Showing 69001 words to 72000 words out of 78322 words

Chapter 24 - MATAN Hafiz Book Complete Document .txt

Unknown   

27 Nov 2024

2523

zuwa daukar khairat dan 'yar kuce babu mai hanawa, amman cewa wani ya dauketa ma bata taso ba inda ga uwarta nan da rai ba mutuwa tai ba, iyaka duk mai son daukarta yazo ya dauketa koma dai kwana zatayi wajensa babu damuwa iyaka in yarinya taji yunwa akawota ga uwarta, dan Allah kudinga sakawa zuciyarku salama kullum fa girma kuke qarayi amman baku gani kudinga lallasar zuqatanku akan abinda kukeso khairat dai tamuce takuce takowa ce, kuma ina muku addu'an Allah baku naku kuma masu albarka Allah shi qara hada kawunanku kuma...
Sosai hjy amina tadinga lallasansu harsaida taga sun sauko snn ta tafi.
to tundaga ranar kuma saiya zamana acikin su biyun in wnn ta dauki khairat yau ta wuni hannunta wnn kuma zata dauketa gobe,
da ta fara wayau ko har shopping suke zuwa da ita wai tazabi abinda take so a nufinsu, ita ko saidai taita musu gwaranci tana bingilewa da dariya, ko Hafiz gani suke baikaisu son yarinyar ba, shima kansa ya jinjina musu kan soyayyar dasukewa khairat saidai fa babu abinda ya sauya naqin uwarta a zuqatansu, kwanci tashi har khairat ta isa yaye aikam zee tai tsalle ta dire da cewar ita zata amshi yayen khairat Fatima kuwa tace ai abinda bai yuyuwa knn kuma wlh tayi tsururu ruwa ma ya fita gudu, wnn karan kam saida Hafiz yai musu jan ido irin basu na sojoji snn suka nutsu dan cewa yai inda yayen wata 2 ne zasuyi ma khairat to su raba 2, wnn tayi wata 1 hannunta wnn tayi wata daya hannunta, to dayake yayen ba dole ne dan basmah gwarnai tai ynz haka wani cikin take dashi na wata 3, shiyasa bata damu ba dan sun dauke mata nauyin khairat dan damn fulako take nunawa kan khairat a matsayinta Na 'yar fari shiyasa bata sakin jiki taiwa khairat din wasu abubuwa, zamu iya cewa basmah ta gado fulakon tane daga amminta dan Ammi da wuya kaga ta zauna suna mgn da Yaya mus'ab inba ta kama ba,


to hakan kuwa akayi kmr ynda Hafiz ya tsara musu renon khairat haka sukayi, gata na gidan duniya babu wacce bata gwadawa khairat cikin su ba dan har haushin su qawayensu suka dingaji Na danmi zasu liqewa diyar kishiya abin banza dudda suma baby khairat tai musu ammn hassada yahanasu nunawa, suko sukance Indai akan khairat ne wlh suma ce musu komi bazasu damu ba,
ahaka har watannin yayen khairat ya qare maimakon su medota ga uwarta gaba daya sai suka koma shifting2 da ita, wato in ta kwana a dakin uwar wanshekare saita kwana dakin zee wanshekare saita kwana dakin heema wan shekare saita kwana dakin Fatima haka sukeyi, har Baby khairat ta fara wayau, a lokacin ne basma ta kuma haihuwan namiji akasa masa mukarram, to saifa lokacin basmah tasan danta yazauna hannunta dan sunfi maida hankali ga khairat su zee har ynz yayinda heema da basmah da Hafiz suke tattalin mukarram su kuma..
akwana atashi har Baby khairat ta isa shiga nursery wayau radam a bakinta gata da kaifin basira yarinyar koda yaushe qara shiga ran jama'a take kowa ya ganta zakaji yanata fadin khairat, saidai har lokacin khairat tarasa tantance wacece taqamaiman mamanta a tsakanin matan baban nata, kowa na bata kulawa iyakar iyawarta basmah mace take danyin baya baya da ita dudda zuciyarta na cike dason yarta ammn kunya ta hanata nunawa,
khairat sai daga bayan tashiga makaranta snn tagane basmah ce ainihin momynta, su sultan nazuwa suyi hutu su koma hajiyan Hafiz kuwa intaso zata zo ta dauketa takaisu wajensu sultana yaran suyita murnar ganin khairat aranar kuwa zee da Fatima a gidan hjyn Hafiz suka wuni suma, sai dare snn Hafiz yazo daukarsu,
haka khairat take rayuwarta cikin sa'a ata ko'ina,
yarinyar mai kokarin addinin islama da boko ce dan itake dauko Na daya a ajinsu, inko kaji tana karatun kur'ani saikayi mamaki aduka shekarunta da basufi 6 ba a duniya,
inta taso boko ake zuwa kaita tahfiz anan cikin islamiyyan anguwar.


kamar yau data dawo makaranta anan falo ta samu zee uwa tana dakon dawowarta kuwa,rungume juna sukai cikin farinciki zee take cewa ''oyoyo Rabin raina, yar dariyarta ta yara khairat tayi gamida rungume zee tana cewa "oyoyo sweet momy na, qagala nadawo gida na ganki, tayi mgnr cikin wayonta, sumbatarta zee tayi tace to gani ay muje daki na miki wanka dan yau na ajiyemi Abu mai dad'i, kamata tai takaita dakinta tayi mata wanka gamida gyara mata gashinta ta tsantsara mata kwalliya tasa mata yan kanti riga da wando da facing cap dinsu snn ta jawota jikinta gamida miqa mata coconut caculate din da tasan tafiso, aiko khairat taita murna ta fita da gudu zee ta biyota tana dariya, sosai takeson ganin ta farantawa khairat a rayuwarta, had'e rai Zee tai ganin Fatima ta shigo gidan ga alama dawowarta knn daga aiki, duqawa Fatima tai bayan cilli da jikkart datai ta bude hannuwanta da gudu khairat ta qaraso ta shige jikinta kuwa suka hau qyalqyata dariya tare, sum6atar goshinta Fatima tai gamida shafa gashin kanta tace "'inye my khairat wayai miki kwalliya haka?, khairat cikin murna ta juyo gamida nuna mata zee dake bayan su tace "sweet Momy ce tamin"
(dayake haka take cewa zee sweet Momy ita kuma Fatima tace mata sugar Momy, ita kuma heema tace mata big Momy yayinda take cewa mamanta basmah Momy kawai.
aiko khairat na fadar hakan nan take fatima ta ya mutse fuska,dan haduwar idanunsu da zee snn ta medo kallonta ga khairat tasakar mata murmurshi snn tace "nasiyo miki biscuit dinki muje daki na baki"
saurin qarasowa wajensu zee tai ta qwace khairat gamida riqeta a jikinta tace


"dakata malama khairat tawa ce yau kokin manta sai gobe zata dawo hannunki?
please kowa yariqe matsayinsa fatan zaki kiyaye" sakin baki Fatima tai snn tace " to knn bnda ikon yin magana da ita knn ma dan taqamar tana wajenki koko?"
ko amsa zee bata bata ba ta duqo tacewa khairat
"oya jeki ki gaida su momynki kiyi maza kidawo ina jiranki" haka khairat ta tsalla da gudu zuwa dakin basmah, sai lokacin zee tadubi Fatima tace "da inada ikon hakan danayi kebari ma kiji gaskiyan batu da da ynda zanyi sai kinvar ma sata idanunki sanda take wajena wlh da nayi"
akufule Fatima tace
"to wlh baki isaba qaramar marar kunya khairat nima tawa ce bake kadai ke iko da ita ba kima san da wnn kiyi maza kidawo hayyacinki inkin fita cikinsa"
tsoki zee tayi snn tace
" kul naqarajin klmr nan daga bakinki ki in ba hakaba wlh saina zubda miki haqoran gaba harkin isa kice khairat takice ke daya Toni uwarwa ta cinyemun matsayina a gunta?"
kan kice mi rigima ta sawo kai a tsakanin har suna shirin dambatawa ganin khairat din ta dawo ne yasa su suka nutsu, dan basuson tasan zamnda sukeyi da junansu har ynz musammn da suka taba yin fada gabnta kwanaki sau 1 har Hafiz kecewa in suna HK a gabn khairat wlh zai dauketa yakaiwa momynsa ta hadasu dasu sultan ta riqe dan bazai yarda 'yar sa ta taso da kalar halayen su ba a kwanyarta, tun tana qaramarta,
ganin khairat din yasa sukayi shiru aka koma kallon banza a tsakani,
zee taga khairat na matse kwallan alamun kuka takeson yi dasauri ta riqota tace "ya akayi ne khairat!!?"
cikin muryan kukan khairat tace ''naje wajen big Momy bata nan ita kuma Momy naje gunta ta koroni tamun tsawa wai kada na tayar mata da mukarram yana bacci"
fuu Fatima tayi dakin basmah zee har zata bita sai kuma tafasa tadauki khairat suka shige dakinta zuciyarta cikeda da takaicin basmah danmi zata ma yarinyar ta tsawa so take ta gigitata mata ita komi,amman ba komi bashi taci wlh .
Fatima ko tana shiga dakin ta samu basmah na aikin taje gashin kanta jikinta sanye da qananun kaya aikam tasa hannu ta dauki mukarram ta girgizasa sama, tuni yaran ya tashi a firgice ya tsanyare da kuka snn ta maidasa ta ajiye tadubi basmah tace "sakamakon abinda kikaiwa khairat knn na rama mata, abinda kina guda har kina korota mana ita da kuka toni shine nazo na haifar"
tana gama fadin haka tafice, murmurshi kawai basmah tayi gamida girgiza kai ta dauki mukarram ta rarrashesa snn yakoma barci, waisu tunaninsu sunfita son yarta knn? Yar dariya kawai tayi gamida furta
"Alright Allah tayaku riqo dai"
dayake heema taje gida a lokacin Hafiz kuwa baya gari sunje Ibadan aiki amman wnn satin zai dawo,
Zee suna can a daki itada khairat tana qara koya mata karatun school..washegari khairat ta dawo hannun Fatima Fatima kam tabawa direbansu umarnin inya dauko khairat yakai mata ita asibiti dan batajin zata iya bararwa zee ita dudda tana gida.
maimakon data taso aikin su wuce gida sai tawuce da ita gidan wasan yara sukaita yawo ciki abinsu bacin kayan maqulashe datai ta siyawa khairat din, sai kusan magrib snn suka dawo.


zee kuwa da suka dawon har yadawa Fatima mgn tai da cewa itafa kada a 6ata mata 'ya da yawon gantali tun ynz,
take Fatima ta mayar mata da amsar cewa
"yawo naci na girma kuma shi zan daurata akai ballagaza kawai dake munafuka aike zancema kada ki koya mata salo salon makircinki kuma Allah ya fiki"
wata ashar zee ta lailayo tace kan ubancan kai dakuwa anyi bara uba a gidan nan, tsoki Fatima tayi tace bura uba ai cikinta kike tuni.
nan ta shige daki tabar zee tana bubutai.
ran da Hafiz zai dawo kuwa gidan ya kacame kowa so take ta hada masa abincin dazai yaba mata, haka suka hada masa tebur dam da kayan ciyeciye,
da yazo yaga wajenko abin baqaramin farinciki ya sashi ba gani yake komi yazo karshe hadewar kawunansu kawai yakeso ynz.
dayake dakin heema ya sauka aranar ko heema ta gurzu sun gurji juna matuqa sai sa tinta gakeyi wai please ta fada masa minenen Sirrin da yaji ta dawo gamgam ynz,
itako cikin kunya ta shige jikinsa tana shafa qirjinsa shima ya rungumeta yana dariya gamida shafa bayanta, saida yai kwana uku snn yasauka dakin Fatima daga nan yadawo dakin zee daga dakin zee kuma sai dakin basmah, shikam gaba daya matsansa babu ta yarwa kowace tana kokarin gyara kanta shikam ynz yasan yana aure Alhamdulilla,
Kamar yau ta kama asabar zai bar dakin basmah sai kukan shagawaba takeyi knr ko yaushe, riqota yai yana bin jikinta da wani hautsinannen kallo mai kashe jiki, wata doguwar top din riga ce a jikinta mai budadden wuya da tabi jikinta ta kwanta,
itama kallonsa takeyi tana turo baki shikam ganin ta yakeyi kamar wata matashiyar budurwa wacce bata taba haihuwa ba domin babu abinda ya canza a jikinta har ynz, fizgota cikin kirjinsa yai ya manneta yafara shinshina qamshinta itama qam qam tai mugun rungumesa tana sauke numfashi,sunjima tsaye a haka snn taji dirar hannuwansa a saman cikakkun kirjinta hannunta takai a jikinsa itama, nan take suka runtse ido a tare suna maida numfashi, dauketa yai tsagwayam ya dire a gado gamida shigewa jikinta Bacin rabata dayai da komi na jikinta, hannuwansa ya d'ora saman dukiyar fulaninta yahau mutsittsikasu yana wasa dasu itako sai miqa takeyi sabida banan kadai ya tsayaba saida yakaita maqura snn yaja musu bargo suka shiga raya sunna sosai babu kama hannun yaro, saida suka gamsu iya gamsuwa snn suka shiga wanka tare, suka maida kayanau ta dauko mukarram ya amshe sa yana masa wasa shiko sai dariya yake bangalawa dadyn nasa , ahaka suka jero suka fito, breakfast, basu samu kowa dinig ba saida suka zauna da mintoci snn suka fara firfitowa, hannun Fatima riqeda khairat dan a wajenta ta kwana, yau zata komo hannun heema,
suna gama beaks fast dayake weakened ne nan suka baje falo dukansu,
khairat na jikin zee sukaji tace
"dady nadawo wajenka na zauna?"
murmurshi Hafiz yai gamida ajiye abinda yakeyi da wayarsa yace
"sosai ma kuwa daughter taho gun abbunki"
nan ya bude mata hannuwan sa cikin murmushi ta taho ta shige jikinsa tana murna tace "dady kasan malamin islamiyan mu yace kamin mu aikata Abu mufara da tambaya akai, snn kuma yace bin umarnin iyaye wajibi ne danson gamawa da duniya lfy kayi rayuwa mai kyau a duniya da lahira, yace bin iyaye abune mai kyau hakane ko dady?" gyadakai Hafiz yai yace "kwarai kuwa hakane daughter na ynz ina kika tsaya karatun kurani a islamiyya?"
riqe baki tai kmr mai tunani snn kuma zuwa can tasaki murmushinta tace
"izu 1 Mike yan ajinmu"
cikin tsokana yace
"ynz inna dauko Qur'anic zaki faramin daga farkon karatunki har zuwa sabbi knn?"
dariya ta qyalqyace dashi tace "ehman dady ai basaima ka dauko qurani ba ana tafiyar mana karatunne da hadda, danzaro ido Hafiz yai yace kayy ashedai yar tawa hafiza ce, duknsu wajen akai dariya snn yace to faro mun daga suratul nasi inji dan kada nayi yabon dan kuturu, zee tai karaf tace
"haba yallabai yar tawa ai gifted ce"
Fatima ta amshe da cewa
"ina mai tabbatar maka cewa yallabai my khairat zata baka mamaki yau ban bantaba jin qarya ta fito daga bakintaba komi tacema ta iyashi ko tayi to hakana ne din"
hada ido Zee da Fatima sukai sanda ta qarashe mgnr sai dai kawai suka sakarwa juna harara a kaikaice,heema tace "qwarai kuwa Fatima maganarki dutse Allah shi rays mana ita dan khairat inta girma Allah kadai yasan ilimin da zata dauko akan nan nata"
tayi mgnr tana shafa kan khairat dayake tana kusa da Hafiz, murmushi Hafiz yai yace
"naji bakinku saura nata dan in har na tabbatar da hkn my daughter kinada kyauta ta musammn kuwa"
dariya khairat ta kumayi tace "jazakallahu bijannatul Firdausi dady,
gani sukai ta nutsu sosai gamida saka yar himar dinta akanta ta lumshe idanunta dan qaramin bakinta yafara motsawa, da bismilla ta fara snn ta fara karatun tun daga nasi cikin yanayin k'iri'an da ake koya musu a makrnta a nutse take rairo karatunta mai shiga jiki bata dureba saida ta kai qarshen sabbi,snn ta bude ido tana kallonsu cikin murmushi. kabbara sukai mata duknsu Sosai Hafiz yayi mamakin kwanyar yarinyar aikam d'agata sama yai ya cafe gamida sake rungumeta ajikinsa yanajin kaunarta sanka sanka na qara ratsa sa,
dagota yai yadubeta cikin fara'a yafara da cewa
"Allah ya albarkaci rayuwarki khairat, naji dadin hkn snn kuma kifadi komi kikeso zan miki kinji my daughter"

'yar dariya tai snn tace ''abinda nakeso dady zan fadama knn?"
Yace "eh khairat"
shiru tai tana tuanani zuwa can tace "babban abinda nakeso a rayuwa ku dukanku anan dady, kaga ina son sonka dady inason sweet momy ina son sugar momy inason big momy da kuma momy na da mukarram dasu sultana dayan gidan hajiyan mecca da kaku mlm , sai abu na biyu malaminmu yace idan yara qananu suka rasu Allah na rayuwantar dasu a cikin makarantar annabi Ibrahim wace tafi kowace makaranta haske ga abubuwan morewa da sukafi na ko ina inason naje makarntar dady na dinga muko addu'a daga can, shin nima inna mutu zan shiga makarantar ko dady?, amman banson na tafi nabarku kuma shiknn bazan qara ganinku ba idan natafi ko dady?, dan mlm yace mana wanda ya mutu baya ta6a dawowa haka ne ko dady?, amman nayi mafarki har na shiga makarntar fa dady munata wasa dawasu yaran larabawa kaima zakazo muje dady saimu dawo tare ko?" ta qarashe mgnr kanta a langabe tana kallon dadyn sai kuma ta juya ga su zee tana maida tambayar garesu suma.
gaba daya tambayar yarinyar ta qarshe ta dokesu gaba daya aka rasa wnda zai amsa mata dan mgnr tata saitai musu kamar ta mai wasiyyar barin duniya,
da zaka saurara zakaji dukan qirjin zee dana Fatima gamida heema a wajen dashi kansa Hafiz din,
ammn basmah ta maida mgnr khairat ta mgnr yara ce kawai musammn abinda yara suke so zakaji suna yawan ambaton sa, sosai ta zubawa 'yar tata ido ita kanta bata taba tsayawa ta qarewa yar tata kallo ba kamanr yau jitai wata sabuwar soyayyar yar tata na nunkuwa azuciyarta, itako khairat tana riqeda mukarram tana masa wasa dantaji iyayen aunyi shiru da tambayar tata shiyasa ta fita batun takamo hannun mukram tana cewa "mukarram zo nai maka wasan doki kuma snn muje na saka a motarka mai jiniyar sojoji irin tasu dady sai muyi ta wasan mu ko"
riqo hannunta Hafiz yai cikin qarfin zuciya ya dawo da ita jikinsa yana murmurshi yana mai goge qwalla daga idonsa wadda shi kansa bai iya cewa gata yanda akayi tazo masa kota micece ba




.
[8/4, 10:10 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




*Gargad'i*


Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.




46.


In confidence ya ce
"my daughter khairat hakane kmr ynda kika fada, amman kisani mutum bai mutuwa inba lokacinsa ne yai ba, akoda yaushe muna fatan in tamu tazo ubangiji Allah ya kyautata karshenmu kije kuyi wasanku da mukarram Allah yayi ma rayuwarku albarka"
haka khairat taja hannun mukarram cikin murna tana cewa "aminn dady,
kasan ina son amin addu'a musammn taku yafimin abani abu mai dadi dan Mlm yace adduan iyaye itace jigon cigaba a rayuwar mutum tana sama da komi ngd abbu na, saikuma ta ce yawwa abbu yaushe zaka kaini wajensu sultan ma?"
murmushi Hafiz yasaki gamida gyara zamansa yace
"yaushe kike so?''
cikin yar dariyarta tace
"ko yaushe kace abbu"
"to kibari nan bada jimawa ba zan kaiki"
aiko cikin murna taja hannun mukarram suka shiga dakin da kayan wasansu yake shima mukarram sai murna yakeyi kmr yasan mi akace.
tana barin wajen duk suka saki ajiyan zuciya zee tafara cewa "amman fa kalaman khairat sun kadamun 'yan hanji dazun gsky dan sai sukai kama da mai shirin barin duniya kunsan mafarkin yara wani lokacin na kasantuwa insuka furta, waiii!! Allah na,dafe kirjinta tai tace wlh har ynz zuciyata batabar dokawa ba nikeji ma" Fatima ta amshe da fadin
"nidai abar jawa 'yata mutuwa ynz batakai ga ma sanin rayuwar ba shi knn yaro baida daman yayi labari sai ana dangantasa da matacce to wlh bata bakin mutum ba insha Allah sai na goya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login