Showing 66001 words to 69000 words out of 85627 words

Chapter 23 - MUSAYAR ZUCIYA COMPLETE BOOK by Hajja Ce.txt

Hajja Ce   

14 Sep 2025

42

ta yana matsar ta da gashin kanta, nuna mai tayi hakan ya tayar mai da hankali duk iya k'ok'arinta na ganin ya samu nutsuwa abin ya faskar sai da kawai ya nuna mata yayi normal sabida baya son damuwarta yasan da zata iya d'auke blood d'in da yanzu tayi.

"Baby Ina abincin Aishan, kawo naje nakai mata zan biya can gurin Anas akwai abinda zan k'ar6o a gurinsa."

Kallonsa tayi tasan k'ila yaje gurin Aisha, amma a k'a'ida yau itace dashi sai dai baxata so ta ganshi cikin matsala ba, tayi murmushin yak'e tana shafar gashin da ya lullu6e k'ewayan bakinsa tace.

"Yana falo na zuba."

Tashi yayi ya mayar da kayansa ta rakosa ya d'auki basket d'in k'irjinta na bugawa dan tana zargin akwai abinda zai had'asa da INdo amma tasan basa shiri zai iya sharewa ya jira har lokacin da zata samu tsarki.

"Bye-bye baby ina dawowa zanci abinci nayi bacci dan agajiye nake munyi kwanan mota."

"Toh sai ka dawo ayi mata sannu, kona zo muje tare?!"

Kallonta yayi na 'yan dak'ik'a kafin yayi murmushi yace.

"Yanzu kika dawo daga gurin aiki, sannan kice zaki fita bayan mijinki ya dawo daga tafiya me nisa. No ki zauna ki tanadar min dadd'ar hirar da zaki min idan na dawo."

Fateema tayi dariya tare da d'aga mai hannu ya fita tana kallonsa kishinsa fal cikin k'ahon ziciyarta.

Yana fita ya shiga mota yayi gidan INdo, yana zuwa a bud'e yaga gidan yayi parking a gefen gidan ya d'auki kayan abinci ya Shiga. Babu kowa har ya shiga cikin bedroom d'inta bayan ya ajiya abincin a falo. Tararwa yayi ta idar da sallah, ya tsaya a bayanta yau INdo ce take sallah harda su addu'a, lallai Allah buwayi mai sauyin lamari kamar yadda ya sauya salon alak'arsu daga malamin ta zuwa mijin twinnie d'insa daga nan ya sauya zuwa mijinta.

"Humairah."

Taji ya fad'a k'irjinta yayi tsananin bugawa tayi saurin waigawa tana kallonsa ido waje. Murmushi ya sakar mata tayi saurin d'auke kai dacta ya fad'a mata jin muryar data fara kiranta da sunan. Anya ba munafuntar ta akayi ba Sadeeq ya mutu aka raina wayonta aka ce Abubakar ne, anya shima ba yaudararta yake yi ba aka had'a baki dashi zasu raina mata hankali.

Bata gama dai-dai tuwa ba taji ya zauna a kusa da ita har suna gogar juna ya lek'a fuskarta tare da cewa.

"Tunanin me kikeyi haka? Ni ko Abubakar."

Ta zame hijjab d'inta ba tare da ta kallesa ba. Shin me yayi mata a cikin rayuwarta da zata wani dinga tunaninsa, wanda yayi matan ya koma ga Allah ko kuma dan yayi mata ciki shine zai sa ta dunga tuna sa kila haka yake nufi.

"Okey yanzu bazaki kulani bama.?"

"Welcome back malam Sadeeq."

"Sai da na rok'a, ai ba haka kikewa M twinnie ba oya hug me."

"Kitchen zani mafa ko indomie na dafa, nasan dai kai bazakaci ba."

"I said kiyi min Oyo-yo, kamar yadda kika min ranar danaje d'akkoki kika yi tunanin marigayi ne, oya am waiting."

Tura baki tayi tana mamakinsa ganin irin yadda dacta yake mata abubuwa tace.

"Ni a'a, ka kyaleni naje wallahi inajin yunwa."

"Na kawo miki abinci, amma sai kin min oyo-yo sannan zan baki."

A hankali ta juya ganin ya takura mata ta rungumesa bayan ta rintsa idanuwa. Jin k'irjinta a nasa ya sashi jin wani shock ya sanya hannunsa ya mak'alota gabaki d'ayanta jikinsa ya hau rawa tana jin haka ta kwace kanta ya samu da kyar yajata suka fita falo.

Da kanshi yaje ya d’akko plate a kitchen ya zuba mata, tunda taji k'amshin kifi take jin tamkar ta cinye abin miyar ya zuba musu tare sai kallonsa take yi ganin yanzu yana mata wasu abubuwan da marigayi yake mata hakan kuma ya sa ta d'an sakar masa tun yana bata a yangance taji ko abinda ke cikin nata besan ana bata abinci ba yasa ta cewa.

"Kawo ni na dinga baka gaskiya."

A tunaninsa ko ta fara sonsa yayi murmushi tare da sakar mata spoon da pork d'in, idan ta bashi sau d'aya sai tayi kusan spoon biyar sannan zata kuma bashi, ya dinga bin fuskarta da kallo yana jin wani abu tamkar magnet yana fisgarsa. Sai da suka k'oshi sannan ta kwashe kwanukan takai wajan wanke-wanke yana binta da kallo duk da cewar doguwar riga ce a jikinta sai dai komai na jikinta rawa yake yi Sadeeq ya jingina da kujera shi kam bazai iya kwana a haka ba, tunda yasawa ransa idan ya dawo zai samu nutsuwa koda a gurin Fateema ne toh gashi tana off yayi 3mothns a wahale bazai iya kwana haka ba.

"Sir Sadeeq na gode sosai, a cewa Fateema itama na gode ga kwanukanta."

INdo ta fad'a tana k'ok'arin ajiye kwandon akan center table. Shi kuwa tamkar me bacci haka yayi nan kuwa yana kallonta ta k'asan ido yaga tana kallonsa jin yayi shiru yasa ta shiga d'aki ta zauna a bakin gado tare da d'akko jakar makarantar ta ta fito da books d'in wanda duk iya kunshesun da tayi a jiki saida ruwa ya ta6a su ta bubbud'e su akan gado tana turo baki ganin duk sun sha ruwa.

Ta bayanta taji ya rik'o ta, sharesa tayi ta cigaba da hura book d'in hannunta da baki ya sa hannu ya k'ar6a ya ajiye akan gadon ita kuma ya jata suka kwanta akan gado INdo tace.

"Ana k'iran sallar la'asar."

"Uhmm naji Humaira but I need your help please."

"Tofa name.?!"

"I need you, dan Allah humaira karki min wata fassarar karki hanani ina cikin matsala humaira wallahi I love you... I love you Aisha karkiyi tunanin kodan wannan abun ne."

Jikin INdo yahau rawa ta fashe da kuka tana jin yadda yake mata amma ta kasa hanasa domin tana jin hirar matan ajinsu akan mazajen su. Shi kuma jin bata yi masa irin na farko ba yasa shi cikin karyar da kai da nuna tsantsar nadama yasa har ya cinma muradinsa akan ta sannan shima yahau yin nasa hawayen.

_"Twinnie kasan nifa ni bazai yuwu nazo gidana naga matata ba sannan na kyaleta ba no Zuciya ta baza ta bari bama tunda nasan mallakina ce."_

Ya tuno irin hirarrakin su da Abubakar cikin shak'kk'iyar murya Sadeeq yace wa INdo.

"Skukran-laki Aisha Humaira. Do you love me? Please humaira love me as I love koda na iya yau ne kawai."

"Malam S.."

Ya rufe mata baki da nasa cikin son katse ta da sunan da yaji zata kirasa sannan ya cire yace.

"Don't call me malam again. please change my name in dai har kin yadda zaki soni kamar yadda kike son twinnie d'ina."

Hannunsa zagaye da wuyan ta suna had'a numfashi INdo tace.....











*HAJJA CE*👈
[7/31, 5:13 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
♥♥

A true life story

Na

*K.A.S Precious Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*DEDICTEED TO:* Sanah Isma'il Matazu.

*VOTE me on wattpad @Hajjac*


Page *33*


"Toh mezan ce maka? Kaga kaima Fateema ka fara aura, kuma ita kake so kafin ni. Toh nima ina sonka amma nafison marigayi dacta nima kaga ma an raba kar wani yaji haushin wani."

Fuskarta yakai dai-dai tata ya had'e hancinsu guri d'aya yana rik'e da hannunta yace.

"No Humaira wannan ba magana bane har yanzu ke yarinya ce. Idan nace zan dinga nuna miki soyayyar Fateema a fili zaki sha wahala tunda kinga ina nuna mata itama zata fallasa nata. While ke kuma idan kika ce zaki fifita soyayyar m twinnie a gurina babu abinda zanji sabida yadda muke dashi kuma baya raye bare ya dinga rama miki kamar yadda zamu yi nida Fateema a gabanki. So kidena kawo wannan abun a ranki yanzu ni zaki saka a cikin zuciyarki ba wani ba."

INdo ta juya baya tare da cewa.

"I love him tayaya zank'i fad'a kawai dan ya mutu? Dama haka soyayya da amana take idan ka mutu a shafe babin rayuwarka? No gaskiya nayi mai alk'awarin bazan manta da shiba har k'arshen rayuwa ta."

Rintsa idanuwa Sadeeq yayi, sam
Baiyi tunanin zaiji kishi haka ba amma yaji ransa na sosuwa jin yadda take cewa tana son wani mamaci ba shiba. No wonder mutane suke tsoron auran matar mamaci sabida koyaya zaka yi mata abu sai ta fad'esa ta nuna maka yafika, shi kam ya shiga uku gashi wani sanyayyan sonta sai sake shigarsa yake. Ba shakka indai haka Abubakar yaji a baya dole ya rikice yace yana sonta a duk yadda take, dole ya kira ta zuciyarsa sabida yadda a yanzu ta kuma shiga cikin tunanin Sadeeq d'in.

"Juyo toh kiji."

Yayi maganar yana kallon bayanta, a hankali ta juyo sai dai idanunta a kulle suke gam yace.

"Zaki bini idan zan koma kwara state? Karki ce min a'a kinga ina son hakan so nake na shirya yadda zanyi tun daga yanzu."

"Kai karatuna fa?!"

"Karki tashi hankalinki kina dani zan dinga yi miki wannan makarantar duk k'aryar banza ce. Ki bini kigani zaki sha mamaki in a few days."

(Kunji wayo... Wai makaranta ce karyar banza dan kawai yana son yi mata wayo maxa..maza mutanan mu).

"Amma kuma fa malam Sadeeq..."

Yayi saurin katseta bayan ya janyo ta jikinsa yana zagaye hands d'inshi a k'irjinta yace.

Shhhii “ba anan zaki dinga kirana malam ba sai munje teburin d'aukar darasi but wannan gurin kam ki dinga kirana da wani sunan special da zai zama kene kike k'irana dashi”

“Kamar irin su honey, sweetie, heartbeat, July juice, mango, touch light, tomato, vest....."

"Ke.. Ke..! Uhm..uhm duk wannan sunan fa, na waye ne.?!"

"Toh ai lissafo maka nakeyi sai ka za6a a ciki."

"Shine harda su July juice, vest, tomato? You ko.."

Ya fad'a tare da ja mata hanci tayi dariya har hak'oranta suka fito murya k'asa-k'asa tace.

"Ashe kaima wata ran kanada kirki..?!"

"Eh dama kece bakya lura but yanzu ai kin fara gani, tashi muje muyi wanka gashi bamu yi sallah ba."

"Toh amma ka fara yi."

"A'a tare xamuyi tunda komai tare muke yi."

"Innalillahi nidai gaskiya ka fara zuwa ka yi."

"Yauwa kin tuna min ma, baki gaya min ba zaki bini muje? Kinga a lokacin nake son dana koma na sake bud'e wani gurin kema ya kasan ce idan muje kina da naki d'akin, bana son business a nan sabida sa ido da nan kawai zan dawo gabaki d'aya."

Shiru INdo tayi dan a gaskiya bata son zuwa garin tunda yanzu ta fara iya turancinta, itada ba kwarewa ta gama yi ba kawai ya jata su tafi sai sun je shima ya sauya mata tana tsoron Allah tana tsoron butulcin d'an Adam.

"Tunda ba gobe zan tafi ba zan kyaleki kiyi shawara kinji?!"

"Toh."

Ta fad'a ya mik'e ya shiga toilet ya tarar musu ruwa ya dawo, da kyar ta bari suka je wanka suka yi tare duk da dakyar ta tsaya.

Sai da suka d'auro alwala sannan suka fito yana rik'e da ita duk asan samunsa na ganin ta aminta dashi ta saki jiki ta kuma yadda da shid'in me sonta ne da gaskiya. Riga tasa ta atamfa da skirt sannan ta shimfid'a musu sallaya ta bishi da kallo ganinsa a zaune bashi da niyar sa kaya tace.

"Sallan fa, kona yi tawa?!"

Ido ya lumshe tare da hura iskar bakinsa yace "wane kayan zansa.?!"

"Lallai ni ina na sani, ai kasan fa ko hularka babu a cikin gidan nan. Nidai bari nayi tawa sai ka tafi gidan Fateema kayi acan."

Tana fad'a ta fara k'ok'arin tayar da sallah ya mik'e tsaye tare da tsayawa a gabanta yace.

"A'a bari nasa riga ta ai doguwa ce ta rufe min gwiwa."

"Nashiga uku haka zaka yi babu wando ji kafafuwa a waje a haka zaka yi sallan? Oh ni INdo..."

"Eh aini an hallarta min yin hakan kune dai aka haramta muku yin sallah idan baku lullu6e jikinku duka ba, Allahu akubar²."

Taji kawai ya tayar. A ranta kawai ta barsa dan tasan sallar malam Sadeeq bata kar6u ba. Suna idarwa sai ga su Haleema tayi sauri zata mik'e ta fita Sadeeq ya rik'ota suka yiwa juna kallon ciki ido.

"Ina zaki?"

"Su Haleema nefa ba kaji muryar su ba."

"Naji amma ai baki tsaya kinyi addu'a ba kamar d'azu, zo kiyi addu'a sai ki fita gurin nasu."

Komawa tayi ta zauna su kuma sai rangad'a sallama suke yi jin shiru yasa Aminatu lek'awa d'akin.

"Au ashe sallah suke yi Yaya ma nanan."

Guri suka samu a falon suka zauna suna jiran fitowar su. Matsawa yayi kusa da ita tana addu'a saitin kunnanta yace.

"Kiyi mana addu'a, amma dan Allah karki rok’ar min mutuwa da gaggawa."

Bata juyo ba tayi murmushi jin abinda ya fad'a. Shi kuwa tsoran irin addu'o'in da takeyi mai a baya ne yasa shi fad'ar haka yanzu tunda sun fara shryawa . Kuma mik'ewa tayi ya janyota tare da waigawa yana kallon k'ofa sannan ya sumbaci saman lip d'inta ta fita.

"Aunty Humaira ya gida??"

Ta zauna tana kallon Haleema sabida itace me kallonta tunda ta fito, INdo tace.

"Ke wai meye ne? Sai wani kallon tuhuma kike min."

"Kai aunty Humaira, missing d'inki nayi fa kinsan kwana hud'un nan duk a cikin hostel nayi su, bama haduwa sai naji kamar shekara nayi ban ganki ba."

"Oho ni kuwa banyi wani missing d'inki ba sabida kullum idan baki zoba bacci na nakeyi."

"Aisha.."

Sadeeq ya kira ta ta mik'e taje d'akin. Tsaye ta gansa yana gyaran hular kansa ta d'an tsaya nesa dashi ya janyo ta yace.

"Zan fita anjima zan zo muyi sallama."

Tace "Toh sai kazo."

"Is this all abinda zaki ce min?!"

INdo ta d'an kallesa kafin tace.

"Toh kayi shaving wannan gemun yayi ma yawa."

"Sunnah ce fa cutie amma tunda bakya so zan cire."

"Toh sai ka dawo."

"Kin gaji ne? Na tafi na baki guri ko?"

"Ah kawai kaga dai su Haleematu na nan."

"Okey bari naje na dawo, give me good bye hug."

Ya fad'a yana bud'e mata hannuwa, ya zata yi dole taje ta rungumesa ya matseta a jikinsa kafin ya sake ta suka fito tare, 'yan k'annan nasa suka gaidashi sannan ya fita ita kuma ta zauna gurin su suka sha hira har Aminatu ta dafa musu Indomie suka ci.

Sadeeq kuwa gidan Fateema ya koma, tare suka yi sallan isha sam be nuna mata cewar gidan INdo yaje ba nuna mata yayi yana kai abinci gurin Anas ya wuce. Suna idar da sallahn isha'i yace mata.

"Baby na bari naje can gidan nayi mata saida safe, daga can zan tsaya nayi aski ki dafa min tea kafin na dawo."

Fateema da shagwa6a tasan yana son shagwa6a tana jikinsa a tsaye tace.

"Gaskiya Baby karka yi aski ni dai ka barshi ina son shi yayi ma kyau."

Idanuwa Sadeeq ya zaro jin ita kuma abinda tace, INdo tace bata so ita kuma tace ya barshi tana so ya shiga uku.

"Menene naga ka zaro idanuwa haka? Shikenan jeka aske tunda baka son ka barmin kuma ina so."

"Ah baby na isa, tunda kina so ai dole na barshi uwar gida sarautar gida. Bari toh naje na dawo."

Fateema tayi murmushin jin dad'i ganin yana yi mata duk abinda take so. Sai da ta raka shi har gate ya juyo yana kallonta bayan yayi kalar tausayi yace.

"No bye bye kiss ko? Shikenan nayi fushi."

Da gudu ta rik'osa ganin zai fice tana dariya ta kamo wuyansa ya sunkuyo da kansa tayi kissing d'inshi tare da cewa.

"Sai ka dawo karka dad'e."

"Okey as you wish baby."

Sannan ya fita yana tunanin yadda zai yi musu. Su Haleema kuwa Sai wajan k'arfe takwas na dare sannan suka tafi gida ya rage sai INdo kawai tayi sallahn isha'i ta cigaba da gyaran littattafanta.

Jam-luck tasa hakan yasa yana sanya mukulli k'ofar ta bud'e. Shiga yayi tana jin motsinsa tayi saurin kwanciya tayi baccin k'arya. Kallonta yayi ganin yadda ta kwanta akan books d'in gashi ta kudindine fuska cikin bargo, ya k'arasa kan gadon tare da sanya hannu ya cire mata shi daga fuskar ta.

"Oh harma bacci kika yi bayan nace miki zan dawo ko?!"

Yayi maganar cikin kunnanta, INdo tayi mik'a alamar wai ya tashe ta sannan ta fara mistsike idanuwa murya a shak'e tace.

"Au ka dawo?!"

"A'a ina can."

Ya bata amsa yana kallon fuskarta ta wani maze tamkar daga baccin gaske ta tashi.

"Shikenan sai da safe in tafi..?!"

"Eh sai da safe amma 8:00am zan tafi makaranta fa."

"Ba nace kin dena zuwa ba?!"

"Kai malam Sadeeq weekend fa nake zuwa ita kuma Fateema yau da gobe bata da aiki kuma dama acan kake toh kaga ai ba abin hanani zuwa, ni dai gaskiya zani Ina son school d'in gashi malamin shima yana son yaga na iya wallahi yana da k'irk'i yana sona."

"Yana sonki kuma?!"

Cewar Sadeeq a mamakance, cikin rashin fahimtar fassarar dayayi ma maganar INdo tace.

"Eh wallahi har extra lesson yake min."

"What...!"

"Kai malam Sadeeq dafa ace bankai kaina wannan makarantar ba da nasan wallahi har yanzu baxakai marmarin so naba. Toh meyasa yanzu na shiga kake kuma k'ok'arin rabani da ita bayan akan rashin iyawa t...."

Be bare ta k'arasa magana ba taji bakinsa cikin nata. Irin deep nd passionate kissing d'in nan ya dinga tura mata har jikinta ya kasa d'aukarta ta shiga biye mai ba tare da tasan ta iya hakan ba. Cikin rashin sani suka sake kasan cewa da juna musamman Sadeeq da sai da ya jima sannan ya gano da tabbacin abinda ya sake faruwa.

"Na barki... Na barki Humaira kiyi karatunki zan cigaba da baki nawa gudun mawar insha Allahu. I love you with all my heart and soul Aisha please say you love me dan Allah...."

Shiru INdo tayi ta kasa fad'a ji take yi tamkar idan ta fad'a tayi k'arya dan bataji wani love dinsa ba dazai iya sawa ta gaya masa.

"In tafi bakya sona ko?!"

"A'ah ni bance ba, amma ka tafi dare nayi Fateema na jiranka."

"Aisha bakya sona ko? Shikenan."

"Toh ina sonka, aini bance bana sonka ba."

Agogo ya duba yaga sha biyu saura minti goma, da kyar ya tashi ya sa kaya INdo na kwance idanunta a rufe yaje ya sumbaceta sannan ya tafi ya kullo mata gidan da mukulli.

Yana zuwa ta dinga kallonsa wanda yasa shi tsarguwa yayi murmushi tare da d'aukar ta suka wuce bedroom. Romance d'inta ya dinga yi har sai da ya nuna mata shima fa yana buk'ata yasan hakan ne kawai zai wankesa da zargin da ya hango a cikin idanunta, ganin ya fita birkicewa ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login