Showing 1 words to 3000 words out of 85627 words

Chapter 1 - MUSAYAR ZUCIYA COMPLETE BOOK by Hajja Ce.txt

Hajja Ce   

14 Sep 2025

12

[7/1, 4:48 PM] Aisha Galadima: *⚗⚗ MUSAYAR ZUCIYA...⚗⚗*
                    ♥
                 ♥♥
         A true life story

Na

*K.A.S Precious Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSOCIATION*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*DEDICATED TO* Sanah Isma'il matazu.

Bismillahir Rahmanur Rahim.....

  "Hakk'in mallakar Hajja ne, kar wanda yayi min sauyi a cikin sa please."


Page *1*

A makaranta.

   "Uwani halilu?"
     "Present sir.."
   "Baraka lado?"
     "Present sir.."
  "Sahura Ayuba?"
      "Present sir.."
   "Indo malam Hamza?"
  "Labbaika, present, sir, mah, nazo..."

Saurin kallon ta malamin yayi jin yauma a yadda ta amsa mai kafin ya zare glass d'in dake manne akan saman idan fuskar shi, ya d'ora dara-daran idanun shi akan nata da nufin ko zata ji tsoron sa sai yaga ta kafeshi da idanuwan ta tamkar zata cinye shi, yayi saurin wurga mata uwar harara ranshi a matuk'ar had'e yace mata cikin tsawa.

"Ke..! Baki da hankali ne...?!"

Indo ta mik'e tsaye tana gyaran hijjab d'in ta wanda yayi dikil-dikil da daud'a wuyan ya yage tun daga wuya har zuwa k'irjinta sannan tace,

"Da sauk'i dai malam..!"

"Naga alama ai koma gurinki ki zauna wawuya kawai.."

Ya fad'a ba tare da ya kalleta ba. Komawa tayi ta zauna sai faman soshe-soshe take yi akan ta wanda hakan da alama ba za'a rasa kwaron kwarkwata ba dan yadda take yi ya nuna hakan. sai da ya kammala kiran sunayen su tas! sannan ya mik'e ya fita yana jiran lokaci ya cika sai ya kuma dawowa yayi musu subject d'in turanci wanda aka sari basa fahimtar uban komai a ciki, idan kuwa yana son su fahimta toh sai ya had'a musu da yaren hausa sannan zaiji ruwan amsa da tambayoyi amma idan da turanci zai kwana yana yi sai dai su kafamai idanuwa tamkar zasu cinye shi.

Yana fita wajan mintuna biyar sai gashi ya kuma dawowa hannun shi d'auke da wasu littattafai manya da kananu. yana shiga ya tarar duk sun kaure da surutu yayin da ya kai idanunshi can k'arshen ajin ya hango INdo da wani yaro taci uwar d'amara da hijjabin ta suna dambe. Dorinar hannun shi ya d'akko yayi gurin. sauran yara na ganin shi suka fara watsewa aka bar INdo da lurwanu a gurin. yana zuwa ya fara tsulawa INdo dorinar ganin ita ce me fifik'arewa kafin ya tsulawa lurwanu yana cewa.

"Ke! Sakar mai riga wawuya kawai."

Axabar bulalar ne yasa ta saki amma da ba tayi niyar sakin shi ba sai ta fasa mai baki kamar yadda ta furta tun farkon fad'an nasu. Malam Sadeeq na kallon su yace.

"Me ya had'a Ku?!"

Idanu kwal-kwal zasu kawo ruwan kuka lurwanu yace.

"Malam itace..."

Caraf be k'arasa fad'a ba INdo tace,

"Malam wallahi k'arya yake shine ya fara..."

Shima lurwanu dan kar tamai sharri ya kuma tare zan cen,

"Wallahi malam k'arya take yi kawai na ajiye..."

"Billahillaxi malam shine ya..."

"Keep silent or something else's, sha-sha-shai kawai.."

Babu abin da suka fahimta a cikin abin da yace dasu sai dai yana yin yadda yayi musu maganar da kuma kalaman shi na karshe ya tabbatar musu da cewar fad'a yake musu hakan yasa suka yi shiru suna bin kyakyawan bakin shi da kallo ba kamar INdo da take tunanin ko alawace ji take kamar ta lasa dan yadda ya burgeta.

Komawa yayi wajan teburin shi ya zauna sannan yayi musu alamar suzo baki d'ayan, suka bishi INDO sai faman ture lurwanu take yi a haka suka k'arasa wajan da malam Sadeeq yake jiran su,

"Kai me ya had'a ku da ita?!"

"Malam itace kawai muna zaune sai tazo tana tab'ani da kafa nayi mata magana ta dena takani shine tak'i taci gaba har muka fara fad'a da ita."

Tun kafin ya bata izinin magana INdo ta fara tana hararar lurwana bakin ta har kumfar yawu yake sabida masifa,

"Kai..Kain uban can..! Na rantse da Allah malam shine ya d'alamin kaure a baya na shine na rama ya kuma yi min kawai muka fara fad'a dan shi masifaffe ne ya raina ni.."

"Ya isah haka kowa yaje ya zauna bana son surutun ban za."

Tashi suka yi suka tafi dama can karshen aji nan ne wajan zaman INdo dan haka ta tafi malam Sadeeq yayi saurin dawo da ita, tana zuwa yace da 'yan layin gaba suyi mata guri anan ta zauna cike da jin haushin malamin dan taga alamar baya son ta bare yabi bayan ta a duk cikin al'amarinta.

A haka ya kammala musu yabar ajin duk sun gundure shi ga haushin basa ganewa da turanci har sai yayi da Hausa. Ana tashi ya hau mashin d'in sa kai tsaye ya wuce inda ya sauka. Wanka yayi sannan yayi sallar azahar ya koma gefe ya zauna bayan ya janyo wayar shi, laluban d'an uwan shi ya fara yi cikin sa'a ta fara k'ara yana d'agawa yace,

"Hi twins ya gida ya gurin aikin naka?!"

Daga can 6angaran ya amsa cikin sanyin murya kamar yana rad'a,

"Lafiya lau all twins ya student's da fatan dai kana samun yadda kake so koh?!"

Shafa k'eya yayi tamkar yana ganin shi sannan ya lashi lips d'in shi yace,

"Nop! Twins ga baki d'aya makarantar bata yi ba wallahi, gashi nazo an wani bani formaster teaching kuwa sai dai nayi da hausa wata Kalmar ma ban san yadda zan fassara musu ba wallahi sai dai na barsu a haka."

Dariya yayi mai sauti ya san dole a bawa d'an uwan shi haushi duba da yadda baya son wasa a harkar karatu gashi an kai shi inda zasu samai hawan jini, cikin basarwa yace.

"Common Sadeeq ka sani ko anan ma girlfriend d'inka take, dan Allah kasaki ranka kasan 'yan kauye da son mutane za kaji dad'i kuma zasu soka kai dai kawai ka samo mana wifey d'in ka acan..!"

Kit! Sadeeq ya kashe wayan sam beji dad'in wayar da suka yi da d'an uwan nashi ba yau, a maimakwan ya lallab'a shima a'a sai ma yi mai fatan tsiya da yake yi na samo mata dan wulakanci. shi kam Abubakar murmushi yayi jin ya katse ya san haushi yaji sabida yayi mai fatan tsiya. zai samu yaje garin har gurin shi ya bashi hakuri yaga kuma yadda suke yi.

***

Bayan wasu awanni, Sauri yake yi ya k'arasa cikin masallacin dan gudun kar a tayar yana hanya, sai da yazo dai-dai wajan wata kwata zai tsallaka kawai yaji an kwararo ruwan kanzo gabaki d'aya aka b'ata mai wandon dake jikin shi. Bin katangar gidan yayi da kallo cikin wani mugun takaici kafin yayi wani yunk'urin tuni an fara zagaye shi abin takai cin ma harda d'aliban shi. sai sannu suke zabga mai tamkar wanda yaji ciwo.

"Kai subhanallahi Malam Sadeeq ya a kai haka?"

Kafin ya bashi amsa wanda yayi maganar ya kalli wani yaro tare da cewa,

"Kai yi maza shiga nan gidan kace a temaka mana da ruwa a buta."

Juyawa yaron yayi shi kuma headmaster ya kalli Sadeeq cikin jimami yace.

"Garin Yaya hakan ta faru Malam Sadeeq?!"

Da kyar ya samu ya tsaida takaicikin shi kafin ya kalli headmaster yana kallon inda aka b'ata mai yace,

"Wucewa zan yi zuwa masallaci, su kuma ba tare da suna kulaba kawai suka watso k'azanta sai kace a cikin gidan su duk ba wannan ba sun b'atan lokaci na rasa jam'i."

"Ashha-ashha malam yi hakuri kasan kauyan namu ne sai hakuri duk haka suke yi kayi hakuri dan Allah.

Dai-dai lokacin yaron da aka aika suka fito shi da INDO hannunta rik'e da buta gefen butar ya fashe sai da ta d'an kar-kata ta taho tana cewa,

"Waye yake neman ruwa a buta?!"

Karaf suka had'a idanu da shi da sauri ta dashare baki tana matsawa wajan shi ruwan sai zuba yake ta kalleshi tare da cewa,

"La'ilaha'illallahu Malam Sadeeq kaine a k'ofar gidan mu yau?!"

Banza yayi mata yana kallon butar ganinta jage-jage gashi duk ta fashe ya sashi yin saurin juyawa tare da kallon headmaster yana cewa,

"Rankashi dad'e bari  kawai na koma gida naga nan duk b'ata lokaci ne na gode..."

Ba musu headmaster yayi mai sallama da sauri ya wuce sauran mutane na bashi hakuri ita kuma INDO tana fad'in,

"Malam ruwanfa? ko na biyo ka dahi koka ka fasa na maidahi gida?!"

K'in kulata yayi ganin haka yasa INdo ta murgud'a mai baki tamkar yana ganinta sannan ta koma gida tana mitar kawai yasa sunyi asarar ruwan su a k'asa bayan suma babu kala ne suke yi.

***

  Yau kwana biyu kenan INdo bata zuwa makaranta, sai a kwana na uku taje tun daga bakin k'ofa zaka tabbatar da yau tazo sabida yadda ajin ya kaure da shegen surutu da hayani. yana shiga ya ganta zaune akan tabur d'in da malamai ke zama idanunta sanye cikin eye glass wanda idanun (glass) d'in suka ciccire ta rik'e pencil tare da d'ora kafa d'aya kan d'aya tana yin irin na Malam Sadeeq,

"Mary alto."
"Zuwaira jamilu."
"Mansur bawa."

Gabaki d'aya ajin aka d'auki ihu da shewa dan sam basu kula da zuwan shi ba. har INdo ta mik'e tsaye tana dariya tare da cewa,

"Alkur'an haka malam Sadeeq yake yi.."

Suka k'ara tuntsurewa da dariya ana cewa,

"Ohhh ke INDO...!"

Tsittt taji anyi hakan yasa ta waigawa bakin k'ofar dan ganin yadda kowa ke kallon wajan, karaf suka yi idanuwa hudu da malam Sadeeq wanda yayi kicin-kicin da fuska tamkar hadari tayi saurin komawa wajan zamanta wanda in dai shine a ajin toh anan take zama sai ya fita take komawa gurinta na ai na hi wato karshen aji.

Yana shiga duk aka tashi ana gaida shi kowa ka gani cikin tsoro yake dan basu san matakin da zai d'auka akai ba,

"Good morning sir..!"

Sai da ya samu guri ya ajiye register da sauran littattafan hannun shi sannan ya kalle su yayi musu alamar su zauna da hannu, gyara glass d'in idanun shi yayi sannan ya kalli inda INdo take zaune ta kwalalo mai idanuwa yace mata,

"You! come here.."

Tashi tayi cikin d'ari-d'ari dan babu wanda be san kalmar come ba, tana zuwa ya matsa mata tare da nuna mata kujerar gurin yace,

"Seat down..." (Zauna)

Zama tayi dan taga ne abinda yace sabida yau da gobe idan sun gaida malamai ana ce musu seat down so kuwa ya san kalmar, ta zauna sai wulkita idanu take. register ya d'akko tare da bud'ewa ya mik'a mata jan biro da blue tare da cewa,

"Oya started."

Tayi saurin kallon shi tare da cewa,

"Na'am malam.."

Keya ya salle mata da hannunsa tare da cewa,

"Ki fara kiran sunan idan ba haka ba zaki sha wahala dan naga alamar kin raina ni so ina son kiyi musu yadda nake yi nima na gani.."

Kallon register d'in tayi sam kasa gane yadda take tayi bare aje ga karanto sunayen ciki ba zata iya ba kuma nan J.S one, kallon shi tayi tare da marairaicewa ta fara ba shi hakuri.

"Malam dan Allah idan kana kaunar iyayanka kayi hakuri wallahi tallahi ba zan sake ba."

"Au ba zaki fara ba sai na zane ki...?!"

Ya fad'a yana gyara dorinar hannun shi, nan da nan INdo ta fara kuka dan tak'i jinin a doke ta da bulala. tayi saurin zamewa k'asa tare da sake bashi hakuri akan ya kyaleta ta tuba tabi Allah tabi shi.

Ganin duk ta gigice yasa shi ce mata,

"Tashi ki dawo nan kiyi naildown."

"Malam baka hakura ba dan Allah?!"

Ta fad'a tana matse idanuwa dan hawaye su fito amma ko d'igo, ganin yaje ya zauna ya fara kiran suna yasa INdo tashi taje tayi abinda ya sakata dan ta san ba hakura yayi ba. sai da ya kammala kiran sunan ya fara koyar dasu ya gama sannan ya kalleta yana nunata da yatsa yace,

"Idan kika sake yin abinda nake yi in dai ba na karatu bane sai na 6allaki kina jina?!"

"Eh malam ai baxan kuma bama."

"Yafi miki.."

Ya fad'a tare da kwashe kayan shi yabar ajin yana tunanin inda zai yi ya samu ayi mishi transfer ya tsani makarantar sam ba tayi mishi ba.

Bayan sati biyu ranar wata Monday Sadeeq na shirin tafiya class d'in shi ya d'auki duk wani abu da yake buk'ata yana shirin fita kawai yaga Abubakar twins d'in shi tsaye cikin kananun kaya riga seegreen me dogwan hannu da wando baki sai farin eye glass wanda yayi mai matukar kyau, sosai suke matukar kama babu ta inda zaka iya bambance su sabida tsabar kamannin su. kallon shi Sadeeq yayi cikin tsananin mamaki tare da k'arasawa ya kalleshi cikin mamaki yace,

"Yanzu muka gama waya da kai amma shine baka gaya min kana hanya ba why?!"

Kafad'a Abubakar ya d'aga alamar ba komai sannan ya shiga ciki ya zauna tare da cewa,

"Twin ko class zaka shiga ne?!"

"Eh but tunda kazo sai mu wuce gida ka huta gobe na shigar musu."

Yayi maganar yana k'okarin maida littattafan dake hannun shi, da sauri Abubakar ya mik'e tsaye yana tsayar dashi ta hanyar rik'e hannun shi yace,

"No kazo muje sai na tsayaka ina nan tare da kai har zuwa gobe."

Kafad'a Sadeeq ya d'aga sannan ya d'auka tare da juyawa yana fad'in.

"Toh muje."

Tafiya suke wanda ita kanta iri d'aya ce suke yi suna yi suna hira yara kuwa daga cikin tagogin ajin su sai lekowa suke suna mamaki da al'ajabi ganin malam Sadeeq guda biyu a haka suka k'arasa barandar ajin su INdo. Yauma kamar kullum cikin surutu suka gansu sam basu lura da zuwan su ba INdo suka hango a saman dest tana rik'e da kugunta sai gwada musu yadda malam Sadeeq yake tsayuwar shi take yi taji Uwani halilu ta janyota tare da nuna mata k'ofar ajin tana hango su ta shige k'ark'ashin benci cikinta sai kululululu yake sabida ta san yauma ta shiga uku.

"Goody morning sirsss..!"

'Yan aji suka fad'a baki d'ayan su tare da mik'ewa tsaye. ciki suka shiga sosai Abubakar sai kallon su yake su kuma sun rasa gane waye malamin nasu a ciki. Sadeeq ya k'arasa wajan bencin da INdo ke k'ark'a shi yace.

"Ke! Tashi ki fito ko na mareki.."

Jikinta na rawa ta d'ago ai tana ganin still biyu take ganin shi sai ta koma tana ihu tare da cewa.

"Wayyo Allah na higa uku malam nayi min fatalwa, wallahi tallahi ban yi niyar yi ba amma Maryam Aliyu tace nayi zata bani naira biyar dan Allah malam kadenayi min fatalwa wallahi ba zan sake yi ba idan na k'ara ka...."

Bata k'arasa ba taji an janyo kafar ta sai ganinta tayi a gaban allo tana d'agowa still ta kuma ganin su biyu kawai a take ta sulale a wajan ta sume sabida tsabar kad'uwa da shiga cikin rud'ani.

Ko gezau Abubakar beyi ba bare yayi yinkurin yin temako sai kallonta kawai da yayi yana mamakin ganin hauka irin nata, da sauri Sadeeq ya girgizata yana kiran sunanta cikin tashin hankali kar yaje ta mutu ya shiga uku 'yan aji kuma sai suka fara kuka cewar INdo ta mutu.

"Aisha! Aisha!! Ke Aisha!!! Tashi mana me aka yi miki haka...?!"

Sadeeq ya fara kiran sunanta ganin duk ya rud'e yasa Abubakar k'arasawa wajan ya dafa shi sannan ya kalle shi a hankali cikin rashin sonyin maganar shi yace,

"Sorry my twins ba mutuwa tayi ba suma tayi da ansa mata ruwa zata farfad'o.."

Shaf Sadeeq mantawa yayi da cewar d'an uwanshi likita ne sai da Abubakar ya samo ruwan wata yarinya a jarka ya shafawa INdo sannan ta farfad'o yana jin sanda d'an uwan nashi ya sauke ajiyar zuciya mai k'arfen gaske na farin ciki.

Tana farfad'owa idanunta suka sauka a kansu da sauri tayi baya jikinta na rawa, ganin haka yasa Abubakar dama shine wanda baya d'aukar raini ya buga mata wata uwar tsawa tare da zare mata idanuwa tsit INdo tayi jikinta sai faman rawa yake.

"Ke..! Karna sake jin bakin ki yayi mana ihu, wawuya baki san ana haifar 'yan biyu ba? Ko kinga munyi miki kama da mayu ko aljanu..?!"

Cewar Abubakar wanda ke tsaye akan INdo, da sauri ta girgiza mai kai cikin tsananin tsoro sannan ya ce mata,

"Tashi kije ki zauna na san yanzu garau kike ba kya buk'atar wani hutu."

Da sauri ta mik'a ta wuce gurin zamanta, mik'ewa Sadeeq yayi ya koma kan kujera tare da janyo d'ayar ya nunawa Abubakar alamar ya zauna. kallon kujerar yayi sannan ya kallo inda yake hango INdo cikin yatsina fuska yace mata,

"Ke..! Zo nan."

Da sauri ta k'arasa tare da zubewa a gurin shi tace.

"Gani malam."

"Karki kuma kirana da malam kinji ko? Ni ba malamin Ku bane..!"

Baki na rawa INdo tace.

"Toh sir."

Had'e rai yayi tare da tsuke baki cikin takaici yace,

"Waye sir d'in?!"

INdo tace,

"Kai ne sir. ."

Hard'e k'afa yayi yana kallonta cikin b'acin rai yace,

"Stupid...! Ya sunan namijin saniya? ya ake kiran shi da hausa?!"

Cikin sauri ba tare da takawo komai a cikin zuciyar ta ba tace,

"Sunan shi sah."

Abubakar yace,

"Ahha kin ga nayi miki kama da shi?!"

Da sauri ta girgiza Kai alamar a'a tana mamakin wannan abu, toh me zata ce mishi tace malam yace baya so tace mai sir yace ta kirashi da sunan dabba toh ko sunan shi yake son ta fad'a ko tace mai baba amma ai be haifeta ba bare tace mai hakan.

Jan baya yayi kad'an tare da cewa,

"Zoki gogemin kujerar da zan zauna."

INdo ta mik'e tana mamakin toh yau malam sadeeq mugu ya zama kokuwa ba shi bane dan har lokacin bata  tantance waye malam Sadeeq ba cikin suba. kalle-kalle ta din ga yi ko zata samu wani kyallen da zata goge mai amma babu ganin haka yasa shi yin magana,

"Ke..! wai ba zaki yi aikin da na saki ba kin barni a tsaye fa."

"Mal.. Si.."

Ta rasa me zata ce mai kawai ta kalleshi tana turo baki dan ya gundire ta tace,

"Ai babu tsumma shi yasa."

Cikin rashin damuwa ya kalleta daga sama har k'asa ya tab'e baki sannan yace,

"Meye amfanin hijjabin jikinki ko d'ankwalin kanki su d'in ba tsumma bane?!"

Da sauri INdo ta kalleshi ya d'aga mata gira guda d'aya tayi saurin kallon Sadeeq dake zaune ga mamakin ta register ma yake bud'ewa ta kalli hijjab d'inta wanda duk ruwan kashu ya dafar dashi gashi wuyan ya yage tace mai.

"Ai hijjab d'ina ne bafa tsumma bane ba."

"Idan baki cire kin goge min na zauna ba ranki zai 6aci yanzun nan kinji na gaya miki."

Ya fad'a cikin tsawa wadda take a slow, ba yadda ta iya haka ta kama k'asan hijjab d'inta ta goge mai kujerar sannan ya zauna ita kuma ta koma wajan da malam Sadeeq d'in ya tanadar mata a gaba. Malam Sadeeq ya fara kiran sunaye sannan da ya gama yayi musu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login