Showing 69001 words to 72000 words out of 85627 words

Chapter 24 - MUSAYAR ZUCIYA COMPLETE BOOK by Hajja Ce.txt

Hajja Ce   

14 Sep 2025

56

kuma ya tayar mata da hankali ta koma bashi hakuri tana lallashinsa sannan yace.

"Toh baby ya zanyi bari kawai naje nayi wanka amma kwanakin da kikeyi sunyi yawa har 7days."

Tana nan kwance yaje yayi wanka ta had'a masa tea yasha sannan suka kwanta bacci bayan sun nanik'i juna kamar za'a sace d'aya.

Sai da yayi kwana biyu a gidan Fateema sannan ranar lahadi da daddare ya koma gidan INdo wanda a lokacin sai da tayi rok'on zuwan period amma ina sabida cikin jikinta gashi a gurinta kawai yake hucewa tunda ya dawo har ta fara jin haushinsa amma baya damuwa bare ya nuna ya gane nufinta.

Abu d'aya yake mata ya d'auke hankalinta shine zai ce tazo suyi lesson wannan abun kawai yake sawa yaga ta sakar mai jiki har itama takan faranta masa ta hanyar kwanciya a jikinsa.

Sadeeq kuwa ta k'arfi da yaji ya zama mak'arya ci a gurin INdo sabida tace bata son gemun Fateema kuma tana so dole yace wa INdo inda ake mai askin ne suka yi gobara yanzu gyara gurin suke yi sai sun gama, gashi shi baya son zuwa ko'ina idan ba gurin ba. Ita kuma Fateema ya rasa yadda zai sanar mata da cikin INdo domin zata yi mamakin tayaya hakan ta faru shida baya nan har tsawon 3months.

***
Ranar Sunday misalin k'arfe 4:30pm Sadeeq da Fateema suna toilet sai rigima suke yi ya rik'e mata hannuwa yana cewa.

"Bake kika hanani yin shaving d'in ba dan haka yanzu babu abinda zai sa kice sai nayi tunda kina so."

"Nidai to yanzu ka rage please, Allah yanzu ta sake yin yawa."

Ganin ta kafe ne yasa shi k'ar6a yayi ya rage iya yadda yake barinsa sannan suka yi wanka suka fito. Shiryawa sukai ko wannce cikin shigar daya fiso sannan suka fito zuwa gidan INdo dan can gidan su Mama zai kaisu ana kawo kayan sa ranar Haleematu.

"Wait anan inje insa ta fito karku shiga ku shantake."

Tashi yayi yashiga gidan ita kuma ta zaro phone d'inta ta kunna data kafin su fito. Yana shiga zaune ya tarar da ita tayi shirinta tsab mayafinta a kan cinyarta yayi sallama ta amsa tare da kai idanunta kansa, har ya k'arasa bata dena kallonsa ba ya mik'a mata hannu ta bashi nata ya d'ago ta tayi murmushi tare da cewa.

"Ko kaifa da kayi wani kamar tsoho.."

"Okey ko shi yasa ma kallon tsufan da kike min yasa kikak'i kar6ar tayin soyayyata?!"

"A'a nidai ban fad'a ba."

Yana rik'e da hannunta ya durkusa yasa gwiwarsa d'aya a k'asa d'ayar kuma ya ajiye ta kamar dai yadda turawa sukeyi yana faman kashe mata narkakkon eye's d'insa yace.

"Humaira kina sona?!"

Ta kallesa ta tuna ajinsa da matsayinsa da kud'insa da martabarsa tun tana cikin duhun kai amma yazo yana rok'on ta so shi duk da har yanzu bata kai matarsa ilimi ba amma itama ta waye dan duk wanda ya kalleta sai yayi tunanin ko ta kammala degree ko tana kanyi. Murmushin jin dad'i tayi sannan tace.

"Ina sonka amma sai kayi k'ok'arin wajan Musanya Zuciya ta daga kan doctor domin har yanzu yana cikin Zuciya ta bazan munafince kaba."

"Aisha...! Are you in your right sence?I'm your husband but kullum sai kin min zancen marigayi why? Please we should help ourselves in one way or the other. Yanzu dai am asking you kina sona??"

"Eh ina sonka.. I love you."

Yana jin ta fad'a ya mik'e tsaye tare da yi mata alama da ta zo su wuce. Har ya d'an tafi yaji ta rik'osa ya kalleta fuskarta a narke ya tsaya yana zaro ido yace.

"Menene kuma?!"

INdo tace "kayi hakuri nafa ce ina sonka."

Rik'ota yayi yana murmushi sannan ya kar6i mayafin ya yafa mata suka fito ya kulle falon still yaga tana kallonsa yaje ya rungume yana cewa.

"Is okay cutie na yadda but sai kin fara nuna min from now on kinji ko?!"

"Toh.."

Ta fad'a tare da gyara swagger bag d'in hannunta. Itace ta fara fita shi kuma ya tsaya rufe gidan. Zaune taga Fateema tana danna waya a gaba ta yatsina fuska ganin sai dai fa ta shiga baya sannan taje ta zauna suna yiwa juna kallon yake har ya shiga shima ya zauna ya tayar da motar suka tafi.

Suna zuwa tare suka shiga lokacin har an kawo kayan anata gani.

'Dakin Mama suka shiga nan suka ga su Hawwah aikuwa suka had'u suna ta hirar su. Har aka yi magrib suna tare sai da INdo ta cire mayafi ta shiga toilet tayo alwala tana fitowa taga suna kallonta alamar dai sunyi gulmarta Hawwa tayi dariya tare da cewa.

"Su aunty Humaira kuma ashe-ashe...."

INdo ta ta6a baki cikin rashin fahimta tace.

"Ashe-ashe me?!"

"Wallahi matar broth wannan ciki ne, haba shi yasa sai wani shining kike yi sannan kin kuma yin kubul-kubul ga shi kuma ya fita."

"Toh ai ba haramun bane ko kin manta a gidan miji nake. Allah sister Hawwah keda Hali dubu (Haleema) kun saka min ido ya isheku haka."

Tunda suka fara magana Fateema take kallon cikin INdo, tabbas wannan ciki ne ba te6a ba. K'irjinta ne ya dinga bugawa yana mata wani rad'ad'i har tana jin tamkar zai fasa mata zuciya. Lallai no wonder taji Sadeeq yanzu baya mata zance yana son yaga ta haihu ashe tuni yaje ya kunsawa INdo.

Babu wanda beyi magana ba a cikin d'akin face Fateema domin idan tace zata tanka babu shakka hawaye zata yi har a samu wasu suce bak'in ciki takeyi mata, sai kawai tayi shiru dama a kwance take hakan yasa ta lumshe idanuwa har aka kira sallan isha'i sannan ta fita basu sake sanya ta a ido ba har Sadeeq yazo d'aukar su...


*Page d'in naki ne aunty Mammn Mu'aleem. Ina fatan zai sanyaya miki rai kamar yadda naji dad'in kulawarki.*🤩













*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *âš—âš— MUSAYAR ZUCIYA...âš—âš—*
♥♥
♥
A true life story

Na

*K.A.S Precious Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu.

*VOTE me on wattpad @Hajjac*


Page *35*

Shirin zuwa Sumaila kauyen sani suke farin ciki ya cika zuciyar INdo har ta kasa 6oyewa, kallonta yayi bayan ta rufo d'akinta ta juyo gashi cikinta ya fito yace.

"Cutie koma d'aki gaskiya mun fasa zuwa."

K'irjin INdo ya shiga bugawa hankalinta duk yayi mugun tashi ta kallesa dan san tabbatar da maganarsa. Gani tayi yana dariya hakan yasa ta yin kansa zata dokesa yayi saurin guduwa cikin shagwa6ar da ta farayi wadda yanzu take neman zame mata jiki tace.

"Ka tayar min da hankali Allah ya dawo damu lafiya sai na rama."

Fitowa suka yi suka shiga mota Sadeeq ya d'auki hanya, wannan karan cikin hira suka ta kai da ka gansu kasan masoyane sa6anin lokacin da aka ce ya kaita garinsu ya dinga kumbura tamkar wanda aka sanyawa yeast. Cikin kwanciyar hankali suka shiga garin sumaila, suna zuwa kan kwanar da zasu shiga kauyen sani adeeq ya kalleta yana murmushi yace.

"Cutie ga barkono da gyad'a bazaki siya bane?!"

Juyawa tayi tana kallon gurin kafin tace.

"Eh wallahi kuwa, dan Allah kaje ka siyo min kwano d'aya-d'aya."

"Ke wasa nake miki ni."

Ya fad'a yana tafiya, kallonsa tayi shima ya kalleta tare da d'aga mata girarsa. Hannunsa yasa ya janyo nata yana matsawa ta lumshe idanuwa tana shafar cikinta da d'ayan hannunta.

A k'ofar gidan su yayi parking, gidan yana nan yadda yake tun lokacin da Abubakar ya gyara musu katangar su ya maida ita ta bulo sa6anin da datake na k'asa. INdo ta kallesa tare da Kama hannunsa tace.

"Wait for me, naje na sanar ma Inna zaka shigo ku gaisa."

"Hmm lalle wariyar launin fata, meyasa ni bazan shiga direct ba sai an wani yi min iso? Ban yadda ba tare zamu shiga kema ai idan mukaje gidan Mama wani sa'inma kina rigani shiga."

"Hehehehe lallaima, toh ai ni macace zan iya shiga direct, kaifa sabida su Mubasheer na zuwa su shiga kai tsaye kasa duk muke kulle gidajen sai an buga munji ko waye sannan mu bud'e."

"Toh ai ni har yanzu saurayi ne, su kuma su Inna sun tsufa toh meye a ciki."

"Kai My super glue, wallahi Inna ta ba tsohowa bace rayuwa ce kawai ta maida su haka amma ka bari na kammala karatuna sannan cinikin zo6o ya kankama zaka sha mamakin Inna da baba wallahi. Kuma kasan dai ai abban ku dasu Mama sun girmi su Innata."

"Kaiii cutie..?!"

"Yanzu dai bazaka barni in shiga ba."

Tayi maganar tana turo baki,janta yayi kasan cewar tinted glass ne yasa ba'a ganinsu. Sadeeq ya shafo cikinta tare da cewa.

"Yau dai ina zata ga k'ok'arina, but dan Allah cutie karki bari ta ankara harsai nazo mun gaisa na fito, wallahi kuma sai naji inajin kunya."

"Kunya kuma? Hahahah ta6 ai aikin gama ya riga ya gama, yanzu wannan abun taya yaya za'aiyi ya 6oyu? Dama hijabi ne ko duguwar riga shine zan iya d'anyin dabara amma ai yanzu kuwa ka makaro hakan nan zan shiga Inna ta gani kuma ka shiga ku gaisa da ita."

Sadeeq ya turo bakinsa tare da dafe kuncinsa yana kallonta yace.

"Toh ya zanyi? Dole na shigo tunda an banike."

Tana dariya ta bud'e k'ofar yaran unguwar da suka zo gurin suka dinga kallon INdo wasu na cewa itace wasu kuma suna cewa ai k'anwar Inna ce dan ga kama nan. Gidan ta shige tana dariya jin abinda suke fad'a, tana zuwa tsab ta ajiye cewa itace 'yar fari ta d'ane Inna dake sharce gurin da tayi wanke-wanke.

"Oh ni Maryamu waike yaushe ne zaki san kin girma 'yar nan.?!"

Inna ta fad'a tana janye jikinta daga na INdo. Dariya kawai ita kuma takeyi tare da kallon Innar tana cewa.

"Kai Inna Oyo-yo fa mukayi, nayi missing d'inku wallahi Inna dake da baba tunda aka kaini baku jeba sai su d'an rainin hankalinnan Sagiru..."

"Ga INdo... Ga INdo, yeeeeee sannunku da zuwa."

Nafeesah ta fad'a tana rungume INdo, murmushi tayi cikin nunawa wayewa da kuma zaman birni tare da nuna zaman teburin class ta kamo hannunta tace.

"Su Feenah 'yan mata daga ina haka..?!"

Ta fad'a tana jan hannunta suka nufi cikin d'akin Inna.

"Kinga Feenah d'auki tabarmar baba ki shimd'a anan sabida Malam Sadeeq zai shigo su gaisa da Inna."

Sabuwar tabarmar malam Hamza aka shimfid'a sannan INdo ta ciro d'ari biyar ta bawa Nafeesah cikin k'asa-k'asa da murya tace.

"Mazaki siyo min lemon roba da ruwa zanba shi yasha."

Kar6ar kud'in Nafeesah tayi sannan ta fita da saurinta, sai da ta kuma tsayawa wajan Sadeeq yana tsokanarta kafin ta wuce zuwa shagon da zata iya samowa mijin yayarta ta lemo da ruwan jarka.

"Sannun ku da zuwa, ke d'aya kika zo ko hardashi me gidan naki?!"

"Inna tare muke dashi zai shigo ku gaisa ma, wai ina baba?!"

"Malam yana can gurin sana'arsa, bari wani ya shigo sai yaje ya kirasa ku gaisa."

INdo dake bakin gadon Inna na k'arfe tace "toh.". 'Dan kuma gyara d'akin tayi sannan ta share shi ta ciro turare a handbag d'inta ta fesawa d'akin da kan tabarmar da Sadeeq zai sauna sannan tace.

"Inna bari nace ya shigo ko? Karya ga an barshi a mota shi d'aya."

"Toh kice ya shigo barina saka mayafi na nima."

Fita tayi suka yi karo da k'awarta Uwani da Sahura da alama sunji labarin zuwanta.

"Ahhhh kaga su hajiya INdo amaryar Malam Sadeeq oh harda su abinga."

Sahura ta fad'a tana d'aga mayafin jikin INdo, kaf d'insu sunyi wani bululumu dasu Uwani ma harda tsohon ciki kai idan ka gansu bazaka ce k'awayanta bane sabida tsabar yadda kalar wayewar ta bambanta.

"Kai sahura kina nan da gulmarki, ku shiga ciki ina zuwa."

Ta fad'a tare da dukan bayan Uwani ganin yadda ta rik'e ha6arta tana kallonta. Cikin gidan suka shiga ita kuma ta shiga motar Sadeeq wanda ke jingine jikin kujera ya sanya hularsa a fuska yana kuma zagaye kwantaccen quarter million d'in fuskarsa.

Jin an bud'e k'ofar motar ne yasa shi cire hularsa ya kalleta, zama tayi tana kallonsa da murmushi a fuskarta yace.

"Uhmmm wato anzo gida harma kin manta tare muka zo ko?"

Hannunsa ta kamo cikin nata cikin kalar jimami tace.

"Ni na isa, tunda na shiga mafa koda Inna bamu gaisa ba kuma babu kowa duk basa nan amma ni banajin zan iya mantaka a yanzu domin ka zama ni na zama kai kadena sawa ranka cewar duk inda zan shiga wai Zan manta dakai no, idan nayi haka toh Zan iya mantawa da kaina nima."

Sadeeq ya lumshe idanuwa tare da jan hannunta murya a shak'e cikin wani irin salo yace.

"Kina nufin kenan munyi *MUSAYAR ZUCIYA* dani dake a yanzu? Ba kamar da ba yadda kike nuna min cewar zuciyarki ta M twinnie ce shi kad'ai yanzu zaki iya mallaka min ita...?!"

"Sosai ma kuwa na baka ita ina fatan ka rik'eta amana. Anan aka d'aura mana aure dan haka anan na kuma baka amanar kaina da duk abinda ya shafeni."

"Na kar6a cutie Allah kuma ya bani ikon rik'ewa gam-gam, a baya ma *Illar Zuciya* ce tasa nake ganin kamar anyi min ba dai-dai ba amma a yanzu..."

Yakai bakinsa kan hannunta ya sumbace shi yana kashe mata idanuwa tayi saurin kawar da kai tana dariya. Nafeesa ta hango hakan yasa INdo fitowa da sauri. Amsar aikenta tayi ta shiga ciki Nafeesah kuma ta tsaya a gurinsa suka dinga hira har su Shehu suka dawo suma suka gaida shi. Cikin gida kuma INdo ta gama jerawa Sadeeq abin tarba dan inna ta gama dafa wake da shinkafa Allah sarki harda yanka mai lawashin albasa kuma duk INdo bata hana ba domin ta haka ne zata iya kuma tabbatar da kaunar da yake cewa yana mata dan marigayi baya kyan-kyamin duk abinda zata bashi bare yanzu tasan kanta tasan me takeyi ta kuma san waye mijinta.

"Lallai INdo wai duk malam Sadeeq d'in kikewa wannan tanadin?!"

Uwani ta tambaya tana ta6e baki, gani take kamar INdo ta zurma da yawa duk miji akewa wannan hidimar.

"Toh Uwani bakin ciki kikeyi ko me? Ina zan samu kifi ma dan yana son wake da shinkafa da kifi ko dafaffen kwai."

"Ta6 lallai INdo Hamza, toh k'ila dai yana baki kema ba irin muba da sai dai komai kayiwa kanka."

"Kwaji dashi gulmammu, Inna bari naje nace ya shigo."

Tana fad'a ta kuma fita tace ya shigo. Jerawa suka yi shida Nafeesah yana kallon INdo daga baya. Gaskiya ikon Allah baya k'arewa a duniya ko kana menene sai ya nuna ikonsa akanka yau shine da INdo harda kunshin cikinsa a jikinta "Allah astagfurullah."

Ya fad'a cikin ransa tare da shiga gidan yana sallama, su Sahura da Uwani suka amsa bakinsu a washe yayin da Inna ke tsaye kanta a k'asa sam bata iya kallonsu tun zamanin Abubakar. Cikin d'aki Nafeesah ta shigar dashi ya zauna yana sosa keya yana shafa wuya.

Daga bak'in k'ofa Inna ta tsugunna suka gaisa da Sadeeq sannan su Uwani ma suka sake gaidashi duk da cewar sun gaidashi a cikin mota INdo ta kallesu tare da makewa Sahura hannu ganin yadda take leken sadeeq tana wangale baki.

"Kedallah can malama kina da miji kina kallon mijin wasu haba."

"Kai INdo bana san herri."

Tashi Inna tayi ta shiga rumfar malam Hamza bayan ta tura Nafeesah tace ta kirasa. Kallonsu tayi tace.

"Zan shiga daga ciki, karku ce na barku anan."

"Lallai ma INdo toh ba abinci zaici ba? Toh ki zauna muyi shira mana kafin ya gama."

Uwani ta fad'a tana hararta cikin jin haushin yadda take wani nan-nan da malam Sadeeq sai kace su basuda mijin.

"Toh kuje ku gama muna nan hajiya INdo."

"Toh hajiya Sahura."

Itama ta fad'a tare da shiga cikin d'akin. Kallonta yayi ta zauna kusa dashi tare da d'akko Coca-Cola ta bud'e mai cikin halin damuwa tace.

"Kayi hakuri kasha a haka da bakin jarkar, nan gidan bamu da kofuna kaji my super glue ka daure."

"INdo Aisha ta zaria med'an kallabi..!"

Ya fad'a tare da matsawa kusa da ita. Lek'awa yayi k'ofa aikuwa karaf suka had'a ido dasu Sahura da Uwani suna lek'owa yayi dariya tare da Kai bakinsa saitin kunnen INdo yace.

"Gaskiya d'aliban nan nawa gulmammu ne, sai lek'en mu suke kamar a gidan zoo."

Itama dariya tayi cikin hillata da shagalta yaci wake da shinkafar nan dan sai da suka cinye ta cikin kwanon silbar da Inna ta kawo musu. Suma su Sahura da suka kasa suka tsare aka zuba musu sukaci lokacin malam Hamza ya shigo fuskarsa kunshe da fara'a Sadeeq yayi saurin tura kwanon gaban INdo da ragowar lemonsa da ledar yajin ya maze sai wani danne-dannen waya yake shi a dole beci da yawa ba.

INdo kuwa banda dariya babu abinda takeyi mai amma still ya maze su Uwani na jiyo ta sai mamakin abinda yasa ta dariyar suke yi.

"Sadeequ ashe kunzo? Sannunku da zuwa. Ah kaga uwata an zama manya."

Sadeeq ya fara motsi yana gyarawa malam Hamza guri dan ya shigo. Gaida shi suka yi sannan yayi ta sanyawa Sadeeq da marigayi albarka ganin yadda INdo ta canza tamkar ba 'yarsu ba.

Tare da malam Hamza Sadeeq suka fita ita kuma INdo ta koma tsakar gida gurin su sahura Inna ma taje ta zauna. Suna zaune Rukayya ta shigo murna ba'a magana sabida ganin INdo da ciki, nan fa suka shiga hira baji ba gani amma duk da haka zuciyar INdo bata manta da Sadeeq a mota ba. Nafeesah ya d'auka suka shiga cikin garin har sai bayan sallan la'asar sannan ya dawo dan su tafi.

"Gaskiya Inna zan baki kud'i a hannunki a samu dan Allah a gyara band'akin nan, habba wallahi za'a iya d'aukar larura tunda aka haifeni a haka yake. Ga dubu sha biyar nan ita kad'aice a hannuna nasan k'ila malam Sadeeq zai bawa baba ma wasu amma idan be bayar bama dan Allah Inna a fara da wannan kud'in ko buhu d'aya ne na siminti a siyo a malale k'asan band'akin can kosu Sagiru ne da Shehu sai suyi ai sun iya."

Kwallah Inna ta share tare da yin godiya sam bata ta6a tsammanin akwai ranar da 'ya'yanta zasu yi mata wani abunba ganin itama ba tayi wa nata komai sabida rashi gashi ance sai kanayi za'ayi maka.

"Inna ya kike kuka? Karki bari na tafi haka dan bazan yafewa kaina ba bayan na barki cikin kuka."

Murmushi Inna tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login