Showing 9001 words to 12000 words out of 78322 words
ta shiga hada kayanta sauri sauri saboda mugun shakar Hafiz take saboda kwarjini yake mata gashi Allah ya jarabceta da mugun kaunarshi a zuciyarta bayan ta gama ta shiga wanka ta na fitowa ta saka bakar abaya babu laifi Fateema kyakyawa ce ita ma.
Su Hafiz kuma bayan komai ya lafa suka shiga wanka suna fitowa yayi saurin maida kayanshi saboda jirgin karfe tara zasu shiga yanzu kuma takwas da minti ashirin, sai kiransa ake a waya du wannan saurin da yake hannunsa daya na cikin rigar Raheema ya na shafa bbynsa ita kuma sai shagwaba take masa hannunta ya rike ya bata kudi ya ce ta rike wannan kafin Allah ya dawo dashi ya mata kiss a goshi ya bar dakin ta Na mishi Addu'ar dawowa lfy da kuma godiya, wannan halin na Heema shi yake kara mishi kaunarta a zuciyarsa duk abinda zai bata sai ta yi godiya. Ya na shiga dakin Zainab ya ajiye mata kudi ita ma ko tsayawa bai yi ba har zai wuce dakin Fateema ya ga rashin dacewar Haka saboda ko babu komai a matsayin matarshi take dole ne ya bata kulawa ita ma kuma gashi tare za su yi tafiyar, a hankali ya tura kofar dakinta da sauri ta daga idanunwanta ta zuba mishi wani irin kwarjini yayi mata kawar da fuskarta ta yi ta na gaisheshi, amsawa yayi a dakile ba dan kada Mahaifiyasa ta yi fushi dan me zai yi tafiya da matar da baya so? Juyawa yayi ya bar dakin.
Takaici bakinciki sune suka saukar ma Fateema a lokaci guda kome ta tuna oho na ga dai ta na murmushi abubuwa da yawa ta ke ayanawa a ranta tunani take yadda za ta zabga rashin mutunci idan Hafiz ya shigo hannunta. Da sauri ta Mike ta ja akwatinta ta bi bayan shi har ya shiga motar yana jiranta sai cika yake Yana batsewa, da kanta ta saka a kwatin bayan but ta bude baya za ta shiga kallan da ya watsa mata ta yi saurin bude gidan gaba ta shiga, da mugun karfi ya ja motar Kadan ya rage yayi gaba da maigadin gidan shi ya ruga dakinshi a guje har Yana tuntube, Mussa mai gadi ya ce, "Kai wannan Amaryar dai bata shigo gidan a sa'a, tunda aka yi auren nan ya daina ganin dariyar maigidanshi Allah dai ya kyauta".
Ya rufe gidan ya zauna bisa dadumar shi ya na karanta littafin Hisnun musulm.
Hafiz suna isa filin jirgi ba su dauki wani lokaci ba aka fara Kiran sunayen matafiya abokansa sai tsiya suke mishi yayi banza da su, Sun gaishe da Fateema suna janta da hira irin na abokan miji, shi dai Hafiz shiru yayi musu ya na tunanin Matansa da yadda za su tafiyar masa da gidansa kafin ya dawo kowacce da tata matsalar da ya tuna da halin da suka kasance shi da Heema yayi murmushi da Haka aka Kira sunanshi saboda ita Fateema ta shiga tuni har ta zauna mazauninta ba'a jima ba sai ga Hafiz ya shiga ya zauna kusa da ita har yanzu fuskar tashi a hade take jirgin na su ya daga...
[7/12, 8:33 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!
*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.
Written by.
*FOUR GORGEOUS WRITERS*
-Raheenat mahmud.
-Mmn Abduljalal.
-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).
-Matan Borno.
*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*
Bismillahirrahmanirraheem.
7.
"Ke kad'ai ce mace a gidannan ne? Ko a kanki aka fara kishiya?
Ita Heemah bata da raine da tayi hakuri ta danne abinda take ji sai ke zaki d'agawa mutane hankali.
Da ba a yi ke za a kawo ki?
Ko kin manta kema zuwa kikayi kika samu wata?"
Cikin hasala ta d'aga mishi hanu.
"Ni ba wata ba ce, ni Zainab ce kaga kamar yadda suna suka bambanta haka ma halayya.
Ni ba irin lusaran matannan bane da basu san muhimmancin mazajensu ba.
Ina son mijina kuma ina qaunarshi dole in nuna kishina kan abinda nakeso.
Ko ka tab'a ganin anyi kishi kan abinda ba a so?"
Abinka da shaid'an da a ko da yaushe bibiyar al'umma yakeyi yaga tab'arb'arewarsu.
Take zcyr Hafiz ta fara ayyana mishi cewar yanzu Raheema ta daina sonshi shi yasa bata kishinsa.
Wani irin b'acin raine ya ziyarceshi ba shiri ya daka mata wata uwar tsawar da saida ta razana yana cewa.
"Get out of my room idiot."
Gaba dayansu haushinsu yakeji.
Da gudu zainab ta bar dakin dan ba karamin tsorata tayi ba.
Dakinta ta shige ta fada kan gado tana rabza kukan bakin ciki.
Ko ta kansu bai bi ba washe gari ya fara shirin tafiya.
Su ma d'in babu wacce tu kulashi a cikin su.
Abinci ma a ranar a gidan su yaje yaci ya kuma samu ya zauna da yaran shi sosai suke rage mishi b'acin ran da yakeji.
Sallamar tafiyar ma dukansu sama sama yayi musu ya ajiye musu kud'i yayi gaba.
*****
Fatima kam bata yarda mahaifiyarta ko cikin 'yan uwanta sun gane cewar tana da wata matsala ba.
Saboda kawarta ta zo sunyi shawara kuma ta kawo mata mafita da take gani shi zai ficce ta .
***
Duk da ango bayanan shirye shiryen biki akeyi ba kama hanun yaro daga gidansu ango da amarya.
Su kam Matan Hafiz basu san wainar da ake toyawa ba saboda basu sake ji daga gareshi ba.
Bai cika kiransu kamar da ba idan baya gida.
Saidai su su kirashi.
Wani lokacin kuma zainab ce take dagewa tayi ta wayar karya tana zuba shagwab'a idan taga Raheema kusa da ita.
Tun abin na damun Raheemah har ta fahimci iya shege ne kawai ranar tayi mata mai kankat.
Suna zaune ta dauki waya ta fara zuba kalaman soyayya a zuwan a na fada mata ne tana mayar da martani.
Kallonta Raheema tayi lokacin da ta katse tana murmusawa tace.
"Wannan shi ake kira isar da ba a isa ba.
Ni fa idan ban manta ba kin sha cewar kinfi karfin ayi miki kishiya, ni dinma kinfi karfin zama dani.
Sai kuma gashi nima na gagareki har kuma shirin karo miki wata akeyi."
Kokarin kore kunyarta da hauka ta fara inda ta tuntsire da dariya tare da fad'in.
"Dadin abindai dukanmu biyu zaa yi wa kishiyar."
"A yanzu dai zan iya cewa kishiya taki ce tunda nidai an riga da anyi min, kuma an dai karya alkadarinki , cika baki ya riga da ya kare sai kuma a ci gaba da karyar soyayyar waya da miji."
Raheemah na gama fad'in haka ta wuce zuciyarta k'al ko ba komai ta d'an rage rad'ad'in da takeji a zuciyarta.
Tun daga ranar zainab tayi sanyi qlau a gidan.
*****
Tunda aka fara hidimar bikin ake zuba idon ganin ango amma har akaci aka sud'e babu alamunshi.
Biki kam ya kayatar dan dangin ango sunyi rawar gani sun nuna bajinta.
Uwar gidaye kuma sunyi iyakar kokarinsu dukansu biyu ba a samu wani tangard'a ta b'angarensu ba kasancewar suna tare da 'yan uwansu masu basu shawarwari nagari.
Wa'azi da nasiha kuma sun sha su kamar ba gobe.
An watse biki lafiya inda aka bar amarya da uwargidayenta saidai babu ango.
Kamar yadda uwargidayen suke kokarin rike girmansu haka ita ma amaryar take nata kokarin wajen ganin ta basu girmarsu.
Ko wace wayewar gari sai tazo ta gaishesu da dad'daya , hakama takan fito idan taji d'ayarsu a babban falo ko a kitchen a kokarinta nason karantar yadda rayuwar gidan ke tafiya.
****
Kamar yadda ta saba zuwa gaishesu kowace wayewar gari hakama yau ta fara da d'akin Raheema kamar yadda ta saba.
Daga can ta wuce d'akin zainab.
Zainab dake dakon isowarta tayi saurin kara wayarta a kunne kafin ta yi sallama ta fara cewa.
"K'awata ai ina fad'a miki babu wata maganar kishi tsakanina da matannan.
abinda kema kinsan ni d'in ta dabance.
Itama fa amaryar kwana biyu zaki ji ana maganar ciki gareta abinda kinsan maigidan kuma baya so.
Daga haihuwa kuma yaya kike tsammani zata zama?
Kinga zata koma tamkar ita uwargidan komai a sassake, itama cikin k'ank'anin lokaci a juya mata baya kamar dai waccar."
Saida ta d'anyi shiru na d'an lokaci snn ta d'an dara tare da cewa.
"Balle kuma kinsan ita kam ba wani sonta yakeyi ba, mahaifiyarshi ce ta tilasta shi ya aureta.
Kinga ko lekowa yayi ne?
inda zaki tabbatar da bata da fada a gurinshi kenan ai."
fashewa tayi da dariya snn ta kara da cewa.
"Zata shigo gaisuwa yanzu Baiwar Allah, ni har tausayi ma take bani.
Zamuyi magana anjima bye."
Komawa baya Fatima tayi tana jin kirjinta na bugawa.
Lallai fa gwara da ta shigo yanzu ta ji wannan babban sirri.
Ashe shi yasa zainab take shanawarta kullum kaji tana waya da miji tana baza kalamai.
Saida ta daidaita nitsuwarta kafin tayi sallama ta shiga.
Gaisawa sukayi a mutunce kamar yadda suka saba har tana cewa Fatima mai gidan ya ce a gaishesu.
****
Saida akayi sati guda da biki sannan Hafiz ya samu zuwa.
Rashin nuna marmarin shi kan amaryar ya tabbatarwa da dukkansu cewar da gaske dai ba sonta ya ke ba.
Ya dai had'asu yayi musu nasiha.
Daga nan bai sake kula amaryar tashi.
Ko da ya je gidansu ma saida umma tayi ta ja mishi kunne kan amaryar tashi tare da jadadda mishi cewar lallai da ita zai koma.
Ranar farko Raheema ce dashi, ta tanadeshi yadda ya dace.
Sai washegari zainab itama an shana sai rawar kai takeyi da fi'ili.
A rana ta uku yayi niyyar tafiya tare da amarya.
Tun dare zainab ta fara mishi complain na ciwon kai, washegari ta kwanta riris zazzab'i takeji.
sai surutai takeyi ita tasan kewarshi zai kasheta.
Kuka takeyi rurus da nuna mishi irin kewarshi da zatayi.
Ita tayi hakanne ko zai tausaya mata ya fasa tafiya da amarya ya tafi da ita.
Abinda bata sani ba hakan da tayi ya sa mishi tunani ne kan Raheemah.
Ya riga ya tabbata Raheemah bata damu dashi ba tunda ko da ya shiga gurinta bayan ya dawo masallaci har fatan zaman lafiya tayi mishi da fatima.
Gashi ko nuna damuwarta kan tafiyar batayi ba.
D'akin Raheemar ya koma ya sameta zaune ta d'ora kafa d'aya kan d'aya , hanunta rike da waya.
Yana da tabbacin karatun nata na jaraba takeyi da sassafe.
Ita bata da wani damuwa sai karatu kawai.
Kwace wayar yayi yai jifa da ita yana huci.
"Daddyn sultan lafiya?"
ta fada a tsorace.
"Raheemah wai wani irin mutuwar zuciya gareki ne?"
ya tambaya da kakkausar murya.
"Me kuma nayi?"
ta tambaya hawaye na taruwa a idonta saboda kalmar mutuwar zuciyar ya mata zafi.
"Ke wace irin mace ce da bata san muhimmancin mijinta a gareta ba.
Duba fa yanzu tafiya zanyi, baki san ranar da zan dawo ba, baki da masaniyar zamu sake had'uwa ko kuma rabuwar kenan har abada ,amma baki damu da wannan ba,!
Damuwar ki kawai karanta labaran banza, kima dauki na amfanin cikinsu kinqi to ina amfanin karanta abinda bazasu amfaneki ba duniya da lahira...???"!!!!
[7/12, 8:33 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!
*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.
Written by.
*FOUR GORGEOUS WRITERS*
-Raheenat mahmud.
-Mmn Abduljalal.
-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).
-Matan Borno.
*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*
Bismillahirrahmanirraheem.
*Gargad'i*
Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.
9.
Haka dai rayuwa ya cigaba da tafiya a gidan Hafiz, yau dadi gobe akasin Haka tun bayan tafiyarshi da Fateema. Zainab ta karo wani iskanci sai ta yi zaune a falo ta yi ta zage zage, Raheema bata biye mata saboda ita ta kanta take jikin Nata ya kara nauyi sosai watanin cikinta takwas, zaune take a dakinta abin duniya duk ya bi ya isheta zafi ake a garin ba na Wasa ba, ta kunna fanka duk a banza tunawa tayi da rayuwarsu na baya ita da Hafiz a lokacin da bai auro Zainab ba, Yana bata kulawa yana nan nan da ita kamar kwai amma gashi yanzu duk ya rage. tun da suka yi tafiyar nan yana kiranta a Kai a Kai watansu uku a can bata taba fada mishi abubuwan da Zainab take mata a gidan, ta fi so ya zo ya gani da idonshi falo take zama ta rike rimot a hannunta ta ce,
"babu shegiyar da ta isa ta kalli wani wajen".
to dama ita kallo bai dameta ba a tambayeta dai karance karancen littafi na Hausa su ma yanzu ta rage kadan ba kamar da ba.
"Assalamu alaikum, wai ko babu kowa a gidan ne?"
Wata kyakkyawar matashiyar budurwa ce mai kama da Hafiz sak ba za ta wuce shekaru 25 year ba doguwa ce marar jiki hannunta rike da wata yarinya yar shekara hudu, Zainab ta na zaune a falo ta yi banza da ita, shegowa matar ta yi ta rike baki ta na kare ma Zainab kallo ta ce,
"Amma dai Zainab wuyanki ya isa yanka, dan tsabar jakanci irin naki na shigo gidan dan uwana na yi sallama ba za ki amsa mini ba? Ai ko dan saboda ladar kin amsa ko?.."
Hannu Zainab ta daga mata ta ce,
"Ba zan amsa d'in ba, na ce ba zan amsa ba da kike maganar wuyana ya isa yanka sai yanzu kika sani? Sai ki yankata ki kaima waccen munafukar uwar tak..."
Marin da Mufeeda ta zabga mata shi ne yayi sanadiyar hadewar sauran maganartata nan da nan fada ya kaure sakaninsu, har Mufeeda tayi nasarar kadata ta na ta dukanta ta ko ina, bby Ayman sai kuka take. Ihun Zainab da zagin da take shi ne ya falkar da Raheema daga barci a hankali ta sauko daga gadon ta nufi falon turus ta yi ta na kallon ikon Allah idan ta ce ta rabasu ciwo za su ji mata shi ya sa ta nufi hanyar waje cikin tashin hankali domin duk Sun jima juna ciwuka a jiki musamman Zainab da take kasa Mufeeda na ruwan cikinta,
"Mai gadi! mai gadi! Mai gadi!! "
Heema sai kwala masa Kira take ya fito a gigice Yana tambayarta lafiya, ta kasa magana sai nuna masa kofar falon su take da hannunta da gudu ya shiga falon yayi kansu gadan gadan da kyar ya rabasu numfashin Zainab na kokarin daukewa.
Rigar Mufeeda ya yage har ana ganin gefan nonuwanta kawar da fuskarsa maigadin yayi ya shiga tambayarsu abinda ya hadasu.
Mufeeda ta ce
"da ka kyaleni na halakata shegiya yar iska har kin isa ki zagi uwarmu ko kina tunanin duk wani iskancin da kike tantawa bamu San da shiba??!, bayaga zagin da kike wa hajiyarmu yana dawowa kunnuwanmu to wlh iskanci ya ishemu nice dai dai kowace shegiya a gidan nan dan haka zamu cigaba da kwasar 'yan kallo nidake muddin baki canza ba kika dawo hankalinki to nima bazan canza ba banza ballagaza juya kawai sai dai aci kawai a cika ma yaya na gida da qattan kashi ba ribar aure,
banda kaddara ma me yaya Hafiz zai yi dake? Yau shekara hud'u da aurenku har yanzu baki taba koda 6ari ba garama waccen kazamar Raheematu ita ta haihu"
aiko cikin tsananin takaicin rashin kunyar mufeeda garesu uwa ba matan yayan ta ba zainab ta rarimi kwalbar lemun data gama sha a gefan ta ta shammaci Mufeeda ta buga mata ita a ka, jikake fasssss!!!!!
nan da nan jini ya wankewa mufeeda fuska gamida jiri daya kwasheta ta zube a kasa a sume jini na ta cigaba da zuba...
" Innalillahi wa inna ilaihin raji'un aifa
shi kenan, shi kenan shi ne kawai"!!!!
abinda mai gadin yake ta fada, da sauri heema ta yi kan Mufeeda ta na girgiza ta amma ina ko motsi bata yi...
*😍By 4 writer's Fasaha*
[7/12, 8:33 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!
*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.
Written by.
*FOUR GORGEOUS WRITERS*
-Raheenat mahmud.
-Mmn Abduljalal.
-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).
-Matan Borno.
*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*
Bismillahirrahmanirraheem.
*Gargad'i*
Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.
10.
Mikewa Heema ta yi da sauri ta nufi dakinta wayarta ta dauka tana neman layin Hajiyar su Hafiz, Yana kara amma ba'a daga ba a na ukun aka daga tare da yin sallama, magana ta shiga yi cikin sarkewar harshe ai hajiyar bata tsaya jin karshen maganar ba ta yi hanyar waje tana kiren direbanta cike da tashin hankali sai addu'a take Allah ya sa ba mutuwa Mufeeda ta yi ba, kullum fada take mata a kan ta rabu da matan Hafiz ta barta da su ita za ta yi maganinsu amma yarinyar nan taki sai shegen taurin kan tsiya.
Suna zuwa gidan ko parking direban bai dai-dai ta ba ta bude motar ta nufin falon gadan gadan, "Innalillahi wa inna ilaihin raji'un"!.
shi ne abinda ta furta saboda hango Mufeeda ta yi a sakiyar falon jini Nata Malala, magana take so tayi amma ta kasa ilahirin jikinta Bari yake, direbanta da maigadin gidan Hafiz ne suka saka Mufeeda a mota bby Aymana sai kuka take ta na Mmy Mmy, daukarta hajiyar tayi ta shiga baya tare da Mufeeda, heema kuma ta shiga gaba da gudu dreban yaja motar Hajiyar tana ce masa yayi saurin kada jinin Nata ya kare, ikon Allah ne kawai ya kaisu asibitin mlm Aminu kano,
dama Hajiya ta Kira mijinta wato dadyn Hafiz ta sanar dashi komai dan babban likita ne a asibitin, dan haka jiran isowar su kawai yake, suna zuwa lokitoci suka kawo gadon daukar marasa lafiya aka wuce da ita emergency domin bata taimakon gaggawa.
Bari mu koma wajen Hafiz a Cameron muga me yake wakana wajen na su.
Yanzu Hafiz ya daina takura ma Fateema kamar da saboda ya sameta a cikakiyar mace ba lafi sai dai Heema ta fi ta iya dadin mu'amala kullum idan zai kusanci Heema tamkar zuma yake jinta saboda wajen Nata a tsuke yake ba zaka ce ta haifi yara har biyu na ukun Yana hanya ba, ita kuma Fateema ya jita wani irin shi yasa bai fiye zuwa gareta tunda suka zo so hudu kawai ya nemeta a cikin wata uku wai hakan ma yayi kokari saboda bakar wahala yake sha da zafi ita ma sai tayi ta kuka ga saurin gajiya, abinda Heema bata taba yi mashi ba sai dai shi ya tausaya mata ya kyaleta.
(Mata a kula a dage wajen gyran jiki da cin ababen kara ni'ima, ruwan zafi kadai idan mace ta rikesa wallahi an wuce wajen saboda zai taimaka miki sosai, Yana hanaki kamuwa da wasu cututtuka marar kan gado irin su infections da warin gaba kuma zai matseki sosai yar uwa kiyi tsarki da ruwan zafi ki shiga daki ki shafa miski hmmm , kuma ki samu kankana da ayaba da dabino da aya ki markada su ki tace ruwan ki zuba Zuma Kadan kisha za ki ba wasu labari, ko kuma ki samu kwai guda daya ki fasa acikin dan roba ki zuba