Showing 21001 words to 24000 words out of 184891 words

Chapter 8 - DAURIN BOYE Complete Document by Safiya Abdullahi Huguma.txt

alwashin bata sake hawa motar,duk da ba tsufa ne yasata yin hakan ba,uban motar da take ci ne kawai da kuma halin tsiyar qarfen nasara,inda Allah ya taqaita saida sukazo kwanar gidan nasu ta kakare musu a nan,itakam aysha na gefanta,baki daya bata ga abun bacin rai ba,don dai yau kadai.



"Malam ka cikani,Allah bazan biya ba"
"Wallahi saika biya kaji na gaya maka,ba inda zan sakeka kaje" hayaniyar mutum biyu kenan data cika kunnensu gab da zasu qarasa qofar gidansu,hayaniyar na tashi ne daga wani dan case dake maqale da gidan maqocinsu dake kallon nasu gidan,case ne da mai gadin gidan ya bude yana saida katin waya da sauran 'yan qananun abubuwa da ba'a samu cikin unguwar sai sunje waje mai nisa saboda yanayin unguwar tasu,dukkansu hankalinsu yakai wajen,asma'u ta ganeshi tsaf,yayin da aysha taso ta shaida fuskar,da sauri asma'u ta dauke kanta,hakanan taji gabanta na faduwa,ta yaya akai yasan gidansu?,me yake a layinsu?,fatanta daya kada Allah yasa ya nuna ya santa,don ta fuskanci yana da wata zarra da rashin fargaba.



Saidai ko daya addu'arta bata ci ba,don kafin tayi qwararan taku guda goma ya samu isa gabansu,murmushi yake jifanta da shi wanda ya haddasa mata faduwar gaba,babu shakka ba qarya yana da kyau wanda ko gasa ya shiga idan baizo na daya ba zaiyi na biyu,saidai baida makamin da zai tayashi yaqin shiga inda yakeso
"Ranki ya dade....ashe nan ne gidanku?" Ya fadi yana qarewa gidan nasu kallo kamar da gaske yau dinne ya soma tozali da shi,itama gidan ta kalla kaman yau ta soma gani sannan ta maido dubanta gareshi,cikin tsiwa da tsaurin ido tace
"Nan ne,sai yaya?" Murmushi ya saki sannan yace
"Nayi farinciki sosai.....hakan ya nuna Allah yana sona" tana niyyar maida masa habu mai trader da suka tarar suna taqaddama ya qaraso yana sakw fadin
"Mallam ka sallameni ka biyani kudina zan koma bakin aikina"
"Karka damu yanzu za'a biyaka...." Sai ya dubi asma'u dake dubansu galala tana tabe baki
"Ranki ya dade taimaka ki ranta min wasu kudi mana 'yan kadan ba masu yawa ba" kallon banza tayi masa,wani bacin rai na tokare wuyanta,yanzu ita asma'u har tayi arahar da saurayi mai cin bashi wajen masu qananun akurkin shaguna zai tsaya kafada da kafada da ita yana magana?,baqinciki yasa ta kasa magana illa dogon tsaki da taja ta wuce zuwa bakin wangalelen get din gidansu kamar zata saki kuka,koma meye motarsu ce ta jawo mata,da bai isa ya ganta ba bare ya tsaya da ita.




Binta sukayi da kallo duk su ukun har ta shige cikin gidan kafin kowanne ya maido idanunsa inda suke,idanu suka hada shida ayshan,sai kuma ta danyi turus cikin rashin sabo ganinta gaban maza har biyu abinda bata saba da shi ba,sai a sannan ta soma tuhumar kanta name ta tsaya yi a wajen,a hankali ta ciro jakar ta dake rataye a kafadarta ta bude tana fatan samun wani abu a ciki,cikin sanyin muryarta ta daga idanunta ta dubi habu mai trader
"Nawa ne kudin naka?"
"Eh...ammm....dari biyar.....dari biyar ce" dubu daya ta ciro ta miqa masa
"Gashi bani da canji....ka bashi canjin dari biyar din ya riqea hannunshi" tana gama fadi ta maida jakarta kafadarta ta nufi cikin gidan,tana ganin rashin kyautatawarta qarara,tana gani tunda har ya karya billensa ya tambaya buqata gareshi,bai kamata kana da shi ka hana wanda baida shi ba,batasan dalilinsa na tambayarta ba.




Tun kan ta isa parlour din take jiyo banbamin fadan asma'u,tsaye ta sameta gaban mommy sa'adah da alamu labari take bata da kuma nuna bacin ranta
"Sannu da gida mummy..." Aysha ta furta tana dan rusunawa cikin girmamawa
"Yauwa.....ina ke kuma kika tsaya?" Ta tambayeta tana dubanta
"Ta tsaya tana kallonmu salon ta sake samun damar rainani.....munafuka....waya sani ma ko kin sanshi....koma kece kika turoshi?" Bata ce komai ba ta juya ta nufi bangaren da dakinta yake,tana iya jiyo muryar asma'un tana ci gaba da cewa
"Banza baqauya kawai....Allah mommy cikin satin nan indai daddy bai sauya min mota ba Allah na bar zuwa school,ai ba girma na bane a ganni mota tana bani matsala...haba don Allah mommy...sau biyu fa tana min haka" kai ta kada kawai,sau tari tana mamakin halayya irin ta asma'un,itakam har yau cikin duniyar nan bata ga wani abu da zai burgeta ya shiga zuciyarta da yawa har irin haka ba,me ta nema?,meta rasa?,amma ko yaushe qari take nema,ko yaushe so take taga ta zama perfect,ko yaushe so take taga komai nata yafi na kowa,ko yaushe yadda ta tsara ma kanta haka takeso taga ya kasance,tafi dukkan sauran 'yan uwanta mata uku buri da kai kanta can wata uwa duniya,duniyar da ma'abota buri da hangen duniya da tsaho suke yunqurin isa.




Dukka tana wannan tunanin ne tana cire kayan jikinta don wanka take da buqatar yi saboda tsananin ranar da ake kodawa,da wannan tunanin ta shiga bandaki ta sakarwa kanta ruwan shower mai sanyi ba tare data sirka da ruwan dumi ba,koda sanyi ake indai ba tsananta yayi ba tana iya wanka abinta da ruwa mai sanyi,saboda sabo da tayi da wata iriyar rayuwar da tayi can a baya.




Dari biyar din habu mai gadi ya miqa masa yana cikin rusunawa tamkar bashi ya gama cin kwalarsa dazu ba yana cewa
"Gashi yallabai...." Daga kai khalipha yayi ya dubi kudin sannan hannayensa zube cikin aljihun wandon jeans din jikinsa 'yan gwanjo wanda ya ara wajen habun ya dora kan t.shirt dinsa da ainihin wandon jikinsa
"Bakai aikin da kyau ba habu" cikin fargabar ko kada yadda ya ringa cacimarsa ne ya bata masa rai yace
"Tuba nake yallabai...." Murmushi khalipha yayi ya amshi dubu dayan da yake miqa masa yana cewa
"Nan gaba kayi da gaske,ka daina tuna waye ni,kayi kaman ka kama mutumin da yaci bashinka shekara guda ya tsere yau ka kamashi" dariya ya bawa habun har sai daya dara,yana mamakin sauqin kai irin na khalipha,dama akwai masu kudin dake da sauqin kai haka,amma mamakinsa meye dalilin da yasa khaliphan ya maida kansa talaka a idanuwansu?.




Isowar wani matashi cikin shigar coat baqaqe dauke da briefcase wajen ya sanya habu tsagaita dariyar da yake,briefcase din mutumin ya zuge ya miqowa khalipha,dubu dayan daya karba ya jefa cikin sabbain bandiran kudin dake cikin jakar,sannan ya zaro bandir din 'yan ashirin ashirin ya miqawa habu,cikin rawar jiki da murna yace
"Duka wannan nawa ne yallabai?" Kai ya gyada masa sannan yace
"Next term zanci bashin credit....karka manta"
"Allah ya kaimu yallabai...yaushe zakazo"
"Ba lokaci....saika ganni kawai" ya fada yana amsar wayoyinsa daga hannun matashin tare da duba miscal din daya tara zaman da yayi wajen habun,sannan ya soma takawa a hankali zuwa wajen motocinsa dake can bakin layin suna jiransu.




Mai kawai ta shafa ta zura doguwar rigar atamfa a jikinta,bacci takeji sosai saboda jiya bata samu tayi isashshen bacci ba,tayi karatu sosai hakan ya hanata bacci da wuri,kan gadonta ta koma ta janyo wayarta ta soma lalubar lambar aliya wadda bata jin dadi bata samu ta shigo ba,ringing uku aliyar ta daga tana fadin
"Yanzu nake zancanki cikin raina" murmushi ta saki mai dan sauti,tana jin dadin yadda aliyar ke nuna mata qauna
"Nima kina raina,lactures ne yau sunyi zafi da yawa aliya,kaina har ciwo ciwo yake wallahi" ta qarashe maganar da sanyin muryarta,dariya aliya tayi
"Tofa....alhuda huda yau da kanta take fadin haka?,lallai yau kun gasu" 'yar dariya itama tayi
"Eh lallai jiki yayi kyau tunda har kike da bakin tsokanata....to Allah ya qara lafiya"
"Amin sashin(haka take kiranta wasu lokutan),naso na shigo makarantar yauma,mama ce tace na bari na qara jin dama zuwa jibi da muke da lacture"
"Allah sarki mama...ki gaidamin ita don Allah"
"Keee....wai me kike nufi?...banfa dauke miki dubiya ba" dariya ce ta qwacewa aysha ba tare data shirya ba
"To kuma me kika ji nace?"
"Baki ce ba amma i know you in and and out eesha....bakyason zuwa gidanmu bakison zuwa gidan kowa....bansan me yasa ba..ko kina tantamar qaunar da nake miki" tabbas ba qarya aliya take ba,hakanan take jin kaman bata dace data rabi kowa ba,bata kai matsayin hada alaqa da kowa ba tunda har uwarta mahaifiya ma bata da buqatarta
"Kiyi haquri sashin...gobe zan shigo in sha Allahu"zaro ido aliya tayi kaman tana gabanta cikin mamaki da doki
"What...da gaske kike?"
"Na taba miki qarya?" Ta amsa mata cikin dariya dariya
"Heee....Allah ya nuna mana gobe....breaking news yau a kunnen mama...kinga bari naje na soma shiri tun yau...sai anjima" ta fadi cikin zumudi gami da katse wayar tabar aysha da dariya,tasan dole aliya taji dadi saboda yadda take qaunar ayshan,bugu da qari tunda suke zuwanta gidansu daya sanda mamanta bata da lafiya wannan shine na biyun.



Wayarta ce ta sake ruri a karo na biyu,sake jawo wayar tayi tana tsammanin aliya ce ta sake kira,idanunta ta zaro zuciyarta na bugawa ganin sunan wadda ke yawo saman screen din wayarta,a zabure ta miqe ta zauna sosai saman gado bugun zuciyarta na qaruwa,UMMI NA sunan data yi serving number mahaifiyarta dashi shike yawo saman wayar,tunda take karo na farko da lambar wayar ummin ta soma yawo akan wayarta ba tare da ita tayi gangancin kiranta ba,cikin zumudi farinciki cakude da wani irin tsoro ta amsa kiran tana mai cike da fatan ummin tata ce da gaske.




Gauruwar ajiyar zuciya ta sauke sanda tajiyo muryar Basma




"Anty indo...basma ce" ta fada cikin zumudi
"Wai...yau kin tuna ni basma" ta fada tana jin dadi cikin ranta,ko banza yarinyar na sonta cikin 'yanuwanta
"Anty bani da waya shi yasa bana kiranki.....yanzu ma ummi na wanka na dauka bata sani ba"
"Ina ummi basma...tana tunawa da ni?...tana zancena?...." Ta fada cikin karyayyiyar murya
"Ummi bata son ana........."
"Basmah!" Aysha ta jiyo murya ummin na kiran sunan basman cikin tsawa,da alamu ma kusa da ita take
"Uban wa kike kira?"ta sake tambayar yarinyar cikin hargagi
"Kiyi haq....haquri um...mi..." Abinda aysha ta jiyo kenan wayar ta katse,sauke wayar itama tayi daga kunnenta cikin fargaba,muryar mahaifiyarta Kawai data jiyo da fadanta ya sanya jikinta yin laushi tare da tsoro tamkar tana gabanta,zuciyarta ta karye sai hawaye ya soma sintiri saman kuncinta
"Ya Allah" ta furta a sanyaye tana kwantar da kanta saman pillow,fatanta daya Allah yasa kada ta yiwa yarinyar irin mugun dukan data saba,bata taba mance yadda dukan ummin nasu yake,bata mancewa da irin fushinta,bata manta yanayin hukuncinta,gefe daya zuciyarta na saqe saqe kala kala irin wanda ta saba,tasha qaryata mutane da kanta cewa ummin mahaifiyarta ce,saidai an sha gaya mata,kowa ma hakan yake gaya mata itace mahaifiyarta sau shurin masaki,ita ta tsugunna ta haifeta,saidai garin yaya?,me yasa?me ya faru?me tayi mata?,Allah masani har yau bata samu wannan amsa tata ba,ta dade tana kuka saman gadon ita daya har baccin data kwanta dominsa yazo ya sureta
*_WANNAN LITTAFIN NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARINH,IDAN KINA DA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*






*HUGUMA*








11






Washegari kusan wunin kitchen tayi,tana yi tana duba agogo kar lokacin da ta yiwa Aliya alqawarin zata je ya wuce,duk wani snacks da sukeyi su ajjiye cikin freezer dinsu sai data yisu dama ita keyi,tayi packaging dinsu kamar yadda ta saba sai suya a duk sanda buqatar hakan ta taso.




Tana fitowa a kitchen din anty safiyya ta shigo,inna laraba dauke da yaronta al_amin,ba laifi duk cikin yaran mummy sa'adatu ta fisu kirki,tana da dadin mu'amala da son jama'a,tana da fadin gsky saidai tana da fada idan akai ba dai dai ba,cikin fara'a aysha ta qarasa ta karbe al'amin daga hannu inna,ta dosana kan hannun daya daga cikin kujerun falon ta zauna tanawa al'amin wasa ta basu dama su gama gaisawa da mummy sa'ada dake baje a falon cikin takardu tana lissafe lissafen business dinta
"Aysha indo 'yammata....,ba'a ganinku sai anzo gidanku ko?" Cewar anty safiyya tana duban aysha cikin murmushi,itama murmushi tayi ta soma gaidata ba tare data amsata ba,tana cikin tambayarta sauran yaranta asma'u ta sauko daga sama,tayi kwalliya sosai cikin wani irin yadi wanda cikin tsarabar daddy ce,tayi masifar kyau,don dama itadin ba baya bace wajen kwalliya
"Mara mutunci" anty safiyya ta fadi tana gasa mata harara,narke fuska asma'un tayi tana cewa
"Mummy ki mata magana Allah,kinga daga zuwanta ko?"
"Hala wancan me shegen jin kanne yazo" ta sake fadi tana jifanta da harara
"Allah mummy kiyi mata magana.....duk yadda yake ganin mutuncinki shine zaki gaya masa haka?"ta fada cikin bacin rai shimfide saman fuskarta,miqewa aysha tayi ta miqa mata al'amin daya soma neman nono ta soma barin wajen sanda anty safiyya ke cewa
" to basai ki rama masa ba....tunda na zagi qanin mummy"
"Ya isa haka safiyya...ke kullum qorafinki kan hamid ne....kinsan kuma indai ita tana wajen baida aibu" fuuuu asma'un ta wuce ranta naci gaba da baci,babban takaicinta ma yadda anty safiyyan tayi mata a gaban ayshan,yarinyar da taqi jini,ta kuma qi jinin ta rainata ko a disgata agabanta.




Bayan komawarta daki wanka ta sauya ta soma shiryawa,madaidaiciyar kwalliya tayi,tayi kyau cikin laffayar data nade jikinta marron mai adon baqi,tana cikin fesa turare aka turo qofan,asma'u ce ta dubeta
"Ki tambayi lantana kayan da na saka a hada min ki dauko ki kawo min,muna gefan garden"
"To" kawai aysha tace ba tare data dubeta ba,saboda babu abinda ta tsana a rayuwarta irin hamid din yazo asma'u tace taje ta kai musu wani abu,batasan me yasa takeson mata hakan ba,ko da yake hakan baya rasa nasaba da yadda ko yaushe bata da burin daya wuce taga ta qasqantar da ayshan ta kuma nuna cewa ita ba kowa bace a wajenta,hakanan ita din ba jininta bace iqirarinta kenan koda yaushe.




Harta tura qofar dakin sai kuma ta sake dawowa tace
"Ke" tana dubanta,fararen idanunta kawai ta daga ta dubeta
"in zaki zo ki nemi hijabi ki saka,karki zomin a haka" tana gama fadi tayi gaba,hakanan taga ayshan tayi mata kyau,yadda marron din laffayar ta zauna saman fatar farar bufalatanar mace hakan ya sata qyashin ganinta a haka.




Sai data gama komai ta dauko jakarta ta fito baki daya sannan ta qarasa kitchen ta amshi kyakkyawan farantin da aka cika da kayan motsa baki ta nufi inda ta gaya matan.




Suna zaune daf da juna kan fararen kujerun da aka aje a wajen saboda zama da shan iska,isowarta wajen baisa sun gyara zamansu ba,idanun hamid jifa jifa nakan asma'un rabi na kan wayarshi,yayin da asma'un ta tattara dukka nutsuwarta da idanunta a kansa,sallama tayi ta dire sannan tace
"Ina yini" kai ya daga ya dubeta sannan ya maida kan wayar kafin ya amsa,juyawa tayi tana qoqarin wucewa
"Sai yanzu kika ga damar kawo wa?..." Ta fadi da saigar tambaya,tsaiwa kawai tayi ba tare data amsa kota ce wani abu ba,tsaki ta saki sannan tace
"Me kika tsaya kuma yi....aisaiki wuce ko malama" nan bata tanka ta ba ta juya tabar wajen,halayen asma'un ba baqo bane wajenta,koma waye tana iya masa haka idan taso,abu daya ta sani kome mutanen gidan suke mata suna da qima a idanunta,na farko koba komai sun riqeta suna zaune da ita,ta samu ingantuwar rayuwarta wadda abaya bata zaceta ba bakuma ta tsammaci samunta ba,na biyu kuma girma da qimar daddy ya shafe komai,ya danne duk wani abu da za'a mata,karamcinsa a gunta ba abune mai yiwuwa a manta da shi ba.




Ciki ta koma kawai tayiwa mommy sallama ta amsa mata,tana shirin juyawa zata fita a falon sukayi karo da ahmad dan gidan hajiya laraba,murmushi ya sakar mata itama saita maida masa tana matsawa gefe
"Ina zuwa haka da wannan yammacin?"
"Ina yini" ta zabi gaidashi maimakon amsa mishi tambayarsa
"Mu qarasa ciki saimu gaisa ko?....ko zan bata miki lokaci?" Ba haka taso ba,amma sai ta kada kanta kawai tana juyawa zuwa cikin.




Da fara'a mommy ta tarbeshi,aysha na gefe ta gaidashi sannan ta miqe
"Shiga ciki ki samo masa wani abun" cewar mummy,duk da cewa ko cikin kitchen din akwai masu aiki dake aikin abincin dare.




Miqewa yayi ya soma yiwa mummy sallama sanda aysha ta sake ficewa da niyyar tafiya
"Saurin me kike haka ina zuwa?" Tajishi daga bayanta yana fadi,ahmad ne,murmusawa kadan tayi tana noqewa baya kadan saboda qarasowa da yayi yana niyyar jerawa da ita
"Zani dubiyar wata qawata ne" ta amsa masa
"Ohk...muje na saukeki mana" kai ta kada
"A'ah...na gode....zan qarasa na hau napep"
"Amma ina duka drivers din gidan?,bansan gidan nan ana hawa abun haya ba..."
"Wataqila basa nan"ta fada cikin zaquwar ya tsaya daga nan,don sun kusa isa wajen aje motoci,ga asma'u data hango daga nesa idanunta na kansu
"Fine....tunda wataqila basa nan muje ni na saukeki"
"Allah ka barshi"
"Bakison na samu ladar gaida mara lafiya kenan?"
"A'ah ai....."
"Indai ba haka bane muje na kaiki" ya katseta,batasan me kuma zata sake ce masa ba,hakan ya sanya tilas ta bishi wajen motarshi.




Tana gefen sit din driver amma jinta take a matuqar takure ,jinta take kamar wadda ta aikata babban zunubi,kanta na qasa ta jiyoshi yana cewa
"Malama aysha....ya makaranta ya kuma samari?" Banbarakwai ta ji maganar,itakam tsahon rayuwarta ba zata iya tuna wani qwaqwaqwaran saurayi data taba yi ba,tun tana qauye zuwa yanzu,dama makarantar yace dai,kusan yanzu bata da wani abu da ya wuce makarantar a wajenta
"Ya kika yi shuru?" Ya sake tambayarta yana kallonta kafin ya dauke kai
"Makaranta alhmdlh" ta fada tana sauke boyayyar ajiyar zuciya
"Ma sha Allah,samarin fa?" Ya fada yana murmushi
"Hmmmm" kawai tace
"Hmm...kardai kice min babu?" Ya fada cikin sigar zolaya,gaba daya a takure take,sam batason maganar,jinta take kaman ta girmi kanta,bata ma da muhalli ko gurbi sam a rayuwarta ta yanzu,buri gareta na karatu mai zurfi,wanda zai zameta qaqqarfar garkuwa da zata tare duk wani abu mai cutarwa daka iya ci gaba da kawowa rayuwarta farmaki
"Idan har da gaske ne babun?...me zai hana ni a bani dama na shiga layi kuma mutum na farko ko?"shiru tayi tana jin zuciyarta na bugawa,kaman yaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login