Showing 108001 words to 111000 words out of 126031 words

Chapter 37 - Aalimah Complete 1,2,3,4 Free Book by Takori .txt

daura dana juna. A washegari Mu’azzam sammako yayi ya fice office ko karyawa bai yi ba, tana iya jiyo fitar motarsa daga gidan. Tana daga kwance a gadonta tayi ajiyar zuciya. A lokacin zuciyarta tayi zurfi cikin tunani mai dimbin yawa. Shikenan rayuwarta da Aboulkhair ta zama tarihi? Mu’azzam ne zai maye duk wani gurbi da Aboulkhair ke kai a baya? Ta yaya hakan zai kasance?
Bata taba yiwa Mu’azzam wani kallo bayan na Yayan su ba, ko ta ce Yayan mijinta. Rayuwar shi da tata ba iri daya bace; ratar dake a tsakani mai tsananin fadi da girma ce. Ga matsalar da yake ciki wadda bata san ranar warkewar ta ba. Saidai tana da tabbacin aggressiveness dinsa bazai shafe ta da komai ba. Zata iya yin nisa da shi a duk lokacin da taga alamun yana kokarin shiga cikin sa. Tunda Aboulkhair ya gaya mata yadda yake. Wanda ana daukan shekaru ma hakan bai faru ba. To amma babbar lalurar fa?
Aalimah ta nisa, ta aje gwauron numfashi.
Ko lokacin da take tare da Aboulkhair ita ba mai son yawan auratayya bace, wancan ma kenan da ya kasance soyayya ce mai tsanani a tsakani balle wannan da ya zamo hadin iyaye, ba da son ran ko dayansu ba.
Tana matukar ganin girman Mu’azzam da ganin kimar sa cikin idanunta, bata fatan zuwan ranar da zama irin na auratayya zai kasance tsakanin su. Koma dai yaya ne, tasa a ranta zaman iyayensu zata yi a gidan nan ba zaman Mu’azzam ba, wanda take da tabbacin shima ba son auren yake yi ba koda ace bai bude baki ya furta ba. Alamu duk sun gama bayyana kansu.
Data gaji da tunanin wanda ta amince bazai kawo mata mafita ba cikin tarin kalubalen dake gabanta, sai ta tattara komai ta mikawa Ubangiji. Ta tashi ta dauro alwala ta shiga gabatar da nafilfili.
Lokacin gari yayi haske, ta yunkura ta mike daga kwanciyar bayan ta ture bargon rufarta. Kai tsaye toilet ta fada tayi wanka tayi brushing bakinta ta dauro towell ta fito. Ta bude closet dinta ta soma ruwan idon kayan sanyawa. Ba Mu’azzam take da niyyar yiwa kwalliya ba kawai ta samu kanta yau cikin sukunin zuciya irin wanda bata taba samu ba tun rasuwar Aboulkhair. Lallai ne da ake ce aure rahma ne, kuma gidan miji ‘yanci ne ga diya mace koda wane iri ne kuwa.
Ruwan idonta ya tsaya akan wata doguwar riga ‘dark blue’ wadda nauyin duwatsun jikinta yafi yadin rigar nauyi, ta cirota ta zura a jikinta sannan ta zauna kan stool gaban dressing mirrow tana gyara dogon sassalkan gashin kanta wanda saida dabara take iya tazarsa.
Wayarta dake kan bed-side tayi kara da kiran sallah wanda shine ringing tone dinta. Mikewa tayi ta isa ga wayar ta dauka. Ganin sunan mai kiran sai ta zauna a gefen gadonta cike da farinciki tana amsawa.
Mama ce.
Bayan sun gaisa cike da shauki irin na Da da mahaifi ta tambayi lafiyar kowa na gida, Mama ta tabbatar mata kowa lafiya, ashe Daddy na kusa, don Mama mikawa Daddy wayar tayi tace shi ke son magana da ita. Aalimah ta gaisheshi shi kuma ya dinga zuba mata albarka akan biyayyar data yi masa, ko daga sautin muryarta ya fahimci ta kwantar da hankalinta yanzu ta kuma rungumi kaddararta da hannu bibbiyu.
Dr. Mansur yace “Aalimah kinsan dai ni na haifeki ko?†Ta gyada kai cikin tabbatarwa kamar yana ganin ta. Yace “to ki yarda bazan taba yin abinda zai cutar da ke ba. Kada rashin lafiyar Mu’azzam yasa kiyi tunanin don bazai samu matar aure bane yasa muka aurar dake gareshi, ko kadan, Ko ‘yar wa Mu’azzam yake so a fadin kasar Nijar zai aura mun dai ga bashi da niyya ne. Bari in gaya miki wani abu wanda ko uban Mu’azzam da ya haifeshi bai sani ba.
Rana ta karshe dana gana da Aboulkhair a dakina, munyi maganganu masu yawa akan Mu’azzam, kin san dai fannin rashin lafiyar Mu’azzam ya karanta har matakin consultant, kuma yake kan cigaba da zurfafa ilmi akai a jami’ar Johns Hopkins, ya gaya min bincike na karshe da suke kan yi of recent research ya nuna Mu’azzam zai iya warkewa gabadaya, zai koma normal sexual life bayan shekaru kamar goma in dai an kula da bashi treatment. Ya gaya min yana so ya gayawa Mu’azzam amma ya fasa don kada yace sai ya warke zai yi aure, amma ko likitansa Nebrass yasan Mu’azzam zai iya warkewa daga yanzu zuwa kowanne lokaci in aka kidaya yawan shekarun da ya kwashe cikin lalurar karkashin kyakkyawar kulawa kuma zai iya rayuwar aure yanzu haka (under treatment).
Shine dai yake tsaurarawa kansa damuwa da ganin cewa rayuwar sa ta gama amfani. Amma babu cutar da Allah ya saukar a duniya ba tare da ya saukar da ita tare da maganin ta ba. Ki yi tawakkali ki tattara komai ki barwa Allah. Kiyi addu’a kan Allah ya hada kanku da kuma zukatanku wuri guda, ki zubawa sarautarsa ido.
Ni Mansur Sarhamu Raazee na tabbatar miki sai kinyi alfahari da wannan auren watarana kuma sai kin zo kin gode mini. Soyayyata gareki ce tasa nayi miki wannan zabin. Zabin da duk cikin family din RAAZEE babu mai kamar naki. Ki kwantar da hankalinki a gidanki kinji Aalimah? Ki kuma yi hakuri da halin Mu’azzam mutum ne mai wuyar sha’ani. A matsayin ki na mace, zaki iya canza shi zuwa duk irin yadda kikeso ya koma. Mu’azzam is a nice person kuma idan kinyi hakuri zaki ci riba wataranaâ€.
Aalimah hawaye take yi tana sharewa da bayan hannunta. Ta san Daddy na sonta amma zata iya bayar da shaidar son da yake yiwa Mu’azzam ya nunka nata sau goma. Zuciyarta na mai amanna da kowacce kalma dake fita daga bakinsa.
Cikin rishin kuka Aalimah take fadin.
“Don Allah Daddy ka yafe mun gardamar dana yi maka a baya. Na rasa nutsuwa ta ne a lokacin. Ba kiyayya nake yiwa Mu’azzam ba, sannan ba rashin lafiyar sa ke damuna ba, ina dai duba kusancinsa da Aboulkhair ne. Amma daga yau na yi maka alkawarin cire komai daga raina insha Allahu, na yarda haka Allah ya rubuto mana bakidayan mu. Na san aure a tsakaninmu halastacce ne. Na yarda da duk abinda ka fada, ko Mu’azzam ba zai warke ba zan zauna dashi insha Allahu har karshen rayuwata. Ka taya ni addu’a Allah yasa nima ya so ni irin yadda Aboulkhair ke so na......!â€.
Sai kukan ya kwace mata bakidaya.
7/9/21, 7:20 PM - Buhainat: Aalimah






















Dan guntun scene din da ya faru a dakin Mu’azzam ta ke ta tunawa da ta koma nata dakin, wani ta yi murmushi, wani ta yi ajiyar zuciya. Ta kai gwauro ta kai mari a tsakiyar dakinta, tana mai naushin hannunta cikin tafin hannunta. Aalimah, ta samu kanta da son yin kyakkyawan bincike na ilmi bayan wanda Aboulkhair ya gaya mata a kan lalurar maigidanta Engnr. Mu’azzam Ishaq Raazee. Ta hakan ne zata san irin matakin da zata dauka akan zaman su da yadda zata bullowa rayuwar auren su, tunda kuwa abu ne wanda ba su da damar gujewa dukkanninsu. Auren su is inevitable. Don haka maganar wahalar da zukatansu ba shine mafita ba, mafitar itace ta nemi hanyoyin da zasu dorar da zaman nasu. Ciki kuwa har sai ta fahimci lalurorin sa bakidaya a ilmance, a likitance, a rubuce, a mu’amalance sannan in theory and practice.


Ta fara da shiga manhajar google inda ta binciki cikakken bayani a kan what the problem is all about? Sannan ta ke shiga library din Mu’azzam idan ya fita office, tana masa bincike, yana da manyan littattafai da suka shafi compulsive sexual disorder. Cikin manyan littattafan da ta debo daga library dinsa zuwa dakinta akwai ‘A Psychometric Investigation of the Hypersexual Disorder Screening Inventory’ (By J. Engel. 2019). ‘The Danger of Hypersexual Disorder’ (Dr. Martin Kafka), sai kuma ‘Compulsive Sexual Behaviour’ (A Review of the Literature) NCBI (By KL Derbyshire, 2015).


In takaice miki Aalimah sai da ta zama kamar wata ‘yar karamar Farfesa (Professor) a kan lalurar Mu’azzam sabida karatu da bincike, inda ta fahinci komai ta gane kan komai, ba tare da Mu’azzam din ya san tana yi ba.


Abu na gaba da ta ke son yi shi ne, ganawa da Dr. Nebrass Sheldon, ta kuma rasa hanyar yin hakan, tunda ba ta ganshi yana zuwa gidan su ba, ba ta kuma san a ina suke haduwa ba shi da Mu’azzam din. A lokacin da ta fahimci behaviour din, sai ta ga ba maraba da yadda Aboulkhair ya labarta mata. Ta dai samu faffadan bayani ne da cikakken ilmi akan lalurar.
Aalimah ta manta da wani abu wai shi ‘AURE’ dake tsakaninta da Mu’azzam, sai motive na ‘yan uwantaka. Sosai ta ke jin son ta tallafi rayuwar shi a haka, a hakan da yake da wannan lalurar, yadda Halima ta kasa. Ta ke ji a ranta cikin kowanne hali, za ta iya jimirin zama da Mu’azzam sabida biyayyar iyaye da kauna ta jini.
Ba abin da Uncle Ishaq bai yi mata a rayuwa ba! Ta tuno dauki ba dadin da ya dinga yi da matarsa a kanta. Ranar da ya gane Mummy ta hanata zuwa makaranta har na tsawon sati biyu ta maida ita boyi-boyin gidanta. In bata manta ba a ranar har hawaye yayi a kanta. Ya rungumeta a jikinsa kamar shi ya haife ta ya bata hakuri kamar zai ciro zuciyar sa ya bata don tayi hakuri ta cigaba da zama da su. Ya yi mata komai a rayuwa daga zamanta a gidansa har zuwa yau data auri Mu’azzam. Da yardar Allah jininsa bazai tozarta a hannunta ba.
Ta ji tana son shiga cikin rayuwar Mu’azzam ta kowanne bangare, ta fahimce shi yadda Aboulkhair ya fahimce shi, ta taimaka wa lafiyarsa yadda Aboulkhair ke taimakawa, ta kawo murmushi akan fatar bakinsa, ta kawo sauyin rayuwa mai tattare da nishadi. Duk da ba ta da shaidar ilimin da ya danganci wannan lalurar a yanzu, tana da fahimta a kai daidai gwargwado. Tana so ta shiga rayuwarsa ta ko ina yadda Aboulkhair ya shiga. Ta taimaka ta ko’ina, yadda Aboulkhair ke taimakawa. Har ake ganin murmushi a fatar bakinsa idan har suna tare, tana yiwa kanta kwadayin samun irin wannan matsayin a wurin Mu’azzam idan har zata samu dama! Tana rokon Allah Ubangiji ya dafa mata, ya agaza mata a bisa wannan niyya tata ta alkhairi akan mijinta.


******
Misalin karfe biyar na yamma Mu’azzam ya dawo office. Bai tsaya a ko’ina ba, kai tsaye cikin yanayin tafiyarsa mai kama data jinin sarauta ya soma taka matattakala ya haye upstairs don isa ga dakin barcinsa.
Bai dade da shiga ba ya ji Aalimah tana kwankwasawa. Wani abu da ba ta cika yi ba a tsayin watannin da suka kwashe tare, wato shigo masa daki in ba da kwakkwaran dalili ba, sai dai ta girka masa delicious ya ci ya more, in ba ta da lafiya ya kan kai ta asibiti, wanda sau biyu ne ma kawai tayi ciwon mara, ta fada masa abubuwan da ta ke bukata na cefane ya sa Harrison ya kawo mata. Ya lura bata komai yanzu sai karatu a library wanda bai san na menene ba. Ta dauki hankalinta da lokacinta kacokam ta mallakawa library, ko dakinta ya shiga zai ganta da glass tana karatu a ipad dinta, abinda ke gudana a tsakaninsu kenan a tsayin watannin su masu dan dama tare.
A tunaninsa tun wancan zuwan nata dakinsa da ya gaya mata maganar da ba ta taba zato ba, sanda tace ya maida ta makaranta ko aikin ta na pharmacy ba ta kara gigin zuwa dakin shi ba, don ta fahimci kamar ya gama karbar auren nasu, tana kuma tsoron abinda zai biyo bayan hakan, don haka tun daga lokacin ta janye jiki ta koma rufe jikinta a cikin hijabi yayin zirga-zirgar ta a gabansa, a falo ne ko a madafi. Duk wannan kwalliyar da ake cancadawa an daina. A wurin sa hakan ba karamin taimako ya zamo a gare shi ba, sabida ganin da yake yawan yi mata da dan kusancin da ya soma ginuwa a tsakaninsu ya soma birkita shi, ya gaya wa Nebrass yana so ya kara dose din magungunansa, kamar fa sun daina aiki a jikinsa kwanakin nan, don ya gaya masa yana kasa barci a yawancin lokuta da tunanin matar sa kuma ba ya son ya rabe ta. He is afraid of his new mood and the consequences.
Sun zauna sun yi magana heart-to-heart shi da likitocinsa, sun tabbatar masa zai iya rayuwar aure fa ya daina zancen a kara dose, amma ba lallai matar ta samu yadda ta ke so daga gare shi ba muddin yana cigaba da shan anti-androgens kamar yadda ya saba, bi ma’ana, ba lallai ya gamsar da ita a shimfida ba sabida karfin magungunan da suke bashi. Wadanda aikinsu shine kashe tasirin sex hormones a cikin jikinsa. Idan kuma aka dauke shansu shi ma matsala ne babba ga lafiyarsa, career dinsa da zaman lafiyarsa, don al’amarin zai zamo out of control. He will need nothing but sex. Mu’azzam ya gaya musu ya zabi ya zauna da ‘yar uwarsa a haka, cikin zabin da suka bayar duka babu mai sauki, babu wanda za’a ce gara shi. Tun dai ita ba ta nuna kosawa da zaman nasu a haka ba. Kuma da ma ba soyayya ce tsakaninsu ba.
Yana da tabbacin ta san lalurarsa, duk da ba su taba yin zance makamancin wannan da ita ba. Amma ai ta zauna da ABOULKHAIR.
Shi ya lura ma yanzu hankalinta ba ya kansa. Yana ga karance -karancen ta da rubuce-rubucen ta kamar mai rubutun thesis. A ganinsa zata fi kyau da zama malamar makaranta ba mai harhada magunguna ba.


To sai kuma yau da ya ji ta tana kwankwasa kofar sa. Bayan shigarsa dakin da mintuna biyu, ko zama bai kai ga yi ba, don haka daga inda yake tsaye ya bude kofar. Aalimah rike da zazzafan coffee cikin kofi mai zurfi ta dora akan karamin faranti na tangaran ta mika masa. Karba ya yi ya koma cikin lallausar kujerar dakin kwaya daya tal ya zauna. Itama ta zauna a gefensa dab da shi. A zuciyarsa gode mata yake yi sau ba adadi. Ta yi matukar sanin abin da yake bukata ta fannin ci da sha. Ta kuma san abin da ya kamata ta bai wa mutum ya ci ko ya sha a yanayi da lokacin da ya dace.
Ko da ya zauna coffee din ya hau sipping duk da zafinsa ba tare da ya cire takalman kafafunsa ba.
A yadda Aalimah ta sa a ranta daga yau ne za ta canza akalar rayuwar ta da Mu’azzam tunda ta gama research dinta. Ta gaji da wannan rayuwar da suke yi mara focus. Hijabi ne a jikinta dogo daga sama har kasa. Hannu tasa ta cire shi gabadaya ta ajiye a hannun kujerar da suke zaune. Saukowa ta yi ta gurfana a gabansa, ta debi kafafunsa ta hau cire masa takalman, ta gama ta hau zare masa safa (socks) ta debe su ta kai shoe rack, wato ma’adanar takalmansa. Ta jefa safar cikin kwandon kayan wanki.
Har ransa ya ji dadin wannan taimako data yi masa amma ko akan fuskarsa bazaka gane ba. Ba ta tsaya a nan ba, toilet dinsa ta wuce kai tsaye ta hada masa ruwan wanka mai dumi daidai da yanayin da garin ke ciki. Ta zuba turaren wankansa na desire dunhill ta aje masa towell a kusa, sannan ta fito.
A inda ta barshi ta same shi ko motsi bai yi ba yana mamakin ta da karfin halinta. Tunda yake a rayuwarshi ba wanda ya taba shigar mishi toilet including Aboulkhair. Tana fitowa tsugunnawa ta yi a gabansa hannunta akan kafafunsa cikin sanyin murya da kaskantar da kai ta ce,
“Yaya Mu’azzam na hada maka ruwan wankaâ€.
Cikin idanunta ya dube ta yana dan zaro ido na mamakin wannan canji da yake ta gani yau a tare da ita, bai ga komai ba cikin idanun ta sai tsantsar kulawa gare shi. Ko da ya mike don rage kayan jikin sa sai ta fita. Duk karfin halin ta da kankanbar ta ta kasa tsayawa. Murmushi yayi shi kadai sannan ya sunce ya shiga. Kafin ya fito daga wankan ya yi sallah, ta hada lafiyayyen lunch ta kawo masa.
Ta sanshi da son lemon Sangria Mocktail, ta san shi ne abin da ya tare ta da shi a zuwanta na farko gidansa tare da Aboulkhair. Bazata taba maanar ba. Ranar da ta fara ganin c a rayuwarta. Don haka tun safe ta duba procedure din yadda ake yi a yanar gizo, ta zage ta hada masa shi da kyau da ban sha’awa.
Sanda ya fito tawul ne mai fadi daure a jikinsa iya kugunsa, da wani a hannun sa yana goge

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login