Showing 15001 words to 18000 words out of 78322 words

Chapter 6 - MATAN Hafiz Book Complete Document .txt

Unknown   

27 Nov 2024

2509

shidin ma cikakken mutum ne nutsattse kamili mai son tsananin son addinin sa dan shedar hakanma gata a goshinsa wato d'igon baqin shedar sallayan sa, hakan kuwa baqaramin sake fiddo masa da sihirtaccen kyaunsa ya kumayi ba na usulin larabawa jinin mahaifiyarsa uwa uba gashi matashin saurayi ingarman namijin zaki dan 32,yrs ga masu gida rana kai Allah na gode ma gskia dolema nazo na canza taku nima kodan sake cusa qauna ta a cikin zuciyars...
hure mata idanuwa taji yayi hakanne yasata sauke ajiyar xuciya tareda dubansa.


kanne mata ido 1 yai gamida furta "yadai mom twins kada kiciyeni da kallon nan fa" dariya heema ta qyalqake dashi tasa hannu tana shafa gefen fuskarsa tace
"Yes my man inma na cinye ka nawa ne ay ko my soja?".
sake zuba mata idanu yai yace "yes amman miye haka kike sha my heema a cup?" Yy mgnr idanunsa nabin cup din hannunta da ido yana sake leqawa, murmushi tai tace
"abbun sultana had'in abin shan kwadayin masu cikine ko zaka sha kaima?"
waro idanuwa yai yace


"to aini bnd@ ciki fa, kuma yaza'ay nasha madam inba cikin zaki mun ba nima em?" Yy mgnr yana mata wani kallo mai kashe lakkan jikin wnda ake jifarsa dashi. Murmushi tai tace
"basai masu ciki ba kowa ma zai iya sha ay"
sake kanne mata ido yai yace "to na yarda zansha amman innayi cikin snn OK?"
dariya sosai mgnrsa ta bata tama kasa mgn sbd kunyar mgnrsa.
miqewa tsaye yai yana sakin murmushi bayan duqowa dayai yayi kissing babyn cikinta, dagowa tai tabisa da kallo tana yaba ynda uniform din sojojin yamasa kyau sosai ajikin farar fatar sa uwa yau ta fara ganinsa, yamutsa fuskarsa yayi bayan yaduba agogon diamond din hannunsa, sam baison late, sunkuyowa yai ya bata Peck a lips din ta gamida zuqo kwakwr datasa a bakinta yayi murmushi ya nufi dakin fateema.
yasamu tana wanka bakin toilet din ya qarasa ya mata mgn snn yawuce compound din gidan inda motocinsa suke.
yana fitows waje yaji sautin wayarsa ta dauki Ringing. tabe baki yai dan yasan bai wuce zainab bace, sam baida wani burin sake zama da dud macen dabata dauki iyayensa da Kima ba da daraja ba. saida ya shiga direbnsa wani kurtun soja ya iso gun da sauri ya bude masa motar ya shiga shima ya shiga yaja suka fiita,


sun hau hanya sosai yaji wani kiran ya kuma shigowa a wayar tasa, cikin kufula ya zare Bluetooth din kunnuwan sa daya sa ya na kai dubansa ga wayan da shirin d'agawa ya yarfa mata rashin mutuncin da ya qudur tama zuciyar sa kota shafa masa lfy ammsn saiyaga sa6anin hkn wato sunan surikinsa mlm usman maihaifin zee din ne yaga yake shawagi a kan wayar tasa..




lumshe idanunsa yai gamida sakin wani iriyar huci mai zafi daya furzo daga bakinsa dan idanunsa har sun fara sakin kalar ja....


"Ya salam"
abinda ya furta knn biyo bayan bud'e idanunsa dayai....












*From 4 writer's fasaha*😍
[7/12, 8:33 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




*Gargad'i*


Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.




13.


Sosai yake ganin qimar Mlm usman baban zainab,dan kuwa aminin baban sane sosai kuma tun tashinsa yagansu tareda mahaifinsa a abokai, (dan mahaifin ta shine da kansa ya samu baban sa da mgnr yabawa dansa 'yarsa dan qara danqon zumuncin da ya jima a tsakaninsu, mafarin knn mahaifinsa a lkcn shikuma yakirasa ya masa mgnr, Sam bai iya jayayya da umarnin babansa mafarin knn ya amince dan a lokacin aurensa da heema basui irin jimawar nan ba, dan a lokcn ma ko wata 5 baiba da fara aikin sojan saba wnda yarsnsu 2 lkcn ne, kusan Kansu daya dan wasu cewa masu ma twins,
dan wani lkcn in sukai wani abun like a qwafi sukaima irin na 'yan biyu,
a farko hafiz sam bai damu da zainab ba Amman dayake sarkin wayau da dabara ce ga iyayi da shegen sanabe kissa da kisisina da tattali gamida tsabta ga girki na musamman da bada himma a fagen auratayya tattalin miji batareda nuna gajiyawarta ba sune ya jawo hankakinsa gareta Wanda hkn baqaramin gudummawa yasamrba daga abubuwan da heema ta Gaza masa ita zainab takeyi masa mafarin knn da itama zainab tasamu kulawa daga garesa danshi mutum ne mai son a kulasa da abubuwan daya shafi rayuwarsa nayau da kullum,


mugun halin zainab ya fara fitowa tun sanda taga atashin farko heema Allah ya azurtata da haihuwan kai da kai a gidan Hz, wato yan sultan da sultanan oga hafiz knn yaransa kyawawa, aifanan ta dunga nunawa herman hassada da baqin ciki musamman data ga ta Shari kusan 2 yrs a gidan Hafiz ko 6atan wata bata ta6a yiba, taje kuma ganin likita ba adadi amman sai dai ace babu wata matsala Allah dai kebai kawo mata haihuwar ba, haka ta dawo ta haqura badan taso ba, rashin kulawa da twins da heema batayi sosai Abu kadan zasuyi mata sai duka, akwai sanda ta kama sultan ta bugesa haryaji ciwo saiga hajiyar hafiz, sosai zuciyarta ta sosu danba qaramin so takewa jikokin nan nata ba, aiko nan taita fad'a ta inda tashiga bata nan tk fitaba uwa zata doke heeman, tay mata gargadi akan kada ta qara duknsu in bazata iya riqesu ba ita zata riqe,


wnn mgnr kuwa sam ko cikin kunnen heema bata Shiga ba dan wata rana tana tsaka da karanta wani novel a wayrta wnda ta jima tana nemansa said a qyar wata qawarta ta samo mata shi takuwa share waje ta kwanta tana karantawa cikin tsananin farinciki har dariya tk tana lumshe ido , kawai taji girkin data daura yana wani mugun qauri, danta mnta ma shaf ita tana wani girkin,
ajiye wayartai da gudu taje kitchen ta kashe gas din tana bude tukunyar taga abincin ya kone baqiqirin sai hayaki yake,tsoki tai ta jika tukunyar da ruwa ta komarta falo danufin qarashe karatun ta aranta fadi tak" oho dai kobanza inada sauran 2 hours kamin abbun sultan yadawo kamin llkcn nasan nagama karatun inyaso ko indomie ce na sulala masa (dudda tasan shidin bai dauki indomie abincin dazai ci ya gamsu ba, kuma ranar itakeda girkin.
dan zainab na side dinta abinta banda toshe kunnuwenta da air piece ta kunna waqa a wayarta tana ta dafsar rawa bata komi,)hmnn *matan hafiz* knn hayaqi baka fitowar banza kowace da kalar tata matsalar a garesa.
a lkcn kuwa heema na qarasawa a inda tabar wayarta tasamu sultan da sultana sunata wasan table tennis da ita , dasauri ta qarasa da shirin kwacewa dan gudun kada su fitar mata daga inda ta tsaya a karatun nata, hartana musu tsawa amman kojin tama basuyi ba, tana qarasowa gunsu daidai nan kuwa sultan ya tullowa sultana ita da hannunsa kamin ta amshe saiji kake tushhh !!!
wayar ta fadi qasa ta tarwatse, wani kukan kura tayi zata cimamiyosu suka gudu dakin zee,
dagudu ko ta bisu suka buya bayan xee data cire air piece tana kallon ikon Allah ganin ynda ta kama yaran nata tana duka had'ida musu gware da kawuna tana surfacesu da zagi, tana fadin
"kun qara tabamun waya?"!
suna kuka suna fadin
"a'a momy kiyi shorry shory(kiyi sorry)dan Allah" Amman duknsu kawai takeyi bata saurarensu ma dan idanunta sun rufe da bacin ran abinda sukai mata.
zainab ko zamatai a gefen gadonta gamida daura kafa 1 bisa daya a rants tana furta "Allah sa ki kashesu ma mayyar waya kawai,
da wlh nida kaina zankaiwa BBC Hausa labarin wata takashe yaranta sabida wayarta"
daga qarshe sumewa yaran sukai, aiko zee cikin kukan kissa ta kirawo hajiyan hafiz tana sheda mata qarya da gskia,dan tasan baqaramin so take musu ba dan kuma a batawa heeman tai hakn.
tana kashe wayan ko taita dariya.


heema tafiyarta tai,
tazuri hijab ta fice xuwa kai gyaran waya da adduan Allah sa batai missing komi ba a ciki.
Qarshe da aka duba wayan haka akace saidai tai haquri dan tayi condom ma gabaki 1, tatafo tana kukan takaicin muhimman litattafanta na waya data rasa a wayarta zuciyarta na gaya mata ba shakka sultan da sultana sun kuma yiwa wayar tata qwafi kamr ynda suka tabayi mata a baya data ta6a dunguresu akan sun dau mata wayn Suna angela game tunkn sukai hakama girma.
Aiko da hajiyn hafiz tazo ta kwashi yaran sai asibiti daqyr numfashinsu ya dawo kaitsaye gidanta ta wuce dasu aranar kuma tadawo gidan Takori heema Wanda hafiz a lkcn bai gari.
saida qyar da zufar goshi baban hema yaita bada haquri ga baban hafiz snn ya lallahi hjyn heema ta dawo dakinta Bacon ja mata kunne datai again, tundag lkccn hema ta rage nacewa waya kashi 20 cikin 100, (Niko nace ananan dai)
sai dai qazantarta nanan, kuma tun lkcn ne su sultana suka koma gun hjn da zama gaba 1, saitaso snn suke zuwa gidan nasu.
kuma itama heema tarage matsa musu tana basu kuluwa dud insunzo Hutu wata sabuwr soyayyr yaranta ke sake shigarta kodan basu tare? Shiyass in sukazo Hutu kmr kada su tafi takeji to wnn knn.




kiran da aka kumayi yasake shigowa wayar hafiz dinne yasashi qara sa gyara zamansa yana sakin doguwar ajiyar zuciya, da sallma ya daga wayar daga can shasehn Mlm usman ya amsa sallmar da furta "aminwaalaikslm d'ana ykk da iyalinka fatn suna lfy?". cikin jin nauyi hafiz ya furta Alhamdulillah baba, cikin muryar dattijantaka Mlm usman yace "masha Allah hafiz nace dan Allah in babu takura kazo ina gida inason muyi ngn dakai"
shiru yai yana tunanin lashakka yaji batun sakin zainab kuwa dayayi, sauke ajiyan zuciyanyai snda yaji Mlm usman nasake furta "kanakn layi kuwa hafiz?"


"to baba ynx inakan hanya zanje wajen aikine Amman insha Allah da nadawo tanan zan biyo"


"to, to ,shiknn Hafiz babu damuwa saina jika"
daga haka sukai sallama, dayake hands free wayar take shiyasa zainab taji komi, baban baice mata komi ba yawuce dakinsa (dayake maman zainab bata gidan sun rabu da bbnta sai kakarta wato Maman babanta ta dawo gidn da zama kuma itama taje ganin gida can garinsu bata nan.
Share qwalla zainab tayi ta lafe a jikin bango, aqalla tundataga 4 tayi taketa zuwa leqen kofan gida dan tasan lkcn dawowarsa daga aiki knn lokutta da dama, 5 daura dagudu ta dawo cikin d'aki sanda ta hango motarsa ta shigo layin yai parking motarsa kofar gidan,
a d'aki zee mazurai kawai takeyi dan tasan kuwa dole hafiz yafada ma babnta rashin mutuncin dataiwa mamansa da qanwarsa shiknn taga ta knta, daura hannuwa tai aka gamida furta "na shiga 1000 ni zainab ya zanyi da qaryar danaiwa baba?''
bata qara tsinkewa ba kuwa saida taji mahaifinta naqwala mata Kira dasauri ta miqe ta na tafe cikin mutuwar jiki wata xuciyar nacewa anya kuwa zainab bazakibi shawaran hafsa ba qawarki kishiga layin malaman zauren nan ba 'yan yayi kodan ki kama zuciyar Hafiz tsaf ta dawo gareki ke d'aya ba,????
kiran da babanta ya kumayi matane yasata ida isa gun dasuke da sauri, zaune shida hafiz bisa tabarma , tana ganin Hafiz gabnta ya qara tsinkewa da azababbiyan kaunarsa dan kwana biyun nn dabata gnsaba ganitai yaqara mata wani danyen kyau na tashin hknki, da haiba gamida qwarjini , saitaji kishin fateema yasake ratsata kuma,haka tazauna tana ta satar kallonsa yayin shi hafiz ko sau daya bai ko kalli inda takeba hankalinsa na ga malm usman yana mai furta




" barka da yammaci baba.....














*By 4 writer's fasaha😍*
[7/12, 8:33 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




*Gargad'i*


Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.




14.




"Barka da yammaci baba" abinda Hafiz ya furtawa Mlm usman knn yayinda shi kuma ya amsa cikin fara'ar sa.


sam baba usman bai tuntubi jin farkon batu ba daga bakin Hafiz dan haka cigaba da cewa yai
"shi al'amarin rayuwar duniya da kuke ganinsa baqaramin Abu bane musamman in zama ya had'aka da mutum kuma ace zaman nan na har abada ne to dole fa yau da gobe asamu wasu kura kurai daga juna wnn ya 6atawa wa wnn da Sani ko akasin hkn, dan HK har kullum zakuji anacewa ma'aurata ayita haquri a zamn aure dan samun dace ranar gobe qiyama,
to zakaga wasu na cewa musammn ma sudin sabon aure ne zakaji suna fadin 'to haqurin mi zasuyi da juna bacin Suna qaunar juna to bazasu gane abinda ake mgn ba sai yau da gobe ta gifta,
dan haka a rayuwa no condition is permanent,
dadi bai daurewa haka wahala bata daurewa a rayuwur duniya"


d'an tsagaitawa yai snn yadubi zainsb ya jefeta da tanbayar data sake hautsina mata yen ciki, shiru zainab tai tareda sunkwi da kanta, tsawa mahaifinta ya daka mata tareda maimaita mgnr da fadin "zainab nace ko zaki iya qara maimaitamun mgnr da kikai man anan gameda Hafiz?"!


cikin rawar jiki zainab ta dago bakinta na rawa tace


"kayi haquri Baba wlh nama alqwarin bazaka sake jin ance ga abinda naiba"


" oh kenn dama mgnta ta zama gskiy danace qarya kike a maganganunki kan sakin da Hafiz yy miki ko?"


matse qwalla tay takasa mgn kuma.


gyad'a kai yai gamida juyowa gun Hafiz yace


"kayi haquri d'ana dn Allah ka fad'amin gskian lamarin abinda ya faru kaida zainsb"


batareda bata lkc ba Hafiz ya kwashe dud iriyar wutar da zainab ta jima tana rurawa a gidnsa gamida had'as@ da matars sa kan tana masa sace sace zuwa raina yn uwansa datai har kawo fadan dasu kai da qanwarsa da hukuncin daya zartar kansa Kn yaji zafin maganganun da taiwa hajiyarsa shikuma.


sam kasa mgn Mlm usman yai sai zuwa can yaja numfashi kamin yaita bawa Hafiz haquri gamida wanke zainab da fad'a harda markuka 2 tasha da zazzafan ranqwashi aka, taita kuka abin ya hade mata 2, baban yayi rantsuwa muddin takuma hasala Hafiz ya saketa saidai tanemi dangin mahaifiyarta suci gaba da riqonts a bazawara wlh badai shi ba, sosai kuma yasa tabawa Hafiz haquri qafafu bibbiyu,
babu ynda za'ayi hafiz ya iya ja inja da lattijon arzikin nn aminin babnsa kuma,
dole tasa ya haqura yace babu komi ya maidata,
baban kuma yaroqi Hafiz akan daganan yatabvatr yakai zainsb tabawa hjyr sa haquri, haka Hafiz ya tashi ya fice zuwa motarsa zuciyarsa Bb dadi dn gskia babu ynda ya iya ne da har abada da ya gama zmn aure da zainab sai kuma inaa Allah bai nufa ba,


zee kuwa jiki na rawa ta kwaso akwatin kayanta ta fito tabude motan yafigeta da gudu ya wuce sukahau hanya
batareda ya ko kalle taba.


Ita ko sai satar kallonsa tk ammsn kwarjininsa ya danne mgnr datake kokarin masa. Kofar gidsnsu (main house)
ya tsaida motan yaqi mgn kuma shi bai fita ba, ganin tana niyyar 6ata masa lkc yasa shi juyowa gamida watsa mata mugun kallo a hassale yace


"koko saina sake maimaita mk abinds mahaifin nk yace kixo gidan kiyi dayake kwalwan kifi gareki ko?"


da sauri ta gane nufinsa


"Kayi haquri Dan Allah"
ta furta gamida ficewa daga motar.


ya bita da dogon tsoki gamida dauke Kansa gefe yana fadin
"mad woman kawai.


tayi rashin sa'a babu kowa gidan sai 'yan aiki dan HK ta dawo ta sheda masa hjyn basu nan bayn ta shiga motar, baice nata qala ba yaja motar suka wuce gida aranta quta kawai takeyi dud zatay maganinsu shida uwar tasa sudai shigo hannun ta saisun zama soory wlh.


tay sa'a babu kowa falon dan HK da sauri ta haye saman side dinta gamida sauke ajiyar zuciya dan daman tsoronta samu sauran matan nasa sugnta da akwati sufahimci wani Abu,shima dakinsa yawuce dan qagare yake yajisa yasakarwa kansa shower dan rage zafin da zuciyarsa ke masa,


dudda abincin da fateema amarya ta shirya masa ta killacesa a dakinta bisa carpet tanata tsumayin dawowarsa saidai sanda ya shigo bata saniba tanacen sun qule a cikin bedroom da qawar ta mufeeda cikin d'aki wanda ko minti 5 cikakke batayi da zuwa ba,


Mufeedan tace "to nidai na fada miki ki tashi tsaye wlh inda kinji ance baison haihuwa to kikiyaye zuwa nn gaba inkin kamasa da hannunki saikiyata sambado yara wlh kicike gidan dasu dam ynda zasu gaji arziqin ubansu ynda yake da kudin nan haka ga aiki yanayi ga kasuwanci motors motors kala kala guy din fa yayi kud'i kota Ina baida Case dasu kudi ay sune rayuwar dama, shawarace nake baki qawata wlh ynda kike babbar likitan nan kinsan kuma magunun da zakiyi amfani dashi kina sha, kada ki kuskura ki dauki ciki ynx kizama bora uwa waccen heeman kmr yadda kikaji zainab din tace"


dariya suka kwashe dashi suka taba snn mufeeda tace "shiyasa nk sonki Qawata akwai iya bada Shawara mai kyau, yanda kikace HK za'ayi, ynx kmr nawa kike ganin za'a kaiwa malamin nn yaimana aiki kan Hafiz din ya zamana baida tunanin kowa da soyayr kowace mace a ransa a duniyar nn hatta wann addababbiyar mahaifiyar tasa face ni??"


mufeeda tace "Kada ki damu saidai kin jini bari na wuce komi knn kyaji wayata" fateema tace to shiknn nima hutun dana dauka na amarci ya qare jibi zan koma aiki"


mufeeda tace
" to ay koba komi kinsha amarci doctor temo dubi yadda kike ta qyalli fa, dariya suka kumayi tare tawuce itakuma tahau duba kayan dazata saka Dan bata jima da fitowa wnka ba, nan akabi aka cancada kwalliya a fuska, balaifi doctor fateema itama masha Allah tanada kyaunta, wata farar atamfa tasa dinkin buba doguwar riga, snn takashe d'auri tajawo wayarta danufin kallon lkcn dawowar Hafiz din.
" to miya tsaidasa yau?" Tanbayar dataiwa kanta knn tana dogon nazari,


'daammmm!!!!


wata zuciyarta ta buga bayan cewa Mata datai kodai yana can tareda wata ne? Dasauri ta miqe tana zagaye dakin tana fadin Kay INA bai yuyuwa, dasauri ta nufi window din dakin taleqa motor park, to gadai motoci nan iri2 ciki hadda ta sojoji Amman tarasa tantance da wacce ya fita bare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login