Showing 3001 words to 6000 words out of 78322 words
da kissa, saidai shi tunda ya fahimci inda ta dosa ya taka mata birki.
Babu abinda ke dad'a tunzurata irin ganin kamar Raheema bata da wata matsala a rayuwarta.
Dan wani lokacin ko ita kad'ai take zauna zaka ga fiskartad'auke da murmushi.
Wani lokacin kuma kuma tana rike da waya zata ta sakin murmushi ko ma ta tuntsire da dariya.
Hakan ke sa zainab ta tsargu tayi tunanin ko da maigidan suke chatting.
Shi yasa ita kullum cikin kiranshi da tura mishi sakonni masu dauke da zakakan kalamai take idan ya fita aiki.
Abinda bata sani ba ita Raheema bata da lokacin wannan, lokacinta na karatun novels ne kuma idan ta tuna abinda ta karanta ya burgeta take sakin murmushi ko kuma idan tana karanta guri mai dad'i ko anyi abinda dariya sai tayi ta dariya tamkar da mutum takeyi.
Batun kiran waya kuma dama bata saba ba tun farko ya sabar mata shi yake kiranta yaji lafiyarta idan ya fita ita kuma yanzun da ya rage ma bata damu ba tunda tana da abinda yake d'ebe mata kewa.
Wani lokacin har goranta mata yakeyi ya nuna mata ta rika koyi da Zainab.
Duk da idan ya fad'a mata hakan tana jin zafi amma fa sam bata canza halinnata ba.
Ta gefen dangin miji ma tayi iya shisshiginta amma bata samu matsayin da ya d'ara na Raheemar ba yadda take so.
Don ko ba komai Raheema tana da sakin fiska kuma abin hanunta sam bai rufe mata ido ba.
Bata nuna musu wani hali na daban.
Duk da ba wani girki take yi ba idan sukazo bata yi musu iyaka da kitchen, duk abinda suke so shi suke ci.
Ana haka Raheema ta fara laulayin ciki.
Tun zainab bata gane ba har tazo ta fahimci cewar ciwon Raheema na laulayi ne duba da yadda Hafiz yake rawar k'afa da nuna farin cikinshi a bayyane.
A kullum neman mafita Zainab take ta yadda zata raba tsakaninsu idan a sonta ma ya kore ta a gidan.
Tunanin sake k'ala mata sharrin sata tayi tunda taga yadda ta d'aga hankalinta wancan lokacin kumashima maigidan ya nuna b'acin ranshi duk dai bata san dalilin da ya hana shi d'aukar mataki ba.
Da farko ce mishi tayi sark'a da 'yan kunnenta na Gold sun b'ata.
Ce mata kawai yayi ta bincika da kyau.
Daga nan bai sake bata kofar ci gaba da korafi ba.
Dama kuma ya saba yi mata hakan idan ya fiskanci tana kokarin kawo mishi wani korafin kan Raheema ya ke bagarar da zancen.
A kwana a tashi taga hakan baiyi mata ba ta sake d'aukan kud'in Hafiz ta had'a da 'yan kunne da sarkar gold d'inta taje ta b'oye a d'akin Raheema ba tare da Raheemar ta sani ba.
Tayi ta sa hankali taji ko zaiyi maganar kud'i taji shiru.
Sai ta fara nuna mishi tana bukatar kud'i.
Abin mamaki da takaici a gareta shine ba tare da nuna wata damuwa ba ya bata.
Aka kwana biyu ta sake tambayarshi nan ma ya bata.
Daga nan fa abin ya fara bata tsoro.
Ranan suna zaune a falo suna hira da, Raheema kuma tana kwance kan kujera.
Tashi Zainab tayi tana wani karairaya tana cewa.
"My love na had'a maka drinks na manta ban kawo maka ba."
Da kallo kawai ya bita sai ya maida kallonshi ga Raheema dake kwance idanunta a lumshe yana ayyana wani abu a ranshi.
"Zainab."
Ya kirata.
"Yes love."
Ta amsa tana juyawa tare da farfara idanu.
Daukowa Raheema malt din da na ajiye mata dazu a fridge.
Duk da taji haushi amma sai ta danne tace " Yes your Highness."
Saida ta kawo malt din ta ajiye ta koma kawo mishi nashi drink d'in.
Tana isowa taji yana cewa Raheema da ke kurb'an malt a hankali kamar bata so.
"Heemah kinga ajiyar da nayi a d'akinki?"
Girgiza mishi kai tayi tace "Ban gani ba."
"Idan kin tashi ki duba ta bayan gadon ki akwai wani brief case ki dauka duk abinda ke ciki nakine.
Dum dum, kirjin zainab ya buga,gabanta ya yanke ya fad'i har ta kusa faduwa ya taro ta yana fad'in.
"Hankali mana Zee."
"Sannu." Ya sake ce mata yana kallonta.
Inaa, ai ita bata masan abinda yake cewa ba sai tashin hankalin da yake dad'a mamayeta.
Da kyar ta ta samu ta ajiye tray din hanunta da ta d'ora jug da kofuna.
Niyyarta tazo ta zuba musu tare suna kurb'a suna hira irinta masoya tunda ta lura yanzu kwata kwata Raheemar bata cika son yin magana ba saboda laulayin da ya nik'ata.
Ya maida dubansa ga Raheema yana cewa.
"Ko zamuje in tayaki dubawa?"
Gyad'a mishi kai kawai tayi ya mike ya mika mata hanu ta miko nata ya mikar da ita suka shige sashinta suka bar Zainab cikin mummunan tashin hankali.
Ita dai Raheema da zai barta tayi kwanciyarta ma ya fi mata.
Binshi takeyi kawai ita a yanzu babu abinda ke mata dad'i.
Karance karancenma kaso sittin duk ta rage saboda sai ta d'anji dama dama take yi.
Shi ya bude yana dubawa, ganin harda sark'ar zainab a ciki yasashi gyad'a kai yana dariyar mugunta a zuciyarshi.
"Gashi nan nakine ki sayi duk abinda ranki yakeso, kiyi yadda kikeso dashi."
Shi ya shigar cikin drawer ya saka makulli ya kulle.
Godiya tayi mishi a sanyaye.
Yana kallonta cikin tausayawa yace .
"Ko zaki kwanta ne?"
Mikewa tayi a hankali tana amsawa da "eh."
ta nufi toilet.
*****
Zaune ya samu zainab dirshan kan center carpet na falon ta buga uban tagumi abin duniya ya isheta ta ma rasa ta yadda zata b'ullowa al'amarin.
Abin tambayar shine ?
Yaya akayi hakan ta kasance , ita da batayi tsammanin yasan da zaman jakar a d'akin Raheema ba?
Menene makomar sarkarta?
....
[7/12, 8:33 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!
*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.
Written by.
*FOUR GORGEOUS WRITERS*
-Raheenat mahmud.
-Mmn Abduljalal.
-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).
-Matan Borno.
*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*
Bismillahirrahmanirraheem.
4.
Cikin zullumi ta kwana a ranar ko bacci bata samu tayi ba sai kusan asuba.
Duk da bata da tabbacin ajiyar da tayi ne yake cewa ya bata, hankalinta ba karamin tashi yayi ba saboda daidai gurin da tayi ajiyar ya kwatanta.
Washe gari ta gagara nitsuwa, kuma bata son ya fahimci wani abu daga gareta.
Iya dauriya ta daure tayi breakfast suka karya tare.
Saida taga zai fita aiki snn tace ta yi kudunbala tace.
"Ina da magana."
Ba tare da ya kalleta ba yaci gaba da tafiya yana cewa.
"Sai na dawo."
Binshi tayi kamar yadda ta saba tayi mishi rakiya babu walwala a tare da ita.
******
Tsaye tayi kofar Raheema tana tunanin ta shiga wata zuciyar na hanata.
Shin idan ta shiga tace mata mene?
Yaya zata fara tambayarta kyautar da aka yi mata?
Har ta juya zata tafi ta sake yanke shawarar shiga ko zata ga abinda zai sa ta fahimci wani abu.
Tura kofar tayi bakinta dauke da sallama.
Bata sameta a falo ba ta leka cikin d'akin.
Tana kwance kan tiles daga ita sai towel da alama sanyin wajen take bi dan sai juye juye take yi alaman dai tana son sanyin ya game ko ina na jikinta.
Ta jima tana tsaye tana dube dube daga bisani tayi sand'a ta fita ba tare da Raheema ta san ta shiga dakin ba.
Haka ta wuni a ranar cikin bacin rai da fargaba dan tasan idan har ajiyar da tayi ya kyautar to fa ya cuceta.
Saboda gold din da ta saka a ciki na wanda yayi mata na kayan lefenta ne kuma sau d'aya ta sakashi.
Kuma ta tabbata ba karamin kud'i aka kashe wajen sayanshi ba.
*****
Saida yayi sallar la'asar ya shigo gidan.
D'akin Raheema ya fara zuwa ya dubata saida ya tabattar ta sha malt da cabin biscuit wadanda suka kasance abincinta a yanzu kafin ya fita ya koma nashi d'akin.
Ya samu tuni zainab ta had'a mishi ruwan wanka kamar yadda ta saba.
Saida yayi wanka ya kimtsa snn ya isa dining table ya samu zainab zaune tana jiranshi.
Tasha kwalliya tayi fes da ita sai kamshi ke tashi.
Kallonta yayi suka sakarwa juna murmushi.
"Sannu da aiki my Zee."
Ya fad'a yana gyara zama.
Fad'ada murmushinta tayi tana kashe murya tace.
"Barka dai your highness."
Cikin salo da kwarewa tayi serving dinshi ta dauka da niyyar ta ciyar dashi ya dakatar da ita da cewa.
"Huta abinki Zainab, hakanma Allah yayi albarka."
Gyara zamanta tayi cikin farinciki tana binshi da kallo tace.
"Ameen my love."
A tsanake yake cin abinci tana kallonshi tare da yaba yadda sutura ke karb'ar jikinshi.
Idan ya shiga uniform sai kace dan shi aka hallici uniform din.
Idan manyan kayane nanma tamkar kada ya cire.
Haka ma English wears kamar kada ka daina kallonshi.
Har ya gana tana zaune tana satar kallonshi.
Kamar daga sama ta tsinkayo muryarshi.
"D'azu kikace kina da magana"
Dan kallonshi tayi lokaci guda kuma taji ta diririce ta rasa ta yadda zata fara.
"Ina jinki."
Sake kallonshi tayi taga ya kafe ta da idanuwa hakan yasa ta sauke kanta k'asatana wasa da yatsunta.
A tsorace ta bud'e baki tace.
"My love ina fatar abinda zan fad'a bazai b'ata maka rai ba."
"Go on."
Yace har yanzu idanunshi a kanta.
"A iya zamana da kai nasan kai d'in adali ne, ka saba kuma mun shaida kana kwatanta adalci a tsakanina da Aunty Raheema, amma...
Sai da ta d'anyi shiru na da'an lokaci kafin ta ci gaba da cewa.
"Amma abinda kayi jiya ya bani mamaki...
Jin tayi shiru yasa ya sake cewa.
"Umhum?
"Kyauta naji kayi mata kuma ita kad'ai ba tare da kayi yadda ka saba ba."
"Adalcin kenan nayi Zainab."
Ya bata amsa tamkar dama abinda yake jira kenan.
Kallonshi tayi sosai kana tace.
"Adalci? ina adalci anan?
ita kad'ai kabawa fa.
Ayanzu ko za a samin wuka a wuya bansan kyautar da kayi mata ba.
Fi sabilillahi ka nemi zaman lafiya kenan?.
"Kwantar da hankalinki zainab, kinsan kwanaki kin rokeni kud'i masu yawa har sau biyu kuma na baki.
Gani nayi idan ban bata nata ba ban yi adalci ba duk da bata san lokacin da nake bakin ba, amma ai nasan Allah yana gani.
shi yasa na bata nata yanzu dan kar Allah ya kama ni da laifin danne mata haqqi.
Wani irin bakin ciki ne ya tokare Zainab.
Ai rokan kudin da tayi ita ba dan tana bukatarsu bane, tayi ne dan ya fahimci babu ajiyar da yayi acikin dakinsa.
Daurewa tayi tace "To naji wannan, Kwanaki nayi maka maganar an an sace min sark'a baka ce min komai ba."
"Bani da b'arawo a cikin gidana shi yasa."
ya bata amsa ba tare da wata damuwa ba.
"Baka da b'arawo? Kamar ya?"
"To akwai ne?"
Ya jefa mata tambayar.
"Akwai mana tunda kwanaki anyi maka kaima ka gani."
wata 'yar dariyar rainin hankali ya sakar mata snn ya kalleta cikin ido yace "Idan nayi ratsuwa bazan yi kaffara ba, wacce kike tunanin bata aikata ba saboda haka ki sani babu b'arawo a gidannan, idan har kin nemi abu kin rasa ki binciki kanki watakil hanunki ne ya d'aga."
wani kullutun bakin ciki ya tokareta cikin hasala tace "kana nufin nice b'arauniyar kenan?"
"Kinji na fad'a?"
ya tambayeta.
Murmushin d'ura takaicin da ya ke mata ya dad'a hasalata take ta mike cikin d'aga murya tace.
"Wallahi bazan lamunta ba, bazaiyu ayi min irin wannan asara ba ka shashantar dani ko ni da kaina zan shiga in bincika kayana."
Wani kallo ya watsa mata sannan yace.
"A dakinki ba, daga nan banga inda zaki shiga kiyi bincike ba, dan na tabbata hanun da ya ajiye shi ya d'auka."
Lokaci guda jikinta yayi sanyi k'alau ta fara tunanin ko dai yasan abinda ta aikata ne.
Ganin ya tashi yana tafiya tayi karfin halin shan gabanshi dan wata zuciyarta na karfafa mata gwiwa.
"Nifa gaskiya kasan yadda zakayi da ni, wlh ban shirya asarar sark'ata ba."
Cikin kwanciyar hankali yace.
"Bani na sayeta ba? To na yafe, ko ma waye ya d'auka ya riga ya fita rabon ki sai kiyi hakuri."
Cikin kid'ima ta cafko rigarshi ganin wucewa zaiyi ya barta.
"Wallahi kunyi kad'an ku cutar dani in kyaleku.
Idan ba butulci irinna d'a namiji ba duk wahalan da nakeyi a kanka baka gani?"
Tsayawa yayi yana kallonta da mamaki.
"Ba domin Allah kikeyi ba ?"
Cikin hargagi tace "Ko domin Allah nakeyi ya kamata ka nuna min nafi wacce bata san zafin ka ba, ya kamata kasan cewar nice mai kaunarka da gaskiya, nice kuma wacce tasan mutuncinka.?
Fincikewa yayi zai wuce saboda b'acin ran da yakeji yana mamayeshi.
Cikin azama ta riko kwalar rigarshi.
"Allah ya isa tsakanina daku, Azzalumi, munafuki wadda baisan halacci ba."
wani wawan bangaza da yayi mata saida ta fad'i k'asa.
Ya d'aga kafa zai takata yaji ance.
"Kai Hafizu."
Ko bai ganta ba yasan wannan muryar Ummarshice.
Sosai yaji nauyin halin da suka samesu a ciki, ita kuwa bata tsaya b'ata lokaci ba ta nufi kofar Raheema kanwarshi ta mara mata baya tana mamakin abinda ta gani, dama ita Raheemar sukazo dubawa da jiki suka tadda su haka.
Ita zainab ganin umma yasata narkewa tana k'ara k'arfin kukanta tare da fatar Umma ta tambayeta dalili.
Wani kallo ya watsa mata mai cike da gargad'i ya bi bayan su Umma.
A can ya isketa suka gaisa yana tsoron ta tambayeshi dalilin fadansu saidai ita ko da wasa bata yi niyyar tambayar ba.
Basu wani dad'e ba suka fita daga gidan ba tare da sun gaisa da Zainab ba, dan ita zainab ba karamin haushin shariyan da umman ta nuna taji ba.
Har suka koma gida umma bata yi magana ba sai juya al'amarin takeyi a ranta....
****
Zainab kwance kan gadonta da waya a kunne tana bawa kawarta labarin yadda reshe ya kusa juyewa da rijiya.
Wani irin wawan tsaki kawar tata ta ja bayan ta gama saurarenta tace.
"Amma zainab kin bani mamaki.
Duk dabaran ki da iya kissanki ban zaci zaki yi irin wannan shirme ba.
Idan ya nuna yak'i ganewa ai sai kema kiyi shiru ki kyaleshi kiyi tamkar ma baki san da zancen kudinshi ba.
Sannan maganar sark'a idan kinga dama ai cikin kissa zaki sa shi ya biyaki wadda yafi wannan ma ba tare da wani tashin hankali ba.
ai wannan sai kisa ya ganoki ma ai.... mtseew."
Ta karishe maganar tana kuma jan tsaki.
Shiru tayi tana sauraren kawar tata, kuma ta yarda gaskiya ta fad'a mata.
Amma ai ta kasa daurewa neapolitan, kudad'en ba kad'an bane ga kuma k'arin sark'a, buk'ata kuma bata biya ba, ai dole taji ba dad'i.
"Yanzu yaya kuke ciki da Sojan naki."
Ta jiyo kawar tata tana tambayarta.
"Wlh Azeena tun shekaran jiya da wannan abu ya faru bai sake cin abinci na ba, nayi rokon, nayi magiyan, nayi rarrashin ko kallona bayayi, bayan gaisuwa babu abinda ke shiga tsakaninmu, yaya zanyine Azeena?"
"Hakuri zakiyi ki cigaba da binshi har ya sauko, komai zai daidaita in sha Allah.....
[7/12, 8:33 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!
*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.
Written by.
*FOUR GORGEOUS WRITERS*
-Raheenat mahmud.
-Mmn Abduljalal.
-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).
-Matan Borno.
*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*
Bismillahirrahmanirraheem.
6.
Cikin kad'uwa ya d'ago yana duban ummantasa saboda yadda maganarta ta dakeshi.
Wai dama shirun da tayi ba kyaleshi tayi ba tana nan tana shiri akanshi.
Shin me yasa shi kad'ai ta sawa iyalanshi ido bayan ga yayyunshi bata tab'a umartan wani da ya k'ara aure ba?
Ganin yadda yayi zugum tamkar bai fahimceta ba ya sata fad'in.
"Wai Hafiz ba dakai nake ba?
Nace kaje gidan ummanku Ruqayya kawata ku fahimci juna da 'yar wajenta Fatima.
Kuma bana son wasa, Umarni nake baka ba neman shawara ba.
Sannan kuma ka samu abbanku da batun suje su nema maka aurenta.
Ta wajenmu mukam mun gama magana kai muke jira.
Kada kuma abin ya d'auki lokaci.
Sai a lokacin ya magantu.
Yace "Amma umma da an d'an hakura har Raheema ta haihu kafin ayi maganar auren."
"A'a Hafizu, ba za ayi haka ba, bazamu tsaya wani b'ata lokaci ba, inace yanzu ka gama ce min anyi maka transfer zaka je kaga waje ka zo ka tafi da d'ayarsu?
Cikin kwanannan za ayi bikin idan yaso sai ka tafi da Fatimar.
Yanzu dai zaka bada kud'i zan bawa 'yan uwanka suyi duk abinda ya dace.
Nidai kaje wajenta ku gana kafin ka tafi idan yaso ko baka nan za a yi bikin.
"To umma."
Kawai ya iya ce mata ya sallameta ya bar gidan.
Cikin rashin walwala da kwarin jiki ya koma gida.
Duk yadda yaso ya b'oye saida suka fahimta.
Amma sai ya ce musu maganar transfer din da akayi mishi ne yake damunshi domin bayaso yayi nisa da iyalansa.
Zainab ce ta dage da kwantar mishi da hankali kan yayi fatar hakan ya zamo mishi alkhairi.
Kuma ma ai zai iya tafiya da iyalannashi idan yaso.
Hmm kawai ya iya cewa dan ya fahimci ita rawar kan da takeyi a lissafinta zai tafi da itane tunda Heemah ciki gareta.
****
Kamar yadda ummarshi ta umarceshi washe gari da yamma daga wajen aiki da Uniform ya zarce gidansu Fatima.
Da yake ta riga da tasan da maganar kuma tayi na'am da zab'in farin cikin ta ya gaza b'oyuwa.
Tarba na musamman ya samu daga mutanen gidan.
Kwalliyar da fatima ta yi tamkar zata je wurin gasar sarauniyar kyau sai baza kamshi take.
Saidai duk yadda taso gwada mishi matsayinshi a zuciyarta kasawa tayi lokacin da tayi kicib'is da kyakkyawar fiskarshi ma'abocin kwarjini da cikar kamala.
A nutse ta gaisheshi daga nan ta koma nesa da shi ta d'an d'osana tare da dukar da kanta tana wasa da yatsun hanunta.
Badon kada tayi karya ba zatace bata tab'a ganin mutumin da khakin soja yayiwa kyau kamarshi ba.
Ko sau d'aya bai kalleta ba sai ma waje guda da ya kurawa idanu yana jin wani iri a zuciyarshi.
Idan ba don biyayyayar da yakeso yayi wa mahaifiyarshi ba mai zai sake kawo shi wajen wata mace kuma ma wai aurenta zaiyi?
Su biyu da ya ajiye a gida ma yaya ya k'are dasu kowacce da kalar damuwarta.
Can dai ya d'ago ya d'an dubeta yace.
"Well,Umma ce tace nazo mu fahimci juna da Fatima, duk da dai bansan wani irin fahimtar juna bane na dai bi umarni, ko ba haka ba?"
Mikewa yayi ya zura hanu cikin aljihu ya zaro kud'i 'yan dubu dubu ya ajiye kan kujeran da ke kusa dashi.
"Ni zan wuce, ina fatar kina da labarin cewar ina da mata biyu har da yara?"
ya fad'a cikin halin ko in kula sannan ya juya ya fita.
Ji tayi tamkar anyi zipping bakinta , kwakkwaran motsi ta kasayi.
Yau ita namiji ke wulakantawa haka?
Tayi tunanin sanar da mahaifiyarta amma wata zcyr ta kwab'e kan in har ta fad'a ba mamaki a fasa auren tunda ya nuna baya so.
Wayarta ta d'aga a take ta kira kawarta ta labarta mata komai.
Bud'an bakin k'awar tace "Kutumelesiii. Lallai ya nuna miki tabbacin zaki zama bora a gidanshi kenan dan babu alamun so cikin kalamanshi."
"Ciikin rawar murya take tambayar kawar tata yaya zatayi dan ita fa sonshi takeyi da gaske.
Kwantar mata da hankali kawar tata tayi da cewar zata zo ta sameta su nemi mafita.
****
Bai tafi ba saboda akwai abubawan dabai gama had'awa ba .
Batun maganar aurenshi kuma ya basu kudi suyi duk abin