Showing 81001 words to 84000 words out of 85627 words
zuciyarta na k'una ta janyo pillow ta rungume tare da rufe idanuwa.
Sai wajan 10:15pm ya shigo hannunsa rik'e da ledoji, kayan ya ajiye a falo sannan ya fita ya tayar da injin taja tsaki tamkar yana gurin ta kuma rufe idanuwa dan ba k'aramin haushinsa takeji ba na watsar da su d'in da yayi.
"Cutie..! Cutie..!"
Yaji shiru sai ya shiga cikin d'akin, kwance ya gansu da alama sunyi bacci ya lalla6a ya k'arasa kusa da ita yana son juyo da ita yaji tayi tauri hakan ya tabbatar masa da cewar idanunta biyu.
"Haba cutie ba Oyo-yo shine zaki zo ki wani kwanta tashi muje falo."
"Sorry bacci nake ji ka koma inda kafi so."
"What..?!"
Banza tayi mai ya kuma komawa wajan fuskarta yana matsa hannunta yace.
"Amma ki bari sai munzo kwanciya sai muyi wannan wasan but yanzu dai taho muje falo."
"Nace kayi tafiyar ka wajan matarka, nasan dama can itace za6in zuciyar ka bani ba da aka lik'a maka, toh kaje katafi gurin Fateema daka fi so na bar mata kai. Banda mutuwa ma me fallasa ai da hakan bata faruba bare kamin wulak'anci harda cewa toh kaima ka tafi wajan Fateema shine sai yanzu goma da wani abun zaka ce ka dawo in tashi."
Ta k'arasa maganar cikin kuka tare da tura fuskarta k'ark'ashin pillon da kanta yake kai. Ba k'aramin tashin hankali Sadeeq ya shiga ba jin abinda take fad'a, ya janyo ta yana lallashi kan ta sanar mai da abinda yayi mata amma tak'i, har zai rabu da ita yaji bazai iya ba sabida zuciyar da take tsananin sonta tak'i jin haushinta sai ma k'ara k'ask'antar da kansa da yayi yana cewa.
"Kinga ba wai da gangan kika ga nayi dare haka ba no, ana yin sallahn magrib muka tafi gidan wani malami nida Abba bamu dawo ba sai bayan sallahn isha'i naje nakaisa gida sannan nayo muku siyayya naje ko dad'ewa banyi ba a gidan Fateema nayo nan amma shine zaki min wulak'anci ko? Shikenan tunda har kin fara yi min mumunan zato."
Yana fad'a ya fara k'ok'arin sauka a gadon sai kuma yaji ta rik'osa, itama bazata iya fushi dashi ba ya lek'a fuskarta ta kallesa sannan ya tashi tare da d'agata suka nufi falo.
"Cutie ki dena min saurin fushi bana so yana sani cikin damuwa da tashin hankali kinji?!"
"Toh amma nima ka dena barmin gidan ka dad'e baka dawo ba tunda kana garin."
"Insha Allahu."
Ya fad'a, kitchen taje ta d'akko plate da cups ta dawo. Gashasshiyr kaza ce da aka sanya mata kwai tasha kayan lambu ga yajin tafarnuwa suka zauna suka ciyar da juna ranar sunyi kwanan farin ciki marar bayyanawa bare rubutawa.
Satin INdo uku da dawowa da kyar da nuna jajircewar shine mijin ba ita ba ta yadda zata bisa zuwa kwara state sabida ta kafe ita karatunta zata koma amma yak'i har kuka tayi suka yi fad'an kwana biyu amma yaki sakkowa dole ta hakura ta bisa suka tafi aka bar Fateema...
Nd Page finale is loading🤨
#love you
#my fan's
*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥
♥
A true life story
Na
*K.A.S Precious Hajja ce*👈
*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)
*DEDICATED TO:* Sanah Isma'il Matazu.
*TUKWAICI GA:-* Dota Fateema (Marok'i).
*DAN JIN DAD'INKI:-* Billy S Fari.
*VOTE me on wattpad @Hajjac*
*End*
Page *40*
Tun a cikin mota suke yin fad'a k'asa-k'asa yadda ba kowa ne zai gane ba bare aji. INdo mita kawai take masa sabida tsabar ta gaji da zama bata ta6a yin tafiya irin me nisan haka ba gashi tun a cikin motar ta fara ganin ban-bancin kano da inda za suje domin duk cikin motar yare ne basufi su shida bane hausawa kuma suma ba wai zaune suke a guri d'aya ba kowa yana kan kujerarsa. Wani yare dake kusa dasu yana ta kallon Ayman ya zuro hannunsa yana shafar kanshi tare da tambayar INdo ya sunan d'an cikin yarbanci k'irjin INdo ya dinga bugawa jin bata gane abinda yake nufi ba, sai kallon mutumin take shi kuma yana faman kuma tambayarta. Kallon Sadeeq tayi kawai taga yayi tamkar baya jinsu yana karanta jarida tasa hannu ta zunguro shi ya kalleta sannan ta kawar da kai tare da cewa.
"Ana maka magana fah."
Kallonta yayi yana k'umshe dariyar sa kafin ya kalli bayeraben sai taji ya gaya masa sunan Ayman bayeraben ya jinjina kai bakinsa a washe ya cewa Sadeeq yaron yana da kyau Sadeeq yayi dariya duk babu abinda INdo taji a cikin maganar gashi sai dariya bayeranen yake hakan ya sake k'ona mata rai domin abinda take gudu ne yake shirin faruwa wato a dinga magana bata son me ake cewa ba. Sun tsaya anyi sallah anci abinci an rage mara sannan suka kuma d'aukar hanya ran INdo ba k'aramin 6aci yayi ba har suka k'arasa garin cikin tsakiyar dare. Duk da tayi bacci a mota amma ji take tamkar bata ta6a yin bacci a rayuwarta ba, ko wanka bata yi ba dakyar ya samu tayi sallan magrib da isha'i tabi lafiyar gado.
Da kyar Sadeeq ya samu ta farka k'arfe takwas tayi sallah dan tunda ta kwanta ba tayi juyi ba, ko kukan Ayman bataji sai dai shi ya farka ya ciro.. sannan ya samai abincinsa a baki idan ya saki kuma sai ya mayar mata sam bata sani ba sai da tazo suna gaisawa yake bata labari suka dinga dariya. Fita Sadeeq yayi ita kuma ta shiga taga yadda gidan yake bayan ta goya Ayman. Be jima ba ya dawo hannunsa rik'e da leda yaje kitchen ya juye musu abincin daya siyo musu suka tafi falo.
"Wannan kuma bak'in abun menene haka."
"Amala ce da miyar ayayo da dad'i kuma cutie ci kiji."
Zama tayi suka faraci tana sawa abaki ta dinga yatsina fuska daga k'arshe ta matsa ta had'iye ta cikin bakinta da kyar. Sadeeq ya kalleta cikin mamaki yace.
"Cutie ya haka? Ba kya ci ne?"
"Gaskiya bana ci wallahi wannan abu a samo min wani."
Shima jiyayyi sam ba zai iya ci ba duk kuwa da son amala da yake yi. Kallonsa tayi tana goge hannu cikin shagwa6e fuska tace.
"Kuma ni yunwa nakeji wallahi kamar inci babu, ko cinyeka nayi ji nake bazan k'oshi bama gashi da Ayman ya farka zaice zai sha kuma babu komai a ciki wallahi duk ya tsotse."
"Kai cutie wai ba komai a ciki, toh duk meye wannan abun a ciki?!"
Yayi magana yana kallonta da mamaki, ta kuma narkewa cikin nuna jin yunwa sosai tace.
"Shikenan tunda baka yadda ba, ni dai ka samo min abinci."
Tashi yayi da sauri tun yanzu yaga ban-banci tsakanin su da Fateema domin duk abinda ya siyo ko bata ta6a ciba toh zata ci amma ita common amala tace wai ba dad'i. Tunani ya dinga yi yana neman abinda zai siyo mata gasu da shegen tsadar abubuwa daya rasa yadda zai yi kawai sai yaje gurin wata k'awarsa cinyere da take dafamai abu idan bezo da Fateema ba yasa ta dafa mai indomie da ruwan tea ya kar6a ya kai ma INdo, harda su murmushi tayi mai sabida ganin abinda zata iya ci. Kad'an yaci kasan cewar bata damesa ba ita kuwa taci sosai kad'an ta bari tasha tea sannan walwalarta ta dawo taje kuma ta dinga narke mai tana takura mai.
Satinsu d'aya da zuwa garin babu inda INdo take zuwa ko lek'e batayi ba, aranar kuma ya fara fita gurin aikinsa yana tafiya ita kuma tana gyaran gidan sai ga wasu 'yan mata kowacce da 'yar bingilar riga da mini skirt suka shigo.
"Madam excuse us,can we come in please?"
INdo ta bisu da kallo ita kuwa me ya had'a ta da arna da har suke neman shigo mata gida? Ganin tayi shiru ne yasa d'aya daga cikin su tace.
"We are friends of your husband,can you let us in..Mrs sadeeq?!”
"Me..? For what reason??"
"Don't get wrong Mrs sadeeq,we are friends of sadeeq ,we just came by to see his newly born baby”
Shi kuma ya rasa da suwa zai yi k'awance sai da mata dan rainin hankali, toh baxata bada d'an su ganshi ba bama su da kunya basu santa ba kawai zasu wani zo k'ilama k'arya suke salon su sace mata d'ah ne.
"Madam please..."
"Eyyah m sorry he is sleeping.."
Ta fad'a tana d'ari-d'ari kar su gano cewar 'yar koyo ce a cikin yaren turancin. Suka ce zasu dawo anjima ko gobe, suna fita ta kulle gidan bata bud'e ba sai da ya dawo ya buga mata waya taje ta bud'e.
"Ya aka yine cutie wallahi yanzu kin fiye rigima kamar ma k'aruwa take yi. Sam kamar baki haihuba yanzu kuma meye ya faru ko yaro nane ya ta6oki ne..?!"
Yana rik'e da hannunta suka shiga falon ta kuma had'e rai ya juyo da ita suna kallon juna yace.
"Gaya min menene ko kina nufin dad'ewa nayi ban dawo ba?!"
Zaunar dashi tayi taje ta kawo ruwa yasha kad'an sabida baya tare da k'ishi dan kar tayi zargin wani abun ne yasa shi yasha. Zama tayi Ayman na kan kujera yana bacci ta kwantar da kanta a cinyarsa yana jan hancinta tace.
"Bayan ka fitane wasu mata arnaye gunduma-gunduma suka shigo su hudu ko wacce da wani banzan skirt, wai dan son maidani wata sakarai suke ce min sunzo ganin Ayman ne wai ka gaya musu kanada d'ah."
"Ohh su Juliet ne da blessing sauran ne dai ban gane ko suwaye ba. Toh kin basu sun ganshi ko?"
"Kut in basu kuma..?! Wai kaima ka d'auka har yanzu bani da hankali ne? Kawai ban san su ba baka yi min bayanin su ba zan d'auki d'ana na basu, lallai da hankalina wallahi yanzu ba dah bane."
Kallonta yake shi yanzu baya ganin wani aibunta komai tayi sai yaji zuciyarsa ta aminta da abun koda kuwa yana son yi mata gyara. Hannunta ya rik'o ya sumbata sannan ya fara shafar fuskarta yace.
"Cutie su Juliet mak'otan mune wannan benan na jikin mu shine gidan su, please ki bari kuyi mutunci musulunci be hana ba suna da kirki basuda matsala suna ganin girmana sosai."
"Lallai in rasa da wad'an da zanyi k'awance sai da arna wallahi ba ruwa na bazan yi ba sam."
Shafa kanta yayi lallai ashe akwai gwarmai domin idan yazo da Fateema suna zuwa kuma bata kyarar su hakan yasa suka saba ita kuma ko me ta d'auki Christians oho mata. Share zancen yayi ya d'agata tare da janta suka shiga kitchen dan yaga alamar har lokacin haushin bak'in basu barta ba.
"Cutien Sadeeq da Ayman a dafa min wannan abun."
Yafad'a yana ciro wani magani a cikin aljihunsa, tana tsaye tasa shi ya d'akko tukunya tace ya tari ruwa a sink ta kunna gas ya zuba maganin yana dariya k'asa-k'asa dan dama yasan INdon sa tun a tsefawa 'yar rigima ce dan haka yanzu in tayi abin bazai damesa ba sosai kuma tafishi gaskiya tunda bata sansu ba tayi hankali da ta hanasu dan za'a iya zuwa a damfareta hakan kuma da tayi ta nuna mai ba da kowa zata dinga yadda ba kamar yadda wasu suke ganin hakan cinyewa ne sai kuma an cucesu suzo suna kuka. Har ya dahu suna kitchen d'in tana ta6ara.
"Muje falo naga wasu littattafan turanci, tunda maganin ya dahu kafin ya huce na karanta maka kaji."
Hannunsa ta fara jah yayi saurin rik'ota tare da girgiza mata kai ta had'e rai. Maganin ya d'auka ya kai bathroom ya juye cikin bahon wankan Ayman sannan ya mayar da tukunyar kitchen ya kalleta ta zauna kan kujera sai cuno baki take yi ya zauna kusa da ita yana rik'o hannunta murya a sark'e yana narke mata idanuwa yace.
"Cutie rigima, zo muje ai naki ne shiga ciki zaki yi."
INdo ta zaro idanuwa fuskarta a d'aure tana mai wani irin bahagwan kallo, ganin yadda take kallansa a hagunce yasa shi shafar fuskarta yace.
"Whats wrong?"
"Shin bakajin nutsuwa dani ne ko kuwa dai wani abun kakeji a tattare dani? Ko kuma me kake nufi malam Sadeeq da zaka kawon abu wai in shiga ciki...?!"
Hannu yasa ya rik'e kansa tare da rintsa ido jin yadda ta mayar mai da abunsa. 'Dagowa yayi idanunsa jawur sabida yadda ransa ya sosu dajin abinda tace ba tare da yayi magana ba ya d'auki phone ya kira Fateema bayan ya had'iye 6acin ransa.
"Hello baby na ya aiki? Yasu my sweet Ayman?!"
"Lafiya lau baby ya skull kin dawo ko?"
INdo ta mik'e zata bar gurin yayi saurin rik'ota ta fara k'ok'arin kwatar kanta dan wani haushinsa takeji. Ji tayi ya cigaba da yin wayarsa hankali kwance kafin taji yace.
"Ammm baby ko kina son na taho miki da wannan ganyen maganin naga wannan zuwan ma na kawo shi kina so?!"
"Woww babyna ina so mana dan Allah kaje ka siyo karya k'are please my awesome husband."
"Okey tom zan kawo miki insha Allahu bye zan kiraki anjima."
"Thank you baby a gaida min da Ayman my son."
"Insha Allahu."
Kashewa yayi yana kallon INdo wadda still fuskarta a had'e take. Janyo ta yayi ta fad'o jikinsa tana turesa ya matseta tare da zura kansa saitin wuyanta yace.
"Banyi tunanin cewar akwai abinda zan saki kiyi amma ki tsaya tuhumata ba, Aisha ko wuta na rura nace kishiga hakan ya nuna min bazaki shiga ba sabida bakya sona da kina sona duk abinda zan ce kiyi bazaki tsaya wani tunani ko gaddama ba sai gashi kinyi na gani shi kenan na gode Allah yaso ina da wadda ta yadda dani 100%."
INdo najin haka ta saka kuka shi kuma ya tureta ya juya kan kujerar yayi kwanciyar sa duk da yanajin kukan har cikin k'ahon zuciyarsa. Tashi tayi a hankali tana kukan ta shiga bathroom, shiga tayi cikin ruwan tana ciki tana jan majina yayi murmushi ya kuma k'i bin bayanta, bata fito ba har sai dashi kansa yaga dacewar lokacin tafito yayi amma tak'i fitowa.
Zaune ya ganta a ciki ta saka fuskarta tsakankanin jinyoyinta sai gunjin kuka takeyi, k'arasawa yayi ya tsugunna a gabanta tare da saka hannu ya fara k'ok'arin d'ago fuskar ta amma tak'i ta kafe. Taurin kai na INdo sai addu'a ya mik'e tare ya d'agota cikin nuna k'arfi sannan ya fito da ita suka shiga bedroom yana rungume da ita suka zauna a bakin gado.
A gabanta ya zauna tare da rik'o hannunta kanta a k'asa idanuwanta a rufe sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi. Kallon fuskarta yakeyi cikin tsananin sonta da kaunarta yace.
"Cutie nine fah ya kamata nayi kuka sabida kin kasa yadda dani, cutie i love you..ban san yadda zanyi na misalta miki ba duk abinda kikaga nayi dan ina sonki ne. Cutie koda kikaga na dage sai kin biyoni nan karkiyi tunanin cewar ko bana son kiyi karatune a'a ina son zuwa dake ne sabida ko bayan rai na kiyi alfaharin kema naje dake inda nake zuwa shi yasa kika ga na dage sai kin bini amma duk abinda nayi miki na rashin dad'i cikin sani ko rashinsa kiyi hakuri ki yafemin."
Hawaye suka kuma zubo mata ya tashi ya zauna kusa da ita tare da janyo ta jikinsa yana buga bayanta cikin muryar kuka take magana.
"Ni ka dena bani hakuri bayan baka min komai ba, nice zan baka hakuri sabida nice nake 6ata maka rai amma dan Allah abu Ayman kayi hakuri ka dinga yafemin koda a cikin zuciyar kane nasan ina 6ata maka rai dan All..."
A hankali yasa hannunsa ya toshe mata baki yana kad'a mata kai alamar tayi shiru, da sauri ta rungumesa suka k'ank'ame junansu cikin shauk'i. Basu fito ba sai da kowa yasan ya farantawa d'an uwansa sannan suka yi wanka suka ci gaba da soyayyarsu yana kuma koya mata karatunta cike da kwarewa yadda kuma zata gane ta fahimta duk da cewar tana d'an dad'ewa kafin ya zauna a kwakwalwarta danma understanding takeyi ba wai hadda ba.
Bayan sati uku
Lokacin sun cika wata d'aya da zuwa cikin ikon Allah kuma ya samu INdo ta fara sakarwa su blessing fuska sai dai yawanci sunfi yin wasa da Ayman kasan cewar turancin INdo ba nisa yayi ba kamar su da yazama shine yarensu na biyu da suke ji bayan inyamuranci. Itama takan d'an lek'a gidan su amma ba sosai ba dan su kan yi yarensu wanda yafi bawa INdo haushi sabida ko "zo" bata iya ba su kuma sunfi yinsa.
Sosai suka sake kulla babin soyayya dan zaman su anan su biyu ya kuma kulla sabuwar alak'a dan har basa son wani yayi nisa sukanji har zazza6i amma da an had'u sai a warke zuciyar su ta riga ta zama d'aya, duk abinda d'aya yakeji wala na dad'i ko rashinsa sai duk sunji yanayin a jikinsu, ciwon kai idan d'aya yayi sai d'ayan ma yayi koda kuwa fad'uwar gaba ce wannan yanayin yana basu mamaki da al'ajabi, sun kuma sake tabbatar da cewa sunyi *MUSAYAR ZUCIYA* ya kar6i tata itama ta k'ar6i tashi suna kula da junansu sannan ta rage yi masa taurin kai musamman da yake karanto mata tarihin annabawa duk dare idan sunje bacci.
Ayman yana ta wayo suna kula dashi sosai sannan koda second d'aya Sadeeq be ta6a manta Fateema ba yakan buga mata waya a rana kusan sau biyar yayi missing d'inta sosai domin ko wacce mace tana da nata matsayin a zuciyar miji musamman da ya kasan ce ita ya fara furtawa kalmar So ya kuma fara auranta ya fara saninta a matsayin matarsa. Yana jin dad'in zama da matansa su duka musamman yanzu da soyayyarsa ta kuma zama a cikin zuciyar INdo, yafi ta sonta amma yakan daure domin karya d'ora mata girman kai karta dinga d'aukar kanta a wani abun tunda yanzu ne yake d'orata akan sabuwar rayuwa dan yanzu ne take kuma sanin komai na rayuwa duk abinda ya d'orata akai zai ga shi takeyi bata ta6a k'etare duk wani abu da ya karanto mata ya fassara mata.
Watansu biyu suka shirya komawa lokacin INdo ta kuma wayewa tayi kyau tayi k'iba ta zama tamkar wata k'aramar hajiya tayi dam kwanciyar hankali ya fito a jikinta da yanayinta dama yadda take