah"
"Nera hamsin kuWin kwana, in bawali zaka yi a banWaki kuma nera biyar, ba haya nera goma, wanka nera ashirin, ruwan zafi ma ashirin." Wani Wan yuniyon dinne yace.
"Haruna ka fiye surutu, ka Wauki jakarshi dallah ka rakashi masauki" Wanda aka kira Haruna ya tuntsure da dariya yace.
"Ai gara muyi gwari_gwari dai." Jakar kayan Gwadabe ya saSa a bayanshi yace.
"Biyoni muje in kai ka" A baya Gwadabe ya bishi zuwa can cikin tashar, wani gida mai kama dana masu zaman banza suka shiga. Maza da mata, da ?an daudu ne a cakuWe suna caca, masu ?idan garaya kuma sai kiWa suke yi, ga masu shan tabar sigari, ga masu cin goro da tomtom kowa dai da abinda yakeyi. ?yauran wani Waki Haruna ya buWe suka shiga. Matasane a ciki fin su takwas, wasu sunyi bacci, wasu na bacci, wasu abinci suke ci. Tabarmace malala a Wakin, sai kayi matashin kai da buhun kayanka. Gwadabe bai gama ?arema dakin kallo ba Haruna ya mi?o mishi hannunshi. Nera hamsin ya bashi.
"To ka raSa ta can lungun ka kwanta. Kana bu?atar abinci ne?'
"E ina bu?ata, amman tuwo nake so" Haruna yace.
"Tuwo miyar kukace kaWai tayi ragowa. Ko wacce malmala nera ashirin ce, nama kuma ko wanne tsoka nera goma, man shanu ko wanne cokali nera biyar" Dariya Gwadabe yayi, duk da damuwar da yake ciki. Shima harunan dariya yayi. Nera Wari ya mi?a mishi.
"To a haWa komai da komai na Wari harda ruwan sha"
Zaman Gwadabe ke da wuya sai ga kiran wayar Shafa.
"Assalamu alaikum Shafa barka da dare, har izuwa irin wannan lokacin baki yi bacci ba?" ?an murmusawa tayi, cikin taushi da za?in murya tace.
"Na kasa baccin inata jiran kiranka kace mun ka isa Takai in samu nutsuwar ruhi tukunna. Jin shiru ne yasa nace dai bari in nemeka"
?an murmushin wahala yayi mata yace.
"Ayya. Kin ganni a Kano bamu daWe da shigowa ba ma. Sai zuwa gobe in Allah ya kaimu zan karasa takai Win." Iska ta fesar daga bakinta.
"To Allah ya nuna mana. Bari in barka ka samu ka huta, zuwa safiya in ka isa Takai mayi waya" Bai bata amsaba ?it wayar ta Wauke chaji ya ?are, a ajjihu ya wurga wayar ya samu ya gyara zaman ?atuwar jakar buhunshi. Wata budurwace ta shigo mishi da tuwo. Bayan ya gama ci kuma sai yayi jigum a zaune yanata faman tunanin yadda za'ayi gobe kafin tafiyarshi yaga Iyabo ko da basu yi magana ba. Wata zuchiyar tace dashi."?ila ma tana can gidan mijinta ta mance dakai" take gabanshi ya tattake ya faWi. Da wannan zulumin ya kwana. Sassafe bayan sallar asuba ya fice a tashar bayan yaba Haruna ajjiyar jakar kayanshi. Kai tsaye motar layin su Iyabo ya shiga. Tun daga hango gidan damuwarshi ta sake yin tsanani, bugun zuchiyarshi yaci gaba da ?arfi. Iyaa Debisi ya hango tana ma yara masu kawo ni?a ni?an wani abu haka kamar gero, kamar dawa. Yana isa wajen ta kalleshi ta zuba mishi harara harda tsa?i, ta mayar da hankali a kan ni?anta. Shi ko ?i?am yayi yana jiran ta kashe injin Win su gaisa. Amman bayan fa gaisuwar baisan me zai soma cewa ba. Ya

NAMA YA DAHU....
ROMO ?ANYE
BOOK 2

6

Yaya Hambali ya gano a zaune ya jingina da garu, Babala tana zaune a kujera, Auta na ?asa a gefen ?afar Babala. ?akin Babala yasha gyara kujerunma sababbi fil, hatta labule sababbi ne aka zuba.
"Babala lafiya na ganku kunyi jigum?
"Hmm lafiya ba lafiya ba Gwadabe. Kaine a tafe sassafe haka?" Babala ta bashi amsa. Waje ya samu ya zauna, Babala ya soma gaisarwa, kafin Yaya Hambali. Babu yabo babu fallasa ya amsa, dan ko juyowa ya kalleshi bai samu wannan darajar ba. Auta ce tace.
"Yaya Gwadabe sannu da zuwa" Jiki a mace yace.
"Yauwa Auta, ya mai gidan naki?" Shiru bata amsaba, Babala tace.
"Yaya ka baro su Yaya Magaji, da fitinannun matanshi marasa daraja?" ?an murmushi yayi, a ranshi yace.
"Babala ba zata canja ba" A fili kuma yace.
"Malam yana Saudiyya shi da Baba Fhatsima yau kwanansu biyar ma. Duk kowa yana lafiya, sunce ma in gaisheki" Mikewa tsulum Yaya Hambali yayi.
"Babala ki gama dashi na dawo in kum gama. Dan bazan iya zama inuwa Waya da wannan kangararren yaron marar jin maganarki ba" Yana gama faWin haka ya fice, Gwadabe ya bishi da idanu galala. Babala ta amsa mishi da cewa.
"Kangararre fa, yaro aita nuna mishi annabi yana runtse idanu. Ni kaga banyi ma tunanin zai sake zuwa dubamu ba" Yaya Hambali dake tsaye yana sa takalmi yace.
"Sabida Bara'u ?anin ubanshi yazo, da wannan Wan nashi me cakuWe da jinin yarbawa ai" Yana gama kunna Babala yayi tafiyarshi. Ai fa nan Babala ta inda take shiga ba tanan take fita ba.
"Shima Bara'un ashe kangararrene irinka?. Yasa wannan yaro Wan wajen beyerabiyar tsohuwar matarka a makarantar boko Har gida naje na samu Sakina matarshi nace da'ita ina son ganin shi Bara'un. Wallahi ko da yazo na zayyanama Bara'u bana son wannnan Wa yayi boko. Yaronnan ya shafa toka a idanunshi yace in yi ha?uri dole a yanzu yara suna bu?atar ilimin boko. Ko da wanku ya shiga zancan ?arshe ma Bara'u ce mai yayi ai shima yaranshi na zuwa boko dole shima wannan Wan yarbawa yayi boko. Zan yi maganinku dukka, har wajen uwarshi naje na kai ?ararshi ai" Gwadabe dai yayi jim yana saurarenta sai zuga faWa take yi. Sai da ta gama tayi mai isarta yace.
"Ayi ha?uri dai Babala dan Allah." Hannu yasa a ajjihu ya zaro kuWin da Yaya Tasi'u ya bashi ya kawo mata."
"Ga wannan inji Yaya Tasi'u yace a kawo miki, matarshi ma ta bada tsaraba" Hannu tasa ta fisge kuWin da ?arfi. Gwadabe dai in da sabo ya saba. Tsarabar daya tawo dashi duk ya cicciro ya baza a gaban Babala. Yadinga mata bayanin mutanen gida da za a rarrabama. Ya ware nata dana Auta dana Yaya Halima.
"Banga na yayyenka su Fodiyo ba, balle nasu Da u. Me kake nufi kenan Gwadabe?" Sauke kai yayi ?asa yayi jim kaWan.
"Kiyi ha?uri nan gaba in zan tawo zan tawo musu dashi, amman yanzu kam babu nasu"
"Baka isaba dan ubanka. Yayanku meye a rayuwarnan bai yi maka ba? Ya ciyar dakai ya shayar dakai, yayi maka sutura, ya goyaka a bayanshi ya kai ka makarantar allo data boko da guminshi. Yau sabida wata ?ar iskar beyerabiya shine kake shirin yanke hala?arka da ?an uwanka maza? To ni zan tattare duk abinda ka bani in basu bana bu?atar ka sake kawo mun komai madamar ba zaka baiwa ?an uwanka ba. Kasan ai sunfi ?arfinka ta Sangaren arziki. Yanzu haka duk mota suke ja har Da'u. Jebeka kai a fige a bushe, sai uban naWin buzaye a ?aron kanka. In baka yi wasa ba ma a haka zaka ?are Gwadabe" hawayene suka gangaro da gudu zuwa kan kuncinshi. Ya kasa furta daidai da kalma.
"Bama son duk abinda zai fito daga hannunka Gwadabe. Munfi ?arfinka,tun da majina a hancinka nake juya kuWi. Da wasa kar kayi gigi ?afarka ta tako gidana bana son yin hulWa da kai har gaban abada mitsiyaci" Cewar Yaya Hambali dake tsaye a dokin ?ofa, yaji dukkan tattaunawar Gwadabe da Babala kan tsaraba. Babala ta turo ma Gwadabe tsarabar da yayo mata dana su Yaya Halima.
"Gashi dani da ?a?ana bama bu?atar komai daga gareka. Wannan dai da aka baka sa?o ka kawo mun na karSa. Matan gida kuma kaje ka rarraba musu da kan ka"
"Babala kiy mun rai kiyi ha?uri. Yaya Hambali kaima kayi ha?uri. Duk tsawon watanninnan tsarabarnan nake ta siye ina jefarwa. Iyakar abinda kuWina ya iya siya kenan." Ya faWa cikin sigar rarrashi. Kamar sake tunzura Yaya Hambali yayi ma.
"Shine nace maka kaine mitsiyaci Gwadabe. Dan wannan duk tsarabar bata wuce in siyeta a take in bayar da'ita sadaka ba" Babala tace.
"FaWa mishi dai. Baka ga yanda arzikinshi yaci uban nada bane. Gidanshi na kano an ruguje ya dawo gidan bene Ai kaga yanda gidannam ya dawo ko gidan mai gari albarka, ga babbar motarshi a ?ofar gida" Gwadabe yana zaune suka ?are mishi tanadi tsab, ko tari baiyi ba, idanunshi sun kaWa sun zama jawur. Yanzu iyayenmu sun zama abinda suka zama. Nuna fifiko akan ?a?ansu masu sukuni akan waWanda su Allah bai basu ba. Mi?ewa yayi da tsarabar matan gidan ya kaima Goggo Yabi yace ta raba a tsakankaninsu. Bayan ya dawo Wakin Babala ne tace.
"Ya batun Aure, ko kanaso kace ba zaka sake aure bane tunda ka rabu da ?anwar uwarka Iyatu? Ga Laila tayi aurenta, yarinya da kyanta Allah ya taimaketa ta auri mashahurin Wan siyasa, baka ga gidanta ba."
"Aure zanyi Babala. Baba Magaji ya haWani da ?arshi Bazawara Hadiza harma mun sasanta kanmu, Lokaci kawai ake jira. Kuma..." Ta katseshi da cewa.
"Kuma me? Dama shi Yaya Magaji abinda yake so kenan shi yasa ya goyi bayanka ka bijere akan auren Laila, ashe tashi ?ar yake ma tanadin talaka kamarka? Na lura so yake ya yanke zumunci damu, domin matsawar Iyatu taji wannan batu zata yi fishi. Dan kawai Allah ya jarabceta da Wiya me ciwon sata." Nan Babala taita jujjuya zancan. Gwadabe na son ya faWa mata batun ?anwar Tamu, amman tsoro ya hanashi, dole ya ja bakinshi ya tsuke.
"Babala ni zan shiga ciki in yi wanka. Jazuli yana ciki ne?" Ya tambaya da dariya a ?o?arinshi na danne damuwar data addabi zuchiyarshi.
"Ka dai je Wakin nasan a buWe yake. Wake zama baya neman arziki? Jazuli yana Kano Yayanku ya buWe mishi shago, ya kan dai shigo Takai lokaci zuwa lokaci" Kai kawai ya girgiza ya Wauki jakarshi yana shirin fita Babala tace.
"Kazo ka kwashi tsiyarka fa Gwadabe" Fita yayi tare da cewa.
"Ni lada nake nema. Ko zubarwa kikayi daidai ne Babala" Har yabar barayin bai dena juyo sababin Babala ba. Wanka yayi ya shiga Wakin Jazuli ya zauna a bakin katifa yana mai cike da zulumin irin furucin da Babala ta daWe tana jifanshi dashi na rashin arziki. Gashi duk abinda yasa a gaba baya samun nasara sam. Ko ha?on zinari ya shiga rijiyar zaiyi. To sai dai fa yasha wahalar banza. Sau huWu ya taSa samun dutsen zinare ?ananu suma. Amman Auwala da Mammada sau nawa suka samu, sai dai fa in an siyar su Wan tsakura mishi na kashewa. Dan aikin ha?an zinare ba aiki bane na wasa, balle har wanda ya ha?a ya baka kuWi me yawa, aikine mai cinye ?arfi da ?uruciya sosai. A hakanma yaga ?o?arin su Auwala da suke sammishi wani abun. Dan kullum fa a cikin shan ?wayar bature suke maganin ciyon gabSai. Ga auren mata biyu a gabanshi, bai tara ba bai ba wani ajjiya ba. Atampa biyu kawai ya ajjiye. Auwala kuwa ya gama haWa kayan akwatinshi tsab, takalmane kawai ya rage. Iska ya furzar a bakinshi a fili yace.
"Anya bazan fito in faWa ma Tamu gaskiya ba kuwa? Ni bani da ?arfi, kar in auri mata biyu in zo in gaza wajen kulawa dasu. Yana da kyau Tamu yasan yanayin samuna fa. Amman bari inje in samu Bara'u inji ta bakinshi" Zuruf ya mi?e cikinshi ya wani juya mishi. Sai lokacin ya tuna ashe fa baici abinci ba ma. A ?ofar gida ya tarad da Yaya Hambali da abokinshi Inusa yaron mai gari.
"Gwadabe kaine a garin namu?" Ya tambeshi da fara'a. Fuska Gwadabe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login