Showing 18001 words to 21000 words out of 78322 words
tai tunanin koya dawon bata sani ba.
Heema CE baje cikin dakinta komi ya hargitse a cikinsa can undie can bra can pant can kayan daud'a komai dai barkace , Amman Sam takasa kimtsawa Dn rabon dakin yaga gyra tun zuwan yan gidansu, tsoki tai matsalr Hafiz yaqi ajiyemusu mai share sharen dakuna iyaka saidai mai share falo dasauran wuraren gidan. dancewa yai daki Sirrin maishi ne kowata gyara nata, samutai tamiqe daqyar tadan tsince kayan daudan takaisu cikin matching ta tsubesu, Amman batun sharar dakinma ko zomata arai baiba Dan tun fitar Hafiz tadawo daki ta kwanta tanata dannar wayar ta ibada sai ynx da caji yaqare ta haqura ta ajeta ta sata a cajin.
rabon ta da wanka yau 2 days knn gashi sai faman kartar kay takeyi Wanda yajima a kwance shima bakitso ba kula, samutai ta sharce kan ta qullesa dudda ba gashi gareta ba tabarsa ya kakkabe Amman yana iya yin parking harda dan saura,
d'an martabar cikin jikinta ne yasa gashin yafara dawowa sakamon da dayabi ya kakkabe SBD qazanta ko parking baiyi.
Samu tai tayo wanka Sama Sama koda ta fito tsane jikinta tai batareda tashafa maiba bare turaren dahar ynz batason qamshinsa, tazura rigar ta doguwa a sharp ta yadin material ja ta fice falo dan yunwa ta isheta.
bataga komi ba a dining tsoki tai tarasa gane cikin zainab da fateema wakeda girkin bai ba,
sabida tsabar wulaqanci abar mutum da yunwa.
Kitchen ta wuce tahado madara da snack ta tsaya ta ci ta koshi snn ta fito falo, ta zauna.
ko minti 5 batayiba da fitowa saiga zainab ta fito anci wanka na wani tamfatsetsen less Riga da siket sai qamshi take bulawawa abinta,
tafiya tk cikin takun isa tana waya da qawarta tana fadin
"to shiknn saina jiki goben kishigo pls ramla akwai mgn OK by saina ganki".
katse kiran tai ta zauna kujerar dake facing herma ta dubeta ta tave baki tana cigaba da taunar cwingum yanata qara Qas Qas, takaici taji ganin cikin heema sai barazanar shirin fitowa duniya yake, aranta cewa tai
"hmnn basai kin haifi d'an cikin naki da ranshi ba, target dina na farko kan cikin jikinki zai fara heema dan bazai yiyu inaji ina gani kicika gidan hafiz da ya'ya ba niko babu amo babu labari, kamin najuya kan waccen dayar shashar matar tasa(tana nufin fateema, Niko nace hmnn zee fatimar da kikasani bata ynz ba Amman dai bari muga ko matan Hafiz din zasuyi nasara kan mijin nasu a junansu)
"Hey sannu hjy hema mai ciki yakikaji da qwarin jikin?"
abinda zainab tace knn wa hema a raine da kllon wulaqanci. Kallonta hema tai dudda tafahimci da salon mgnr zee Amman saita share gamida furta
"lfy"
daga haka taja bakinta ta tsuke tamaida hankalinta ga TV tana kallon wani Indian film mai suna
Asaka Tara(poris) munaqisan dake cikinsa a baqaramin mamaki takeyiba kodayake ba abun mamaki bane HK rayuwar take a koina.
Fateema ta fito daga daki ganin matan Hafiz zaune yasata mamakin toku yadawo ne?
zama tayi a wata one theater tana binsu da wani kallon raini tana tabe baki,
wayarta ta fiddo tana buga game tanata sheqa dariya.
zee ta qufula damn taji haushin fateema datazo ko miqo gaisuwa baitawa kowace ba kmr ynda ta saba saima wani kallon banza dataga kmr tana musu, kodai idonta bainuna mata daidaiba?, danhaka fuska daure ta dakawa fateema tsawa da fadin
"dalla malama daina mana dariyar hauka anan wnn ai wawanci ne tsabar kin rainamu kinzo kinsamu manyanki a waje ko sallma babu bare gaisuwa wnn yanuna ba'a samo tarbiyya ba a gida ga alamdai gidan ku ba manya k..... tun kamin zee ta qarasa Fatima ta miqe afusace itama dantaji ciwon mgnr datai mata, tamayar mata da cewa " ke saurara kece dai gidanku ba manya dan kowa kikaga tana zagin iyayen wasu to uwarsa da ubansa ya raina su, sanna ynz daidai Nike da kowace 'yar iska wlh a gidan nan ynz ba da bace kowace tacemun kulle zan cemata cas koda dinma da kukaga inamuku lubbu lubbu dannaga kamin luddenkune kuma nafahimta anyi walqiya ta haska mun Ku dan haka kowacce ta riqe kanta imba hakaba kuwa mukwashi yan kallo yanda kike taqama da kanki haka nike taqama da nawa dan kinsan ko qashi zamu hada baki isa ki d'ibi komi a jikina ba bare su o'e kilishi ba abin sai kwadayin ayi cikin a haihu ba'asan ynda za'a kula da miji ba a faranta masa tayi mgnr tana jifan raheema da harara tana riqe da qugu.
ko kallonta raheema bataiba amman abun yamata ciwo wato dudda suna abinsu bata samasu baki ba amman hakan baisa ta tsira ba knn saida aka gaya mata ba dadi? zee kuwa tsabar mamakin fateema yasata surrender tasaki baki kawai tana kallon ta, daqyar ta had'a yawu ta dubi heema tace
"heema yaushe fateema ta koma tambadadiyar watsattsiyar yarinya ban sani ba wacce ta kwashe kayanta daga gaban manzo?"
kamin heema tace wani Abu sukaji mgnr Oga Hafiz kamar daga Sama yana fad'in......
*By 4 writers fasaha*😍
[7/12, 8:34 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!
*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.
Written by.
*FOUR GORGEOUS WRITERS*
-Raheenat mahmud.
-Mmn Abduljalal.
-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).
-Matan Borno.
*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*
Bismillahirrahmanirraheem.
*Gargad'i*
Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.
15.
Wai ke Zainab yaushe zaki yi hankali ne? Ta na shirin yin magana ya Daga mata hannu ya cigaba da cewa "Ba fa tsoronku nake ji ba da nayi shiru na kyaleku kuna iskancin da kuka ga dama, har kunya nake ji abokaina su zo gidana saboda kada kuyi mini hauka a gabansu, A ido dai gaku Kamar masu hankali Amma ko mintu biyu mutum ya zauna daku sai yayi Allah wadai daku, to ya isheku hakanan ko wacce ta gyara halinta idan ba haka ba Kuma hmmm ya sa Kai ya bar musu gidan gabaki daya."
Takaici bakinci sune suka Hana Heema ko motsin kirki, ita dai ta shiga uku a wannan gidan. kowa tashi jabarshi sai ya hada da ita, bata shiga harkar kowa Amma kullum sai anci mutuncinta. Magangannun Hafiz sun Kona mata rai sosai maimakon ya hukunta Zainab da Fateema da suke matsifar su aa Saida ya hada da dukansu. Zage zagen da su Fateema suke shi ne ya dawo da ita a duniyar tunanin da ta lula, dogon tsaki taja ta bar musu falon ta shige dakinta.
Asalin labarin
Alhaji Ahmed dane a wajen malam Ismail da Inna Lami, manomi ne Wanda yake zaune a garin Niger republic jahar Damagaran, malam Ismail mutum ne da ya dogara da kansa kasancewa su biyu ne mahaifansa suka haifa shi da kanwarsa Maryam bayan rasuwar mahaifansa da wata biyu kanwarsa ma ta zo ta rasu a lokacin yanada shekara ashirin da uku a duniya ya zama maraya gaba da baya ba uwa ba uba danginshi duk sun guje shi, ko yaje inda suke korarshi suke haka yake shiga gari yayi dako ya samu abinda zai ci saboda karatun ma ya ajiye shi gefe tun bayan rasuwar mahaifansa, Inna Lami sunyi auren soyayya shi da ita diyar maigarin garin ce ta na da kyau ba laifi uwa uba ga kunya, kasancewa maigarin ya san mahaifin malam Ismail bai wani tsaya dogon bincike ya bashi auren diyarshi lami, bayan tarewar lami abubuwa suka Kara kwabe ma malam Ismail ya rasa yadda zai yi wani lokacin haka zai fita gari ya wuni Yana neman aiki ya kasa samu, yauw ma Kamar kullum tafe yake Yana zullumi da tunani yadda rayuwarsu zai cigaba da tafiya a haka har ya karaso gida yayi sallama ya shigo gidan, da sauri lami ta amshi ledar hannunsa tana murna saboda jiya ruwa kawai suka Sha suka kwanta, bude ledar tayi taga garin kwaki ne da suga sai madarar gari leda biyu, ta juyo ta kalli maigidan nata ta ce,
"Malam Ina ka samo mana wannan?"
Murmushin karfin hali yayi ya ce,
"Na biya wajen mussa mai shagone abokina shi ne fa ya bani ledar ni banma bude ba".
Kai Alhamdulillah Allah mun gode maka ka Kara mana kwanciyar hankali da lafiyar jiki, ya amsa da "Amine" wannan halin na lami shi ne yasa take Kara shiga ranshi Yana sonta so mai sanani. Katse mishi tunanin tayi tare da mika mishi ruwa, karba yayi ya kafa kanshi yasha sosai sai ya ajiye yayi hamdallahi, yauwa malam da zu maigari ya aiko wani yaro Yana nemanka... Da sauri ya kalleta tare da cewa,
."Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un, shi kenan lami rabani za'ayi dake dama na sani watarana sai an rabamu saboda na kasa Baki Kulawa yadda ta dace, duk hakinki da ya rataya a wuyana bana cikashi wani lokacin haka muke kwana Bamuci ba ya karashe maganar idanunsa Yana ciko da kwallar tausayin kansu".
Doguwar ajiyar zuciya lami ta sauke ta ce "Babu Wanda ya isa ya rabamu sai Allah, bafa abinda kake tunani bane saboda ni ban taba zuwa gida nace ga halin da muke ciki dan haka ka cire tunanin komai a ranka ka shiga bandaki kayi wanka sai ka je kaji abinda yasa ake kiranka"
Ajiyar zuciya ya sauke ya Mike ya shiga bandakin, Bai wani Jima sosai ya fito ya shirya ya kama hanya ya tafi Kiran surikin nashi tana mishi adawo lafiya ya amsa da Allah ya sa. Da isar shi fadar maigari an tarbeshi hannun bibbiyu an kawo mishi ruwa da abin motsa Baki, saida ya natsu tukunna mai gari ya fada mishi abinda ya sa ya kirashi Kamar haka, "Na kiraka ne saboda ganin irin halin da kake ciki na yanke hukuncin baka daya Daga cikin gonakina na malaka maka su har abada ko bayan raina naka ne, ga takardun ma duk na canca na saka sunanka ya karshe maganar Yana murmurshi".
Hannunshi na karkarwa ya amshi takardu cikin murna da farinciki ya shiga mishi godiya da addu'o'i hawaye na zubo mishi, da kyar maigarin ya shiga kwantar mishi da hankali ta hanyar nuna mishi wannan abin ba komai bane, saboda sunyi zaman mutunci da amana da mahaifansa kafin su rasu Dan haka ya daina godiyar hakanan fatanshi kawai Allah ya sanya mishi albarka aciki ya amsa da amine da haka yayi sallama da maigarin ya wuce gidanshi sai murna yake. Yana zuwa gidan ya nuna ma matarshi Lami abinda ya samesu ta tayashi murna da fatan alheri.
Haka dai rayuwa ya dinga tafiya ya dinga noma a gonar tashi inda ya saka hatsi Alhamdulillah kafin shekara hudu arziki yana ta shigo mishi saboda yana Kai buhuhuwan hatsin shi kauyuka masu yawa Yana Saidaa, yanzu ya ma daina nomar ya dauki yaran da suke mishi, saidai kawai a kawo mishi kudinshi yayi nisafi hata yanayin gidanshi ya canza komai da komai surikin nashi ma Yana yawan mishi alheri da mutanen gari Baki daya, haihuwa ne har yanzu shiru shekarar su takwas da lami har yanzu ko batan wata bata taba yi ba, Bai taba nuna mata damuwarta saboda Yana da ilimin addini sosai ya san cewa hahuwa nufin Allah ne, shi da kanshi yake kwantar mata da hankali watarana. A wani daren juma'a suna zaune ita da lami suna hira misalin karfe Tara na dara sai ganin lami yayi ta mike da sauri tayi hanyar waje tana kwarara amai cikin tashin hankali ya bi bayanta Yana mata sannu tareda mika mata ruwa ta wanke bakinta duk ta galabaita sai ajiyar zuciya take sauke ya riketa suka koma daki jikin nata zafi radau, Daren ranar Basu runtsa ba Daga ita har shi, washegari misalin karfe takwas na safe suka tafi asibiti sun yi sa'a Babu mutane daya mutum biyu kawai suka iske ya je ya yanko kati suka shiga domin ganin Dr, ya mata tambayoyi da Kuma yadda take jin ajikinta da ta mishi bayani yace mata ta je a dauki jikinta domin Kara tabbatar da zarginshi, bata wani jimawa ba ta dawo ya ce su tafi gida karfe uku na rana su dawo domin amsar sakamako.
Bai samu damar zuwa amsar results dinba sai wajen karfe biyar saboda bakin da yayi sun zo neman taimako Saida ya sallame su ya samu damar fita, Yana zuwa a office din Dr ya tura kofar tare da yin sallam ya amsha mishi Yana wasu rubuce rubuce a wasu takardu, ya nuna mishi kojerar da hannunshi ma'ana ya zauna. Yana gamawa suka Kara gaisawa ya mika mishi sakamakon tare da tayashi murna, cike da zumundi ya amsa ya bude Yana gode ma Allah da ya azurtashi da samun karuwa, likitan har dariya yake mishi kudi ya mika ma Dr din masu yawa ya fita ya shiga motarshi yayi hanyar gidanshi ko parking Bai tsaya yayi da kyau ya shiga kwalla ma lami Kira Yana fada mata irin abin farincikin da ya same su, dadi ne taji sosai ta Kara rungumeshi da kyau suka wuce daki, haka dai suka cigaba da rainon cikinsu har ya shiga wata na Tara ta sha wahala sosai saboda tunda safe da aka kaita asibiti sai wajen karfe hudu ta haifi danta namiji kyakyyawa dashi sak tamkar mahaifinsa sai washe gari aka samesu maigari ya aiko mata da wata tsohuwa ta zauna mata har tayi arba'in, ranar sunan yawon yaci suna Ahmed sun dauki son duniyar nan sun Dora mishi kowa kaunar yaron yake saboda yanada saurin shiga rai...
*Yan uwa ku bimu a hankali domin gane inda muka da so, yanzu labarin kankanin Hafiz muke bada wajen mahaifinsa✊🏾.*
*By 4 writers fasaha*
[7/12, 8:34 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!
*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.
Written by.
*FOUR GORGEOUS WRITERS*
-Raheenat mahmud.
-Mmn Abduljalal.
-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).
-Matan Borno.
*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*
Bismillahirrahmanirraheem.
*Gargad'i*
Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.
16.
Kwance tashi Babu wuya a wajen Allah, sai gashi Ahmed ya cika shekara goma a duniya Yana aji d'aya a college, makaranta ce ta 'ya'yan masu kudi makudan kudade malam Ismail ya biya kasancewar makantar kwana ce, acan ake Basu komai week-end kadai yake zuwa gida yayi shima wani lokacin baya zuwa, Ahmed Yana da kokari sosai saboda kullum na daya yake zuwa a ajinsu shi yasa malamai da dama suke kaunarshi.
Tun daga kan Ahmed Allah Bai Kara Basu haihuwa ba, shi ya sa suke bashi Kulawa na musamman Kuma hakan Bai Hana su sawatar mishi idan yayi laifi.
Shekarar na juyowa malam Ismail ya baiyama iyalenshi gaba daya aikin haji harda surukansa da limamin unguwarsu, Kai ya sha addu'o'i wajen mutanen nan sosai ya nuna musu cewa Babu komai Komai mukaddari ne daga rabbil izati. Ahmed yana Kara girma a ko da yaushe kyawanshi yana Kara bayana kasancewa iyayenshi fulani ne gaba da baya, sai ya kasance shi ba fari ba koma ba Baki ba.
Bayan shekara ashirin da shida abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda kammala karatun Ahmed na sacondry har ya fara University idan ya zabi fannin likita, mahaifansa malam Ismail ya Kara manyanta kokari yake ya sama mishi gurbin karatu a garin Madina saboda ya cigaba da karatunshi a can, Alhamdulillah kafin sati daya ya gama hada komai washe gari zai bar kasar. Misalin karfe goma na dare zaune yake a gaban iyayenshi inda suke mishi nasihohi na yauw da kullum irin ya rike mutuncinshi da darajar da Allah ya mishi Babu ruwanshi da kulla abokan banza, yayi karatun da ya kaishi kawai malam Ismail Yana gama jawabinshi cikin hikima ya goge hawayenshi ya kalli matarshi da tun da zu take kuka ya ce "Haba Hajiya lami ya zaki saka yaro a gaba ki dinga kuka? Salon ki karya mishi da zuciya yace ya fasa tafiyar, bana so ki daina addu'a zaki mishi Allah ya dawo mana da shi lafiya ya bashi nasara a kan abinda ya kaishi".
Da kyar ta mishi addu'o'i tana son Ahmed Kamar ranta da tana da iko da ta Hana wannan tafiyar Amma Babu yadda za ta iya an fita iko. Bayan sun gama ya mike ya wuce dakinshi hawaye na zubo mishi shima tabbas zai yi kewar iyayenshi ba kadan ba da Haka har barci yayi awan gaba da shi.
Washe gari misalin karfe takwas suna filin jirgi da wani takardu da ya kamata ya cika yayi saida jirgin nasu ya tashi suna dawo gida tare da kewar tilon Dan nasu.
Haka dai rayuwa ya dinga tafiya shekaru nata wuce wa har gashi yanzu Ahmed ya cika shegara shida a Madina sauran shekara biyu ya gama ya zama Dan gari kullum suna waya da mahaifansa karatun nashi ma yana tafiya dai-dai tun shigowarshi makarantar ya haru da wata yarinya ana ce mata ana ce mata Amina tana yawan zuwa ajinsu saboda yayi mata Karin haske a kan karatunta na banki tun Yana dari dari da ita har ya saki jikinsa, watarana idan bata zo bama sai ya shiga damuwa.
Wacece Amina? Amina Diya ce wajen Alhaji Anwar da Hajiya Khadija su biyu kawai iyayensu suka Haifa ita da kanwarta Kaltum, a kwai ta da saurin shiga rai gata da kyau kun dai san larabawa Allah yayi musu ruwan kyau batada tsayi gajera ce Amma ba can ba tanada manyan idanuwa Masha Allah shekararta ashirin da hudu a lokacin, iyayenta suna zaune a garin Madina sosai suke sonta Amina yarinya ce mai rawarar Kai idan har tana son Abu duk rintsi sai ta sami abin gata bata da hakuri ko kadan wannan shi ne kadan daga cikin tahirin Amina mahaifiyar Hafiz wannan kenan.
Wasa Wasa soyayya mai karfi ya shiga tsakanin Ahmed da Amina su kansu Basu San yadda aka Yi kawai tsintar kansu suka yi da tsananin kaunar juna. Ahmed Bai fada ma iyayenshi ba ita Kuma Amina tsoron fadi take saboda su larabawa basa auren wani jinshi Amma ta kudurta ma kanta duk tashin hankalin da za'a ba zata iya rabuwa da Ahmed saboda ko wanne bugun zuciyarta sonshi karuwa yake a ranta, kullum idan Ahmed ya ce zai zo gidansu sai ta nuna mishi iyayenta sunyi tafiya wannan abin yana damunshi sosai yauw dai ya sakama ranshi sai idan sun fita aji zai jirata ta fada mishi idan har da wata matsala ne ta sanar dashi.karfe biyar na yama bayan sun fito daga ajin karatu zaune suke a karkashin wani bishiyar