Showing 9001 words to 12000 words out of 85627 words

Chapter 4 - MUSAYAR ZUCIYA COMPLETE BOOK by Hajja Ce.txt

Hajja Ce   

14 Sep 2025

31

d'ibi man shanu ta shafa dama tana sato chuck ta d'auki d'aya ta daddaka tayi hoda da shi ta shafa tayi kwalliya jagirar nan har wajan kunne ta sanya kantakile a lab6anta sannan ta d'aura d'an kwali tayi waje Inna na ta faman kiranta amma ko waigowa bata yi ba.

K'ofar gidan taje ta zauna tana jiran su dawo, ana idar da sallah suka dawo gida tun daga nesa suka hangota kamar aljana dariya ta kusa kama Sadeeq ya daure yak'i yi a fili yayin da yace wa Abubakar.

"Twinnie ga tanan fa kayi mata gorin wanka tayo tazo ta nuna maka." Dai-dai suka je k'ofa Abubakar ya kalleta wani takaici ya kuma kamashi INdo tace.

"Gani yanzu kunsan abinda yasa bana kwalliya? Sabida mazan garin nan sun fiya kallona shi yasa amma ni bana zarni."

Ta fad'a tana bubbuga kanta tare da sosawa, mtwww "ke wai kinga sa'anki anan gurin ne?"

Kallon shi tayi tare da kura mai ido tamkar zata cinye sa ya d'aga hannu kamar zai bugeta tayi saurin matsawa tace.

"Yoo ni ina ruwa na wannan ai ba wasa bane kuma idan anyi duniya da manzo na dena zuwa makaranta wata za'a sake min irin ta 'ya'yan gidan kansilan mu."

Mtwwww Abubakar ya ja tsaki tare da shigewa gidan, itama ta doka cinyarta ta kalli Sadeeq tace "Duk haka kuke babu me imani."

Sadeeq ya bita da kallo yana tunanin k'ila tana da aljanu yace.

"Kije kiyi brush."

Abubakar daya fito da car key dinsa yace.

"Bakin ta kamar kashi. Kinga yadda ake son aga hakora ba irin naki ba kamar kina shan d'orawa."

Ya fad'a yana nuna mata hak'orinsa fari kal. Wucewa yayi gurin motar sa Sadeeq yabi bayan sa dan suyi sallama, suna kallon sanda ta wuce tana sanya k'asan hijabin ta tana goge hak'orin. Sallama suka yi abubakhr na sake bawa Sadeeq shawarar ya k'arbi transfer ya k'ara da cewa.

"Bazan sake zuwa garin nan ba sai dai na hakura har ka dinga zuwa can gida ma dinga had'uwa amma wannan garin beyi min ba."

"Insha Allahu doctor karka damu kayi min addu'ar abinda yafi alkairi."

"Toh amin ni na wuce."

Suka yi sallama ya tafi shima ya Shiga gida. Tunda ga ranar kuwa har aka yi hutu Sadeeq be sake ganin INdo a makaranta ba sai dai a unguwar su ya ganta suna wasa ko da farantin tallah..










*HAJJA CE*👈
[7/1, 4:49 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
                    ♥
                 ♥♥
         A true life story

Na

*K.A.S Precious Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu.

Note:- Assalamu alaikum masoya wannan labarin, dan Allah adalci d'aya zaku yi min idan kuna so toh ku ringa adanawa. Idan nayi nisa kuka ce na turo muku sai na rasa yadda zanyi gashi wayar ba lafiya gareta ba dan Allah kuyi min wannan agajin please.🤭


Page *5*

Tafiya take tana dirzar hak’oran ta da k'asan hijjab ko zata samu suyi fari itama, ai kuwa da ta gogo zata duba jikin hijjabin taga gurin yayi yellow ta girgiza kai tare da cewa. "Kai...! Kuma fa da gaskiyar sa wallahi, dan gahi ina kankarowa yalo na fitowa, amma shi hak'oran sa har wuta-wuta suke yi sabida kyau."

Wani shago ta tsaya a nan kusa da gidan su Sahura ta kalli me shagon tace.

"Idirisu kana siyar da burushi da abin matsawa...?!"

Yace "A'a bana siyo shi INdo sabida ba'a siyan shi, sai dai kije kasuwa ranar laraba ki siyo."

Tsaki tayi tare da fad'awa gidan su Sahura, ita dai sam ba ta son zaman gidan su domin bata ta6a yin cikakkiyar awa d'aya sai ta fita, bata taya Inna da aikin komai sai dai da taji yinwa taje taci idan ba'a gama ba ta hau sababi. Sai kusan magariba sannan ta koma gida shima dan tana son tambayar baban su kud'i zata je mahad'a wato inda 'yan mata da samari ke had'uwa suyi hira.

"Baba sannu da gida."

Yana jin haka ya san akwai abinda zata tambaye sa dan haka yayi mata banza, ta kuma fad'a sai ya d'aga mata kai kurum ta ciza yatsan ta cikin ranta tace,

"Wallahi sai ka bani abinda nake so, kaji shi daga gani na baba yayi wani shiru."

Kusa dashi ta k'arasa ta zauna shi kuma da yake a kishin gid'e yayi saurin dan ne aljihun sa me kud'in a ciki dan ya san tun da ta fara wannan shisshige mai d'in toh rok'on sa zata yi shi kuma naira d'ari da sittin ne garesa kuma goma ba zai bata ba dan yau da kyar ya samu a gurin sana'ar sa. INdo ta cire hijjab d'in jikinta sannan ta kalli mahaifin nasu duk da ya had'e rai hakan besa taji zata fasa tambayar Sa ba, cikin rashin ladabin magana ta kallesa tace.

"Baba nera (naira) hamsin zaka bani anjima zanje mahad'a, daga can idan naje kaga zan siyo burushi harda abin matsawa sai kuma ka bani nera ashirin wadda zan siya abubuwa naci.."

"Bani da kud'i uwata yanzu, amma ki bari gobe idan na samu zan baki."

Kallonsa tayi da alama bata yadda da abinda yace ba, ganin tana kallan sa yasa shi kuma kishin gid'a kan aljihun kud'in yana k'ara volume d'in rediyon sa duk kuwa da yana jin ana k'iran sallar magriba amma ba shi da alamar ta shi yayi alwala.

"..'Yar nan zo kije kiyi alwala bana jin yauma ko sallar asubahi kinyi bare kiyi sauran." Inna ta fad'a tana kashe wutar kararen da ta gama tuwo. INdo naji ta turo baki sam bata kaunar taji ance tayi wani abun a harkar rayuwar ta abu in dai ba wasa bane ko kuma naci toh sam bata kaunarsa bare tayi. Bacci ma ban da 6arawo ne da baza ta dinga yi ba, ta mik'e tsaye ta shiga d'aki ganin baban nasu bashi da niyar bata ko sisi.

Garam-garam inna ta jiyo ta tana tatta6a mata kwanukan jeranta na d'aki, saurin bin bayan ta tayi nan taga sai faman bud'e-bud'e take yi mata cikin fad'a inna ke magana tana kallon INdon tace.

"Me kike nema anan? Ko kinyi ajiya a gurin ne zaki d'auka..?!"

INdo ta ajiye kwanon hannunta kana ta kalli Innar ta tace, "Inna fisabilillahi baba ba zai bani kud'i naje mahad'a ba, salan naje naga su maryam su sahura Sa sauran k'awaye na suna siyan abubuwa su yi min gori...?"

"Toh banda abinki baya ce miki babu ba idan ya samu zai baki, toh kiyi hak'uri mana nima kuma basu gare ni ba bare na baki."

K'ad..! INdo tayi da harshe alamar jin haushi sannan tayi waje fuuuuu babu wanda ya kula ta shima baban nasu yana ji ana k'iran sallah amma ba shi da niyar tashi yayi yana kishingid'e abin sa. Tana fita ta shiga gidan Rukayya wadda amarya ce aka kawo ta unguwar take yin kayan siyarwa su alawar madara, gullisuwa, k'alli-k'a-k'au, yajin masau da dai sauran kayan siyarwa na yara, shine INdo take zuwa ta kar6a tana siyar mata sai ita kuma ta ringa bata ladan nera talatin ko asshirin da biyar.

"Uhm su INdo sai yanzu aka ga damar zuwa ko..?!"

Rukayya ta fad'a tana kallan ta, zama tayi a kan tabarma tana dariya Rukayya ta idar da alwala tazo ta zauna kusa da INdon tana kallonta tace "Toh me ya hanaki zuwa yau da wuri gashi ma har an siyar sabida yau na samu 'yan sari duk sun siye sauran albishir kawai na naira tamanin.."

INdo ta zaro idanuwa tare da dafe k’irjinta yau kenan ba ta da kud'in siyan gyad'a, cikin karad'i tace, "kai Rukayya amma ko ki jira nazo ba komai tun da abin 'yar haka ce..!"

Rukayya tace "A'a INdo ina zan ta jiranki bayan har gidan Ku na tura kizo aka ce min bakya nan, sai kawai na zauna jiranki bayan ga kustoma sun zo.."

"Ai shikenan yanzu ki bani albishir d'in na tafi dahi.."

Shiga cikin d'aki Rukayya tayi ta fito hannunta rik'e da leda ta mik'a mata. k'ar6a INdo tayi ta lek'a cikin ledar sannan tayi dariya cikin ranta tana addu'ar Allah yasa yau ta had'u da Shu'aibu saurayin ta ya ce ta shanye ya biya kud'in. Mik'ewa tayi tasa takalma tana cewa Rukayya.

"Toh na tafi sai na dawo Rukayya kiyi mana adda'a (addu'ah).."

Tayi dariya tana gyara hijabi tace, "Toh INdo Allah ya ba da sa'a a siyar baki d'aya."

Tana fita ta d'auki guda d'aya tare da jefawa cikin bakin ta, zak'in ya gauraye mata bak'i ta lumshe ido tare da sosa cikin kunnanta. K'ofar wani shago taga malam Sadeeq hakan yasa ta k'arasa tamkar bata ganshi ba ta kalli me shagon tace.

"Wale kana sai da burushi da abin matsawa..?!"

Wale me shago yana k'ok'arin bawa malam Sadeeq klin da sabulon da ya siya yace. "Eh guda nawa za'a baki..?" INdo ta kuma kallon malam Sadeeq sai taga ko kallon tama baya yi sai kud'i da ya zaro yana k'irgawa zai bawa me shagwon ta ta6e baki. Yana sane ya zamar da naira d'ari k'asa as in be sani d'in nan ba sannan ya mik'awa wale kud'in sa ya mai da sauran aljihu. INdo na ganin kud'in tayi kamar zata d'auki dotse kawai ta d'auke d'arin ta maze sai mazurai take yi taji ko wani zai ce ya ga sanda ta d'auka, da taga babu wanda yace komai sai ta mik'awa wale kud'in tana cewa.

"Toh bani guda d'aya-d'aya ka bani canji na." Sadeeq na gani ya wuce yana mamakin ta ashe har sace-sace da d'auke-d'auke take yi, lallai yarinyar bata da tarbiya sam sai dai be san dalilin da yasa yak'i yi mata magana ba bayan ya san hakan da tayi ba dai-dai bane ba a cikin addini dama rayuwar ta gaba d'aya.

D'akko mata yayi sannan ya bata canjin naira talatin ta k'ar6a tayi gaba abinta. Cikin mararta ta tura brush da makilin d'in sannan tayi gaba tana d'aukar albishir tana sanyawa a cikin bakinta sai farin ciki take yi yau ta fito da sa'a zata yi brush ta basu mamaki gobe.

Tana zuwa zata sha kwana taji ance mata "ke zo nan." Ta juya tana kallansa ganin malam Sadeeq yasan ya ta rik'e kugunta tana girgiza jijinta tana harararsa "yes.." Ganin yadda take mai ne yasa shi kuma d'aure fuska yace mata "fito min da naira d'ari ta da kika d'auke ko kin d'auka ban ganki ba."

INdo najin haka ta gyara tsayuwar ta tare da sake danna brush d'in dan karya gani, cikin wayan basarwa tace "kai malam Sadeeq kud'in ka? yaushe na d'auka zaka ce in baka...?"

Matsawa yayi kusa da ita tayi saurin yin baya ya mik'a mata dogon hannunsa tare da bud'e mata tattausan tafukan hannun da nufin ta sako mai kud'in sa ta kallesa tana muzurai tare da tsuke baki cikin yake tace.

"Ni ban d'auki kud'in kaba, a inama muka had'u bare na gani na d'auka."

Ya kuma had'e rai sai taga yayi mata kwarjini k'irjin ta ya hau harbawa ta fara jin tsoron Kodai ya ganta, toh me zai mata ko ba malam Sadeeq bane d'ayan ne masifaffan. Ganin yak'i d'auke hannunsa yasa ta tabbatar da cewar lallai ya ga sanda ta sace amma ya aka yi be nuna ya ganta ba a gurin? Cikin borin kunya tace.

"Toh na d'auka abakacin kalamin herrin maita da kayi, ai dama nace ban yafe ba toh yanzu ka biya ni hike nan."

"Ki mik'o min kud'ina nace bana son maganar banza kina jina..."

Jin yana masifa yasa ta cewa "Toh na siyo burushi dasu ba kune kuka min wulak'anci ba, shi yasa nasiya nima na dinga yi wallahi a gobe zaku ga bakina sai yafi naku fari."

Tana kaiwa nan tayi gaba haushi da takaici suka cika Sadeeq yama rasa gane meye matsalar yarinyar sai dai yafi dan gana hakan da cewar k'ila tana da aljanu. Gida ya wuce domin so yake daya gama had'a result ya tafi gida tunda anyi hutu sai kuma an dawo wanda yake son kafin sannan ya samu canjin gurin aiki.

Cikin kwanaki uku ya kammala komai yabar garin sai farin ciki yake yi dan ba k'aramin takura yake yi ba da k'auyan.

_Fatan alkairi ga masu bibiyar wannan labarin, ina ganin sakwannin ku Allah ya bar kauna. Muje ga page d'in gaba wanda daga shi ne zaku fara gano sirrin cikin labarin._🤭







*HAJJA CE*👈
[7/1, 4:49 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
                    ♥
                 ♥♥
         A true life story

Na

*K.A.S Precious Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu.


Page *6*

Zaune suke a cikin d'akin su, babban d'aki ne domin a da a matsayin sitting room yake lokacin da suka taso suka zama samari yasa abban su ya bar musu shi suka gyara shi aka sanya musu katifu guda biyu d'aya na gefen hagu d'aya na dama sai durowar kayan su ko wanne ya d'auki gefe d'aya domin kayan nasu ya bambanta. Abubakar shine yafi son sanya k'ananun kaya sa6anin Sadeeq daya fi son manya kamar su shadda boyal da sauran su.

Shiru Sadeeq yayi idanunsa a sama kai da ka ganshi kasan ya fad'a cikin zurfaffan tunani, kallan sa Abubakar yayi cikin ta6e baki yace.

"Twinnie ya aka yi ne kake wannan zurfaffan tunanin?"

Sadeeq ya numfasa tare da tashi zaune ya janyo kofin zobon da Maman su ta aiko musu dashi ya d'iba yasha sannan ya zuba wani ya mik'awa Abubakar yana cewa.

"Twinnie ina tuna nin maganar Mama ne ta jiya, kaga tace Abba zura mana ido kawai yake yaga dame zamu fara. Gaskiya ni yanzu na fara tunanin gara na fara yin gini na tunda ya riga ya bamu filayen kuma yace duk inda muka ga ya kakare mana toh muyi mai magana gara kawai nazo na fara dan ina son lokacin da zan fara neman aure toh ya zamto koda ban k'arasa ginin ba to ya zamana sauran k'arashe shi yasa kaji nayi shiru ina tunani."

Kai kurum Abubakar ya jin-jina sannan ya mik'e tsaye, shirin tafiya asibiti yayi ganin be ce komai ba yasa Sadeeq cewa. "Toh kai naji baka ce komai ba ka kuma tashi zaka tafi meke nan hakan da kayi..?!"

Shafa gashin kansa yayi tare da d'aukar turare ya fesa. "Karka damu twinnie da rashin maganata, kasan dole idan naga ka fara nima na fara har addu'a nake mana Allah yasa mu samu matan aure 'yan biyu kawai mu aure su, dan haka karka damu kai dai ka fara samo matar tukun na."

Sadeeq yayi dariya tare da komawa ya kishin gid'a, yana murmushi yake cewa. "Lallai kuma a ce mun had'a gida kuma kamar su d'aya like me n you, ta6 ai sai mu kasa ganewa haka kurum wata rana in dirfafi matar ka ko kai ka shigar min gona toh a'a.."

Abubakar ya kyal-kyale da dariya irin wadda be ta6a yi ba ya kalli Saddeq yana nuna shi da yatsa yace. "Amma dai my twinnie muguwar fassara gareka, babu abin da zai faru kai dai kayi mana fatan alkairi.."

"Toh ai gaskiya na fad'a ko kuma matar ka ta fito ta ganni tayi tunanin kaine tazo ta mak'ale min ni bazan hanata ba tunda jiki da jini, ko kuma tawa matar ta ganka tayi tunanin nine gaskiya twinnie ka dena yi mana fatan auran twins dan ni gaskiya ka san bani da kauda kai, shi yasa ma da Abba yace baxai bamu gida kusa da juna ba banji haushi ba."

"Hahaha twinnie ai ina tausa yawa duk wadda zata aure ka wallahi domin zata sha wahala, kana gani a yanzu ma baka da auran sai kayi dreaming sau uku hud'u bare kana ganin ta."

Murmushi Sadeeq yayi tare da gyara kwanciyar sa yace "twinnie kayi tafiyar ka kana yin late ga marasa lafiya can na jiranka ni bacci ma zanyi dan ban gama va ka tashe ni bye."

"Hmmm ka dai kore ni toh Allah ya baka mata a kauyan daka baro tun da baka son muyi iri d'aya."

"Wallahi ba amin ba, duk basu da hankali musamman ma INdo kai! wannan yarinya ba hauka ne yake damunta ba harda jahilci kasan shi yafi hauka. Gasu k'azamai tunda naje garin banga wayayye ko wayyayi ya ba wallahi, ba amin ba dan kamar yadda kake son nutsattsiyar mata haka nima nake so kuma 'yar gayu mai ilimin zamani da na addini.."

"Twinnie kad'auki zafi da yawa so sorry dan Allah, bari naje na dawo bye.."

"Ok sai ka dawo."

Da haka suka rabu sai da Abubakar ya shiga cikin gidan yayi sallama dasu Maman sa sannan ya fita, yayin da Sadeeq ya kwanta duk da cewar maganar da d'an uwan nasa ya fad'a tasa baccin ya gudu sabida takaici hakan yasa ya tuno da INdo yaja tsaki tare da mik'ewa ya koma cikin gida ko zaiji dad'in ranshi a gurin su Maman su.

*IHSAN MEDICAL CENTER*

Ahankali yake karasawa asibitin na ihsan medical center dake unguwar sultan road nassarawa gra agarin na kano,sanye yake cikin kananun kaya kirar suit blue tacikin kuma fara ce hannunsa rike da jakar laptop d’insa fuskarsa sakale da farin glass se bulbula kamshi yake haka yashiga harabar asibitin,yana shiga ya hango nurse hidaya k’ok’arin juyawa yake ta cinmashi da sauri,

“Welkm Doctor,Ina kwana..?!”

“Fine Alhamdulillah nurse hidaya..”
Yana gama fada yai gaba ya barta wajen

Office d’insa ya nufa inda sunansa ke rubuce boldly ajikin k’ofar office din
‘Dr Abubakhr’ kamar kullum Mani Cleaner ne aciki yana tsaftace office din se mopping terrazzo din yake dake ta shekin kyalli,da sauri Mani ya tsugunna yana kwasar gaisuwa

“Sannu da xuwa yallabai Barka da safiya”

“Barka dai Mani.”

Kan kujera dr abubkhr ya xauna yana dudduba files din kan tebur din one by one,har Mani yakarasa ya feshe office din da freshener,

“Yallabai na kammala”

“Yawwa Mani godia nake xaka iya tafiya”

Har Mani yakai kofa yadawo yana sosa keya,

“Yallabai anbani sako wajenka amma wallahi na sha’afa da sunan,nurse dinnan ce de da tai transfer daga Cotonou”

Sarai abubkhr ya gano wacece naccaciyar yarinyar data nace masa ce,

“To Mani ba damuwa tunda kamanta sunan kaje kawai”

Shiru Mani yai da alama ya zurfafa tunani be jima ba ya dago yana murmushi,

“Yallabai natuno nurse natasha ce da sassafe xuwana kenan tabani sako nabaka nikuma hartamin alkhairin Naira dubu yallabai”

“Toh madallah”cewar Abubkhr

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login