Showing 1 words to 3000 words out of 78322 words

Chapter 1 - MATAN Hafiz Book Complete Document .txt

Unknown   

27 Nov 2024

2502

Compiled By Umar Dalha Funtua.


Copy By Xayyneb ( Xexen Fasaha).


*♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




*Gargad'i*


Bamu yarda a juya mana littafi ko ta wacce siga ba tare da izini ba.




1.




"Menene wannan? uhmm.Nace menene wannan?
Ya fad'a cikin kufula tare da watsa mata d'aurin kud'ade a jikinta.


Da mamaki karara a fiskarta take dubanshi , ta gagara ko motsa bakinta balle tayi magana.


"Ba anan kikace bakisan na shigo da kud'i gidannan ba? Yaya akayi kuma na samesu cikin bedroom dinki har cikin handbag dinki.


Sai a lokacin ta samu damar furta "Inna lillahi wa Inna ilaihir rajiuna."


Sassauta murya kadan yayi.
"Yaushe Kika zama haka?
Me yasa kishi ya rufe miki ido kike neman ki b'ata sunanki da rayuwarki?
Tunda zainab ta shigo gidannan kika gagara kwantar da hankalinki a zauna lafiya, fitinar yau daban na gobe daban.
Shin akanki aka fara kishiya?
Barin fad'a miki bazan lamunta ba. Wannan shine na karshe, idan na sake kamaki da wani laifin wlh zan wulakanta ki wulakanci mafi muni kafin ki bar gidannan.


Yana gama fadin haka ya kwashe kudaden da ya zuba mata a jiki ya juya cikin zafin nama ya barta a wajen daskare tana binshi da kallo.


Kuka take sonyi amma yaki zuwar mata sai zafin da zuciyarta ke mata.


Wannan wani irin bala'i ne?
Bayan hakurin kara mata kishiyar da akayi har kuma sharri sai suyi ta biyo baya?


Kwanaki anyi mata sharrin ta zuba sugar a abincin kishiya, ta dandana kuma taji sugar'n.
An sake cewa ta ajiye laya a dakin kishiya.
Ance ta yanka d'ankwalin kishiya , kuma an nuna mata ta gani a yanken.
Tana tabbaci zainab ce ke aikata hakan da kanta kuma ta ce itace.
Bata b'oye mata ba ta sha fad'a mata cewar sakacinta yasa aka aurota.
Ta sha cika mata baki cewar da ace itace matar Hafiz ta fari bazai yi mata kishiya ba har abada.
Ta sha sanar da ita cewa yanzunma kuma bazata zauna da kishiya na tsawon lokaci ba.


A yanzun ma tana da tabbacin shirin zainab ce kai mata kudin Hafiz har cikin d'akinta a cikin handbag nan kuma bata ma san ya shigo gidan da wani kud'i ba.


Tsam ta mike ta nufi d'akinshi.
Tare da samesu ta zainab yana had'a kudaden cikin jaka.
Kud'ade ne masu yawa.
Duk yawan kudaden da ya fitar daga dakinta basu kai rabin wadannan ba.


Zainab ke tambayarshi kudin na meye ne cikin kinibibi da kisisina shi kuma yana basarwa, sai huci yakeyi yana ci gaba da jera kudaden.


A kansu ta tsaya tana binsu da wani irin kallon tsana yayin da zainab ta d'ago da jefeta da munafukin murmushi tare da kashe mata ido d'aya.


"Hafiz" ta kirashi da murya mai cike da b'acin rai.


Duk da yadda ta kira shin ya tab'a shi, dan bata kiranshi da sunanshi ko kafin suyi aure ma.
Hakan kuwa baisa ya dago ba balle ya amsa mata ba.


Bata damu da rashin amsawar ba tace.
"A shekarun da mukayi da kai a gidannan natab'a yi maka sata?


Sata fa?
ta sake maimaita kalmar satar da alamun kalmar yana kona mata zuciya.


"Kada ka manta, tun baka kai haka ba nake tare da kai.
Ta dan ja fasali snn ta kuma cewa.
"Kuma na tabbata kasan da cewar ba don kudinka na aureka ba, tunda a lokacin dai ba wani arzikin a zo a gani kake dashi ba.
Idan ka gaji da ni kana so ka rabu da ni ba sai ka jefe ni da sharrin sata ba.
Gida naka ne igiyar auren a hanunka take, duk lokacin da ka ga dama zaka iya datse ta ba sai ka bi ta haka ba.
Saboda haka na gaji , kasan yadda zakayi dani yau a gidannan dan naga abin naku ba mai karewa bane.


"Ke kuma."
tace bayan ta maida kallonta ga zainab dake jin dadin dramar da ake tafkawa a dakin.
Ta ci gaba da cewa.
"Ki sani Allah baya barci, shi masani ne akan duk abinda kike aikatawa na b'oye da na bayyane.
Zan ci gaba da kai kuka na gareshi yayi min sakayya daidai da sharrukan da kike kulla min.
Allah zai min maganinku."


Ta karashe maganarta murya na rawa.
Sosai maganar satan yayi mata zafi.


Fuuu ta fice ta nufi falonta, kamar zata zauna anan saidai zuciyarta na azalzalarta da ta dauki mataki.
Cikin zafin nama ta shige dakinta ta janyo madaidaiciyar jaka tana zuba kayanta.


***


Tunda ta fita Hafiz yayi tsai yana jujjuya maganganunta a cikin kwakwalwar shi.
Gaba daya jikinsa yayi sanyi.
Idan ya fahimceta duk abinda yake faruwa a gidan bata da masaniya shiri ne kawai dan a shiga tsakaninsu.


"Ikon Allah."
ya tsinkayo muryar zainab take fada cikin alamun mamaki.


"Ko meye dalili sanya ni ciki ni kuma? Wannan shi ake kira da kora kunya da hauka."


kallonta yayi kamar zaiyi magana sai ya fasa ya ture jakar hanunshi ya fita da sauri.


Kofar falonta ya sanyawa makulli ya kulle ya zare ya jefa cikin aljihunshi.


Haka kawai jikinshi ke bashi zata iya tafiya akan maganar nan.
Shi kuma abin kunya ne a wajenshi a ce daga yin sabon aure uwargida ta bar gida.


Kuma ma ko ba komai uwar 'ya 'yanshi ce.
Bai kamata ace an ji su akan kud'i ba, kudin ma da tare sukayi gwagwarmayar rayuwa kafin ya samesu.




****


Wani iri zainab taji ganin ya fita baice komai ba.
Bata san abinda ke zuciyarshi ba.
Shin maganganun Raheema sunyi tasiri a kanshi ko kuwa.


Ta jima tana tsaye a dakin nashi cikin rashin abin yi sannan ta koma can babban falonsu ta zauna ta kasa kunne tana jiran tashin hayaniya amma gidan tsit tamkar babu kowa a ciki.




****


Ita kuwa Raheema zuciyarta bai bar tafasa ba har ta gama hada kayanta cikin jakanta ta ratayo gyale tare da dauko jakan.


Turuss ta ja ta tsaya jin kofar falonnata a garkame.
Murda handle ta sakeyi nanma ko motsi.


Jifa tayi da jakar a kofar tana cewa.
"Yau ko kafi Umma kokari (Uwarshi kenan) sai na tafi gidanmu.
Dan ita a yanzu Umman tafi bata haushi dan ita ta assasa maganar karin auren Hafiz din.


****


Tafe yake cikin motarshi yana tunanin rayuwarshi da Raheema.


Itace Uwargidanshi, sunyi soyayya kwarai da gaske, tun yana makaranta ta jira shi ya kare sukayi aure kafin ma ya samu aikin sojan da yake matukar so.
Da ke yana da'n tab'a sana'a dashi sukayi ta lallab'a rayuwa har Allah ya azurtashi.


Hafiz mutum ne mai zuciyan neman na kanshi, abin wani bai dameshi ba.
Ga shi da saukin kai da kyautata wa duk wadda ke tare dashi.
Shi yasa kannenshi suke ji dashi.


Duk da cewa mahaifinsu yana da rufin asirinshi daidai gwargwado amma shi yana iya kokarinshi wajen ganin ya kyautatawa iyayenshi da kannen nashi.


Suna matukar kaunar juna shi da Raheema.


Suna kuma zaman lafiya, saidai matsalar Raheema shine.
Ta fi bawa karance karance muhimmanci akan komai na rayuwarta.
Kullum zaka sameta rike da novel ko waya tana karanta litattafan hausa.


Da farko hakan bai dameshi ba, dan har yakan zauna ta bashi labaran da ta karanta.


Wani lokacin ma tana kwance jikinshi take karanta musu labaran a bayyane.


Raheema tana da tsaftar jikinta matuka, gurin gayu da kamshi bata da matsala, haka ma tana gyara kanta ciki da waje.


Saidai tsaftar muhalline dai sai a hankali.
Farkon aurensu tare suke gyara gidan shi yasa bai fahimci tana da wannan matsala ba saida tafiya tayi tafiya.
Sannan ya samu aikin soja baya zama sosai a gidan daganan rashin kulawar matar gidan ya bayyana.
Shi kuma gashi da son tsafta, yana so a kullum ya kasance muhallin da yake rayuwa cikin shi tsaftatacce ne.
Yayi fadan, yayi nasiha , yabi da lallami duk dai babu canji hakan yasa ya kyaleta kawai kasancewar bawai kwata kwata bata yi bane, tana yi sa'i da lokaci.
Yakance mata bai ga amfanin karance karancen da takeyi ba tunda bata daukan darrusan dake cikin su.
Ita kuwa dariya kawai takeyi ta ce "Baza ka gane bane."


Bayan haka sai rashin girki, zata wuni tana shan fruits, milk, snacks da drinks .
Sam bata damu da girki saidai ya sayo ya kawo musu.
Girkin ma sa'i da lokaci take yinshi.


Sallah ne kam idan ta kuskura ya kamata tana karatu a lokacin sallah, yakan kwace littafin ya yaga, idan kuma wayane ya kwace ya b'oye.
Hakan yasa bata wasa da lokacin sallah.


Tafiya tayi tafiya har kannenshi suka fahimci irin rayuwar da akeyi a gidanshi suka sanar da mahaifiyarsu.


Hakan ba karamin kona mata rai yayi ba dan shima kanshi saida ta nuna mishi ba'acin ranta kuma taje gidan ta gargadi Raheema da ta canza hali ko ta dauki mataki.


Da fari ta sauya halinta duk da dai abin yana mata wahala haka ta jure.


Saida tayi haihuwar farko abubuwa suka fara yi mata yawa ta fara komawa ruwa.


Haka kuma suka ci gaba da rayuwa har ta haifi yarta ta biyu.


Duk da kaunar da take yiwa yaran bata basu kulawa yadda ya dace , hakan ke haddasa rikici tsakaninta da ubansu.


Nanma kannen nashi ne suka kai rahoto inda Ummanshi ta dage lallai sai ya k'ara aure........


[7/12, 8:33 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




2.




Wannan shine dalilin karin auren Hafiz.


Zainab macece mai shegen wayo, ga ta wayayya.
Akwai iya kirsa da kuma tattalin miji.


Tunda zainab ta shigo gidan rayuwar Hafiz ta canza.
Ya fara jin kanshi cikakken namiji saboda yadda zainab take riritashi da bashi kulawa.
Gata da tsafta ta ko wani fanni kamar dai yadda yake so.


Cikin kankanin lokaci ta gama mamayeshi saboda ta gama fahimtar inda matsalar kishiyarta yake.


Dalilin haka kuma yasa Raheema basa shiri sam da Hafiz dan gani take yayi aure yana wulakantata.


Samun wannan dama yasa zainab tayi amfani da halayen Raheema take k'ala mata sharri son ranta shi kuma yake hawa kai ya zauna ba tare da bincike ba.
Har zuwa yau da abin yakai ga maganar sata.


Tabbas yau maganganun Raheema sun tab'a shi har ya fara ganin laifin kanshi da yayi sakaci har yake yanke hukunci ba tare da bincike ba.


Har ya isa gidansu bai daina sakawa da kwancewa ba.


****


Zainab ta jima tana zaune a wajen dan son sanin abinda ke wakana amma shiru kake ji.
Hakan yasa ta tashi taje ta tab'a kofar Raheema dake a kulle.


murmushi ta saki tana fad'in "Allah yasa ta kwab'e muku, wata kila ma tafiyan kenan."


Cikin yanayi na farin ciki tabar wajen ta nufi kitchen domin samawa mijinta abinda zai ci.


***


Tana jin alamun bud'e kofa ta had'e ranta tsaf babu annuri a tare da ita dan ta sawa ranta tafiya kam sai ta yishi.


"Talam mummy."
Tajiyo muryar karamar 'yarta mai shekara biyu. Ita yarinyar a dole tayi sallama kenan.)😆
Wani irin sanyi taji yana ratsa ta mai gauraye da farin ciki.


Yaranta kenan su biyu Allah ya bata (Sultan da Sultana)
Sultan d'an shekara hud'u mai sunan Baban Hafiz.


Sai Sultana yar shekara biyu mai sunan Mamarta.


Da gudu Sultana tazo ta fad'a mata tana dariya.


"Assalamu alaikum mummy."
Ta tsinkayo muryar Sultan.


"Wa alaikumussalam D'an albarka."


Cuno baki Sultana tayi tana b'ata fuska alamun za tayi kuka tace "Mummy Talam."


Shafa kanta tayi tana dariya "Sweetheart hoo, Wa alaikumussalam 'yar albarka."


Washe bakinta sultana tayi har fararen hakoranta suka bayyana.
Shima Sultan din jikinta yazo ya zauna fuskarshi fal farin cikin ganin mahaifiyarshi.


Me yafi wannan dadi mutum ya kasance tare da gudan jininshi amma sam dangin ubansu suna neman su rabata dasu.
Ko da yaushe yara suna wajensu har su ma sun saba.


Tana cikin tunanin taji kamshin turaren Hafiz.


Ko da wasa bata dago ta kalleshi ba gaba daya hankalinta na ga yaran da suke bata labari.


"Hy kids, kuje dakina kuga kayan wasan da na saya muku."


Ai da gudu suka tashi suka fita daga d'akin.


Kamar jira take itama ta mike fiskarta a d'inke zata bar mishi d'akin yayi saurin shan gabanta yana bin fiskarta da sassanyar kallo.


Canza hanya tayi ya sake tare ta tare da d'an tureta da kirjinshi.


"Me haka?"
Ta fada cikin b'acin rai.


"I am sorry my wife, Afuwan lillah."


"Kasan inda matar ka take, ni kaban wuri in wuce."


Yunkurin barin wajen tayi ya sa hanu ta bayanta ya mannota da jikinshi.


"Bani da wata matar da tasha gabanki Raheema, Kece macen da na fara ambata a rayuwata kuma kece farko a ko da yaushe ina kuma fatar hakan ya kasance har karshen rayuwar mu har ma a aljannah ke nake fatar ki zamo shugabar matana,
A duk lokacin da za a ambaci maganar iyali kece kike fara fad'o min a rai
Babu kamar ki tauraruwar zuciyata..."


Katse shi tayi da cewa "Dan Allah rabani da dadin baki".
Snn ta fincike ta koma kan stool din dressing mirror dinta ta zauna har yanzu babu sassauci a fiskarta.


Karasowa yayi kusa da ita ya zauna a bakin gado.
"Ni mai laifine a gareki Heemah,
Nasan ban kyauta miki ba, ki yafemin Annurina."!


Idanunta suka cika da kwalla ta dan kawar dakai tana ciza leb'e.


"Sata fa Daddyn sultan?!!,
Nifa kace na maka satan kud'i?!".


"Ya wuce Heemah bakiyi ba, Ki daina mayar da magana dan Allah."


cikin shakewar murya tace "Bazai yiyu ba, dole sai an shiga tsakanina da ku dan na gaji da tayar min hankali da kukeyi kai da matarka a gidannan,
Ban shiga harkarku ba me yasa kuke bibiyata da sharri?"


matsowa yayi daff da ita "Dan Allah Noory , baki yi ba na tabbata,
Rashin fahimta ne yasa nayi tunanin ko kinyi amma nasan baki tab'a yi min ba kuma na yarda yanzunma ba kiyi ba,
B'acin ran da na nuna miki ma tsoron kada kishi ya canza min ke ya gurb'ata tunaninki ne."


"Wallahi Daddyn sultan ban maka sata ba."
"Na yarda" ya fada da sauri.


"Ban tab'a zuba abu a abinci dan na lalata shi ba.
Ban tab'a zuwa gurin boka ko malami dan kayi aure ba.
Bansan ina layan nan ya fito ba,
Amma duk kun d'ora min cewar ni nayi, Wannan wani irin daukan alhaki ne?!"
ta karishe maganar tana fashewa da kuka.


Cikin nitsuwa ya dagota ya dorata kan cinyarshi.


ciki rauni yace "Rashin fahimta ya kawo haka, shi yasa a ke son fahimtar juna a zaman takewa.
Da ace na sameki a tsanake mukayi magana ta fahimta ina da tabbacin zaki fahimtar dani gaskiyar abinda ke tafiya.
In sha Allahu za'a gyara,
Ki daina min asarar hawayenki a banza, in sha Allahu ba za kuma irin haka ba."
Yana magana yana share mata hawayen.


Tsakanin mata da miji cikin kankanin lokaci ya kalallameta da dadin baki suka shirya a ranshi kuma ya kuduri niyyar sa ido sosai a yanayin zamantakewar gidanshi.


Ranar tare da ita da yaranshi suka wuni sai lallab'ata yake yi yana k'ara nuna mata muhimmancinta a gareshi.
Hatta abinci ita ta girka musu suka ci.
Ko da zainab ta kirashi ta gama girki baizo ya ci ba ce mata yayi ta kawo falon Raheema zaici tare da yaranshi.


Zuciyar zainab kamar za tayi bindiga saboda bakin cikin ganin yadda ya sake suna hira cikin raha maimakon ace sunyi mummunan b'atawa.
A sonta ma zuwa yanzu Raheemah ta wuce gidansu shine kuma suka zo mata da wani sabon salon iskanci wanda ba zata iya d'auka ba.


A ranta kuwa kissima yadda zata tarwatsa zamannasu kawai takeyi Raheemah ta bar mata gidan ita kadai.
Dan ta su Sultan bata da matsala da wannan tunda basu cika zama a gidan uban nasu ba.


Hafiz kuwa saboda ya faranta mata rai a ranar tare da yaranta ta kwana.
Dan cewa Umma yayi tayi hakuri sai gobe zai mayar mata su.


Tun daga lokacin kuma zaman nasu ya sauya salon.
Dan sosai Hafiz yake mutunta Raheemah, Sannan babu boye boye yake sanar da ita yadda zata gyara aurenta kuma a hankali tana kokarin kiyayewa duk da dai abubuwan sai a hankali.
Ta riga da tayi amanna da karance karance.


Tsabar iya kirsar zainab sai ta nuna mishi ta ma fishi jin dadin daidaituwar al'amuranshi da Raheemah....
[7/12, 8:33 AM] Xainab Documen: *♨️♨️MATAN HAFIZ♨️♨️*!!!




*FASAHA ONLINE WRITERS*
F.o.w.


Written by.


*FOUR GORGEOUS WRITERS*


-Raheenat mahmud.


-Mmn Abduljalal.


-Xayyneb💤💤 (xexen Fasaha).


-Matan Borno.




*♨️Impacting valuable knowledge and entertainment is our concern.♨️*


Bismillahirrahmanirraheem.




3.


A zahiri gidan Hafiz ana zaman lafiya tunda shi dai baisan wainar da ake toyawa idan baya gida ba.
Snn kasancewar Zainab akwai kirsa bata tab'a nuna cewar akwai abu a zuciyarta game da Raheema a gaban mutane ba.
Hasalima wani irin girmamata takeyi a gaban mijinnasu ko a gaban dangin Raheeman ko dangin Hafiz.


Ammafa idan su biyu suka had'u , bakaken maganganu da habaici, rashin kunya sai abinda zainab ta manta.


Ita kuwa Raheema ta fahimci ramin da Zainab take kokarin hak'a mata shi yasa ta rike girmanta bata nunawa kowa tana da matsala da zainab.
Zainab bata so hakan ba , taso ne Raheema tayi ta tayar da hankalinta suna rikici da Hafiz har ta bar gidan.


Dan kullum ce mata take, ita tafi karfin ace miji zaman hakuri yakeyi da ita har ya fadawa kishiya, maganganu dai daban daban marasa dadin ji wadanda suke nuni da cewa daga bakin Hafiz take jinsu.
Tunda ta nuna mishi b'acin ranta sau daya ya nuna mata baisan zancen ba daga nan bata kuma nuna mishi komai ba.


Tun Raheema najin zafin kalaman da ta zainab take furta mata har ta cire abin a ranta ta d'auke shi a matsayin makamin da zainab ta rike dan kashe mata aure ne.
Tunda dai shi Hafiz baya nuna mata wani halin na daban kuma yana kokarin adalci daidai gwargwadon iyawanshi.
Ita kam tunda tana karanta litattafa ai tasan makircin kishiyoyi kala daban daban.


Matsalar da suke fiskanta har yanzu da Hafiz dai rashin maida hankali kan kula da gidanta wanda ko da ta fara kwatantawa kwana biyu take sakewa dan fa hankalinta na kan novels.
Shi kuma Hafiz baya gajiyawa da yi mata magana kan hakan.


Gwara wani lokacin idan tana cikin karatun idan taci karo da inda akayi fadakarwa game da kula da miji da gida tana dagewa ta kwatanta dan taji ta zamo tamkar star din littafin da take karantawa.


Cikin wannan hali suka k'ara daukar shekara guda da watanni.
Duk bakin cikin da Zainab zata d'ura mata da zaran ta fara karanta labarin da ya nishadantar da ita take mantawa har zainab dinma jikinta ya fara sanyi da al'amarin Raheemar saboda watsi da al'amuranta da takeyi.
Sai kuma karin tashin hankalin Zainab yanzu shekaru uku kenan da aurenta babu ko b'atan wata gashi kuma tana bala'in so taga ta haihu da Hafiz ko don ganin yadda yake ji da yaranshi yake nuna musu k'auna da gata.


Ta kuma sawa ranta kishi da kyashin Raheema ganin duk kokari da tattalin Hafiz da takeyi baisa ya fifitata akan Raheemar ba.
Duk yadda taso ci wa Raheemar fiska baya bari.
Saboda wani lokacin sai suna zaune dukansu suna hira zata fara shisshige mishi cikin yauki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login