Showing 24001 words to 27000 words out of 78322 words

Chapter 9 - MATAN Hafiz Book Complete Document .txt

Unknown   

27 Nov 2024

2510

din na biye da ita a baya, har office dinta tajasa taimasa nuni da have a st, bayan yazauna gaba daya hankalinsa na gareta, babbar likitace qwararriya ata fannin matsalar mata Wanda shekarunta zasukai 55 a yanzun Amman tsabar hutu yasa bazakai tunanin takai hakan ba zasuyi kusan sa'a da momynsa.


Hafiz yakad'u matuqa dayaji tana sheda masa zubewar cikin dake jikin heema dudda sunyi iya qoqarinsu amman Allah bai yarda ba,
wanda dole suka ida yi mata wankin ciki ynzun tanacan tana barci sakamakon alluran da suka samata a drip kuma sun bata bedrest na tsawon sati guda domin samun nutsuwar mahaifarta.
sosai idanun Hafiz suka kad'a jajir kawai sadda kansa yai a jikin table din gabansa zuciyarsa na fat-fat, har ga Allah ya qwallafa rai a cikin jikin heema domin yanada son yara a rayuwarsa matuqa, jin ynda doctor din keta tausarsa yasashi lumshe ido gamida had'iye wani busassan miyau.
tunowa dayai Allahn daya basa wnn din shi zai sake bashi wani, sosai yake jan adduo'in tausan zuciya a ransa snn yasamu qarfin gwiwan Barin office din bayn yasamu excuse din shiga room din da aka kwantar da heema din, sosai yake cigaba da tausar zuciyarsa ahankali yake takunsa uwa wani patient don idanunsa na qasa kawai da zuciyarsa yake nakaltar inda zai dosa zuciyarsa babu cikakken dad'i.
babu zato yaji sunyi karo da juna kamin ya dag'o yaji an furta sautin
"washhh Allah na abbu"!!!
dasauri yakai dubansa gabansa dudda baiga fuskarta ba dan a lkcn durqushe take a gabansa sakamon turo qofan da yayi zai fito daga office din doctor blessing ita kuma ta zo shigowa kowanensu Yakama handlng din kofan Amman shi yarigata fara turowa mafarin knn gegen for head dinta ya dan bugu da qofan harta duqe qasa tana cigaba da furta wash idanunta a runtse tana yarfe hannnu lkc daya hawaye nabin kuncinta batareda ta sanma suna zubowa ba, zuba mata sanyayyun idanuwansa yai dake saqe da damuwa still gamida dan duqowa gareta tana furta "sorry bansan akwai wani a wajen bane.. dasauri ta miqe tunowa da halin da mahaifinta keciki tuni zafin ciwon ya dauke mata lokaci daya suka dubi juna.


wani irin mummunan bugu zuciyar Hafiz tai lokaci 1 yaji numfashinsa na masa seizing dan cin karo da asalin kyakkyawr fuskar yarinyar dayai wacce kalarta yayi kama da usulin Fulani camaron..kasa cigaba da mgnr dayakeyi yai ya tsaya can yana binta da kallo..
siraran labbanta yaga sun motsa a hankali daqyar yaji ta furta"bkm nayafe maka"
ganin datai yayi tsaye a hnya yakasa wani kyakkywan motsi sai binta da kallo yake uwa maison gano wani abun a jikin baby face dinta, aikam da sauri zagaye sa tawuce zuwa office din doctor blessing tana shiga tayi kneeling a gabanta murya na rawa ta fara furta
"dan Allah doctor ki taimaka aiwa babana aikin nan wlh kuwa da zarar kawuna yadawo zamu biya kudin, please doctor kitaimaki rayuwar abbuna,
wlh ko aikin sharar asibitin nan naku ne zanyi muku koda kawuna baidawo ba da wuri har mu biyaku kudin ku barema nasan yayana zai dawo n...daka mata tsawa doctor blessing tayi gamida furta "hey stop girl, oya get out ko angaya miki nan wajen wasa ne?, to bari kiji I swear to Jesus nan da 1 hour in baku kawu dubu 300 nanba ba aikin babanki zamu tarkataku ne muyi plshing naku a waje dan nan ba asibitin mahaukata bane...nonsense girl I say get out"!!!!








*By 4 writer's*😍
[7/12, 8:34 AM] Xainab Documen: .*♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




*Gargad'i*


Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.


*Muna wa daukacin musulman duniya murna ansha ruwa lfy Allah ya amshi ibadunmu aminn.*

~Happy salla dears~🙋‍♀️


*Masha Allah mundawo yanzun matan Hafiz zai daura muna godiya masoya*


20.


*Matashiya....*


Motsa red Lip's dinsa yai gamida shafar kwantaccen sajen fuskarsa wanda keta sheqi.


fararen idanunsa ya sake sauqewa a kanta daga nan inda yake tsaye bayan maida wayar sa a aljihun jeans din jikinsa na kakin sojoji dayai had'e da rigarsu da pacing cap dinsu.


"Mike damunta to?!!!"


tambayar da yaiwa zuciyarsa knn a farko.
zuciyarsa na tunanin shin ya qarasa gunta yaji damuwar ta koko ya koma wajen heema dan qara rarrashinta akan rashin da sukayi?"


bai tsaya sake tunanin komi ba ya cira qafarsa gamida dosar inda basmah take a zaune, ta had'e kai da gwiwa sam batasan da tsayuwar mutum ba a gun, dudda tanajin tashin wani sansanyan perfume a gun amman saitai tunanin ta dauro ko masu gittawa ne ta wajen, koda ya isa inda take bai sake cewa uffan ba tun bayan sallamar sa ta farko yaji shiru ga alama ta zurfafa a tunani ne, zura hannuwansa duka biyun yai a aljihun sa gamida yin gyaran murya mai sauti.


a zabure ta dago da fuskarta babu bata lokaci idanunsu suka sake had'ewa a cikin na juna a karo na 2 a haduwar su tun farko.


miqewa tayi tsaye da dan sauri tana Gyara zaman hijab dinta gamida furta
"mlm wani abu?"
bai bata amsa yayinda ita kuma jikinta ya fara sabuwar rawa dan ko a tunaninta doctor ce ta turo mata wnn sojan yayi musu fatata sbd basu biya kudi ba har yanxun,
wahayen da suka zubo mata nai tai saurin shareware ganin datai fuskarsa babu alamun wasa dasauri ta sake ja da baya ganin yana sake takowa gabanta, abinka da tsoratacciya tuni ta fashe da kuka tana waige waige uwa wacce ke neman hanyan guduwa,


Aiko da sauri ta raba sa zata wuce...


"inasan kiban minti 1 zuwa 2 zamuyi mgn dake"


ai kamar yasata qara sauri dan kuwa sosai dakakkiyar muryarsa ta sake bugun zuciyarta da gudu gudu tabar gun ta shige dakin da aka kwantar da abbu har tana had'awa da tuntube, itadai fatanta ta tserewa sojan nan mai bada tsoro dudda kallo 1 data masa a yanzun taga ba qaramin kyakkyawa bane amman tsabar tsoron datakeji nasa a lkcn ya danne tunanin kyawan fuskar tasa a zuciyarta, a rude ammi ta ga basmah ta shigo dakin tana haki, dagudu ta rungume maman tana sakin kuka abbu dake kwance yana numfashi daqyar Amman ahaka ya ke kokarin ruqo 'yar tasa yaji dalilin gigicewarta haka, yayinda ammi keta famn hero tambayoyi lfy, daqyar basmah ta riqo hannun abbu da ammi tace
"Ammi inaga sun turo mana sojoji ne su koramu a asibitin nan inda mun gagara biyansu kudin aikin da za'aiwa abbu, ammu mukama abbu mutafi dashi gida kada suzo su sake tabo mana lafiyan Abba sojiji basuda imani ammi mutafi...mutafi... hawaye abbu yakeyi hakama ammi gabaki 1 duniyar tai musu qunci, basu taba tunanin haka talauci yake da zafi ba, amman bakomi akwai Allah domin Allah shine mafi sanin dai dai ,Allah na sane dasu kuma dukkan wnda ya maida lamurransa garesa bazai taba ta6ewa ba, ganin da ammi tai lokacin da aka ibar musu ya wuce da kusan minti 10 , da sauri ta miqe tafara hada kayansu yayinda basma ke kokarin tada mahaifinta sukaji an banko qofa da qarfin gaske, doctor blessing ce ta shigo wasu maza guda 2 na take mata baya da kalar wani tsanwan uniform ga alama security din hospital din ne.
nan tafara musifa cikin gwamatsattsiyar hausar ta take furta
"oya oya let's go talakawan banza kubar mana hospital tunkan nasa amun fata fata daku dan asibitin nan bana faqirai bane,
bacin tsiya da tsabar talauci kunsan bakuda kudin jinya zaku wani kwaso jiki Ku nufo mana hospital ko? to saidai Ku tafi wata matsiyata kawai dakikai marassa daraj.... maganar ta datsewa tai sakamakon wanda tagani a gabanta yana jifanta da wani fititannen kallo ko dauke idanunsa baiyi ba a kanta,


"sorryy sir"


abinda mazan security din sukace masa knn da sauri bacin wani hayaqaqqen kallo daya koma aika musu suma da musu alamun su fice, dasauri suka bar room din kuwa.


Hafiz ya dawo da kallonsa kan doctor blessing datai tsuru tsuru gaba daya a kidime take dan batasan Hafiz din yana gun ba tun data fara wulaqancin nata ya shigo sai ynz ya ida bayyana gabanta, jikinta har rawa ya fara tsoronta kada ya fadawa dadynsa doctor Ahamed har hakan yazamo silar barinta asibitin dantasan doctor Ahmed bai lazumci wulaqanta wani ba a cikin asibitinsa ba ko yaya mutun yake, kowa kuwa yai gigin hakan saiya fuskanci hukuncin sa, tuni jikinta ya sake kabewa da rawa qafafunta sun gagara tsayawa waje daya har batasan sanda ta durqushe a qasan gun ba tana furta
"sorry woo sir Hafiz,! i mean ba da haka nai niyyan musu ba I beg you kada ka fadawa yallabai pleasesss and please..!!!"
rai bace Hafiz ya furta...




*From 4 writer's😍*










~Fasaha online writers (f.o.w.)~




*Muna baran addu'anku sisters 1 daga cikin marubutan matan Hafiz bata lfy Raheenat Mahmoud👏🏼*.
[7/12, 8:34 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




*Gargad'i*


Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.




19.


Cikin gigicewa da tsoron tsawar da doctor blessing take mata yasata sake fashewa da kuka ta na durqushe sosai kan qafanta, ta furta
"to doctor na amince amman dan Allah kimana haqurin zuwa safiya inbamu kawo kudinba saiki koremu kinga yanzun inmun dauki abbun mu mun tafi dare ne qarfe biyu da mintoci fa nasan ko abin hawa wuya zai mana"!.


hararta doctor blessing tai tace " jinyi s'a ni mace ce mai son abu mai matuqar kyau dan haka kije kinci albarkacin tsantsar kyawunki yarinya, amman kisani gobe 11:nasafe inbaku kawo kudin aikin nanba nazo kada kuyi mamakin wulaqancin dazan muku, mtsww mutane HK kuke kodan kunga mai asibitin na tausaya muku yanawa wasunku aiki har kyauta?! to shidin bainan ni kuma daidai nake da kowane qaramin dan iskan talaka, talakawa kunada kudi kuki fiddowa ayi muku magani Amman said ku tsaya kunai musu dogon buri, mtsww dalla bacemin da gani


"dasauri ko ta miqe tabar wajen ko ganin gabanta batayi, can wajen asibitin ta nufa tazauna qasan wata baranda ta had'e kai tana kuka, gaba daya duniyar jitake tana mata yawo a idanunta, dudda dare ne harya raba alokacin amman Sam ko alamun bacci babu a idanunta.


daqyar ta samu ta rarrashi kanta ta lumshe idanunta tana hadiyar kukan nata kanta jingine da wall din gun tana karanta kowace addua tazo bakinta ta samun nutsuwa.
jitai an dafata gamida furta


"basmah"


dasauri ta bude idanunta jin muryan amminta, cikin dabara ta goge hawayenta gamida qaqaro myrmushi.


zuba mata idanuwa amminta tai tace"basmah bazaki daina kukan nan haka ba ko? ciwo fa ba mutuwa ake bane tun jia da muka zo asibitun nan kike faman kuka yakamata ki sarara wa zuciyanki kinji dan Allah, insha Allah jikina yana bani malam zai tashi kiyi haquri,
ajiyan zuciya basma ta sauke gamida furta kiyi haquri ammuna wlh bansan snda kukan ke zuwa ba, sosai nake tausayan abbun mu, ammuna cutan nan na matuqar wahalar dashi kiduba fa ammu ko numfashi daqyar abbu yake saukewa ga zubar jini a jikinsa ammu shiba mace ba komi ba, kuma Yaya tunda yatafi bai dawo ba naje wajen doctor na roqeta suyi masa aikin nan inyaso kodaga baya ma biya ko ma ni su riqeni anan din harsai mun biyasu amman sunqiya ammi..kasa ida mgnr tai ta rushe da wani sabon kukan mai jijjiga jiki.
zama ammun tayi kusa da 'yar tata takasa furta komi gaba dayansu suka shiga zurfaffan tunani rayuwarsu ma.


*Suwaye Ammu da Abbu da Yaya da basmah ne?*


Mlm Muhammad Osama ladan haifaffen qasar Cameron ne gaba da baya uwa da uba da 'yan uwa suna can, koda Mlm Muhammad Osama ladan yatashi mutum ne mai matuqar nacin neman karatun addini hakane yasa yatashi cikin tsantsar ilimin islama wanda kankacemi a shekarunsa a aduniya kusan 58 yazama babban malamin da duk yankinsu babu Wanda bai sansa ba a fannin ilimin Islam, tafsir tafsir wa'azuzzuka dasauransu shima ba'a barsa a baya ba, matarsa guda daya mai suna maryamu, wacce yaranta ke kiranta da ammu, sosai yake gudanar da koyawar sa makarantu2.
saidai akwai wani cuta da Mlm Muhammad Osama ke fama da ita tun tashinsa Amman bata ta'azzara ba saida girma ya fara shigarsa snn.


to koda ya ankara da ita saiya fara ziyartar asibitoci karbar magani cikin ikon Allah saigashi dayasha magungunan shiknn yakan samu sauqi, musamamn wani doctor Hussain daya daurasa kan magunguna masu dausashe cutar.
Yaran mlm Muhammad osama 2, namijin shine mus'ab sai macen basmah, Mlm Muhammad nazuwa cikin yankaunan garuruwa domin gudanar da kasuwancin sa,
sai yai yan kwanaki snn yadawo gida.
cikin ikon Allah sai gashi yasami uban gida suna siyar da hatsi a nan kano, dawasa da wasa har abokin Mlm Muhammad Osama ladan wato Alhj muttaqa yajawo ra'ayinsa kan yadawo nan da iyalansa a garin kano din da zama,a memakon jeka kadawo dazai tayi kusan kullum Inda kasuwancin nasa yafi qarfi anan kano din.


saigashi Mlm Muhammad Osama ladan baisami Marsala ta fannin iyayensa ba suna samusu albarka adawowarsu kano din.
Ahj muttaqa mutumin kirki ne matuqa kowa ya rabesa saiya ji dadi, dan haka ganin aminin nasa mlm Muhammad osama ladan yadawo kusa dashi, shida kansa ya basa kyautar wani gidansa mai dakuna hudu da girman tsakan gida da qatuwar baranda ga famfo a cikinsa haddda rijiya , daga wajen gidan kuma akwai baranda mai girma, Mlm Muhammad Osama ladan yayi godiya sosai haka suka cigaba da zama cikin aminci.


ahaka suka kwashe kusan shekara yayinda Mlm Muhammad Osama ladan ya bud'e makaranta dud bayan sallar isha'e kullum shi Mlm Muhammad Osama ladan ke koyarda mutane manya nan a kofar gidan nasa hadda Alhj muttaqa kuwa cikin daliban,
wato yanda kasuwancin Alhj muttaqa da Mlm Muhammad Osama ladan ke tafiya shine ,shi Alhj muttaqa ke kawo kaya shikuma Mlm Muhammad Osama ladan ya karba ya rabawa abokan kasuwancin su in an siyar saiya basa nashi kason, sai gashi da kudaden da yake samu a wajen Alhj muttaqa dana hannunsa shima saiya kama qaramin shago ya saka kwanikan hatsi wato su gero dawa alkama,


shi kuma alhj muttaqa saiya qara masa da kyutar buhu 2 na masara 1 na ridi daya na wake, shima ya fara cin gabn kansa dud shekara kuma yana komawa Cameron yayi noma snn yadawo wajen iyalinsa.


ashekar 2020 ne Allah ya amshi ran iyayen Mlm Muhammad Osama ladan Wanda suka rasu ata hanyar 'yan fashi da makami da suka dirarwa yankin shiyyarsu sukai kashe kashe suka kwashi dukiyoyi sukai gaba.


sunji mutuwan abbu har suma yai lkcn da lbrn ya iske su SBD tsabar firgici,amman haka aka share makoki watansu guda da dawowa kano shida iyalinsa bayan rasuwar iyayen nasu sai kuma babban amininsa Alhj muttaqa shima ya amsa kiran mahaliccinsa ta hnyar hatsarin mota a hanyarsa ta dawowa daga fatauci a birnin gwari, sosai mutuwar ya girgiza Mlm Muhammad Osama ladan dan har rashin lfy saida ya kwanta ta kwana 2, haqiqa yayi babban rashi na aminin qwarai dud duniya baida amini na qut da qut kamrsa, yayi kuka yayi masa addua da fatan halinsa na gari ya bisa dan haqiqa bashi kadai ba ya sheda alherin Alhj muttaqa garesa kowa ma ya sheda, kowa kaji yabuda baki yabon sa ake.


(damn ance shedun duniya sune ba qiyama Allah kadatar damu amin)


wata 5 da mutuwar Alhj muttaqa tsohon ciwon Mlm Muhammad Osama ladan ya taso gadan gadan Wanda har saida suka dangana da babban asibiti dadyn Hafiz, likitoci sun sheda aiki za'ayi masa a fidda masa cutar dake cikinsa wacce take sashi zubda jini kuma kudin aikin zai kama dubu 300 gashi basuda gaba basuda baya, dan d'an jarin Mlm Muhammad Osama ladan din baifi dubu 100 ba a yanzun, hidimar rayuwa ga dawainiyar karatun iyali da sauransu sai dai godiyan Allah, mus'ab babban dan Mlm Muhammad Osama ladan Wanda shekarunsa 31 yana mataki na qarshe a karatunsa na digree yayinda maibi masa itace basman a shekarunta ynzu 19 tana matakin qarshe na secondary school wnn knn.


a yanzun haka tun jia da likitan yasheda musu kudin aikin mahaifinsu sukai yanke Shawara shi mus'ab da mamansa kan yaje can gida Cameron ayiwa gonar ta kudi wacce ta gada a wajen babnta konawa yakama asiyar yakawo kudin saisu biya, to tun jia da azhur yatafi amman har yanzun washe garin ranar har gashi dare ya qara shigowa amman shiru kakeji bai dawo ba, kuma cikin awannin da aka dauka za'aiwa Mlm Muhammad Osama ladan aiki saura awa daya shi baccin da aka qara musu lkc zuwa safiyan gobe da basusan ynda zasuyi ba.


*cigaban labarin*

ammi da basma sun yi jugum jigum bayanda basmah ta shedawa ummun ynda sukayi da doctor blessing ynz suna
jiran hukuncin Allah,
gashi babu mai waya a cikinsu bare a kirasa aji lfy( Dan ita basmah babnta yahanata amfani dawaya yace saita gama karatu zai siya mata)
daqyar ammi tashawo kan basma suka tashi daga bakin darbejian sukayo alwala gamida gabatar da salla kan wata baranda da majinyata ke hutawa a wajen sunyi addu'a sosai kan samun lfyn abbu.
sunanan har saida sukayi sallan asuba gari ya waye basma tasiyo musu kalaci wajen asibitin sukayi snn
suka wuce dakin da aka kwantar da Mlm Muhammad Osama ladan danasa a hannunsu, har lkcn kwance yake komotsawa bayayi sosai, saidai yakalli wnn ya kalli wnn saikuma ya rufe ido, cikin boyewa basma ke share hawayenta da dogon hijab dinta kanta a qasa.


cikin dabara ammi take basa kalacin , luddai 3 yai na koko daqyar snn ya koma ya kwanta2


Wuzin 10 na safe nan daliban Mlm fa sukaita zuwa musu yamai jiki da dan alherinsu, sam basuji labarin kudin da ake nema ba tabbas da sai sunyi masa karo karo to ba'asin shine sam ahalin Mlm din basuda tabi'ar roqo shiyasa ammi bata d'aga mgnr ba bare basma.
su daliban sunzata rashin lfy ne daine ke damun Mlm din nasu, fatan samun lfy da addu'@ sukai ta masa dud Wanda yazo, basmah kuwa kadan kadan zata dubi agogon hannunta tana kallon lkc fashewa tai da kuka sanda taga saura 1 hour qa'idan korarsu asibitin ya cika.



a can gidan Hafiz kuwa daqyar yakirasu yashe musu halinda aje ciki, jin dasukayi heema ta farfado amamn babu labarin ciki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login