Showing 57001 words to 60000 words out of 85627 words
muje mu dawo."
Yana fad'a suka fice ita kuma ta shiga d'aki. Ko Ina tas-tas a gidanta bata barin k'azanta sannan kullum cikin k'anshin turaran tsinke d'akin yake dan haka INdo tana samun customers a rana sai ta dura jarkokin zobo dana kunun aya guda d'ari biyu amma baya kaiwa dare Allah yasanya mata nasibi a ciki.
A ranar bataga Mubasheer ba har kwana biyu sai gashi yazo, tsayawa yayi yace ya gama mata komai zuwa kawai zata farayi domin sai da ya sanar da abban su ya kuma bada goyan baya sosai. Juma'a na zuwa ta fara zuwa cikin tsoro da fargabar yadda zata tun kari malamai da d'alibai dan tasan duk sun fita k'ok'ari.
"Matar broth ga class d'inku nan."
Mubasheer ya fad'a yana nunawa INdo ajinsu. Ido ta dinga kwalowa waje hannun ta na dama dafe da k'irji ta kalli Mubasheer cikin tsoro tace.
"Anya bazan koma gida ba, Mubasheer tsoro nakeji wallahi."
"Kai Matar broth wallahi karkiji tsoro kowa fa da kika gani zuwa yayi a koya mai, idan kika nuna musu kina jin tsoro zasu raina ki kedai karki fasa yin abinda kike so ki shiga kawai."
"Toh bari naje idan mun tashi zan yi maka waya kazo ka maidani gida."
"Toh Matar broth Allah ya bada sa'a."
A hankali INdo ta shiga tashin farko ganin yadda hall d'in yake yasa gabanta bugawa da k'arfi sannan ga d'alibai nan a zazzau ne duk sai ta daburce ta rasa inda zataje cikin sauri ta juya zata fita sai taga Mubasheer a tsaye yana dariya, cikin tsananin jin kunya tace.
"Maidani gida bazan shiga ba."
"Hahaha...! Wallahi babu inda zaki, muje na shigar dake haka kurum dan ayi asarar kud'i sai da aka gama komai zaki wani ce kin fasa."
Yana gaba tana bayansa har ya k'arasar da ita tsakiyar kujerun sannan yayi wa wata budurwa magana cewar gata nan dan Allah ta fara helping d'inta ta wasu abubuwan. Karimatu tayi murmushi tare da mik'awa INdo hannu suka gaisa ta zauna a d'ari-d'ari kamar munafuka sai wulkita idanuwa take a haka Mubasheer ya barta yayi tafiyarsa.
Malami na shiga ta fara sunkuyar da kai, nan aka fara gabatar da lesson kasan cewar ajin masu koyan turanci ne hakan yasa komai ake yi musu dalla-dalla cikin hikima da kuma kwarewar malaman ita dai INdo tayi tsit bata ko kwakwaran motsi dan karma malamin yayi mata tambaya koya saka mata ido. Alhamdulillahi kuma ta tsinto abubuwa kasan cewar sai anta maimaita musu abu anji kowa ya gane an kuma fahimta sannan za'a shiga wani abun haka aka dinga yi musu tana kuma zuwa duk juma'a asabar da lahadi da safe.
****
Wata d'aya da sati biyu su Sadeeq sukayi a kwara state sannan suka juyo suka dawo kano. Lokacin satin INdo biyu da fara zuwa makaranta, sam bata yi wani murna da dawowarsa ba sema haushi da takaici dataji. Sai da yayi kwana biyu a gidan Fateema sannan ya waiwayo yau zaije gidan da INdo take.
K'ofar gidan ta tsaya wajan k'arfe sha biyu na dare, key d'insa na gidan ya zura ya dan bud'e abu ya gagara sai yahau buga mata tana kwance a kan gado da littafi a hannunta tana Home work d'in da aka basu, tanaji saidai batasan kowaye ba dan haka batayi ma niyar tashi zuwa ta gano ba.
Mtwwww yaja tsaki tare da ciro wayarsa ya nemo layin Haleema, mtwww ya kuma jan wani tsakin jin tana amfani da ita ya sake kiran khaleel cikin sa'a ya d'auka murya a shak'e Sadeeq tace.
"Dan turo min da number'n Aisha."
Khaleel yace "Yaya bani da ita sai dai ko yah Mubasheer."
"Cene masa ya turo min."
Ya fad'a a dak'ire sabida babu kowa unguwar sai shi kad’ai ga duhu. Yana tsaye yaji an turo ya kira number'n kamar bazata d'auka ba sai kuma tayi picking tare dayin shiru dan taji me maganar.
"Ke zoki bud'e min gida kinaji Ina bugawa kik'ak'i zuwa ki bud'e min."
Harzai katse yaji tace. "Waye kai d'in? Wa kuma kake nema..?!"
"Au bakima san waye ba dan rainin hankali Aisha?!"
Tace "Kai kaga k'ila wrong number ne go and check."
Kafin yayi magana ta katse kiran ta cigaba da aikin ta, Sadeeq yabi fuskar wayar da kallon mamaki ya sake buga gate d'in da karfi cikin jin haushi amma tak'i bud'ewa cikin 6acin rai ya buga number'n Mama tana bacci Haleema ta d'auka tana dubawa taga Sadeeq dan haka ta d'an janye wayarta daga kunne da takeyi da saurayinta ta kara tare da cewa.
"Yaya lafiya? Mama tayi bacci fa."
"Yauwa Haleema kira number'n Aisha kice ta bud'e min gidan Ina waje."
"Okey tom Yaya sai da safe."
Tana kashewa ta kira layin INdo, tana kwance duk tama rasa yadda zatayi Home work d'inta taga kira ta duba a tunaninta number'n d'azu ce tayi niyar d'agawa tayi mai rashin mutunci sai kuma taga Mmn dacta da haka akayi mata saving sunan tayi murmushi tare da karawa a kunne tana shirin gaida ita taji Haleema na cewa.
"Aunty Humairah Yaya fa yana k'ofar gida yace kije ki bud'e mai nidai sai da safe."
"Dama shine? No wonder naji ya fad'a da gadara zoki bud'e min gida, d'an rainin hankali ai na d'auka harka koma bazaka zo ba."
Hijabi tasa ta d'auki mukulli tayi waje, cire kwad'on (pad lock) d'in tayi ta bud'e mai ya shigo sannan ta juya ta koma, shi ya bud'e gate din yasa motar sannan ya rufe gidan ya shiga ciki. Bata falo ya bita bedroom fuskarsa a had'e yana shiga ya ganta kwance da littattafai a gabanta da biro da alama rubutu takeyi baki bud'e cikin tsananin mamaki yace...
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu.
Page *29*
"Aisha wannan kuma books d'in waye kike ta lalatawa haka.?!"
Cikin rashin damuwa tace, "is my own."
"Ooh your own?!"
"Yes..!?"
"Toh zane-zane kikeyi or what.?!"
"Home work nake yi."
Tayi maganar tana sake karkad'a biron hannunta, Sadeeq ya zaro idanuwa yana rik'e da ha6arsa kafin ya matsa kusa da ita yanan kallon littafin da take yin rubutun yana jijiga kai ganin note d'in tamkar tafiyar tsutsa wani yayi k'asa wani tsakiya wani sama ya zauna bakin gadon tare da kallon littattafan gurin ya gansu duk na turanci. Karo na farko daya fara zama kusa da ita duk da cewar ba kusa da jikinta ya zauna ba ya d'an bada gap.
'Daukar littafin kusa da ita yazo zai yi INdo tayi saurin janyewa ta 6oye k'ark'ashin cikinta tana faman harhad'e fuska dan bata son ya kushe mata rubutunta, ya ta6e baki tare da d'aga kafad’a yana cewa.
"Toh furniture's d'in d'akin kike drawing d'insu ko me kike yi hakan?!"
"A'a ba d'aya malam Sadeeq, makaranta nake zuwa kuma acan ake koya min wannan karatu."
"Ooh which school ne suka iya d'aukarki a haka Aisha..?!"
Cikin jin haushin sa INdo ta tashi zaune tana kuma 6oye book d'inta tana rurufe idanuwa tace.
"Dan Allah malam Sadeeq ka kyale ni haka nayi abuna ka takura min, neman ilimi naje yi sai yanzu Allah yayi zanyi, lokacin da marigayi dacta yana da rai bashi da wani buri daya wuce yaga nayi karatu amma kai sai afkin yiwa mutane gori toh nima na shiga school yanzu zan zama tauraruwa wata rana so what.?!"
Sadeeq ya tsaya kallonta, sosai tayi k'iba tayi bulbul da ita tayi fresh, duk da Cewar sleeping gown ce a jikinta kuma me d'an kauri hakan be hana bayyana yadda cikar halittar k'irjinta bayyana ba, Sadeeq ya d'auke kansa tare da ta6e bakinsa yace.
"Kinyiwa kanki gata kuwa Aisha, sai dai nasan zaki sha wahala tunda ba iyawa kika yi ba tun farko sai yanzu ne kika fara, shin waye ya kaiki school d'in and waye yake biya miki kud'in?!"
"I am, kasan ance sa kai yafi bauta."
Ta fad'a tana jin tsoran kartaje ya gwasaleta yace ba haka zata ce I am ba, sai kuma taji yace.
"Good hakan ma yayi kyau, but zan cigaba da biya miki ai ilimin yana da dad'i nan gaba zakiji dad'insa idan kika yi."
"No kabar abunka zanyi abuna da kaina, ko ka manta sabida rashin Ilimi na yasa kace ba zaka tafi dani inda kukaje da Fateema ba? Hmm! Allah yaji k'an dacta na, cewa yayi wallahi babu inda baxai iya shiga da niba dan har gaban Obama zai iya zuwa dani kuma yace matarsa ce. Ka tashi ka tafi ka kwanta ni bacci nakeji."
Tayi maganar tana share hawayen daya fad'o mata. Kallonta yayi tsab yaga ta tsuke fuska bayan ta goge kwallar sannan yace.
"Aisha ki lalla6ani, wallahi Zan iya hanaki zuwa school d'in inga ta tsiya dan dama baki gaya min ba ai kika fara zuwa."
Tace "lallai malam Sadeeq, ai wallahi tallahi sai dai ka sakeni in tafi gida dama baka sona nima bana Sanka kaga sai kaje kaji da matarka Fateema nima inje inyi karatuna so what."
"Wato har yanzu baki da kunya ko Aisha? Wallahi zaki sha mamaki na."
Ya fad'a tare da barin d'akin cikin sauri ya koma falo yana jin wani mugun 6acin rai, ko wane munafikin ne yazo ya gaya mata wannan maganar, wannan yarinyar idan ta kuma wayewa sai tafi k'arfinsa gara ma ya togeta daga makarantar ya sanyata islamiya ko zata dinga rissinawa.
***
Washe gari yana farkawa ya fito yayi hanyar bathroom d'in tsakar gida, yana zuwa yaga kaji gaba d'aya gurin ya zama tamkar dama dansu yayi, cikin tsananin mamaki ya fara tunanin toh kajin waye ta kar6o haka dan wulak'anci ake 6ata mai gida. A fusace ya koma ciki ya nufi bedroom d'inta, tana kwance sai shak'ar bacci take tayi d'ai-d'ai da ita books d'in wasu sun fad'i k'asa wasu kuma ta dannesu ya k'arasa kusa da ita cike da masifa zai tashe ta yaga abunda yasa shi saurin shigewa toilet d'inta yana dafe k'irjinsa.
Ya dad'e a tsaye kafin yayi alwala ya fito beko kalleta ba ya fita falo yayi sallah, yarinyar akwai d'aukar hankali komai nata a wannan stage d'in ya cika yaja tsaki tunowa da yayi sanda take zuwa da yagaggun kaya ya kwanta akan doguwar kujera yana sauke numfashi.
Jiyo motsinta yayi sai da ya d'an dad'e har gari ya fara wayewa sannan ya mik'e ya shiga cikin bedroom d'in nata. Tararwa yayi tana k'ok'arin fitowa suka yi karo da goshinan su INdo ta dafe gurin tare da fad'in.
"Kai-kai-kai..!"
Shareta yayi domin shima sauran k'iris yayi wai-wai-wai sabida tsabar zugi amma ya maze.
"Ke meye wancan a bayin waje.?!"
"Ina kwana?"
Itama ta fad'a kafin ta bashi amsar daya tambaye ta, a ciki ya amsa bata damu ba tace.
"Kaji nane."
"Wai Aisha haka kikeyin duk abinda kika ga dama ne? Yanzu me kikeyi da kaji.?"
"Masu kwai nefa malam, idan suka yi kwai nikuma sai na siyar, ance macen da bata sana'a aurace toh ni Ina yi kuma da kud'ad'an na shiga makaranta nayi kud'in napep. Malam tunda ka dawo baka ce INdo sau nawa kikayi rashin lafiya ba amma sai tambaya ta kakeyi abubuwan k'aruwata."
Shiru yayi domin tafishi gaskiya kuma sam beyi tunanin tambayar tata ba dan haka a wannan maganar yaji kunya, amma dan ya raina ta sai cewa yayi.
"Toh dama ke kina rashin lafiya ne? Naga tunda ban ta6a jin ance kinyi cuta ba, kuma da kinyi toh Abba zai gaya min."
Shiru tayi ta shiga kitchen, indomie ta jik'a sannan ta jajjaga kayan miya ta ajiye tare da komawa cikin d'aki yana zaune a falo yana waya da Fateema ta sharesa dan sam batajin haushi bare ya d'aga mata hankali. Sai da ta dubi lokaci tasan indomie d'in ta jik'u sannan ta shiga kitchen ta soya ta dafa tea ta kawo kan center table ta ajiye da kofu na guda biyu ta zauna tare da cewa.
"Ga abinci malam Sadeeq."
Lokacin sun gama waya yana chatting ya kalleta ya kalli agogon dake kafe a falon yaga k'arfe bakwai sauran minti uku, yanzu ne za'ayi breakfast sai kace ba yanzu aka tashi daga bacci ba yace.
"Tun yanzu ake yin karin kumallo.?!"
"Eh ai garin ya waye malam Sadeeq me zamu jira."
"Aci lafiya toh."
Ya fad'a ta kallesa cikin mamaki sannan ta fara had'a tea d'inta, ta iya cin abincin kuwa kad'an kad'an harta gama ci yana satar kallon ta. Tana gamawa taje ta fara dafa zo6on ta kasan cewar ranar Monday ce batada school ta wanke ayarta tana jiran lokacin da almajirinta zai zo ya kai mata markad'e.
Shima Sadeeq bacci yayi yana jiran lokaci yayi ya tafi gidan Fatima yayi wanka dan zaije lecture. Bata tashesa ba sannan duk batasan zai fita ba domin be sanar mata ba har tara da kusan kwata sannan ya farka yana duba agogo yaga har lokaci yayi da sauri ya mik'e ya d'auki mukullin motarsa, beyi mata sallama ba kawai sai tashin motarsa tajiyo taja tsaki sam malam Sadeeq bashida mutunci a jerin da ta sanya shi kenan.
***
Yana zuwa gidan Fateema yayi wanka ya shirya ya tafi, around 12:30pm ya dawo, cikin murna ta tare sa tare da rungumeshi ya d'agota yana cewa.
"Akwai bayani baby na zauna ki gaya min."
Sakinsa tayi ta k'arasa kan TV stand ta d'akko mai wata takadda, bud'ewa yayi ya karanta tare da zaro idanuwa yana kallonta cikin murna ya kuma rungumeta yana cewa.
"Woww babyna am so much happy wallahi, kin zama malama sai yau Allah yayi."
"Aikuwa baby kaji yadda naji kuwa, anjima zanje gidan Aisha idan zaka tafi please zanje kaga mun jima bamu had'u ba."
"Toh kinsan itama ta koma school fa."
"Kai baby shine koka gaya min sai yanzu danace zani gidan?
Sadeeq yace "A'afa nima sai jiya naji kuma kinga ai ban zauna ba sai yanzu, kinga bani abinci naci."
Tashi tayi ta shiga kitchen yayi farin cikin samun aikinta sosai domin yana son abinda take so, yana kuma son farin cikinta. Egg into egg ta kawo mai tare da kunun gyad'a ta zuba mai yasha madara ya zauna a hankali ta dinga bashi harya cinye yasha kunnun sannan suka ci gaba da soyayyar su tamkar babu gobe har mantawa suke yi da matsayin INdo.
Bayan yaje gidan Mama ya dawo sai ya d'auke ta suka tafi, gidan cike da masu siyan zo6o da kunun aya wasu na fita wasu na shiga inji yana tayi mamaki ya cika ransu sai da suka shiga sannan suka tarar da ita a zaune gaban k'atuwar kula duk wanda ya bata kud'i saita bud'e tabashi ya tafi, Sadeeq ya shiga ciki ransa a mugun 6ace shin yarinyar nan meta maidashi ne, wato ma ashe harta zama big hajiya besani ba Allah ya kaisu dare sai ya 6ata mata rai.
Sosai suka yi hira da fateema ta yadda har ta gano lallai itace star a gurin Sadeeq, anayin magariba ya maida ita gida wajan k'arfe goma yazo gidan INdo lokacin tana zaune a falo tana kallon film d'in Basaja na farko.
"Ke Aisha daman haka kika mayar min da gida tamkar gidan kallo? Maza da mata su dinga min strolling a ciki?!"
Tayi shiru ya kuma harzuk'a ta kuma yi mai shiru ganin yana masifa yasa ta cewa.
"Wai malam me yasa ka tsaneni ne? Nifa kamar yadda bakai kace kana sona ba haka nima bance Ina sonka ba. Yanzu da yake ita Fateema matarka ce ta so ai d'azu tazo ta nuna min takardar fara teaching d'inta kai da kanka ka kawo ta sai ni da nake sana'a a cikin gida da kud'ina amma ka dinga min fad'a kana Sa min ido? Toh ka sake ni dan Allah ka gani idan bazan rayuwa ba."
"Ni zaki cewa na sakeki Aisha? Toh bazan sakeki ba kuma karna sake ganin wani yaro ko yarinya sun shigo min gida."
Yana kaiwa nan ya kuma barin gidan sai dai be fita da mota ba, anya ta d'aura a zuciyarta na cewar bazata denaba tunda taga alamar bakin cikin ganin tacigaba yakeyi. 11:49pm ta d'auki pad lock zata kulle gidan taji sa daga waje jikin gate din yace.
"Malama karki rufemin gida."
"Gidan hayan."
Ta fad'a tana shiga falo yayi kwafa tare da shigowa ya rufe. Tuni ta shiga d'aki ya bita dan sake ja mata kunne kawai ya tarar ta cire riga tana niyar saka ta bacci hankalinsa yayi mugun tashi ya kasa controlling d'in kansa ita kuwa sam batasan yana tsaye ba saida ta gama saka rigar ta tashi tsaye domin da a zaune take ta ta6e baki tare da hayewa kan gadon.
Jikinsa na rawa dama Yaya lafiyar kura domin yana da tsananin buk'ata tun yana saurayi bare yanzu domin fateema harta saba da halinsa.
Cikin rawar jiki ya k'arasa kusa da ita kan gadon ya hau sam bata kulasa ba kawai taji ya janyo ta jikinsa suka fara fad'a Sadeeq yayi nasarar rungumota jinta a jikinsa yasa jikinsa ya kuma narkewa ya rasa abinda yake tunzura shi duk da irin naushin da yake sha a gurinta amma yak'i ya saketa.
"Wai meye hakan ne kake yi min."
"Shhhiiii..."
Yace da ita a dai-dai kunnanta, duk k'arfin INdo amma ta gaza kwatar jikinta Sadeeq ya sake rungumeta jikinsa sai karkarwa yake yi, cikin k'arfi da yaji sai da Sadeeq ya samu abinda zuciyarsa take muradi a gurin INdo. Jikinta daya raina yau sun had'u danasa, bakinta da yake ganin koda million d'ari bazai iya ta6awa ba yau sai da suka had'u danata tana ta kuka ya rasa yadda zai yi a ganinsa tunda tayi aure ta riga tasan komai be ta6a tunanin zai jita a yadda yaji yanzu ba (k'ila ya manta suna cikin amarci Allah ya d'auke mata angon domin Abubakar ba kullum yake yi mata ba wani sa'in making romance kawai zaiyi da ita) INdo cikin kuka tace.
"Tun farko haka zaka ce ga abinda kake so dani bawai ka hanani yin sana'a taba. Wallahi malam Sadeeq bana sanka duk da a makaranta ance bakyau a gayawa miji haka wallahi ni bana sonka Allah kuma saiya saka min."
"Please Aisha b..."
"Karka yi min magana tsakani na dakai babu magana daga yau wallahi bazan sake yi maka magana ba ko me zakayi min."
Ya kasa rik'ota domin daya kai hannu zata yi mai wata uwar