Showing 72001 words to 75000 words out of 85627 words
tare da cewa.
"Allah nakewa godiya 'yar nan domin ban ta6a zata zanga irin wannan ranar ba musamman akanki, sai gashi Allah ya shirya minke ya kuma azurtaki gashi har kina tallafa mana da abinda kike dashi, Allah yayi muku albarka dukanku."
"Amin Inna ta, karki damu dana gama karatu na kware insha Allah zanyi kud'i duk gidan nan sai an gyarasa."
"Toh Allah ya yassare miki."
"Feenah dan Allah idan ya koma kwara state zan cewa Sagiru ya kawoki mu zauna tare ko bakya so?!"
"Ke! Ina so mana ai wallahi kin more gidan miji INdo."
Mtwww "Ban hanaki cemin INdo ba gatsal? Ki kirani yayya Aisha ko Yaya INdo karki sake cemin wani INdo mara kunya."
Kallonta Nafeesa tayi tana ta6a baki kafin ta kad'a kai tabar d'akin. Har zaure Inna ta raka ta tana yi musu fatan alkhairi bayan Sadeeq yazo sunyi sallama. Dubu d'aya ta kar6a gurin Sadeeq ta bawa su Sahura su raba d'ari biyar-biyar suka dinga godiya suna k'ara jinjina arzikin da INdo ta samu sannan ta shiga mota suka tafi cike da farin ciki.
***
Kwanaki biyar yayi bayan sunje kauyan Sani sannan suka d'aga suka tafi kwara state da Fateema bayan yayi yayi da INdo ta bishi tak'i sabida karatunta. Yana tafiya da kwana biyu tasa Sagiru ya kawo Nafeesa duk ranar school d'inta zasu je tare ta zauna a barandar ajinsu INdo idan sun tashi su koma gida ta koya mata abinda ta iya itama hakan ya k'ara bud'e brain d'inta ga cikinta yana ta girma cikin kwanciyar hankali.
Duk wata Sadeeq suke dawowa kuma INdo bata nuna damuwarta duk da bata son tafiyarsa amma bata son nuna mai dan karya kansile mata karatunta, gashi dama ya sanyata a makarantar dare ta islamiya ta matan aure anan unguwarsu hakan yasa ta kuma zama busy tana kuma wayewa ta fannoni da yawa a cikin rayuwarta.
Cikinta har ya shiga 10months bata haihu ba sai dai yayi girma har bata iya zuwa ko'ina. Ranar wata laraba cikin dare ta farka lokacin Sadeeq na mak'ale da ita duk da girman cikin jikinta hakan baya hanashi nanik'arta. Kallonsa tayi tana faman rintsa ido cikin wani irin mugun rik'o yaji ta rik'e mai hannu hakan yasa shi saurin farkawa.
"Cutie what happen?" Shiru sai cizon lips d'inta takeyi tana matse idanuwa ya mik'e tsaye ya sakko yace.
"Cutie kodai haihuwa ce? Bari nazo muje asibiti."
A gigice ya sanya jallabiya ya zari mukulli yayi parking lot. Motar ya fitar da ita shiru garin babu kowa ya kuma komawa gidan da kyar ya kimtsata ya fito da ita mota lokacin mak'ocinsa ya leko sabida yaji k'arar mota. Ganin halin da ake ciki ne yasa shi taso matarsa ta bisu zuwa asibitin.
Duk ya rud'e ya bugawa Fateema ya gaya mata itama hankalinta ya tashi gashi babu abin hawa bare tabisu gata mace. Ganin abun yayi yawa ne yasa suka kira Sadeeq d'in ciki INdo tana ta kuka ya rik'e hannunta zuciyarsa na bugawa da k'arfi da k'arfi tace.
"Dama a makaranta malama tace idan mace zata haihu k'afarta d'aya a duniya d'aya kuma a k'abari. Malam Sadeeq kayi hakuri nasan nima yau dacta zan..."
Sadeeq yayi saurin rufe mata baki yana kad'a kai, da k'arfi ta fizge kanta ta juyar da kai tana ci gaba da magana.
"Sai na fad'a d'in ka bari in gaya maka mana, dacta zanbi nima yau amma dan Allah tunda ance namiji zan haifa dan Allah koda na tafi malam Sadeeq ka sawa d'an suna Abubakar Sadeeq kar kuma a 6oye mai suna dan Allah."
Jikin sadeeq ya dinga rawa gumi gaba d'aya ya gama jik'asa, tana gama yin magana kawai nurse d'in dake gurin tasa hannun zureren jariri ya santalo kan hannun nurse d'in INdo na kwance tayi shiru yayin da Sadeeq ya bud'e baki yana kallon fuskarta gumi na d'iga akan hannunta na jikin fuskarsa....
*Fatan alkairi gareku masoya, a koda yaushe Ina alfahari daku cikin labarin MUSAYAR ZUCIYA. Hajja ce take muku fatan alkairi tare da d'in bin godiya marar adadi*π
*HAJJA CE*π
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *ββ MUSAYAR ZUCIYA...ββ*
β₯β₯
β₯
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*π
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*π‘
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu.
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
Happiest bday ASMY B ALIYUπyou are truly one of the most amazing writers I knw..Forever and a lifetimes to come tawan...π
Page *34*
Tana fita napep ta tare ya kaita gidan su. Tana shiga ta fashe da kuka tare da fad'awa kan kujerar d'aya daga cikin falon.
"Ke lafiya kuwa kamar wadda aka yiwa mutuwa?"
Cewar yayan ta Shamsu yana kallonta, Fateema bata yi shiru ba tana ta kuka Shamsu ya tashi ya dinga mata fad'a yace idan baza tayi magana ba ta tashi ta koma inda ta fito. Mama ma kallonta take yi tana jiran jin abinda zata fad'a ranta cike da addu'ar Allah yasa ba tsakaninta bane da mijin.
"Ke wallahi karki bari na tashi tsaye dan sai na fasa miki baki, aikin banza kawai kiyi magana shine zaki tsaya yiwa mutane kuka."
"Mama Sadeeq ya munafurce ni, Mama be ta6a gaya min matarsa Aisha nada ciki ba sai yau da muka gani gashi har ya fito. Wallahi bazan koma gidan saba yaje can su k'arata munafiki kawai, dama ance duk wacce ta d'auki namiji uba toh lallai zata mutu ma..."
Mtwww "Shut-up Fateema, bakida hankali ne? Toh sakinki kike so yayi?!"
"Nidai kam bazan koma ba yaje can su k'arata."
"Toh idan ya sakeki sai kizo na aureki nine kawai idan na aureki za'a haramta min k'ara aure bare har matar ta rigaki haihuwa."
"Yaya Shamsu ka aureni kuma?!"
"Eh toh kince maza ba 'yan goyo bane, kinga ni uwa d'aya uba d'aya muke ki goyani na goyaki babu mejin haushin wani, amma ko barin Sadeeq kikayi toh wani mijin zaki aura kuma shima wata ran zai miki wani abun sannan ba lallai ki kuma samun saurayi ba sai da kema ki shiga gidan wata."
"Umma...."
"Karki min magana Fateema, dai-dai gwargwado kina da ilimin addini shin na zamani ne ya rinjayi da addininki ko kuwa wani saban iskancinne haka? Karki manta wannan auran nasu had'in Allah ne duk wanda yace zai ja da ikonsa akan lamarin toh bazai kwana cikin jin dad'i ba. Fateema karki manta nima da yanzu bani bace mahaifiyarku, amma kinga da yake Allah yayi ta hanyata zai samu haihuwa sai ya d'auke matarsa ta farko da kyar mahaifinku ya yadda ya aureni da yace ya gama aure amma a satin da na tare a satin na samu cikin yayan ku ki gaya min da mahaifinku yayi butulci ya kafe akan bazai sake aure ba ta wace hanya zai sameku tunda Allah yayi yana da rabonku a duniya?!"
Fateema ta kuma fashewa da kuka tare da mik'ewa zaune tace.
"Toh Umma kiyi hakuri wallahi sharrin shaid'anne, amma kuma me yasa koda wasa be gaya min ba ya yi min shiru sai yau naji na kuma gani?!"
"Hmm Fateema kenan, toh ko tunda kuka yi auran Sadeeq be ta6a kusantarki bane har sai da aka yi musu aure da ita Aishan?!"
"Kai Umma.."
Fateema ta fad'a da alama nauyi tambayar tayi mata, kallon Yaya Shamsu tayi k'asa-k'asa kawai suka had'a idanuwa ya zabga mata harara tare da cewa.
"Ke..! Kallon me kike yi min haka? Ko kin d'auka bansan meye auran ba sai ke kika sani.??"
Da sauri ta zaro udanuwa hannunta a baki tana girgizawa tare da kallon Umma Fateema taga Umman ma ita take kallo, lallai Yaya bashi da kunya ma wallahi a gaban Ummansu. Koda yake itace ta kallesa dole yayi mata bayani.
"Fateema karki yadda ki nunawa mijinki bak'in cikinki akan cikin matarsa, ina son ki nuna masa kinfishi son cikin ma. Sannan karki bari abban ku ya dawo ya ganki a cikin gidan nan wallahi kinsan ranki ne zai 6aci abanza, gara kije kiyi zaman aurenki har Allah ya baki kema wata rana idan kina da rabo."
"Toh Umma, amma dan Allah ki tayani da addu'a dan wallahi ina jin zuciyata nayin zafi da nauyi."
"Kidena sawa a ranki insha Allahu zaki ji bakya ji shaid'an ne kawai yake son shiga cikin lamarinki, ki yawaita azkar zakiji dad'in ranki."
Wayarta ce dake cikin jaka taji tana ta ringing amma tak'i d'agawa dan tasan baxai wuce Sadeeq ba ita kuma bata shirya abinda zata ce masa ba. Tashi tayi suka yi sallama Yaya Shamsu yace bari ya kaita gidan da kansa, suna tafiya yana k'ara bata shawarwari wani maganar ma har mamakinsa takeyi lallai yayan nata aure kawai yake jira amma babu abinda be sani ba.
***
Shi kuwa Sadeeq k'arfe tara yaje d'aukar su amma aka ce Fateema bata nan, duk an duba bata gidan ya kira ta yafi sau goma amma ba'a d'agawa hakan yasa yace INdo ta fito su tafi. Gidan Fateeman suka fara biyawa amma akulle hakan yasa Sadeeq tafiya yakai INdo gida tunda ranar a gidan Fateema yake.
"Malam Sadeeq d'an tsaya a can gurin me balangun can na kan kwana ka siya min."
Kallonta yayi sai yaga ita kalle-kalle takeyi abinta cikin mamakin daya mak'ale mai a wuya yace.
"Cutie ballangu kuma."
"Eh dan Allah kace su sa yaji daban."
"Ikon Allah shi kike son ci kenan."
"Eh, akwai fura da nono da ake damawa a gurin, ana sa kwakwa da ayaba da madara please dan Allah itama ka siyo min."
Dai-dai lokacin suka tsaya a gurin ya kalleta tare da cewa.
"Toh ke ya akayi kika son nan gurin harda abubuwan da ake siyarwa.?!"
Juyawa tayi ta kallesa suka kalli junansu tayi murmushi tare da cewa.
"Bafa zuwa nake yi ba da kai na, a'a ina dai bawa khaleefa yana siyo min nima rannan ne Abba ya aiko min dashi. Naci naji dad'i shine nake bayarwa yana siyo min."
"Okey yanzu naji batu na d'auka kinyi tunanin nan ma kauyan Sani ne, kowa zai iya fita san ransa."
Baki ta turo tana yatsina fuska ya fita, leda biyu yayo musu sannan ya dawo motar yana kallonta yaga still a shagwa6e fuskarta take ya shareta domin so yake su k'arasa gida zaifi jin dad'in lalla6a ta.
A bakin gate ya tsaya ta fito suka shiga gidan, tun a parking space ya rik'ota tana turesa yayi niyar d'aukarta sai dai yana ganin bazai iya ba sabida cikinta gashi ba laifi INdo kamar (Ummi Aisha take ba ruwa na lol).
"Goya ni toh."
Sadeeq ya zaro idanuwa jin abinda ta fad'a, yana kamo hannunta suna tafiya yace.
"Ina tunanin yadda zan iya d'aukarki ke kina cewa na goyaki kin manta abinda yake cikin ki ko."
"Toh gaskiya tunda kayi niyya malam Sadeeq to ka goya ni."
"A'ah cutie ni ba niyya nayi ba, cewa nayi Ina tunanin yadda zan d'aukeki kekuma ma goyo zaki ce."
A bakin k'ofar d'akin ta tsaya ya ajiye leda d'aya kusa da k'ofar yaje ya tayar da gen ya d'auka ta shiga ciki amma sai ya ganta tayi kalar tausayi ta kuma turo baki yayi dariya.
"Mata problem. Nan kiyi can tayi Allah ya sa in iya muku."
'Daukarta yayi suka shiga ya dinga k'ak'aro nishi tana dariya, yana ajiyeta ya zauna ya d'aura kansa akan cinyarta.
"Masha Allah sati d'ayan da nayi a garin nan yasa kin kuma yin k'iba, nan gaba sai kin kasa tashi cutie Aisha."
"Ni kadena cemin nayi k'iba."
"Na dena ina balagun naki?ko bazan ci ba?!"
INdo tace. "Kaje kuci kaida Fateema nima kaga mu biyu zamu ci wannan."
"Nak'i wayon wannan zanci."
Tashi yayi yaje ya shigo da ledar ya kuma zuwa ya d'akko plate da zo6o tare da kofina ya ajiye, anan falon ya rage kayan jikinta ta zauna daga under wear sai have vest kasan cewar yanzu bata sanya bra tana d'an takura mata ciwon k'irji.
Kallonta yake tamkar zai shige cikin jikinta farat d'aya, remote ta d'auka tare da kunna TV ta juyo zata ci naman taga sai kallonta yake cikin mamaki tace.
"Wai ya haka ne?!"
Sadeeq ya shafa k'eya tare da komawa kusa da ita ya zauna ya sanya hannu ya rik'ota tare da kwanciya a bayanta murya sassanya yace.
"Aisha banyi tunanin zaki dawo haka ba, lokacin da kuna j.s one ko k'irg..."
Bata bari ya k'arasa ba tayi saurin rufe mai baki da hannunta. Dariya ya dinga yi ta d'auki naman tafara ci sannan ta sakar mai baki yace.
"Zanci."
'Daukowa tayi ya rik'e mata hannu, fuskarta ya kama sannan ya sanya bakinsa a hankali cikin nata sai faman zaro ido takeyi. Gani tayi ya ciro na cikin bakin nata yana k'arasa taunawa ta bishi da kallon mamaki, yanzu kam ta tabbatar da cewa Sadeeq yana sonta, a shirye yake tsab da ya shiga cikin rayuwarta yayi mata duk abinda take so. Jiyayi kawai ta rungumesa tsam a jikinta a hankali kuma yaji tana zubar da hawaye ya d'agota yace.
"Sorry na 6ata miki rai ko? Bazan sake ba, bana son ganin hawayenki musamman ace nine silar zubar su."
Sabo ta d'akko tasa mai a bakin yayi murmushi ya fara taunawa idanunsa akanta, tana ganin ya fara taunawa itama ta rintsa ido tare da kai nata bakin cikin nasa kamar yadda taga yayi mata ya tura mata shi a bakinta da kanshi sa6anin shi da ya ciro nata da harshensa.
"Ashe ba haushi kikaji ba d'azu?!"
Ya fad'a yana lasar lips d'inshi. Juyawa tayi tana murmushi ta fara dangwala yaji tana sawa a baki. Mik'ewa yayi yana gyaran rigarsa yace.
"Na tafi na tabbata duk inda taje yanzu ta dawo, idan na isa zan kiraki."
"Toh a gaida ita."
"Ba rakiya?"
Dariya tayi ta mik'e suka fita tare, kamar karsu rabu haka sukeji amma babu yadda zasu yi dole ya fita ita kuma ta rufe gidan ta koma ciki zuciyarta fal Sadeeq domin ya tafine ya barta da abinda bazata ta6a manta shi bakoda da second d'aya ne.
****
A falo ya zauna tare da d'aukar laptop d'insa daya bari jikin charge. Fateema na jinsa ta d'an Lek'o har lokacin tunanin abinda zata cemai takeyi, ganin tana k'arasa 6ata lokaci yasa tayi shahada kawai ta shiga falon tana sanye cikin kayan bacci me wando k'arami wanda ko cinyarta be gama rufewa ba.
Kusa da k'afarsa taje ta zauna, shafar k'afar ta farayi wanda take cike da kwantaccen bak'in gashi. Sak'e mak'alo k'afar tayi sannan ya saki mai kuka a hankali hawayen na sauka a k'afarsa, har cikin zuciyarsa yake jin kukan amma ya shareta yana aikinsa, ganin haka yasa ta fara magana.
"Baby kayi hakuri dan Allah, wallahi raina ne ya 6aci akan abinda ka 6oye min kaida Aisha."
Jin abinda ta fad'a ne yasa shi cewa,
"Me kuma muka yi? Duk abinda muka yi Fateema ya dace idan har na kiraki ki amsa min amma kikak'i toh ina kikaje ma tukunna..?"
"Kayi hakuri baby, yanzu duk matsayin da nake a gurinka na matarka ace ka kasa gaya min cewar Aisha ciki gareta? Ko kana ganin kamar zan cutar da itane? Wallahi kaji dalilin da yasa kawai da na gani yau kawai sai na tafi gida, can kuma ina zuwa Yaya Shamsu ya dinga min fad'a, baby kayi hakuri da 6ata maka rai danayi dan Allah."
Zuciyarsa ce tayi sanyi jin itace ma take basa hakuri, ture laptop d'in yayi tare da janyo ta jikin sa. Gashin kanta da bata mai kitso ya dinga shafawa sannan ya numfasa yace.
"Kamata yayi tunda nine na kaiku duk abinda zai faru ki tsaya naxo na d'auke ku, amma ba komai nasan sharrin iblis ne. Sannan kuma ke ya kamata nayiwa wannan k'orafin cewar baki sanar min da cewar Aisha nada ciki ba sabida ku na bari tare har tsawon 3months amma baki gayan ba sai da na dawo na gani why baby?!"
Fateema ta d'ago tare da kwantar da kai cikin maganar tace.
"Wallahi ban ta6a lura ba kuma dai gaskiya bana wannan tunanin ganin nima har yanzu babu. Sai d'azu da na ji Hawwa na fad'a kuma na gani a zahiri."
Sadeeq ya sake kamota tare da cewa.
"Kinga kenan duk babu me laifi, Fateema bana son ki tashi hankalinki domin ina sonki a duk yadda kike. Kema Allah ba mantawa yayi dake ba domin da yawan aikin ne toh da yaci ace kema yanzu kin kusa ma saukewa amma fa Allah me meyi, yanzu three months da tafiya ta ita kuma cikinta wata hudu kinga kenan bayin kaina bane. Ina son dan Allah karki tayar da hankalinki rashin haihuwarki bazai rage soyayyarki ba a cikin Zuciya taba *I love you* Fateema Allah shine shedata."
" *I love you too* baby nima ka taya ni da addu'a na samu kafin na mutu."
Shhhiiii yayi mata bayan ya d'ora yatsansa akan lips d'inta. Shiru tayi sannan ya janyo ledar da ya shigo da ita taje ta d'akko cup's ta zuba musu furar suna manne da juna suna cin abin su idansa akan agoga yana son ya kira INdo kamar yadda yayi mata alk'awari.
Daya rasa yadda zai yi kawai sai ya tura mata text message.
"Affuwan cutie na ba credit da yawa a ciki gashi masu shops sun rufe, zamu had'u gobe I love nd miss you (#DeepKiss)."
Yana ganin sak'on ya tafi ya gogesa tas daga cikin wayar (tamkar miss Xoxo da take da cutar clearing masseges).
INdo na kwance ta gama duba littafin ta taji shigowar sako, a hankali d'aya bayan d'aya (word by word) ta karance sakon kafin ta tattarashi ciki kwakwalwarta ta sake nanata sakon gaba d'ayan sa sannan tayi murmushi ta kashe wayar ta kwanta, wani sabon yanayi na soyayyarsa yana shigarta haka ta dinga murmushi ita kad'ai a kan gado har bacci ya d'auketa.
Yayin da shi kuma yake can suna soyewa da Fateema wadda itama fatan ta da burinta da addu'arta a daren be wuce itama Allah ya azurtata da ganin gudan jininta ba.
*HAJJA CE*π
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *ββ MUSAYAR ZUCIYA...ββ*
β₯β₯
β₯
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*π
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*π‘
(Home of