Showing 30001 words to 33000 words out of 78322 words

Chapter 11 - MATAN Hafiz Book Complete Document .txt

Unknown   

27 Nov 2024

2517

(xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


*Gargad'i*


*Bamu yarda a juya mana littafi kotawace siga batareda izini ba akiyaye.*


23.
Samun ammi da basma tai suna kokarin tayarda abbu dan sun rigaya da sun yanke shawara gwamma subar asibitin tun kan akuma yi musu wulaqancin da yafi na wanda doctor blessing din tai musu, sun kwammace suyita zamn jira a gida har sanda yayan zai dawo.
dasauri doctor blessing ta qarasa gunsu gamida furta "a'a mikuke shirinyi haka kuma?" ammi tace "tafiya zamuyi likita kamin mu samu kudin saimu dawo ai masa aiki, kinga bazamu cigaba da zama anan ba alhalin bamuda taqaimaimain lokacin da zamu iya biyan kudin aikin nan , a hakan ma mun gode da lamunin da kukai mana na tsawon awanni" murmushi doctor blessing tai gamida qara sakin fuskarta sosai snn tace "bakuda wnn tantamar yanzun domin wani bawan Allah ya dauki nauyin biyan kud'in aikin naku"


da sauri suka dubeta hadda abbun kuwa, kara sakin murmushi doctor blessing tai gamida gyada kai tace "yes kwarai kuwa kada kuyi mamakin jin hakan domin bama Ku kadai ba hadda sauran mutanen cikin asibitin da basuda halin sayen magunguna ko kuma wa'inda za'awa aiki, haka shike mutumin, kyautatawa mutane a jinin sa yake wnn ba abin mamamki bane domin daman dud bayan lokaci yakan shigo asibitin nan ya dinga irin wnn alheran tuntuni ma ba yanzun ba dan haka kuma gashi hakan ya rutsa daku".
basmah batsan sanda tace
"amman Anty ko zamu iya sanin kowanene shi din please? "
shiru doctor blessing tai domin tuntuni tasan Hafiz yaqi jinin yayi alheri a bayyanasa da shi dinne yayi, dan haka ta kasa mgn tana gudun sake ballowa kanta wasu ruwa indai ta bayyana sunannsa bacin tasamu ambaliyar ruwan ta lafa mata kuma, ammi tace "gsky ne ko gdy ne sai muyi masa ay" tayi mgnr tana kallon fyskan doctor blessing Wanda fuskar ammi tacika da farinciki a lkcn gamida godiyar Allah.
sauke ajiyar zuciya doctor blessing din tai gamida cewa "nop kada kudamu da sanin kowaye shi din,kunsan akwai manyan mutanen da basuson adinga bayyan sunayensu akowane alheri sukai ga al'umma to shima wnn mutumin na daya daga cikinsu dan haka kuyi masa addu'a zaifi jin dadinsa akan godiyarku" taqarashe mgnr cikin fara'a.
shuru basma tai xuciyarta na mata tunani kan mutumin daya shigo dazun anya kuwa?.
yayinda ammi ta gyada kai taja sansanyen numfashi gamida furta ''hakane muna roqon Allah ya haskaka rayuwarsa gaba da bayanta yabasa kwanciyar hankali akomi nasa daya shafi rayuwarsa da nutsattsun iyalai da ahali, qarshe kuma muna masa fatan gamawa da iyaye da duniya lfy yasamu babban rabo ranar gobe domin tabbas kowaye zai temakeka a cikin halin buqata da kake ciki alhalin baka sansaba bai sanka ba ba qaramin ma'alheranci bane mungode Allah ya qara bud'i" da amin doctor blessing tai ta amsawa uwa itace tai alherin, yayinda ta dubi abbu tace "baba komi ya wuce zuwa nanda awa 2 za'a zo atafi dakai dakin aiki" gyada kai abbu yai yayinda a hankali ya furta " Allah saka da alheri" sbd har lkcn ciwon baqaramin cinsa yakeba ajiki mgnr ma daqyar ta fito


(kayy!! Ciwo! Ciwo!! Ciwo!!!Allah shibawa marassa lafiyanmu lfy a ko Ina suke dan alfarmar Annabi Muhammad saw amin)


doctor blessing ta duba masa wasu magunguna tabawa ammi tace abasasu ynz yasha ammi ta karba cikin kulawa tana gdy, yayinda basma tabi bayan doctor blessing da sauri wace ta fita, bayan tacewa ammi tana dawowa ynz.
dasauri ta nufi qarasa wajen doctor blessing dake kokarin barin bangaren nasu tace "doctor da d'an sautinta mai sanyi" juwowa Doctor tai ta dubeta, itadai kyaun yarinyar yana matuqar rudarta uwa an zanata dudda kuwa cikin hijab dinta take dogo har qasa, kuma dagani babu mahalukin dazai ganta baiji ta kwanta masa ba, ahaka basmah ta iso kusa da ita ta tsaya tace "dan Allah zan miki wata tambaya guda 1 inba takura doctor" jinjina kai doctor blessing tai tace "to ina sauraranki beauty girl"
(sunan data rada mata knn a xuciyarta harya fito fili)
shiru basmah tayi tana tunanin anya kuwa doctor bazata fassara ta dawata manufa ba akan mgnr dazatai mata? d'an matse bakinta tai wata zuciyar nacewa aikedai da nufin son gano ainihin wani zance ne zaki Mata tambayar bawai kmr ynda zata xata ba dan ynda doctor ta rikice a gabnsa dazun da walaki akwai wani boyayyen abu gamedashi, ad'an shagwabe wnda hkn yabi jikinta, indai zatai mgn zakaga kmr shagwaba take akan haka wanda habitually dinta ne, a hankali tace "emmm ...damn.. damn.... ce. cewa zanyi doctor wannan mutumin.., sai kuma tayi shiru tana sauke ajiyan zuciya mai qarfi... Doctor tace " kiyi mgnr ki kai tsaye wanne mutumin kike mgn kuma miya faru?
ban gane manufarki ba beauty girl,
ko zaki iya mun ynda zanna fahimceki a sosai ?"
d'ago fararen idanunta basma tai ta kuma kallonta kai tsaye tace ....


"daman cewa zanyi wnn mutumin mai kayan sojoji dayashigo room dinmu dazun wai so.....






*By 4 writer's*👩‍👩‍👧‍👧😍
[7/12, 8:34 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




*Gargad'i*


Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.




25.
Idanunsa sanye cikin farin glass,jikinsa sanye cikin wani lallausan farin boyel sai kyalli yk, gaba daya qamshinsa ya gama baibayeta a wajen.
da qyar basmah ta iya bud'e bakinta cikin murmushi ta furta ''Yaya hamiz sauqar yaushe?"
'yar dariya hamiz yayi yace "sauqar yanzun m k'anwarmu, gida kawai naje na ajiye kayana nayo nan dan idanuwana cike suke da qishin ruwan ganinki"
yayi mgnr yana mai sakin tattausan murmushi,
ganin kallon da take masa na kmr mai tunanin wani abu yasa yayi saurin gyara zancen da fad'ar "ke da su ammi sosai nakejin kewarku sbd haka ynz koma ina zaki to haqura zakiyi mu koma gida musha hirar zumunci da muka saba hadda ammi dan nasan abbu yana tareda dalibai ynz haka"
jitai kwalla sun taru a idanunta na tuno inda ta baro abbu ynz haka, batada tabbacin ma ya farka koko"
"Subhanalla, miya faru qanwrmu?!,
daga mgn sai kuka? kona takura miki ne?!, kinga wasa nk miki in akwai inda zaki nikuma sai na qarasa gidan da kaina ay, jin bata ce komi ba saijan ajiyan zuciya datai ne yasa yadan qara matsowa gabnta sosai murya qasa qasa snn yace
"ko kinason na rakaki ne?" girgiza kai tai ta furta "yaya hamiz ahalin ynz ba kowa gida dan abbu ne bashida lfy har ankwanta dashi asibiti" "inalilahe, hamiz ya furta gamida cewa "badai ciwon nasa bane ya yaso ko?"!
gyada kai tayi gamida furta shine amman alhmdlla an masa aiki ynz sauraron farkowarsa mukeyi ynzn ma daka ganni abinci nadawo nayi mana zan koma"
dasauri yabata umarnin tashiga motar tasa, nan tashiga kai tsaye suka nufi hospital din kmr ynda ta fada masa sunan hospital din.


hamiz knn, matashin saurayi dan shekara 31 Wanda zamu iya kiransa shiba dogo ba shiba gajere ba tsaka tsaki yana da kyaunsa shima wankan tarwada ne, shine babban dan marigayi Alhj muttaqa sai qanwarsa nusaiaba su 2 kadai ne yaran marigayin Alhj muttaqa, sai mamarsu hjy Aisha, hjy Aisha ta kasance mace ce mai matuqar son abin duniya shiyasa taketa sawa yayan aminanta masu kudi ana kawowa hamiz din pic's dinsu danya zabi ta aure cikinsu amman shikam yaqi kulawa sbd so 1 tak a ransa shine yamiqawa basma dudda bai shaida mata ba kuwa, sam hjy Aisha ta tsani yanda yake mu'amala da gidansu basmah dandai babu yacce zatayi amman itakam ta tsani talakka wai ina ka fito tsiya ina zaka tsiya komi nasu a tsiyace banda shi mlm usaman mai kashin tsiyane bashida rabon arziqi a duniya ynda ya zauna da marigayi mijinta alhj muttaqa aiyaci ace yayi arziqi shima tuni, bata tunanin arziqin nufin allah ne, shiyasa 'yarta nusaiba ma ta gado ta, hamiz ne kadai ya dauko halin babansa na kyautatawa kowa, sosai hjy Aisha take business din manyan lasa lasai da sarqoqi 6arayin gold da na gasken, wanda a ynzun hamiz shi kuma ya kammala karatunsa yana aiki a nan matatar mai, yanzun ma tafiya yai gano qanin babansa kawu musa a jihar katsina da bashida lfy kwana 6 yai sai yau ya dawo tareda nufo gidansu basma, harga Allah shi kansa baisan iya adadin sonda yakewa basmah ma a rayuwarsa, Wanda koda yaushe zuciyarsa na raya masa yaje yasamu babnta da mgnr ammn nauyin abbu yakeji, wata zuciyar kecewa to ka bari kunya tasa kayi nauyin baki har wani ya shigo cikin rayuwarta, ya rasa dai ta yadda zai bullowa lamarin mafarin knn ya yanke shawarar dosar mus'ab da mgnr insun zauna,
Wnn knn.
*
sanda suka shigo hospital din har dakin dasu abbu yake suka isa tana gaba yana biye, sosai basma tayi farincikin ganin abbu zaune suna mgn fa doctor husain da yake tambayr sa ya yakejin yanayin jikin nasa, abbun nace masa lfy lau saidai yanayin rashin qarfin jiki doctor yayi rubutu awata takarda fara ya dubi ammi yace "mun aunasa babu sauran wata matsala ynz insha Allah, snn wnn magungunan a nemosu ynz zanzo nayi muku bayanin ynda zai dinga amfani dasu, yayi mgnr yana miqawa ammi takardar, ammi ta amsa likitan ya fita shi kuma hamiz na gaisheau gamida yiwa abbun ya jiki abbu ya amsa " Alhmdlla hamiz yaushe ka dawo?"


"yanzu na dawo abbu nakejin lbrn tashin ciwonka a bakin basmah da muka hadu a hnya"
abbu yace hakane to masha Allah ya kabaro mai jikin?"
"da sauqi abbu"
ammi ma ta ce "to Allah qaro afuwa"
yace "amin ammi"
d'an shiru yai snn sukaci gaba da mgn shida abbu hamiz din na cewa yasan su momynsa basu saniba ammn zai kawosu gobe, yayinda ammi take tunanin ina zasu sami kudin siyan wadan nan magungunan nan kuma da likita ya buqata ynz su ba shi ba?, gashi bata san yawan kudin ba ma kuma tana tunanin kudin data sa basmah ta dauko ko 4k basu rufa ba, to misali ma kudin maganin sunkai 4k to mizasu dinga siya sunaci knn da wanne kudin?!.
shiru tai tama kasa bude takakar sai sake jujjuyata takeyi a hannu da qyar dai ta duba,,sosai ta girgiza da ganin abinda aka buqata na maganin, kamin tai wani motsi sai jitai basmah ta amshi takardar tafara dubawa, zaro idanuwa tai waje gamida dafe qirji jin datai kirjin ya buga da qarfi sai 6al 6al3 yake sbd razana, wnn wanne magungu nane guda 5 kudin har dubu 28? Wata zufa taji tana sauqo mata babu shiri zuwa can kuma ruwan kwalla suka cika mata idanuwa tabbb lokaci daya suka had'a idanu da ammi, ammi ta girgiza mata kai akan kada ta kuskura hawayen nn su sauqo...
[7/12, 8:34 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




*Gargad'i*


Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.




24.
"Daman cewa zanyi wnn mutumin mai kayan sojoji da ya shigo room dinmu d'azun wai so nake nace waye shi d'in?"
dubanta doctor blessing tai tace "miyasa kikai mn wnn tambyar beauty?"
d'an turo baki ta danyi snn tace "nima ban sani ba doctor inadai son insan shi d'in waye please"
shiru doctor blessing tai tana kallon kyakkyawar baby face din yarinayar, juyawa tai damanta da hauninta da gabnta da bayanta taga babu mutane sosai gefensu snn ta juyo ta dubi basma tace "dan dai kin shiga raina ne beauty yasa zan fad'a miki matsayinsa anan din, shi din ba ma'aikacin asibiti bane kmr ynda kike zato a tunanina,
shi din land army ne babba, snn kuma matsayinsa anan asibitin ya kasance shi din d'an mai asibitin nan ne ina fatan kin fahimta batun nawa?"
(hmn basma knn sarkin tambaya, wnda dmn babban burinta a rayuwarta ta zama cikakkiyar 'yar jarida wnda ammi da abbu da yy mus'ab kansu sunsn da wnn burin nata)
ynz ma haka ta kasance maimakon ta bawa Doctor blessing din amsarta da "eh" ko a'a saita kuma jeho mata wata sabuwar tambayar da cewa "knn shine ya biyawa abbu kudin aiki doctor?"!
zaro idanuwa doctor blessing tai gamida dafe qirji tace
"waaaa a inaaaa???!
bansan da wnn zancen ba beauty, tayi mgnr tana mai saurin barin gun gamida qarasa cewa "nawuce duba patients" da kallo basmah ta bita kawai, sauke ajiyar zuciya tai gamida juyawa tabar gun ta koma dakinsu aman bawai dan tabar batun ba.
hakan kuwa akayi awa 2 na cika akazo aka dauki Abbu zuwa dakin aikin, cikin ikon Allah zuwa magrib angama yiwa abbu aikinsa andawo dashi dakin nasu saidai har lokacin bai farko ba amman likitocin sun basu tabbacin zai iya farkawa koda yaushe lfy,
Cikin ikon Allah kuwa sai gashi bayan sallar isha'e abbu ya farka, dasauri ammi dake bisa sallaya tana lazumi ta miqe sakamon muryarsa dataji yana ambaton sunanta, zama tai gefensa ta riqo hannunsa ta na share hawayen farinciki ganin datai abbun ya farko lfy, cikin murmushi da d'an qarfin jiki abbu ya miqe ya jingina bayansa da kan gadon yana furta "Alhamdulillah ala kullihalin"


"Alhmdlla ala kulli halin"
itama ammi ta fada, cikin sabon farinciki ammi take tambayrsa ya jikin abbu ya amsa da jiki Alhamdulillah yai masa dad'i a ynda yakeji ynz.
cikin murna ammi ta miqe zata fita abbu yatambya ina zata tace "dmn Doctor yace inka farka akirasa"


"ya amsa da to masha Allah, amman ina basma ne?"


yayi tambayar yana dudduba dakin, anan ammi tace
'' da naso ta siyo mana abinci ne to sakamon babu kud'in a hannunmu ne yasa na ce taje gida akwai wasu yan kud'i nawa da dana ajiye na sana'a nace ta dauko su sai ayi abinda za'ayi mlm"
shiru abbu yai yana jinjina matuqar halacci irin na maryamu , haqiqa tacika mace ta qwarai jaruma mai tsayawa kan kafafunta akowane hali na tausasawa da temakwa matuqa garesu koda yaushe,
sosai yakejin farinciki samunta a matsayin matarsa haqiqa Allah yayi masa kyauta mafi girma a rayuwarsa domin samun mace kamr maryamu baqaramin alheri bane kuma yana fatan yaransu zasuyi koyi da halayen qwarai suma a koina suka kasance godiya ya dingayi wa Allah a zuciyarsa kamin yace "Allah shi miki albarka maryamu, cikin jin kunya da kuma farinciki ammi tace aminn Mlm domin har ranta tanson wnn dua'in nasa.
"mus'ab har yanzun shiru ko?"
abbun yayi mata tambya, tace wlh kam mlm bansan miya tsayar da shi ba"
shiru abbu yai kamin yasaki ajiyan zuciya yace
"to Allah sa lfy"
ammi tace "amin, ni mlm inatunanin ko ba'a samu mai siyan gonar bane kas@n ynkinmu ynz mutane sunyi qaranci masu kudin dud sunyi hijira sabida rashin kwanciyar hankali a yankin na 'yan ta'adda dasuke yawan kai farmaki"
ajiyar zuciya abbu ya sauke yace "wnn qasa tamu Allah dai ya kawo mana kwanciyar hankali cikinta domin ko'ina babu inda bai amsaba da wnn jarabta, amman kamin nan dole sai mu mutane mun gyara tsakaninmu da ubangijinmu, hadda sabawa ubangijj da mike yawanyi ne yake jarabtarmu da yawancin shuwaganni marassa jin tausayinmu amman muddin mukaji k'an junanmu muka daina zalunci hassada giba dasauransu to muma Allah zai kyautata mana ta inda bamuyi tsammaniba dudda ba duka aka taru mutane aka zama 1 dayaba, amman tabbas wasu ke jawa wasu, Allah shi kawo mana dai qarshen wnn tashe tashen hankulan shikuma mus'ab din muna fatan Allah me dosa lfy"
" amin Mlm bari na je nakira likitan"
cewar ammi snn ta fita.


basma ko data samu ta qarasa gida a qafa tun daga asibitin dudda tsananin nisan da ke tsakanin asibitin zuwa gidansu, dan haka sai wajen magrib ta 'isa daqyar kuma ajigace dudda a hanya kamin ma ta iso ita kanta bata iya tantance masu manyan motoci nawa ne suka faka da nufin yimata Left ba taqi basu fuska ba,
wani mai nacin nema har motarsa ya sauko yaita gamata da Allah kan tahau saidai tai masa qaryar matar aurece mijinta take jira snn yawuce itakuma tahau istigfarin qaryar datai, ahakanma sadda taja qasan hijab dinta mai gemu tai niqab da Rabin fuskarta da shi snn ta samu sauqin mutane aranta tanajin haushin rashin fitowa da niqab dinta da bataiba ta mnta shaf, dan tariga tasaba da yawo da niqb abinta ko ina hankali kwance, dan ko hr ynz abbu bai bata damar tsayawa da kowane namiji ba sakamakon akwai wani buri dayakeso ya cika a ransa hakan yake yawan ce mata,saidai bata taba tambayrsa minene burin nasa ba,
a ran abbu wato yanada burin aurawa bababn dan amininsa marigayi alhj muttaqa ita, dan sosai ya yaba da hankalin hamiz,
kusan kullum hamis yana gidan da sunan zuwa yk gaishesu, sosai abbun yafahimci hamiz din nason basma sai dai ita basmah din yalura bata fahimci hakanba dan ynda ta dauki yayanta mus'ab haka ta daukesa ko da suna fira in yazo,wanda ammi kanta tasan da wnn buri na Abba na alaqan dayakeso ya hada,
mus'ab da basmahn ne kawai nm basusan da labarin ba..
Wnn knn


*
dan haka basma na isa gida tayi dabarar dafa musu jallof din shinkafa ta juye a kula ta
yi wanka gamida canza kayan jikinta zuwa wata ash and black doguwar riga kalar ta larabawa mai 'yar himar, ta fito, bakin titi ta tsaya jiran abin hawa dan a lokacin har an gama sallar isaha'e ma a masallacin anguwarsu,


wanda tagani ne ya fito daga motarsa bayan parking dayai a gabanta yasa ta bude baki cikin mamaki gamida zaro fararen idanuwanta waje tana cigaba da kallon isowarsa gareta dan kwata kwata batai tunanin ganin sa ba a wannan lokacin ba,
cikin wani tsadadden murmushinsa ya tsaya gabanta idanunsa sanye cikin farin Glass jikinsa sanye da wani lallausan farin boyel sai kyalli yk, gaba ki daya qamshinsa yagama baibayeta a wajen..






~tofa niko nace Hafiz dinne ko hamiz?🤔~


*By 4 writers*👩‍👩‍👧‍👧😍
[7/12, 8:34 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




*Gargad'i*


Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.




27.
A marairaice ya langabar da kai gamida kama kunnuwansa alamun neman afuwa gamida furta "afuwan my sweet wife, ni kaina nasan na cancanci kimin ma fiye da haka, amman nasan ke mai yawan uxuri ce gareni sabida yanayin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login