Showing 51001 words to 54000 words out of 126031 words
Chapter 18 - Aalimah Complete 1,2,3,4 Free Book by Takori .txt
canja, wata sabuwar Zulaiha ce wannan ba wadda ya dade da sani ba.
Ba karamin jin dadi da kwanciyar hankali hakan ya haifar masa ba. Har wata ‘yar kiba ya yi a dan tsukin. Gidan Ishaq Raazee a garin Boston ya koma wani sansani na zaman lafiya da fahimtar juna. A gefe soyayyar Aalimah da Abulkhair na kara gawurta. Duk da a waya kawai suke tare da juna.
A wannan satin su Aalimah suka samu hutun karshen shekara, maimakon yadda Daddy ya tsara da farko, cewa ita da Gumsu za su zo, sai ya hado har da Basma. Za su yi sati biyu a Nijar su wuce Nigeria gidan su Aalimah su karasa hutunsu.
Murnar zuwansu a wurin al’ummar gidan ba a magana, kada Inna Kasisi ta ji labari. A dakinta Gumsu ta sauka maimakon na yayarta Bintou.
Inna Bintou na ta mata tsiya wai ta zabi suruka ta barta. Kan ka ce me ye wannan? Gidan ya cika da ‘yammatan family din. Su Balkissa da Roumana mutanen Aalimah. Aka shiga yawo gida-gida gaida dangi. Kwanansu uku a Niamey suka wayi gari cikin shirin tafiya Arlit, za su raka Gumsu ganin gida. Wannan karon ma Hamoud ne ya kai su, sun kwana biyu a can suka wuce birnin Agadez gidan su tsohon mijin Gumsu, ganin ‘ya’yanta, wadanda ke hannun kakanninsu.
Aalimah sai da ta yi hawaye lokacin da ‘ya’yan Gumsu, Adizatou da Jamilatou suka rungume mahaifiyarsu suna kukan ba za su kara yarda ta tafi ta barsu ba. Da ‘yar shekara takwas da ‘yar shekara shidda. Duk kayan da ta sayo musu sun ce ba sa so ita suke so su bi, Basma kasa jurewa ta yi sai da ta gaya wa Daddy a waya. A daren ranar ya kira Gumsu ya ce, idan kakannin yaran za su yarda su taho tare da su, zai yi musu visa. Kememe dattijan sun ki, sun ce su kadai gare su da za su dinga tuna musu dansu Jibreel suna yi masa addu’a, Gumsu ta yi hakuri.
Yaran na kuka su Aalimah na yi suka bar Agadez a washegari. Gumsu ta yi dauriya sosai.
Soyayyar Gumsu da ‘ya’yanta ita ta sa Aalimah kasa cika sati biyu a Nijar. Kwanansu goma hankalinta ya yi gun nata iyayen, da yau shekara daya da kwana goma rabonta da su. Yayansu Hamoud ya sako su a jirgi mai tasowa daga Niamey zuwa Kano, Nigeria.
6/28/21, 7:33 AM - Buhainat: ADAMU DANKOLI
¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥¥
£££££££££££££££££££
******
Garin Kanon-Dabo, bai canza wa Aalimah da komai ba. Sai karin tsayin gine-gine kawai. Sun tadda Aboubacar ya zo daukansu don tun tasowarsu Hamoud ya gaya masa. karon farko wani miracle ne ya afku tun a filin jirgin saman Malam Aminu Kano. Basma ta kalli Aboubacar Yayan Aalimah, ma’aikacin bankin GT a halin yanzu, ta kara kallonsa ba ta iya kara yi masa kallo na uku ba, sabida tsanantar bugun zuciya a gare ta.
Suna tafe a sabuwar motar Aboubacar kirar Honda Accord da bai fi watanni biyu da sayenta ba a hanyarsu ta zuwa gida, Aalimah nata yi masa karadi, amma hankalinsa ba ya kanta. Basma yake satar kallo ta madubi, wadda duk kaudi irin nata ta ji yau ta kama kanta. Maimakon Aboubacar ya dauki hanyar B.U.K Road don isa ga gidansu wanda ke cikin rukunin gidajen malamai na sabuwar jami’ar Bayero sai ta ga ya dauke kan motar ya yi Nassarawa, billa can, billa nan sai ga su a kebantacciyar unguwar Sultan Road.
Aalimah ta ce, “Yaya Aboubacar ina za mu je ne?â€
Bai juyo ya kalle ta ba ya amsa, “Gidaâ€.
Daidai lokacin da ya sanya hancin motar a gate din wani kyakkyawan gida, wanda da ganinsa ka san sabon gini ne. Ba ta gama wannan mamakin ba ta hango fitowar kannenta a guje. Sultana a gaba, Suhaima biye da ita, Sabrina a bayansu. Mama ma ta kasa hakurin shigowar Aalimah, fitowa ta yi kofar shiga falon sai murmushi ta ke yi. Kasa jiran Aboubacar ya gama parking, Aalimah ta yi ta balle murfin motar ta fice saura kadan ta fadi. Tun daga nesa ta bude dukkan hannuwanta su Sultana suka shiga bakidayansu ta rungume su. Daga bayan wuyansu ta hango Mama sai kallonta ta ke tana murmushi. A kokarin mikewa ta kusa faduwa, sai da Basma ta rike ta ta mikar da ita. Ta karasa da gudu ta rungume Mamanta. Maman ta rike ta sosai a jikinta tana fadin, “Aalimah ta! Sannu da zuwaâ€.
Aboubacar ya karaso dauke da jakunkunansu, sai fada yake yi wa Aalimah, wai sai ka ce yau ta taba ganinsu. Shi ai ba ta yi masa irin wannan tarbar ba. Ga bakuwa ta kyale kamar ta manta da ita. Wannan karon ne Basma ta yi magana tana satar kallonsa komai da yake yi burge ta yake, very gentle da shi.
“Ni ba bakuwa ba ceâ€.
Ya juyo ya dan kalle ta ta saman idonsa, ya ce, “Ke da ki ka zo kasa ya kasa zuwa na farko ya kamata a karrama ki, duk da gidanku neâ€.
Murmushi ta yi, Aboubacar ya yi saurin dauke kansa sabida wasu abu masu kama da electrical shocking da suka fito daga cikin murmushinta zuwa idanunsa.
Mama ta saki Aalimah ta kamo hannun Basma ta ja ta suka shige har bedroom dinta su Sultana suka shiga hidimar shirya abinci a dining. Aalimah sai bin gidan ta ke da kallon tsoro da mamaki, don kuwa ta san mahaifinta malamin jami’a ne, bayan wannan ba shi da wata sana’a. A cikinta suke ci suke sha, suke zaune cikin rufin asiri. Ko wata sana’ar ya samu bayan barinta gida bai isa a ce ya tara abin da zai mallaki wannan gidan cikin shekara daya ba. Mama sai ina-ta-ka-saka-ina-ta-ka-aje ta ke yi da Basma, ita kuma babu bakunta sai zuba hira suke da su Sultana, kannen Aalimah sun ba ta sha’awa, ga su nan kusan kai daya sabida bai fi shekaru bibbiyu ne a tsakaninsu ba. Sultana ce babba, shekarunta goma sha biyu, Suhaima goma, Sabrina takwas.
Mama ta tambayi Basma abinci za ta fara ci ko wanka? Ta ce, “Wankan dai Mama. Jikina fa har ya fara bashiâ€.
Aboubacar ya dago kansa daga kan wayarsa dariya ta kama shi. Ko a jikinta, ta ce, “Mama kada ki so in matso kusa da ke, tun a Nijar ya fara bashiâ€.
Dariya Mama ta yi ta nuna mata Aboubacar da ya zuba mata ido zaune a kan stool din madubi ta ce,
“Basma Yayanku yana jin ki fa!â€
Ta juya da sauri suka yi ido hudu, da gudu ta kwasa ta yi toilet. Ya girgiza kai ya fita yana dariyarta.
A ransa ya ce, “Yar gayu da ke Basma! I’m sure in na matso kamshi zan jiâ€.
Mama ta kama hannun Aalimah cike da farin ciki, ta ce, “Come and seeâ€.
Gidan suka zagaye tana nuna mata ko’ina. Self content family house wanda da ma mamakinsa ke damun Aalimah. A karshe suka dire a dakin da ke kallon na su Sabrina. Mama ta sa mukulli ta bude, Aalimah ko Mama ba ta fada ba, ta gane dakinta ne. Chinese bed madaidaici, wardrove din dakin ta jikin bango ce, sai madubin gadon da stool na kwalliya. An shimfide dakin da carpet ruwan bula mai duhu, kalar labulen dakin. A gefe teburin karatu ne da na’urar kan tebur (desktop), na’urar sanyaya daki na ta aiki gwanin dadi, kai ka ce iyayen Aalimah ko kuma wanda ya shirya dakin bai da niyyar aurar da ita watarana. RungumeMama ta yi don murna, sannan ta ce, “Shin don Allah Mama wa ya saya wa Daddy gidan nan?â€
Mama ta ce, “Abin sirri ne Aalimah, kawai ki yi godiya ga Allah, ki kuma yi wa kowaye addu’ar Allah ya ba shi duk abin da yake so duniya da lahiraâ€.
Basma ta shigo tana fadin, “Mama dakin Aalimah ai ya fi naki kyauâ€.
Dariya ta yi ta ce, “Kin santa da son blue shi ne Aboubacar ya sa komai blue ba mu dade da dawowa gidan baâ€.
Ta ce, “Shi kenan in aka yi mata aure ni sai in dawo. I love the house da mutanen cikinsaâ€.
“Mutanen gidan ma bakidayansu suna sonki Basma, suna maraba da keâ€. In ji Mama.
Aalimah ta harare ta, “Ni ba auren da zan yi, ke dai za a yi wa sai a kawo ki gidan nan dinâ€.
Mama ta fice ta barsu tana fadin, “Duk tare za mu aurar da ku mu huta. Kun zama wasu gandama-gandaman ‘yammata in a nan ne ina za a bari ku kara shekara guda?â€
Dariya suka yi dukkansu don a wajen Mummy Zulaiha Basma har gobe ba ta wuce goyo ba, in har za ta iya goya tan.
Sai dare Daddynsu ya dawo su Aalimah suka tadda shi a falonsa. Ya kasa boye jin dadinsa na ganin yadda ‘yarsa Aalimah ta koma. Ya yi maraba da zuwan Basma har fiye da Aalimah. Wannan ya nuna da gaske dan uwan nasa yake da ya ce zai gyara kuskurensa na baya. Nan suka zauna hira bayan sun ci abincin dare tare har Yaya Aboubacar, Basma ce ta fara tashi ta barsu sabida barci da ya soma dibanta.
Aalimah da iyayenta sun raba dare suna hira, labarin zamanta gidan kawunta a America ta ke ba su, wanda duk ciki babu wanda ba alkhairi ba, ko da kuskure da tuntuben harshe ba ta ce Mummy ta taba yi mata rashin kyautawa ba. Sai labarin yanayin karatunta da yadda ta tsinci kanta a matsayin dalibar jami’ar Boston wanda har gobe ta ke gani kamar mafarki. A cikin maganganunta tana ambaton Abulkhair da kyawawan halayensa da yawan kyautayinshi gare ta. Idan ka kalli kwayar idanunta kauna ce zallah. Daddy bai gane komai ba, amma Mama ta sanya wa maganganun Aalimah masu yawa a kan Abulkhair ayar tambaya.
Tambayar da Daddy ya yi wa Aalimah ta dan jefa ta a tunani.
“You praises Abulkhair so much,(kin yabi Aboulkhair da yawa) amma ko sau daya ban ji kin ambaci Dana ba, bayan ya fi shi kirki, ya fi shi son zumunci. Shi Abulkhair bature ne irin Babansaâ€.
“Wa kenan ka ke nufi Daddy?†Ta tambaya cikin dan yamutsa fuska na rashin fahimta.
“Dana MU’AZZAM!â€.
“A ina yake? Ni ban sanshi baâ€.
Cikin mamaki Mama da Daddy suka hada baki, “Mu’azzam fa Yayan su Basma, wanda Abulkhair ke bi a haihuwaâ€.
Tunani Aalimah ta fada don son gano wanda suke nufi, amma iyaka tunaninta bai ba ta ba. Girgiza kai ta yi, “I’ve never saw him (ban taba ganinsa ba)â€.
Daddy ya ce, “Mu’azzam din?†A cikin muryarsa akwai mamaki.
Aalimah ta ce, “Ni ko sunansa ban taba ji ba, ban da yanzu a bakinku. To ko shi ne wanda su Basma ke yawan fadin yana wani gari Las Vegas?â€.
“An yi haka! A can yake. To amma ko a can yake aiki ya za ki ce ba ya zuwa gidansu?â€
“Wallahi Daddy bai taba zuwa ina nan ba, su Mummy din ne ke zuwa inda yake. Mummy tana zuwa sosai. Shi ma Daddyn kwanaki na ji ya je duba shiâ€.
Da haka suka bar zancen, Mama na fadi cikin ranta,
“Wani abu sai bature. Iyaye ne ke zuwa gaida dansu ba dan ne ke zuwa gaida su ba!â€.
Sabanin Mama shi ‘yar hirar nan da ta fito daga bakin Aalimah a kan Mu’azzam a zurfin tunani ta jefa shi. Ishaq ya dade yana boye masa abubuwan da suka shafi Mu’azzam tun daga kan auren katsahan din da suka yi masa shekarun baya, dawowar matar daga America da karewar auren. Tun daga lokacin yake cewa ba shi da lafiya ya dinga sa shi a addu’a bayan shi bai ga wani alamun rashin lafiya tare da shi ba, ko a watanni uku baya ya zo Nigeria. Ya siya masa wannan gidan da yake ciki, ya ce ya bar New site gidan gwamnati ne in ya yi retire zai bukaci gidan kansa gara ya kama gidan tun yanzu shekaru turawa suke yi, me ya hana Mu’azzam aure har yau?
In rabuwa ce ta shiga tsakaninsa da wadda ya aura, me ya hana shi sake aure? Tukunna ma wane rashin lafiya ke damunsa da Baban nasa ke dauka da muhimmanci haka? Har da zai goyi bayansa ya ki yin aure? Ya sa a ransa gobe zai yi wa Yayansa Ishaq Raazee wadannan tambayoyin ko da ba zai amsa masa ba.
Washegari Yaya Aboubacar ya ba su layin wayar Mtn dukkansu. Godiya sosai suka yi, musamman Aalimah, Basma na daga gefensa zaune, Aalimah da Sabrina na gefe tana mata kalba a dogon gashin kanta. Ya sassauta murya yadda su Aalimah ba za su ji ba, ya ce da Basma,
“Sai ki ji dadin kiran saurayinkiâ€.
Da sauri ta dago suka hada ido, ba shiri ta dauke idonta. “Ya Allah!†Basma ta ce a hankali idonta a kasa, “Believe me, I don’t have (ka yarda da ni, ba ni da shi)â€.
Aboubacar wani irin sanyi ya ji a ransa, amma nan take zuciyarsa ta shiga cautioning din shi, tana gaya masa ya danne ko ma mene ne yake cin ransa a kan Basma, ta fi karfinshi. An haife ta a U.S, ta girma a can, rayuwarta gaba daya tana can. Shi ba kowa ba ne face karamin ma’aikacin banki. Gidan da suke ciki a yanzu ma Yayanta ne ya saya musu. Ya aure ta ya kai ta ina? Ban da giggiwa irin ta zuciya?
A sanyaye ya tashi ya bar falon. Basma ta bi shi da kallon mamaki da wata irin ragaita cikin kwayar idanunta.
Sosai ya janye jikinsa da zama cikin gidan. A ganinsa ganinta da yake yi ne yake jaza masa komai. Basma kuma rashin ganinsa a cikin gidan sai ya sabbaba mata rashin walwala, duk ta zama wata irin sukuku. Har Aalimah ta soma zargin ko zaman gidansu ne ba ta so. Ko ta kasa jure irin tasu rayuwar? Ko kuma tunanin gida ne ya addabe ta? Da ta ishe ta da tambaya ta ce kome ta ke tuhumarta ta je ta yi ta tuhuma, ta yi abin da za ta yi, amma ta daina damunta da magana. Haushi ya kama Aalimah ta ce, “To ko in dawo da booking dinki jibi ki koma ni na taho daga baya?â€
Saura kadan ta mare ta, Aalimah na iya ganin hakan cikin idanunta.
Dariya ta yi, ta ce, “To Basma na kasa gane miki. Kin zo da walwala kwana biyu kin koma min hakaâ€.
A fusace Basma ta ce, “Lokacin da ki ka fara son Monsieur Aboulkhair, na takura miki da tambaya? Ba idanu na sa miki har na gano da kaina ba? Amma ni kin sa ni gaba kin sa min ido, har da sharri da kazafi. Wai na gaji da Najeriya. To in gajiyar na yi kunyarki nake ji da zan kasa gaya miki?â€
Aalimah ta kama baki tana kallonta, “Me ya kawo wannan tambayar?â€
“You want to know?†Basma ta fada a raunane.
“Yes, I doâ€. Aalimah ta amsa.
Sunkuyar da kai ta yi.
“Yaya Aboubacar ya daina shigowa gidan nan saboda ba ya son ganinaâ€. Sai hawaye.
Aalimah ta karasa kusa da ita sosai, tuni ta fahimci matsalar ‘yar uwarta. Hannayenta biyu ta kama, “Kina nufin damuwarki kenan?â€
Basma ta daga kai, “Mu kuma kaddararmu kenan, son ‘yan uwanmu?â€
Da sauri Basma ta cira kai ta dube ta,
“Sonsa nake yi?â€
Murmushi Aalimah ta yi, “Ask yourself, not me. It’s your heart, not mine (tambayi kanki ba ni ba, zuciyarki ce ba tawa ba)â€.
A hankali Basma ta zare hannayenta daga na Aalimah ta juya mata baya, “Idan dai yadda na damu da lamarinsa din nan da rashin ganinsa shi ne so, Aalimah ina son Yayanki…â€. Kalaman da suka shiga kunnen Mama kenan, ta juya ta fasa shigowa kada Basma ta gane ta ji zancenta.
Aalimah ta dafa kafadunta, ta ce, “Basma!â€
Ta juyo ta dube ta cikin damuwa, “Idan har za ki iya zaman Nigeria auren Yaya Aboubacar ya fi komai sauki a gare ki. In ba za ki iya ba ne da matsala. Amma kada ki bari ya gane kin damu haka. Ki dawo cikin walwalarki, tun zuwanmu ina lura da shi shi ma ya damu da lamarinki. Ki bi shi da duk ta inda ya billo, insha Allahu tsakaninku alheri neâ€.
Da sauri Basma ta rungume Aalimah.
“Ni ko a jeji ne zan iya zama da shi Aal. Ba Nigeria ba, ko cikin bukka neâ€.
******
Ya aka yi-ya-aka-yi? Cikin hira Aboubacar ya gaya wa Mahmoud zuwan Aalimah. Kwanansu bakwai sai ga shi a Kano. Gidansu na New site ya fara zuwa, inda aka gaya masa sun tashi. Ya kira Aboubacar a waya, shi ya kwatanta masa sabon gidansu da ke Sultan Road.
‘Yammatan biyu na zaune a falo sun dau wanka, kowacce da abin da ta ke yi. Basma tashar Arewa 24 ta ke kallo ana diramar Dadin Kowa, sosai abin ya dauki hankalinta yadda ake nuna typical Nigerian life da ba ta sani ba. Aalimah chatting suke yi da Abulkhair, wani abu da ya zame musu jiki tun zuwanta saboda ta roke shi kada ya kira ta ko sau daya, ba ta so Mama ta san akwai wani abu a tsakaninsu, za ta shiga damuwa a kan karatunta. Za ta yi tunanin ko ma ba karatu ta ke ba, tunda a gidansu ta ke.
Abulkhair ya fahimce ta, kuma shi ma yanzu ta kansa yake yi, ya shiga shekara ta biyun karshe a karatunsa, ko lokacin da yake chatting din da ita ma squeezing dinsa yake yi, saboda yana so ko me ta ke ciki ya sani, kada nisa ya nesanta shi da ita.
Aboubacar ya shigo, Mahmoud a bayansa, bayan sun yi sallama. Aalimah ta amsa ba tare da ta dago ba, komin canjin da rayuwa za ta kawo Mahmoud ba zai kasa gane Aalimah ba. Jikinta ne ya ba ta ana kallonta, kuma kamar yaya Aboubacar ba shi kadai ba ne ya shigo. Da sauri ta cira kai, suka yi ido hudu da Mahmoud. Sai da gabanta ya fadi, yana nan a yadda ta sanshi sai dan gogewa da ya yi. Yana sanye da shudiyar shadda kansa babu hula. Ajiyar zuciya ta yi ta janyo mayafinta a gefe ta lulluba, ya samu waje kusa da Aboubacar ya zauna, jikinsa a sanyaye. Yanzu ya kara tabbatarwa ya rasa Aalimah a bisa dalilai da dama.
Aboubacar da Basma sai kallon-kallo, kwana uku kenan bai shigo gidan ba sai yau a dalilin abokinsa ta ganshi. Aalimah ta rusuna ta gaida Mahmoud cike da jin wani irin nauyi domin har gobe Mahmoud