Showing 78001 words to 81000 words out of 85627 words

Chapter 27 - MUSAYAR ZUCIYA COMPLETE BOOK by Hajja Ce.txt

Hajja Ce   

14 Sep 2025

55

daga wannan sai ace maka wannan.

"In zuba maka yanzu ko sai kayi sallan azahar naga an kusa kirawo wa."

"Bari sai nayi sallah cutie, dawo nan in dinga jin duminki a jikina."

Matsawa tayi ya rungumeta, yana yawo a jikinta da hannunsa ita kuma ta lumshe ido tana sauraransa. Sallamar su Uwani suka jiyo Sadeeq yayi saurin zame hannunsa daga jikinta yana yatsina fuska yace..

"Su waye?"

"Inajin su Maryam ne naji muryar su da Uwani da Sahura."

"Kai nashiga uku ni Sadeeq, wai hardasu nake aure ne da kullum na shigo garin nan sai sunzo sun samin ido? Ko 'yan uwanku ne cutie?"

"A'ah k'awaye nane amma kuma su haka suke duk inda sukaji labarin wani abun tofa sai ka gansu sabida dama ba wani tambayar miji fita suke yi ba."

"Ai munafukai ne wallahi."

Ya fad'a a kufule kafin ya matsa sun shigo cikin d'akin bakunansu a washe.

Zama suka yi daga bakin k'ofar amma hakan be hana warin ranar jikinsu da kaurin icen girki shiga cikin hancin Sadeeq ba ya tuna da tuni itama INdon haka take amma Allah ya d'aukaka ta.

Da kyar ya amsa musu a ciki-ciki sabida yadda suke kallansu suna rik'e ha6a sabida sunga sun manne jikin juna.

"Cutie zanyi alwala."

"Okey toh bari akawo ruwa k'ofar gida, ko zaka yi anan ciki."

"A'ah Inna na nan da dai bata nan sai nayi."

Tashi yayi suka d'an ra6e ya wuce sannan INdo ta fito suma suka bita a baya, tunda tazo gida suke bibiyarta ganinta suke tamkar Matar wani shugaban me rik'e da wani muk'amin.

Ruwa ta zuba tasa mayafi takai mai wajan mota sannan ta koma ciki.

Hira suka farayi dasu har aka idar da sallah Sadeeq ya dawo daga massalaci dan har tsayawa yayi suka d'anyi hira da principal d'in tsefawa makarantar su INdo daya bari.

Nafeesah ce ta kuma fita ta shigo dashi sannan INdo ta bishi su kuma su Uwani suka ci gaba da hira da Inna duk da bata cika sanya musu baki ba.

"Cutie Ina baby na kika kaishi?"

"Inna ta goyashi ko na kar6osa?!"

"Ah no kyalesa kar ace nayi rashin kunya."

Waina ta zuba masa da miya sannan ta matsa kusa dashi, had'e hannuwa yayi a k'ijinsa tare da bud'e baki alamar ta bashi da kanta.

Murmushi tayi tana girgiza kai ta fara bashi kunnuwansa har motsawa suke yi sabida yadda miyar tayi mai dad'i idan ta bashi sau d'aya itama sai ya tura mata wanda ta kuma d’ebowa yasa mata a baki haka suka dinga yi har suka kusa cinyewa yace ya k'oshi.

"Cutie gaskiya ranar Sunday zaki koma zanyi duk iya yadda zanyi na tabbatar da an kawo kayan nan, sannan direct za'a wuce dake can gidan marigayi acan zaki ci gaba da zama an raba gado Abba yace idan kin koma zaizo yayi miki bayani kinji.?!"

Kifta idanuwa ta shiga yi alamar hawaye take son karsu fito ya janyo ta tare da kamo fuskarta yana san saka kwayar idanunsa cikin nata.

"Karki zubar min da hawaye kinga nima ina tattala nawa, keda ma ba'ayi miki da yawa ba tunda an baki me kamadashi iri d'aya sak sannan kina cikin zuciya ta kamar rai. Ni kuwa tare muka taso mu kwana tare muyi fad'a mu shirya ba tare da kowa ya sani ba, shine ni nine shi amma yau babu shi."

"Ka d'auka kaima a ranka nice shi tunda dama silarsa ce ta sa muka zama abu d'aya dakai, na zame maka shi kaima karka sake yin kuka mun riga munyi *MUSAYAR ZUCIYA* ni da kai fatana a yanzu shine na zama tauraruwa kamar yadda yake so yaga na zama kayi min addu'a malama Hannatu tace addu'ar miji akan matarsa tana saurin kar6owa."

Bakinsa da yake ta motsi tun d'azu shi ya zura cikin nata cikin wani mugun tausayinta da wata azababbar kaunarta da soyayyarta da ta taso mai. Kissing d'in ta yake cikin wani irin salo wanda yasa INdo ta kasa gane kansa, ya shagala kawai suka ji muryar malam Hamza a tsakar gida amma Sadeeq ji yayi tamkar a tsakiyar d'akin yayi sabida tsabar tsoro.

"Na tafi cutie kar nayi abun kunya a gidannan a d'akin baba dan naga kema ba hanani zaki ba."

Dariya INdo take yi sosai wanda tasa Sadeeq kallonta yana hararata dan har rik'e ciki takeyi ya matsa can bakin k'ofa-k'ofa tare da maida hularsa yana jiran shigowar malam Hamza d'akin dan yaji Inna tana cewa suna ciki.


"Matsoraci kawai Abu Ayman, uhm...uhm..uhm.."

INdo ta fad'a cikin dariya ya juya yana mata gwalo shima. muryar malam Hamzan yaji a bakin k'ofar Sadeeq yayi saurin d'aga labulen ita kuma INdo ta fara matsar da kayan da suka ci abinci kamar masu gaskiya.

"Baba sannu da shigowa, gashi duk mun tsare maka d'akin."

Sadeeq ya fad'a yana gyara zama tare da turo hula gaba yana kuma mai da ita baya alamar kunya ya keji.

Malam Hamza yayi dariya tare da k'arasawa cikin d'akin ya zauna a bakin gadon sa yana cewa ba komai Gaidashi Sadeeq yayi cike da girmamawa har suka d'an fara hira ita kuma INdo ta kwashe kayan ta fita dasu can su Uwani aka ci ragowar ana jinjinawa INdo ganin duk da kud'inta tayi wannan shagalin.

Malam Hamza da Sadeeq sun jima suna hira kafin malam Hamza ya fita INdo ta shiga tare da d'ora mai ayman akan k'afarsa kasan cewar ta kar6o masa shi dan tasan yana son ganinsa.

"Cutie ni kikawa dariyar mugunta ko? Hmmm zan rama ai zaki zo inda nake."

"Toh ai kaine da abin dariya wallahi."

"Za dai mu had'e you will see."

Kallon ayman yayi tare da cewa.

"Cutie wannan da wa yake kama sam na kasa ganewa?!"

"Ban sani ba nima kasan ance ba'a gane kamanin jarirai harsai sun fara girma."

"Ki dinga karanta mai ayatul kursiyu kina tofa mai a mad'igarsa ai kin iya ta ko?"

Tana kallonsa yatsan hannunta k'arami a cikin bakinta tace.

"Eh na iya mana."

"Matso nan toh kiyi min inji ko dai-dai ne."

Cikin jin wani iri dan kar ta kakare ta matsa jikinsa ya rik'ota, a hankali ta fara karanto mai inda yaji zata 6ata wani gurin sai ya gyara mata harta gama sannan yace.

"Yauwa ki dinga yi mai Allah ya kare mana shi daga sharrin shaid'anu."

"Amin abu Ayman."

"Zan wuce sai kinzo cutie ki yo shiri sosai dan wannan karan hmmmm."

Dariya ta kuma yi sannan ya zaro kud'i 10k ya bata ko zata yi wani abun idan zata dawo sannan ya mik'e itama ta tashi suka rungumi juna kamar basa son rabuwa cikin yanayi na ba haka aka so ba Sadeeq ya bata Ayman sannan ya fita suka yi sallama da Inna su Uwani sai subirbid'a mai addu'ar sauka lafiya suke yi dan har lokacin suna gidan.

A zaure Sadeeq yaga malam Hamza kan wata guntuwar tabarma yana gyaran redio suka yi sallama bayan ya ajiye mai 5k yana ta godiya.

Yana shiga mota INdo tazo nan ma suka yi sallama ji yake tamkar ya tafi da ita amma ba yadda zai yi dole ta fita yaja motar ya tafi cike da kewarta ji yake ma tamkar basu had'u ba kamar yanzu ne ma yake kan hanyar zuwa ya gansu....







*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥

A true life story

Na

*K.A.S Precious Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*DEDICATED TO:* Sanah Isma'il Matazu.

*VOTE me on wattpad @Hajjac*


Page *39*


Tunda Sadeeq ya koma gida be sanar da kowa zancen da suka yi da INdo ba kasan cewar baya son duk wani abinda zaija ayi mata gori akai ba. Gidan k'anwarsa Hawwa yaje suka yi magana hakan yasa duk abinda ya siyo ita yake kaiwa ga shirin gidan da ake yi mata wanda zata koma.

Cikin kwana biyu ya gama had'awa washe gari ana sauran kwana biyu INdo ta dawo yasa aka kai hawwa gidan su INdon takai kayan. Sosai aka dinga murna ana yiwa INdo barkar cewar mijinta ya fitar da ita kunya da kayan da babu wacce aka ta6a yiwa kowacce mace irinsa a kauyan. Shiri tayi sosai ciki da waje Rukayya ta kawo mata kayan INdo ta sake yin wani sassanyan kyau sam bata bari a sauya mata ak'idar da take da ita dan yanzu a kauyan akwai 'yan matan da suke kwaikwayar shigarta da kwalliyarta har yafa mayafi ma.

***

"Gaskiya Fateema kina da hakuri, ki duba ki gani a cikin shekara d'aya da auranku kishiyarki tayi zaman gidaje gashi yanzu mijinku d'aya amma zata koma wannan uban gidan na alfarma ke kina wannan duk da cewar shima yana da kyau amma nata yafi girma da kuma kyau ya kamata kema kiyi bori wallahi asan yadda za'ayi dake."

Cewar wata malama da suke k'awance da Fateema tun zuwanta school d'in. Numfasawa Fateema tayi tana jin k'irjinta na bugawa zuciyarta na zafi dan ta tabbatar da zancen aunty Hafsat gaskiya ne, gashi uwa uba ita bata haihuwa duk da bata fitar da rai da rahamar ubangiji ba a kan samun ciki.

"Amma ni ina ganin ba wani abun d'aga hankali bane Hafsat ganin dama tun farko a cikinsa ta fara zama, karki manta gidan mijinta ne na farko kafin tazo mu had'e. Kuma a k'ishin-k'ishin d'in da naji cewar an bashi gidan kinga dan ya mayar da ita baxan d'aga hankalina ba tunda itace ta fara zama a cikinsa."

"Lallai Fateema toh ai nan gaba na san zaki gane abinda nakeso ki fahimta."

Murmushi tayi kawai bata son nuna hassada akan lamarin tunda taga wanda ya narka kud'in yayi abunsa Allah be barsa yaji dad'in da ya tanadarwa rayuwarsa a cikin gidan ba. Idan ta tashi hankalinta akan abun itama Allah sai ya d'auke ta aga ta tsiya tunda kamar yadda Ummanta ta fad'a auran Sadeeq da Aisha Had'in Allah ne.

Shiga yayi gidan ya tarar tayi tagumi sam ba taji shigowarsa ba sai tsayuwar sa taji Sadeeq ya zauna a gefenta yana kallonta. Murmushi tayi mai sai dai iyakarsa le6anta kasan cewar ita kanta taga yadda yake rawar k'afar dawowar matarsa dan yakan iya gaya mata zata dawo kusan sau biyar arana duk shigowa sai ya gaya mata hakan yake bata mamaki har take tunanin ko yanzu ya dena sonta ne, duk da cewar be sauya mata ba yana nuna mata soyayya fiye da tunanin me tunani.

"Baby tunanin me kike yi haka?"

"Babu komai baby kawai ina tunanin rayuwa ne."

"Hmmm da alama dai zaman kad'aicin nan ne yasa ki shiga tunani, toh na dawo kuma bazan fita ba yau ina tare dake soyayya zamu yi."

Yayi maganar yana rik'ota yana shak'ar k'amshinta, ita ma tayi k'ok'arin Kawar da abinda yake damun cikin ranta.

"Kai baka gajiya da aiki ne baby?"

"Ehmm kinsan ai ked'aya ce yanzu, kuma duka duka yaushe na dawo ai kinga nayi k'ok'ari baby."

Dariya tayi tana shafa kanshi ya lumshe idanuwa. Wato mata biyu Lafiya ne daga nan kayi nan babu fargaba bare tashin hankali dole maza suyiwa Allah godiya daya basu wannan damar. Sai gaf da magriba ya samu ya fita bayan sallan isha'i suka yi waya da INdo sannan ya shiga gidan ba tare da Fateema ta gane sunyi ba. washe gari ya tafi Sumaila kauyan Sani yaje ya d'akko matarsa.

Yana zuwa ya buga mata waya ba'a d'auka ba sai gani yayi Sagiru ya fito, gaisawa suka yi sannan ya sanar masa cewar tana wanka Sadeeq yace ba komai sannan Sagiru ya koma gidan. Tana fitowa ta buga mai ya katse ya kirata da kanshi dan shine yafi can-cantar yin hakan ba itaba.

"Cutie meye nayin wanka, da kin bari idan mun koma gida sai muyi tare."

"Hahaha..lallai a haka kake son na bar Sani zuwa cikin gari ko? Ban yadda ba gashi na fito kaya kurum zansa sai mutafi."

"Shikenan ai tunda abun 'yar haka ne, ki turo a kawo min yaro na mu fara gaisawa nayi missing d'insa."

"Okey shi zaka fara gani ba niba ma ko?shi kenan bari a kawo shi sai ku tafi ni saina zauna a gidan."

"Wayyo cutie ki rufamin asiri I can die idan kika k'i bina Zuciya ta zata iya shiga rud'ani zan iya rasa nutsuwa ta. Cutie kin zamo wani jego a cikin rayuwata Ina sonki dan zan iya cewa nafi m twinnie kaunarki Ina jin zuciyata na bugawa a duk lokacin dana tuna cewar bani na fara nuna miki soyayya ba but ki yadda cewar ni d'in ina wahala a cikin raina da rayuwata idan bake a kusa dani, please kiyi sauri ki fito mu tafi dan Allah."

"Gani nan fitowa barima a fara fito da kayan namu."

Tana fad'a ta ajiye wayan sannan ta lek'a tsakar gida ta kira su shehu suka fitar da kayansu. Tsab INdo ta shirya Nafeesah ta shirya Ayman sannan ta fitar dashi, sai da suka gama shiryawa ta fita kallansa tayi ta glass d'in motar tare da cewa.

"One minute."

Mak'ota suka shisshiga suka dinga yi musu sallama har sai da suka zagaye unguwar sannan suka koma Sadeeq ya gaida Inna sannan INdo suka yi sallama da kowa na gidan suka shiga mota Sadeeq yaja zuciyarsa shar daya juya yagan su sai yaji wani farin ciki yana kuma ratsashi.

"Cutie me d'ah, wai ke dan Allah bakya mamakin hakan?"

"Bana yi, kai da ace fa marigayi be d'akko ni daga Saye ba da inajin yanzu 'ya'yana biyu ko uku da wani saurayi na salele."

"Toh naji abar maganar waye wani salele ba ko dad'in ji. Cutie nayi missing d'inki amma ke da alama kamar bakiyi nawa ba."

"Abu Ayman kenan, karka fad'i haka domin zaka zalince ni. Kawai ba yadda zanyi ne ko na nuna babu yadda zanyi tunda ko a gidan ka na zauna dole baka nan amma nayi missing dinka dan ma akwai Ayman ina kallonsa Zuciya ta na ganin kamar kaine shi yasa kaga banyi ramar rashinka ba."

Dariya yayi hannunsa na ta6o k'afar Ayman, haka suka dinga hirar yadda suka yi rashin juna har suka k'arasa k'ofar gidan marigayi wanda zata ci gaba da rayuwa a cikinsa.

K'irjinta ne ya dinga bugawa Sadeeq yaje ya bud'e gate ya shigar da motar duk yana ganin yadda ta sauya jikinta yayi sanyi hannunta dafe da k'irjinta idanunta a rufe. Hannunsa INdo taji a wuyanta hakan ya sake tayar mata da hankali kawai sai ta sakar masa kuka mai sauti.

Ayman ya k'ar6a kafin yayi wani abun su Haleema sun fito suna musu oyo-yo kasan cewar suna ciki sune 'yan taryar su.

"Cutie ya haka? Kuka? Ohh ya subahanallahi danasan zaki kuka da wallahi baxan yadda na kawoki gidannan ba, cutie bakya sona ko? Please dan Allah kiyi shiru bazan iya barin ki fita daga motar nan ba alharin kina kuka dan kinga mun shiga nan gidan ba. Ki dinga sawa a ranki nine Abubakar Sadeeq gaba d'aya ki tuna cewar kina da irinsa kamar yadda nima nake ganinki a matsayinsa please."

Share mata fuska yayi sannan yasa hannu a baya ya d'akko jakarta ya zare powder da kanshi ya shafa mata ya gyara mata fuskar ya sakar mata murmushi tare da cewa.

"Kinfi ma kyau yanzu da nayi miki kwalliyar kin ganki kuwa Son Sadeeq k'in wanda ya rasa zuk'i..."

Dariya yaga tayi sannan yayi unlock d'in motar su Haleema suka bud'e tana kar6ar Ayman tana cewa.

"Wai toh me kuke yi a motar kuka dad'e aunty Humaira."

"Toh gulmammiya ina ruwanki bana son saka idofa."

"Sorry broth sannun da hanya."

Shareta yayi yana hararta INdo dasu Aminatu suka shiga ciki shima yabiyo bayansu. Kujerun d'ayan falon na ciki wanda ba'a shiga su aka dawo mata dashi falon farko kasan cewar da nata aka kai mata can gidan Sadeeq dining room d'inta yana nan tad'al-tad'al tayi fuskarta nason yin hawaye amma murmushi kwance a fuskarta lokacin da take tuno yadda suka yi rayuwa da marigayi,Sadeeq ya shiga tare da kama hannunta ya nufi bedroom su Haleematu suka zare idanuwa hannu rik'e da ha6a sannan suka ta6e baki.

Suna shiga ya jata jikinsa suka tsaya wajan madubi yana kallonta. Hannu ya d'ora saman k'irjinta yana wasa dashi bakinsa saitin kunnanta yace.

"What happen to my cutie angel ne? Aisha I love you but naga ke har yanzu akwai marigayi a cikin zuciyarki kin kasa sanyani a ranki why.?”

Numfashinta na sama-sama sabida yadda taji yana mata murya a sark'e tana narke mai sabida yadda k'afarta take neman kasa d'aukarta tace.

"Wa yace maka baka cikin raina? Shin duk yadda nake cewa kana cikin raina kazama ni nazama Kai duk a tatsuniya kake d'aukar su?"

Juyo da ita yayi yana kallonta yace.

"Na kasa ganewa but prove me now."

A hankali ta sanya hannu a wuyansa ta sargafo shi tare da had'e hancinsu guri guda cikin salo ta zuro bakinta cikin nasa Sadeeq yayi saurin kar6ar sakon tare da rik'ota shima. Kukan Ayman ne ya sanya suka tsaya da abinda suke yi jin kamar hanyar d'akin aka yo dashi, sadeeq na matsawa sai ga Sajida da Ayman tana cewa.

"Aunty Humaira wai kuka yakeyi inji yayya Haleema."

Kar6arsa tayi sannan ta fita Sadeeq ya zauna a bakin gado yana cewa.

"Wallahi munafincin Haleematu ne dama naga take-taken su nasan ganin gulma."

INdo tayi dariya tana k'ok'arin ba Ayman.... Sadeeq ya mik'e yana cewa.

"Bari naje na maida su gida bana son kinibibin yaran nan."

"A'a dan Allah ka rabu dasu kana ganinfa ko gaisawa bamu yi ba."

"Yanzu cutie kin fison su zauna akan ni na zauna?!"

"A'ah ba haka nake nufi ba, amma kaga ba dad'i ka kyalesu basu yi niyar tafiya ba toh ka kyakesu dan Allah."

"Shikenan toh bari naje d'ayan gidan ai Fateema na nan."

Yana fad'a ya fita INdo ta bishi da kallo, ai dole yace haka tunda ta dawo gurin sa. Tashi tayi ta koma falo wajan su haleema suka fara murnar dawowa da hirar yaushe gamo.

Sai da akayi magariba sannan su Haleematu suka tafi ita kuma ta cigaba da gyara kayanta. Har kusan tara na dare Sadeeq be shigo gidan ba hakan ya 6atawa INdo rai ganin ko dai ya dawo da itane dan ya fara wulak'anta ta. Shirin bacci suka yi itada Ayman gashi ko gen ba'a kunna musu ba kuma bata damu ba domin a can gidan su ko wearing na nefa basu dashi, tana gamawa tayi kwanciyar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login