Showing 57001 words to 60000 words out of 126031 words

Chapter 20 - Aalimah Complete 1,2,3,4 Free Book by Takori .txt

kan Aalimah? Da ma ana ci wa ‘ya mace alwashi a hana ta aure ne?â€
Nan Daddy Ishaq ya warware musu komai kan ba shi ya dauki nauyin karatun Aalimah ba. Ya gaya musu duk abin da ya wakana.
Dr. Mansour Raazee ya dubi yayansa kamar zai yi kuka, “Ba ka kyauta min ba Yaya! Shekaru biyar Aboulkhair na dakon soyayyar Aalimah bayan kai kanka mai daura mata aure ne. Aseeya ke son karatun nan ba ni ba, kuma ita ma in ta san Aboulkhair ne zai auri Aalimah ba za ta hana ba. Shekara biyar Yaya? Ban ji dadi ba ko kadan. A kalla da ka gaya mini ko shawara ce mu yi,. Idan har yanzu Aboulkhair na son Aalimah bai canja shawara ba sabida nisan shekarun da aka sanya shi jira, na ba shi ita duniya da lahira, kuma ban da sadaki ban dora masa komai ba. Sadakin ma in an amince min, zan biya masaâ€.
Uncle Oussama ya ce, “To ba a amince maka din ba. Shi zai biya ni daga aljihunsa. Aboubacar da Basma fa? Me suke ciki? Shin zancen da Inna Bintou ke fadi cewa sun hada kansu gaskiya ne?â€
Shiru Dr. Mansour ya yi, sannan a sanyaye ya ce, “Na san zancen, sai dai ban taba ba shi muhimmanci ba, a bisa hujjojina kwararaâ€.
“Wane Aboubacar din da wace Basman?†Daddy Ishaq ya tambaya cikin mamaki da kuma dokantuwa da a fidda shi cikin duhu.
Nan Malam ya gaya masa shi ya dade da sanin zancen a bakin iyayensu mata. Ya yi zaton ya sani shi ya sa ya yi ta zuba ido yana jira su zo masa da zancen. Da ya ga suna nufin sai bayan ransa shi ya sa yake so a yi ta ta kare a yau. Ko bai ga ‘ya’yansu ba, ya shaida aurensu ya gode wa Allah.
Daddy ya dubi kaninsa zuciyarsa na ninkaya cikin farin cikin da ya gaza boyuwa a kan fuskarsa.
“Ba ka bai wa zancen muhimmanci ba sabida wadanne hujjoji naka? Da ni da kai wa ya fi rashin kyauta wa dan uwansa?â€
Murmushi ya yi ya sunkuyar da kansa, “Ku fahimce ni bakidaya, dukkaninsu ba mai iya zama a kasar da dan uwansa ke zaune. Kowanne yana da tsararriyar rayuwa a inda yake. Sannan abu ne mai wahala Basma ta iya baro iyaye da ‘yan uwanta ta zauna da mu a Nigeria. Sannan ina tunanin kamar karfin samunsa bai isa ya rike ta ba in aka yi duba da irin rayuwar da ta taso a cikiâ€.
Murmushi Daddy Ishaq ya yi, kanin nasa na kara shiga ransa. Idan zai yi abu sai ya duba shi (from every sphere, he leave no stone unturned),
“To ai ni kaina na kusa barin Americarâ€.
Ba Mummy Zulaiha kadai ba, kowa a falon sai da ya juyo ya dube shi. Gyada kai ya yi don tabbatar musu da furucinsa, sannan ya ci gaba da bayani yana kallon matarsa.
“Saboda Mu’azzam na kai wannan lokacin a America, saboda yana karbar proper medical treatment, kuma bana so mu taho gabadaya mu barshi shi kadai, ga aikinsa ga yanayin da yake ciki, a ce ba shi da kowa a kasar da yake zaune. Amma ni tun farkon faruwar matsalolin nasa kasar Amurka ta fice min a rai. Ina ta dakon damuwar Mu’azzam. Yau da na fayyace muku sai na ji kamar an dauke min wani nannauyen dutse daga kirjina. A kalla nasan ba ni kadai nake jigilar damuwar ba, ina da masu taya ni ko da da addu’a ne. Target dina na yanzu shi ne, Aboulkhair ya kama aiki, ya yi aure ya zauna kusa da shi, ni kuma in nemi aiki a nan Niamey in dawoâ€.
“Allah ya yi maka albarkaâ€. Inji Malam Raazee, “Shi kuma Allah ya ba shi lafiyaâ€. In ji Uncle Oussama da Uncle Edrissa.
Ba su tashi daga wannan zaman ba sai da suka yanke lokacin auren yaran nasu hudu. Daddy ya gaya musu ita Khaleesat yana da buri a kanta, ya dade da gane shirin da ke tsakaninta da Hamoud kafin ya tafi Japan, inda yake kwas din aikin sojan ruwa, shekara mai zuwa zai kammala. Uncle Oussama rasa me zai ce ya yi, danshi yake wa tanadinta, amma ya gaya masa maganganu marasa dadi dazu. Matsar kwalla ya shiga yi yana cewa, “Pardonne-mon frereâ€. Wato (ka yafe min dan uwa da harshen faransanci).
“Ni ba ka yi min komai ba Yaya. Kauna ce ta saka damuwa da lamarin Mu’azzamâ€.
Addu’a mahaifin nasu ya daga hannu ya yi musu bakidayansu. Ya sa musu albarka, ya roki Allah ya sa su gama da duniya lafiya, ya kara musu kaunar junansu.


*****
Watanni uku aka sanya auren Aboulkhair da Aalimah, Aboubacar da Basma. A wannan lokacin Aboulkhair ya haye jarrabawarsa ta specialty da suke kira primaries a Psychiatry, ya zama junior registrar. Shekaru biyu baya ya sake yin jarrabawa part 1 ya haye cike da dumbin nasara ya zama senior registrar in Psychiatry. Asibitin Desert Parkway dake garin Las Vegas nan ya tura takardunsa neman aiki, don kawai ya zauna kusa da dan uwansa ya kula da shi, shi ya sa bai nema a garin da iyayensa suke zaune ba.
A ganinsa Mu’azzam ya fi su bukatarsa kusa da shi duk da ya san Mu’az ba zai yarda su zauna gida guda ba sabida rashin son hayaniyarsa, amma a kalla suna gari daya, koyaushe yake son ganinsa zai je, zai maido da kulawarsa bakidaya wuyansa, tunda dama saboda shi ya karanci wannan bangaren.
Idan ya yi shekaru biyu ko uku yana practicing kuma zai koma John Hopkins ya sake yin wata jarrabawar part 2 suke kiranshi, idan har ya ci shi kenan ya zama cikakken consultant (neuro psychiatrist). Duka wannan wahala da jajircewa ba don kowa Aboulkhair ke yi ba, ba don kansa ba, ba don shiryawa kai future ba, sai don ya kula da lafiyar Yayansa Mu’azzam.
6/29/21, 9:00 AM - Buhainat: 6




Sanda ya shigo gidan, Aalimah na kwance a three seater, idanunta a lumshe kamar mai barci da carbi a hannunta. Ko kusa ba ta ji shigowarsa ba sai zamansa bayan ya kwashe kafafunta ya zauna a muhallinsu, ya maida su bisa cinyoyinsa. Yatsun kafar ya shiga kallo kamar yau ya fara ganinsu. A hankali ya shiga ja mata yatsun daya bayan daya, uffan bai ce ba, gabadaya tafukan kafar nata masu tsananin taushi da suka sha adon jan lalle suna cikin hannayensa. Aalimah ta dada runtse idonta, wani abu ne da bai taba faruwa da ita batun tashin ta. Wato jikinta ya kusanci na wani da namiji, balle wannan ba wani ba ne face mutumin da zuciya da ruhinta suka dade suna mafarkin mallaka, Aboulkhair ne, dan uwanta da a yanzu yake amsa sunan mijinta, mahadin rayuwarta.
Katon mayafin ya shiga zarewa a hankali yana kiran sunanta. Dagota ya yi bakidaya ya aza a jikinsa, bayan ya yi nasarar zare mayafin, ya saura daga Aalimah sai rigar barcin da Gumsu ta zaba mata, wadda a cewarta ita ce ta dace da wannan ranar a gare ta, kuma irinta ta zaba wa Basma. Sunanta kawai yake kira, yana so ta bude ido ya kalli kwayar idanunta da ya dade bai samu alfarmar gani ba.Yayin da hannayensa biyu ke karadewa suna rungume ta a dukkan jikinshi.
Wata irin ajiyar zuciya Aboulkhair da ita kanta Aalimah ke saukewa akai-akai, zuciyoyinsu na tuno musu tsawon lokacin da suka dauka suna dakon zuwan wannan ranar, shekaru biyar cif! Ashe komai in aka yi hakuri aka bi dokar Ubangiji, aka yi biyayya ga iyaye komai nisansa watarana za a kai ga cimmasa ta tsaftacciyar hanya.
A wannan rana mai dumbin tarihi cikin rayuwarta, Aboulkhair Ishaq Raazee ya tabbatar mata ya wahala ba kadan ba, cikin dakon kaunarta da jiran wannan muhimmiyar rana a gare shi, wadda ranakunta suka shude a daddafe tamkar ba za ta taba zuwa ba. Kaunar ya nuna mata filla-filla da wani irin salo mai tsayawa a zuciyar diya mace. Aalimah, ta yarda ta amince; a daren yau son da Aboulkhair ke mata ya rinjayi nata, duk da yadda a baya ta ke zaton zuciyarta mai kankanba ce a kansa. Tun tana sanya wa ranta juriya da ganin cewa, lamarin mai iyaka ne tunda dai Aboulkhair mai sonta ne, mai tausayinta ne, har ta amince wannan ita ce ranar rashin tausayi ta duniya a rayuwar Aboulkhair. Ba ta kuma da wani yunkuri da za ta iya na kwatar kai, ko ceton kai, sai yadda Aboulkhair ya ga dama da rayuwarta.
A tsayin daren bakidaya Aboulkhair bai dawo Aboulkhairinsa ba sai da ya fahimci Aalimah duk juriya da dauriyarta da ta ke yi domin ya samu nutsuwa, domin ya tabbatar ba shi kadai ya yi wahalar shekaru biyar ba, ita din kuma ya cutar da lafiyarta ba dan kadan ba.
Shi likita, ita mai bada magani, don haka taruwa suka yi suka taimaki kansu ba tare da taimakon kowa ba, ba tare da wani ya ji ya gani ba. Ko Gumsu da suka biyo yi musu sallama washegari ta yi tsokanar duniyar nan, Aalimah ba ta tanka ba, sai murmushi da rufe ido. Shi kuma suna zuwa ya bar gidan ko gaisawa ba su yi ba. Rana ta farko da ya ji yana jin kunyar Mummy a rayuwarsa. Ya gode wa Allah da Mu’az ba ya nan, kallon cikin idanunsa a yau ya tambaye shi ya amarya ta kwana babban tashin hankali ne a gare shi. Saboda Mu’az ya san komai nasa tamkar a tafin hannunshi, ko da kuwa bai furta masa ba.
Ba su dade ba suka yi sallama da ita suka tafi, direban Mu’az har Massachusetts zai kai su, ya hana su bi motar kasuwa, kuma ya ce kada su sa Aboulkhair tuki ya bar matarsa a garin ita kadai bata saba ba.


******
“Sun tafi?†Aboulkhair ya tambayi Aalimah daga bakin kofa, yana mai leko kansa dakin kamar mara gaskiya.
Murmushi ta yi ba tare da ta juyo ba ta ci gaba da shafa manta a lallausar fatar jikinta. Alamu sun nuna daga wanka ta fito.
Ya karasa shigowa dakin ya isa gare ta, ya rungume ta ta baya yana sunsunar bathrobbs din da ta yi amfani da shi, suka kama fatar jikinta da karfin gaske, yana wani lumshe idanu. A karshe ya juyo ta bakidaya suka fuskanci juna. Kallonta ya yi, kamar ya hadiye ta don so, hannayensa na bisa kafadunta, goshinsa hade da nata, karan hancinsu na zungurar na juna.


Ya ce, “Kwanta ‘yar Gumsu in duba stitches dinâ€.
Hannayenta biyu ta sa ta rufe fuskarta tare da yin baya da sauri za ta gudu. Da azama ya cafko ta.
“Mun wuce wannan stage din Aalimah, ki kwanta in dubaâ€.
Yadda ya yi maganar cikin seriousness ya sa ta bi umarninsa.
Rungume ta ya yi sosai, yana fadin, “I’m sorry Aal, really sorry. Ba Aboulkhair ba ne ya aikata wannan laifin sabon mijin Aalimah ne. Shi Aboulkhair ai kin san shi mai tausayi ne ko?â€.
Ya hau sumbatarta kusfa-kusfa yana rokonta ta yafe masa. Toshe masa baki ta yi da tausasan yatsunta.
“Aalimahr is nothing but his wife wadda Allah ya yi masa izinin ya zo mata sanda ya so, duk ta inda ya yi umarni, ita din gona ce a gare shi. In dai Aboulkhair ne yanzu ma ya maimaita goman laifin nan a shirye Aalimah take da karbarsa cikin kowanne hali Monsieur Aboulkhair. Na san ba rashin so ba ne, kauna ce. Kaunar ma ta Aboulkhair ga Aalimah, ‘yar asali, mai dogon tarihi, wadda ta cancanci bugawa a littafi da na iya rubutuâ€.
Murmushi Aboulkhair yake ta yi, wanda ke fitowa kai tsaye daga zuciyarsa, a lokaci guda yana mai cakuda yatsunsa cikin lallausar gashin kanta, ya ce,
“Gara da ba ki iya ba. haka kawai! Masu karantawar su ce… su ce…â€
Dariya Aalimah ta saki, ta ce, “Su ce me?â€
Karan hancinta ya kama ya ja da karfi, ya ce, “Na ki fada din, balle ki fara rubutun a kaina. Ki dai fara a kan wannan Gumsun uwar taki mai budurwar zuciyaâ€.
Dukkansu dariya suka saki suna kewarta.
Ya ce, “A duniya ina son Aunty Gumsu, amma kwanan nan tana shigar min hanci, she’sannoyingâ€.
Aalimah ta ce, “Ba ka ga abin da ta yi wa Basma ba, namu nafila ne. Har daga zanin gadon ta ke tana shiga da shi daki-daki wai wadanda ba su gani ba su zo su ganiâ€.
Ya girgiza kai, ya ce, “Shi ya sa na zage na wanke abuna kada ta dauki hoto ta tura Nigerâ€.


******
Kwanaki uku da suka biyo baya wata irin rayuwa ce mai cike da soyayyah, Aboulkhair da Aalimah ke gudanarwa a gidansu. Su yi girki tare, su ci abinci tare, su yi wasa su yi dariya, su sanya juna nishadi. Tarairayarta yake da jinya har ta warware. In ba wani abu da ya kama dole zai sayo musu ba, ba ya fita. Sallah kuwa jam’inta suke su biyu sau biyar a rana. Nata dakin sun kulle shi da nashi suke amfani. Sun yi wata irin shakuwa mai ban mamaki fiye da shekaru biyar din baya.
Yau suna zaune a dan karamin dining dinsu mai kujeru biyu kacal, wanda ke cikin kitchen dinsu suna cin abincin rana. Wayarsa ta yi kara, ya kalle ta da gefen ido, bai yi niyyar amsawa ba don a kwanakin nan ma amsa waya wahala yake masa, ta fi zama a kashe a yawancin lokuta kafin ya karasa cinye kwanakin hutunsa da suka rage. Amma ganin mai kiran da sauri ya dauka.
Aalimah na ganin yadda ya tattara bakidaya hankalinsa a kan wayar, ya kuma mike tsaye. Hatta muryarsa canzawa ta yi, magana yake with utmost respect.
“Ban san ka shigo gari ba, da tuni na zo na kwance jaka. A yi min izini na kawo Aalimah ta kwashi gaisuwa wajen babban Yaya, ba ta taba ganinka baâ€.
Ba ta ji amsar da Mu’azzam din ya bayar ba, ta dai ga Aboulkhair ya kara nutsuwa yana rokonsa ya barsu su zo. Har yana fadin, ya fadi iya mintunan da zai iya ba su da bakinsa in suka haura gobe kada ya barsu su sake zuwa. Takaici ya kashe Aalimah daga zaune, sarkin ina ne wannan? Dole ne zuwa wajen nasa? Me yake rabawa da sai an roke shi za a je inda yake?
Ba ta gama wannan tunanin ba ta ga Aboulkhair ya cillar da wayar tasa gefe ya rarume ta ya mikar. Cike da zumudi ya ce, “kiyi girki, wanda ya fi kowanne dadi mu kai wa Mu’azzam, ki hanzarta mintuna talatin kawai ya ba mu in mun je, yana da wata seminar gobe da (Concophillips oil Gass) yana shiri, kada ki bata lokaciâ€.
Aalimah ta rausayar da kai, ta ce,
“Me zan dafa? Ban san me yake so ba?â€
Ya koma ya zauna ya hau lissafi.
“Girkin da ya fi kowanne dadi with aroma and maggiâ€.
Ba ta san sanda ta saki dariya ba, ta tabbata Aboulkhair yana matukar son Yayansa, ba ta taba ganin ya dau lamarin wani da muhimmanci irin haka ba.
“Kowanne girki ai dole a sa masa aroma da maggi, I mean irin abincin da yake soâ€.
“Tashin hankaliâ€. In ji Aboulkhair, “Ai wato menu ake ba shi daga WALDORF ASTORIA (mafi shaharar restaurant a Las Vegas) ya zabi abin da yake so, ni kaina ban sani ba. amma ke me ki ka ga ya dace?â€
Aalimah kamar ta yi kuka, a ranta ta ce, ‘Haka kawai ina zaman-zamana za ka taro min aradu da ka, wannan basaraken naka ai sai kaiâ€. A fili kuma ta ce, “Burabisko da miyar tausheâ€.
Ya zaro ido, ya ce, “You are not serious. Gero zaki dafa masa ya shaqe shi? Tukunna ma kin san wai wajen wa nake magana ne?â€
“Ka ce sunansa Mu’azzamâ€.
Ya ce, “Ba ki san Yayanmu ba ne?â€
Ganin kamar ya soma harzuka ta shiga nutsuwarta sosai, ita haka kawai ranta bai son Mu’azzam din nan tun daga lokacin da ta fahimci irin life style dinsa, da maganganun da kannensa ke yi a kansa na irin rashin kirkinsa da ginshirarsa, sannan shekaru biyar ta kwashe a gidan Ishaq Raazee daidai da rana daya ba ta taba ganin sawun wannan Mu’azzam din a gidan ba, da sunan ya zo gaida iyayensa. Sai dai kullum ta ji Mummy a hanyar zuwa gidansa, what a life! Sannan yanzu ta kara fahimtar wani abu, Aboulkhair ba ya hada lamarin Mu’azzam da na kowa, ita kanta ba a bakin komai ta ke ba in dai a kan Mu’azzam ne. She has to be careful don tsira da mutuncinta a idon mijinta-mai-kaunarta.
Da kyakkyawan sauti ta ce, “Ina ganin mu yi masa tuwo. Ka fahimce ni Mon Amour (my love), ba abin da ya saba ci ya kamata mu kai masa ba, ba za mu burge shi ba. African cuisine shi ya kamata. Idan Mu’azzam ya kasa cin tuwo na ka mare ni sau ukuâ€.
Bai san sanda ya yi murmushi ba, amma kwarai ta bata masa rai da farko, zancen Mu’azzam fa yake mata, amma ta maida shi kamar wani marainin wayonta. Kodayake ya mata uzuri, ba ta sanshi ba, ba ta taba ganinsa ba, ba ta san komai a kanshi ba.
Wanka ya shiga kafin ta gama, ita kuma ta dukufa sarrafa kyakkyawan farin tuwon shinkafa da miyar danyar kubewa da ta markadata da blander. Ta yi masa kyakkyawan tuki, ta kwashe shi kananan malmala a farar leda ta jera a food warmer madaidaiciya. Kafin ta saka kaza a miyar sai da ta soya ta, sannan ta zuba su a miyar suka dahu tare. Kafin ta gama zobon da ta jika da ruwan zafi ya jiku, ta tace ta yi masa hadin danyar abarba da danyar ginger (citta), ta sa sukari da pineapple flavour. Ta juye a cooler irin ta zuwa picnick din nan. Ta jera komai a kwandon abinci har farantai da cokullan da za su yi amfani da su ta dauka. Sannan ta fada wanka.
Dukkansu sun yi tsaf cikin Hausa Attire, sai kamshi suke yi. Suna tafe a hanya Aboulkhair ya kunna musu kira’ar Abdurrahman Sudaith cikin suratul Ma’idah, wadda ta kara sanya nutsuwa da kwanciyar hankali a zukatansu. Aalimah cikin ranta cewa ta ke yi, yau dai za ta ga Mu’azzam din nan, ta ga shin me ya taka a rayuwarsa? Wane ne shi? Wane irin mutum ne shi? Zaman me yake yi shi kadai a gida babu iyali? Ba mamaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login