Showing 12001 words to 15000 words out of 85627 words

Chapter 5 - MUSAYAR ZUCIYA COMPLETE BOOK by Hajja Ce.txt

Hajja Ce   

14 Sep 2025

33

tareda shan kunu

Kyakkyawar farar takarda datasha xanen heart Mani ya ajiye akan tebur se faman sosa keya yake don wannan bashine karo na farko ba da nurses suka sabayiwa ogan nasa haka,cikin dakakkiyar murya Abubkhr yace

“Jeka Mani sena neme ka..”

“To Yallabai Nagode ahuta lapia..”

Mani nafita abubkhr yaja tsaki ko duban takardr beyiba ya mike don yin round na patients fitarsa kenan suka kusan yin gware da nurse Deexah uniform dinnan sun matse koina na jikinta ya bayyana se wani rausaya take tana karkada jiki,

“Dr..Pls”tace hakan cikin wata irin siga

“Please what ?!inada patients daxan duba pls..”yakarasa hade da kaucewa ta gefanta xe wuce tai hanxarin shan gabansa bayan tahada tafukan hannayenta biyu sama alamar roko,

“Dan Allah dr ka saurareni minti d’aya pls”

Allah data ambata yasanya shi tsayawa ba tare daya karasa tafiya ba amma bejiyo ba fuskarsa kan agogon dake daure a hannunsa yana jiran minti dayan ta cika,

“Ki magana kafin minti dayan ki tacika pls”

“Dr Meyasa kake mun haka? Kaso me sonka,ka agaxawa xuciyata kaceto ta daga fadawa kogin halaka,duk asibitin nan babu wanda na xaba amatsayin wanda zuciata take muradi sekai”

Karasa maganar ta yayi dede da cikar minti dayan data ambata don haka yai gaba abinsa yashiga bin round na patients sedaya kammala tsaf sannan yashiga office din abokinsa wato dr luqman,

Sundan taba hira sunayi suna tafawa sannan luqman yashigo da wata hirar,

“Nikwa Abokina nagaji da kawo korarrafin da ake kawomun akanka wlhy,yanxunnan nurse deexah tafita hawaye kwance shabe shabe kan fuskarta dukde akan ka,dama yanxun nake maganar koba ka shigo ba xanxo na sameka don nikam nagaji”

Murmushin takaici Abubkhr yayi cikin nutsuwa yace,

“Toh Aboki bani shawara shin mexanyi akai?”

“Ni Ina ganin kaxabi d’aya kawai ka aura kaga ai dole sauran su kyale ka ko?!”

Ajiyar zuciya Abubakhr yai kafin yace,

“Gaskia Aboki kabani mamaki wallahi domin bantaba saka a sahun mutanen daxasu bani shawarar naxabi d’aya daga cikin nurses dinnan na aura ba,karka manta duk wani namiji yana sone ya auro yarinya yar mutunci me dattako da sanin yakamata wadda ‘yayan daxata haifa ma xasuyi alfahari da kasancewarta uwa tagari,

To axahirin gaskia de magana d’aya ce xanyi wallahi duk cikin nurses dinnan babu wadda xan iya xaba a matsayin wacce xan dauka nakai ta gidana wai amatsayin matata ta aure,Kowa Allah ya hadashi da rabonsa kawai ko ya kagani?!”

Shiru dr luqman yai yana cin faratansa da alama yarasa tacewa,knocking akai a kofa har sau uku hakan yasanya abubkhr bada izinin shigowa bayan yace,

“Yess”

Shigowa tai sanye cikin abaya baka bakinta dauke da sallama hannuwanta rike da files cikin siririyar muryarta kamar anbusa sarewa tace,

“Gashi Doctor,duk nagama komai har room 13 dakace nayi mata inducing ruwan..”

“Okay nurse Mareeyah thank you..Xaki iya tafiya”

Dama abinda Mareeya ke jira kenan tai hanxarin ficewa abinta,baki galala abubkhr yabude yanabin k'ofar data rufe da kallo kafin yadawo da kallonsa kan Doctor luqman cikin sauri yace,

“Dr ai naxatan nurses d'innan sun gama aikinsu sun koma ya kuma Naga wannan?!”

“Oh mareeyah riketa mukai wallahi yarinyar ta iya aikinta ga hankali da nutsuwa wallahi ba ruwanta da shiga harkar mutane kullum ita kad’ai xakaga tana aikinta”

“Mareeyah..”Dr abubkhr ya maimata sunan

“Kwarai sunanta mareeyah..A’a kode kafada’a da...”ai luqman ne k’arasa ba abubkhar yai hanxarin ficewa

Cikin sa’a ya hangota tsaye a corridor tana shimfida sallaya xatai sallah,

“Salam alykm..”cewar Abubkhr daga bayanta..

“Wa alykm Salam”tabashi amsa tana k’ok’arin gyara mayafin data yafa

Ya salam,,abubkhr yafurta azuciyarsa Dakyar da lalubo salati yasamu ya saisaita kansa kamar bashi ba yace,

“Dama uhm..Idan baxaki damu ba magana nakeso nayi dake”

“Babu damuwa amma xanyi sallah de tukun..”

“Tohm shikenan take ur time xanjira”cewar abubkhr

Ya jima azaune sedata idar tai addu’ointa tukun sannan ta nannade praying mat dinta ta mayar cikin jaka,

“Ina jinka dr..”

“Okay.. Sunana Dr Abubkhr..”

“Allah sarki..Ni sunana mareeyatul qibdiyya.”

“Nice name qibdiyyah,”

Nande abubkhr yashiga gaya mata meke tafe dashi da abunda ke cikin zuciyarsa,itade mareeyah kawai kallonsa take tana mamakin dama yana magana haka?!Abubkhr be bar maareryah ba har seda ya tabbatar ya dana mata tarkon son sa tukun sannan sukai exchanging numbers zuciyarsa fes yakoma gidah,

Kullum de abinda ke faruwa kenan abubkhr har gidah yake xuwa xance wajen mareeyah ashema basuda nisa su su abubkhr suna unguwar Court Road ita kuma Mareeyah tana Hausawa,Sosai suke gwangwaje soyayya abun su shikuwa sadeeq har yanzu be samu wadda ta kwanta masa ba duk ya gwada amma babu sa’a ga cuku cukun transfer dayake nema amma yakasa samu haka ya hak’ura yafara shirin komawa makarantar tsefawa dake kauyen Sani a k’aramar hukumar sumaila..

****

Ranar asabar da safe sadeeq yatasamma titin sumaila bayan yasha adduoi daga mahaifansa da kuma dan uwansa abubkhr wanda sam be so komawar d'an uwan nasa kauyan kayayau d'inba,

Yana shiga cikin unguwar kuka sunan unguwar tasu kenan ya fara jiyo hayaniya sama sama be tabbatar da muryar ba seda yaxo daf da dandaxon jama’ar da suka taru suna kallon fadan da ake ta muryarta yagane kowacece siririn tsaki yasaki jin muryar INdo ce dan turmutsawa taron yai ya hangota sanye cikin kodadd'un kayanta se jurwayen fitsari riga daban xani daban d"ankwali kuwa ba'a xancensa se tumurmusar fad'a suke da wasu yara maza kuma duk itace me karfin ciki,wani daga cikin taron ne yace

“Ke y’ar nan kome sukai miki ki hak’ura ki kyalesu tunda ke macace dan allah”

Cikin turo baki had'e da k'ank"ace idanuwa tana girgixa kugunta data d'aure da shamilallan hijabinta tace,

“Ta kwarankwasa baxan hakura ba,Babban bala'in can,se in xauna gani sokuwa sumin lefin sannan na hakura wallahi babu xancen hak’uri a dishenari(dictionary)na ramuwa ta da ta taxama dole..”

Tana gama fada tacigaba da kokawar da take yu cikin xafin nama sadeeq ya k'arasa cikin su ya wanke mata fuska da mari hade da hankadata gefe yatsan sa yasa yashiga nuna ta,

“Ke wai wacce irin kidahuma ce ne eh?! Kina mace kike fad'a? fad'anma da maxa dandaxon mutane akanki ko kunya bakya ji? Tukun nama me akai miki da kika kamasu kina duka kaman wata tinkiya..”

Rike baki Indo tai tana kada Kai

“Kai ka Kai Kai Kai wacece tinkiyar?!”

“Kece tinkiyar”

“To wallahi ka bude kunnuwanka kaji niba tinkiya bace kuma kwarankwatsa ka kara cemin tinkiya seka gani. Haba nifa kana shiga rayuwata da yawa makaranta ce de nace ni INdo Malam hamxa nadena xuwa tsefawa inifam d'ina ma na yadashi amma saboda tsabar shisshigi da neman sani seka tsoma wannnan bakin naka a xancen da ba naka ba”

Tana gama fada ta shuri bokitan su ubale da idi na talla da suke fad'a tai gaba dasu tana sharara uban gudu,ganin haka yasanya su ubale binta a d'ari suna rokonta da tabasu bokintan tallansu da ta kwashe,

Karkad'a kai kawai sadeeq yai wani b'angare na zuciyarsa na tabbatar masa da lallai yarinyar nan ba aljanu bane kad’ai da ita Lallai babu shakku aciki kwakwalwarta ta tabu, da haka ya k'arasa gidansa yashiga bakinsa d'auke da sallama tamkar da mutane a ciki.







*HAJJA CE*👈
[7/1, 4:53 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*

♥♥
A true life story

Na


*K.A.S Precious Hajja ce*👈


*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*DEDICATED TO*:- Sanah Isma'il matazu.

_Yau page d'in nakine k'anwara ta gidan mu, ki sani kina cikin ran Hajja domin Hajja takici my *MISS HAFCY BCH* dear kidena damuwa kina raina kun zama H³🤙mu shirya kinji..💋_


Page *8*

INdo kuwa tunda ta koma gida take wanke hakorinta ko abinci k'in ci tayi sabida kar yayi daud'a malam Sadeeq ya hanata kyauta. kwanciya tayi male-male a tsakar gida kan tabarma tamkar me yin azumi, takaici da haushi suka cika inna ta kalleta tana daga tsaye Innan tace.

"Ke! 'Yar nan ki rufawa kanki asiri kizo kici abinci kin ganin min sakarya, banda malamin naku mugune taya zai hanaku cin abinci sabida wani an goge baki, toh bari ki kashe kanki ai kinyi wa kanki..."

INdo tayi shiru tana ci gaba da rik'e ciki tana birgima, baban su ne ya shigo ganin yadda INdo keyi ne yasa shi tambayar inna nan ta sanar mishi aikuwa ya fara fad'a tare da cewa ta tashi taci abincinta amma ko motsi INdo tayi shiru sai hawaye da take fitarwa a hankali. Juyawa baban nasu yayi direct ya wuce gidan da Sadeeq yake ciki, kwankwasawa yayi yazo ya bud'e sam be san shiba dan haka ya fara mai kallon rashin fahimta baban INdo yace.

"Sunana malam Hamza uban INdo d'alibarku ta makarantar tsefawa, ga 'yata can zata mutu tak'ici tak'i sha sabilida kunsa musu dokar yin buruhi. Toh bazai yiwuba, tun wuri kaje kasa taci abinci dan idan ta mutu akan wata kyautar ku ba yafewa zanyi ba kur'anikuwa.."

"Subahanallahi malam ai ni ba haka nake nufi ba itada ma ba..." Sadeeq be k'arasa magana ba malam Hamza ya cafe zancen ta hanyar d'aga masa hannu yace.

"Karkayi min wani batukaji ko, tanacan tana malan geruwa dagani har uwarta munyi-munyi taci abunci tak'iya wai kar bakinta yayi daud'a. Ita Uwata ai batada jimirin yinwa ko azumi goma bata iyawa dan haka kokaje kasa taci abinci konaje har gidan protocol (principal) d'in nayi mai bayani zaka kashe mana 'ya'ya."

Tsaki Sadeeq yaja a k'asan zuciyarsa sannan ya rufe gidan ya kalli baban INdo yace "Muje toh amma ni ba haka nake nufin suyi ba."

Kwance suka tarar da ita tayi shame-shame tamkar wadda zata mutu gaban malam Sadeeq ya buga mamaki da tsoro suka dirar mai cikin sanyin jiki ya kalli INdo bakin sa yayi mai nauyi ya daure dai yayi mata magana cikin dakiya.

"Aisha tashi zaune please."

Da kyar INdo ta samu ta iya d'ago kwayar idonta tana kallon malam sadeeq d'in yayi mata alama da ka nan ta mik'e zaune da kyar jikinta duk yayi fututu da k'asar gurin da ta kwanta rigar jikinta daga wajan hammatar ta yage sikert d'in ma duk yasha faci tana son mik'ewa amma ta kasa, hankalinsa ya kuma tashi lokacin wayarsa na ta faman ringing amma ya kasa d'agawa bare yasan ko waye. Daurewa yayi ya kuma matsawa kusa da ita yana kallonta yace.

"Aisha tashi kici abinci ai ni ba haka nake nufi ba, kinga idan kin gama cin abincin ma zaki iya yin brush d'in amma ba'a zama da yinwa idan ba haka ba mutuwa ake yi tashi kinji."

Kasa mik'ewa tayi saida baban ta yace da innar ta mik'ar da ita sannan aka zaunar da ita ta jingina da jikin bango jikin duk babu kwari tayi zuru-zuru da ita kai daka ganta kasan tana cikin wani hali. Kallon Inna malam Sadeeq yayi gabaki d'aya tausaya musu yake sabida ganin halin da suke ciki na rashi, ya karyar da baki yace.

"Mama a kawo mata abincin taci."

Sai Inna taji wani banbarakwai daya kirata da Mama yayin da INdo ta ke numfashi da kyar dan da kyar take iya bud'e ido. Inna ta kawo dambun mazara ta turawa INdo gabanta Sadeeq ya kalli kwanon sam babu alamar akwai mai a ciki ya kuma kallon INdo wadda ta luma daddaud'an hannunta wanda duk k'asa ta 6atashi yaga ta fara watsa danbun cikin bakinta, mamaki yasa shi yin shiru ba tare da yayi magana ba har ta cinyee besani ba yana tsugunne yana tunani.

Sai da ta gama cinyewa sannan Malam Sadeeq ya mik'e, ya yiwa Inna sallama sannan ya fita. A k'ofar gida ya tarar da baban INdo nan ya kuma bashi hak’uri da kuma k'ara yi mai bayanin abinda yake nufi akan su, mahaifin INdo naji ya dinga 6oye hakoransa wad'anda suke jawur sabida tsabar cin goro da rashin kula dasu.

Yana shiga gida ya zaro wayarsa missed call ya tarar na Abubakar, sai da ya zauna a bakin katifarsa sannan ya kira layin har sai da ta kusan yankewa sannan yaji an d'aga.

"Sadeeq ina ka shiga ne inata kira baka d'aga ba..?!"

Cewar Abubakar cikin sanyin muryarsa da jan aji, Sadeeq ya shafa kai yana kuma sauke ajiyar zuciya yace.

"Twinnie ina jin sai na d'auki shawararka, wannan kauyan yafi karfina wallahi haukan su yayi yawa sosai."

Yayi shiru yana sauke numfashin takaici kafin Abubakar d'in yace.

"Da kyau gara tun yanzu ka fara gane cewar kafi k'arfin secondary teaching ka dawo nan gara ko FCE kano ne kaje kayi lecturing."

Shiru suka yi na d'an lokaci kafin Sadeeq yace.

"Toh zan kuma yin shawara amma nima abun kauyan nan ya fara isata, abun nasu yayi yawa ga gidadanci."

"Twinnie kullum haka kake cewa yanzu kawai aiwatarwa zaka yi mudai muna nan muna yi maka fatan alkairi."

"Ok insha Allahu sai munyi waya anjima a gaida min da qibdiyyah."

"Zataji dakyau gata nan ma muna tare."

Beyadda sun gaisa da itaba ya kashe wayar dan yaji ta fiye shiru da yawa kuma shima ba surutu garesa ba.

***

Tun ranar laraba Rukayya ta wanke mata kai bayan tasa mata fiya-fiya kwarkwatar sun mutu sannan tayi mata zanan Hausa shuku, kai idan kaga kan bazakayi tunani na jiya bane sabida ya kitsu sai dai jan gashi gareta ba bak'i ba. Uniform d'inta kuma ranar alhamis tasa zare da allura ta d'inke so gabaki d'aya inda ya yage ta kuma wanke su duk da sun riga sun kod'e kuma bata da wasu ba kud'in yin sabo ta goge fason k'afarta k'afar tayi kyau duk kuwa da be fitaba gaba d'aya.

Gidan innatuwa me kunshi taje tasiyo lallen goma da talatin din da rukayya tabata,da kanta rukayyan ta yarfa mata jan lallen ta rufe mata fason kafarnan,a ranar da yamma indo tatafi kasuwar dakali wajen idi shoe shiner hannuwanta rike da wasu jemammun takalma kambos duksun fatattake,

“Idi xaka iya gyara wannan takalman”

“Mugansu”cewar idi

“Gasu kambas(kambos) ne idi kaga insipehen(inspection)malamin mu xeyi ranar juma’ar nan kuma bakaga kyautar dayake be nikuma so nake naci shadda ma yasin”

“Bari na gwada nagani xasu gyaru mana sede xaki biya kudi dayawa”

“Kai idi nawa?!”

“Nera hansin”

Rantsuwa Indo ta dinga kwasowa tana kalallame idi da kalamai tana faman xabga masa roko ta karkare da,

“Dan manzon salati idi kayi hak’uri ka temakamin nice fa indo..Indo Malam hamxa ta makarantar tsefawa nan nan kusa dakai.”

Cikeda isar nacin da take masa idi ya wafci takalman yashiga gyara su,yadau lokaci yana dinkecan nane can da gum sannan yai polish d’insa se kyalli yake Kai kace bashi bane sannan ya mikawa Indo ,cikin murna ta karba harda lashe kasan takalmin

“Ta kwarankwatsa ya fita kuma,lalle aiki seme hi,Sannu idi yasin kaci abaka hinkafa da miyar ja me nama”

“Allah ko Indo?”

“Yasin idi”

Cikin sake gyara kananun kayan da sukai yawa ajikinsa Wai shi gaye yace,

“Toh Indo nikuwa ina lami?(kawar Indo)”

“Oh lami tana nan,oho de bansan mata bama kasan makarantar gangare take tunda mijin kanwar babar su ixama chayamen(chairman)”

Kada Kai idi yai yana murmushi,cikin tsokana Indo tace,

“Wai haryanxu kana ciki ne?!”

“Eh mana Inason lami wallahi kawaide bata sona ne tafison shehulle”

Cikin karkad'a kugu had'e da rausaya idanuwa INdo tace,

“To ai kaine idi,dole lami tafison shehulle kullum fa tanada daurin tsire da leman roba na yangayu Kai kwa se mammakon bala'i”

“Ba haka bane Indo amma xan gyara..”

Da haka sukai sallama da ita tana tafe tana jujjuya takalmanta ranar kuwa barkakkiyar safar da tayi shekaru batako kallansu hasalima kama tukunya ake dasu ta dinga durxa tana wankesu ruwa uku tai musu ,Kai kowa mamakin Indo yake har inna tafara sanyata a sujjada idan tai sallah don gani take aljanun tsafta ne suka shafeta kwanan nan..

***
Rana bata Karya sedai uwar d'iya taji kunya yau take juma’a tashin Indo uku kafin asubah inna tana korata waita xata safiya tai,asubar fari kuwa ta mike tai bandaki ranar de atakaice baccin kirki Indo batai ba.

Sega Indo tai wanka abinda yabawa kowa mamaki agidan nasu sede basu da man shafawa sai dai manshanu ko na girki shi kuma bashi garesu ba dan haka tana saka kayan makaranta ta fita zuwa gidan Rukayya lokacin mijinta na nan INdo ta kwankwasa musu k'ofar d'aki tare DA cewa,

"Rukayya kina ciki kuwa? Zuwa nayi ki aramin kayan kwalliyarki inyi zani makaranta.." Ta k'arasa fad'a tana me shiga cikin d'akin sukayi kicib'is da ita, "Au ashe kinji ni."

"Eh INdo bari na d'akko miki su nan tsakar gida."

Cikin d'akin ta koma ta d'ebu mata su lokacin mijin ta shima yazo zai fita INdo ta ganshi ta dashare baki tace

"Au kaima d'anlami ashe kana ciki yanzu ka tashi a bacci ne?" Ya tsaya kusa da ita yana kallonta yace "Eh INdo yau kuma za'a makarantar kenan."

Tace "Eh gahima kuwa." Rukayya ce ta fito ta mik'awa INdo kayan kwalliyar shi kuma d'anlami yasa kai ya fita. Tana zaune tana yi Rukayya na kwarzanta ta wai tayi kyau ai yau sai dai in bak'in cikin ne zai hana malam sadeeq ya bata kyauta. Zuciyar INdo ta kuma shiga cikin wani irin yanayi najin dad'i, ita dakanta tanajin sauyi a cikin jikinta sabida iskar da take shigarta ta k'ofofin gashin jikinta. Da sauri ta kammala kwalliyar

Tashi Rukayya tayi bayan ta kwashi kayan kwalliyar ta shiga cikin d'aki ta mayar dasu ta mik'awa INdo turare sai faman dariya take sabida yadda takejin ta wani daban yau. Tafeshe rigarta Rukayya tayi saurin cewa.

"Haba INdo ya kike kuma 6ata kayan makaranta salan yaga jirwaye ya hanaki...? A jikin hammatarki zaki fesa.!" INdo tayi yadda ta gaya mata sannan tace.

"Sai nazo kawo miki kayan da zan samo Rukayya..."

Tayi dariya itama cikin jin dad'i da fatan alheri tace "Toh INdo Allah ya baki sa'a sai kun dawo."

Gida ta shiga yau ko karin kumallo bata tsaya yi ba sabida kar bakin yayi daud'a tayiwa Inna sallama tabar gidan yau harda littattafanta da suka yayyage tazuba a leda ta tafi burinta yau ta samu atamfar ko ya bata wani abun da zata dinga alfahari dashi, yau sai da ta riga kowa a makarantar zuwa principal ne kawai da masu kula da makarantar bata riga ba taje ta zauna kusa da farkon aji da niyar ko masu gurin sunje bazata tashi ba tafi son a fara ta kanta yau.

***
Lokacin 8:15am yana gaf da shiga ajin aka yo mai waya hakan yasa shi tsayawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login