Showing 27001 words to 30000 words out of 85627 words

Chapter 10 - MUSAYAR ZUCIYA COMPLETE BOOK by Hajja Ce.txt

Hajja Ce   

14 Sep 2025

40

        ♥
                 ♥♥
         A true life story

Na

*K.A.S Precious Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu.

*VOTE me on wattpad @Hajjac*


_Ina ganinku dearest comments d'inku na k'ayatar danifa_
*K'anwata Stylish, my Xoxo, Faxyfation, phartzarah, Nuceeyluv, khady, Mmn gausiya, UmmuMuhammad, Khady M/kano, Mmn nuceey, sumeey Q, Meela adeel, Mummy, Hafsat A Fulani buchi, Hafsat A shitu, aunty Ag,💞 Ummul Meenal, Habeeba M, aunty baraka, Mmn Nazir👜* gaskiya bazan iya duka ba kuyi hakuri naga nakusa yin rabin wani paragraphs d'in🤪.


Page *14*

Yana zuwa unguwar ya ganta a k'ofar gida a zaune tayi wanka tayi kwalliya irinta zamani lokacin ba'a gama sanin su concealer ba, amma tasa eyeshado red janbaki tayi kuma jagira.Tana ganin mota a k'ofar gidan su ta shek’a da gudu tana gayawa su Inna yazo kafin ta kuma fita kamar wata saban kamu lokacin harya fito yana rik'e da murfin ya kalleta itama ta kallesa.

Sanye yake cikin wata dakakkiyar shadda getzner light blue anyi mata dinki na dark blue ya d'ora hula fuskarsa har wani kyali-kyali takeyi kawai INdo ta saki baki da hanci tana kallansa kallo na kurrullah tamkar tana son ganin wani abu ya mik'a hannunsa yana zagaya shi a saitin fuskarta tayi firgigita tare da yin dariya tace.

"Dacta Habubakar wallahi kanada kyau ta6 heyau na ta6a ganin haka."

Murmushi yayi tare da rufe k'ofar ga yara sun fara mai dandazo ya ciro 2k yabasu sannan ya shiga zauran gidan su ta bishi ya tsaya yana kallonta ganin tayi mai wankan dayace tayi harda kwalli sai ya ce.

"Humaira babu gaisuwa? Bafa ki gaida niba."

INdo tace "Au hakane fa ina yini ya gida ya iyaye..?!"

"Lafiya lau baki tambaye ni malam Sadeeq ba why..?!"

"Ta6 narasa wanda zan tambaya hewani malam Sadeeq Allah ya tsare ni wallahi."

Kyaleta yayi ganin bilhakk'i bata son Sadeeq tun lokacin daya hanata atamfa, kallonta yayi yace.

"Ina baba yake?”

Tace "Baya nan."

Abubakar yace "Toh Inna fa?"

INdo tace "tana ciki."

"Toh jekiki ce zanzo mu gaisa da ita."

"Kai dacta Habubakar, kawai kashiga meye na tsayawa ai bazata hanaka ba."

"A'a Humaira ba'ayin haka a musulinci dole sai kinje kin gaya mata."

"Toh hikenan tunda baka yadda dani ba."

Tana magana tana shiga gida, yana jiyo sanda take gayawa Inna sak'on duk maganar da sukeyi yana jiyo su.

"Kai Inna toh meye na saka hijjabi dan nace miki dacta habubakar zai shigo. Lallai saban salo."

Rintsa ido yayi jin yadda INdon keyin magana da mahaifiyarta, lallai yarinyar nan indai yana sonta yadda yake so toh akwai jan aiki a gabansa. Dawowarta kawai ya gani beji motsinta ba, tana dariya tare da wasa da gefen mayafinta tace.

"Tace ka higo an hinfid'a maka tabarma a k'ofar d'aki."

Tana gaba yana bayanta har suka k'arasa ya zauna, daga bakin k'ofar d'akin Inna ta tsuguna suka fara gaisawa. Shiru babu wanda ya sake magana sai gasu Nafeesa sun shigo itada k'awarta suka gaidashi, Abubakar yace ma Inna.

"Inna dan Allah idan babu damuwa ina son ki bani aron su Humaira suyi min rakiya nan cikin gari."

Shiru yaji Inna tayi kafin can kuma yaji tace.

"Toh gata nan ai Nafeesah sai tazo kuje tare harda ita."

"Toh Inna na gode."

Tashi yayi yafita su kuma suka bi bayansa. A baya Nafeesa ta zauna yayin daya kwashe ledojin kayan yasa a k'asa wajan dazata saka k'afa tace ta shiga ta zauna sannan shima ya zagaya drive seat ya zauna tare da tayar da motar suka tafi 'yan kauyan sai gulmarsu akeyi.

Cikin garin Sumaila suka shiga INdo badai surutu ba sai labari takeyi musu sanyin A.c yana ratsata ga k'amshi a cikin motar ta kalli Abubakar tace.

"Dacta Habubakar wannan motar taka akwai sanyi karmuyi mura a bud'e gilahin."

Dariya yayi sannan ya mik'a hannu ya rage A.c ya juya yana kallanta itama shi take kallo yace.

"Humaira ya akayi ne?!"

INdo tayi dariya tana tafa hannuwa tace.

"Meye kuwa, wai Ina zaka kaimu ne hefanan tafiya muke..?"

Parking yayi a bakin titi wajan wani shagon saloon ya kalleta yaga sai kallon window take ya juya bayansa Nafeesa sai bacci take a hankali ya mik'a hannu zai ta6a kafad'un INdo sai kuma yayi saurin janyewa tare da bud'e k'ofar yafita. Zagayawa yayi ya bud'e mata ta fito yace su shiga cikin shagon abar Nafeesah tunda tana bacci suka nufi shagon ya tsaya ta glass inyamurar ta hango su ta fito cikin azama.

"Hey!good evening sir how are you.?!"

"Fine madam how is your business."

"Fine..fine oooh."

INdo tabisu da kallo sai faman tabe baki takeyi ta samu sumintin gurin ta zauna tana kallon titi. Saidai Sadeeq ya gama gayawa madam Gloria abinda za'ayiwa INdo sannan ya kalleta yace.

"Yauwa toh Humaira tashi ku shiga ciki."

INdo ta kalli madam gloria cikin mamaki ta maida kallonta gurin Abubakar tace.

"Mezai kaini wajan arniya dacta Habubakar? Arniya cefa kake cewa naje gurinta, me zata min...?!"

Ganin yadda takeyi ne yasa hankalin Abubakar tashi har mutane sun fara taruwa da k’yar ya satayi shiru yace mata.

"Kayanki zata baki amma tunda bakya so zomu tafi gida."

Da sauri ta nufi madam guloriya tana cemai. "Yo toh ai kaine bakayi min bayani ba."Gloria na gaba tana bin bayanta Abubakar ya girgiza kai sannan ya koma wajan mota yana jiran fitowar Gloria .

INdo kuwa suna shiga gurin taga abubuwa birjic ga manyan madubai ta kalli fuskarta sosai sannan ta fara gyara kwallin daya zazzago mata wajan kumatu Tese yarinyar Gloria ta cewa INdo.

"Sister come and seat here."

Sam INdo batasan da ita ake ba Tese ta kuma yi mata magana still INdo bata juyo ba Tese taja tsaki tare da zuwa ta janyo hannun INdo tare da zaunar da ita a wajan wankin kan sai masifa take da turanci ita kuma INdo tana Hausa.

Cige d'ankwalin Tese tayi taja wani uban tsaki ganin ko tsefewa batayi ba, gashi Mommy d'inta tace tabita a hankali dan wanda ya kawota yace zata iya guduwa. Kibiya tad'auka ta tsefe mata gashi akwai laushi da tsayi saidai babu cika gashi kuma jah ne. Mayukan wanke gashi ta d'ebo sannan ta janyo kan INdo ta malala mata sai mita takeyi har aka gama Madam guloriya ta kuma shigowa hannunta d'auke da riga da takalmi wanda Abubakar ya bata yace abata tasa ayi mata kwalliya.

Lokacin da aka saka kan INdo a dryer taji zafi sai ta saki wani uban ihu wai zafi, Madam Gloria tazo tana d'anyi mata wasa tare da takura mata har aka gama kannan yayi kyau gashi an tura mata shi yayi baki Tese ta nuna mata bathroom a shagwan ta nuna mata tace tayi wanka, INdo tayi da sabulai masu k'amshi gashi ruwan d'umi sannan ta fito sanya da kayan data cire babu wanda ya kulata Tese tayi mata kwalliya sannan aka bata doguwar rigar suka ce ta saka. Duk bayanin da sukeyi mata toh da hannun suke nuna mata tamkar wasu bebaye.

Wata irin had'add'iyar abaya ce pink da belt black sai kwalliyan ma black ta jikin rigan, fitowa tayi daga d'akin bayan tasa saidai jikinta babu bra madam Gloria ta tambaye ta bayan ta nuna mata ta jikinta kasan cewar itama INdo akwa breast d'in ta turo baki tana k'unk'una da alamar dai batada ita.

Babu kunya madam Gloria tafita wajan Abubakar yana zaune suna hira da Nafeesa tace k'anwarsa batada bra amma suna siyarwa ya bada kud'in. Abubakar kunya ta lullu6esa yace toh abata zai had'a a cikin kud'in gyara sannan ta koma aka cire dai-dai size d'inta ta saka suka d'aure mata belt d'in sai ta koma tamkar ba wadda ta shigo d'azu ba. Tese ta sa mata veil bayan ta jera mata ribbon INdo tayi d'as da ita tamkar ba INdo malam Hamza ba.

"Wowww nawawoo see this girl ooooh, you look so beautiful my daughter."

Ita kanta INdo data kalleta a cikin madubi saida ta sake ta6a fuskarta dan a tunaninta ba ita bace, Madam Gloria ta fesa mata turaruka sannan ta kamo hannunta suka fito Tese sai dariya takeyi. Abubakar na ganin sun fito ya mik'e yana kallon INdo k'irjinsa na mugun bugawa, ita kuma ta kasa kallonsa domin wata irin kunya ce da nauyinsa suka dirar mata a lokaci d'aya. Da kyar Abubakar ya iya kallon madam Gloria yayi mata godiya tare da zaro 15k ya mik'a mata ta k'ar6a sai k'ara kod'a INdo takeyi shi kuma ya juya tare da bud'e mata k'ofa ta shiga ta zauna ya rufe.

Cikin tsananin mamaki Nafeesa ke zuro kai tana lek'en fuskarta kafin tace.

"INdo..! Koba kebace ne? Nashiga uku, wallahi kece dan ga fashin gohi nan."

Banza da Nafeesa INdo tayi domin ita kanta tunda aka haifeta bata ta6ajin ta a wani irin yanayi na cikar kamala ba irin yanzu. Abubakar ya kalleta yana lek'en fuskarta shima yayi murmushi tare da cewa.

"Humairah kinyi kyau sosai."

K'irjin INdo ya kuma bugawa kanta ya fara sarawa jitakeyi tamkar an sauyata gabaki d'aya, bakinta kuwa ji takeyi tamkar ansa zare da allura an d'inkeshi ta kasa cewa ko uffan ta kuma kasa kallonshi.

Kunna motar yayi suka fara tafiya sai magana suke mata shida Nafeesa amma tayi shiru, farin ciki takeyi yau gata cikin rigar da ko a cikin mafarki bata ta6a zaton zata sanya taba ga takalmi d'an ubansu tayi shigar da duk kauyen Sani babu wanda ya ta6ayin irinta. Shin mezata cewa dacta habubakar akan wannan abun dayayi mata, shida ba yayanta ba, ba wani nata ba a'a d'an uwane a gurin wani malamin su..!

Saida ya tsaya a wani shago ya siyo musu abubuwan kwalan da makulashe sannan ya nufi kauyen Sani. Daga shi sai Nafeesa kawai suke magana amma ita batayi rigar jikinta kawai take kallo tanajin ina ma salele zaizo yau ya ganta ta zama sabuwa.

A k'ofar gida ya tsaya Nafeesa ta fito ya bata ledojin INdo ma tazo zata k'ar6a ya girgiza mata kai sai da Nafeesa ta dawo ya bata harda ragowar kayanta sannan ya kalleta yace.

"Humaira kina son yin karatu..?!"

Shiru tayi tana faman muzurai, a zahirin gaskiya batada wani sha'awar yin karatu domin tun farko dama batasa shi a cikin tsarin rayuwar taba.

Gani takeyi ma yanzu wace makarantar zatayi dan tafi k'arfin tsefawa sabida duk mate d'inta sunyi candy dan haka ma ta kuma cire san makaranta a zuciyarta. Kallonta yayi yaga yanayinta ya canza ya ciro wayarsa yana yi mata photo wannan kuwa harda su style, ya d'an matsa kusa da kujerarta tare da cewa.

"Matso toh muyi photon tare."

INdo ta matsa suka kusan had'e fuska yayi musu selfie kusan sau biyar yana d'aukar su gaba d'aya sunyi kyau musamman Abubakar dayasan shika-shikan iya selfe. Agogon tsintsiyar hannunsa ya kalla biyar sauran minti uku yace mata.

"Humairah zan tafi sai na dawo please take care."

Murmushi kawai tayi mai sabida bata san abinda ya fad'a ba bayaga (zan tafi sai na dawo). Ya zaro 5k ya mik'a mata tana kallonsu ta wutsiyar ido tana son k'ar6a tana jin wani iri ya d'ora mata a kan cinyarta ta d'auka zata bud'e k'ofar yayi saurin rufewa tare da cewa.

"Humairah baki min godiya bafa zaki tafi, haka akeyi daman."

Tayi saurin rufe idanu tare da cewa.

"Kayi hakuri inata son yima na manta, angode Allah ya k'ara bud'i."

Yace "yauwa kokefa harnaji dad'i, duk wanda yayi miki kyauta ki dinga ce mai angode kinji ko?!"

Tace "Toh zanyi sai anjima yaushe xaka dawo garin mu?!"

Da sauri ya kuma kallonta jin tana neman ya dawo, cikin wata irin murya yace.

"Humairah kina son na kuma dawowa?!"

INdo ta d'aga kai alamar eh yayi murmushin jin dad'i sannan yace.

"Toh shikenan wani satin zan dawo amma ki dinga kwalliya gashi can na siyo miki kayan kinji..?!"

"Toh Nagode ka kaida gida."

"Zasuji amma bakice nagaida malamin kuba."

Tace tana yatsina fuska.

"Ai bayida kirki da kaine bakada kirki amma yanzu shine bashida kirki."

"Toh kiyi hakuri ya dena kinga 'dan biyu nane."

"Naji na dena kace ina gaidahi."

"Zaiji a gaiheda Inna da baba."

Yafad'a cikin kwaikwayon maganarsu, ta fita daga motar lokacin su Uwani halilu sunzo gulma, shi kuma yaja motarsa yabar unguwar zuciyarsa na kudurta mai son auranta.









*HAJJA CE*👈
[7/3, 10:06 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥

A true life story

Na

*K.A.S Precious Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*VOTE me on wattpad @Hajjac*

*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu


_Shafin yau naki ne *Yayya Nabeelah* ina miki fatan alkairi aduk inda kike #much_😘


Page *15*

Da sauri ta shiga gidan su Uwani da Maryam na biye da ita lokacin su duk da yaransu sunyi aure,tana zuwa taga Nafeesah tayi d'aya-d'aya da kayayyakin cikin ledar su Sagiru da shehu sai shan sweet da chocolate sukeyi INdo tayi kukan kura tare da fad'awa kan kayan tana yiwa Nafeesah masifa.

"Dan uwarki wane d'an iskan ne yace idan kin higo ki bud'e min kaya na? Kodan kin rakani hine zaki dinga min hihigi cikin abubawa na, ai danni aka siyo. Bani kayana banza kawai sutofes (stupid)."

"Ke INdon nan wallahi masiffiya ce, ba mubiyu ya siyowa kayancin ba, ai na san kayan sawar naki ne amma ai daya higa shigon nan ya dawo cewa yayi idan mun dawo muhya. Ke wallahi rintoh gareki."

"Ah Kakan cewa yayi mu raba. ke waima wayake son ya dinga yiwa mutunci? Ni ko keh?"

"Oho ba'a sani ba, kuma yasin komai rabahi za'ayi dai-dai."

Sagiru daya hango wata alawa k'ark'ashin k'afar INdo yayi wuf ya d'auke tare da 6arewa yasa baki da sauri dan karta juyo yana cewa.

"Wallahi kuwa Nafi karki sake ta cuceki a raba shi ki fara d'auka."

Da sauri cikin bala'i wanda har rufe mata ido yake yi tace,

"Toh munafiki algungumi zugata, wallahi hekaja ink'i rabawar banza kawai..."

"Oho dai a raba mugani."

Ya kuma fad'a cikin tsokana tayi mai banza tare da maida kayan da jakar kayan kwalliyar ta cikin leda sannan ta kalli Nafeesah tana hararart tace.

"Ki za6a raban Allah za'ayi ko kuma raban gaskiya kike so..?!"

Nafeesah ta murgud'a baki tare da cewa.

"Rainin hankali, toh raban Allah da ma'aiki zaki yi mana babu wani rabon gaskiya 'yar latsi..!"

Suna kallonta saida ta fara ware komai daban sannan ta kwashi me yawan ta turawa Nafeesah kad'an tace.

"Gashi nan."

Nafeesar ta kwaso wata uwar ashariya ta zubeta sannan tace.

"Idan kin isa kice ba uwatace ta haifeni ba kanbala'i..."

Inna na kallonsu tun shigowar INdo k'irjinta ya fara bugawa kanta yana juyawa ganin yadda 'yar tata tadawo sabuwa, Allah yasa dai ba wani abun yayi mata ba ko yake son yimata ya fara kowa mata shiga masu kyau. Duk fad'an da suke yi ta kasa cewa dasu uffan bakinta fal addu'a da fatan Allah ya cire mata wasi-wasin da take yi akan lamarin Abubakar.

"Gaskiya kema INdo kinso kanki dayawa, taya ance kiyi rabo tsakani da Allah sai kiyi yadda kikaga dama dan mugunta..."

Cewar Maryam Aliyu tana bawa d'anta nono. Can Sagiru ma yace rabo beyi ba Nafesah karta yadda ita kuma Uwani tana bayan INdo dankar sai an gama fad'an ta hanata komai. INdo ta matse nata tsakanin cinyoyinta tare da cewa.

"Saida na tambaye ki rabon Allah ko rabon gaskiya kika ce na Allah toh ai Allah baya rabawa dai-dai sai dai yabawa wannan meyawa ya bawa wani kad'an, alal misali kinga ai Maryam ke mijinki yafi na uwani kayan gona kuma dacta Habubakar shima yafi baban mu kud'i ko ba haka ba..?!"

"Oho miki banza muguwa kuma bari ya dawo saina gaya mihi."

"Sai ki fad'a ko'a jikina wallahi."

Ta fad'a tana jan tsaki. d'aya-d'aya ta bamawa su Uwani, babu wanda beji haushinta ba sabida ko 'ya'yansu bata bawaba suka tashi suka tafi. Kallon Inna INdo tayi ganin tayi tagumi yasa tacewa.

"Inna kizo kiga kayan da ya kawo min, ya kaini aka sani a inji mezafi aka gasa min kai aka dinga hyafamin wasu abubuwa akaina Inna jibi yadda gahina ya zama.."

Tana magana tana bud'e kanta, gabaki d'ayansu suka kalleta baki bud'e cikin mamaki Inna tace.

"Nahiga uku ni Maryamu 'yarnan kanki nekuwa?"

"Hehehe kaji Inna da wani batu, toh inba nawa bane jikin kuma nawaye kema dai."

"Ta6 lallai INdo anyi klin kinga yadda aka nannad'a miki gahinki kamar na indiyawa."

Cewar sagiru yana kwakulo chocolate d'in daya mak'ale jikin jajayan hak'oransa. Banza tayi mai taci gaba da nunawa Inna kayayyakin daya siyo mata, Inna tayi godiya cikin rashin nuna kyashi ga uwa a wani bigire da wasu 'ya'yan keyi INdo ta d'akko wani flat shoe tare da janyo k'afar Inna tana cewa.

"Inna saka wannan mugani kozai yi miki."

Tana saka mata kuwa yayi cif-cif a k'afar Inna INdo tayi dariya tare da fad'in. "Inna k'afarmu d'aya Ashe, toh nabar miki wannan innata kema kidinga sakawa idan zaki unguwa ko kauyen ku."

Da sauri Inna ta zare takalmin daga k'afarta tare da rik'o hannun INdo tace. "A'a 'yarnan barshi na gode miki Allah yayi albarka amma bazan k'ar6a ba, sabida ke aka bawa tayaya zan k'ar6e miki ya gansu a jikina a'ah."

"Toh danya gani kuma Inna heme? Zece kibahi ne? Kawai ki k'ar6a nina baki ai yariga ya siya min."

Ganin ta dage yasa Inna ta k'ar6a tare dayin godiya sannan INdo ta shiga da kayanta cikin d'aki ta zuba a cikin Ghana must go d'inta. Tashi tayi tafita zuwa gidan Rukayya, duk inda tayi mutane sai sunyi mata magana, maza kuma su tsayar da iya amma sai hura anci take kanta a d'age tana 6are alawa tana sha hankalinta kwance duniya tayi mata sabunta jinta takeyi tamkar akan iska.

****

Qarfe 2:35pm ya fito daga office d'inshi, sauri yake yaje gida yayi wanka dan yana son zuwa sani a yau. Da sauri yafita yana zuwa gida wanka yayi tare da shiryawa cikin k'ananun kaya white jeans da black shirt me dogwan hannu ya d'ora facing cap dama ya riga yayi sallah yaci abinci a office dan haka ledar d'in kunan daya bawa Hawwa ta d'inkawa INdo su ya d'auka yafita sai bulala k'amshi yake tamkar anyi 6arin turaren.

Passenger seat ya ajiye kayan sannan ya tada motar ya wuce domin yau kwanansa goma sha hud'u rabansa da kauyan Sani, yayi missing d'in INdo ba kad'an ba domin babu waya a hannunta.

Yana shiga unguwar yara suka yayyame shi yayinda suke ta mik'a mai gaisuwa, yau kam suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login