Showing 27001 words to 30000 words out of 78322 words

Chapter 10 - MATAN Hafiz Book Complete Document .txt

Unknown   

27 Nov 2024

2511

yabi ruwa, murna kawai zee keyi yadda sufa a kan gado, dasauri fateema tanufi shashin zee domin ta kai mata guman heema(dan a zatonta ita kadai Hafiz yakira ya sheds wa)


nan taji zee nata dariya hadda kyakkyatawa ga alama waya ma take, labewa fateema tayi tan sauraronta, nataji zee nabawa qawarta lamra labarin wato haqarta ta cimma ruwa na ruwan kilin dataje ta watsa a matakalan bene sanda taji Heeman naqoqarin fitowa daga dakinta, dankomi gabn ta akai tundaga sulmiyowanta a bene kawo shigowan Hafiz a gidan, danhaka ranta wasai tashiga zuba zance hadda mgnr dataiwa fatiman na qarya cewa Hafiz baison haihuwa.
ba tabar gunba saida taji zee ta gama wayan, sosai Fatima ta shiga kidima, da tashin hankali,lallaima wato ita wnn muguwar matar zata yaudara, gashi ta riga ta banbanka ma cikinta kwayoyin hana haihuwa,


"tab to wlh saidai ayi mutuwar kasko na rashin haihuwa agidan nan, yadda ban haihu ba ba shegiyar da zata haihu kuwa daga wnn lkcn".
abinda Fatima ta furta knn tabar gun.
fateeam kuwa daman Hafiz ya bata umarni ta shiryo wa heema abinda zataci dan haka tai amfani da wnn damar cikin kakkauran tea din data hadawa heema hadda wasu mugayen qwayoyin lalata mahaifa gaba 1 ta saka mata a ciki tana dariya a fili take furta
"yanda nasha kwayan nan nima babu wata shegiyar dazan bari ta dauki ciki a gidan nan( in Baku mnta ba masu karatu sanda zee keyin wayan qarya kwanki ai fateema tajita tana fadar cewa Hafiz baison haihuwa to tun daga lokacin ita fatiman tazata da gske ne tajetasha wasu magunguna Nasu na likitocin wanda haihuwa sai illa masha 'Allah, to daga baya sai ta fahimci anya ba qarya Zee takeyi mata ba, duba da ynda taga yake tarairayan yaransa sultan da sultana, sai ynz dataji gskian zance a bakin zee zarginda tk mata ya tabbata.
qutawa tai tana share qwallan baqinciki dan haka data gama girkin a yanzun tafakaici idon zee tajuye mata nata maganin a abinci wato cikin miya,
dayake tuwon shinkafa da miyan agushi tayi musu hadda asibitin, danhaka qwayar ma datasawa zee irinta heeama ce, daukan abincin tai har daki takaiwa zee uwa basune sukai fada dazun ba,zee kuwa ta yatsine fuska uwa bataji dadin ganin abincinba, nankuwa noqewa tai dan cikinta fall yunwa, dan haka fatema na fita ta hau zaqar abincin nan ba ko bismilla uwa Allah ya aikota, saida ta cinye tas nan tayi gyatsa tamaida kayan kicin ta dawo tai kwanciyarta tana charts hankali kwance.,


Fatima ta shirya tsab ta dukar basket din abincin ta fito tashige motarta direct tanufo asibiti zuciyarta cikeda mugun quduri.


Hafi kuwa tun bayan daya samu yajanye qafansa daga Inda suka hadu da yarinyar nan yanufi dakin da aka kwantar da heema zuciyarsa kwata2 kamanin yarinyar taqi goge masa, sai yaji ma yana kwadayin sake son ganin baby face din nan nata da sound dinta


"bkm nayafe maka"


abinda yatuno knn a mgnrta dashi 1,
samun kansa da d'an sakin murmushin kasan lebe yai,
ga alama yarinyar nada sauqin hali,


ahaka yashiga dakin da heema ke ciki yanayi yana waiwayan ko Allah zaisa yasake *gamdakatar* da ganin yarinyar amman shiru dan HK jiki a matuqar sake sanyaye ya qaraso bakin gadon da heema ke kai, kallonsa heema tai kawai sai ta fashe da kuka danta tabbata babu cikin jikinta kuwa dudda qwallafa rai datai dashi itama,....
zama Hafiz yai gamida kamota zaune ya rungumeta tsam a jikinsa yana d'an bubbuga bayanta alamun rarrashi...karar wayarsa yasashi dan janyewa daga gareta, ganin hajiyarsa CE yasadhi saurin barin gun, waje ya fita ya daga wayar nan take cemasa taga missed Cull dinsa ynz lfy? Nan yasheda mata hinda heema take ciki, sosai hjyn taji tausayin heema dan haka tacewa Hafiz gatana zuwa asibitin ta dudata, dan a lokacin ma yakeji daga bakinta ashe dadynsa yayi tafia Egypt. Ajiye wayan yai yana shirin juyowa ya koma dakin heema idanunsa suka sake hango masa yarinyar dayake mararin sake gani a rayuwarsa, sosai yayi mamkin yanda ya hangeta tawuce tana share qwalla, kan yayi wani motsi sai gashi Fatima ta 6ullo a gabansa hannunta dauke da basket din kalacin su, saida ta gaishesa hadda masa yamai jiki snn tawuce dakin da take tunanin heema na ciki, yayinda shi kuma yajuya Inda yarinyar take bai ganta ba, aqalla yayi 3 mnt yana dube dube bai hange ta ba, d'an tabe baki yai gamida daga kafafunda alamun oho harzai juya kmr ance ya kalli setin wata darbejiya, aiko canya hangota ta hade kai da qafa alamun kukan takeyi, tsura mata ido yai sosai daga nan Inda yake tsaye yana hangota,


lumshe idanunsa yai lkc daya yaji shigowan text message a wayansa, zaro wayan ya duba, major general dinsu ne me Neman sa a barrack ynx, abinda saqon ya qunsa knn,


motsa red Lip's sa yai gamida shafar kwantaccen sajen fuskarsa Wanda keta sheqi.
fararen idanunsa ya sake saukewa a kanta daga nan Inda yk tsaye bacin maida wayansa a aljihun jeans din jikinsa na kakin sojoji dayai had'da rigarsa da facing cab dinsu,


"mike da munta to?!!!"


tanbayr dayaiwa zuciyarsa knn a farko.
zuciyarsa na tunanin shin yaqarsa gunta yaji damuwarta koko Yakoma wajen heema dan qara rarrashinta akan rashin da sukayi???






*To readers insha Allah nan zamu tsaya a labarin Matan hafix sai Allah yakaimu angama azumi snn zaku sake jinmu insha Allah mun dawo gareku.*


*Allan datar damu albarkar dake cikin watan Ramadan amin ya karbi adduo'inmu ya yafe mana yabiya mana buqatanmu na alhreri amin*👏🏼


*Bissalam🤝🏻*






*By 4 writer's😍*
[7/12, 8:34 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




*Gargad'i*


Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.


*Sisters mungode da addo'inku ga marar lafiyarmu Allah ya qara zumunci a tsakani🤝🏻🤝🏻*




21.
...Rai bace Hafiz ya furta "dakata naji komi daga bakinki doctor blessing basai kin cemun wani abu ba, yana gama furta hakan ya zaro wayarsa yana lallatsawa, sosai Dr blessing ta qara tsurewa dan tabbas ranta ya bata mahaifin sa zai kira, bata Ankara ba ko taji hawaye na biyo mata itako ta shiga ukku da wnn aikin take ciyarda kanta da yaranta ta fantama iyason ranta tayi qaryarta ynz idan aka rabata dashi ai karyarta ta qare mutane dariya zasuyi mata musamman wanda takewa kallon hadarin kaji.
Sukuwa su ammi suncika da mamakin abinda ke faruwa wajen, tambayoyi cikeda cikinsu fall, shin wnn sojan mike hadinsu da Dr blessing haka har take durqushin bashi haquri dudda rashin kirkin nata?
(dan kwata 2 basuyi tunanin shi d'an mai asibitin bane)
kuma ga alamu shi ba likita bane to ya akayi ne?''
tambayar dake cigaba da kewaye kwakwalunsu knn amman babu damar yi.
dan shi kuwa abbu a lkcn ma yaji kamar an tsokano masa ciwon nasa, shi kadai yasan yanda yakeji don sama sama kawai yakejin mike faruwa yayinda basmah har lokacin batabar sharar kwalla ba hannunta cikin na abbun ta.


"Hello bro kana inane? OK to please ina hospital din ku shigo please kaida bro nuran, OK ina sauraranku ynx"

Katse wayar yai, ya medo dubansa ga Dr blessing fuska babau annuri ya furta da yarenta
"nawane kud'in aikin nasu"


da sauri ta sadda kanta qasa tana in ina tama kasa mgn, biyoni, abinda yace knn yajuya ya har zai fita saikuma yadawo gabnsu ammi fuska a dan sake dudda har lokacin ransa babu dadi ya ce "kuyi haquri dan Allah ba aladar asibitin nan bane wulaqanta mutane mai asibitin ma bai laminci haknba, kunsan mutane akwai d'alihan akwai salihan ako inane ammn kuyi haquri kada ku tafi ina zuwa, kamin ammi tace wani yayi saurin ficewa itama Dr blessing tabi bayansa jiki babu kwari.
basma ta dauke idanunta akansa gamida ajiyesu kan na amminta bayan ta share kwallan shigewa tai jikin ammi tana sakin wani sabon kukan qasa qasa.


**
fateema kuwa koda ta shiga wajen heema Sam bata nuna mata wani mugun hali ba saima rarrashinta take da bata haquri kan rashin da sukayi na asaran beby, har take bata qarfin gwiwan kada tadamu dan mijin nasu ai gwarzo ne zasu samu wani babyn soon kada ta damu.
a zuciyarta kuwa cewa take munafuka keda haihuwa a gidan Hafiz saidai kuga anayi keda dayar munafukar zee, wlh mutuwar kasko zamuyi gaba daynmu ynda ban haihuba kuma kunyi kadan, fatana dai kidai sha tea din nan komi zaimin dai-dai ne.
cikin kissa ta daukowa heema kakkauran tea din nan data hado mata Wanda pills din datasaka a ciki sun jima da gama narkewa,
wani munafikin murmushi ta saki gamida gyad'a kai ta cije lips , ahaka ta juyo ta dawo ta zauna kan gefen bed din da heema ke akai tace "sannu heema amshi tea din nan kisha nasan zakiji dadi 'yan hanjinki zasu warware dan nasan baki sawa cikinki komiba, kuma abinci ki da kikafi so ma shi nayo miki kici ko kyaji karfin jikinki dan zama da ciwo ga yunwa mu likitoci munsan ba qaramin illa yake sake haifarwa patients ba"


jiki babu kwari heema ta amshi cup din tareda qaqaro murmushi dudda bata buqatar tea din amman ta furta
"ngd da kulawanki gareni fateema..., katseta fateema tai a d'an murnushe ta furta " shihh,,,, kisha tea din dai ai babu gdy a tsakaninmu sbd na fahimci ke mutuniyar kirkice heema fiyeda zee kuma insha Allah zaki sameni da koyi dake a kyawawn halayenki musamman na haquri da kauda kai, bazan qara biyewa zee ba zanso mu had'a kanmu mu ukun nan a matsayinmu na *matan Hafiz,* fad'a ya qare a tsakaninmu insha Allah oga Hafiz yagama kukan rashin jin dad'in mu'amalanmu da juna a gidansa saidai san barka inda ynz tafiyarmu tazama d'aya daku" taqarashe mgnr a sigar wani rainin wayau.
heema ko ta aminta da gaske fateema take mgnrta har zucci, sai murmushi ta keyi taji kaso cikin 100 na damuwar 6arin datai kashi 60 sun tafi,


fateeam ganin kamar heema na jinkirin shan tea din gashi batason wani ya shigo ya rosa mata tsari ga kuma hafiz tabarosa waje tadauro ya shigo ynz musammn ma data lura kmr heema bata buqatar shayin abincin take buqata gashi kuma iya tea din ta saka maganin kuma tasan Hafiz na shigowa inya fahimci tafi buqatar abincin to tabbas shi zata ci, danshi bai lamunci takurawa wani ba a rayuwa kan ra'ayinsa da sauransu,dan haka fateeam amsar cup din tayi daga hannun heema a yaudare ta nufi bakin heeman dashi tana furta


"please sha kinji sis...










*By 4 writers👩‍👩‍👧‍👧😍*
[7/12, 8:34 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




*Gargad'i*


Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.




22.
"Please sha kinji sis daure ko kyaji kuzari kincin abincin bashine mafita ba".


ahaka heema ta dinga kurbar tea din badan tana so ba, yayinda fateema bata sauke cup din a bakinta ba face saida ya zama empty.
ajiye cup din tai gamida sakin wani narkakken munafikin murmushin jin dadin ta gama aikinta, tasan inda har heema tai gigin shan shayin nan data sawa wnn hatsabibiyar qwayar to haihuwa ko tarigaya datayi bye bye da ita, yayinda a fili fateema ta saki 'yar dariya tana kakkabe hannuwanta tana cewa
"shikenan ay fam fam fam, bagashi har angama da wuce wajen ba, yanzun zaki iya cin abincin in kinso"
kallonta heeama tai da mamakin jin kalmarta ta qarshe "in kinso?" kmr dai ba ita bace ynz ta gama lallaba ta kan tasha tea ba? to kodai wani abun ne ta shirya mata Dn itakam ynz kishiya tajima da sanin mugayen halinta, dasauri kuma ta kauda zancen a ranta tana tunanin ai koyaya ne Fatima tafi zee kirki inda ita ko leqota bataiba gashi ita fateema tazo har ma tana lallaba ta akan taci abunci Wanda mijinsu yadace ace yana wnn fagen bata wnn kulawan yanzun bawai kishiya ba, saitai tunanin may be Fatima bata son matsa mata ne kan ta qaracin wani abun kuma tunda tasamu ta shanye tea din duka, murmushi heema tayi gamida furta"zubomin d'an kadan shima dan kince abincin mutumina ne kikayo, inyaso shauran naci in an jima" miqewa fateema tayi batareda tace komiba ahakan tazubo ta ajiye mata plat din, ngd" cewar heema wa Fatima, wani guntun murmushi tai tace nima ngd sis heema, tayi mgnr a qudundune (wato bima'ana godiyarta Kn temakwa datai tasha maganin nan batareda sanin ta ba)
cokali uku tai ta ajiye cokalin tace "fateema ko kinga yallabanmu kuwa?"
janye fuskarta fateema tai daga kan wayarta daga latse latsen da take kamin tadan tabe baki tace "uhm dazun dai da zan ahigo nabarosa waje yana waya kilan wani uzirin ne ya taso masu kinsan aikinsu akwai ujila" shuru heema tai gamida tunanin duka duka yaushe aka auro ta ko watannni bata rufaba dahar take fada mata ujilar aikin mijinta itada ta share Sama da shekaru taredashi tasani tasan3 Indai aikin soja ne babu zama to wa kuma zaizo yabata lbr daga baya?,
d'an murmushi dai tayi gamida gyada kai tareda furta "hakane fateema Allah medo mana da shi lfy" fateema tace "amin"
a taqaice gamida zura earpieces a kunne tanajin kid'a abunta, yayinda heema ta kishingida hannunta a saman cikinta idanunta a lumshe qasan zuciyart na qarajin rashin dadin zubewar cikin nata still.


Hafiz kuwa tun fitowarsa a room din su abbu yaja bakin motarsa ya tsaya ransa bace, ahaka doctor blessing ta iso ta samesa tana dad'a basa haquri aman ko kallonta baiba saima kallon watch din hanunnunsa dayake famanyi time to time, isowar yayun sa haisam da imran ne yasa shi miqewa tsaye sosai daga jinginar dayai a jikin motar tasa, yayinda Doctor blessing ta qara tsurewa ganin antafo harda haisam dan shima zafine dashi zata iya cewa ma kwamma kwamma Hafiz dashi wani lkcn kan amsar afuwa, ta tabbata da shine jin kunnuwansa yaji tana wulaqanta patient din nan da tuni ta jima da sanin inda dare yai mata,
nura ne mai sauqin cikinsu ma.
nan suka qaraso gamida shaking da hannun juna suka rungimi juna su ukun, haisam yace "yadai sojanmu? ka buqaci ganin mu kmr kasan kuwa muna tareda nuran"
dan guntun murmushi Hafiz yai yace "brothers nakiraku danna sheda muku dady na tufkan kirki a hospital din nan ana warware masa ita da tsiya"!
"kamary bamu ganeba fa Hafiz, miya faru?"!!
Juyawa yai yana kallon dr bleesing dake tsiyayar da kwalla yace "nayi zaton tunda jimawa kin gyara halayenki kmr ynda naji dady na yawan complained akanki akan sauran doctors na asibitin nan, nazata dakikaga yanda nashiga rudu sakamakon halinda kika ga nashiga na rashin da mukayi da matata harkika iya rarashin kika kwantarmun da hankali, Azatona kowane patients a hospital din nan irin kular da kike basa knn a matsayinki na babba wacce ta mallaki hankalin ta,
ki kwatanta kigani a misali dakece a matsayin bayin Allahn can aka maki hakan yazakiji knn?
Zatayi mgn yadakat da ita a matuqar tsawace gamida furta "wait ban gama ba ay, snn yaci gabada furta ''knn dady ya daukeki aikine don ki dinga wulaqanta mutane in sunzo? Kokuma komin dare ki dinga korasu in basu kawo abinda aka buqata ba? Knn dady yna qoqarin ganin yana kyautata tsakaninsa da majinyatansa Amman ke kina sawa anawa asibitinsa kallon dud likitoci cikin asibitin marassa kirki ne?!
domin irinkune kuke sawa akewa likitoci kudin goro dan haka Yaya haisam abunda yafaru shine ..... nan ya fada mu su komi ya ji gameda abinda yafaru da su abbu da ita, da kalar tozarcin datai, Hafiz ya kara kallonta yace kiyankewa kanki hukuncin dakikaga ya dace dake kwatankwacin abinda kika shuka da zaki girbe OK"
Haisam yace Hafiz aibasai ka bata choice ba kawai ta fuskanci gate shine kawai mgn danmu bamu tareda mawulaqantan mutane"
sosai ta kuma rudewa, kuka share share hadda majina ta zube qasa takama qafafun Hafiz Dana haisam tana tuba tana ahi amman sunki kulata, sosai tausayinta yakama nura dan haka ya furta "brothers muyi haquri please mubata change na qarshe muddin bata gyaraba shiknn taiwa kanta".
(haka al'adar yan uwan take muddin suka hadu kan wani batu kuma wani yakawo ra'ayinsa a kai suna amsa)


hakance ta faru ynz, Dr blessing taci albarkacin nura dan haka sosai taji sauqi a ranta, tai ta gdy uwa bakinta ya yage, tajuya knn zata tafi haisam yace "zamusa idanuwanmu akanki zamu bibiyeki zakuma muji daga bakin mutane muddin baki canza ba ko? Hmnn zamu dauki hukunci tunkan ma dady yaji batun wnda munsn shima abinda zaiyi knn.
tayi saurin cewa
"ay wallayi baja akumaba ganin idon Jesus na tuba"
tsoki hafiz yai gamida dafe kai dubanta yai yace "kuma ki tabbatar dakin je kinba mutanen nan haquri snn zan biya kudin aikin nasu, bama su kadaiba dud Wasu masu karamin karfi dake kwance anan basuda halin yin wani abun kimin list ina sauraranki, dasauri ta dinga amsawa da to, to, sun gode yallabai"
Hafiz dauke kansa yai kmr baijin mitake cewa ma, snn tabar gun tanufi room dinsu ammi dasauri har tana buga tuntube.


haka yan uwan sukaci gaba da tataunawa Kn lamarin har Hafiz yafada musu abinda yafaru dasu gameda heema nan sukaje room din datake kwance suka mata ya jikin, cikin kisisina ma Fatima ta gaidasu dasuka tashi tafiya ko kowanne saida ya ajiyewa heema bandir na 100k snn suka wuce,fateema ko taji baqincikin hakan 6oyewa dai tai tana musu gdy.


bayan Hafiz yarakasu sun shiga mota yana shirin komawa room din knn wayar ogansu ta kuma shugowa,


"ya'ilahee Allah"!
ya furta gamida dafe kai, shaf tension din dake kansa yasa shi mantawa ogansa na nemnsa a barrack tun kiran dayai masa dazun kuwa har ya amsa masa da gashi nan zuwa, haquri yabasa gamida basa uzurin daya riqesa wato iyalinsa yakawo hospital aman gashinan zuwa ynz, dasauri ko ya bude motarsa ya tayar da ita gamida barin asibitin gaba daya.


Doctor blessing ko cikin sakin fuska gamida washe baki ta shiga room dinsu ammi uwa ba ita bace tagama sharban kuka ba kuwa ynx








*By 4 writers*👩‍👩‍👧‍👧😍
[7/12, 8:34 AM] Xainab Documen: .*♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login