Showing 123001 words to 126000 words out of 126031 words

Chapter 42 - Aalimah Complete 1,2,3,4 Free Book by Takori .txt

ba amma kisa a ranki duk a cikin son da suke miki ne. Fatan su da burinsu shine mu kasance tare, mu raini ‘ya’yan mu tare.
Me nake da shi a duniya da zan sakawa Aboulkhair wannan sacrifice din da yayi min? Wallahi babu. I love him to an extent. Ji nake idan zan yi ta haihuwar ‘ya’ya maza ina saka musu Aboulkhair yayi kadan ya nuna godiyata a gare shiâ€.
Haka suka karar da wunin yau bakidaya a gadon barcinsu, sallah kadai ke tada su. Abinci daga hotel din ake shigo musu dashi, Ilham ta ce zata aiko Mu’azzam ya ce ta bar shi. Baya son ko kuda ya gitta a tsakanin su. A shekaru bakwai da suka yi tare a baya, basu taba samun shaquwar da suka samu a kwanaki ukun nan da sukayi a Ontario ba. Soyayyar ta ninku, ta karu, ta rubanya. Basa ganin kowa a gabansu sai junansu.
Mu’azzam ya kira Madame Ruqayya mai rainon su Basma yace ta bashi Aboulkhair da Basma. Basma na karba ya mikawa Aalimah, sallama kawai Aalimah tayi Basma ta shaida ta, soyayyar uwa da Da sai Allah. Maimakon Basma tayi murna da jin mamarta kuka ta saki, tana fadin Mummy kin guje mu, kin barmu mu kadai a wajen Madame da Daddy, kin ki dawowa saboda kin daina sonmu.....â€.
“Basma uwa tana daina son dan ta? Wannan impossible ne. Baki San uzrina ba Bassy, I’ve a green great giant surprise gift for you. Tare da sabon Baby zan dawo, mace ko namiji wanne kika fi so?†Nan da nan Basma ta share hawaye ta saki dariya tana fadin “Allah Mummy? In dai da gaske kike to na daina fushi, dama duk ‘yan ajin mu suna da baby a gidan su banda ni, yaushe zaki dawo?â€
Aboulkhair ya kwace wayar daga hannun Basma, “Daddy your boy is missing you, yaushe zaka dawo?†Aalimah ta lumshe idon ta, soyayyar uwa da Da na ratsa ta. “Yaron na Daddy ne kadai ko? Ya manta da Mamansa?†Aboulkhair ya zabura, ya sake kankame wayar a hannunsa. “Mummy ke ce?†Nice Monsieur Aboulkhair, ina fatan ba ka yiwa Madame Ruqayyah rikici?†Shima sai yasa kuka yana fadin “mummy me muka yi miki kika tafi kika bar mu mu kadai? Ko a waya bakya kiran mu? Daddy kullum baya bacci sabida kin ki dawowa, don Allah Mummy ki dawo bana son zama da Madame Ruqayya ke da Daddy nake so....â€.
Ta kasa tsayar da hawayen da suka shimfido mata, ta kai yatsunta ta share su, tace “Aboulkhair it’s a promise nan da kwana biyu zaka ganni a Vegas tare da Daddy. Amma sai ka daina cewa baka son zama da Madame Ruqayyah, kaga bazata ji dadi ba tana iya kokarinta a kan kuâ€. Ya juya ya dubi matar ya yi mata murmushi ya ce “Madame sorry. My Mummy is coming back soonâ€.
Yau dai wayar ta uwar da ‘ya’yanta ce ko uban basu nema ba har suka kare hirar, wadda ake yin ta ana sharar hawaye da koke-koke. Mu’azzam yana daga gefe Aalimah ta yi matashi da gadon bayan sa duk yana jin su yana murmushi.
Ya karbi wayar daga hannunta ya kira Malam Razee, ita kuma ta shiga toilet don yin alwala. Tana jin su suna hira yana gaya masa ai yazo yayi biko gashi a hotel tare da Aalimah. Daga bayin Aalimah ta saki salati tana fadin “haba haba Ya Mu’az? Haba don Allah†Malam Razee yace “hotel kuma? A wane gari kuma?†Yace “wani kayataccen hotel ne a birnin Ontario, ita Ontario din cikin kasar Canada take, nan Aalimah tayi hijira gidan Baffanta na wajen uwa, a cewar ta tunda bakwa son taâ€.
Murmushi Malam Raazee yayi yana hamdala a fili da boye saida ya baiwa Mu’azzam tausayi. Ya tabbata har hawaye yake yi duk da baya ganinsa. Malam yace “ko yau mutuwa ta zo, burika sun gama cikka. Kowa dake cikin ‘ya’ya da jikoki na ya samu rayuwar da hankalina ya kwanta da ita. Ka rike ‘yar uwar ka amana Mu’azzam ku rufa asirin juna. Allah yayi muku albarka, ya albarkaci zuri’ar kuâ€.
7/13/21, 6:00 PM - Buhainat: Kafin kace meye wannan zance ya tadda su Inna Kasisi, Inna Bintou, gidan su kawu Oussama da gidan Daddy1. Aalimah da Mu'azzam sun koma har sun tafi yawon amarci. Zancen ya baiwa Gumsu dariya tace da wanda ya zo ya gaya musu “wane amarci da zungureren cikin?†Amma zuciyar ta kal kamar takarda.
Gumsu ta dau waya ta hau doka kira Nigeria, Basmah ta kira tace “kin ji wai yar tawayen can ta gaji da zaman gida ta koma gidan ta har an tafi honeymoon wata kasa, nace wane yawon amarci da zungureren ciki?†Basmah tace “kayyasa! Dadi na da gidan Malam Raazee karawa miya gishiri, wani lokacin har da onga, ba wani yawon amarci da suka tafi dama tana can shine ya bita†Gumsu tace “wai ba tana gidansu ba?†Basmah tace “tunda son kai ya rufe maku ido yaushe zaku damu da inda take? To masu sonta sun dauketa zuwa Canada ko wata daya bata rufa anan Kano baâ€. Gumsu ta ji duk kunya ta kama ta, tunda Aalimah ta bar Niamey bata kara neman ta ba balle ta tambayi lafiyar cikin jikin ta tace “don Allah ki bani lambar taâ€. Basmah tace “wallahi banni badawa, in da kunya ai baza ki nemeta ba yanzu data dawo gidan Dan ki. Watanni sama da hudu baki kirata ba ko don jin lafiyar abinda ke cikinta sai yanzu data yarda ta koma gidan dan ki? Wannan son kai a fili da me yayi kama!â€.
Gumsu tace “ki yarda dani Basmah ba son kai bane ba, tausayin Mu’azzam da yaran nake ji. Yanzu data yarda ta koma baki ji dadin dana ji ba, ba shikenan komai ya wuce ba?†Basmah tace “to shi da kike jin tausayi baya tausayin kansa, da yana tausayin kansa da ya dade da neman sulhuâ€. Sai da Gumsu ta kafa naci sannan Basmah ta hakura ta bata lamabar Aalimah ta Ontario.
Sanda Gumsu ta kirata Mu’azzam take wa cumbing kanshi ya fito daga wanka. Don haka bata daga ba sai da ta gama, ta kuma taimaka masa ya gama shiryawa, Mus’ab ne zai zo ya daukesu zuwa gidan Uncle suyi sallama ta hada kayanta don gobe jirgin asubah zasu bi zuwa U.S. Gumsu bata fasa kira akai-akai ba har Mu’azzam ya gaji yace ta daga wayar nan. Tana dagawa taji Gumsu. Ajiyar zuciya tayi tace “ko dai wrong number ne?†Gumsu da borin kunyar ta tayi ta bata hakuri tana gaya mata abinda take hange na barinta gaban ‘ya’yanta tunda in ta ki Mu’azzam ta ki Aboulkhair karshenta dole wani daban zata aura ta bar yaran cikin maraici ita abinda bata so kenan tayi hakuri ta fahimceta ta daina kullatar kowa akan haka, soyayyar da suke yi mata ne ya janyo hakanâ€. Mu'azzam ya gaji da jiran Aalimah su fita yace da hannu wacece ne? A hankali ta motsa labbanta tace masa “Gumsu-Moiram†murmushi yayi ya karbi wayar yace “inason fita da iyali na, ko za’a bar wayar sai mun dawo?â€
Gumsu ta shaqa tace “ina can ina maka kamfen, har gaba na kulla sabida kai, kana nan kana min kora da hali ko?â€
Yace “to ai ni ban sa ki ba, dadi na dake sa-kai a uku babu gaira babu daliliâ€. Aalimah bata san sanda ta saki dariya ba, in Mu’azzam ya san yadda Gumsu ta damu da al’amarinsa da bai yi mata haka ba. Ta karbi wayar tace mata ta hakura, sannan ta barsu suka fita.
Sunyi kwalliya ta alfarma cikin shigar mutanen Nijar dukkansu. Mus’ab na tuki suna baya. Ya dan juyo ya dubi Aalimah yace “we’re gonna miss you so much Adda, kwana ukun nan da baki gidan baki ji yadda gidan ya koma boring ba kowa baya walwala musamman Maryamâ€. Murmushi tayi tace “nima zanyi kewar ku, yadda halshe bazai iya bayyanawa ba, duka gidan I enjoyed your company so muchâ€. Mu’azzam yana jin su bai ce musu komai ba.
Daidai lokacin da suka iso gidan, duk mutanen gidan suka tarar a falo. Kowa yayi jigum kamar wadanda aka yiwa mutuwa. Aalimah na shigowa Maryam ta nufe ta ta rungume tana kuka tana rokonta kada ta tafi. Daddy yace “yau naji ikon Allah in da za’a ce kada mace ta je gidan miji, kema kwana nawa zakiyi a gidan da zaki hanata zuwa nata? Kuma wai don rashin kunya a gaban mijin ta?†Su Taufeeqah suka hau dariyar Maryam, Mu’azzam yace “Maryam duk sanda kike son ganin Adda zan miki visa kije Las Vegas. I promisedâ€. Ai nan da nan Maryam ta saki Aalimah ta hau tsalle.
Anan suka ci abincin dare suka nitsa hira har saida yaran suka yi barci, Anty da kanta ta hadawa Aalimah kayanta tsab, Mus’ab ya sanya a mota. Anan suka karar da rabin daren, sai da zasu tafi Anty ta fiddo sayayyar data yi mata na kayan jarirai unisex cikin katuwar jakka, dana su Basmah suma kowa ya samu jaka guda. Daddy kuwa kudi ya zuba mata cikin account din da ya dade da bude mata tun zuwanta kamar sauran ‘ya’yansa, duk wata yana saka musu kudi don bukatocinsu, yace in tana so ta kwashe ta mayar U.S account din ta ta rufe account din in kuma zata bar shi to, Aalimah sai hawaye, ta rasa bakin godiya, tace bayan dawainiyar da suka sha da ita wata da watanni, kuma har da karin wannan dawainiyar. Uncle Suraj Kashim yace “akul! Ta sake kira masa dawainiya, dole ne yayiwa Asseya da ‘ya’yan ta dawainiyar don bata da kowa sai shiâ€. Da haka suka yi sallama Aalimah na ta kuka. Don ji take kamar wannan shine lokaci na farko da zata je gidan miji.
Basu samu sunyi barci ba don suna shigowa lokacin sallar asubah na yi. Sallah suka yi daga nan suka kimtsa. Chauffeur na hotel din shi ya kaisu filin jirgi tare da kayan su.
******
A cikin jirgi Aalimah ta kwantar da kai a kafadun Mu’azzam, rayuwarta bakidaya ta dinga gilma mata tamkar a majigi. Ta faro ne daga zuwanta Boston, inda daga nan tarihin rayuwar ta ya fara, rayuwarta gidansu Mu’azazam, haduwar ta da Aboulkhair, aurensu har zuwa rabuwar su. Aurenta da Mu’azazam da irin kalubalen data fuskanta a cikin auren, haihuwarsu zuwa rabuwarsu da kuma kalubalen data fuskanta a cikin rabuwar. Har kuma zuwa yau da Ubangiji ya sake binding dinsu together. Hakan kadai ya ishi bawa ya yarda Ubangiji Subhana mai yawan hikima ne, komai yayi kada bawa yasanya ayar tambaya. Duk abinda ya tsara ya san dalilin yinsa. Data yi hakuri da kaddarar auren Mu’azzam yau gashi ta ci ribar hakurin ta. Ubangiji ya san cewa Mu’azzam shine mafi alkhairi gareta akan Aboulkhair shiyasa ya canza rayuwar su ta fuskar da ya ga dama. Hakurin data yi a zama da Mu’azzam bai tashi a banza ba. Hakika kowa ya bi iyayensa ya kuma fawwala al’amarinsa ga Allah zai iya masa.
The fact that ana son juna kamar a hadiye juna baya hana rabuwa a wa’adin da Allah ya tsara, ko ba’a mutu ba rayuwa tafe take da kaddarori kala-kala masu sabbaba rabuwar. Kuma karfin soyayya baya hana karewar aure a wa’adin da Ubangiji ya nufa. Wannan shine ya faru tsakanin ta da Aboulkhair wanda har abada bazata manta ba a karkashin zuciyar ta. Abu guda take da tabbacinsa; daga ranar da ta soma son Mu’azzam a matsayinsa na mijinta, daga ranar da ta zama sirrin Mu’azzam ya zama sirrinta, gabadaya rayuwar data yi da Aboulkhair ta zama shudadden al’amarin da bata sake tunawa da wani feeling ba. Aboulkhair ya rikide ya juye ya koma kamar Yaya Aboubacar a idanunta.


******

Kada kaso kallon soyayyar data afku tsakanin Aalimah da Mu’azzam da yaransu a filin sauka da tashin jirage na garin Nevada (Las Vegas) a wannan rana, wadanda Harrison ya debo ya taho dasu don su tarbi iyayen nasu. It was so emotional da har ya fiddo hawaye daga idanun Aalimah. Kwannaki suka cigaba da juyewa zuwa satittika har Aalimah ta shiga watan haihuwar ta.
A wadannan satittikan numfashi ne kawai Mu’azzam baya yiwa Aalimah sabida tattali da soyayya. Idan ofis ya tafi hankalinsa yana kansu, Allah-Allah yake ya dawo gida ya tadda su, idan yana gida lokutansa nata ne. Har Allah ya nufi Aalimah da haihuwa lafiya ta haifi da namiji tamkar Mu’azzam yayi kakhi ya tofar.
Wannan karon rigima ta barke tsakanin matar da mijin kan sunan da za’a sanyawa yaron, Mu’azzam yace wancan lokacin ya bata dama ta sa Basmah wannan karon ta bar masa Malam Raazee zai sa, ita kuma ta dage Daddy 1 (Ishaq) za’a sanya, bazata taba manta gudummuwar sa da soyayyar sa cikin rayuwarta ba, cikin halin dadi ko sauyin rayuwar da suka samu kansu. Rigima kafin ranar suna tsakaninsu ta ki karewa har kunnen Daddy 2. Ba da wata-wata ba ya bi bayan Mu’azzam yace ta bari asa tsohonsu, shekara mai zuwa war haka tasa himma ta sake haifowa sai asa mata Ishaq din. Tsohon mu mai ran karfe ki bari mu samu magajinsa. Aalimah tayi narai-narai da ido kamar zata yi kuka tace “Daddy, abinda yasa nace asa Daddy 1 sabida Khaleesat ta saka Malam recently ko wata biyu ba’a yi ba†Daddy yace “Malam Raazee ai baya isar mu, ya kamata a ce dukkan ku ya kasance cikin ‘ya’yan ku da Malam Raazee, na Khaleesat daban naki dabanâ€. Aalimah ta sakar masu don sun fita gaskiya.


Ranar suna Mu’azzam ya yiwa jaririnsa khutbah da suna Ibrahim (Sarham). Lokacin da ya kira Malam Raazee ya gaya masa baya jin dadi, jikin girma ya motsa masa, a kwance yake amma don farin ciki cewa yayi wannan karon sai ya taka kafafunsa gidan Mu’azzam har kasar Amurka.
Shi da Oncle Oussama da Eidrissa Mu’azzam ya yi wa visa zuwa U.S. Duk da tsufa da karancin koshin lafiya yace sai yaje gidan Mu’azzam koda sau daya ne a rayuwar sa. Mu’azzam din kuma ya kudurce a ransa zai yi amfani da damar a duba masa lafiyar Malam din sosai. Mummy, Gumsu, Daddy 1 da Daddy 2, Mama Aseeya, Hamoud da matarsa Khaleesat, Aboubacar da matarsa Basmah duk haka suka dunguma zuwa birnin Las Vegas. In da suka tarar da Dr. Aboulkhair da iyalin sa (Sa’eedah da danta Abu Turab) suma sun zo daga Boston don halartar sunan Sarham.


Aalimah ta kasa tsaye ta kasa zaune da shirin tarbar iyaye da ‘yan uwansu, wadanda za su zo takanas don taya su murnar alherin da ya same su na karin girman da Mu’azzam ya samu a CHEVRON da kuma haihuwar magajin Malam wato Sarham. Ita da Aunty Sa’eedah ke ta wannan shirye-shiryen tun gabanin zuwan bakin nasu da kwanaki uku. Kafin bakin su iso hatta cokalin da za su ci abinci sun tanada. Sun yi time-table na girke-girken da zasu ke musu a kullum a tsayin kwana bakwai da za su yi tare da su. Sun tsara za su rike matan a nan gidan Mu’azzam tunda yana da girma, Malam Raazee ma a gidan zai zauna, sun gyare masa daki a downstairs kada ya sha wahalar hawa bene, maza kuma tuni Mu’azzam ya kama musu hotel din da za su sauka.
A ranar da za su iso, bakidaya iyalin Mu’azzam dana Aboulkhair suka dunguma filin jirgin saman (John F. Kennedy) suka tarbo su zuwa gida.
Mummy Zulaiha don farin ciki tana arba da Mu’azzam da Aboulkhair tsaye a tare, sun juya baya suna magana da junansu, ta tuno lokutan data kwashe cikin kukan zuci dana fili, na tunanin Aboulkhair ya bar su kenan har abada, da lalurar Mu’azzam da bata taba barin ta kwanciyar hankali ba tsayin shekaru masu yawa, hakan kadai ya ishi bawa ya kara imani, ya tsoraci Allah, mutuwa ba karya bace, tana iya zuwa a kowanne lokaci babu notice, bazamu taba guje mata ba, sai in lokaci bai yi ba, haka rashin lafiya duk arzikin ka da gatan ka sai idan Ubangiji ya ga damar yaye maka a lokacin da ya so. Ji kawai suka yi Mummy ta rungume su ta baya su duka biyun ta saki kuka mai sauti tana hamdala a fili. Dukkan su sai suka sanyata a tsakiyar su suka rungumeta suna lallashin ta.
Ko da suka iso gida hira ce ta yaushe gamo ta tsinke a tsakanin wannan family don daga Aboulkhair har Mu’azzam da iyalinsu sun kwashi lokaci ba su je gida ba. Gumsu nata aikin nata na bada dariya, ba ruwanta da surukai ko Kakanni, komai ya zo bakin ta fade take.
Aalimah da Sa’eedah suka hade da su Basma da Khaleesat, Yesmin da karamarsu Nurat suka yi ta dawainiya da iyayensu da Kakansu. Kowaccen su ta aje iyali abin gwanin ban sha’awa. Yau Basma da Aalimah da Khaleesat har rayuwar Boston sai da aka tabo aka dara cikin nishadi.


Masha Allahu laquwwata illa billah.
Karshen littafin AALIMAH kenan.
Kuskuren da ke ciki ku taya ni rokon Allah ya yafe mini. Alherin da ke ciki, Allah ya raba mana ladarsa ni da ku bakidaya.
Taku har abada; Sumayyah Abdulkadir.
TAKORI


Karin Bayani
Na samu fatawar malamai mabanbanta akan makomar auren Aalimah da Mu’azzam, bayan bayyanar Aboulkhair, fahimta fuska, wasu malaman sun ce miji na farko shi ke da mata amma wannan fatawar ta tsaya ne akan shekaru hudu da bacewar mijin bai bayyana ba, kuma babu iddar mutuwa, Abulkhair sai bayan shekaru bakwai ya bayyana, sannan da iddar mutuwa, don haka nayi amfani da mafi rinjayen fatawar malamai wadda tace miji na biyu keda mata, ko a bata zabi ita matar, ta zabi wanda take son cigaba da zama da shi a tsakanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login