Showing 117001 words to 120000 words out of 126031 words

Chapter 40 - Aalimah Complete 1,2,3,4 Free Book by Takori .txt

ce ta fadowa rayuwar ‘ya’yanta haka! Aboulkhair kuma ya sunkuyar da kansa, hawaye na tsirgowa daga cikin idanunsa, cike da nadamar dawowar sa cikinsu.
Da ya san abinda zai tarar kenan, da abinda dawowar sa zata haifar a rayuwar Mu’azzam, da ko kusa bai yi gigin dawowa ba.
Da ya karasa rayuwarsa can inda yake, a matsayin matacce a garesu.
Bai so ya zamo barrier ga farin cikin rayuwar Mu’azzam ba!.
Bai so dawowarsa ta rusa kyakkyawar rayuwar Mu’azzam da iyalin sa ba!!
Ya yarda rabuwarsa da Aalimah a yanzu, daidai yake da maida hannun agogo baya!!!
Haka suka koma gida kowa jiki a mace. Kowa ka gani gidan Malam Raazee a wannan rana sai ka fahimci akwai babban al’amarin da ya taba zuciyarsa.
Walwalarsu ta ragu, kuzarinsu ya ragu, kowa jikinsa a sanyaye.
Amma Oncle Mainasara ya ji dadin wannan lamari. Ya tabbata wannan karon Dan sa Anas zai samu abinda ya dade yana so. Tsuntsu ne ya fado daga sama gasashshe.


A daren ranar Mu’azzam yayi booking zai tashi U.S a safiyar washegari tare da ‘ya’yansa.
Ko a fuska bai canzawa Aboulkhair ba, Aboulkhair din ne ya kasance cikin damuwar da har ta kai shi ga kuka akan cinyar Mu’azzam. Ba kukan Aalimah bata zabi zama da shi yake yi ba, kukan zamowar sa silar rugurgujewar farin cikin rayuwar Mu’azzam ne.
A ganinsa Mu’azzam bai cancanci haka daga gareshi ba. Me yasa ya kasa sadaukar masa da Aalimah tun a tashin farko?
Gashi yanzu an bata goma daya bata gyaru ba.
Ji yayi soyayyar Aaliman tana yin wani irin fiffike tana ficewa!!!
Domin Mu’azzam ya cancanci ya bashi rayuwarsa dungurungum in ana badawa.


Bai gayawa Aboulkhair yayi booking ba ganin halin damuwar da yake ciki ya kuma kasa tsaida hawayen idanunsa tun dawowar su daga kotu kada ya kara masa damuwa.
Baya so ya kara raunana shi.


Amma dole da asubahin ranar bayan sun dawo masallaci ya gaya masa zai tashi Las Vegas da karfe goma na safe, yana bashi shawara idan ya kara hutawa ya gaggauta zuwa ya taho da matarsa Sa’eedah.
Hankalin Aboulkhair ya kara tashi, shi ya manta da Sa’eedah. Fargabar halin da Mu’azzam zai fada in ya koma gida shi kadai da kananan yara ya addabi zuciyar sa. Ko bai fada ba Mu’azzam ya ga hakan a kwayar idonsa.


Murmushi yayi ya dafa kafadunsa da hannayensa biyu yace “Aboulkhair relax, Mu’azzam din daka sani a baya bafa shine yanzu ba. Akwai improvement mai tarin yawa a lafiyarsa ta yanzu. I promised you i will be safe, kuma ga su Basma zasu debe min kewa I will not be aloneâ€.
Ya tsugunna a gabansa ya dora tafin hannunsa bisa tafin kafar kanin nasa.
“Ina neman gafarar ka, for all the inconveniences!!!â€.
Aboulkhair couldn’t keep it, banda ya rungume Mu’azzam da karfi ya saki kuka. A lokacin shima ya soma neman gafararsa, ya gaya masa yayi nadamar dawowa, da ya san abinda dawowarsa zata janyo kenan da ko kusa bai yi ta ba.
Da sauri Mu’azzam ya toshe masa baki yace “Ka isa ka kankare abinda Allah ya rubuta ne Aboulkhair? Bana son wannan maganar kar ka sake yin irin ta. Dawowar ka ta fiye min mata dari a doron duniya. Zan iya sake Aalimah amma kai bazan iya taba sake ka ba. Allah ya riga ya rubuta karshen zaman mu kenan. Wani wayo ko dabara ko dana sani bai isa ya kankare wannan kaddarar ba.
Ina mai kara gaya maka Zan iya sake Aalimah, amma kai bazan taba sake ka ba. Kai na yiwa laifi Aboulkhair dana biyewa zuciyata ta fada cikin soyayyar macen dana san ka tafi ka bari ne ba don ka daina so ba! Ka yarda dani a baya nayi duk kokarin da zan yi kada sabo ya shiga tsakanin mu, all my efforts was futile sabida nagartattun halayenta. But i trust myself now. I can manage a life without Aalimah. After all ta bani mafi darajar abinda zai debe min kewarta; ‘ya’ya har guda biyu a lokaci dayaâ€.
Yayi Murmushi mai taushi “so ka daina damuwa, ka bar ni in tafi sabida ofis da makarantar yara, insha Allah ba abinda zai faru damu sai alkhairi. Aalimah will soon come and regret her judgement ni kuma zan bata mamaki, na gama zama da ita kenan insha.....â€.
“.... Please Mu’az.....daina fadin haka, har zuwa abubuwan su lafa a zuciyar ta. Tension ne kawai ke damun ta ba wani abu ba. I’m sure da sannu zata huce, kuma komai zai koma daidai. Tunda da kanta tace ta zabi cigaba da zama da kai sabida ‘ya’yan dake tsakaninku, haka kuma sabida su ne zata huce bada jimawa ba. Alhmdulillah da ka yi amfani da hankali da tunanin ka wajen yin sakin da muslunci ke so.
Ni yanzu kallon Basma da Khaleesat nake yiwa Aalimah! Wallahi komai da ya dangance ce ta ya shafe daga kaina da zuciyata. Ni na jawo komai kuma ni zan gyara da yardar UBANGIJI, don Allah kada kayi fushi da itaâ€.
Mu’azzam ya hau girgiza kai. Ya dafa kafadar Aboulkhair, kana iya karantar kwantaccen bacin rai cikin kyawawan idanun sa. Abinda Aalimah tayi a court ya bata masa rai sosai, akalla in shi ta ki shi, to ta tuna kananan ‘ya’yan ta da za ta mayar marayun dole at a tender age. Cikin kaushin murya yace da Aboulkhair.
“For now, ka bar zancen Aalimah a tsakanin mu. Mu fuskanci muhimman abubuwan dake gaban mu, yadda zaka koma aikin ka, garin da zaka zabi zama da hijirar iyalinka. Aboulkhair dole ka baro Jeddah you don’t have a life there. You are a medical consultant not a shepherd (baka da rayuwa a can, kai likita ne mai matsayin consultatant ba makiyayi ba). Yanzu kokarin da zan yi dana koma shine na nemo takardunka dana ke ta boye dasu, na nema maka aiki a garin da ka zabi zamaâ€.
Kawai sai Aboulkhair ya fashe da kuka, ya sake rungume Mu’azzam yana mai jin Aalimah da komai nata na kara yin wani irin NESA cikin dubban kilometres daga zuciyarsa… ji yake ko ita kadai ta saura ‘ya mace a duniya daga yau ya haramtawa kansa ita, ya barwa Mu’azzam iyalinsa. Haka Allah ya rubuta musu cewa zai fara aurenta, amma uwar ‘ya’yan Mu’azzam ce. Wannan itace rubutacciyar kaddararsu. Zai yi duk kokarin da zai iya na ganin cewa ta koma gaban ‘ya’yanta.


Da gari ya yi haske bayan sun yi wanka sun shirya tare suka tafi gidan Daddy don yin sallama dashi da Mummy, bai fada musu tun jiya ba cewa yau zai koma kada su dakatar da shi, ba ya jin akwai abinda zai yarda ya hana shi tafiyar nan tareda ‘ya’yan sa a yau ba sai gobe ba, don ita ce kadai kwanciyar hankalinsa, kamar yadda Aalimah tace rabuwa dashi shine kwanciyar hankalin ta. Zai nesanta kansa da ita, nesantawa da babu ranar waiwaye don ta samu kwanciyar hankalin da ta ke hangowa.
Ya saya kwayan idanunsa cikin bakin PRADA mai duhu ainun. Shadda ce fara kal (getzner) a jikin sa dinkin tazarce. Kasancewar ba kasafai yake irin wannan dressing din ba sai ya fito kala daban a yau. Hakika kalar mamansa ‘yar asalin kasar Nigeria yau ta nuna sosai a jikin sa. Ko turare bai iya ya fesa ba sabida yadda yake sauri ya bar kasar Niger, amma kamshin sa ya riga ya kama komai nasa.
Sanda suka shigo Daddy da matan sa guda biyu da Yesmin tare da yaran Gumsu hudu Nurat da kannenta su Ikhram suna karin kumallo. Daddy ya bisu da kallo suna shigowa, wani farin cikin sake ganin su a tare ya tsirga masa. Yayi godiya ga mahaliccinsa mai yawan hikima da kyautayi ga bayin Sa. Murmushi yayi yana ja musu kujera akan dining din. Har kasa suka tsugunna suka gaida iyayensu sannan suka zauna a kujerar da Daddy yayi musu tayi aka cigaba da karin kumallon tare da su. Gumsu ta daina surutu, ta yarda yanzu babu muhallin yinsa. Sosai ta kame bakinta.
Suna gamawa Mu’azzam yake gaya musu sallama yazo musu zai wuce yanzu sabida ofis, kuma tare da su Basma zai tafi. Mummy ta zaro ido tace “ka bar min su mana Mu’azzam yaya zaka yi da kananan yara har biyu?†Babu kunya Mu’azzam yace ai babu matsala zai iya kula dasu. Tare zasu dinga fita ya saukesu makaranta ya wuce ofis, sanda yake tasowa suke tashi suma, kuma zai daukar musu dattijuwa mai raino musulma.
Mummy zata sake magana Daddy ya tare ta yace “Allah ya tsare, ya kiyaye ku, yayi muku albarkaâ€. Ya mikawa Aboulkhair mukullin motarsa yace ya kai su filin jirgi. Ya kara da duban Aboulkhair sosai wani abu ya fado masa, da sauri yace “drive with care. Fasten your belt. Da bismillah da ayatul kursiyyu kafa bakwai kafin tukin motaâ€. Aboulkhair ya amsa, tare da cewa “insha Allahuâ€.
Gumsu dakinta ta shige hawaye na zubo mata na tausayin Mu’azzam. Haushin Aalimah ya cika ta, har cewa tayi a ranta ba ita ba Aalimah insha Allahu. Tunda bata da tausayi ko kankani, kanta kawai ta sani da maslahar kanta. In bata tausayawa Mu’azzam ba, ai ta ji tausayin kananan yaranta.
Gidan Malam Razee suka koma, shine yaso batawa Mu’azzam lokaci don cewa yayi sam bai yarda ya tafi ba, ya zauna har Aalimah ta huce a maida aurensu su koma tare. Abinda Mu’azzam bai taba yi masa ba yau yayi masa wato gardama. Nan ya gane da gaske yake tafiyar yake so kuma ya yi fushi da Aalimah fushi mai tsanani. Aboulkhair shi ya ciwo kan Kakan nasu da kyar ya hakura ya yarjewa Mu’azzam tafiyar. Don ya gaya masa (a matsayin sa na likita) Mu’azzam is okay. He can handle himself.


Aalimah bata jima da tashi daga barci ba suna karyawa da yaranta a falon Inna Bintou ta tsinkayi sallamar Mu’azzam a tsakar kanta. Sallamar data ratsa har cikin kashi da bargon ta. Wuta ta dauke mata na lokaci mai tsawo domin sosai muryar ta ratsa cikin kunnuwa da jijiyoyinta. Su Basma suka dangwarar mata da kofin shayin ta har ya bare a jikinta, basu bi ta kanta ba suka kwasa da gudu sai wurin mahaifinsu. Rage tsaho yayi ya bude musu hannuwa suka shige ciki yana sumbatarsu daya bayan daya, ba tare da bata lokaci ba yace.
“Oya! Kowa ya dauko jakar kayansa tafiya zamuyiâ€.
Nan da nan suka hau tsalle suka runtuma daki da gudu sai ga kowanne rike da takalminsa a hannu, janye da trolley din kayansa. Basma tace “Mummy ki tashi ki dauko kayan ki†Mu’azzam yace “No Bassy, Mummy will stay at home, tana da abun yiâ€. Ya hau saka musu takalmansu. Tana zaune kamar an dasa ta tana kallon ikon Allah. Zuciyar ta na wani irin raurawa. Ya iso har gabanta ya ajiye mata passport dinta bisa cinyar ta. Ya kama hannun ‘ya’yansa yaja jakunkunan suka fice. Inna Bintou nata yi musu addu’a yana amsawa suka fice daga dakin.
Aalimah ta rasa abun da zata yi a wannan lokacin, kawai sai ta dora hannayenta biyu aka ta rushe da wani irin kakkarfan kuka, ta yaya zai zo har gabanta ya kwashe mata ‘ya’ya? Zuwa wata uwa duniyar da babu mai kula dasu???
Inna Bintou yi tayi kamar bata san da ita a dakin ba ta dau mayafi ta yafa ta fice don yiwa ‘yan biyu rakiya bakin mota.


Aalimah ta san ba mai kula ta ko kukan jini zata yi, haka ta tattara ta shige uwar daka, duniyar bakidaya tayi mata zafi. Ta rasa inda zata tsoma ranta ta ji sanyi. ‘ya’yanta sanyin idaniyarta, ‘yan biyun ta abin farin cikin ta, wadanda bata iya barci batare da ta jisu cikin jikinta ba.
Haka ta ci kukan ta ta koshi, wanda ya haddasa mata ciwon kai mai tsanani, ko sannu bata samu daga jama’ar gidan ba. Nasu mai sauki ne akan na Inna Kasisi, wadda ko gaisuwarta bata amsawa yanzu.
7/12/21, 4:49 PM - Buhainat: Inna Bintou ta zubowa jikanyar ta Hafsu shinkafa da miya ta shi go dakin da shi, Hafsu kai tsaye ta nufi Aalimah da abincin nan tana fadin ta sakko su ci. Warin miyar wadda taji tafarnuwa ya bigi hancin Aalimah. Wani bala’i ya ziyarceta kafin ta yunkura ta zauna ta kwararo wani uban amai wanda ya wanke Hafsu da shinkafar ta, ta cigaba da sheko shi kamar zata amayar da kayan cikin ta.
Da gudu Hafsu ta fita ta kira Inna Bintou. Wai Aunty Aalimah tana amai. Bintou da Kasisi dake madafi suka yi kasake! Suna kallon yarinyar tana digar amai kafin su juya su kalli juna. “Amai dai?†suka hada baki wurin tambayar ta. Daga bisani Bintou ta yunkura tabi bayan yarinyar zuwa dakin nata.
Ita ta taimaka mata ta wanke jikin ta, ta kuma gyara wajen ta kunna fanka da turaren wuta. Tun daga ranar Aalimah ta kwanta jinya, komai taci sai ya dawo, ta kuma ki yarda a kaita asibiti, kuka ma ta sakawa Inna Bintou ita Kano zata koma. Inna taje ta fadawa Malam halin da Aalimah ke ciki da Kano da take son komawa. Ta kuma ce tana zargin Aalimah karamin ciki gareta.
Malam yace zai turo Aboulkhair ya dubata, zai kuma sa shi ya saya mata tikitin tafiya Kanon.
Bayan fitar Bintou Malam Raazèe ya fada a tunani, wato hikimomin Ubangiji yawa gare su. Zuri’a tsakanin Aalimah da Mu’azzam ashe bata kare ba. Duk yadda Ubangiji ya shirya al’amarinsa dole bawa ya karba yayi imani. Idan Allah ya rubuta akwai sauran zama a tsakaninsu Aalimah bata da tsimi bata da dabara. Ga auren da kakar sa ke nema masa. Wanda shi sam hankalinsa bai kwanta da shi ba, don yana tsoron abinda ka je yazo, tunda Mu’azzam ba wai warkewa yayi daga lalurorinsa ba, su kadai suka san yadda suke zaune da junansu.
Aboulkhair Malam ya kira a waya yace yazo ya duba masa Aalimah bata da lafiya, ya sayo abinda yasan mara lafiya zai iya ci ya kawo mata kumallo take yi kullum. Abinci baya zama a cikin ta.
Shi da Yesmin suka zo gidan, Yesmin niki-niki da ledojin sayayyar da suka yo mata a supermarket. Dakin Inna Kasisi suka fara shiga suka gaisa, yace.
“Inna Aalimah muka zo dibawaâ€.
A take far’ar fuskarta ta canza tace.
“Kun bani ajiyarta ne?â€
Ko kadan Aboulkhair bai ji dadin abinda ya fahimta daga Kakar su akan Aalimah ba, ya san kuma abinda ya janyo hakan, zama yayi ya soma yiwa Inna nasiha yana gaya mata Aalimah bata isa ta tsarawa kanta rayuwa ba face abinda Ubangijin ta ya tsara mata, idan Allah yace iyakar zamanta da Mu’azzam kenan fushinta da ita bazai canza komai ba, da ita da Mu’azzam duka jikokinta ne, nunawa daya soyayya akan daya ko bin bayan daya ba nata bane. Yana rokonta ta zamo mai adalci a tsakanin su.
Inna Kasisi bata ce komai ba amma jikinta yayi sanyi ainun. Mamakin juriyar Aboulkhair ya kamata, kamar ba shine wannan da ada ake tunanin bazai iya rayuwa ba sai da Aalimah. Ta san kuma ba komai ya sa shi sadaukar da sayayyar ba sai kaunarsa ga Mu’azzam. Tana mai addu’ar Allah yasa wannan zumuncin nasu ya zame musu silar shiga aljannah.
Ta dubi Yesmin tace “to wadannan uban kayyayakin da kuka kwaso kuma na menene?†Yesmin tace “kayan dubiya ne†tace “to a sammin nawa†Yesmin tayi dariya tace “sai in zaki taso muje dubiyar tare†Inna tace “albarkacin kaza ai kadangare na shan ruwan kasko, muje mu ganta, koda dai ciwon nata ai ba mai warkewa bane sai ranar da ya bushi iskaâ€.
Aboulkhair ya fiddo ‘fresh milk’ mai sanyi daga cikin kayan ya dauki tambulan ya cika shi taf ya mikawa Inna yana murmushin jin abinda ta fada. Duk da bai gane hausar sosai ba. Ta karba tana sha tace “amman wannan madara da gardi take, gara ma ku bar min don bazata zauna a cikin ta baâ€. Saida Inna ta gama shan madara tana santi, Aboulkhair na kara cika mata kofi, duk don ya lallashe ta taje ta duba Aalimah.
Saida ta sha ta koshi, tana yi tana binkito masa tsofaffin laifuffukan Aalimah a gareta tun fara maganar auren ta da Mu’azzam da irin kiyayyar data nunawa auren, tace ta san dole aka yi mata zama da Mu’azzam, amma tunda ga zuri’a a tsakani shi kuma data kwallafawa rai yayi aurensa tun kan ya dawo don me bazata hakura ba? Ai ga aya nan Allah ya nuna mata haihuwa da Mu’azzam yanzu ta fara.
Da sauri Aboulkhair ya daga kai ya dubi Inna yana son gane me take nufi, amma bata kara cewa komai ba tace su wuce su je tana dakin Bintou.


Aalimah na kwance bisa doguwar kujerar falon Inna Bintou, duk ta dashe tayi fari fat. Ta rame ta fita hayyacinta, idonta na fuskantar kofa sanda Aboulkhair ya sawo kai, Yesmin biye da shi da katuwar leda, sai Inna Kasisi karshen shigowa. Mamakin ganin Inna ya kasa boyuwa a idanunta. Kallo daya Inna Kasisi tayi mata ta tabbatar da zargin da suke mata. Aboulkhair tsintsiyar hannunta ya kama na wasu ‘yan mintuna ya kuma gwale idonta sannan ya taba temperature na wuyanta. Yace “tun yaushe ne kika fara vomiting din?†Ta rufe idanunta a hankali tace “last week†yace “banda aman sai me kuma?†Ta dan cuno baki tana kunkuni ita an dame ta. Haushi ya kama Inna tace “zaki bude baki kiyi magana ko ya tafi ya barki da ciwon ki?†Ta zumburo baki kafin tace “ciwon kai da zazzabin dareâ€. Aboulkhair ya dan kura mata ido kafin yace “when last kika ga period dinki?â€.
Zaro ido tayi tana masa kallon tsoro da razana. Ita ta san rabonta da period tun a Las Vegas, bata taba damuwa ba sabida dama ta kanyi tsallaken wata, amma yanzu daya yi mata wannan tambayar sai taji damuwar duniya ta rufto mata. Shiru tayi ta kasa cewa komai. Sai zuciyarta dake ta kai kawo a allon kirjinta tana son fitowa ta bakinta sabida tsabar kidima. Ta zazzaro ido kawai tana kallonsa.
Murmushi yayi mata ya zauna sosai a gaban ta. Kayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login