Showing 6001 words to 9000 words out of 78322 words

Chapter 3 - MATAN Hafiz Book Complete Document .txt

Unknown   

27 Nov 2024

2507

da ya dace, saidai ko da wasa ba sanar da matanshi ba dan yana gudun tashin hankali baranma Raheema mai karamin ciki.
Dan yanzu cikin yana da wata uku yana neman na hudu.
Ta fara samun saukin laulayinta dan tana cin abinci kuma tana shiga kitchen ta girka.


Babu tsammani kawai suka ga ana shigo musu da kaya niki niki ko wacce aka kai mata d'akinta wai inji umma na fad'ar kishiya.


Mamaki da kad'uwa ne ya mamayesu dukansu biyu dan basu da labari kuma ko alama bai nuna musu yana neman aure ba.


Aiko ranar ko abinci ba a barshi yaci ba dan zainab taso shi gaba tayi sai ya gaya mata dame ta rageshi da zai mata kishiya.
Duk yadda yaso ta fahimci ba shi ya nemi auren ba k'i tayi har ya gaji ya kyaleta.
Gaba d"aya kuma sai hankalinshi ya koma kan Raheema da tunda ya shigo sau d'aya ya ganta ta mishi sannu da dawowa ta bar wajen.
Shirunta ya dameshi.
Hankalinshi ya gaza kwanciya gwara dai yaje yaga halin da take ciki.


Ita kuwa Raheema ba k'aramin ciwo abin yayi mata ba amma da ta tuna yadda zainab take cika bakin tafi karfin akawo wata bayanta take taji saukin b'acin ran da take ciki, ta sawa ranta cewar Zainab za a yiwa kishiya ba itaba.


Saidai fa kishi na cinta kasa kasa bata dai yi niyyar nunawa bane.


Ta fito daga wanka ya shigo dakin.
Kallo d'aya tayi masa ta kawar da kanta ta nufi dressing mirror.


Gaba d'aya sai yaji ya daburce ya rasa me ma zaice mata.
Karasawa yayi kusa da ita yana sa hanunshi kan wuyanta kamar maison tab'awa yaji ko da zafi.


"Heemah babu wata matsala ko?"
Wani irin haushinsa taji kamar ta gantsarawa hanun cizo taji amma ta dake tace mishi "Babu komai."
ta kama shafa manta.


Tsiyaya man yayi shima ya duka ya kama kafarta yana shafa mata.
Ji take kamar ta hanb'areshi da kafar ko zataji sauki a ranta.


"D'an satan kallonshi tayi tace "Daddyn sultan mun ga kaya mun gode Allah ya nuna mana lokacin."


kamar wadda aka watsawa ruwan sanyi a jiki haka yaji.


"Heemah, iya abinda zaki ce kenan?"
yace mata.


Dakewa tayi tace "To wacece amaryar tamu?
Haka kakeso ince ko?"
A hankali ya mike ya koma bakin gado ya zauna yana dafe kanshi.




"Ni ba haka nace ba, idan akwai abinda ke cikin zuciyarki ki fitar kawai kada kizo ki cutu.


"In akwai d'in zan fitar ai daddyn sultan babunne.?"


Ta fad'a murmushi shimfide a fiskarta ganin yadda ya bi ya tsargi kanshi.


Shiru ne ya biyo baya kafin ya daure yace.
"Kiyi hakuri Heemah, ban tab'a tsammanin zanyi rayuwa da wasu matan bayan ke ba, amma ya muka iya da rubutaccen al'amari.
Wlh nima lokaci guda umma ta kirani take sanar dani maganar auren."


"Allah yasa ayi a sa'a."
Ta fad'a tana fiddo kayan da zata saka.


Fita yayi jiki a salub'e ya shiga falonshi.
Nan ya tarar da zainab ta jibge mishi akwatunan kayan da aka kawo mata tana zaune sai cika take tana batsewa.




Bai tankata ba zai wuce ta jawo rigarshi ta baya.


"Malam ko ka tattari kayanka kasan yadda kayi dasu ko kuma in konasu wlh."


Gyara tsayuwarsa yayi yana binta da wani irin kallo..
[7/12, 8:33 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahir rahmanir raheem.




5.


Wannan abu da Umma ta gani gidan Hafiz ya tsaya mata arai ta kasa mantawa da shi, gani take kamar haka rayuwar gidan yake tafiya a kullum dan dai Hafiz mai hakuri ne shi yasa bai tab'a fad'a ba.


A jima kad'an tace "Ashe har yanzu dai Hafizu baiyi dacen aure ba."


Saidai ko sau daya ba ta kawo mishi maganar ba duk da kuwa yana zuwa gidan.


Shima tun yana d'ari d'ari har yaxo ya saki jiki saboda sam bashi da niyar fitar da sirrin gidansa.


B'angaren Zainab kuwa tabi shi sau ba adadi amma har yanzu bata samu fiska ba idan ma ta matsa mishi da rokon yaci abinci sai ya ce mata shi bazaici abinda za a zo daga baya ana goranta mishi ba.


Wannan abu ba karamin daga mata hankali yake yi ba.
Duk wa'yanda ta nemi shawararsu daga 'yan uwanta har kawayenta hakuri suke kara bata da kuma nuna mata dabaru da hanyoyin da zata bi dan komai ya daidaita tsakaninta da mijinta.
Wata kawarta ce ta bata shawarar taje ta nemi maganin da zata mallakeshi kawai ta juya shi yadda takeso.
Saidai ita kuma Zainab ko kad'an bata da ra'ayin harkar bin bokaye..
Bawai dan imani ne yayi mata yawa ba.
Ta saba ganin fina fina ko jin labarai na bokaye da 'yan tsubbu.
Ita sam basu tab'a burgeta ba saboda kyama ma suke bata.
Ta yaya zata fara zuwa gurin wani da daga ganin shi ma kaga tarin daud'a da datti tace tazo neman biyan bukata.
Bata karb'i wannan shawarar ba ko kad'an , tafi yarda da ta jure ta bishi da lalama har su daidaita kansu.


Hajiya Raheema kam duk da taga canji tsakanin su bata tab'a kawo mishi maganar ba dan ita ta kanta ma takeyi.




******


"Da lafiya ma ya aka k'are balle kuma an zama tab'ani langwai."


D'ago kai Raheema tayi ta kalli yayarta dake magana, ta sani sarai da ita takeyi.
Kusan ko da yaushe idan 'yan uwanta sunzo gidan abinda ke had'a su fad'a kenan dan sun rika yada maganganun kan rashin gyara gurinta yadda ya kamata.


Tab'e bakinta yayar tayi ta cewa kanwar su da suka zo tare.
"Kareema mu gyara mata ba don halinta ba."


Kallonsu kawai tayi t tab'e bakinta tana cewa "Za ku daiji da shi."


Ganin gyaran nasu sosai ne ta tashi tana daukar wayarta tare da cewa.
"Ni kam ina dakin Daddyn sultan, kuma kada kusa min turare amai yake sani."


Can dakin Hafiz dinma ta gagara zama saboda kamshin turaren wuta da Zainab ta saka bayan ta gyara.


Sai fita tayi kawai taje garden din gidan ta zauna kan lilo da musamman saboda su sultan aka tanadeshi.


'Yan karance karancenta tayi kafin ta fara jin bacci na fiskarta ta sauka ta koma babban falon gidan ta bude windows duk dai gudun kamshin turaren wuta ta kwanta cikin kujera nan ma saida ta cire d'an kwalin kanta ta toshe hancinta ta samu tayi baccinta cikin kwanciyar hankali.


Tsaf ta samu sun gyara mata d'aki irin gyaran da d'akin ya jima bai gani komai tsaf tsaf har wani ni'imraccen iska na musamman taji yake shiga jikinta.


"Kuma ban godeba."
tace musu tana shigewa ban d'aki.


"Oho dai, d'aki yaga tsaftar da bai tab'a gani yau dai har magana yayi dan yayi godiyan da kanshi."
cewar kanwarta.


Bata kulata ba ta karasa shigewa.


Daga ciki take jiyo yayar ta ta tana cewa.
"Mace har mace ga kyau ga gayu ga aji amma kar a zo muhallinta kamar ba nata ba.
Ni wallahi mamaki ma take bani, ta yaya zan kasance kullum cikin tsafta kuma inyi rayuwa wajen da babu isasshen tsafta.
Wlh Kareema zan iya kirga miki zuwan da nayi gidannanna samu d'akin Raheema a tsaftace yadda ya kamata."


Kareema ta amshe zancen da cewa "Ba dole ayi mata kishiya bama."


yayarsu ta sake cewa "Da akayi mata kishiyar kinga wani canji ne, ai inaga Raheema kam zuciyar ta mutu gaba d'aya.
Dan Allah kiga yadda amaryarta take tsaftace gurin ta kullum k'al k'al ita kuwa ko oho."
Magana suke suna d'aga murya dan tajisu da kyau daga can ban dakin.


Yayar ta k'ara da cewa "Ita Raheema babu abinda ta iya sai karanta novel.
Idan kina so kiga zak'ewa tambayeta labarin littafi kiga yadda zata baki kanun labarai har da kwaikwayon muryoyinsu da actions dinsu takeyi kai kace a gabanta a kayi komai, maimakon ma ta d'auki abubuwa masu amfani da ta karanta amma tayi amfani dasu amma inaaa, ba dai Raheemarmu ba ."


Daga ita sai towel ta fito daga toilet tana yatsina fiska.
"Gulma haram."
ta fada tana zama bakin gadonta.


"Yo a bayan idanunki mukayi da zaki wani ce mana gulma?


"Kun dameni wallahi da surutu.
Nifa idan kunga k'ura a d'akinnan to daga sama suka zubo ehen."


Kallon saman sukayi dukansu da mamaki kamar wasu sakarkaru.


D'an murmushi tayi kad'an tace "Babu mai ganin b'ulin da k'uran yake bi ya zubo ba sai ma cikakkaken imani kamar dai ni da Daddyn Sultan."


A tare suka ja tsaki sannan yayar tace "Ana fad'a miki gaskiya kina shiririta."


"Kareema yunwa nakeji wlh."
ta fad'a tana langab'e kanta.


"Ki bari idan mai cikakken imani irinki ya dawo yazo yabaki abinda zaki ci 'yar rainin wayo kawai."


Ranar ta samu ta d'an tab'a abinci kasancewarta tare da 'yan uwanta ya mata dad'i duk da dai ana hira ana fad'a ne.
Sun bata shawarwari ita kanta ta sani idan zata bisu zata mori zaman gidan mijinta.


Ko da Hafiz ma ya shigo d'akin a ranar saida yayi ta zolayar ta yana cewa ya tabbata bak'i kayi d'akinnan ya canza dan yasan mai d'akin kam da lafiyarta ma yaushe tayi.




*****




Kunun gyad'a take damawa a kitchen shi kuwa ogan yana tsaye kikam a bayanta kamar wani bodyguard fiska murtuke.


Da marmarinta take damawa saboda ya dad'e bai bata aiki ba balle ma na abinci.
Saidai tsayuwanshi a wajen da kuma yanayin fiskarshi ya kulle mata kai.


Har ta gama ta zuba mishi cikin flask.
Ya karb'a yace ta biyoshi da cups.




Falon Raheema suka shiga ya ajiye a gabanta saboda ita tace tana sha'awan sha.
Cup din ya karb'a daga hanun Raheema ya bud'e flask din yana tsiyaya mata tare da fad'in "Zaki bari ya d'an huce yanzu Zainab ta dama shi."


Kallonshi tayi ba tare da tayi magana ba ta d'auke kanta.


"Ina tsaye a wajen ta fara har ta gama, kisha babu abinda zai faru."


Wani irin dumm, Zainab taji take taji kirjinta na mata rad'ad'i tajuya ta fice da ga cikin d'akin.


Itama kanta Raheemar maganarshi ta bata mamaki shi yasa tace "Haba daddyn sultan, ai wannan cin fiska ne?"


"ke sau nawa nayi miki a a gabanta kuma kan laifin da ba naki ba kika hakura."


Shiru kawai tayi tana jinjina hali irin na d'a namiji.
Bashi da tabbas, bashi da gwani, yau idan yana tare da ke gobe ga 'yar uwarki.
Shi yasa idan kina da hankali bai kamata kiga namiji yana wulakanta kishiyarki kiji dad'i ba don tabbas zai dawo kanki wata rana.


****


Saida ta tabbatar ya shiga d'akinshi ta biyoshi.
Da ganin fiskarta taci kuka ba kad'an ba.


D'auke kanshi yayi tamkar bai ganta ba har ta durkusa a gabanshi.


"Yaya kake so nayi da rayuwata Sojana? Na baka hakuri kak'i ka saurareni.
Yanzu kuma ka nuna zargina kakeyi, me ba tab'a yi da har kake zargina haka.
A ganinka zan iya kashe matarka ne?
ko zan cutar da d'an cikinta.
Dan Allah ka gaya min ko don ban haihu ba kake min haka.
Idan don laifin da nayi maka ne yaci a ce ka huce.
Muna neman kusan wata biyu kan abu guda...."


Ta kasa karashe maganar saboda matsanancin kukan da ya tirniketa.


Da gaske yau ta bashi tausayi .
Maida hankalinshi yayi kanta yace.
"Kina nufin baki san kinyi abinda za a zarge ki ba?
Layan da kika fitar kwanaki a d'akinki daga ina kika samoshi.
Meye dalilinki na yanke d'ankwalinki kuma kikace Raheema ce ta yanke?
Idan ba harkan tsubbu kikeyi ba yaya akayi kika san da wad'annan abubuwa?"


Tirkashi , wannan shi ake kira munafurci dodo yakan ci mai shi.
Ita da take gani ta gama da wannan babi ta saka mishi wasuwasi akan Raheema sai kuma abu ya dawo kanta?
Yaya ma akayi yasan ita ta shirya wad'annan abubuwa.


Yadda ta zaro idanuwa tana kallonshi baki sake saida abin yaso bashi dariya amma ya fuske yaci gaba da fad'in.


"Duk abinda mutum zai aikata a rayuwa ya sani akwai Allah, kuma yana ganinshi koda cikin rami ya shiga ya aikata kuwa.
Saboda haka ni a ganina ba laifi bane dan na nuna ban yarda da ke akan Raheema ba, saboda nasan duk abunda kike aikatawa ita kuma ta sani dan dai bata da tashin hankaline shi yasa bata biye miki."


A yanzu kam ya gama d'aureta, ta fahimci yana sane ya kyautar da sark'art dan ya maganceta, amma ta yaya ya sani.


Kunya da nadama suka had'u suka rufe take ta gurfana ta fara neman gafara, dan maganar gaskiya tana son mijinta kuma bata so tayi wasa da igiyoyin aurenta.


Saida ya sata taje ta bawa Raheema hakuri sannan suka daidaita...
[7/12, 8:33 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




*Gargad'i*


Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.




8.


Yanzu saboda Allah karatun littafin da nake shi ne na banza Abban Sultan?


Hafiz ya ce "Na banza ne mana saboda ni dai ban ga abinda ya anfana miki sai lalaci da son jiki, a da ai ba Haka kike ba Heema amma yanzu duk kin zama wata iri kuma kin daina bani kulawa a matsayina na mijinki"


"Ni fa na gaji da wannan tozarcin da kake mini, kun fi so kullum ku ganni zaune bakincikin ku ya kasheni Kai da yan uwanka da matanka? karantun nan fa da nake shi ne yake rage min damuwa da sanya ni farinciki to ba zan daina ba, maganar kulawa kuma ai ba ni kadai bace matarka, idan Kana so ka kirani da ko wacce suna ba zan damu ba, tafiya ce za ka yi Kai da matarso amaryarka Allah ya kiyaye hanya ta na gama maganarta ta wuce dakinta ta barshi nan zaune sake da baki ya bi ta da kallo har ta bace ma ganinshi"


"Oh ni Hafiz yaushe Raheema za ta gane cewa ita ce farincikina da ruhina baki daya? Murmushi ne ya baiyana a fuskarsa saboda wannan fushin da ya gani a fuskarta ya nuna cewa ta na kishinsa, dama Duk wannan fadan da nake mata saboda ta gyara halinta ne amma kullum abubuwan ta kara lalacewa suke, da ya ga babu mai bashi amsar tambayoyin shi sai ya mike ya bita dakin".


Yana shirin shiga dakin, sai ya ji ana shewa da dariya, juyawar da zai yi sai ya ga Zainab tsaye ta watsa mishi wani mugun kallo ta ce,


"Tir wallahi an dai ji kunya, Allah ya isa ban yafe ba dama ta na jin haushinshi tunda ya fada musu cewa wannan tafiyar tare da Fateema zai yi ..."


Katseta yayi ta hanyar daka mata tsawa ya ce,


"Zainab zan Saba miki, wai ke me yasa bakida tausayi da Imani? Idan haukan naki ya tashi baki ji baki gani, Kina ganin halin da take ciki fa, a hakan kike so na tafi na barta cikin damuwa alhalin ba ita kadai bace?"


"Hafiz na gaji da haukatani da kake a kan waccen kodadiyar matar taka, ita ka dai ta fara yin cikine? Ko a kanta aka fara yin laulayi, To tsaya ka ji duk wani makircinta ina sane dashi ta na kafewa da cikin ana cin zalina dan Haka ba zan yarda ba, kuma sai Allah ya saka mini wannan tafiyar da za ka yi da Fateema saboda da ni ya dace ayi tafiyar".


Bai bi ta kanta ba ya shiga dakin Raheema ya barta ta na ta zage zage da magangganun da basu da ce ba, idan ya ce ya biye mata halakata zai yi saboda Zainab irin matan nan ne masu bakin kishi ko jibgarsu za a yi bakinsu ba zai mutum ba. Raheema kuma ta na shiga dakin toilette ta wuce ta yi wanka saboda zafi take ji Sosai a Yan kwanakin nan, bayan ta gama ta fito daure da tawel da dan karami ta na goge gashin kanta da ya jike. Hango Hafiz ta yi Yana zaune bakin gado ya zuba mata idanu ba ko kiftawa baya yayi, ita kuma ta dake ta yi kamar bata ganshi ba saboda haushinsa take ji har yanzu, girgiza kansa yayi ya Mike ya isa inda take ta na neman kayan da za ta saka saboda har yanzu bata so ta ji kamshin man shafawarta, rungumeta yayi ta baya a tare suka sauke ajiyar zuciya ya juyo da ita ta na kokarin kwace kanta ya kara mannata a jikinsa Yana shafa bayanta A hankali, da kyar ta iya ce wa "Wai kun fasa tafiyar ne?"


Ya ce mata "Ta yaya kike tunanin zan iya tafiya Alhalin kina fushi dani my Heema? Ai ko na tafi hankalina ba zai kwanta ba, ina sonki Heema ina kaunarki kice mace ta farko da na fara so, ke ce hasken da take haskaka mini gidana ina bukatarki a rayuwata dan Allah ki daina fushin ko dan lafiyar bbynmu ya karasa maganar fuskarsa tattare da damuwa". Shiru ta yi ta na maganar zuci, amma wasu mazan munafukai ne ji yadda ya tsaya a gabana Yana zubo zance sai ka rantse ni kadai ce matarsa, to su wa'ancan da ya aura baya son su ne komai? Bama wannan ba da Yana sona kamar yanda ya ce ai ba zai mini kishiya ba, kuma gashi ya ce tafiya zai yi da Fateema Allah kadai ya san irin kulawar da zai bata a can, a gabana mahaifiyarsa ta ce mai sai ya kara aure, wani irin tsanarsa ta kara ji a zuciyarta, so ta ke ta janye jikinta daga rungumar da yayi mata amma ina ko motsi ta kasa yi dago kanta da za ta yi yayi nasarar hade bakinsu waje daya ya fara sarafa harshensa cikin bakinta, ita kanta ta san cewa ta na son mijinta so Bana Wasa ba kuma ta yi kewarsa sosai kawai dannewa take saboda kada ya fahimta bata san lokacin da ta rike kansa da hannayenta guda biyu ta na maida mishi martani Sun dauki lokaci mai tsayi suna Abu daya tsakanin miji da mata fa sai Allah da na ga Sun nufi bakin gado na ja musu kofar na wuce Zainab sai harara take zabga mini hhhhh.


Dakin Fateema na nufa naga wainar da ta ke toyawa ita kuma, da isa na na ji ta na cewa,


"Wallahi Mufeeda ba zan yarda ba, dole sai na yi maganinsu ta yi shiru ta na sauraren hudubar kawar tata zuwa can ta cigaba da cewa, sabar ya gama zubda mini mutunci har matansa ya fada ma baya sona, yanzu kuma dan ya raina mini hankali ya ce dani zai yi tafiya salon ya ci zalina a can yauwa kawata shi yasa nake sonki insha Allah Haka zan yi sai anjima kada ya iskeni ban hada kayana ba ki gaishe mini da su Mama koma meye idan mun dawo zamu san abin yi bye" ajiye wayar ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login