Showing 72001 words to 75000 words out of 184891 words

Chapter 25 - DAURIN BOYE Complete Document by Safiya Abdullahi Huguma.txt

soma yada qaryar.




Kuka take sosai,tana sake tilawar labarin cikin kwanyarta daya bayan daya,tana fidda kuskuren kowan kowa a ciki,sosai tsoron maza ya kamata,firgici lokaci guda ya shigeta,tana ganin wautarta da kuskurenta na aminta da zama da ahalin khalipha,da wanne ido zasu dauketa wanne kallo zasuyi mata,ashe tabon dake cikin rayuwarta ya wuce iya yanda ita take tunani?.




Sai data ci kukanta sosai ba wanda ya tsaidata a cikinsu,domin dukkaninsu sunsan ba abu bane mai sauqi kashe irin wannan wutar,ba kuma qaramin al'amari bane gyara barnar da tayi shekara da shekaru da afkuwa ko ace tana afkuwa ma,a hankali ta dinga baiwa kanta baki,ta dinga qoqarin tsaida hawayenta,da kumburarrun jajayen idanunta ta dubi gwaggo asabe
"Na gode qwarai gwaggo,na gode da fidda ni da kikayi daga duhu xuwa haske,na gode da kika budemin abinda na jima ina neman sani a kai,na gode da kika kwancemin DAURIN BOYE" tana kaiwa nan ta miqe ta shiga bandaki,alwalar sallar magariba ta daura wadda ta gabato sannan ta fito ta soma shirin salla
"Kici daga da addu'a indo...komai mai wucewa ne da yardar Allah" cewar mero dake duban aysha cike da tausayi,murmushi mai ciwo wanda kai tsaye za'a iya kiranshi dana yaqe ta saki sannan tace
"Na sani mero...kuma ina fata wataran hakan ya zama tarihi"
"Amin ya Allah" ta fada itama tana shiga bandakin don daura alwalar.




Tana saman abun sallarta bayan ta idar,tunaninta ya rarrabu kashi kashi,daga nan inda take tana iya jiyo hayaniyar 'yan biki wadanda ke shirin tafiya dinner din asma'u,wayarta da tayi qara ita ta yanke tunaninta,ta waiwaya ta jawota sannan ta daga ta kara a kunneta,aliya ce tayi sallama cikin tsokana,wannan karon ranta cunkushe yake shi yasa bata samu damar maida mata ba
"Gobe ne tafiya qauyen ko?" Aliyan ta tambayeta bayan sun gama gaisawa
"Ke da kika ce ba zaki ba?....." Ayshan ta tambayeta a sanyaye
"Haba sashen,ko mafarki kikayi nace haka zaki yarda?....wasa nake miki...ko ramin kurege kika shiga ai naa shiga,haushi kika bani da kika qi yarda ko dan jan lalle ayi miki,na rasa wacce iriyar amarya ce haka?"
"Ta buzuzu mana..." Ta bata amsa qaramin murmushi na subucewa daga kan lebanta,sanadiyyar tuna aurenta na fari da tayi,wanda ko wankan arziqi bata yi ba randa za'a kaita bare a kai ga wani gyaran jiki da lalle,gwara wannan ta samu gyaran jiki yadda ya kamata,lallen ma itace bata so ba,jin abinda ayshan ta fada yasa aliya bushewa da dariya
"Au dariya ma kike?.....ni son ganinki ma nake fa akwai maganar da zamuyi"
"Har kin sani zumudi....Allah yasa ta samu" karyar da kai ayshan kawai tayi tana tuna yadda al'amrin ya kasance,tana tuna ayanzu waye khalipha na ainihi...hakan ba qaramin fadar mata da gaba yake ba
"Ko na taho yanzu?" Aliya ta katse mata tunaninta ta hanyar tambayarta
"A'ah....ki barshi kawai...ki bari ma tattauna gobe idan zamu wuce takai"
"To Allah ya kaimu"
"Amin....ki gaida mama"
"Zataji wlh...ai ran daurin aure tare zasu taho takai din da abba"
"Kice mata karta wahalar da kanta...ba komai ma za'ayi ba acan din,kawai nima dai inason asan asalina da tushena...kuma nima na jaddawa kaina wace ni...kar duniya ta rudeni"
"Koke ba zakiyi komai ba mu zamuyi malama....sai da safe" ta fadi tana katse wayar,itama aje wayar tayi,batasan wani matsayi zata baiwa aliyar ba,batasan wanne irin qauna take mata ba,tasani kawai Allah shi ya hada qaunarsu,ba wai don tana da wani abu da za'a qaunaceta ko a sota dominshi ba.




Bata bar kan abun sallar ba sai datayi isha'i,zuwa sannan hayaniyar gidan ta ragu saboda 'yan biki yawancinsu sun tafi sai dai daiku,jifa jifa mero na janta da hira don ta saki jiki tana kuma hada musu kayansu da zasu juya gobe da safe,anty safiyya ce ta shigo da sallama dakin,fuskarta qunshe da fara'a cikin ankon lace wanda sukayi iya su hudu 'ya'yan mummy yayyen amarya,tayi kyau sosai kasancewarta gwanar ado ce da kwalliya,duban aysha tayi tadan bata fuska
"Haba aysha...ya na ganki zaune kuma?,dinner din fa,kowa fa ya wuce iya mu mukai saura" murmushi ta dan saki,ina ita ina wannan waje?,ko giyar wake aka bata tasha ai ta wartsake
"Bana dan jin dadi ne sosai anty....bazan iya zuwa ba...afwa don Allah"
"Ayyah me ya sameki?"
"Dan ciwon kai ne kadan...amma na sha magani ma nasan zai sauka in sha Allahu"
"Sannu Allah ya sawwaqe yasa kaffara...kin kusa tafiya gidanki ki huta baki daya in sha Allah....amma ki miqe ki daure ki saka kayan da akace zaku saka yau din saboda masu shigowa" dan tunani ta shiga kadan wanda tuni har anty safiyya ta dagota
"Karki cemin cikin kayan da daddy yayi muku ba'a kawo miki komai ba?...." Shuru ita dai tayi ba tare data amsa ba,juyawa tayi fuuu zata fice,da sauri ayshan ta cafko hannunta,tayi narai narai da fuska idanunta sukai qwalqwal kamar zata fidda hawaye,dama har yanzu zuciyar a karye take
"Don Allah anty safiyya ki bar zancan nan karki tada komai....kinga dai yau duka abubuwan da suka dinga faruwa...karki silar tashin wani abu kuma,kiyi haquri" cikin sanyin jiki take duban ayshan,tana da sanyin rai da kyakkyawar zuciya,tana da nagarta da dattako,tana mata kaykkyawan fatan tayi dace da abokin rayuwa mai irin halayenta
"Shikenan aysha..ubangiji yayi miki kyakkyawan sakamako....yasa kin dace har abada"
"Amin amin anty safiya" cewar mero,bata sake cewa komai ba ta juya ta fita ranta sam babu dadi,bata jin dadin wasu daga cikin halayen mummyn dana 'yan uwanta,batasan meye laifin yarinyar ba,bata da wani mummunan hali qwaya daya tak,kawai don Allah ya yita cikin jinsin talakawa?,kawai don Allah ya sallada zata zauna qasansu taci arziqin da basu suka baiwa kansu ba,Allah ne ya ara musu donsu tallafi bayinsa mabuqata,gashi cikin ikonsa da buwayarsa ya soma yi mata baiwa da kyauta daga cikin ni'imominsa,tana fatan nagartacce ne wanda zata huta ta manta dukkan wata wahala ta rayuwarta.
*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*




*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_


*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_


*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_


*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_


*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_


*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300




*DB*


27


*Dimbin godiya a gareku masoyan da basu manta halacci da alkhairi*πŸ™πŸ½πŸ™πŸ½πŸ™πŸ½


_Alhamdulillah,wato haka rayuwa take,a duk sanda ka dage kan ka karya wani ko kaga bayanshi matuqar Allah na tare da shi aikin banza kake,matuqar zuciyarsa a tsarkake take zaiyi wuya kaci galaba a kanshi,koda dukka mutanen duniya aljanu da bil'adama masu taimaka maka ne wajen ganin durqushewar wani,a sanda ake fafutukar fidda litattafanmu kota halin qaqa,sai hakan ya zame mana tamkar wata silar alkhairi a garemu,a lokacin ne wasu jama'a ke ninka farashin da muka sanyawa kowanne littafi namu ninkin baninkin su sayeshi a haka saboda sanin daraja da mutuntuka,da kuma zuciyar da bata manta alkhairin mu a garesu a baya,DUKKAN GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MADAUKAKIN SARKI_














Qarfe sha daya na dare ta fita da kwanukan da su baba asabe suka ci abinci,ta bari ne zuwa sannan tana zaton ba kowa falon,idan ma sun dawo daga wajen dinner din tana tsammanin kowa ya tafi makwancinsa,ganin yadda kitchen din yake a hautsine sai ta kasa tafiya ta barshi haka,ta tsaya tana kikkintsa shi tare da gyara abinda zai gyaru a sannan tunda dare ya riga yayi.




A haka lantana daya daga cikin masu aikin gidan ta shigo ta tadda ta
"Lallai indo a gaisheki da qoqari,amarya guda da gyaran kitchen?,lallai" ta fada tana kama habarta alamar mamaki,da murmushi a fuskar aysha ta juyo ta kalli lantanar
"Banda abinki lantana wannan kitchen haka komai a hautsine,ta yaya zakuji dadin yin aikin?" Baki ta dan tabe tana aje farantan hannunta
"Wallahi gajiya nahi aisha....tun safe kana tsaye...ka gyara a bata,kowa kuma da kiran da zai maka....dama kuma kece mai juriyar,nikam nayi iya yina na gaji"
"Allah ya rufa asiri"
"Amin....ai gwara kiyi mana ma na bankwana,zamuyi kewarki wallahi indo" inji lantana tana nuna alhininta a fuskarta zuwa zuciya,sun saba da ayshan saboda sauqin kanta,hakanan sau tari takan amshe ayyukansu tayi idan tana da lokaci,ba ruwanta da qyamar mutum ko girman kai,ba kamar asma'u ba da basu taba jin dadinta ba,ayshan bata ce komai ba sai murmushi da tayi,wanda banda lotsawar da kumatunta yayi ma ba zaka gane hakan ba,kama mata lantanar tayi suka soma gyaran tare.




Basufi mintuna goma ba suka soma jiyo tashin hayaniya daga falon gidan,a hankali muryar anty safiyya tafi ta kowa fitowa
"Mu zasu nunawa iskancin banza iskancin wofi...mu zasu nunawa arziqi?,dama tun ranar kamu nake kula da take takensu,kai tun ranar kawo kaya,ina ruwanmu da wani familynsu ko arziqinsu,abinda muka sani kawai shine mun basu auren 'yar uwarmu,hakanan muma ba'a talauce suka ganmu ba bare suyi mana dagawa" ta qarashe fada tana huci
"Ke kinga yadda suke wani daddaga hanci da kallon kowa d'ai d'ai kamar kansu aka fara kudi,kina fa gani da muka shiga yiwa ango da amarya liqi sauka sukayi daga kan stage dinfa...." Anty kubra ta fada cikin jin haushi itama
"Su taka a hankali mi tsaf zan kora musu jawabi wallahi...ai muma ba tsiya suka ga tana binmu ko?....koma tsiyar ce a haka dansu yaga yarmu yace yana son aure" anty hajja wadda take qanwace ga momy ita ke binta ta fada.




"Kowa ya sayi rariya ai yasan zata zubda ruwa....tun daga yanayin halayyar yaron ya kamata su gane kowanne tsuntsu kukan gidansu yakeyi,don dai kai kawai baka isa ka fada bane baka da ikon gin magana" lantana ta fada,itadai aysha bata ce komai ba,tunda ba huruminta bane,har suka kammala ta wanke hannunta ta yiwa lantana sallama ta juya tabar kitchen din.




A kacame ta tadda falon,asma'u na kumfar baki anty safiyya nayi,da alama wani abun ne ya sake faruwa,tana jin anty safiyya na cewa
"Nikam babu matar data isa na sake jera kafada da ita bare ta wulaqantani bayan Allah bai wulaqantani ba,kije ku qarata ke dasu ke kika zabarwa kanki...banda shi mara mutunci ne har yace ki baiwa yan uwansa haquri sannan ya saurareki?" Cikin kuka asma'u tace
"Kinji ko mummy....wallahi ki mata magana,kinga zata jawo min matsala ko....nasan halin hamid wlh tsaf zai tsiri fushi da ni qarshenta ma sai wani satin za'a qarasa wani abun...nidai ki mata magana kawai"
"Ai na haifu,kuma 'yar halak ce ni...kije Allah ya bada sa'a" anty safiyya ta fada tana barin falon,ta haura sama dakin da suka sauka ita da sauran 'yan uwanta.




"Maganar gaskiya asma'u nima fa naji haushi...kuma hamid ya bani mamaki...ban zaci haka yake babu kwalli a idanunsa ba,giyar kudi na dibansa kenan?" Cewar anty kubra wadda sakuwa ce ta asma'un
"Kinga don Allah bana son qananun maganganu,nice dai zan aureshi na zauna da su,kuma naji ina son abina a haka ko yaya yake tunda shima yana sona" ta fadi cikin fada tana tasowa kubrar kamar zata doketa
"Allah ya bada sa'a" itama ta fada tana barin wajen,sai asma'un ta fada jikin mummy tana rushewa da kuka,duk sun hada mata zafi,gaba daya bikin yana neman juye mata,yaqi zuwa mata a dadin rai yadda taso,ga wannan tirka tirka da takeao ta kunno kai tsakanin dangin hamid din da nata,gefe guda kuma maganar aysha har yau na cin ranta,ba kamar yauma da take sake tambayar hamid waye muhammad abdulhakim mai goron,a yadda yake gaya mata waye shi ta tsorata matuqa,tana tsoron faruwar wani anu,tana tsoron kada reshe ya juye da mujiya,batason abinda zai sanya ta kasance itace a qasa har abada,koda yaushe tafison taga itace a sama sama da kowa.




🧢🧢🧢🧢🧢🧢🧢🧢




Qarfe goma na safiyar washegari suka kammala shirinsu na wucewa takai,a sannan har aliya itama ta iso,ta ishi aysha da tambaya kan maganar data ce zasuyi,murmushi tayi kawai tace
"Me kike ci na baka na zuba?,zamuyi ai".




Sallamar lantana ita taja hankalinsu
"wani ne a waje yake jira wai an turoshi zai kaiku takai" cikin mamaki aysha ke kallon lanta
"Mu kuma?...takai?" Ta fada tana tunanin waye haka zai aiko?,iya tunaninta bata gane ko waye zai mata wannan karamcin ba,hakan yasa dole ya zira hijabinta tace
"Zo muje aliya inga ko waye" suka fice daga dakin.




Tun daga nesa ta gane baquwar mota ce ba irin ta gidansu ba,saidai bata iya ganin waye a ciki har ta qarasa gaban motar ta tsaya,murfin motar ne ya bude,wani matashin dan kimanin shekaru arba'in ya fito,cikin girmamawa yace
"Ranki ya dade boss ne ya aiko ni....ina fatan kun kammala shiryawa"
"Wanne boss?" Murmushi yayi sannan yace
"Wanne boss ne bayan muhammad khalipha?" Hannunta ta daga
"Ohk....ka koma kawai,zamu bi motar haya" ta fadi tana kama hannun aliyar dake binta da kallon tambaya suka juya.




Tana gab da shiga falon wayarta ta dauki ruri,dubawa tayi K ce ta bayyana kamar yadda tayi serving number dinsa




Numfashi ta aje sannan ta daga wayar ta kara a kunneta
"Me ya faru tsakaninki da sani,yace min wai ance ya tafi"
"Bbu komai,zamu bi motar haya ne kawai...."
"Bai dace ba aysha...maida hannun alkhairi baya fa kenan?"aliyata fada tana tsaye daga gefanta
"Aliya....kin san waye?"ta fada tana kallon hanya ba tare data dubi aliyan ba
"a'ah"ta bata amsa tana girgiza kanta dukka idanunta da hankalinta na kan ayshan
" khalipha ne fa aliya,wanda zan aura"
"Arrrrrrhhhhh" aliya ta fada tana rufe bakinta da tafukan hannayenta duka biyun kamar mai maitsoron kar wani yaji ihunta,idanunta a waje hakanan fuskarta qunshe da murmushi
"How comes sashen....tell me pls" juyowa tayi tana duban aliya,hannayenta harde a qirjinta,fuskarta a hade tsaf
"Khalipha ya saka min shakku mai yawa a kansa aliya....ta yaya zaizo min da wata fuska?,ta yaya zaizo min da wata siga?....a yadda khalipha yazo min aliya ashe ba haka bane....wannan ba yaudara bane?"
"Ya salam.....haba...ni nasan kaman na taba sanin face dinshi a wani waje wlh...kaman ya taba zuwa wajen abba na...oh my god...ina zuwa" aliya ta fada tana zame hannunta daga riqon data yiwa aysha,da sauri sauri kaman wadda zata tashi sama ta koma qofar gida,da idanu aysha take kallonta tana mamakin saurin me take ina zata?,me yasa bata ga alamun jimami ko tayata bacin rai kan abinda khaliphan ya aikata ba?.




Tana nan tsaye kaman sakarya har aliyan ta dawo fuskarta washe da fara'a ta kama hannun aysha ta jata zuwa ciki,a parlour suka ga asma'u zaune sanye da kayan bacci,kaman ko yaushe tana saqale da earpiece a kunnenta da alamu ma waya take,harara ta danqara musu wadda kowaccensu ta ganta,wata fara'a ta musamman aliya ta qirqira tana sake riqe hannun aysha sosai tana cewa
"Kinsan me goro family kuwa aysha?....ai ke Allah ne ya tarfawa garinki nono,dare daya dama Allah kanyi bature..." Ta qarashe fada suna tura qofar dakin ayshan suka shige,hannunta aysha ta cire bayan sun shiga din tana kallon aliya gami da kallon qofar dakin nata kaman wani zai shigo,dariya aliya ta bushe da shi har tana duqawa kadan
"Banson fitina aliya kin sani ko?" Ayshan ta fada a narke kamar mai shirin sanya kuka,bata tanka mata ba sai taja hannunta zuwa bakin gadon ayshan ta zaunar da su a tare sannan ta kalli gwaggo asabe
"Gwaggo kiyiwa aysha fada taiwa kanta fada...mijin da Allah ya bata da don jama'a da dama ne ba zata sameshi ba,bama shi ba gwaggo ko mai gadin gidansa ba zasu yarda ta aura ba....duk bata duba haka ba zata tsaya tana wani goce goce maras tushe ko dalili?,khalipha kaman wani tsanin ki ne na fita daga tsangwamar da kika dade kina fuskanta tsahon rayuwarki,Allah ya sani baki ma sanshi ba bare kiyi kwadayin abun hannunshi koda jama'a zasu fadi hakan,ke kinfi kowa sanin kanki,kinfi kowa sanin wacece ke" ta fada tana duban idanun ayshan kai tsaye sannan ta dafa kafadarta
"So pls aysha....ki nutsu ki fuskanci gabanki kawai...." Ta fadi tana sauke hannunta sannan ta cewa su gwaggo
"Ku shirya da sauri gwaggo....angon ya turo driver shi zai kaimu har qofar gida"
"To ma sha Allahu....kinga mun huta hawa ta haya kuwa" gwaggwon ta fada cikin farinciki,sannan daga bisani tayiwa ayshan dan fada da jan hankali,itakam kawai tana zaune tana jinsu,amma harga Allah tana da fargaba...su asma'u kawai sun isheta isharar tsamiyar talaka da mai kudi bata jiquwa waje daya...masu kudi basa qaunar talaka sam,kansu suke so,isu isu suke mu'amala da junansu,amma koma meye ta miqawa Allah zabinta.




Tana zaune waje daya kawai tunda ta gama nata shirin tana binsu da ido wayarta ta dauki qara,ta duba batasan number ba sai ta daga ta kara a kunneta tayi shuru ba tare data ce komai ba taji waye
"Assalamu alaikum warahmatullah" ta jiyo muryar wata mace dattijuwa,cikin mamaki ta amsa sallamar tana son taji wace
"Ina fata aishatu ce" a ladabce ta amsa saboda yadda muryar ke nuna shekarun mai maganar
"To ma sha Allah....me ya faru na saka khalipha ya turo muku driver ya kaiku,sai naji yana waya da driver yana gaya masa ya dawo kawai?" A take ta gane wace,anni ce duk da cewa baifi sai biyu ta taba jin sunanta daga bakinsa ba,diriricewa tayi gami da tsorata kamar wadda ta yiwa sarko qarya har hakan ya bayyana saman fuskarta,aliya dake gefe wadda ke jin duk abinda ke faruwa saita amshi wayar,gaisawa sukayi sannan tace
"Qawar aysha ce,bamu gane waye ya turoshi ba sai daga bisani....amma yanzun haka ma gab muke da gama shiryawa mu wuce"
"To madalla...na zaci daga khalipha ne...Allah ya tsare hanya...a gaida mutanen gidan"
"Amin zasu ji,mun gode" daga haka ta katse wayar itama aliyan ta sauke tana murmushi qasa qasa,hannu ta saka ta daki bayan ayshan
"Saikin biyani ladan yin lauya....haka zakije ki dinga musu wannan sanyin naki da tsoro?...uwar mijinki ce fa ta kira" idanu aysha ta zaro tana duban aliya
"Ke...uwar mijin wa?...mamana zaki ce,a matsayin yayana yake ni da shi babu zancan miji da mata" idanu aliya ta saka tana kallon ayshan,sai kuma tayi turus ayshan tana duban dakin,Allah yasa su biyu ne su gwaggo sun soma fita da kayansu ana kaiwa mota
"Kaman yaya ban gane ba,yimin bayani...."
"Share kawai" ta fada tana miqewa gami da saba jakarta a kafada,itama aliyan tashi tayi tana rataya tata
"Wallahi baki isa ba yarinya kinyi kadan,tunda kika fara fada dole ki fada duka" murmushi tayi tayi gaba...itama tasan hakanne,ba wani boye boye tsakaninsu,idan ta boye dinma tana da wanda zata gayawa ne daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login