Showing 21001 words to 24000 words out of 78322 words
mangoro wajen Babu hayaniya sosai ajiyar zuciya ya sauke ya ce,
"Amina wai me yasa Baki so na zo gidanku? Idan har kinsan baki Sona ki fada mini na kama gabana, ni ba yaro bane da zaki dinga wasa da hankali na. Ki fito fili ki fada mini abinda yake ranki yafi wannan boye boyen da kike mini ya ida maganarshi tare da hade rai."
Cikin tashin hankali ta fara magana "Kayi hakuri Allah ba haka bane ta shiga fada mishi irin kallubalen da yake gabansu da yadda take iya kokarinta wajen ganin ta magance abin."
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "Amina Ni dai kawai ki bani dama in zo gidan insha Allah Babu abinda zai faru sai alheri". Da kyar ta amine akan next week ya zo. Haka dai abubuwan suka dinga wakana shima Ahmed iyayenshi sunki amince mishi ya auri Amina, a cewarsu me zai yi da larabawa su da ba'a musu kishiya ga hausawa Nan iri iri yace sai bare. Malam Saida ya je wajen megari tukunna mahaifansa ya amince ita ma Amina iyayenta sun amince saboda sakasu tayi agaba da kuka Bata cin komai.
Bayan shekara uku abubuwa dayawa sun faru ciki kuwa harda kammala karatun Ahmed da Kuma auren da yayi har Allah ya azurtashi da samun maza 2 haisam da nura sai Aisha,
suna zaune a garin kano kasancewa a can aka turashi aiki.
Aisha tana yin shekara biyu aka haifi Hafiz tun Daga shi haihuwa ta tsaya musu cikin ikon Allah Hafiz Yana yin shekara shida aka Kuma samu Mufeeda bayan wasu shekaru aka samu Nabeela autar Mama kenan, yaran sun taso cikin tsananin kulawar mahaifansu su yaya nura sunyi aure da matayensu, itama Anty Aisha ta gama makarantar ta na jarida Daga Nan aka Yi mata aure tareda wani Dan kasuwa inda ya nuna shi Bai amince tayi aiki ba babu yadda ta iya dole ta hakura badan ta so ba, yaransu uku Imrane, Mubarak, Sudays. Ita ma Mufeeda ta gama school ta auri wani Dr Muhsin yarinyarta daya Aymana, ita Nabeela karatunta take Babu ruwanta da samari saura shekara uku ta gama Burinta ta zama Dr ta gaji mahaifinta. Hafiz ma ya gama karatunsa,
saidai a shekarar ne kuma karayar arziqi ta samu mahaifinsa doctor Ahmed sakamakon kudi daya zuba maqudai a harkar wani kasuwanci nasa da abokansa aka nemi abokan da kudin aka rasa shiyasa rayuwa take d'an gaya musu a lkc,
danma sauqinta yaya haisam da Yaya nura suna temakawa gidan nasu sosai dud in sun samu albashi ,(dashike teaching sukeyi)
Hafiz tun Yana yaro yake sha'awar aikin sojoji da ya fada ma iyayenshi Basu hanashi ba addu'a suka masa Allah ya tsare shi yasa kuma burinsa ya cika, to dayake yanayin qasan tamu inba kanada wani tsayayye ba ko cin hanci a wasu wuraran to ba lalle aiki yazo ma da sauqi ba, shiyasa yahada da yan Neman nakan sa shima a lokacin bai zauna haka ba buga nan buga nan.
hafiz haddaden saurayi dan kimanin shekaru talatin da biyu matashi mai jini ajiki Yan mata sai kawo tallan kansu suke Yana watsar da su saboda shi mutum ne mai son natsatsiyar mace Kamila mai addini da tsabta, dan alokacin bai kula kowa face heema dantun yana karatu ta tsaya jiransa batareda ta kula kowa ba dan sunyi alqawarin aure, farkon haduwansu yafara ne wataran tunda arziqin babansa yafito gidan nasu a mota daya daga motocin gidansu
wabda tuki yake a hankali Yana sauren karatun shek Sudays Yana bin karatun har ya wuce sai ya dawo baya ya tsaya kusa da ita, tana ganinshi ta kauda kanta ta cigaba da tafiyarta da sauri da sauri yunwa take ji saboda saukowarsu Daga islamiya kenan, ta sani naci wallahi dibeshi sai wani binta yake Kamar ya santa watakila irin mutanen nan ne masu bata diyan mutane mtsss taja tsaki ta shige cikin gidan su da gudu.
Raheemat kenan Diyar Alhaji jafar da Farida ita ce ta biyu a wajen mahaifanta ta Kamala karatunta na Family economy tana zaman jiran aiki, tana da kyau dai-dai misali Bata fiye son hayaniya gata da son karatun novel shi yasa basa shiri da mahaifiyata saboda ita ta zauna tana karatun ko motsi Bata yi a shekara kiranta Bata ji, Momy ta tayi bugun har ta hakura yayarta da kanwarta kuwa haushinta suke ji. Wannan kenan
Ajiyar zuciya Hafiz ya sauke ya lumshe idanunsa saboda yarinyar ta tafi da ruhinsa juyawa yayi ya ahiga motarshi ya tafi da nufin gobe zai dawo koda za ta wulakantashi ne shi dai kawai ta saurareshi ko hankalinshi zai kwanta.
Agurguje, haka dai Hafiz ya dinga tsintirin zuwa gidan su Raheema tun tana fitowa da kyar har ya shawo kanta. Soyayya sosai suke ma junan su tamkar su hadiye juna, to ana cikin hkn kuma sai wnn ibtila'e ya fadawa arziqin babnsa,
to a iyayensu suka shiga maganar ba'a dauki wani lokaci mai mai tsayi ba aka daura musu aure abinsu cikin rufin asiri da temakon 'yan uwa na Hafiz din...
*By 4 writers fasaha*
[7/12, 8:34 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!
*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.
Written by.
*FOUR GORGEOUS WRITERS*
-Raheenat mahmud.
-Mmn Abduljalal.
-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).
-Matan Borno.
*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*
Bismillahirrahmanirraheem.
*Gargad'i*
Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.
17.
Iyayen Raheema sunyi rawar a zo a gani, saboda sun Kawata gidan Raheema kujeru ma seti biyu aka saka mata a falon kasancewa yana da girma sosai dakuma shida ne sai katon falonsu bayan yan kawo amarya duk sun watse sai yaba tsarin gidan suke. Bayan Hafiz ya sallami abokanshi ya shigo gida sakiyar gadon ya hangota sai kuka take, da sauri ya karaso wajenta ya rungumeta yana lallashinta ya mikar da ita tsaye suka shiga toilets domin yin Alwala dan gabatar da nafila. Wannan daren dai Hafiz ba zai taba mantawa da ita saboda sun raya daren Heema tasha Albarka ba adadi. Wani irin kulawa Hafiz ya dinga bama Heema burinsa ya faranta mata dudda dai bashi garesa a kokcn ba Amman yana qoqari, sunga rayuwa suma ,sosai hema tai haquri da yanayin samun mujinta in an samu ayi in ba'a samuba kuma a haqura, kullum suna manne da juna , komai tare suke yi.
Inko zaya fita qwadago harda kukanta da kyar yake lallashin ta ya tafi ta zauna bisa daya daga cikin kujerun falonta ta yi tagumi da taga kadaici zai dameta sai ta kunna daga tayi sa'a kuwa an turo littafin da take mugun so nan fa ta fara karanta wani lokacin tayi murmushi ko tayi dariya ita kadai har karfe biyu tayi bata sani, da sauri ta kashe datar ta shiga toilets domin yin Alwala. Haka dai Rayuwrsu ta cigaba da tafiya tun Hafiz yana yi mata fada a kan ta rage karance karancen littattafan da take har ya zuba mata idanu yaga iya gudun ruwanta suna cikin wannan halin ta fara laulayi sosai take shan wahala musamman cikin dare kwana take taba amai sai da cikinta ya shiga wata shida ta samu kanta. Daga nan ta cigaba da sana'arta wato karatun falon nata ma sai tayi sati bata gyara shi ba , dakin barcinsu kuwa sai dai Hafiz ya gyara da kanshi ita bata da aiki sai tayi wanka taci ado ta zauna falo so uku abincinta yana konewa har fushi Hafiz yayi da ita duka da ta gyara Amma a banza a haka dai wata ranar juma'a Allah ya sauketa lafiya ta samu bby boye kyakyyawa dashi ranar suna yaron yaci sunan Sultan, saboda Hafiz ya nuna bai amince taje shan kunu gida sai mahaifiyarta ta aiko mata wata dattijuwa ta cigaba da bata kullawa na musamman, gidan ya gyaru sosai saboda matar kullum cikin aiki take bata gajiya ko kadan har Hafiz yaji aranshi dama ta zauna tare dasu ne. Heema tana yin arba'in Inna Rumana ta tafi kafin sati ungulu ta koma gidanta na tsamiya wato kazancin Heema ya dawo wataranar asabar sabar Takaici Hafiz ya mike yana gyara falon sai sallamar Mahaifiyarsa yaji abakin falon tashigo, subahanallah ni Amina me zan gani? Wato Hafiz sabar iskanci Yar aikinta ka zama? Yana shirin yin magana ta daga mishi hannu, yi mini shiri ko naci mutuncinka yanzun nan marar hankali tsoko kawai, ta juyo tana balla ma Heema harara ko gausuwar da take mata ma bata amsa ba tace, "Raheema ce wace irin mata ce marar tunani da sanin ya kamata? Kina zaune mijinki yana aiki tsabar lalaci da rashin sanin ciwon Kai to tun wuri ki gyara tun lokaci bai kure miki ba tana gama fadar haka ta wuce ta tafi tana ta fada".
abubuwa dayawa dai sunata faruwa a lkcn harda na farinciki, domi kuwa arziqin mahaifin Hafiz yadawo sakamon abokansa nan guda 2 Alhj sabe da Alhj muttaqa sun dawo masa da dukiyarsa hrda riba ba adai(Ashe dasukaje qasan waje wani baban business sukai da kudin kuma sun fidda layukan da za'a samesu sbd ayanda sukaji lbrn business din bakaramin kudi ake qara samuba shiyasa sukabace 6@t basu ba labarinsu don niyyrasu su dawoma da mutumin kirkin abokin nasu doctor Ahmed surprise dan dukiyarsa tafi tasu yawa aciki ba kadan ba kuma gashi kuwa. Familyn Alhj Muhammad farinciki da gidiyan Allah babu tsagaitawa kuwa da sukai a lkcn.
kankance mi arziki yadawo mazauninsa, a kuma shekarar ne Hafiz yasamu aikin soja kuma a babban muqami,snn gefe guda ga kasuwancin da sukeyi da mahaifinsa da sauran yayunsa da suma a lkcn sunbar aikin teaching sun zama manya manyan ma'ikatan gwamnati.
gida hadadde gari guda haifiz ya gina Wanda babu ne kawai babu a cikinsa sultan da mamansa gata suke ta sha gun oga Hafiz dan a yanzun kam basuda matsalr komi na matsin rayuwa sai jin dadi,
wata safiyar juma'a heema ta tashi da ciwon Kai zazzabi mai zafi gaske tana zuwa asibiti likitoci suka tabbatar mata da cewa tanada shigar ciki har tsayin wata biyu tayi mamaki sosai da bata gane cewa tanada shigar sa ba.
nan ta kama kumbure kumbure har ta isa gida ta fada ma Hafiz yayi murna sosai saboda Hafiz yana son yara yayi mata kashedi cewa kada ta kuskura ta salwantar mishi da yaro idan ba haka ba zai saba mata badan ranta ya so ba.
Haka dai ta cigaba da kulawa da yaronta Sultan yana da wata takwas ya cire kanshi nono haka dai abubuwa suka dinga da wakana wata ranar Alhamis Heema ta tashi da nakuda wannan karon bata wani sha wahala sosai ta haifo bbyn ta mace mai kama da Mahaifinsa ranar suna aka rada ma yarinyar Sultana. Tun bayan haihuwar sultana abubuwan suka Kara rincabe mata har watarana Mahaifiyar Hafiz ta zo gidan tana shigowa falon ta koma da baya da sauri saboda wani irin wari da kazani da suka yi mata sallama falon ya baci kaca kaca. Wayarta ta ciro ta Kira Hafiz tace mishi duk abinda yake ya zo gida tana jiranshi ba'a dauki lokaci mai tsayi sai gashi baima gyara parking motarshi da Kyau ya zo wajen Mahaifinsa yana tambayar ta lafiya?" Magana ta fara yi cikin takaici da bakinci "Hafiz ni wacece a wajenka?" Cike da manakin tambayar ya ce "Mahaifiyarta!" Ta ce "To idan har ka daukeni a matsayin Mahaifiya ina so ka Kara aure nan da sati biyu sati biyu kawai na baka ba shawara nake baka ba umarni ne ta sa Kai ta tafi". Ko motsin kirki Hafiz ya kasa yi yana mamakin wannan lamarin, da kyar ya daga kafarshi ya shiga falon ai da sauri ya toshe hancinshi saboda wani irin kazani da falon yake, Sultana da Sultan duk sun bata falon ita ko Heema sai shating take tana murmushi bata ma San ya shigo ba, da sauri ya fisge wayar a hannunta yayi gifa da ita, tana Shirin magana ya balla mata wani uban mari kafin ta dawo hankalinta ya Kara mata wani ta dafe kuncinta tana kuka sosai ta ce"Hafiz ni ka mara?" A zazzafe ya ce "An mareki din nace an mariki ko za ki rama ne? Sakacinki da rashin hankalinki ya janyo mini auren da Ban shirya ba, Ni na kasa gane ce wace irin mata ce? Kalli falon ki yadda ya koma sai ka rantse yayi wata uku ba'a gyara ba, dubi yadda yaran nan suka maida mini falo ko ina jurwayin futsarin su, tana Shirin magana ya daka mata tsama duk ilahirin jikinshi rawa yake idanunshi sunyi jajawur, wallahi kinji na rantse zan nada miki dukan tsiya idan kin bude mini bakin naki, me zaki fada mini? Yayi kofa ya juya ya nufi waje" da karfin tsiya ta daga murya yadda zaiji ta tace "Yo kayi auren mana Dan Allah ka auro mata goma idan ka isa marar mutunci kawai azzalumi Kuma ban yafe maka ba Marin da kamini ta fashe da wani kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro" yana jinta yayi banza da ita saboda yana komawa wajenta zai halakata a yadda yake jin zuciyarshi tana kuna shi yasa ya kyaleta ya shiga motarshi ya koma wajen aiki tare da damuwa mai tarin yawa, shi ba wani yan mata yake kulawa ba ballai a Kai ga maganar aure. Saida Heema tayi kukanta mai isarta ta mike ta gyara falon sab ta kunna turaren wuta ta yi ma yaranta wanka, ta shirya su suka zauna a falo tana Basu Madara da biredi wayarta ta dauka taga duk ya tarwatse ta Kara fashewa da wani uban kukan tana yi ma Hafiz Allah ya isa. Hafiz yana zaune a falonshi sai Mahaifinsa ya kirashi a waya yace mishi idan ya tashi daga aiki ya je ya karbo mishi sako wajen abokinshi, haka ko akayi karfe shida ya wuce gidan ya amso sakon a nan ya hadu da Zainab Babu laifi ta hadu yaji ta kwanta mishi a rai ba'a dauki lokaci mai tsayi aka daura musu aure Zainab ta tare a gidanta. Tunda Zainab ta shigo gidan Heema ta canza kadan tana kokartawa wajen gyara falonta ba kamar da ba Amma babu abinda ya canza gameda karance karancenta littafinta kullum nemanta Zainab take ita kuma bata kulata sai hidimar yaranta take, shi ne watarana bayan ta daki yaran da gudu Zainab ta Kira Mahaifiyar Hafiz ta sanar da ita saboda dama ta tsani ganin yaran a gidan hajiya Amina tana zuwa ta tafi da yaran wannan abin ya ma Zainab dadi sosai. Kullum maganar Hafiz yashe zai samu kwanciyar hankali a gidanshi. Wannan kenan.
*Cigaban labarin*
Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un shi ne Abinda Raheema take ta nanatawa sanda take shirin saukowa daga bene,(dan tun bayan futan Hafiz gidan bata sake safkowa ba kasan said ynz dataji zuciyarta tasamu sassauci daga 6acin ran su zainab dasuka cusa mata hour kusan 7 dasuka wuce itada Fatima a hatsaniyarsu,) ynx ma tunawa tai d'ayar wayarta na falon Inda ta tashi mafarin fitowarta knn santsi ya kwasheta saigata ta gangaro kif a kan karamin tayin cikinta, qara ta sake saki duk ta jike da gumi tana ta cizan yatsa, Hafiz ko dayashigo gidan a lkcn dasauri ya qaraso a rude ya riqota sai sannu yake mata bata ma san Yana Yi ba saboda duk ta fice haiyacinta, wani irin murdawa cikinta yayi ta kurma wani uban ihu tayi Baya luuuu ta fada saman Hafiz idanunwanta suka rufe jikinta yayi sanyi.
da karfi tsiya Hafiz ya shiga girgizata yana kiran sunanta mma Ina ko motsi Bata yi ba. dan girman Allah Heema kada ki mutu kibarni sune kalaman da yaketa nanata wa, ita dai Heema gata nan shimfide a tsaikiyar falon numfashin nata ya tsaya cak...
kankacemi saiga zainab da Fatima sun fito jin Qatar heema, waro idanuwa Hafiz yai qirjinsa ba bugawa sakamon jini dayaga yanabin qasan heema yana malalowa yayinda zuciyar zainab kmr ammata albishir dantasan tsinanen cikin ne yake ficewa daga gidan.
tsawa Hafiz ya dokawa fateema dacewa
"Ina amfanin likitancin naki da baziki iya mata wani taimakon gaggawa ba kike nufi komi?"!
Kamin Fatima tayi wani yunquri haba tuni harya sunkuci heema batareda da damuwar jinin sake binsa ba yayi waje da ita hankali tashe yakejin bazaima iya jiran wata fateema ba...
a hargitse ya iso hospital din mahaifinsa...
*By 4 writers fasaha*
[7/12, 8:34 AM] Xainab Documen: .*♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!
*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.
Written by.
*FOUR GORGEOUS WRITERS*
-Raheenat mahmud.
-Mmn Abduljalal.
-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).
-Matan Borno.
*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*
Bismillahirrahmanirraheem.
*Gargad'i*
Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.
18.
Isarsu hospital din keda wuya emargancy aka shiga da hema, a qalla manyan likitoci kusan 5 ne kewaye da ita suna dubata dan yanda jinin nata keta qara cigaba da 6ul6ulowa. Hafiz kuwa banda sintiri babu abinda yakeyi hankalinsa tashe dudda likitoci 'yan mata na hospital din nata neman shisshige masa da rangwada kodan yaje ya wanke jinin dayai fata fata da rigarsa Amman Sam baida wnn nutsuwar
"it's OK tanz"
abinda ke rabasu dashi knn haka suka gaji suka bar wajen gwiyoyi a sace, dan matuqa Hafiz ke matuqar firgitasu da tsantsar kyaun da Allah ya haliccesa dashi kamarshi ya tsarawa kansa shi, babu macen dazatai arba da handsome army man din nan bata firgita da bugun zuciyan soyayayrsa farad daya ba, saidai rashin ganin fuska ne yasasu basu iya bayyana masa soyayarsu a fili saidai a aikace, hakan na daya daga cikin abinda yasa Hafiz bai cika ziyartar asibitin dadyn nasa ba domin dazarar sun qyalla ido sun gansa zasuyita masa zarya aka da tambyar miyakeso akawo masa ne.
dan qaramin tsoki yaja bayan bin bayan doctor hafsa dayai da harara data bar gun musamman da ita tafi takura masa acikinsu, haushinta yaji yaqara mamaye masa zuciya gani dayai mutum na cikin tension suzo su qara masa wani, a qalla Hafiz ya sake share kusan 3 hours snn yasamu ya zuqunna akan qafafunsa idanunsa a lumshe red lips dinsa na motsawa alamun addu'a yake a ciki .
dan har yagaji da trying number dady Amman bata shiga may be ko wani uzurin ne yanasa isowa asibiti a lokacin, dasauri ya miqe ganin doctor blessing mele ta fito daga dakin da aka shiga da heema sauran doctors