Showing 51001 words to 54000 words out of 85627 words

Chapter 18 - MUSAYAR ZUCIYA COMPLETE BOOK by Hajja Ce.txt

Hajja Ce   

14 Sep 2025

43

zata yiwu ba sabida INdo bata sanka har agabana ta fad'a."

Shiru suka yi na tsawon lokaci gashi dare ya tsala ko'ina yayi shiru sai k'arar gen d'insu kawai akeji. Numfasawa Sadeeq yayi tare da janyota yace.

"Kiyi hakuri baby na yanzu dawowar da kikaga nayi Abba ne ya sanar da ni cewar an d'aura min aure da ita ni kaina ba..."

Jiyayi ta mik'e zaune a razane daga ita sai bra domin rigar ta zame Fateema ta bishi da kallo hannunta dafe da k'irji ya kalleta bayan shima ya tashi zaune. Wata shegiyar harara take wurga mai cikin zafin rai ta fara magana jikinta na rawa.

"Yanzu kana nufin har an d'aura muku aure?"

Sadeeq ya d'aga mata Kai alamar eh yasa hannunsa ya janyo ta a hankali ta fad'a jikinsa ta saki kuka me ban tausayi ya fara lallashinta shi kansa ji yake tamkar yaje ya bindige INdo. Babu yadda zatayi ita kuma haka tata k'addarar take daga yin aure sai kishiya suna cikin more rayuwarsu.

***

A 6angaran INdo kuwa wani uban nishi ta dinga saukewa duk iya k'ok'arin Mama na ta gaya mata matsalar ta sam tayi shiru tak'i yin magana har gari ya waye bata yiwa kowa magana ba Mama ta rasa dalili dan ta saki ranta yasa Mama cewa.

"Aisha gobe za'a kaiki gida kije kiyi kwana biyu kafin Sadeeq d'in ya ware yadda zai yi."

Sai a sannan INdo tayi magana tana dariya tace.

"Toh Mama amma dai ba shine zai maida niba...?!"

"Toh ai Aisha yanzu dai komai yana hannunsa sai abinda yace kiyi mai biyayya kedai anan zaki samu aljanna."

Ba zato cikin subutar baki tace.

"Ta6 d'ijam.."

Mama ta kalleta cikin mamaki amma sai taga INdon na mutsu-mutsu da baki alamar magana take a ranta lallai yaran nan da alama zasu basu mugun mamaki sam basuyi zaton INdo zatak'i Sadeeq ba ganin yadda suke kammani da mijinta ba....

#MZ
#Fan's
#luv-all







*HAJJA CE*πŸ‘ˆ
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *βš—βš—MUSAYAR ZUCIYA...βš—βš—*
β™₯β™₯
β™₯
A true life story

Na

*K.A.S Precious Hajja ce*πŸ‘ˆ

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*πŸ’‘
(Home of expert & perfect writer's)

*VOTE me on wattpad @Hajjac*

*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu


*A gaskiya ina alfahari daku masoya, comments d'in ku yana sani jin dad'i both wattpad & WhatsApp. Bazan iya lissafo sunayanku ba sai dai ina yiwa duk wata mai bibiyar labarin nan fatan alkaira Allah kuma yabar kauna da soyayya love you all*❀


Page *26*

A 6angaran su Sadeeq kuwa dakyar ya iya fita lecture, itama Fateema bata fasa yi mai breakfast ba sai dai duk babu wanda ya iya ci. Yana tafiya Fateema ta shiga cikin d'aki taci kuka sannan ta d'auki wayarta ta k'ira Ummanta, tana d'agawa ta fashe da kuka hankalin Umma yayi matuk'ar tashi tana tambayar lafiya.

"Kiyi shiru kiyi min magana dan sai kin min bayani sannan zansan matsalarki."

Cewar Umman ta cikin lalla6ata dan ta gaya mata. Cikin kukan Fateema tace.

"Umma Sadeeq ne ya k'ara aure jiya..."

Tayi maganar muryarta na hard'ewa hankalin Umman ta ya tashi tace.

"Fateema a ina yayi auran bako labari?"

"Umma yazan yi matar d'an uwansa aka aura mai jiya shima be sani ba, sai da Abban su ya k'irasa ya gaya mishi."

Ji tayi Umma ta sauk'e ajiyar Zuciya hankalin Fateema ya tashi tana cikin bargo amma wani irin mugun sanyi takeji yana ratsata, jita yi Umma na cewa.

"Oho Allah sarki, Fateema toh karki damu kinga kema wannan kaddarar batak'i ta sauka a kanki ba, kiyi hakuri ki zauna ki taya mijinki zama da ita ba'a san abinda Allah ya shirya ba akan al'amarin. Ina son ki kwantar da hankalinki karki sake ki nuna masa cewar kina bak'in cikin wannan auran idan kikayi haka nan gaba kezakiji kunya sabida shirin na Allah ne dan da be d'auki Abubakar ba da hakan baxata faru ba, ki kankaro mana mutuncin mu ta hanyar k'ar6ar wannan auran cikin nuna farin ciki koda ba hakan bane a ranki."

Wani irin kuka Fateema ta kuma fashewa dashi wanda da kyar ta iya yin sallama da Umman tata. Kuma k'udindinewa tayi a cikin bargo tana cigaba dayin abinta har zazzafan zazza6i ya sake rufar mata.

Sadeeq kuwa yana kammala lecture ya fito daga school d'in, kai tsaye ya wuce gidansu Fateema ya samu ba kowa sai Umma. Shiga yayi har cikin falonta ya zauna suka gaisa cikin fara'a ba tare da ta nuna mai komai ba.

Cike da ladabi Sadeeq yayi ma Umma bayanin yadda lamarin ya wakana sannan ya dad'a da nunawa Umma ta yiwa Fateema nasiha tare da tayashi bata hak'uri, Umma tayi murmushi tare da cewa.

"Karka damu Sadeeq Allah ne yasan abinda ya shirya har akan ta faru, insha Allahu kuma zanyi mata nasiha kaima sai kayi hakuri kasan irin wannan lamarin sai mutum yana kawar dakai dan zakaga ban-banci d'abi'a akan ta baya da kuka yi."

Sadeeq yana sunkuyar dakai yace,

"Insha Allahu Umma na gode Allah ya k'ara girma."

"Amin a gaida mutanan gidan ace muna yi musu Allah ya sanya alkairi."

Batare daya amsa mata ba yayi tafiyarsa baya tunanin ma zai sake zuwa gidan harsai ya samu labarin cewar INdo bata gidan.

A kwance ya tarar da ita ko gidan bata bud'e ba sai da ya sanya mukulli ya bud'e. K'arasawa yayi tare da yaye bargon da ta rufa dashi ya ta6a jikinta mai d'auke da zazzafan zazza6i nan da nan hankalinsa ya tashi ya hau gadon gabaki d'aya ya d'aga zuwa jikinsa yana k'ok'arin san su had'a ido amma tak'i bari hakan ya faru.

"Baby na kinji jikinki kuwa? Meya sameki?!"

Wani kukan ne ya sake zuwar mata cikin rawar murya tace mai.

"Banajin dad'in jikina kaina ciwo yake."

"Oya tashi muje asibiti Allah yasa ma nayi ajiya."

'Dan janye jikinta tayi ba tare da ta kallesa ba ta koma ta kwanta tana cewa...

"Karka damu basai munje asibiti ba dan yanzu ma haka ciwon mara nakeji."

"Wayyo Allah baby na bana son wannan abun wallahi, nida da yadda za'ayi ma da nasa an tsayar miki ki denayin sa."

Shiru tayi mai batayi magana ba shi kuwa duk so yake yi ta dawo dai-dai yadda suke amma ina sai tashi yayi ya koma falo dan bazai juri ganin yadda take sharesa ba, ba kuma yason ya dinga 6ata mata rai.

Yana zaune a falo yana transfer d'in kud'i a account d'in mutanen daya k'ar6i kaya yaji wayarsa na ruri, d'auka yayi yaga Mama sai da k'irjinsa ya buga. Addu'a ya fara yi Allah yasa kar tayi mai zancen INdo domin sam baya k'aunar yaji sa.

"Hello Mama antashi lafiya?!"

"Eh Alhamdulillahi tunda bakaga damar zuwa ba, mekakeyi yanzu?!"

"Kiyi hakuri Mama bak'in zuwa nayi ba yanzun nan na dawo daga lecture, ina gida nazo?!"

"Eh dama cewa zanyi ka shirya kazo kakai Aisha garinsu ta d'anyi musu kwana biyu kafin ka samar mata gurin zama."

Had'e rai yayi tamkar a gaban Maman ransa na suya baya son kuma komawa garin nan duk da cewar sunyi zaman amana dashi amma a yanzu ga Fateema ba lafiya sannan ance yazo yakai INdo garinsu sabida kawai shi aka sakawa ido komai sai ace shi dama shi ya mutu ba Abubakar ba da duk ba'ayi mai wad'annan abubuwan ba.

"Kayi shiru Sadeeq kona shirya tunda nina d'akkota sai na mayar da ita."

Yaji Mama na fad'a cikin fad'a-fad'a. Lumshe idanuwa yayi tare da shafar sajan sa yace.

"A'a Mama kiyi hakuri bari nayi wanka zanzo."

"Toh shikenan kazo kowane lokaci ne sai ka kaita duk ka gama walagigin naka muna nan muna jiranka."

Tana kammala fad'a ta katse k'iran shi kuma yabi fuskar wayar da kallo, shikam ya shiga uku wannan wace irin kaddara ce ta hau kansa. Ya kasa gane abinda Abubakar ya gani a gurinta har yaji yana sonta, ita ba ilimi ba sannan ba Kud'i ba, ba wani shegen kyau ne da itaba sai shashanci ga6untaka kauyanci da rashin wayewa duk ita kad'ai shikam a takaitashi da auranta da aka bashi.

Tashi yayi cikin sanyin jiki ya shiga d'aki, fuskar fateema ya kalla sannan yaje ya shafa fuskar yana kallonta. A hankali ta bud'e sukayi ido hud'u yace.

"Tashi kisha magani kici abinci zansa su Haleema suzo su tayaki zama Mama ta kirani wai zankai Aisha gidan su yanzu kinji.?!"

K'irjin Fateema ya fara harbawa ganin tun yau sun fara raba abubuwa tsakaninsu, da kyar ta daure tace.

"Toh sai kun dawo amma kabar su Haleema basai sunzo ba babu abinda zasu yi min."

Magani ya d'akko ya fita kitchen ya d'akko ruwa sannan ya zauna kusa da ita, dakyar tasha maganin sannan ta kwanta shi kuma ya shiga cikin bathroom yayi wanka gaba d'aya ma besan abinda zaiyi ba akan INdo.

Fitowa yayi d'aure da towel a k'ugunsa ya k'arasa wajan mirror duk Fateema na kallonsa a sace ta cikin bargo. Sai daya gama goge ruwan jikinsa sannan ya zauna kan stool yana shafa mai. Yana gamawa ya nufi wardrobe ya zaro wata shadda blueblack ya sanya tare da d'akko bak'ar hula zannah ya kafa kan goshi, ya sanya agogon hannu ya zura takalmi bak'i tare da feshe jikinsa da turare ya d'auki comb brush ya kwantar da gashin daya zagaye kyakyawan bakinsa.

Duk abinda yake yine yayi amma da Fateema tasan inda zashi sai taji k'irjinta na harbawa zuciyarta na zafi wani bak'in kishi ya mamaye ciki da wajan zuciyarta bata san lokacin da hawaye suka zubo mata ba tayi saurin maida fuskarta cikin bargon ganin zai juyo.

Sadeeq ya k'arasa gurinta bayan ya durk'usa saitin fuskarta ya kura mata ido.

"Babyna karki dinga sanya ranki cikin damuwa, kece mace ta farko dana faraso na kuma fara aura na fara baiyana mata sirrina na kuma yadda da ita, ina so ki dinga alfahari da hakan kina cikin zuciyata bazan ta6a yadda wani ya 6ata miki rai ba ko ya gaya miki ba dad'i in kyalesa.

Ke ko Aisha da aka aura min idan batayi miki biyayya ba sai na sa6a mata wallahi ke nine nace ina sonki ita kuma mutuwar twinnie d'inane yasa aka bani auranta karki dinga damuwa kinji ko.?!"

Sai a lokacin Fateemah taji sanyi ko ba komai ya kwantar mata da hankali da dad'ad'an kalamansa masu zak'in zuma. Kallonsa tayi idanuwanta duk sunyi jah tsabar kuka sannan ya zuro hannu ta shafi fuskarsa tace.

"Nagode da wannan matsayin daka bani, ka tashi kaje kaga da nisa Allah ya dawo min dakai lafiya, a gaidasu Mama."

Murmushi yayi mata tare dakai bakinsa kan nata yayi kissing d'inshi sannan ya mik'e tsaye yana ce mata.

"Amin babyna sai na dawo."

Fita yayi ya shiga mota yabar gidan.

Kai tsaye gidan Mama yayi, a k'ofar gate yayi parking sannan ya fito ta shiga gida cike da tak'ama dan yau jinsa yake tamkar akan iska. Yana shiga k'annansa suka hau gaidashi ya amsa musu sannan ya lek'a d'akin Umma ya tarar tana sallar azahar ya koma ya shiga d'akin Mama.

Cike d'akin yake da k'amshin turaran humra Sadeeq ya bud'e hanci yana shak'a, tsaye yaga INdo ta gama d'aurin d'ankwali ya kalleta tare da jinjina kai. Idan besan asalin INdo ba da ace yau shine karo na farko daya fara ganinta toh bazai mata hausa ba dan babu abinda zai hanashi d'auka cewar batayi degree ba a boko. Sai dai kashhh shine yasanta yasan ko wacece a fannin dak'ik'anci da rashin son karatu tun batakai haka ba dan haka yana shiga gurin Mama ya nufa yana mai cire hular kansa.

"Mama na ina wuni?!"

"Lafiya lau Sadeeq na d'auka ma bazaka zo yanzu ba, ya gidan ya Matar taka?"

Sadeeq ya koma bakin gado ya zauna yana cewa.

"Haba Mama na isa ink'i zuwa, lafiya lau take tana gida ma batajin dad'i."

Yayi maganar yana kuma karya k'arin hularsa. INdo kuwa ci kanka batace masa ba Mama na ganin ikon Allah taga wazai fara yiwa wani magana sai taga kowa yana harkar gabansa. Kasa yin shiru Mama tayi sai da tace.

"Aisha wai bakiga Sadeeq bane, naga ko gaidashi bakiyi ba!"

Ba kunya INdo tace,

"Mama ai yace idan na sake ganinsa na kusala tom d'ina, har wawuya yace min a ranar."

Baki bud'e Sadeeq ya kalleta, rabon daya ganta tun rasuwar Abubakar sai jiya da Abba ya had'asu sai kuma yanzu amma ji sharrin da tayi mai cikin jin haushin ta yace.

"Karki rainawa mutane hankali yaushe na fad'a.?"

Nan ma ba tsoro bare kunya tace.

"Lokacin rasuwar marigayi sanda nazata bashine ya mutuba Ina murna na rik'eka ka tureni kace karna sake kulaka, a lokacin ne na tabbatar da cewa Kaine malam Sadeeq, shi yasa bazan gaida kaiba tunda kace haka."

Tsaki yaja tare da maida hularsa kansa, gaba d'aya ma besan ya fad'a ba yasan dai lokacin ta bashi haushine. Lallai yarinyar nan akwaita da rik'o toh kar Allah yasa ta gaidashi sai me (so what).

Mama ce ta kalleta cikin nuna mata martabar miji tace.

"Aisha ya kamata ki ajiye komai daya wuce tsakaninki da Sadeeq, yanzu mijinki ne dole zaki mai biyayya kamar yadda musulinci ya gindaya. Yanzu ki gaida shi bana son wani tashin zance."

Babu yadda zata yi domin a haka tana ganin k'ima da darajar Mama, cikin turo baki tace mai.

"Ina wuni?!"

Dan kar shima Mama tayi mai magana yasa shi amsawa a takaice yace.

"K'alau."

Mama ta jijiga kai tare da rik'e ha6arta, Sadeeq kawai zata jawa kunne domin shine miji kuma shine sama da INdo duk abinda ya d'orata akai shi zatayi ta kuma k'ara akan wanda take dashi zama tazo yak'i dad'i suji kunya amma zata bari sai ya dawo daga kaita tukunna.

Tashi yayi ya fita bayan yace su sameshi a waje. Sosai sukayi sallama da mutanen gidan suna mata fatan sauka lafiya INdo na amsa musu. Gaba Haleema ta bud'e mata babu gaddama ta shiga shi kuma Sadeeq yaja motarsa suka wuce INdo sai dariya take tana jin dad'in yadda duk suke sonta.

Tunda suka fara tafiya yake amsa waya duk ya cika mata kunne, hannu ta zuwa ta kunna redion motar dan ta riga ta iya Abubakar ya nuna mata sannan ta kunna A.c ta zuge glass d'in kusa da ita. Sadeeq ya sanya hannu ya kashe redion yana wayar sa itama ta kuma kunnawa tare da cewa.

"Haba Malam Sadeeq kana wayarka mana ni kuma ina jin redio na bashi kenan ba."

Wata muguwar harara ya watsa mata ta ta6e baki tare da juyawa tana kallon hanya. Abinda yake k'ona mata rai da turanci yake maganar sai Hausa da yake d'an cillawa. Wayarta ta d'akko wadda tun Abubakar ne daya sai mata ta fara d'aukar photo tana selfie style kala-kala ko kulata beyi ba harya gama wayar ya ajiye ta.

Gajiya yayi kunnuwansa sun cika da k'arar camera ya warce wayar daga hannuta tare da cilla mata ita kan cinya yace.

"Ke bana san kauyan ci fa."

Kallansa tayi hannunta rik'e da ha6arta tana cewa.....











*HAJJA CE*πŸ‘ˆ
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *βš—βš— MUSAYAR ZUCIYA...βš—βš—*
β™₯β™₯
β™₯
A true life story

Na

*K.A.S Precious Hajja ce*πŸ‘ˆ

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*πŸ’‘
(Home of expert & perfect writer's)

*VOTE me on wattpad @Hajjac*

*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu


Page *27*

"Malam Sadeeq kenan, ai da kasani ba yanzu ba."

Shareta yayi ya nuna tamkar ma bejita ba ta juya tana kallonsa ta kuma d'aukar wayarta daya cillo mata. Madubin saitin kujerarta ta bud'e tana gyara fuskarta ya girgiza kai dan shi dama yasan da wahala yarinyar tayi hankali sabida babu arabi ba boko yaja tsaki har kusan sau uku sannan INdo ta kallesa tace.

"Babu kyau fa."

Yace "Ni zaki cewa babu kyau? Ko kin fini sanine da zaki cemin babu kyau?!"

"Allah ya baka hakuri, cewa akayi idan kaji wani ko wata sunyi abinda ba kyau ka tuna masa, toni tuna maka nayi."

"Karki i sake tuna min domin tun kafin kisan hakan nasani, ke karki sake yin magana har muje inda zan kai kina jina.?!"

Bata sake kula shiba har sukaje danja masu tallar abubuwa suka dinga d'ago musu taga me alawar madara da sauri ta zaro d'ari biyu ta mik'a masa ji Sadeeq kawai yayi tana cewa.

"Bani ta dika."

Aikuwa ransa ya kuma mugun 6aci Allah-Allah yake kafin a gama mik'o mata ya figi motar amma danja batazo kansu ba harsai da aka bata tasa a jaka sannan aka basu hannu. Leda d'aya ta mik'a masa tace.

"Malam Sadeeq bisimillah."

"Banasha."

Maidawa tayi cikin jaka ta bud'e leda d'aya tana sha har wani kunkuni takeyi irin na zak'in nan idan ya gauraye kunne. Wayarsa ya d'auka yasa earpiece tare da kiran layin Fateema, sai da ta kusa yankewa sannan yaji ta d'aga cikin sanyin murya tayi mai sallama.

"Ohh babyna har yanzu jikin ne?!"

Ya fad'a cike da damuwa, can 6arin Fateema tace.

"A'ah kawai dai bacci nake, kun tafi ne?"

"Eh muna hanya ma yanzu zan dawo insha Allah, amma ki tashi ko tea ne kisha zaki kuma samun relief."

"Toh Allah ya kiyaye hanya a gaida min ita."

Tana kaiwa nan yaji ta katse, ba haka yaso ba yaso suyi hira ta d'ebe mai kewa amma tariga ta kashe ya cire earpiece d'in yana cigaba da tuk'insa ba tare daya sake kallon koda inda take ba.

"Malam Sadeeq dan Allah ka kar6a kasha, wallahi tayi dad'i madara ce zallah."

Yayi shiru ta kuma cewa.

"Inkaji dan Allah sha d'aya kaji."

A fusace ya juya yana kallonta shi har lokacin be manta yanayin ta na baya ba cikin 6acin rai yace.

"Wai dole sai na Shane? Idan dole ne toh sani insha dan Allah."

Ya fad'a tare da d'an kallon gabansa kafin ya juyo yana dank'ara mata harara, d'aya ta d'akko da sauri ta danna mai ita a baki ya yi saurin furzar da ita a k'asa amma duk da haka sai da zak'in ya shiga ko'ina na cikin bakinsa ya samu gefen titi ya tsaya tare da nuna ta da yatsa yace.

"Wallahi tallahi Aisha ki kiyayeni karkija wata rana na 6allaki yasin. Kinga ina shiga sha'aninki ne? Toh ki kuka da kanki duk rashin kunyarki a tafin hannuna take...!"

Jan bakinta tayi ta tsuke bata sake cewa komai ba har suka shiga garin Sumaila, tana ganin barkono dama sund'an tsaya sabida ana bada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login