Showing 18001 words to 21000 words out of 85627 words

Chapter 7 - MUSAYAR ZUCIYA COMPLETE BOOK by Hajja Ce.txt

Hajja Ce   

14 Sep 2025

41

malam..." Ya zabga mata harara tayi saurin toshe bakinta da hijjab kafin taga ya dena tace. "Kayi hakuri dakta Habubakar mantawa na keyi kace ba sunanka malam ba, amma wallahi nayi niyyar yankewa niko dan naciyo atamfa amma duk saina manta hef (shaf).."

"Ohh muga farcan naki.." Ta fito dashi yasha lalle a yatsun ta nuna mai, hannu yasa ya janyo nata yana kallah murya sanyaye INdo tace mai. "Dan Allah Dacta Habubakar kace ya bani ni yanzu ma zan iya cire farcen, dan iyayanka kace ya bani dan Allah kaji..?!"

Sadeeq ne yazo gurin ya kalli d'an uwan nasa rik'e da hannun INdo hakan ya bashi matuk'ar mamaki da al’ajabi cikin sauri Sadeeq ya zare hannun INdon daga na Abubakar cikin harshen turanci Sadeeq yake mai magana cewa.

"Twinnie why na?am i day dreaming or are you really the one holding a village girl hands,and if you have forgotten about it then I haven’t ,this villagers are cruel,I don’t want them to think something else in their mind ..This is so not you”

Cikin ko’a jikinsa abubkhr ya daga kafada sannan yafara magana,

"Habba twinnie sunan Momcy gareta fa shi yasa, gashi kuma tayi kwalliya irin wadda nake so that's y kaga ina iya rik'e hand's na ta."

Mtwww "inajin baka ganeta bane shi yasa kake sakar mata fuska, toh bari na tuna maka kowa cece INdo malam Hamza, wannan me satar amsar ce me cizon maza nasan yanzu ka harbo ta."

"Really my twinnie? Abubakar ya fad'a yana sake maida kallonsa fuskar INdo, kwakwalwarsa kuma tana sake hasaso mai lakacin daya kamata ta duk'ufa tana kwafar note dan sam koda ta kwafo ma bagurin da aka tambaya bane, ya kuma kallon Sadeeq cikin mamaki yace

"Gaskiya m twinnie kayi k'ok'ari indai haka ne. Ashe k'azan tace duk ta maidasu mahaukata Gaskia I'm sure nan gaba za'a sha mamaki indai suka d'ore da haka za'aji dad'i sosai."

K'afarsa yaji ana jijijigawa hakan yasa shi saurin kallon k'afar kawai yaga INdo ce take mai alamar magiya tana nuna mai ya samo mata kyauta kota meye Sadeeq dake fito da kayan zai bawa wad'anda suka ci ya kalli Abubakar dake kallon INdo kawai yaja tsaki sabida takaici. INdo kam sai nunawa Abubakar malam Sadeeq takeyi alamar be zabo mataba zasu k'are yayi dariya cikin zuciyar sa ya kalli sauran masu kuskuran yace.

"Kuzo nan muyi photo daku." Suna jin haka suka ruga bayansa suka jeru amma sam INdo batayi gigin zuwa ba hankalin ta yana wajan malam Saseeq dayake ta rabo zuciyar ta tamkar ta fito tsabar fargaban karsu k'are.

"Humaira zo mana ayi dake." Abubakar ya fad'a yana kallon Indo , ita kuwa bata masan da ita yake ba tana ji tana gani har malam Sadeeq ya kammala bada kyautukan taji wata muguwar tsanarsa tundaga k'asan zuciyar ta ya game da ilahirin jinin jikinta tayi ta zagba mai harara bemasan tanayi ba yana can yana sake yiwa wad'anda sukaci kyautar nasiha da kuma muhimmancin tsabta da Ilimi.

“Kuje kuma ku zauna kowa yaje gida yayi karatu ranar Monday zanyi muku test duk wanda ya fad'i ni nasan irin hukuncin dazan d'auka akansa kunajina ko?!"

Malam Sadeeq ya fad'a bayan yaga yau twinnie d'in nasa da mutunci ya shigo, duk 'yan ajin suka ce "OK uncle." Dayake yana k'ara d'an wayar dasu, amma INdo data tashi sai da ta d'auki ledar littafinta ta faki idonsu duk da cewar Abubakar nason yayi mata photo da kwalliyar ta yana can yana tambayar Sadeeq mezai iya bata koda ba babba bane ba sukaji tana cewa.

"Baza'ayo karatun tess (test) d'in ba, kai idanma kun sake ganina a makarantar nan dan Allah ku soya ni. Wallahi malam Sadeeq yayi karya kuma ance babba me karya d'an wuta ne gobe k'iyama yana kusa da fir'auna, Allah ya sakamin sabida na kashe kud'ina garin yin kunhi da gyara kambas d'ina sai Allah ya saka min. Yo dan baka bani atamfar ba seme, nima Inna ta zata sai min ai sallah ta kusa."

Tana gama fad'a ta murgud'a baki ta juya da gudu zata arce taji an rik'eta gam cikin tsananin tsoro da tashin hankali tayi k'ok'arin juyawa taga waye sai taga malama Murja ce ta cafketa tare da tura ta cikin ajin, tana zuwa ne da yake period d'inta ya shiga sai taji irin rashin kunyar da takewa malamin hakan yasa tayi shiru sai data kai k'arshe zata gudu tayi saurin kamata.

Tsananin mamakinta suka kama Abubakar, sai yanzu ya kuma tabbatar da cewa itace ya tashi a fusace yayi kanta jin yadda take gayawa twinnie d'in nasa magana. Sadeeq ne yayi saurin taresa yana kad'a mai kai alamar karya doketa, yana wani irin numfashi ya ture hannun Sadeeq d'in daga kafad'arsa yana cewa.

"Ka rabu dani Sadeeq bakaji yadda take had'aka zama da fir'auna ba, barni naci uban shegiyar yarinyar nan da har ina tausaya mata ashe batada mutunci har yanzu."

"A'a twinnie barni da ita, kayi hakuri ka kwantar da ranka. Malama na gode da gudun mawarki, ke kuma zonan..." Sadeeq ya fad'a yana damk'o hannunta Abubakar kuwa jiyake tamkar ya ham6areta sabida 6acin rai. Fita yayi da ita sai ihu take musu har suka k'arasa cikin staff room ya kalleta yace.

"Kama kunnanki."

"Dan Allah malam kuyi hakuri."

Babu wanda ya kulata sai dai duk malam cikin staff room d'in saida suka bada shedar rashin kunyar INdo, ganin babu mebada hakuri ne yasa ta sunkuya ta zura hannunta tana nishi tana cewa "malam wallahi hannuna baya kaiwa abakacin sa kace nayi nibdom (kneel down) kaji."

Jiyosu ma tayi suna hira babu wanda ya kulata dan yau takaisu bango, tun tana magiya har tayi shiru. Ta dad'e tana kamun kunnen kawai suka ganta ta fad'i k'asa Abubakar dake kusa da gefenta besan lokacin daya kai hannu zai tarota ba amma saida tayi k'asan, ashe baccine ya kamata, kuma duk da fad'uwar da tayi hakan besa ta tashi ba saima zarcewa da tayi tafara sauke munshari.

"Twinnie mu wuce tunda ka gama."

Beh jira cewar sa baya k'arasa inda INdo take kwance sai uban munshari takeyi tamkar wata babbar mata a hankali ya dinga k'iran sunanta amma inah ko motsawa batayi ba, hannu yasa dai-dai kafad'arta yana jijjigata nan ma still bata motsaba. Ganin yadda yake bin ta a hankaline yasa Sadeeq mik'ewa ya d'auki dorina yana zuwa ya tsula mata a baya. A razane ta mik'e ta rarumi Abubakar dake tsaye kusa da ita tana cewa.

"Wayo Allah atamfata ce."

Sak'e tsula mata yayi tayi saurin sakin Abubakar tayi k'ark'ashin tebur d'in malam yahaya tana kuka tana sosa gurin cikin kuka take bashi hakuri yayin da shi kuma Abubakar ya fita daga cikin staff room d'in. Sai da wasu malam suka bawa malam Sadeeq hakuri sannan aka ce taje ta tsugunna ta bashi hakuri tayi sannan ya hakuri yace kuma duk sanda ta kuma yin fashin zuwa makaranta sai yasa ankamota yayi mata duka tace toh.

Fitowa yayi amma bega Abubakar d'inba har ya fita gate babu bare alamun motarsa, sosai Sadeeq yayi mamaki sai ya nufi gidan shima amma abin mamaki bako motarsa a gurin hakan yasa shi kiran wayarsa aka sanar mai cewar a rufe take, mamaki ya kuma sark'e Sadeeq. Yana tsaye a gurin har su INdo suka wuce suna gulmarsa be kulasu ba.

Shi kuwa Abubakar yana fita motarsa ya hau yakama hanyar gida, haka kawai yau yaji baya son jin kukan INdo zuciyarsa har zafi take mai duk kuwa da cewar yasan itace batada kunya amma ya rasa dalili, tunda ya taho tunaninta yakeyi yayi-yayi ya halasto qibd'iya ya kasa sai dai INdo da kamanninta ya buga sitiyarin motarsa yafi sau ashirin harya k'arasa gida. Yana shiga yaji Maman su na cewa.

"Kajishi can najiyo tsayuwar motarsa da alama ya dawo. Toh shikenan 'biyu kyautar Allah kaima Allah yayi maka albarka." Sai da ya bari ta kashe dan yasan da Sadeeq takeyin wayar sannan ya shiga cikin gidan nasu bakinsa d'auke da sallama....


_Kuyi hakuri da wannan, kunsan bawa duk yadda yaso yayi abu idan Allah bebashi dama DA iko ba toh babu abinda zai iya yi a rayuwarsa. Nagode luv you all._ Gaisuwa da fatan alkairi zuwa ga aunty Sdy jegal, Ina miki fatan alkairi a duk inda kike, Allah ya raya mana baby boy d'inmu cikin addinin musulinci.😘








*HAJJA CE*👈
[7/1, 4:53 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
                    ♥
                 ♥♥
         A true life story

Na

*K.A.S Precious Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu.


_Shafin yau na kune 'yan grp d'ina wato *HAJJA CE NOVELS GRP* da *ZAURAN BIEBIE ISAH* tare da *🅿HERTY NOVELS* da *MUSHA KARATU N YBK2* gara nayi muku jam'u domin idan na tsaya lissafoku sai kunji haushina kunce dama typing nayi muku da wannan lissafin. Hak'ik'i ina jin dad'in yadda kuke tare dani, comments d'inku nasani dariya da kuma nishad'i uwa uba kwarin gwaiwa. Nagode sosai #ana tare da INdo malama Hamza._🤝😍


Page *10*

Amsawa Maman tayi tana had'a musu zo6o. k'arasawa yayi ya zauna akan kujera 'yar tsugunno sai faman shafa sajen fuskarsa yakeyi. Umma Dijeh ce ta fito daga parlor kasan cewar muhad'u a parlo ne ta kallesa tana murmushi cikin wasa tace mai.

"Likita bokan turai, daga sallar juma'a kuma sai ina? Ko yauma za'a lek'a mak'ota ne..?!"

Wayarsa ya zaro zai kunna domin tunda ya baro makarantar ya kasheta sabida yasan dole Sadeeq ya nemeshi, shikuwa beshirya abinda zai gaya masa ba. Kallan Umma Dije yayi sannan yayi murmushi yace.

"Haba Umma jiya fa naje, kuma yauma bata nan." Dariya suka yi itada Maman sannan ya tashi ya fito yashiga d'akinsu, kayan jikinsa ya rage ya zauna daga shi sai vest da boxer shorts sannan ya kuma d'aukar wayarsa dai-dai lokacin kuma Sadeeq ya kuma kiransa. Babu yadda zaiyi dole ya d'aga kodan ya kare kansa daga wajan abokin haihuwar tasa, cikin basarwa ya kara a jikin kunnansa tare da fad'in, "My twinnie sai kaga na taho ko?!" Sadeeq dake zaune a k'ofar gida ya ta6e baki sannan yace.

"Ba gani nayi ba nemanka nayi na rasa wanda kuma ni bansan dalilin yin hakan ba, twinnie kasan irin tashin hankalin daka sakani? Da police station zanje nakai report sai kuma muka yi waya da Mother take cemin gakanan ka k'arasa why did you do this to me ah?!"

Duk sai Abubakar d'in yaji babu dad'i ganin yadda duk ya tayarwa da d'an uwan nasa hankali, da kyar ya samu mafitar da zai wanke kansa ya numfasa tare da cewa.

"Kayi hakuri nima saida na taho naga rashin dacewar hakan tunda bamuyi sallama ba, abinda ya faru shine ina fitowa Dr Inuwa yake sanar dani ana nemana a cikin asibitin da gaggawa shi yasa duk na rud'e na kashe wayana dan karsu dunga damuna sorry twinnie kaji kayi min afuwa.."

"Okk bakomai yanzu tunda naji kana gida sai anjima."

Kamar ya tambayesa INdo sai kuma yayi shiru suka ajiye wayar shi kansa besan yadda zai fad'i abinda yakeji ba har mamaki yake yi ya ajiye wayar yashiga toilet. Wanka yayi lokacin har an kawo mai abincinsa an ajiye amma ko kallansa beyi ba sai wayar ya sake d'auka ya shiga gallery, hotunan dayayi mata ba tare da kowa ya sani ba. Yana gani yana duba na e so yake yagano meke damunsa amma inah..ya kasa tantancewa sai faman k'aryata zuciyarsa yake yi da abinda take shaida mai.

INdo kuwa tana zuwa gida ta fara cire kayan jikinta tana killarwa ta sanya wata kod'add'iyar shadda doguwar riga wanda ta d'age mata sannan ta dawo tsakar gida ta zauna tana kallon kunshinta. Wani irin tsanar malam Sadeeq da Abubakar suka sake mamaye cikin zuciyarta ta cewa Inna.

"Inna wanki zanyi gobe na tafi gidan yakumbo Tsahare, wallahi billahillazi bazan sake zuwa makaranta ba saye zan yi tafiya ta naga ta tsiyarsu mugaye."

Cikin dafe k'irji Inna tace "ke 'yarnan saye kuma? Kiyiwa Allah da ma'aiki kiyi shiru da maganar tafiyar nan kinsan dai babanku baya son zuwanku garin nan tun abinda ya faru tsakaninsa da jummala."

"Inna wallahi saina tafi, kina jinfa abinda mugun malamin nan yace, wai idan na dena zuwa makaranta saiya saka an d'akkoni toh wallahi barin garin zanyi hena dad'e sannan zan dawo a'he."

Hankalin Inna ya tashi dan tasan idan baban su yaji toh lashakka sai anyi fitina duk da cewar tsaharan k'anwarsa ce amma tun a haihuwar shehu suka samu sa6ani akan naman suna shikenan sukayi baram baram kuwa yace bashi ba d'an wansa sannan yacewa Inna ya haramtawa 'ya'yansa zuwa garin idan sukaje kuma Allah ya isah. Tashi INdo tayi tabar gidan ta shiga gidan Rukayya, tana ganinta ta fara murna tare da cewa.

"Kai INdo shine ko a kawo min kyautar ingani ko?!"

Saida INdo tasamu guri ta zauna sannan tacewa Rukayyan "Yo ai basu bani ba, wai wani ban yanke farce ba ninasan dama malaman nan ba kaunata sukeyi ba kawai dan dai nafi karfin sune bayadda zasu yi dani shegun."

"Kan uba! Yanzu kina nufin babu abinda malam Sadeeq yayi miki?!"

"Sai duka nama dayayi kuma nace Allah ya isa." Nan suka cigaba da hira har INdo na bata labarin tafiyarta saye gobe Rukayya tace.

"Kai INdo sai kuma yauhe zaki dawo?!" INdo na watsa shinkafa da wake tana cewa "babu lokaci idan na tafi henayi aure zan dawo yasin."

"Kai INdo baxaki dawo ba kenan?!"

Rukayya ta kuma tambaya cikin jimami, ita kuwa INdo ko'ajikinta tace "Eh bazan dawo ba he randa malam yadena zuwa garin nan."

"Kai Allah ya wadaran wannan malamin da yaja zaki tafi, zamuyi rashinki INdo barema Inna."

"Kyale Inna can na barota sai masifa take dan nace zani saye wai bazani ba toh alkur'an saina tafi."

Haka suka dinga hira da Rukayya har bayan la'asar sannan ta koma gida inda ta tarar da Inna ta gayawa babansu yace toh babu inda zata ta kule d'aki bata sake fitowa ba. Tun asubar fari ta farka ta tsinci kayanta tasa a d'ankwali ta d'aure ta d'auk'e fitilar da aka haska d'akin da ita wato shekarau mekwayayen nan k'ananu a jikin katako tayi sad'ab-sad'ab gidan a kulle yake ta jefa kullin kayan ta katanga sannan itama ta kama ta dirga ta kwashe kayan nata ta an taya da gudu sai bakin titi ko tsoro bataji.

Tayi tafiya sosai sannan gari ya fara haske daman babu buk'atar yin sallah dan bawani yi takeyi ba sai taga dama. Mota na zuwa ta tsayar dasu ta shiga dama da d'ari ukunta a hannu data ara wajan Rukayya. Can gida kuma tunda suka farka suke neman Inndo, duk gidan da akasan tana zuwa saida akaje bata nan. Kuka Inna tasanya domin tasan yau INdo tayi mata abinda zai iya 6allamata aure, lokacin da baban yaji cewa yayi k'arya Inna takeyi tasan ta tafi dan haka itama ta shirya tabi bayanta su dawo tare kasan cewar sunsan zata iya zuwa. Ko kud'in mota Inna batada su amma a haka malam Hamza ya takura mata kan cewa sai taje ta dawo da INdo haka ta fito tana hawaye. A bakin titi malam Sadeeq ya ganta harya wuce ya dawo duk da cewar ta rufe fuska da mayafin jikinta tana share hawaye yaje yace.

"Baiwar Allah kiyi hakuri lafiya dai ko..?" Shiru batayi magana ba duk da besan kowace ba ya zaro d'ari biyar ya bata babu yadda zata yi ta k'ar6a tana ta zazzaga mai addu'a shidai ya wuce ita kuma mota na zuwa tashiga tana fatan Allah ya temaketa can din INdo ta tafi, ayau bazasu kwanaba zata dawo da ita.

Wajan k'arfe biyu da rabi INdo ta shiga wata rugar fulani anan cikin sayen bakinta a washe hannunta d'auke da kullin kaya, suna zazzaune k'ark'ashin bishiya suka hangota nan da nan yakumbo tsahare ta had'e rai fuskar nan babu yabo babu fallasa tana dakan fura haka INdo ta k'arasa gurin tana dashare musu hak'ora.

"Wacece wannan kamar mai sunan Gwaggo..?!"

Cewar talatu yayar malam Hamza dake kwance, INdo ta k'arasa tare dayin cilli da d'ankwalin kayan nata tace.

"Nice nan yakumbo talatu ahe duk kuna nan, yau dai gani a garin ku ina kwananku...?!"

Duk suka amsa suna tambayar ta su Sagiru da Nafeesa da Shehu tace lafiya lau amma banda yakumbo tsahare daketa faman dakan fura, ko ajikin INdo ta mik'e tare da zuwa wajanta tana cewa.

"Sannu yakumbo tsahare, ina su lawisa take..?!"

"Ke karki yimin rahin kunya aradun Allah kuwa, idanma Ubanki ne yau ya turoki toh dagake harshi d'in zan iyayi muku rahin mutunci jacan ki bani guri ni."

"Allah baki hakuri daga tambaya.."

INdo ta fad'a tare da komawa wajan su yakumbo talatu aka kawo mata d'umamen tuwo da fura da nono tana ci suna hira har su lawisa suka dawo daga tallar nono, murna da farin ciki ba'a magana duk da cewar Lawisan cikima gareta har tayi aure tsiranta da INdo shekara biyu ne.

Cikin gidan suka wuce suna zazzaga shirmen su. Inna kuwa la'asar sakaliya ta iso saye sabida da kyar ta samu motar da ta kawota a d'ari da talatin. Saida tayi sallah sannan taci kwad'on rama da fura bayan sun shaida mata cewar INdo tazo amma sun tafi tatsar nono, hankalin Inna ya tashi tace ta kalli malam iro mijin yakumbo talatu tace.

"So nake a yau mu koma gida gahi bata kusa kuma ina neman yadda zanyi mu samu kud'in komawa." Malam iro ya kalleta da mamaki sannan yace.

"Haba dai Maryamu, yanzu fisabilillahi har yaushe zaku koma gida, hasalima ita INdon bata kusa kuma da kyar idan zata yadda tabiki dan tasamu yara, kuma na tambayeta randa zata koma tace sai an kori wani malami a garin naku."

Inna ta fashe da kuka malam iro ya kalleta yana jin tausayinta dan yasan tsoran d'an uwar matar tasa takeyi. Hakuri ya dinga bata ita dai hawaye kawai takeyi gashi tana matukar kaunar malam Hamza duk da cewar shima yana matukar santa amma hakan baya hanashi yimata wulak'anci. Har magariba su INdo basu dawo ba sai wajan k'arfe takwas na dare, koda taga Inna batayi wani murna ba kotaji tsoro ita kuma nauyin mutane ya hanata yi mata magana.

Cikin dare Inna tasamu INdo ta gama lalla6ata akan ta yarda gobe su koma amma fir tace wallahi bazata koma ba nan zata zauna sai lawisa ta haihu koda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login