Showing 66001 words to 69000 words out of 126031 words

Chapter 23 - Aalimah Complete 1,2,3,4 Free Book by Takori .txt

sex as an escape behaviour. They have intense sexual impulse. And the episode have to last over size months before it can be diagnosed. Drinking alcohol triggers the problem and increase aggression. (fasara; mutane masu fama da compulsive sexual disorder suna amfani da sex matsayin hanyar farko ta samun sauki daga tsoro, kadaici, zafin zuciya, radadin zuci, bacin rai da sauran stresses ba tare da la’akari da abin da hakan zai haifar ba. Ta yadda har hakan zai shafi ayyukan neman abincinsu, lafiyarsu, mu’amalolinsu, iyalinsu da sauran abubuwa na yau da kullum. Halayensu shi ne abnormal sexual drive wato yawan saduwa wanda ba a saba da shi ba, ko wanda ya wuce kima, shan wahala wajen gina soyayya a zukatansu (kamar soyayya ta aure) da gina iyali. Abin da suka fi maida hankali a kai shi ne, having sex to relieve their stresses and pains. Sai dai duka wannan ana iya magance shi da kwayoyin Anti-androgens da kuma mood stabilizers medicines, mara lafiya ya zauna lafiya cikin kyakkyawar rayuwa kamar kowa.
To kin ji Aalimah, wannan ita ce rayuwar Yayana Mu’azzam. Yau shekara goma kenan yana rayuwa cikin shan kwayoyi domin danne sexual urges tare da kuskurewa ba. Ko da aka tilasta masa ya saki Halima ya sake tan, amma ya gaya wa su Daddy kada wanda ya kara dosarshi da zancen aure kuma kada wanda ya kara yi masa aure ba tareda saninsa ba. Yana jin dadin rayuwarsa a haka, and he’s making it profitable. Kwayoyin anti-androgen suke hana Mu’az sha’awar aure kwata-kwata. He cannot even develop emotion balle ya ji yana son wata mace a ransa. Bayan gama MBA dinsa ya samu aiki da kamfanin man fetur na farko a Amurka, wato CHEVRONCORPORATION sun barshi a reshensu na Las Vegas inda yake zaune ya kasa barinta. Akwai sanda aka yi masa sauyin wajen aiki zuwa jihar OHIO amma Muazzam bai yi kaura ya koma can ba. Kullum zuwa yake ya dawo a jirgin kasa, ko ya je ya yi sati biyu ya dawo. A cewarsa Las Vegas is where all the memoirs of his adulthood began..... He cannot go far from it.
Ta canza shi daga spoilt, drunkard Mu’azzam, zuwa matashin da ya san ciwon kansa, ko kusa Mu’azzam ba ya son shiga mutane, har family dinsa kuwa, ya fi son rayuwar da yake yi ta kadaici da maida hankali ga ibadah wadda a shekarun teenage dinsa bai samu alfarmar yi ba sai shan giya. Sai kuma dedication ga aikinsa, saboda bai da wani abin yi mai muhimmanci bayan shi. Kamfanin chevron na ji da Mu’azzam fiye da zatonki, saboda yana daga cikin masu habbaka su da kawo musu innovations.
Tunda na shiga shekarun da na fara hankali, na kuma kai ga fahimtar matsalolin Yayana Mu’azzam na yi kudurin zama neuro-psychiatrist saboda in kula da shi a sauran rayuwarsa… Ina so in canji Nebrass in zamo ni ne mai kulawa da shi ba wani ba. Mu’az bai fiya zuwa Boston ba (Massachusetts) mu muke zuwa inda yake. Mummy ta fi kowa zuwa akai-akai, saboda a yanzu tana jin kanta culprit na duk irin rayuwar da Mu’azzam ke yi a yanzu, tana zuwa ta yi kwanaki tare da shi, a kan idonsa aka haife su Basma daya bayan daya, amma babu wata shakuwa a tsakaninsu, ba ya jansu a jiki, ba ya shiga sha’aninsu, tun suna damuwa har sun daina, sun fidda shi a jerin ‘yan gidan. Khaleesat kan ce ba iyayensu daya ba, he’s adopted. Wato dan tsintuwa ne. Sai dai duk da haka har gobe ba su san matsalarshi ba an barsu a yadda suka dauke shi din saboda a shekarunsu da matakin ilminsu ba za su taba fahimtar matsalarsa ba.
Ki taya ni addu’a Aalimah, Allah ya cika min burina in zama ni ne consultant din Mu’azzam Raazee, in ci gaba da zama tare da shi har karshen rayuwa ta…â€
Sai a lokacin Aboulkhair ya lura matarsa Aalimah kuka ta ke yi, tunda ya yi nisa a ba ta labarin Yayansu Mu’azzam. Kukan kuma ba na komai ba ne, na tausayin Mu’azzam ne.
Murmushi ya yi ya ciccibe ta ya yi dakin barcinsu yana fadin, “My easily crying wife, da na san labarin hawaye zai fiddo daga idon matata da ba’a fara shi baâ€.
Rungume shi ta yi sosai tana ci gaba da kukan, ta ce, “Insha Allah kai za ka koma kula da Mu’azzam, ina rokon Allah Ya cika wannan burin nakaâ€.


******
Sabida yadda labarin Mu’azzam da tausayin shi ke tsunkulinta a zuci, kwananta uku ba ta walwala.
Jin labarin nasa maimakon ya kwantar da kishirwarta a kan saninsa, sai ya tafi ya bankado wasu sababbin inquisitivities din cikin zuciyarta a kan rayuwarsa. Sai dai tana ganin ya kamata ta kyale mijinta haka a kan dan uwan nasa kada ta wuce makadi da rawa. Ya gaya mata abin da zai iya kuma a matsayinsa na likita akwai abin da ba zai iya fada ba a kan patient dinsa, wani abin sirri ne tsakanin likita da patient dinsa kadai.
Ranar da Aboulkhair zai koma aiki ya ce da ita ta sake yin tuwo in ya dawo ya kai wa Mu’az, tunda ya nuna ya yaba, kuma yana so. Da karsashi da karfin gwiwa ta yi sallelen tuwon semo da miyar kuka wannan karon, yana dawowa ko hutawa bai yi ba ya dauka ya kai masa. Da ya dawo yake ba ta labari Mu’azzam ya ci tuwonta sosai fiye da na ranar da suka je, ya ce ya yi mata godiya, amma ya daina wahalar da ita ya barta ta dinga hutawa. Saboda shi ya dauki girki wajen mace wani abu mai matukar wahalarwa a gare ta ya fi dacewa da maza (a cewarsa).
Dariya ta yi, ta ce, “Ashe da zai yi aure da matarsa ta hutaâ€.
Ya ce, “Sosai ma kuwa, in dai ta fannin girki ne, ko Mummy ba ki ga yadda suke kai ruwa rana ba in ta zo, she want to cook for him, a wurinta abincin gida ya fi na restaurant gamsarwa, a wurinsa hakan bautar da mace ne, musamman ita da shekarunta suka soma turawaâ€.


Watanni uku cif! Da auren Aboulkhair da Aalimah, Mu’azzam ya yi kokari ya samar mata aikin da ya yi alkawari a asibitin da mijinta yake.Sabida tana zaune a gida bata komai. Wani pharmacy suka tura ta a babban reshensu wanda shi ba asibitin kwakwalwa ne kawai ba, babban asibiti ne General hospital da ya kunshidepartments na kowanne bangare. Sun tura ta wani pharmacy dinsu a Ophthalmology department (bangaren harhada magunguna a tsangayar ido). Kowanne bangare na asibitin akwai pharmacy a cikinsa, don haka duk inda ka ke so a nan za ka sayi magani cikin katafaren asibitin.
Don haka kullum Aboulkhair sai ya fara sauke ta, ya raka ta har cikin ofishinta, ya cire mata abaya ya dora mata farar rigarsu damini hijab dinta da ba sa hana ta sakawa sabida kare martabar addininta, ya rungume ta ya sumbace ta, sannan yake tafiya.
Idan ya riga ta tashi zai zo ya jira ta har ta tashi, sannan su tafi gida. Idan akwai abin da za su saya su biya kasuwa, sannan su karasa gida. Idan kuma ita ce ta riga shi tashi komai dadewar da zai yi haka za ta zauna ta jira shi. Son juna suke kamar su hadiye junansu, ba sa taba gundura da juna. Soyayyarsu mai ban sha’awa da tsafta, wadda duk inda suka zauna sai ta fallasa kanta.
Tun zuwanta gidan Mu’azzam na farko, ba ta kara yarda ta bi Aboulkhair ba, shi kadai yake zuwa. Ta yarda kin mutane da Mu’azzam ke yi, yana da nasaba da mental state dinsa. Da ace za’a bata dama, da ta zauna dasu Basma ta fahintar dasu wanene Yayan su Mu’azzam? A yanzun sun mallaki hankulan kansu sunyi ilmi mai zurfi, sosai zasu yi masa uzri, su bude zukatansu su bashi gurbi. Gurbi na dan uwa mai tsananin kirki kamar Aboulkhair. Maganin wata guda Aboulkhair ke kai masa. Har ta haddace magungunan Mu’azzam don ita ke hadowa ta ba shi. Dose da mgduka ta rike. Rannan yake gaya mata babban likitan Mu’az ya ce zai kara karfin mood stabilizers dinshi, don a samu ya riki wasu al’amuran na social life bayan aiki da ya kwallafa kafatanin rayuwarsa a kansa. Ba ya tunanin kowa, ba ya tunanin komai, babu kowa babu komai a zuciyarsa sai proffession dinsa.


Mummy Zulaiha hankalinta ya dada kwanciya ganin cewa, Mu’azzam ya samu ‘yan uwa a garin da yake, duk da ba gidansu daya ba, ta san ko ya ya ne za su taimaka masa ta wani fannin. Ba zasu barshi cikin ragaita da zaman kadaicin nan nasa ba koda baya so.Ta san cewa, kulawar lafiyar tasa bakidaya ma yanzu a wuyansu ta ke ba.


Aalimah Mansour, na tsaye tana kare wa dan kyakkyawan ofishinta kallo, tana kuma kallon alert na damin kudin da ya shigo mata daga bankinta WellFargo, wai duk wannan albashinta ne na farko. Iyayenta ta shiga yi wa addu’a ba ji ba gani, har Daddy Ishaq ba ta cire cikin addu’arta ba. Wadanda suka tsaya tsayin daka tayi ilmin da ya bata wnnan matsayin. Fitowa ta yi ta rufo ofishin zuwa Atm mafi kusa ta yi wa Daddy transfer na gabadayan kudin, ko dala guda ba ta rage ba, ta hanyar western money transfer. Kudin na shiga Dr. Mansour ya kira Aalimah.
“Kudin me ki ke ta turo mana ne kamar wata ma’aikaciya? Kin yi ya kai sau hudu ina shiru, na yau yafi na baya, ina ki ke samu? Aalimah kada ki kasance cikin masu dora wa mazansu hidimar da ta fi karfinsu don ki wadata iyayenki. Mu din we’re contented with our life ba mu nemi komai mun rasa ba, Aboulkhair me ya tara, yaushe ya fara aikin da ki ke kwakularsa wadannan makudan kudaden?â€
Dariya Aalimah ta yi, sannan ta soma yi masa bayani, cewa kudin farko, na biyu da na uku duk Mu’azzam ke saka mata cikin ATM don ta yi lalurorin gabanta ba tare da ta roke shi ba. Ita kuma ba ta da bukata shi ya sa ta tura musu. Na yau din kuwa halak dinta ne, guminta ne, albashinta ne na aikin da Mu’azzam ya samo mata daDesert Parkway Health Center.
Dr. Mansour kasa magana ya yi, akwai matashi mai zuciyar riko da zumunci a duniya irin MU’AZZAM ???
“Yaa Allah ka dubi wannan bawa naKa da tarin alherinsa da jin kansa ga ‘yan uwa da sauran al’umma, Ka ba shi lafiyar da ka ke jarrabtarsa a kanta, ya yi rayuwa mai dadi kamar kowanne dan Adamâ€. Addu’ar da Dr. Mansour ya shiga yi wa dansa Mu’azzam kenan, wani Da mafi soyuwa a zuciyarsa cikin dukkan ahalin Raazee, manyan su da yaransu.


*****
Shekaru guda biyu kwarara kenan da wannan aure mai dumbin albarka, wanda ya zamo wani tubali na hadin kan iyalin Malam Ibrahim Raazee bakidaya. Ya kawo alheri mai yawa ga kowannensu. Duk weekend Aalimah da Basma na rike da juna a kan waya, sabida a weekend din kadai ta ke samun lokacin gaisawa da ‘yan uwa da iyayenta, saboda yanayin aikinta da hidimar Aboulkhair da ba ta karewa. Shagwababbe, cingam, super glue din Aalimah, dan gatan Engnr. Mu’azzam Raazee. A karshen shekarar Aboulkhair ya koma John Hopkins University ya zana jarrabawar part 2 dinsa. Ba da jimawa ba sakamako ya fito, ya cinye komai da wata irin madaukakiyar nasara, ya dawo asibitinsu inda aka canza masa ofis a matsayinsa na cikakken consultant (Neuro-Psychiatrist) a halin yanzu.
A wannan lokacin ne Dr. Nebrass likitan Mu’azzam na shekaru masu yawa da suka gabata ya danka wa Dr. Aboulkhair Raazee kulawar dan uwansa Mu’azzam bakidaya, ta hanyar damka masa file dinsa sabida shi kansa jinjinawa kwarewa da fasahar Aboulkhair yake yi, kamar wanda ya shekara goma yana practicing. Bai sani ba, hakan na da alaka ne da zuciyar ‘yan uwantaka da shakuwa wadda aka gina karatun kacokam a kanta, sannan shi din shekarunsa na komawa gida ya huta (retire) sun cika.
Zuwa wannan lokacin Daddy Ishaq ya gama komai na shirin komawarsa gida Niger da iyalinsa mata bakidaya. Abu daya yake jira su ajiye ayyukansu su koma (takardar daukarsa aiki da ministere des affaires etrangeres), wato ministry of foreign affairs, hukumar hulda da kasashen waje ta kasar Niger mai location a babban birni Niamey, wadda wani tsohon abokinsa ma’aikaci a wurin da suka yi aiki tare tun a Niger Consulate America yake ta kokarin nema masa.
Sun hadu ita da su Mummy a Massachusetts sun je wa Aboulkhair jami’ar John Hopkins har can garin Baltimore (Maryland) ranar da ya karbi shaidarsa ta zama consultant, tare da shi suka taho Boston. Kwanansu biyu da iyayen nasu da kannensu su Khaleesat wadda ta gama karatunta ita ma a wannan shekarar, suka koma gidansu.
Kafin su shiga gida ya ce, lallai wannan karon sai sun je ta gaida Mu’azzam. Zuwanta daya a kulliyar zamanta cikin garin da yake, sai dai in suna waya da Aboulkhair yakan ba ta su gaisa a gajarce. Ita girmansa da respect dinta gare shi ke hana ta sakewa da shi, a wani bangaren kuma tausayinsa bakidaya. Yayin da shi kuma a nasa bangaren da ma ba ya sakewa da kowa sai Aboulkhair, sai kuma Daddy da kaninsa Mansour Raazee, da kuma kakansa mai ran karfe. Ko Mummy ba ruwanta da rayuwarsa. In ka ji suna magana mai tsawo, to nata matsalolin ne da ta ke neman ya taimaka mata ta fita daga cikinsu. Da shawarwarin Mu’azzam ne ta tabbatar a yanzu ta zauna lafiya cikin sukunin zuciya da kyakkyawar mu’amala da kishiya da dangin mijinta, mutuncinta ya dawo cikin idanunsu.
A halin yanzu ma ta neme shi kan babban kalubalenta na yanzu (barin aiki da Daddy ke so ta yi su koma gida). Tana cikin damuwa da hakan matuka. Abin da Mu’azzam ya ce da ita shi ne, “Mummy me kuma ki ke nema a rayuwa? Kin aurar da duka manyan ‘ya’yanki bayan kin ba su wadataccen ilmi, nan da shekara daya za ki aurar da wadda ta saura. Kudin da ki ka tara shekaru masu yawa ki ka ba ni, ki ka ce in sayi gida in bar rent, gaya miki ne ban yi ba, hannayen jari na siya miki da su a manyan bankunan Nigeria da Niger. A yanzu haka gidan nan da nake ciki mallakina ne, na dade ina biya da kadan da kadan na kuma hada da wani kaso kadan daga wanda ki ka ba ni. Don haka don Allah Mummy ki yi wa mijinki biyayya kamar yadda ki ka saba, ke ma ki zauna waje daya ki huta kamar kowacce matar aure ki fara rainon jikoki da tarbiyyarsu. Aboulkhair ya gaya min Basma ta kusa haihuwa, shi ma tashi matar ta samu yanzu, ga Khaleesat za ta shiga daga ciki ita ma. Mummy you are blessed ki kara gode wa Allah, ki koma neman lahira. Na yi miki alkawarin 40% na albashina duk wataâ€.
Kuka Mummy Zulaiha ta saka, abin da Mu’azzam ba ya so daga gare ta.
“Mu’azzam ban san da wane harshe zan daina cewa ni na jawo rushewar farin ciki da cikar rayuwarka ba. Ba zan iya daina cewa ka yafe min ba! Ka ambaci kowa zai haihu ban da kai, Mu’azzam naka na fi son gani. Mu’azzam ka taimaka min in sake yi maka aure ko me zai faru. Ni ban yarda da kafiran nan ba, namu addinin ya ce kowacce cuta tana da magani, Malam Raazee da kawunka Edrissa sun ce za su nemo magani…â€
Ta ci gaba da kuka sadidan fiye da wanda ta ke yi a baya.
Mu’azzam ya dafe kansa da hannun damansa, jijiyoyin kansa na sarawa. Da kyar ya ce, “Mummy ki daina maganar nan don Allah. Na riga na karbi kaddarata da hannu bibbiyu. Mummy I don’t have a feeling to give to a woman. Mummy aure is not about having sex and children only, there’s a matter of LOVE and AFFECTION. And Mu’azzam don’t have any, not even a remnant. Ki sa a ranki ‘ya’yan Aboulkhair da Basma ‘ya’yana ne da na haifa tunda in an tsaga jikinsu za a ga jinina. Mummy please..... ki daina kukan nan, kina tayar min da hankali. In Aboulkhair ya san abin da ki ke gaya min zai hana ni yin waya da ke…â€.
Alamun zaman mutum ya ji a kusa da shi, ya daga idanunsa da suka rine da sauri ya dube shi, Aboulkhair ne.
Gabadaya yanayinsa ya canza, bacin rai da tashin hankali sun bayyana karara a kyakkyawar fuskarsa. Idanunsa sun kada sun yi jazir. Mummy ba ta kyauta masa ba. Yana tufka tana warwara, maimakon ta shanye damuwarta ita kadai, ko shi ta kira shi ta yi masa. Me Mu’azzam zai maganta mata ban da ta kara masa damuwa, yana fama da jinyar tashi zuciyar da kwakwalwar? Mu’azzam din ya kamata ta gaya wa halin da ta ke ciki a kansa?
Mikewa ya yi zai fita, Mu’azzam ya rike shi yana daga zaune. Bai iya ya juyo sun hada ido ba saboda idanunsa da suka cicciko da hawaye. Murmushi Mu’azzam din ya yi duk da idanunsa sun kada, ya ce, “Ina ruwanka da hirata da uwata? Wato labe ka koma? Kuma meye laifi don ta yi sharing damuwar zuciyarta da ni?â€
Ba tare da ya juyo ba ya ce, “I’m your doctor. Not a brother. I’m responsible for all the progress and the downfall of your health. Da ni ya kamata ta tattauna abin da ta ke tattaunawa da kai. Mummy ba ta kyauta min ba! Damuwa da tunani suna hana mood stabilizers aiki yadda ya kamata. Kuma na san abin da zan yiâ€.
Ya kwace hannunsa zai fita. Mu’azzam ya daga murya ya ce, “Aboulkhair uwata ce fa! Za ka hana ni magana da ita ne? Ka shiga hankalinka kai da likitancin naka. Rayuwa da ciwo duka a hannun Allah suke. Idan Allah ya ce ma mutuwa zan yi dukkaninku ba abin da za ku iya. Ni gara ma in mutu in huta da wannan rayuwar…!â€
Da gudu Aboulkhair ya dawo ya rungume shi. Hawaye ya soma yana fadin, “Insha Allahu kai za ka binne ni, ba dai ni in ga kabarinka ba Mu’az, ba zan iya jura ba. Zan yi abin da ya fi hauka, ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login