Showing 48001 words to 51000 words out of 85627 words

Chapter 17 - MUSAYAR ZUCIYA COMPLETE BOOK by Hajja Ce.txt

Hajja Ce   

14 Sep 2025

49

Hamza, tsabtar kyawun kwanon da yadda ruwan ciki yake garai-garai abin sha'awa shine ya sanya su Haleema shan ruwan gidan.

Zama Inna tayi suka sake gaisawa Mama tayi gyaran murya bayan tace su Haleema su fita, suna fita tayi murmshi tare da cewa.

"Dama munzo ne mu gaida ku sannan zamu tafi da Aisha za'ayi mata wani gwajin ciki sabida shi marigayi yace yasa mata wani abu wanda koda tana da ciki toh bazata dena jinin al'adaba toh yanzu shine zamuje a duba agani kar abar mata abu ba'a saniba ko yana amfani nan da kwana biyu za'a dawo da ita kinsan likitocin nan da k'ak'ale."

Mama ta kifa Inna domin yanzu so take ta tafi da INdo can. cikin rashin damuwa Inna tace "Allah sarki ai babu komai an zama d'aya bari na aika a k'ira malam dama shine ai ke hanawa da yaji yadda takeyi idan taga shi d'an uwan marigayin."

Fitowa tayi ta lek'a waje ta samu yaro yaje ya k'ira Malam Hamza a gurin sana'ar Sa. Tare da ila suka dawo tunda yaga mota yasan bak'i sukayi yana shiga kuwa Inna tace Maman marigayi ce tazo, d'akin ya shiga suka gaisa da Mama Inna kuma ta kawo mata dambu ta kaiwa su INdo ma. A nan Mama ta kuma tsara malam Hamza yayi jim sannan kamar bazai yadda ba sai kuma yayi murmushi yace.

"Toh ai dama ni hajiya dalilin daya sa na kafe kan cewar saita dawo nan, gani nayi yadda shi Saddiqu suke tsananin kama dashi marigayin. Sannan tun a gurin gaisuwar naji ana zance ta fara rik'esa tana cewa be mutu ba harma sun fara samun sa6ani itada Saddiqun wannan dalilin yasa nace dole abani ita mu dawo nan zaman lafiya hajiya ai yafi zama d'an sarki. Amma yanzu tunda akwai wani dalili wanda kuma kune kuke da hakk'i akai toh saita shirya ku tafi idan an kammala yi mata sai a dawo da ita ai duk an zama guda.."

Wani farin ciki ya lullu6e Mama sai ta share hawaye gani takeyi tamkar Abubakar d'in take yiwa a zahiri. Malam Hamza ya dinga bata hak'uri kafin ya tashi ya fita, gurin su INdo yaje yace ta shirya zasu tafi da ita.

Wanka Mama tace tayi sannan tayi tasa kaya Mama ta girgiza kai domin duk kayan na kwalliya ne babu wanda aka ce na takaba ne dole idan sunje tasa a dinka mata wasu marasa style. Babu wanda yasani don Mama tace kar a fad'awa kowa kawai idan an tambaya tana Ina suce tana gidan su marigayi amma karsu sanar da kowa akwai abinda za'ayiwa INdo suka tafi cikin farin ciki da fatan alkairi.

*****
Tunda suka maida ita Mama ta dakatar da Sadeeq zuwa gidan tace koda itace batada lafiya bata yadda ya shigo ba bare hakan nan. Haka kuka Mama ta cigaba da kula da INdo har aka yi arba'in d'in marigayi Abubakar sannu a hankali kuma Mama tana bibiyar al'amranta na addini tana gyara mata sannan tana k'ara nusar da ita abubuwa wad'anda mafi akasari suke k'ara tunawa INdo mijinta soyayyarsa kuwa bata ta6ajin ta kankare koda d'igo d'aya ne, bata komai sai dai taci tasha tayi bacci, idan kuma su Haleema na nan sai suyi hira d'an turancin da suke yi jefi-jefi itama ta d'an fara tsintar k'ananun tana had'awa da wanda Dr yake yi mata sai dai dakyar take iya rik'ewa dan sai tayi ta rik'e kalma d'aya a kwana biyu ko uku sannan take sake fahimtar wata word d'in.

Kusan kullum sai Malam Hamza ya bugo musu waya tunda suka zo sadakar arba'in ya kar6i number abban su Sadeeq kusan kullum sai ya bugo musu yaji wai ko an cire mata abun sai suce a'a likitocin sun k'ara musu kwanaki da haka har INdo tayi watannin takabar ta wanda har lokacin Sadeeq baya shiga cikin gidan su dan ma Allah ya temake sa yana tafiya k'wara state dan wannan tafiyar tasa da Fateema sukayi sabida yana shan wahala.

Ana sauran kwana biyu INdo ta kammala takaba su Sadeeq suka dawo, Fateema ce kawai taje gidan shi kuma su Mama suka fita parking space suka gaisa ya juya ya tafi.

Ranar da INdo ta kammala takaba Abba ya k'ira Sadeeq yaje ya kaisa Sumaila suna zuwa ya samu malam Hamza bayan gaisuwa Sadeeq na mota a zaune ya bugawa Fateema waya suna hirar soyayyar su dan haka suke tamkar zasu cinye junansu Abba ya kalli malam Hamza yace.

"Toh malam Abubakar dai Allah ya d'auki rayuwarsa a lokacin da yake tunanin ya fara rayuwa, ya tafi yabar matarsa yarinya d'anya yau gashi Allah yasa ta kammala takabarta kamar yadda addini ya tanadar. A zahirin gaskiya ba wani abu da marigayi ya sanyawa Aisha a jikinta, me d'akina ce taga bazata iya barin muku Aishan ba hakan yasa tayi muku dabara kuka bata ita mu kuma duk muka had'e muku kai muka nuna cewar eh lallai haka ne abinda ta fad'a."

Malam Hamza yayi murmushi tare da cewa.

"Ai munyi mamaki har muna tunanin k'ila abin k'in fita yayi ashe soyayya ce tasa kukayi hakan ai bakomi alhaji mune da godiya da baku nuna kyama a garemu ba, Habubakar shine sila hakan yasa bazan gajiya dayi masa addu'ar samun ni'ima a cikin makwancinsa ba, alhaji Allah yajik'ansa yayi masa rahama mun gode madallah."

"Ba komai malam Aisha ma ai 'yata ce, sannan kuma babban abinda ke tafe dani shine. Kaf 'yan uwana da masu d'akina suna tausayawa Aisha, yarinya ce d'anya yau gashi Allah ya jarabce ta idan aka barta zata Shiga layin zawarci, sun had'u sun had'e kai wajan ganin bazasu iya bari matar d'ansu d'an uwansu abokinsu ta zauna a haka ba suna ganin yi mata hakan kamar basu rufawa Abubakar asiri ba hakan yasa ko wannen su yazo min da k'ok'an barar su na cewar mezai hana a mayeta da abokin haihuwar sa, ma'ana mu had'asu aure da Sadeeq domin rufin asirin mu gabaki d'aya sannan munsan Abubakar zai yi alfahari da wannan abun."

Malam Hamza yayi shiru kafin yaje ya k'ira Inna ya kuma k'ira amininsa malam kallah suka zauna, Abba ya kuma maimaita musu zancen auran INdo da Sadeeq Inna dai bata ce komai ba tace sune maza masu d'aura aure dan haka ita addu'a ce kawai tata. Bayan Inna ta koma gida malam Hamza ya amince wasu mutanan suka zo a gurin aka d'aura auran INdo da Sadeeq Abba ya bada sadaki dubu ashirin Sadeeq yana mota a zaune duk wainar da aka toya besani ba har Abba yayi sallama da mutanan garin ya shiga mota Sadeeq d'in ya ajiye wayar suka tafi...

#MZ
#Fan's
#luv-all










*HAJJA CE*πŸ‘ˆ
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *βš—βš—MUSAYAR ZUCIYA...βš—βš—*
β™₯β™₯
β™₯
A true life story

Na

*K.A.S Precious Hajja ce*πŸ‘ˆ

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*πŸ’‘
(Home of expert & perfect writer's)

*VOTE me on wattpad @Hajjac*

*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu


Page *25*

Har sukaje gida Abba be sanar da Sadeeq ba, suna zuwa Abba ya shiga gida shi kuma Sadeeq daya k'agu yaje gida ya juya kan motar ya tafi. Abba na zuwa fuskarsa cike da fara'a ya cewa su Umma.

"Toh hajiya A'i an d'aura aure yau."

"Alhamdulillah Allah ya sanya musu albarka ya kauda fitina ya basu zaman lafiya."

Cewar Umma nan da nan fa gida ya cika da murna INdo kuwa bacci take a lokacin sai bayan da ta farka ne Mama tace.

"Aisha jeki wanka kizo kuje gyaran kai."

Da sauri INdo ta mik'e cike da murna domin tunda ta dawo gidan bata sake koda lek'awa k'ofar gida ba, sam sun hanata ko unguwa Mama zasu sai ta kafa mata doka akan idan ta kuskura ta lek'a waje, yau gashi zata fita kusan kwananta d'ari da takwas raban da ta kalli waje bare taga abinda yake wakana. Ta yi kyau tayi haske fatar jikinta tayi luf-luf sannan tayi k'iba da yake hankalinta a kwance yake suna kula da ita sosai dan ko 'ya'yan gidan basu kaita jin dad'i ba.

Wanka tayi tana fitowa taga saban d'inki an d'akko mata a can gidan Abubakar da takalmi da jaka da mayafi su d'ankune sark'a da kayan kwalliyar su Haleema. Zama tayi tana kallon kayan tare da shafa jakar da takalmin sai hawaye a fili tace.

"Allah sarki dacta kai ka saimin su.."

Tashi tayi tasa kayan sai ga Mama ta shigo cikin wasa tamkar ba suruka ba tace.

"Toh wa kika tambaya da kika d'auka kika sa? Idan kuma nawa nefa..?!"

Dariya INdo tayi tana rufe baki tace,

"Ai Mama ina ganin jakar na gane su, lokacin da zai kaimu gidan abokanansa da nad'akko zan rataya yace min basu yi match da kaya na ba na ajiye ta."

"Allah sarki Abubakar Allah yayi masa rahama Allah yayi baxaku yi tsawon kwanaki tare ba."

Cewar Mama tana d'akko mata humra ta ajiye mata a kusa da kayan tana cewa.

"Daga yau zaki iya sanya komai Aisha sai dai zaki ci gaba dayin abubuwa irinna matan aure domin yanzu kema Matar aure ce."

Sam INdo bata gano inda zancen Mama ya nufa ba, a tunaninta tunda ta ta6a aure toh zata ci gaba da suturce jikinta da kuma d'ora mayafi aka. Tana gama shiryawa Mama ta bata kud'in gyaran kai tasa suka tafi dasu Haleema.

Lokacin da ta fara zura k'afarta a waje ji tayi tamkar yau aka haifeta. Wata ajiyar Zuciya ta sauk'e tare da kallon ko'ina na wajan taga mutane kowa yana harkar gabansa, wasu kuma da suka santa suna sake yi mata gaisuwa tana amsa musu har suka kai bakin titi Haleema ta tare musu napep suka shiga.

Shagon saloon suka shiga sun d'an jima sannan suka fito suka dawo gida. Da dare bayan Abba ya dawo ya k'ira Sadeeq sannan ya k'ira INdo, Mama da Umma duk suna zaune a d'akin. Cikin muryar ta med'an k'arad'i tayi sallama tare da shiga ta zauna tana gaida Abba.

A hankali Sadeeq ya d'ago ya kalleta sannan ya kawar da kai cikin ransa yana tambayar dama tana da ladabi ko kuwa har lokacin mutuwar mijinta na jikinta ta dai kusa tafiya shima ya samu 'yancin shiga gidan ubansa.

Abba ne ya k'ira sunansa ya amsa tare da kallonsa abban yace.

"Toh Sadeeq kamar yadda ka sani tagwai d'inka Allah yayi masa rasuwa ya bar matarsa, yau kuma Allah ya nuna mana cikar wa'adin takabar ta kamar yadda addini ya d'ora mata. Sadeeq kaine mutum na farko daya kamata ya rufawa matar d'an uwanka asiri ka dubi halin da zata shiga idan ta koma garin su ka kuma dubi k'ank'antar da tayi a matsayin bazawara bawai munaja da ikon Allah bane a'a duba da yadda rayuwarta zata fad'a yasa muka yanke wani hukunci akai."

"Babu komai Abba ni dama tuni nayi alk'awarin zan dinga tura mata kud'i sannan zan dinga yi mata abinda take buk'ata idan har befi k'arfina ba dama jira nake ta kammala iddar sai na tambaye ta abinda yak'e matsalarta."

Sadeeq ya fad'a ba tare da ya kawo komai ba dan sam beyi tunanin wani aure tsakaninsa da ita ba, Fateema yake so kuma ita ya aura baya tunanin zai yi *MUSAYAR ZUCIYA* da watanta nan gaba bare kuma nan kusa daga yin aure wata biyar.

"Toh Sadeeq ai wannan abubuwan daka fad'a koni zan iya yi mata shi, mu yanzu fatan mu ka rufa mata asiri a matsayin ta na mace me rauni kuma matashiya domin a d'azu da ka kaini Sumaila k'auyan su naje ne mun d'aura muku aure dakai da ita ka maye gurbin d'an uwanka...!"

A matuk'ar razana Sadeeq ya zaro idanuwa yana kallan Abban shi, zuciyar sace take rawa jikinsa na tsuma ya kalleshi yace.

"Abba wani auran zan kuma yi? Abba ko wata biyar ban cikasa ba ace na kuma yin aure? Tayaya zan iya zama da mata biyu Abba bayan yanzu nayi d'ayan? Abba matar twin d'in zan aura? Ya akayi mutuwa tayi min haka..."

"Kai ya isa haka karkayi min sakarci kaji ko? Idan baka aureta ba ya kakeso tayi bayan tana buk'atar temako da kuma mai lallashi da tausayawa a gareta...?!"

"Amma Abba yau yau d'innan fa tayi takaba amma ace ayau za'a aura mana aure ko fuskanta juna bamuyi ba? Abba ya Fateema zataji wannan labarin."

Ya fad'a tamkar wani maraya Abba ya wurga mai harara cikin 6acin rai yace,

"Da kuma ace kaine ka rasu aka ce Abubakar ya auri Fateeman zakaji dad'i ko kafison ta tafi ta auri wani bare..?!"

"Wallahi Abba gara ta auri bare haba-haba sai kace jira, dan Allah Abba kuyi tunani ni wallahi..."

Bek'arasa ba Abba yayi saurin katse sa ta hanyar cewa.

"Toh shikenan sakarta ni sai na aureta shikenan hakan yayi maka.?!"

Cikin tashin Hankali Sadeeq ya kalli mahaifinsa sai zuba uban gumi yake baki na rawa yace.

"Innalillahi wa'inna'ilaihir raji'un Abba ai babu aure tsakanin ku gara nid'in."

"A'ah aini tausayinta nakeji Sadeeq kuma abinda zanyiwa Abubakar kenan yasan nayi mai kara ka sake ta sai na aureta ko kuma uncle d'inku Ahmad."

"A'a Abba dan Allah ka rufa mana asiri na kar6i auran Allah yajik'an m twinnie yasa can tafiye masa nan."

Duk suka amsa da amin banda INdo wadda tunda taji maganar da akeyi tayi kicin-kicin zuciyarta banda bugawa babu abinda takeyi wani rad'ad'i na shigarta. Abba ya maida hankali wajan ta ya kalleta cikin kulawa yace.

"Aisha muna fatan bamuyi miki shishigi a cikin rayuwarki ba, muna fatan zaki yadda da auran Sadeeq gashi nan komai nashi iri d'aya ne dana marigayi..."

Da sauri INdo tace "A'ah Abba wallahi ba halinsu d'aya ba koda can kafin mu saba."

Abba ya kalli Mama itama shid'in take kallo sannan tace.

"Aisha ai shima Sadeeq zai miki abinda marigayi yayi miki kiyi hakuri idan kuma bakya sonshi shikenan ai ke yanzu babu batun yi miki auran dole za6i gareki a wannan karan ma. Dama munyi haka ne dan karki shiga damuwa ko da idan kinga Sadeeq d'in."

Shiru tayi batace komai ba sukayi-sukayi tayi magana amma tayi shiru Umma tace.

"Toh da alama ta yadda Allah ya bada zaman lafiya."

Tashi Sadeeq yayi ya fita Mama da INdo suma suka fita aka bar Umma kasan cewar itace da girki ranar.

Dakyar ya iya kai kansa gida, lokacin daya shiga Fateema na kwalliya cikin bedroom taji shigowarsa amma bata ga ya shigo d'akin ba, shi kuwa guri ya samu a falo ya zauna kan kujera tare da dafe k'irji kanshi na barazanar fashewa ya tarwatse.

Fateema ce ta fito cikin shirin bacci tayi kyau ta kuma fari kai da kaganta kasan tana cikin kwanciyar hankali, k'arasawa tayi kusa dashi ta d'are kan cinyarsa tana k'ok'arin d'ago mai kai. Janyo ta yayi jikinsa da k'arfi tare da sanya ta a k'irjinsa ya matseta da hannuwansa tamkar zai maida ita ciki ita kanta dakyar take numfashi zuciyar ta cike da mamakin yadda taganshi.

"Wayyo Allah baby zaka karya ni."

Ta fad'a tana k'ok'arin kwatar kanta sabida ba k'aramin azaba takesha a matsar ba. A hankali ya sassauta mata rik'on dayayi mata cikin sanyin murya Fateema ta kallesa tace.

"Baby wai meyake damunka, haka kashigo fa ba sallama kuma naga duk jikinka a sanyaye meya faru..?!"

"Bakomai kinci abinci dai ko?!"

Ya tambaya yana shafar cikinta, kad'a kai tayi tana kallon shi ya lumshe idanuwa tare da kwantota jikinsa yace.

"Toh why?!"

"Baby kasan dai bana iya ci harsai kana nan, meyasa yanzu kake tambaya na...?!"

"Kinsan ai bana son kina zama da yinwa, kinga gobe ina da lecture 9 to 11 kuma gashi banajin dad'in jikina ya zanyi ne.."

Fuskar sa ta tallafo sukayi kallon cikin ido ta sakar masa murmushi tana shafar gashin dake ha6arsa tace.

"Yanzu ai lokaci bek'ure ba goma da rabi saura minti uku kayiwa class captain waya kace musu bazaka samu damar zuwa ba suyi hakuri zaka samu wani time d'in sai kuyi musu amfani dashi..."

"Ai kuma baby ban musu lectures bafa tunda aka koma gashi har an fara tambaya na exam questions, zanje ko abu d'aya ne nayi musu tashi muje kici abinci."

"Inci abinci ko dai muci abinci?!"

Ta tambayesa tana sake lafewa a jikinsa, suna zama yana cewa.

"Kinsan Abba neya k'irani so munci abinci tare dashi."

'Dan hararasa tayi tare da cewa "Ai kasan dai nima nawa yana jiranka dan haka sai kaci babu wani batun kunci da Abba ko zakayi amai kuwa."

Shi sam yarasa ma mezai yi yinwar ma bajinta yake yi ba shi yasa yace mata haka amma dan karta shiga damuwa sai yace.

"Toh baby na ya zanyi amma nasan yau babu abinda zan iya tabuk'awa."

Shi dai dakyar ya samu yaci duk tunanin yadda zai 6ullo mata yake yi a cikin zuciyarsa, sai da ya tabbatar taci ta koshi sannan ta rakashi yayi wanka ta bashi sleeping gown ta maza yasa sannan suka bi lafiyar gado. Kamar yadda ya sabar mata koda bazai yi komai ba toh sai sunyi wasa haka yauma har sai da yaga ya kwantar da kanta kan k'irjinsa zata yi bacci ya bud'e baki dakyar ya k'ira sunanta.

"Zarah..."

Tayi jimmm jin yadda ya k'ira tsohon sunan da yake kiranta dashi tun suna saurayi da budurwa, can dai ta amsa mai tana shafar k'irjinsa shi kuma yana shafar himilin gashin kanta domin akwai suma yace.

"For example nine na rasu ba Abubakar ba idan aka ce ki auresa zaki iya..?!"

Ya k'arasa maganar yana d'an d'ago mata kai. Shiru tayi na tsawon lokaci tana tunanin abinda yasa shi yi mata wannan tambayar marar dad'in ji bare sauraro, sai da ya sake tambayar ta sannan ta numfasa dakyar tace.

"Haba baby ya zaka min wannan tambayar tunda dai bakai ne ka rasun ba?"

Yace "Eh so nake naji zaki yadda idan aka ce ki auri twinnie d'ina ya zakiyi."

"Gaskiya bazan auresa ba haba ai bashi na aura ba."

"Toh idan aka tursasa kifa ko aka aura miki shi ba tare da kin sani ba ya zajiyi..?!"

"Ta6 d'i wallahi baby sai ya sakeni uhm'um ni dan Allah ka dena yin irin wannan tunanin please."

Jikinsa ya sake janyo ta yana shafar bayanta, so yake ya sanar da ita yau basai taji a bakin wani ba amma ya rasa hanyar fad'ar ya dai daure yace.

"Toh idan hakan ta faru tunda ni bakya sona mutu aka ce na auri Humairah ya zakiyi?!"

"Bama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login