Showing 6001 words to 9000 words out of 85627 words
ma k'arya yake mata shine zata zo ta k'ure sa dan tsabar ba ta da kunya. Fuskar sa a murtuke ya kalleta yace,
"You're very stupid."
Tana dariya cikin nishad'i tace,
"Sanki u malam Sadeeq, (thank you) wallahi shi yasa kake birge ni sabida ka iya turanci mai kyau da dad'i. Amma dan Allah malam ka d'an fassaramin abinda ka fad'a da hausa he nima in rik'e gurin na iya sosai..."
"Zaki bar gurin nan ko sai na 6allaki... mara kunya fitsararriya kawai.."
Ya fad'a cikin d'aure fuska. tayi baya-baya tana kallansa tare da kama ha6ar ta tace,
"Kai malam! masifa, daga tambaya sai cibi ya zama k'ari shi kuma k'ari ya zama k'ababa. na tafi kuma ba zan je makaranta ba a-he, sai ayi kuli-kulin tara sisi dani.."
Ta yi maganar tana tafiya da baya da baya har ta shige lungun gidan su Maryam. tsaki yayi ya koma cikin gida yayi kudurin sai ya gyarawa 'yan makarantar zama. kowa tayi wa dan ba ta je makaranta ba oho mata. yara sai rashin kunya basu san komai ba dak'ik'ai zai nuna musu shima bashi da mutunci. Ranar haka ya wuni yana kunci jefi-jefi yakan yi tsaki har dare yayi be fita ba sabida takaicin Indo da sanya idon 'yan gari domin fita dubu shiga dubu sai sun kalle shi gashi ya tsani saka ido cikin lamuran sa.
Washe gari da yaje makaranta Indo bata je ba yaga ashe da gaske take yi, still wata washe garin tayi nan ma babu labarin Indo sai ranar juma'a yana tsaye wajan black board yana koyarwa kawai yaji ana magana a taga, juyawa yayi sai yaga babu kowa domin da taga alamar zai ganta sai tayi saurin yin k'asa, dan haka ya cigaba da abinda yake yi. Can ya kuma jiyo kus-kus yayi a hankali ya kalli gurin caraf suka had'a ido da Indo tana cillowa Sa'ade wani abu a leda, dariya ta sakar masa ya k'arasa bakin tagar yana kallonta. Sanye take cikin house wear hannunta rik'e da faranti an jera kallik'ak'au da yajin masau da alama shi ta cillawa Sa'ade ya had'e girar sa tare da cewa.
"Zo nan..!"
Ita yake kallo amma sai ta juya wai ko zata ga wanda yake kira amma sai taga babu kowa sai ita, dashare mai baki tayi tare da d'an matsawa kad'an ba sosai ba tace.
"Gani malam."
"Jeki zaga yo ta k'ofa."
Ya fad'a, Indo ta tsuke fuska tare da cewa.
“Malam ai ba zuwa nayi ba yau d'in ma tallah nake yiwa mak'ociyar mu. Kasan idan na siyar mata mawa zata bani?”
Yayi mata banza ganin ita yake kallo yasa ta juyawa ta dafe abubuwan cikin farantin ta ruga da gudu dan ba zata yadda taje ya hana ta fitowa.
Kai ya girgiza tare da komawa ya ci gaba da yin aikinsa kuma a kwanaki biyun alhamdulillahi suna ganewa, tamkar dama Indom ce ke hana su rashin fahimta. Yana gamawa ya fita ya koma ofis haka ya dinga ci gaba da koyar musu har aka kusa fara jarabawa wadda daga ita zasu wuce j.s 2 amma Indo bata sake zuwa ba shima har ya manta da ita har ya Saba ma idan yana kiran suna ya samata absent.
Ana gobe za'a fara jarabawa Indo ta dawo makaranta. washe gari aka fara musu sai da suka yi jarabawa hud'u sannan a ta biyar d'in zasu yi English language wato subject d'in malam sadeeq. Kasan cewar tun da aka fara beje ajin ba sai yau da za'a yi tashi jarabawar kuma dole sai yabi aji-aji ya kuma yi musu bayani sannan. Tare da Abubakar suka shiga domin lokacin yazo abinsu gwanin ban sha'awa, zasu gaida su Sadeeq ya hana dan karsu yi hayaniya, can k'arshen aji INdo take ta duk'ufa sai satar amsa take yi cikin littafin Ayuba mati sabida ita bata da ma littafin bare tayi karatu.
Tsayawa Sadeeq yayi a gaban alo domin shi bema san ta samu damar zuwa ba ya fara musu bayani. Malamin dake tsare su yana zaune a kujera Abubakar yana tsaye ya hango wata ko d'agowa ba ta yi hakan yasa shi k'arasawa gurin da take ya lek'a yaga meke faru sai yaga ta bud'e littafi sai kwafa take yi har ta kusan cika shafin farko.
"Ke.....!"
Taji an fad'a dai-dai kunnan ta. tsoro da razana yasa ta sakin tusa burtt ba tare da ta shiryawa hakan ba 'yan aji suka kwashe da dariya ita kuma ta zaro ido ta fara rantse-rantsen kare kai.
"Malam wallahi tallahi...."
Da sauri ya kifawa bakin na ta mari tayi saurin toshewa da hannun ta. matsawa yayi tare da nuna mata hanya yace.
"Fito waje kafin na yayy-yaga ki a gurin nan 6arauniyar amsa.."
"Wallahi mal..."
Zata tsaya yi mai gaddama ya yi saurin fin ciko ta tare da tura ta gaban ajin tayi taga-taga zata fad'a kan tebur Allah ya temake ta tayi saurin sanya hannu. Kwal-kwal idanunta suka kawo ruwa zata yi kuka Abubakar ya k'arasa gurin yace.
"Shanye shi, idan kika bari hawaye suka fito sai na zane ki 6arauniyar amsa."
Maida hawayen tayi tana nan tsaye har Sadeeq ya gama yi musu bayani sannan ya kalli Abubakar hace,
"Twinnie bar yarinyar nan ko tayi ba dubawa zan yi ba sabida ta yaye kanta ba zuwa take yi ba tayi degree yanzu sai zuwa tallah."
"Ohhh! No-wonder ashe dak'ik'iya ce, amma baki yi halin asalin me sunan ba shame on you.. Kawo wannan ta hannun taki da kika sato amsar, ki d'akko sabuwar pepper kizo nan ina jiranki."
Tafiya tayi tana gunguni tare da murgud'a musu baki, sabuwar takarda ta d'akko tare da biro taje ya nuna mata gaban alo yace.
"Zauna kiyi anan."
Kallon gurin tayi sannan ta turo baki kai da kagani kasan zai yi fitsara tace.
"Toh malam ai babu abin d'orawa kuma yagewa takardar zata yi"
Ba tare da ya kalleta ba dama Sadeeq ya fita yace, "ki d'ora akan cinyar ki kiyi."
"Amma malam ai..."
Wata uwar harara daya yi mata ne yasa ta had'iye sauran maganar, zama tayi tana zumbura mai baki yace.
"Idan kika sake kira na da malam sai na fasa miki baki."
Bata sake kula shi ba ganin yafi malam Sadeeq zafi da saurin kai duka, har kowa ya gama ya fita INdo tana zaune a gurin sai raba ido take yi gashi bata rubuta komai ba sai jagwal-gwalo. Ganin bata da niyar kawowa ne yasa Abubakar k'arasawa wajan tayi saurin cukwaikuye takardar ya mik'a mata hannun alamar ta bashi amma taki,
"baza ki kawo ba mara kunya?" Baki ta kuma murgud'awa mai aikuwa ya sanya k'afarsa ya doke shi da takalmin sa. INdo ta kurma wani uban ihu tare da fad'uwa k'asa tana ihu tana birgima.
Sunkuya wa Abubakar yayi ya d'auki takardar ya sanya cikin sauran tare da bawa invigilator d'in, ko takanta be kuma bi ba sai ma tsallake ta da yayi yabar gurin.
Ihu ta kuma saki tana shure-shure har daddaud'an pant dinta ake gani sabida wandon makarantar ya yage d'alibai suka zagaye ta ana bata hakuri da kuma masu yi mata dariya amma bata fasa shure-shuren ba shima malamin yayi tafiyar Sa dan yasan INdo sarai hakan yasa be kulata ba.
"Allah ya isa ban yafe ba mugaye kawai anyi satar amsar, shi dama ba malamin muba yazo yana cin zalin mutane..."
"Hahaha INdo me tusa burtt..."
Uba Aminu ya fad'a yana nuna ta yana dariya, ai kamar jira take yi ta mik'e tare da cakumar sa suka fara fad’a. K'arfi ba d'aya ba shi namiji ya dinga gwarata da alo jikake k'um...k'um amma tak'i sakinsa sabida tsabar jaraba, can akaji Uba ya rushe da wani irin ihu mai had'e da kuka.
"Kai..kai...kai! Lafiya meya faru haka.?!"
Malam Zubairu daya zo wucewa yaji ihu ya tsaya yana tambaya.
"Malam fad'a suke yi."
"Waye da waye?!"
"INdo da Uba."
Ihu Uba yake yana hawaye gashi ya rik'e gaban sa, malam Zubairu ya kallesu ganin INdo na rik'e kugu yasa shi cewa "ku biyo ni ofis yanzun nan."
Abokan Uba suka kamashi suka kaishi k'ofar staff room, ita kuwa tahowa tayi tana bugun cinya alamar bala'in be k'are ba taje ta tsaya malam Zubairu yakai takaddu ya ajiye sannan ya fito dan jin kanun zance, be fara bawa INdo damar magana ba yace Uba ya fara yi amma ya kasa sai shasshek'a yake yi da kuka.
"Ke kuma gaya min gaskiyar abinda ya faru."
Dai-dai lokacin Sadeeq da Abubakar suka fito daga cikin staff room, tsayawa suka yi Abubakar na waya ta fara baya ni.
"Tonona yake yi shine muka fara fad'a."
"Sai kuma aka yi yaya..?!"
"Sai kazo kace mu biyo ka."
"Kai Uba me yasa ka toneta gashi ta saka kuka..?!"
"Malam cizo na tayi a anan."
Ya fad'a yana nuna gurin, duk wad'anda ke gurin suka zaro ido Abubakar dake waya ya zare ta daga kunnansa yana kallon INdo cikin tsananin mamaki yace.
"Ke mayya ce? Baki da hankali?ke wace irin yarinya ce ne da kika fitini kowa ne? Stupid,nonsense, what a fool wawuya kawai, mai wasa da maza karya.."
Haushin maganar sa da kuma turancin da yake yi bata jinsa yasa ta fara murgud'a baki tana motsa lab6anta alamar magana take yi, da sauri Abubakar yayi kanta zai ham6are ta Sadeeq ya rik'osa yana kad'a masa kai alamar kar yayi yayin da zuciyar Abubakar d'in ke tafasa yanajin wani tururi cikin ransa dan yaki jinin rashin kunya da k'in gaskiya. A hankali Sadeeq ya dafa kirjinsa yana kalon INdo wadda ta makure jikin karfe tana jiran jin saukar duka yace...
*HAJJA CE*👈
[7/1, 4:48 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥
♥♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu.
Page *4*
"Aisha zo ki bawa yaron hakuri."
Tamkar ba taji ba sai faman wasan ta take yi da k'asar gurin da d'an yatsan ta wanda alama ce ta baza ta bayar da hakurin ba ya kuma cewa.
"Aisha ba magana nake miki ba kika min shiru ko..?!"
"Malam fa shine ya fara tono na kuma sai na bashi hakuri ta6di jam.."
"Duk da haka ki bashi hakuri tun da kin yi mai ba dai-dai ba.."
"Hu’...uhm." Ta fad'a cikin k'asan mak'oshin ta, Abubakar yayi kamar zai wuce kawai yayi wuf ya dank'e ta, nan da nan ta fara ihu har wasu malaman suna sake fitowa ya damk'eta ta 6are baki tana ihu yaji wani sumumin wari ya fito daga bakin ta yayi saurin kawar da kai tare da hankad'a ta saitin Uba ta fad'i k'asa bata San lokacin da ta furta.
"Allah ya baka hakuri Uba kayi hakuri kaji ka hakura..?!"
"Eh." Uba ya fad'a yana share hawaye malamai aka yi ta yiwa Indo fad'a akan karta sake yin fad'a da Namiji sannan aka sallame su. Ana tashi daga makaranta babu wanda Indo ta kula tayi wuce warta, ba gida ta wuce ba kai tsaye ofishin 'yan agaji ta nufa tana zuwa ta sami ogan ya kalleta yace,
"Yarinya ya aka yi aiko ki aka yi..?!"
Tace "A'a shugaba k'ara na kawo dan ance shari'ar maita bata k'arewa toh wani malamin mu ya Ce min banza maiya jaka, toh ban yafe bane shi yasa na kawo k'ararsa abi min hakkina."
"Au ke cema kika kawo k'arar?"
"Eh sabida ance nan ake kawowa kafin akai kotu."
Sosai ya kalli INdo wadda take faman turo baki tana taunar k'asan hijabin ta da hak'ori.
"Toh naji yanzu shi malamin yana ina kuma a wacce makaranta yake koya muku duk da naga inifam (uniform) d'inki na makarantar tsefawa ne...?!"
"Eh Shugaba acan nake kuma ma shi ba malamin mu bane d'ayan ne malamin mu amma kaga ya mareni, yayi min kutufo da k'afarsa sannan yace min Mayya, ance shira'ar maita baya k'arewa toh yazo ya fad'a a ina nayi maitar."
Shugaban 'yan agaji na k'auyan ya sake kallonta sannan yace,
"Ya sunan ki...?"
Tace "INdo malam Hamza."
"Toh INdo yanzu abinda nake so dake nasan yanzu an tasheku ki bari gobe idan Allahu ya tahemu lafiya he muzo ki nuna mana hi malamin kin ji ko.?!"
"Kai! Shugaba, ai tafiya yake yi kuma idan an gama jarabawa ba dawowa zai yi ba a hanyar gidan mu suke kayiwa Allah kayi ma ma'aiki kazo muje ayi Mai jan kunne ya dena ce min mayya da dak'ik'iya."
"A'a bada ni zakuje ba bari nasa wani yabiki suje yaji abinda ke faruwa."
Ya d'aga murya yana k'iran, "Awaisu! Awaisu!!, zo dan Allah kabi yarinyar nan ta kawo k'arar wani malamin su." Awaisu na zuwa suka tafi suna tafiya suna hira tamkar dama sun saba har suka k'arasa k'ofar gidan su malam Sadeeq wanda shigowar su kenan dan sai da suka tsaya suka yi juyan bak'in mai.
"Kika ce nan ne gidan ko?"
INdo tace "Eh nan ne suna ciki."
Kwan-kwan-kwan, Awaisu ya fara buga k'ofar gidan yana kwad'a sallama. Malam Sadeeq ne ya fito sanye cikin jallabiya ya kalli INdo sannan ya kalli Awaisu cikin rashin fahimta da kuma sanin dalilin zuwansu ya fara magana.
"Lafiya dai ko bawan Allah."
"Eh toh lafiya ba lafiya, wannan yarinyar ce ta kai k'ara cewar kana ce mata mayya. Toh bata yafe bane yasa takai mana k'orafinta shine shugaban mu yace nazo naji dalilin da yasa kake fad'a mata wannan kalmar."
Mamaki da al'ajabi suka cika Sadeeq, sai yanzu ya k'ara tabbatar da hauka da rashin hankalin 'yan garin ya kuma kallon INdo wadda itama shi take kallo yayi shiru yasan Abubakar ne dan haka ya tsaya yana tunanin abin cewa yaji INdon tace.
"Awaisu ka tambaye hi idan shine idan kuma ba hi bane toh d'ayan ne ya fito dan tagwaye ne.."
Kallonta Sadeeq yayi ya sake tabbatar da lallai bata da kunya, shi kuma Awaisu sai d'aga kai yake yana kallon gidan ko zai ga wani ya fito amma ba kowa hakan da sadeeq ya gani ne yasa shi cewa.
"Naga alamar baki da kunya Aisha, toh bazai fito ba ki shiga ki fito dashi fitsararriya kawai. Kai kuma SS ne ko d'an sanda ko soja ko menene da ta d'add'ago ka kuka zo nan..?!"
"A'a mu mune 'yan kungiyar agaji na wannan kauyan kuma turo ni aka yi akan naxo naji abinda yake wakana dan tace bazata yadda ba."
Cewar Awaisu Sadeeq yayi tsaki cike da takaici sannan yace,
"Toh kaji abinda na fad'a idan ba maita ba waye zai ciji mutum a mafitsara? Kuma ma wai fad'a mace da namiji dan iskanci."
"Haka ne kam malam kana da gaskiya ke INdo baki da gaskiya dan haka zanje na sanar cewa ga abinda ya had'a dan haka sai ki tafi gida ki dena wannan halin."
Awaisu na gama fad'ar haka ya bawa Sadeeq hakuri sannan ya juya ya tafi INdo na kallonsa zuciyarta fal haushin sa. Da taga yayi nisa ta juya zata yi magana sai taga ashe shima Sadeeq din ya shiga ciki ta d'aga murya saitin k'ofar tace.
"Kujini da kyau ni ba mayya bace sai dai kunemi mayya, kuma an dena zuwa bokon ai ba aikin Allah bane rawawul ni INdo na dena zuwa tsefawar yo dan banje ba ai ba mutuwa zanyi ba kuje ku cinye makarantar..."
Suna jinta suka yi mata banza Abubakar ya shak'a iya shak'a Allah-Allah yake ya shirya yabar garin dan takaici. Ita kuwa tana gama fad'a tayi tafiyar ta gida tana zagin su tare da d'aura aniyar baza ta sake zuwa makarantar ba tunda ai sai taje zasu ganta har suyi mata maganar banza.
K'arfe 3:34pm Abubakar ya idar da alwalar la'asar yana jiran Sadeeq su wuce masallaci dan da sunyi sallah yake son dawowa ya wuce gida. Jerawa suka yi suna tafiya suna hira abinsu gwanin ban sha'awa mutane sai kallansu ake yi.
Sagiru dake tsaye a k'ofar gida ya hana INdo fita ya tsaya yana kallonsu, ita kuwa INdo ganin yace baza ta fita ba yasa ta komawa cikin gida. Dai-dai katangar gidan zasu wuce kawai Abubakar yaji an cillo wani abu ya rufe mai fuska suka tsaya ya cire yana dubawa yaga hijjab ne yayi dik'il-dik'il dashi ya yarda shi, kafin ya kuma yin taku d'aya yaji an kwad'o mai wani abu a gefen wuyan sa ya kalli k'asa takalmi ne d'an madina silifas yasha d'aurin leda a wajan sanya d'an yatsa suka kalli katangar da ake yo jifan kawai sai suka ga hannu hakan yasa ran Abubakar ya kuma 6aci sai ga k'afa can sai gata ta dirgo tim...!
Da sauri suka matsa inda take tana d'agowa ta gansu a tsaye a gabanta bata san lokacin da ta kuma kurma ihu ba tare da juyawa zata kuma kama katangar ta koma gida Sadeeq yayi saurin janyo rigar ta mutane suka taru yayin da INdo ke faman basu hakuri.
Gabaki d'ayan ta tsami take yi da zarni Abubakar ya tsinketa da mari tare da dungure mata goshi sannan Sadeeq ya sake ta Abubakar yace.
"Baki da mutunci ko?Ke mara kunya kinga abubuwan tsimmar da kika watsa min? Toh ki saita kanki idan ba haka ba kafin nabar garin nan sai na ji miki ciwo idiot kawai sai zarni kike yi mai fitsarin kwance jibe ki dan Allah da wani billanki a goshi kamar zanan one..."
Yana kaiwa nan yayi gaba yayin da Sadeeq ya harare ta shima yayi tafiyar sa suka shige masallaci. Mutane kuma suka k'arasa wajan INdo da tayi shiru tana kallon jikin ta.
"Kedai INdo wallahi kowa sai yace baki da kunya, suma bak'i har kin fara yi musu.."
Cewar Rabi bala wadda makarantar su d'aya amma ita a js 3 take, INdo ta harareta tare da cewa.
"Anyi d'in kizo kiyi kuli-kulin tara sisi dani munafuka kowa yasa dake.."
"Ke INdo dan ta gaya miki gaskiya shine zaki mata rashin kunya."
Wani yaro Bala ya fad'a ta kuma juyawa kanshi cikin masifa tace, "ji banza kai tunda ga kan sunanka ansan kai d'in bala'i ne banza Bala bala'i mtwww."
Nan da nan gurin ya kaure ita kad'ai su kuwa wajan mutum goma amma babu wanda ta ragawa, Sagiru k'aninta ya jata suka shiga gida sai da suka kai har tsakar gida sannan ta ture shi. "Dalla can ni kyale ni banza."
Ruwa ta kindima a buta ta shiga band'aki shi kuma Sagiru ya kuma fita waje yana cewa,
"Dama na barki sunyi miki shegen duka masifaffiya kawai."
Fitowa tayi jikinta sharkaf da ruwa wanda da alama wanka tayo amma ba a saka sabulu ba. Cikin d'aki ta shiga Inna tana sallah ita kuma taje ta sake kaya sannan ta d'an