Showing 39001 words to 42000 words out of 78322 words
tunda ta fara girma kawo yanzun na cikar 'yan matancinta abbu ke musu bayanin ya bada ta?
to waye akaba?!
danshi dai bai sani ba dudda suna taredasu abbun kullum, wnn tambayar kam nacimasa tuwo a qwarya.
dayake mutane iya musu sai Allah dud yanda kake dasu kuwa, ahakan mus'ab din yakejin rad'e rad'en a cikin anguwar wai abbu ganin 'yarsa kyakkyawa ce shine yake korar qananun masu zuwa Neman ta , waiga alama auren jari yake shirin yi mata amman hk dai ya danne bai furtawa kowa ba.
samun waje sukai suka zauna wato a inda suka tashi hakama basmah ta dawo ta zauna a umarnin da abbun ya bata,
abbu ya fad'a musu ammi ynda sukai da mutimin snn ya zarce da cewa
"to ina sauraranki basmah fad'a mana miyafaru waye ya biyokin har yazo neman haqqinsa gareki wanne irin haqqi ne kuma?"
haka abbu yai mata tambayoyin a jere yana
kallonta Ammi da mus'ab ma ita suke kallo.
sunkuyar da kanta tayi qasa tana mai sauqe ajiyar zuciya, sosai taji nutsuwa da abbu ya barta na mintocin nan dan kuwa tasamu ta had'a zarurukan plan dinta yanda zata kubuta daga tambayoyinsu musamman ma taji hankalinta yadan qara kwanciya dataga su abbun sun dawo lfy lau daga wajen nutumin dabatasan waye ba ma.
dan haka murya a sanyaye ta fara cewa "dad....daman jia ne dana shiga gidan adda salma bayn ammi datace inje ta aiko yaronta kirana shine na samu kanwarta badariyya tazo shine kuma adda salma ta aikemu siyan pumpers a store din Alhj haruna na bakin kasuwa to... to shine sai bayan mun fito ne muna hanyarmu ta dawowa gida bamu lura ba muka zubarwa da wani mutum gurasar sa dayakeyi a lokacin, dayake dare ne abbu kuma wajen da yakeyin gurasar yayi d'an duhu shiyasa bamu lura da inda muka saka qafar mu ba akwai wani abun agun, shine ya biyomu yana cewa sai mun biyasa kuma mun basa haquri ya qiya shine ya biyomu har kofan gidan adda salma to munyi sa'a mijinta na nan shine ya basa kudin gurasar da ya fad'a adadinta to shine abinda ya faru abbu" mus'ab yace "to inda an biyasa mizaizo yayi anan kuma har kike tsorata?" da sauri ta ce "ay..ay nazata shine yadawo yau danna tsorata da mutumin nan yah mus'ab sam basshida kirki" "ay inda an biyasa shiknn bazai dawo ba by now kuma kudinga lura a cikin tafiyanku" cewar ammi.
abbun yace "ni fitar daren ce ma banaso garin yaya ma ta fita?"
abbu yayiwa ammi tambayar,ammi tace
"ayi haquri Mlm salman ce ta aiko kiranta jian kuma kaga maqotane snn ga danyen jariri shine nazata kowani aikin ne yataso zata mata" shiru abbu yai yace
" to shikn Allah kyauta gaba" "amin"
suka amsa,
yayinda zuciyar basmah ta samu dan qarin nutsuwa sosai taji dadin kiran da adda salma tai mata jian kuwa dan gashi plan dinta yahau Kan turba,wanda haqiqanin gskyn lamari ba aikensu Adda salma tayi ba aiki tasa su itada qanwar tata a lokacin wato su shirya mata wadrobe dinta dana baby dayake yau kwana 4 dayin sunan babyn tata wadda taci suna humsanatu, komi ya hargitse mata ga tarin gajiya ga batajin dad'i.
shiyasa ma tasasu aikin, da ita zatayi abinta dan sam adda salma batada qyuyan aiki tana da tsabta matuqa gaya ga kirki.
(wacece adda salma?)
adda salma maqotane gasu ammi wanda gida 6 ne ya rabasu, mijinta dan sanda ne wanda asali ba garin Kano suke da zama ba su yan maiduguri ne to silar anyiwa mijin nata muntari d'an sanda transfer na aiki zuwa Kano shine mafarin zamansu anan din wanda a qalla ynzu sun shafe kusan shekara 8 a anguwar, yaransu biyu al'amin dan shekara 5 daga shi kuma sai bata kuma samun haihuwa ba sai ynz data haifi jaririyanta mai suna humsanatu, mijinta nada kirki shima,dan ko kwanciyar da abbu yai asibiti sun jajje musu sau kusan nawa.
adda salma macece mai kirki sosai batada rowa battada baqinciki sosai take sana'arta na kayan mata iri-iri masu kyau da inganci,
sosai mutane ke tururuwan zuwa saye hadda masu sari, tana gyran amare wato ta had'asu ciki da waje shiyasa komi na adda salma tsab tsab.
yanzun ma haka an kusa bikin qanwarta badariyya shiyasa tun bikin yarage wata 2 tasa qanwar tata tazo ta fara hada mata magungunan tana sha masu azabar kyau wato *hana kishiya saqat sai ana hadawa da tsoron Allah,* komi ta ba badariyya ta sha saita bawa basmah a haka suka dauka tsawn nn lkc, acewarta matsayin qanwarta ta dauketa dan haka itama zata fara tsumata tun ynz dan ta ginu kan hakan sabida su dmn hkn al'adar garinsu adda salma ce tsuma mace tun tana qaramarta.
wasu magungunan ma basmah batasan kona miye bane haka taketa dura matasu. hatta dilka da halawa tare take musu sosai jikin basmah yafara canzawa a tsayin sati 4 na dawowar su asibitin, tayi kyau har wani sheqi takeyi. Shiyasa hamiz bai gajiya da surubtun zuwa gidan ynz dan sanyin idaniyar tasa wacce batasn ma yanayi ba, Allah sarki boyayyen so knn.
to ynz wnn satin ake fara events na bikin badariyya dan a jibi ne su adda salma zasu tafi gida domin fara shagulgula,
basmah taso tabisu amman adda tace tabari taje da ita wataran inda ynz sun kusa fara exam next week ga shi kuma ita kadai ce take temakawa ammi a ayyukn gida da sauransu wnn shine kadan daga cikin tarihin adda salma)
har kuka basmah tai dataji adda ta hanata safiyar ranar ko bataje gidan adda salma ba a daka ta wuni tana mad'od'owa gefe daya zuciyarta na qara azalzalarta da tunanin mafita gameda samun kudin mutumin nan dole kanta ya fara ciwo babu shiri sabida tsabar tension din dayafi karfinta, mafita kawai take nema.
*
sintiri kawai yakeyi a cikin babban office dinsa wanda ya qawatu fiye da gaban a misilta, damuwar sa kan rashin sanin inda yarinyar take bai musultuwa kullum abun gaba yakeyi maimakon yasamu sauqin zuciyarsa knta koya manta da lamarin ta amman inaa qaramar mgn ta zama babba zai iya rantsewa da Allah cewar daren jia bai runtsaba kwana yayi sallan kan Allah ya kawo masa mafita kan lamarin, zama yai kan gefen hand chair din office din ya tsurawa coppe dinsa idanu wanda yasa aka kawo masa bai sha ba,ko kalaci bai tsaya yiba haka yai sammakon baro gidan nasa dan a lokacin cikinsu ma babu wacce ta farka, daurewa yai ya sha coffy din gamida chips snn ya Shiga toilet din office din bayan yacire yar tasaman uniform din jikinsa, brush yasakeyi gamida dauro alwala ya fito ya shimfida pray mate yafara gabatar da sallar walha, sosai Hafiz keda ibada azkar koda yaushe bai tsinkewa daga rayuwarsa wanda zamu iyacewa da temakon yawan azkar dinsa ne dayabi jikinsa da zuciyarsa yasa har ynz babu wani tasiri daya fara aiki kansa gameda matansa dasuka fara bin malamai a kokarin kowacensu nason mallakesa inka dauke heema, tabbas annabi yayi gsky yawan yin azkar nakare mutum daga wasu fitinoni na rayuwarsa batareda shi mutum din ya Sani ba, gadai shinan ya faru ga Hafiz ya nama cikin faruwa yanzun zamu iya cewa, ya jima yana addu'oe bayan daya gama sallar, snn ya miqe ya dubi agogo 10 tayi kuma sunada meeting a lokacin suda major general dinsu dasauran ma'aikatan, babu bata lokacin yawuce zuwa meeting din, ana cikin meeting din kuwa wani tunani ya fado masa kan matsalar data taso shi a gaba, aikam kamar yayi tsuntsu yaji a lokacin yatafi amman haka ya daure har aka tashi,
ana tashi daga meeting din ko dasauri ya fito ya fad'a motar sa ya figeta sai hospital din dadynsa street, kai tsaye Dr blessing ya nema, nan ya umarceta data binciko masa file dinsu basmah mai daukeda details dinsu,
Dr blessing tayi mamaki a ranta akan mizaiyi da file dinsu amman bata nuna ba haka ta tafi nemowa, tajima snn tadawo dauke dashi a hannunta, amsa yai ya buda, wani sansanyen boyayyen murmushi yai gamida zaro wayarsa yadan matsa daga gbn Dr blessing yayi hoton address din anguwarsu gamida phone number daya gani a rubuce, ya jiwo ya miqa mata gamida furta "tnzz alot Dr"
dasauri ya nufi motarsa ya qure gudu uwa zai tashi yayinda Dr blessing tabar gun cikin tunanin hakan..
ya shigo layin anguwar kamar yanda ya gani a rubuce wato address din daya biyo na jikin wayan sa a hoton daya dauka,
da tanbaya har ya iso ainihin layin nasu basmah, nesa da gidan ya tsaida motar tasa batareda ya fito ba, sauqe numfashi yayi snn ya bude motar ya fito ya jingina da ita gamida hard'e kafafunsa hannuwansa yayi crossing nasu a chest dinsa fuskarsa saye dawani black ear glass still uniform din sane a jikinsa, kowa yawuce ya gansa tsaye agun sai yayi mamaki miya kawo wnn hadadden sojan a anguwar?, sai dai babu damar tambaya saidai su wuce salin alin suna faman waiwayen sa, 'yan layin wane yaji ga wane wanda kuma suka shiga cikin gida suka fadawa na ciki sai leqe ya tashi, wasu ta kafar qyaure wasu ta maguji , da masu wucewa su ga qwam, sosai zuqatan mutane suka cika da mamakin miya kawo balaraben soja an guwarsu, dan harga Allah sunyi zaton balarabe ne, koda yake d'an balarabian ne babu mamaki, tsarguwa yai da anata faman kallonsa dan haka a hankali ya zare glass din idanunsa yana bin kofofin gidajen da kyawawan idanunsa nan yaga kawunan mutane hawa hawa wasu harta 6ular bango da katanga ya gani suna leqosa, murmushi kawai yai tareda komawa motarsa yajata yabar anguwar dudda yaso ganin burin zuciyar tasa amman anguwarsu zatayi masa wuyar shigowa a wnn rana, saidai bai damu sosai ba inda yaga gidan zai dawo zuwa dare.
sai gashi da daren kuwa wani aiki ya riqesa sai 10 snn ya iso anguwar, yayi mamakin ganin mutane da yawa a qofar gidan ga Alama makaranta ce, saida ya nutsu ya tsaya daga nesa kadan daga inda ya ajiye rova rova machine dinsa ya gane ashe Mlm usamane malamin makarantar knn
(dan da mashin yayi ra'ayin dawowa anguwar wnn karon ba mota ba)
gani yai anyi addua ana kwashe shinfidan ga alama an tashi daga makarantar, ga hadari na motsi kadan, sannu a hankali yaga mutane nata barin wajen wasu a qasa wasu kuma a abin hawansu,
shima Mlm Osama gida ya shiga da dardumarsa ga hannu wajen yai tsit gashi an guwar babu wuta sai masu sana'ar janareto jifa jifa dake hanyar wnda da temakon hakanne haske yadan wadaci area din, a hankali ya qarasa kofar gidan yana tunanin yasan babu ynda za'ayi abar ta tafito yanzun koda kuwa ya aika kiranata dan goma harta gifta, shiru yai gakuma hadari na cigaba da tasowa dan kuwa harya fara sakin walqiya, lumshe idanunsa yai gamida zura dukkanin hannuwan sa a aljihun tattausan yadin jikinsa, jiyake bazai iya barin gunba batareda ya sakata a ido ba koda ruwan nan zai qare kaf a kansa kuwa,
zuciyarsa har hucin zafi take shi kadai yasan miyakeji time din.
yayinda a daidai lokacin basmah na gidan adda salma suna kallon wani film a wayar addan,
bata ankaraba sai jin rugugin hadari tai, zumbur ko ta miqe tsaye bayan data kallo agogon dake cikin wayan adda salma lokacin, afili tace "na shiga 3 adda nawuce lokacin da Ammi tace in dawo gida, kinga 10 har ta wuce kuma nasan su abbu sun tashi a mkrnat ynz, natafi saida safe, dudda haka saida adda salma tasa badariyya ta rakata ta fita daga soron gidan dayake yanada zurfi kuma ga duhu har badariyya tana mata dariya gamida tsokanarta
"basmah sarkin tsoro,abinda ga baki ga hanci" ita dai basmah da d'an gudu gudu ta nufi gida, jin motsin ana nufo inda yake ne ya sashi bud'e idanunsa dan lokacin har ruwa yafara sauqowa, sauqinsa ma gidan nasu basmah cikin baranda yake shiyasa baiji digowan ruwan a jikinsa ba, saidai ita da take kokarin shigowa barandar ta shiga gida ta fara jiqewa, ganin mutum a gefen kofar gidan su ga duhu batasan kowaye ba kuma shine yasata bugun zuciyan tsoro sabida babu kowa agun,
to wane ne? daurewa tai taqaraso zata wuce yayinda Hafiz tun tafowar ta da akayi wata walqiya ya fahimci itace,
wani sansanyan dad'i yaji yana ratsa sa kota ina, ganin ta ra6asa tana shirin shigewa gida yasashi hanzarin riqota, ita ko daman da jininta ya ke kan akaifa ta bud'a baki zata tsala ihu yayi saurin ida janyota jikinsa gamida rufe mata baki da hannunsa 1,
sai mutsu mutsu take abinka ga sarkin kuka tuni ta fara sako qwalla dan a tunainta tayi gamo da masu yankan Kaine ko kidnappers,
shi ko a hankali yasa hannunsa a aljihu yazaro wayarsa ya kunna torchlight gamida haske fuskarsu lokacin 1 , cak kukanta ya tsaya sauyin bugun zuciyarta ya qara hauhawa sabida tsabar firgitar da tai na ganin wanda ke gabanta a yanzun , wato yabiyo sahun kud'insa knn?
aikam sabida gigicewa nan take ta fara ganin lummmm2 a idanunta, a hankali ta fara kokarin yin mgn,
cak! kuma sai tsoro ya ida yin nasarar tafiyar da numfashinta gaba daya ya sumar da ita a jikinsa....
sulalewa take shirin yi daga jikinsa zuwa qasa ,dasauri yatarota ya maidota jikinsa cikin faduwar gaba shima sabida ya fahimci sume masa tai,
gata dai a hannunsa kamar matatta rasa ynda zaiyi ya ceto numfashinta yai gashi lokacin na tafiya ai kam bai sanma sanda ya kamo fuskarta ba da tausasan tafukan hannayensa ya had'e bakinsu waje guda yana hura mata iska domin bata taimakon gaggawa da tunanin kozaya dace ta farka time din,
wani qaqqarfan iska ya taso mai kuwwa da feshin ruwa, kankace mi lokaci daya kuma ruwa ya ida tsugewa shaaaaa ba qaqqautawa uwa da bakin qwarya ..
*By 4 writer's fasaha👩👩👧👧😍*.
[7/12, 8:34 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!
*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.
Written by.
*FOUR GORGEOUS WRITERS*
-Raheenat mahmud.
-Mmn Abduljalal.
-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).
-Matan Borno.
*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*
Bismillahirrahmanirraheem.
*Gargad'i*
Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.
30.
Hafiz kuwa dud yabi ya rud'e matuqa gaya, sosai yake mamakin kan minene ya sumar da ita haka badai ganin sa datai ba ko?!,
to miyasa ganinsa zaina tsoratata harta dinga suma shida yake burin ta zama tasa ta har abada su kasance tare!.
sosai ya qara ruqo fuskarta garesa,
ruwan da ake mai tsananin qarfi da rugugin qarar da akeyi gamida walqiya ga kuma hurawa bakinta iska dayakeyi babu qauqautawa wanda hakan ya yetemaka wajen kawo wani dogon ajiyar zuciya da basmah tayi, lokaci daya ta ware idanunta a kansa, da sauri ta miqe daga jikinsa tana ja da baya baya hawaye Na fita ta fara mgn da cewa ''kayi haquri na dauki alkawarin zan biyaka kudin ka ban samu na biya ba har yanzun,qa qara mun haquri dan wlh ba mancewa naiba kowane bugu na fitar numfashi na da tunanin hkn a raina,kayi haquri yallabai dana samu zan kawo wa Dr blessing ta baka don daman account number dinka da kabani ta 6ace, kada ka daukeni marar cika alqawali a'a ba haka nake ba snn kuma ya'akayi kazo gidanmu bacin bamiyi da kai ba?nace zan biya ka miyasa bazaka mun uziri ba Dan Allah?!".
Zuba mata idanu yai Sam shi yama manta da zancen wasu kudi kwata kwata,
wato tsorar da tai na ganinsa knn ko tayi tunanin kudin yazo amsa ta qarfin tsiya knn shine hadda sume masa?!, wani kasalalllen murmushi ya saki gamida soka dukkanin hannuwansa a aljihun jeans dinsa a hankali ya fara takowa zuwa gabanta yayinda ita kuma cikin tsabar tsoronsa ta dinga ja da baya baya batai zato ba tajita ta fad'a ta baya qasa a kicafff sanadiyyar tudunkar zauren gidansu dataci mata diddige, runtse idanunta tai gamida fashewa da wani sabon kuka hadda yarfa hannu uwa wata yarinya qarama, tsugunnawa a gabnta yai yana kallon fuskarta,
sosai salonta na kamar shagwababbiya ya ke burgesa, dudda bawata faduwa tai sosai ba amman tawane lagwabe qasa uwa mage tana kuka,
sauqe numfashi yai gamida miqewa tsaye, ga tunaninta sai taga ya miqo mata hannunsa alamun ta riqe ta taso, kin miqa masa hannun tai saima ta fara kokarin tashi da kanta,
jitai kugunta ya amsa da wani sauti qassss, rintse idanunta tai ta koma ta sulale qasa tana fidda numfashi a wahale dan kuwa har ga Allah taji buguwar qugunta ba kadan ba, matsowa yai ya sake miqa mata hannun a karo na biyu bayan nad'esa da yai daga qirjinsa a karo na farko data qiya, ganin lkc na tafiya tanason shigewa gida gudun fadan abbu yasata babu arziqi ta miqa masa hannun nata,
taushin hannun junansu daya ratsa jikin kowanensu shine yasasu jin wani shocking a jikinsu batareda sun shirya ba, da sauri ta zare hannunta gamida juyawa zatabar gun, zaraf tagansa yaci gabnta yanan mata wani narkakken kallo, kasa jure cigaba da kallonsa tai mafarin data juya fuskarta gefe knn.
"wayace miki kud'i nazo amsa?"!
ya jefo mata tambaya uwa daga sama, kallonsa tai kamar zatai mgn taji yaci gaba da cewa "hasali ma ni na mance da batun wani shiriritanki na biyan wasu kalilan kudi ni idan na bada Abu shiknn yabar kaina so please kibar mn wnn joking din naki it's enough ok? in har abbu ya isa gareki kuma da girman qaunar dake tsakaninku,ya dan taqaita da mgnr snn ya kuma takowa gabnta har suna jin saukar numfashin junansu ga fusakokinsu dudda shi d'in ya d'arata a tsayi, wani dogon numfashi yaja sannan ya
Cigaba da cewa
"ni Abu daya ya kawoni wajenki a ynzun mai matuqar muhimmanci ne kuma a gareni da rayuwata gaba 1"
jikinta yai sanyi da mgnr dayai mata natabar mgnr kudin nan, itakam har ga Allah ya daureta da jijiyoyin jiki, amman fa kuma tasan ay abbu ya isa gareta fiyeda tunani inda shine silar zuwanta duniya tayaya zata had'asa da wani kalilan abu?, sosai take da tabon soja a rayuwarta shiyasa ta tsani komi nasa a rayuwarta,
wasu hawaye ya sulalo mata tunowa da abinda ya faru da qawarta raf'eah wnda hkn ne dalilin jin ta tsani dud wani army man, ynzunma jitake da tanada iko data