Showing 24001 words to 27000 words out of 85627 words

Chapter 9 - MUSAYAR ZUCIYA COMPLETE BOOK by Hajja Ce.txt

Hajja Ce   

14 Sep 2025

39

ma yayi kyau mutumina, toh Ina Shi Abubakar d'in."

"Yana Spain sun rik'esa amma nan da one month zai shigo k'asar insha Allahu."

"Ahh lallai kaji manya toh Allah ya dawo dashi lafiya muna murna."

"Toh Shamsu godiya yake bari na gudu nima ka kular min da mata."

"hmmm harta zama makenan, Allah ya kiyaye hanya a gaida mutanan gidan."

Suka yi sallama Sadeeq ya tafi, tun daga lokacin indai yana kano toh zaije gidan su Fateema idan baya nan suna mak'ale da waya ta hanyar shamsu domin babanta yaki yadda ta rik'e waya sai ta fara karatu. Sun shaku sosai fateema na sanshi shima yana sonta alkairi kuwa duk zuwa da abinda zai kaimata.

Doctor Abubakar Salman Harun, matashin saurayi mai tak'ama da kyau da ilimi nagarta da wayewa ya zama babban likita wanda duniya ta sanshi take kuma tak'ama dashi. Tun bayan gama karatun sa da shekara biyu a, k'asar Spain suka rik'esa domin suma ya ceto al-ummar su ta hanyar kwarewarsa, yana gudanar da aikin cikin walwala da jin dad'i duk da cewa tunda yabar k'asar tunanin INdo be ta6a gushewa daga cikin al'amransa ba, ya sakawa ransa cewar Allah ne zai bashi INdo bawai wani abun nasaba hakan yasa ya kwantar da hankalinsa yacigaba da karatunsa cikin nutsuwa da sadaukarwa rayuwarsa akan Al-ummah.

Ganin yak'i dawowa ne hakan yasa mahaifinsa ya umarce sa da yadawo gida domin taimakawa 'yan uwansa 'yan Nigeria, bai k'i tayin mahaifin nasa ba saboda shima bak'aramin missing d'in gidan yayi ba. Ga wasu mafarkai dayake yi game da INdo da yake kusan kullum yana son ya ganta yana kaunar sake had'uwa da ita. Hakan yasa yayi niyar komawa gida bayan yayi wa asibitin *CANTABRIA HOSPITAL* bankwana. ba suji dad'in barinsa aiki ba aman sun bashi damar duk lokacin da yake da buk'atar dawowa suna maraba a kowane lokaci..

Wednesday morning at 8:30am cikin airport d'in malam Aminu kano matashin saurayin mai shekaru 32 ya sakko daga cikin jirgin Nigerian airlines. Sanye yake cikin wasu dakakkun suit coffee color sai ta cikin white da cover shoe gashin kansa a saisaye bakikk'irn ya gyara kyakyawan sajansa sai wanda ya ganshi zai iya tantacce d'an wace k'asar ne.

Sadeeq ne ya fara ganinsa dan haka shi yafara k'arasawa wajan cikin fara'a suka rungume junansu. Abba ma ya karasa Abubakar yayi saurin tsugunnawa yana mik'a gaisuwa mutanen gurin sai kallonsu ake, zuciyar Abba tayi fari ganin yadda 'ya'yan nasa suke bashi respect aduk inda suka had'u.

"Welcome twinnie am glad to see you sai daifa yanzu bama kama kazama bature."

Cewar Sadeeq suna tafiya ajere, Abubakar yayi dariya har suka k'arasa cikin mota suna tsokanar junansu. Kwanansa d'aya da dawowa batare da kowa ya sani ba yatafi Sumaila kauyen sani, ba laifi anyiwa kauyan sauye-sauye ya nufi gidan malam Hamza direct cikin ikon Allah kuma ya sameshi a k'ofar gida bayan ya tambaya annuna masa shi.

Bayan sun gaisa ne shi duk a tunaninsa malam Sadeeq ne shi kuma Abubakar be nuna bashi bane ya kalli malam Hamza yace.

"Malam INdo kuwa ta dawo?!"

Malam Hamza ya kad'a kai cikin takaici yace "Ai malam Saddiqu uwata dai k'arfi da yaji ta gujemu, k'iri-k'iri tak'i dawowa, harma gidan su yaron dazata aura acan sayen sun aiko mun kuma bashi dan idan ba haka bama uwata ba dawowa zatayi ba. Wallahi har zuwa nayi da kaina nace mata kabar garin amma tak'i yadda mudawo."

K'irjin Abubakar ya buga jin cewar an aiko, cikin d'imuwa yace.

"Malam wane kauye ta tafi ne? Nidai wallahi inason ganin yarinyar nan tasamu Ilimi koyaya ne, idan babu damuwa kuma ka yadda dani kagaya min kauyan da INdo taje na dawo da ita zan samar mata da rayuwa mai inganci da ikon Allah nidai burina ka yadda dani."

"Toh malam Saddiqu na yadda amma dasharad'in sai munje mun sanarwa dame unguwa, shima yasani da kuma aminina malam 'Dalha.."

"Hakan ma dai-dai ne Malam na gode." Hannu yasa ya ciro kud'i duba ashirin ya mik'awa malam Hamza ya kar6a yana ta godiya tamkar zai mai ruku'u sannan yace suje gidan me unguwar. Suna zuwa aka yi komai sannan suka koma gida Abubakar suka gaida Inna bayan sun kwatanta mai kauyan sayen ya koma gida cike da murna.

Da dare suna zaune a d'aki Abubakar ya kalli Sadeeq yace.

"M twinnie zaka min rakiya gobe dan Allah."

"Zuwa Ina kuma daga dawowarka?!"

Cewar Sadeeq Abubakar yayi dariya tare da cewa.

"Wani guri zamuje wajan k'arfe 12:00pm."

"Allah ya kaimu tunda gurin bashi da nisa, kasan dai Qibd'iyya tayi aure ka yaudare ta."

"A'ah twinnie Allah ne beyi ba." Suka cigaba da hirarsu gwanin ban sha'wa.

Washe gari suka d'auki hanyar zuwa saye cikin suit d'insu iri d'aya da Abubakar ya taho musu dashi. Tafiya suke tun Sadeeq yana kawaici harya fara magana.

"M twinnie wai ko katsina zamu je ne naga mun wuce dawanau..?!"

Abubakar yayi murmushi sannan yace "A'a kaidai zuba ido kayi kallo."

Cigaba sukayi da tafiya har suka d'auki hanyar saye Sadeeq dai yayi shiru idan ya gaji sai ya kira Fateema har yaga sun fara shiga daji da kewaye mugayen ramuka ya kuma yin magana.

"M twinnine ko kafara sana'ar yankan kai shine zaka fara takaina?!"

Abubakar ya kyalkyale da dariya tare da cewa.

"A'a ban faraba zuciyata nazo d'auka a garin."

"Tofa.. Waye zuciyar take twinnie??"

Abubakar yace "Aishat Hamza,what I mean is INdo malam Hamza."

"What.........???!"


_Kuyi hakuri da wannan wallahi unguwa naje amma duk da haka saida nayi muku. Ina godiya a gareku masoya._











*HAJJA CE*👈
[7/1, 7:39 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
                    ♥
                  ♥♥
         A true life story

Na

*K.A.S Precious Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu.

*VOTE me on wattpad @Hajjac*


_page 13 na kune 'yan candidate d'in government girl secondary school Kwah, hope zakuji dad'in shi sannan kuma ina muku fatan alkairi a cikin rayuwarku kamar yadda kuke bin labarin nan_💍


Page *13*

"Amman dai baka min adalci ba kasani ko m twinnie? A k'a'ida yau zanje gidan su fatma sabida gobe nakeson wucewa amma kayi min haka, wallahi danasan gurin wannan wayuwayar zamuzo bazan rakoka ba”mtww

"Sanin idan na gaya maka bazaka yadda ba yasani k'in gaya maka sabida ina son muzo tare dakai."

Sadeeq yayi mai banza har suka shiga cikin rugar fulanin, suna zuwa suka ga 'yan mata yara da manya sunzo zasu wuce. Ra6awa Abubakar yayi da motar gefe kasan cewar bazata wuce canciki ba sannan suka fito Sadeeq sai faman cin uban magani yake yi idonsa sanye cikin dark shade shi kuma Abubakar d'an siriri ne nashi fari kal kamar k'ank'ara.

Suna fitowa INdo dake tsakiyar 'yan matan zasu tafi kasuwar badume tana ganinsu ta ganesu cikin karad'i tace.

"Jakar uban nan,sun biyo ni masifaffun malamn nan." Kallon sauran abokan tafiyarta ta tayi tana gyara mayafinta tace.

"Kowa ya samu sanda zamu k'arasa wajan wad'an can malaman, kawai danace muku kulle kukuma sai ku jibgesu."

Suka ce toh kowa ya juya ya samu sanda harda ita sannan suka nufi gurin suma su Abubakar lokacin sun k'araso ciki sam basu ganeta ba sabida tayi girma ta zama 'yan mata, lokacin da ta baro sani tana 12years yanzu kuma tana 15years gashi tayi 'yar k'iba ta kuma canza. Abubakar shine ya taresu yana kallansu yace.

"K'annena dan Allah muna neman gidan da INdo malam Hamza take, wadda tazo daga kauyen sani."

Caraf ta cafe bayan ta rik'e kugu tace, "ga wata nan lafiya kuka zo inda nake..?!" Duk suka zuba mata ido Sadeeq dariya da takaici suka kusan kamashi ya kalleta kallo irinna raini sannan ya juya zai koma cikin mota yaji tace.

"Wannene kaid'in dacta Habubakar ko kuma malam Sadeeq? Na ganeku rasai."

Ko waigowa beyi ba sabida haushi ita kuma ta kalli Abubakar dake tsaye yana kallonta, sam bega wani aibu a tattare da ita ba yaji zuciyarsa ta sanyaya yanajin tamkar ya rungumeta amma bahali gashi ya gansu da sandina kuma su ba shanu a taredasu bareyayi tunanin cewar kiwo zasuje. Cikin sanyin murya yace. "Humaira inason muyi magana dake, naje munyi magana da mahaifinki sauran ke."

"Allahu akubar kabiran, malam Sadeeq ni ba'a renamin hankali wallahi nan garin yanzu sai nasa su rakaku da duka wallahi."

Ido ya zaro jin abinda take cewa ya fara bin hannayen yaran tare da tuna wata kalma ta bahaushe da yake cewa sarkin yawa yafi sarkin k'arfi, ya d'an kalleta cikin ransa yana tunano ko harsai yaushe ne zata yi hankali. Ya rasa ya zaiyi da su sai yayi murmushi tare da zura hannu cikin suit d'insa ya zaro wallet suka bishi da kallo ya ciro 2k ya mik'awa wata yarinya yace ga wannan kusha alawa.

Kallon kud'in suka yi sai kuma sukayi baya-baya suna zaro idanuwa, ganin dalla-dallan kud'i yasa INdo tayi saurin k'arasawa zata fisge Abubakar yayi saurin janye hannunsa tare da kad'a mata kai yace.

"A'a wannan ba naki bane, naki yana gurin Sadeeq sai kin yadda da abinda zan gaya miki sannan zamu baki su suna can dubu ashirin."

INdo ta dafe k'irji tare da jan baya tace, "Dubu ahirin? Toh kaine dacta Habubakar kenan, meyasa kabari aka bawa malam Sadeeq kud'ina kuma alhalin mugune ba bani zai yi ba..?!"

"Zai baki amma sai kin yadda da maganar da zamu gaya miki."

Tana jin haka tace "kaltume ku kar6i kud'inku, kuyi gaba zan taho daga baya idan na kar6i kud'ina."

Kar6a suka yi sannan suka tafi ita kuma ta yarda icen hannunta tare da goge hannun jikin zaninta, shi kuma sai kallanta yake yi, sam ya rasa abinda ya gani a jikinta yaji zuciyarsa na azabtar dashi, yace.

"Toh kinga wani dutse can muje mu zauna in gaya miki abinda muka zo sanar miki."

Ba musu suka tafi sai juyawa take tana kallon Sadeeq a cikin motar, suna zuwa Abubakar ya zauna ita kuma ta tsaya yace.

"Humaira zauna mana."

"Karkafa kuma cemin wani humaira hekace wata yarinya e'heee."

"Sunan Mamana gareki shima humairan na fad'a ne sabida babu yadda zanyi, ki zauna kijini dakyau abinda zan sanar miki, idan baki yadda ba zamu d'auki wata yarinyar anan kauyan mu bata kud'in."

Da sauri ta zauna ya kalleta yama rasa ta Ina zai fara mata bayani yadda zata faminta ta gane manufarsa karta yi mai hayaniya. Zare glass d'insa yayi sannan ya kalli fuskarta sai faman wasa take da k'ananun duwatsu yace.

"Humairah kina son yin karatu?"

Kai tsaye INdo tace mai,

"A'a aradu nida zanyi aure."

Abubakar ya kuma kallanta, ganin tayi maganar har cikin ranta yasa shi mik'ewa tsaye yace.

"Eh ai zakiyi auran amma ki gaya min idan kinason yin karatu kema wata ran ki zama kamar matar gwamna ko shugaban k'asa kuma kema wata ran ki amfanar da bayin Allah da kuma 'ya'yanki wanda zaki haifa idan kinyi aure."

Rufe ido tayi da tafin hannunta wai kunya sannan tace.

"Eh toh bank'i ta bakinka ba amma ni bazan yi wani karatu ba haka kurum naje malamai su dinga jibgata ba a'hh jikina bana banza bane, kuma ma yazan yi da auran saleleh tunda shaura 'yan makwanni.."

Mtwww Abubakar yaja tsaki jin ta kira salele cikin d'an 6acin rai yace.

"Waye shi salelen? Me gareshi? Ana son fito dake daga cikin duhun kai kina wani sake dulmiya kanki? Kinga humaira ki yadda yanzu mu koma sumaila dake akwai kayan da na tanadar miki sababbi tindaga kan, atamfofi, shaddoji, materials, mayafai takalma, jakunkuna da kayan kwalliya, amma sai kin yadda zaki bimu mu koma can gidan ku..."

Shiru INdo tayi ta fad'a cikin tunani, kallonta yayi ganin tayi shiru ya fara addu'ar karta ce mai bazata ba murya a raunane yace mata.

"Please Humaira talk to me mana."

Kallansa tayi jin yayi mata turanci tace "sake gaya min abinda ka fad'a yanzu da hausa ko da fulatanci sune yarena."

"Oh cewa nayi kiyi magana mana, inason jin matsa yarki I told you zaki samu komai idan muka maida ke sani."

"Kai dacta habubakar kun saba cewa zaku yi amma ni bakwa bani bare ma kuma malam Sadeeq”hmmmm.

"Humaira wannan karan nine zan d'auki duk wani nauyin abunda kike so, fatana da burina ki yadda mu koma nayi miki alk'awarin yi miki duk abinda kike so indai befi k'arfina ba."

"Harda kayan d'aki idan mun tashi yin aure da salele?!"

Ta tambayesa duk da yaji haushi amma be nuna mata ba sai ma eh daya ce mata.

"Toh kuwa zan biku amma hemunje mun gayawa baba iro dasu yakumbo talatu."

Wani farin ciki ya ziyarci zuciyar Abubakar yace mata.

"Toh muje."

Jerawa suka yi INdo sai d'an tsince-tsince takeyi yana hanata da haka har suka k'arasa. Tun a bak'in k'ofa ta fara k'iran yakambo talatu tafito da d'aurin k'irji tana tambayar.

"Lahiya mai sunan uwa.?"

"Anzo tahiya dani gida, ina lawisa da kande suzo muyi bankwana”

A gindin bishiya Abubakar ya tsaya yana kallon inda suke rayuwa ya kuma tuno cikin garin kano kafin ya tunano garin abuja zuciyarsa ta dira a k'asar Spain. Lallai Allah beyi ko ina dai-dai ba, wannan yafika kaima kafi wani sannan ya furta kalmar "Alhamdulillah."

"Ina wanda yazo tahiya dake d'in, karki ce mini wannan ne?"

"Aradu baba iro shine, d'an uwan malamin mune a sani."

Tabarmar kaba aka shimfid'awa Abubakar ya zauna tare da baba iro k'arin bayani da kuma sanar dashi cewar da izinin malam Hamza yazo d'aukarta. Abinciccika aka kawo mai saidai beci ko d'aya ba sannan baba iro yace.

"Toh gaskiya bazan baku yarinyar nan ku tafi da itaba, hedai muje tare har garin, idan kuma ka yankamu kaida Allah domin hine mesakayya."

Babu gaddama Abubakar ya amince, aka sanar da mutanan gari INdo taje ta harhad'a kayanta akayi mata tsaraba da yawa sannan mutane mata da maza suka tafi raka ta gurin mota.

"Yakumbo dan Allah idan salele ya dawo kice mihi na tafi amma ya dinga zuwa sumaila muna gaisawa kafin bikin mu kinji.?!"

INdo ta fad'a Abubakar dake gaba ya dinga jan tsaki yana jin yadda take k'ara jajjada sak'on da za'a gayawa salele suka k'arasa wajan mota dama tundaga nesa Sadeeq ya hangosu ya dinga kwasar dariya ganin yadda sukayo gungo guda sai tada kura sukeyi, suna zuwa ya had'e rai sukuma mutanen suka dinga fad'in ahe 'yan biyu ne.

INdo da baba iro suka shiga gidan baya sannan Abubakar ya zauna a driver seat Sadeeq na kusa dashi ya data motar suka dinga d'aga musu hannu anayiwa baba iro adawo lafiya. Har suka fito daga surkullen babu me magana sai INdo datake lissafo wad'anda zata yi kewa, suna hawa babban titi iska ta fara hurata ta A.C ta mirgina kai sai bacci har rawar sanyi take yi.

*****
Sani...Suna zuwa har k'ofar gidan malam Hamza suka tsaya baba Iro ya tashi INdo duk ta cika su da munshari wanda hakan be damu Abubakar ba amma Sadeeq iya kuluwa ya kulu, ta bud'e k'ofar da sauri tana fitowa 'yan unguwa suka fara cewa.

"Ga INdo... Ga INdo...!"

Ta bud'e ido tare da kuma mistsike shi tana dariya, duk wanda ta gani saita fad'i sunansa kafin ta shige cikin gida da gudu tana k'iran Innar su.

"Kai INdo yaushe kika dawo?!"

Cewar k'aninta shehu yana wankin kayansa, bata kulasa ba Inna ta fito INdo ta d'areta cikin murna tana washe mata baki.

"Oh 'yarnan kina nan da halinki ko??"

"Ta6 Inna kenan Ina zeje, yana nan aradu wai ina Nafeesah da Sagiru duk bangansu ba..?!"

"Suna waje k'ila dai suntai wani gurin ne, ahe yau zaya d'aukoki jiya malam ke gaya min yadda sukayi da malam Saddiqun."

Cewar Inna INdo tayi dariya bata ma bata amsa ba tace,

"Inna ina Rukayya kuwa, oh ni INdo tana nan kuwa?!"

"Tana nan yanzu ma 'ya'yanta uku sai kuma wanda zata kuma haihuwa."

"Kai Inna yanzu cikin wani gareta kama d'ahare ta saye? Bari naje gidan naganta nikam."

"Haba 'yar nan daga dawowar ki?!"

"Eh wallahi Inna ai Rukayya mutuniya tace kinga tunda na tahi ban mance da ita ba."

Tashi tayi ta suri takalma tayi waje, a k'ofar gida taga su malam Sadeeq da baban ta amma ta wuce sai tsayawa take suna gaisawa da mutane. Lokacin da su Abubakar suka gama magana da malam Hamza abubakar kasa tafiya yayi domin yana son suyi sallama, k'ofar gidan Rukayyar ya k'arasa ya tura yaro ya kirata ya kalleta sai faman dashare baki takeyi tana rufe ido yace mata.

"Humaira zan tafi gida, Zan dawo jibi insha Allahu karki dinga tafiya yawo idan ba haka ba bazan baki komai ba."

"Ai bazan yiba dacta, ammafa karkak'i zuwa kaji?!"

Yace "Toh Humaira Zan tafi amma fa kiyi wanka ranar dazan zo."

Tace "Toh dacta Ina jiranka."

Yana tafiya ta koma gidan Rukayya shi kuma ya shiga mota bayan sunyi sallama da malam Hamza da baba iro. Sadeeq yaja mota suka nufi gida. Da daddare suna zaune abin duk ya damu Sadeeq ya kalleshi yana danna laptop yace mai.

"M twinnie can you tell me why cared Nd protect her? I know bawai dan wancen dalilin bane tunda gashi har kana cemin zuciyar kace please tell me."

Ture laptop d'in yayi tare da kwanciya ya sanya hannuwansa ya tallafo kanshi yana kallon fankar sama yace.

"Twinnie bazan 6oye maka ba hakan yasa naje tare dakai muka dawo da ita gida, twinnie I'm in love with her, I can not do anything with out her. Ina son ta zama matata, ina son na mallaka mata ragamar rayuwata koda kuwa bata zama wayayyar da nake da burin aura ba."

Cikin tsananin mamaki da al'ajabi Sadeeq yake kallon Abubakar jin abinda ya fad'a. Ganin Sadeeq na niyar yin magana yasa shi saurin cewa.

"M twinnie kayi min fatan alkairi, ka kuma taya ni yak'in neman yarda da soyayyar Humaira please n please twinnie."

"Allah ya k'ara dankwan soyayya Allah yasa ayi komai muna nan."

Cewar Sadeeq yana kallonsa, Abubakar yayi murmushi tare da cewa.

"Amin m twinnie thank you."

Kowa ya cigaba da abinda yakeyi zuciyar Sadeeq fal mamaki, shi kuma Abubakar tashi kaddarar kenan auran INdo Allah kadiran alaman yasha.

Washe gari Sadeeq ya tafi k'wara state, a day after Abubakar ya shirya tafiya sumaila yayi sallama dasu Mama, sannan ya d'auki k'anwarsu Hawwah ya kaita wani shago yace ta had'a mai kayan kwalliya, tayi-tayi ya gaya mata na meye yak'i tana dariya ta had'a mai komai sannan ya bata kud'i yace tahau napep. Ya wuce a hanya ya tsaya ya shiga wani Boutique ya siyawa INdo wasu tsala-tsalan dogwayan riguna guda biyar da takalma guda uku ya had'asu da kayan kwalliyar sannan ya wuce sani...











*HAJJA CE*👈
[7/2, 6:33 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
           

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login