Showing 36001 words to 39000 words out of 78322 words

Chapter 13 - MATAN Hafiz Book Complete Document .txt

Unknown   

27 Nov 2024

2519

dalilinki na fadar hakan?"
" Jikinane ya bani?"
Ta basa amsa da hakn, kasa mgn yai, sai binta da ido dayake, tsuke fuska tai tace "kai soja ne ko??" shima fuska gimtse yace "idanunki miya gaya miki?"
tabe baki tayi tace
"sun ko gayamun gaskiya dan ga uniform nan kuwa a jikinka, kasan wani abu kuwa?"
kamar ba zai ce komi ba dan yaga yarinyar kamr zatayi tsiwa ga kuma tambayr tsiya, da qyar ya furta "sai naji snn zan Sani" yayi mgnr yana mai tsareta da kaifaffan idanunsa, karaaaf yaji ta ce
"Na tsani dud wani mai kakin soja a rayuwa sbd basuda kirki ko sunyima kirki sai sunzo sun cuceka ni ganau ce ba jiyau ba"


dasauri ya dubeta dan baiyi tsammanin jin hakan daga bakinta ba, dafe gemu yai kawai yana kallon ta, cigaba da cewatai "na tsani dud wani soja a duniya haka zalika natsani temakonsa gareni ko yaya ne dan haka kudin daka biyawa abbu akai masa aiki zan maidoma da abinka ina fatan ka fahinta yallabai?" kwata kwata Hafiz kasa mgn yai har lkcn zuciyarsa cikeda mamakin yarinyar yana ganinta sanyi sanyi ashe haka take?!
to mi soja yai mata ne ta tsanesa hk? bai zataba yaga ta zaro Biro a gabn rigarsa ta kamo hannunsa ta saka masa gamida miqa masa tafin hannunta tace
"your account number?"
abin dariya yaso basa ma shi a lokacin ba shiri,
kwanyarsa tafara tunanin anya kuwa lafiyanta lau yarinyar nan? Amman saiya kanne dariyar danshima yasomajin game din yamasa dadi dan haka baiyi wata wata ba ya rubuta mata number sa kawai a jikin tafin hannun, itako tayi tunain ko account number ne yasa shiyasa bata wani duba ba saima kallonsa datai tace
"aman fa da sharadi inason mgnr tazama sirri tsakanin mu, tasoma tafiya kamin tadan juyo fuska daure tace ''ka saurari jin alert fa koda yaushe" yanda tayi mgnr ne kmr wata hajiya yada baisan sanda ya fashe da dariya ba , tsayawa tai ta hade fuska gamida dawowa gabnsa ta ajiye kayan hannunta tai ta riqe qugu gamida furta "au mahaukaciya ka mayar dani knn?"
rufe bakinsa yai da kyawawan yatsunsa yace "sorry madam bahaka bane" harararsa tai kadan ta qasan ido gamida duqawa ta dauki kayan ta tace "komadai mikenan saika jini"
ahaka ta shige room dinsu, kamr jira yake tabar gun kuwa yasake tuntsirewa da dariya hadda riqe ciki wanda rabonsa dayai dariya HK tsawon rayuwarsa harya mnta, sosai yarinyar ta qara burgesa salonta da nuna qarfin halinta kan abinda ta tunkara, a fili yace "wnn game din yaimun zam zam bazanso ya ya qare ba....."
kai tsaye yabar gun yanufi room din da heema ke ciki wanda yasamu tayi tagumi yayinda Fatima tai d'ai d'ai tanata sharara baccinta, heema na ganinsa ta juya baynata alamum fushi,....
Shikansa yasan yy laifi tun safe bai sake leqowaba sabida busyn dayasha kansa dan haka ya ajiye ledar hannunsa ya zo gabnta a marairaice ya langabr kai gamida kama kunnuwansa alamun Neman afuwa...








*By 4 writers*👩‍👩‍👧‍👧😍
[7/12, 8:34 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




*Gargad'i*


Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.




28.
Saida ya jima wajen sosai snn yasamu ya miqe tsaye jikinsa ya qarashe mutuwa mururus a kokacin, haka ya isa room din da heeman take, zee wacce tun sanda taga shigowarsa asibitin tai azamar dawowa dakin kamar bata fita ba, cikin yatsine yatsine ta zauna kan kujera batace musu komi ba sai surban yoghurt dinta takeyi hankali kwance tana karkada kafa, haka Hafiz ya shigo ya samesu, su kansu sun lura da kamar yana cikin damuwa, amman babu wanda ya tanka sai sannu da dawowa da sukai masa, sauqe ajiyar zuciya yai gamida duban zee ya umarceta data tashi ya mayar da ita gida hakama ya umarci karimat itama tazo ya sauqeta gida ta huta shi sai ya kwana a asibitin, dudda karimat taso ta kwana wajen 'yar uwar tata amman haka taso badan taso ba saidan tasan Hafiz baya mgn 2, haka yasauqe karimat gida bayan biyawa da ita wajen kayan makulashe dayai yasiyi leda hudu kowace da nama da kayan sanyi cikinta danginsu vanilla ya danqa ma ta babbar ledan ta ta amsa tana gdy snn ta shige gida, suma suna isa gidan ya miqawa zee tata ya dauki dayan ya nufi dakin Fatima da ita, samunta yai gaban laptop dinta tana aiki, dasauri ta miqe tana masa welcome hug gamida sakar masa hot kiss a le6ensa, jiyake a halin da yake ciki babu wani feelings tartare dashi dan haka cikin dabara ya janyeta jikinsa gamida ajiye mata ledan a gabnta nan yake sheda mata itama zai koma asibitin ne wajen heema ya kwana cikin kissa ta furta "to yallabai ko muje tare ne?" girgiza mata kai yayi gamida dan rungumota jikinsa yana shafa bayanta itako sai wani sake shisshige masa takeyi tana tunanin turaren da malaminta yabawa mufeeda qawarta ta bata ta shafa kan jawo hankalin Hafiz ne yafara aiki kmr ynda ya bata tabbaci, jitai ya dagota gamida shafa gefen fuskarta yana mai qaqalo murmushi ya furta "kada ki damu kiyi zamanki kici gaba da aikinki kinga kema zakije aiki goben hospital naku ko, to ki kwanciyarki ki huta banson ki wahala" haka ya mayar da ita ya zaunar gamida dan tsotsan lebenta na qasa ya fice da sauri ya barta cikin tsananin buqatarsa dan jitai aikinma datakeyi ynx ya fita kanta dan haka rufe laptop dintai tana mirgina kan gado gamida shaqar qamshin sa daya bar mata a dakin, batasan sanda hawaye suka fara zubo mata ba na tsananin soyayyar Hafiz dataiwa zuciyarta kamun kazar kuku.
daqyar dai tasamu bacci ya figeta cikeda mafarkin oga Hafiz din aikin sarrafata.
zee kuwa nunawa tai qarara tana buqatar mijinta dan a dazun zaman datai office din doctor blessing ta samu ramla a waya sunyi mgn take ce mata dmn shirin kiranta takeyi dan Mlm yace sharadin maganin dazai bata gobe dole saita kwanta da mijinta a daren yau snn zai yi tasiri sabida taurarin nasara dake yawo a yau, dan haka tabi ta manne masa tun bayan dayayo wanka ya shigo dakin da niyyar mata sallama zai koma asibitin, ganin ynda ta wani kankamesa tana masa salo iri iri sai faman shafa majiyarsa takeyi tana tand'e baki uwa mayya nan ya fahimci nufinta, har ga Allah yasan bazai iya tabuka komi ba sbd damuwar dake tartare dashi har ynz, amman yayi kokarin romance dinta sosai har saida yaji jikinta ya saki alamun saqonsa ya gamsheta dn haka cikin dabara ya janye zee a jikinsa
gamida nuna mata 11 ta wuce kuma gashi heeman ba kowa a wajenta tayi haquri sa hadu goben tanaji tana gani ya fice nan ta zube kan gado dafe da kai cikin tsananin takaici babu wanda yaja mata wnn asarar sai qazamar banzar heeman can, mtsww taja tsoki a fili take furta "komi zaiji a jikinta ma da yake rawar qafar zuwa wajenta ya kwana databi ta tsotse dagani babu wata mamora a jikinta qeqasasshiyar banzan heeman nan, atunanin zee a yanayin rashin jikin heema bazati testing ba a auratayya didda itama zata iya cewa kanta dami kwad'o ya d'ararwa gaya, amman tafi heema cika da kad'an, inda ko qirjinta sun d'anfi na heema girma dan tana kula dasu sabanin heema da tsaftar jikinta ma ya aka qare bare wani gyaran Private part of body nata dan jan hankalin miji, saidai Fatima tafisu jiki sosai, hakama qirjinta yafi nasu girma, wato ga breast wanda har sun soma dan kwanciya ga jiki wanda jikin ta ne yahana mata fitowar shape din qugu sai iyayen hips abinta, haka abin ya hade mata, wai danma tana danyin exercise , to a tunanin zee irinta da irin Fatima sune suke luntsum da ni'ima, shiyasa ynz gaba daya kashi 100 cikin hankalin zee dake kan heema yafara karkatowa kan kishiyar amaryar tata Fatima, quta tai a fili ta kuma furta "zanyi maganinku daya bayan daya ne muje zuwa dai, dagaku har wanda ya ajiye Ku dani kuke zancen.


koda ya koma asibitin ya jima yana tsaye gaban room din da su ammi suka bari yana kallon mutanen dake kaikawo wajen ga alama har an saka wasu ma a dakin, lumshe idanunsa yai,
tana masa gizo sosai yarinyar, barin wajen yai ya nufi wajen heema, saida ya tabatr da taci abubuwan sosai snn yarakata tayo brush ya kamota suka dawo kan gadon dakin ya kwantas da ita shi ma ta samu waje ya kwanta kan wata doguwar kujera da yasa aka kawo masa, dudda heema taso ya kwanta Kn gadon amman yaqi sai ya nuna mata gadon bashida fadi sosai kada ya takura mata, bataso hknba dn harta bude baki zatayi mgn yayi mata alamun


"shihhhht"


da yatsansa manuni Kan lips dinsa, haka ta haqura ta kwanta, shima haka ya kwanta ya rungume jikinsa uwa maraya sai juye juye yake qwalwansa na raya masa shin ina ne zai gano details na yarinyar nan wai ko zai samu sauqin zuciyar sa kanta, wai miyakeji kan tane haka abinda bai taba jiba mai girma haka tunda yake akan kowace mace? sometimes har jiyakeyi numfashinsa kmr yanson yimasa gardama ga bugun zuciya why?.
haka suka kwanta zuciyoyi ba dad'i.
washe gari da safe saiga hajiyar sa sunzo, da Anty Aisha yayar Hafiz din sai mufeeda qanwar Hafiz din tareda nabeela Auta sultan da sultana yaran heema na riqe da hannuwanta, da gudu ko yaran suka haye jikin mahaifiyarsu suka qanqameta cikin murnar ganin ta da sukai.
sunma heema ya jiki dayake hajiyan Hafiz ko mgnr arziqi take zakajita kmr tanayin fad'a sbd hakanne yanayinta, nan tace "amman Hafiz yaza'abar qaramar yarinya a CE itake kulawa da marar lfy? karimatun nan qanwar heema hakafa muka samesu jia, mizai hana daya daga cikin matanka kadaukota suyi jinyar tare inda ranar dole sai dole ranar naka kuma sai naka"
(sosai hjy amina Mmn Hafiz keda kirki ammanfa in taso, in ko ta botsare kowa yashigar mata hanci saita fyatosa kmr dai ynda kuka snta, tanada son yaranta batason taga abinda ka daga musu hankali shiyasa take dirje matan Hafiz din tasss sabida rashin son zmn lafiya a tsakaninsu darashin kulawa irinna heema, dan tasan zamn lfy da tsabta suna daya daga cikin jagororin wanzar da farinciki a rayuwar ma'aurata, to hkn yaqi yuyuwa ta ina hankalin d'an nata zai kwanta ga matansa, danma yana jajircewa a gidnsa da abinma saiyafi HK qazancewa wnda silar hkn nema tasa Hafiz auren fateema kmr dai ynda kuka Sani to, wnn knn)
haka ta juya harshe zuwa larabcinsu,
(dayake dud yaran nata sunajin harshen gaba daya,) to nan shima hafiz ya shiga bata haquri da harshen mahaifiyar tasu Na larabcin,yana mai nuna mata za'ayi hakan kamar yanda tace.
Hafiz ya bude baki zai sake mgn knn saiga doctor Yusuf ya shigo shiyasa yayi shiru da mgnr, nan doctor ya sake duba heema yaga komi normal kuma yaji tabbacin babu Inda ke mata ciwo daga bakinta, dan haka a ranar aka sallamesu suka tafi gida, ahakanma said a hjy amina tabisu gidan ta tarasu zee din da heema da Fatima ta qara buga musu warning da cewa har yanzun tana kan bakanta muddin taji wata cikin su na son cigaba da kawo fitina a gidan nan to wlh zata dau mummunan mataki kuwa kowacece ita, saida tamusu tatas snn ta tafi,


wanshekare ko Hafiz da kansa ya tsara cewa heema xata huta dayin girki har na tsawon wata 1 sabida ta qara warwarewa sosai, kuma hkn bayana nufin cewa zai dauke mata kwana bane zai bata hakkinta kmr sauran, haka zee da Fatima suka tashi kowace fuska daure wato suda girki itada kwanciya da miji saidai su dafa taci knn gsky an cucesu cewarsu, hakan ko dokar oga Hafiz ta fara wakana a gidan dole suka dauketa kuwa.


*
tsawon sati biyu knn Abbu ya warware d'alubansa sunata tururuwar zuwa gaidasa da jiki, Alhamduilla a sati na 3 har ya koma shagonsa yana aune aunen kayan hatsinsa, ya koma kuma makarantarsa da d'alibansa sunci gaba da karatun su na addini na dare nan qofar gidan nasa kamar yanda suka saba kullum bayan sallan isha zuwa 10 suke rufe makarantar da addu'a masu aure su wuce wajen iyalansu marassa aure ma suyi nasu wurin, yayinda kusan kullum hamiz ke gidan dayataso daga aiki sai yaje, dan dole yasa momynsa tazo taiwa abbu yajiki kuwa dudda batai niyya ba.
haka ma sunyi nasarar samun mus'ab a waya bacin basmah ta amso gyaran wayar ammi, nan sukeji daga bakinsa cewar tun zuwansa garin aketa cuku cukun neman asayi gonar da kirki ammn mutane sai son rai suke nunawa, wai qaramar gona ce ga gyare gyare cikinta da za'ayi,kuma tayi nesa da gari daqyar dai aka samu Alhj bawale yasiyeta dubu dari biyar da hamsin, Amman bai kaiga bayar da kudin ba yace sai ankawo masa kudin shanunsa wnn satin snn zai bayar, Ammi dudda tasan gonar tata batada wnn matsaltsalolin da suka lissafo kawaidai abin mutane ne na in sunga kana son siyar da abu a lokacin zasu yita maka ynda sukaga dama,kuma aqalla gonar tafi qarfin million bataso dai mus'ab d'in yaci gaba da zama shiyasa ta amsa da ya amso kudin ansan abun yi dasu, Inda nan ma ta basa labarin wani bawan Allah mai temako ga jama'a ya biyawa abbu kudin aikin har anyi cikin nasara,


a haka ammi da mus'ab suka tsaida mgn, danshi abbu koda ta fad'a masa yaso ma kada ta saida gonar sai Ammi ta nuna a'a asiyar dai d'in Inda ko ba'a siyar ba a can d'in gonar da lokacin amfanin gona yayi mutane na zuwa suna ciccirewa dan sunsan masu gonar basu gari kuma ba ajiyarta aka bayar ba, haka suke kwashe abinda ya fito cikinta batareda tunanin haqqin masu itaba, taci gaba da cewa "amman kaga Mlm in aka saida wnn kuma tsakaninsu da wnda ya siya"


wanda anan ammi ke fadawa abbu idan mus'ab ya zo da kud'in zata basa su ya ja jari wato ya bude shagon saida kayan masarufi kodan su dinga rufawa kai asiri, sosai abbu yayi na'am da wnn Shawara tareda sa mata albarka.


yayinda a gefe basmah kullum babu abinda ke damun zuciyar ta irin ta yanda zata biya mutumin nan kudinsa,damuwar hkn ne yafara zata rama a tsattsaye har ammi ke tambayarta bata lfy koko? man take cemata jiki a sanyaye


"lafia lau Ammi, ina jin ko masassarar dare CE ke tsotsana"


"kidinga shan magani kuma Allah sawaqa"
a cewar Ammi d'in,


babban damuwar tama data nemi number da mutumin ya rubuta mata ta rasa dan tayi copy Nata a takarda, kullum cikin damuwa take da tunani, dud tayi zuru-zuru, asatin ne mus'ab ya dawo, nan su Ammi suka tarasu shida basmah suka fada musu shawarar da suka yanke kan kudin, musab yaji dadi ko, yayinda basmah taita yaqe tana satar kallon kudin uwa ta dauka tabiya bashin nan data azawa kanta, amman inaaaaa bazata iyaba, zuciyarta nata mata saqe saqe tanaji kmr ta fada musu ammi gskyn abinda ke ranta ko zasu temaketa su bata kudin ta biya?
yayinda wata zuciyar ke cewa to ynz wnn kudin shine kadai ya rage muku a rayuwa tayaya zasu ba dun? Koda aurenki yazo ta sune za'a samu ayi abinda ya dace kuma dasune zakuna cigaba da rufawa kanku asiri Inda jujjuyasu za'anayi, sana'ar Abbu kuma bamai qarfi bace,


tana wajen sai jitai hawaye suna shirin zubo mata babu shiri, dasauri tayi dabara sharesu tana qoqarin barin wajen knn taji muryar yaron maqocinsu yace
"Assalamu alaikum wai ance ana sallama da basmah inji wani mutum a waje"
arazane ta juyo har tsintsiyar dake hannunta ta sabule qasa dan daman shara take abbu ya kirasu ita da yah mus'ab d'in,


dafe kirji tai gamida fuddo fararen idanunta waje batasan sanda ta furta cewar "innalillahe..wayyo Ammi abbu yah mus'ab na shiga uku shiknn ya biyoni har gida kar6ar haqqinsa"!


dud ta rud'e ta gigice nan ta fara sakin hawayen dataketa boyo tun dazun, tuni su abbu hankalinsu ya dawo gareta har had'a baki sukeyi wajen furta


"subhanalla,!
shi wa kuma basma?"




✍🏻
*By 4 writer's fasaha 👩‍👩‍👧‍👧😍*
[7/12, 8:34 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




*Gargad'i*


Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.




29.
sai lokacin basmah ta ankara da subul da bakan mgnr da tayi, girgiza kai ta hau yi alamun bakomi yayinda ta tsagaita kukan a dauriyance tana goge hawayen ta , amman har lokacin zuciyarta batabar 6allawa ba, abbu ne da mus'ab suka ida isa gabanta yace "ki fad'a mana miya faru basmah ko kinada wasu ne dazaki gayawa damuwarki bayan mu?"
tsit tai tana tunanin dole kam tayi qarya dan kubutar da kanta astagfirillah ta fad'a a ranta tunkan ta yita, zatayi mgn knn abbu yace "tsaya ina zuwa, zo muje mus'ab" ahaka suka fita waje yaron da aka aiko ya wuce su kuma suka tsaya wajen mutumin, sunyi mgn ta fahimta inda nutumin ke cewa abbu shi sunansa Sha'aibu yaga basmah ne yana son ta da aure shiyasa ya biyo sahu ko Allah zaisa rabon sace, cikin hikimar mgn ta manya a tsarance na hikimar iya mgn ta ynda mutum zai fahimta batareda nuna wulaqanci ba abbu ya nuna yaji dad'i dan dud mai son naka ya gama ma komi,
"saidai wani hanzari ba gudu ba Mlm shu'aibu na jima da yiwa basmah miji lokacin nedai muke jira na auran ubangiji Allah ya ida kawowa.. nan abbu ya basa haquri, dayake mutumin mai fahinta ne sai yaiwa su abbun fatan Allah bada zamn lafia ga auran, snn sukai sallama, haka shu'aibu ya wuce dudda yaso ace yasamu basmah a matsayin mata saidai babu yacce ya iya matar mutum qabarinsa, bakomi zaiyi kokarin fidda ta daga cikin zuciyarsa haka Allah ya qadarta.
su abbu ma suka koma cikin gida amman zuciyar mus'ab cikeda tunanin wai shin miyasa dud tarin mazan da suke zuwa neman auren basmah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login