Showing 60001 words to 63000 words out of 126031 words
Chapter 21 - Aalimah Complete 1,2,3,4 Free Book by Takori .txt
ma matan banza yake kai wa gidan, wanda ko gaida iyayensa ba ya yi, ba ta zaton masa wata rayuwa mai albarka. Sosai ta ke jin rashin kaunarsa a zuciyarta. Ta tuno kannensa da yadda suka tsane shi, da kuma yadda kullum zancensa ya ratso cikin hirarrakinsu suke kiransa ANNOYING son of Mum. Kalmar da ke da tarin ma’anoni masu yawa daidai da fahimtarsu. A saninta kalmar annoying na nufin irritating, infuriating, tiresome kuma troublesome. Da ta tattara ma’anonin wadannan kalmomi, hadida tattara su wuri guda in a nutshell suna nufin Yayansu Mu’azzam mai yawan fusata ne, mai tayar musu da hankali (ta hanyar yi musu fada), mai tilasta su su yi abu ko da ba sa so, mai yawan damuwa a karan-kansa, kuma mai tarin matsalolin rayuwa.
Idan ta jimlace wannan fassara a ma’auni na hankali da tunani da zurfin iliminta, za ta iya fahimtar lamarin ba komai ba ne; is simply a subject matter that others around him are not understanding what he is going through. Ita ce makalar da ke tattare da rayuwar Yayansu Mu’azzam, har ta kai ta kawo cewa, he lack positive emotions like happiness and laughter… wanda kannensa suka fassara shi yadda suka ga dama, ba tare da bin ba’asin dalilan da suka mayar da rayuwar tasa hakan ba, ko abin da ya janyo masa wannan rayuwar da yake ciki. everything has CAUSE! Wato komai yana da tushe.
Haka kawai ta ji jikinta ya yi sanyi, zuciyarta ta dugunzumarta da son sanin WANE NE MU’AZZAM??? Za ta bi kwakkwafi ta ji mene ne cikin rayuwarshi haka da ya maida shi hakan ta hanyar mijinta, mafi kusanci da shi ko da hakan na nufin canzawarta daga mai harhada magunguna zuwa ethnographer ne. Shebecame extremely intrigued.
Ta yi nisa cikin wasikar jakinta ta ji yatsun Aboulkhair saman fuskarta yana shafa kuncinta a hankali, ashe ya jima da kashe motar a kofar gidan Mu’azzam.
“Mrs. Thinker tunanin me ki ke yi? Ga mu gidan Mr. Mu’azzam Raazi, taho mu jeâ€.
Sai kuma ya dakata alamar ya yi mantuwa, “In mun shiga kada ki zauna a kusa da ni, kunyarsa nake ji sosai, har fiye da Daddy. Ko hannunki ba zan kama baâ€.
Dariya ta kama Aalimah matuka, da ma akwai wanda Aboulkhair ke jin kunya a duniya? Ta ga dai a gaban Mummy ya ce da Gumsu ta dawo dakinsa su kwana, ita ya bari da ji masa kunyar. Girgiza kai ta yi, ta murguda baki, ta ce, “In ka ce masa ma ba sona ka ke ba sadaka ta aka ba ka, duk daidai neâ€.
Hannu biyu ya dora a ka yana leken idanunta, amma ta ki yarda ta kalle shi, ya ce,
“Ya fi ki sanin yadda nake son naki, da wahalar da na sha kafin in same ki. Ba don shi ba da ba’a kawo yau ba, da tuni na watsar da karatu na rungumi Aalimah a cikin gida. Da ma karatun don shi nake yinsa, kuma with his support and encouragement, yau na tsira da ku bakidaya (ita da karatun)â€.
Murmushi ta yi tana kici-kicin fiddo kwandon abinci daga bayan motar. Ya karbe ta yana fadin, “Idan ina kusa, ko Babyn mu ba za ki dauka ba balle wasu kayaâ€.
Wata harara ta sake masa, “Wai baby, har yaushe akai daren da garin zai waye?†Ta fada a karkashin zuciyarta, tana dubansa ta kasan ido cike da so da kauna.
Aalimah ta daga ido a hankali tana kallon kyakkyawan gidan da aka kira mallakin Mu’azzam Raazee ta hanyar rubutawa a jikin kofar shiga gidan, wanda ke cikin kebantacciyar unguwar HillsboroughEstate, mai hawan sama da kasa. Irin gidajen da suka kira ‘Fairfield Terrace’ wadanda sai dai mallaka ba dai haya ba (rent). Wani mutum yana goge motoci da ya juyo, sai ta gane shi, shi ne direban da ya debo su daga airport ya kuma kai su Mummy gida. Da fara’a ya gaishe su, ya karbi kwandon hannun Aboulkhair ya bi bayansu.
A falon da suka fara tararwa Aboulkhair ya ce ta zauna ya hau sama ya kira shi. Da gudu-gudunsa yake hade steps biyu-uku yana kiran, “Mu’azâ€. Har ta daina ganinsa. Ta shiga wurga ido tana kallon wani irin English parlour da ko a talabijin ba ta taba ganin mai tsari da kayatuwarsa ba. Ta fahimci gidan ba mai girma ba ne da yawa, amma a yalwace yake. Komai fari tas a cikin falon, hatta curtains da kujerun leather duka farare ne kal-kal! Tana nan tana baza ido ta jiyo takun Aboulkhair yana saukowa, amma ba ta ji taku na bayan nasa ba, duk da cewa su biyu suke saukowa. His own steps ba ya making sound sabida babu takalmi a kafarsa. Kuma ma dai hatta tafiyarsu ta bambanta, taku yake kamar basarake.
Kallo daya ta yi masa ta ji ba za ta iya ci gaba ba, kada idanunta su samu rauni, ko nakasu.
Domin kwarai kwarjininsa da cikar zatinsa ya dusashe ‘yan idanunta. Ga wata irin kamala da charismatic personality. Da ganinsa ka ga ruwa biyu (Nigeria da Niger). Cikin iyayensa bai dauko mutum daya ba, mixed appearances dinsu ya debo sabanin Aboulkhair fari tas! Kalar abzinawa masu tarin sumar kai, Ishaq Raazee bakidaya.
Shi Mu’azzam kansa babu tarin suma, wani irin saisaye ne mai aji. Kananan kaya ne a jikinsa (farfetch) army green colour daga T/shirt har wandonta. Wani irin agogo daure a damtsen hannunsa mara walkiya, sai daukar hankali samfurin ‘Blooming Dale’s’ ruwan azurfa. Ya fi Aboulkhair tsayi, ya fi shi kauri. Alamu duk sun gama nuna mata he is living in an affluent life of the western world wanda a duniyarta ba ta san da irin rayuwarshi ba, ko mutane masu irin personality dinsa.
Duka wannan observations Aalimah ta yi su ne a kallon farko da ta yi masa, daga haka ba ta kara ba. Fargaba ma ta shiga ta yadda za ta bai wa wannan handsome GENTLE din tuwo, Aboulkhair ya fi ta gaskiya. Ji ta yi duk ta muzanta, ta soma Allah-Allah su bar gidan don ko a fuskarsa ba ta hango wani maraba da zuwanta gidansa ba.
Sunkuyar da kanta ta yi tana wasa da yatsun hannunta. Tana jin maganganun da suke yi shi da Aboulkhair sai Aboulkhair ya fadi biyar bai ba shi amsar biyu ba, kamar mai ciwon baki. A karshe ta ji zaman mutum a gefe ya ja kujera karama ya zauna yana fuskantarta. Kamar daga sama ta ji yana mata sannu da zuwa cikin harshen Hausa, sannan ya tambaye ta ya ya bakunta, kuma ya ta samu kanta a Las Vegas?
Zamowa ta yi daga kujera tana amsawa, sannan ta gaishe shi cikin nutsuwa.
Ya ce, “Koma kujera ki zauna, ni ba surukinki ba ne, dan uwanki ne. Ya ya Kawu Mansour, Mama Asi da Aboubacar?â€
Mamaki kamar ya zauta Aalimah, sai kuma ta tuna su ma mutanen gidan nasu ai sun sanshi, har mamaki suke da ta ce ita ba ta sanshi ba. Kafin ta samu zarafin amsawa ya mike ya bi wata kofa. Sai ga shi da lemon Sangria Mocktail cikin kofin gilashi biyu, ya mika mata daya ya zauna da daya a hannunsa yana sha a hankali. Aboulkhair ya yi narai-narai da fuska, wai shi ba a ba shi ba.
Murmushi ya yi, ya ce, “Na dade da yayeka, ka bar ni in yi wa bakuwata barka da zuwaâ€.
Ita dai har zuwa lokacin duk da ya saki fuska yana kuma kulata ta kasa sakin jikinta. Ta rike kofin mai cike da kananan fruits kamar fruit-salad cikin ruwan grape juice, sanyinsa na ta ratsa tsokar hannunta. Sosai ta ke so ta sha ko don ta ji ya dandanonsa yake, amma ba za ta iya sha a gabansa ba.
Ya tambaye ta abin da ta karanta, ta gaya masa. Sai ya juya ya dubi Aboulkhair yana masa hararar wasa,
“Da ma kun zo garina ne don ku cika min gida da magani ko?â€
Dariya Aboulkhair ya yi, itama tayi dan murushin abinda yace din, ya ce, “Da na rubuta zan bata ta hado in kawo. In har ita ma za ka nema mata ko cikin pharmacies din asibitinmu neâ€.
Ya ce, “Wannan abu mai sauki? Ka ba wa Dr. Kennieth takardunta. Aalimah could you work at Las Vegas?â€
Murmushi ta yi, ta ce, “In ya amince(tana nufin Aboulkhair)â€.
Ya ce, “Karewar amincewa, ba ni na ce a nema miki ba? Youonly have to eradicate all kind of smiles from your lips, daga sanda kika fita har ki dawo aikinâ€.
Murmushi Mu’azzam ya yi kamar bai ji ba, ya soma duba agogo (kada su shiga lokacinsa). Aboulkhair ya janyo basket din nan gabansa, “Girkin dare ne amarya ta yi maka na neman albarka, ta ce in ka kasa ci in mare ta sau ukuâ€.
Sunkuyawa ya yi ya bude yana murmushi, ya ce, “To zuba min in gani, ko Allah zai sa a yi marin amarya a gabanaâ€.
Murmushi ta yi ta nade mayafi ta hau serving din, amma maimakon ta fara zuba masa, sai ta fara zuba wa mijinta, tukunna ta zuba masa. Mu’azzam ya lura da abin da ta yi, ya kuma yaba da hankalinta a ransa, “Miji first! Before anybodyelseâ€.
“Tastes goodâ€. In ji Mu’azzam.
Daga haka bai kara magana ba sai empty plate ya ajiye wa Aboulkhair a kan cinyarsa,
“Ina ya kamata a mara kenan?â€
Dariyar jin dadi Aboulkhair ke yi. Ya saci kallon Aalimah ita ma murmushin ta ke yi. Ya ce, “Ban taba ganinka kana cin tuwo ba ne shi ya sa na yi mata musu. Ko Mummy ce ta yi sai in ga ta maka wani girkin dabanâ€.
Mu’azzam ya mike yana fadin, “Na gode da ziyara da girki mai dadi amarya Aalimah. Indeed bana son tuwo, amma na ji dadin naki, saboda kin yi shi da nutsuwa ga dukkan alamu. Kamar yadda na fahimci ke ma kanki mai nutsuwa ce. I wish you the best. Have a good stay in Vegasâ€.
Ya ciro biro ya yi rubutu a ‘yar takarda ya ajiye mata tare da wani dan kati, ya juya yana ce da Aboulkhair, “Na sallame ku, zan sha magani in kwanta gobe sammako zan yi zuwa seminar din nan da na gaya makaâ€.
Daga haka ya bi matattakala ya haye upstairs da tafiyarsa mai nutsuwa, wadda babu garaje a cikinta.
6/29/21, 9:00 AM - Buhainat: BEHIND
Aboulkhair ya damki hannayenta ya rike, ya ce, “Wuw! Thirty minutes cif ban kama Aalimah ta ba, gaskiya na yi kokari. Lets go tun kokarina bai tashi a banza ba, ya yi mantuwa ya dawoâ€.
Zame hannayenta ta yi, ta ce, “Da na sani ma kiss na yi maka a gabansaâ€. Ta yi gaba da sauri. Ta ma manta da abin da Mu’azzam din ya ajiye mata, ya dauko ya biyo ta da shi yana fadin, “Ka ji ta kamar gaske, alhalin ke kanki zama ki ka yi kamar wadda ta yi wa sarki karya a gaban nasaâ€.
Sai da ya tada motar ya dora mata katin da takardar a cinyarta. Credint card ne na bankin da Mummy ke aiki JP MORGAN CHASE da pin numbers din ya rubuta a jikin takardar.
“Ba ki ya yi, yarinya kin zama Madame, ki yi ta zara ana karowa duk wata. Ga shi ko shopping mall daya ba ki sani ba. In na koma hutu zan zagaya da ke ki ga gari, amma yanzu lalalala, sai na gama honeymoon dinaâ€. Ya fada yana mai winking dinta. Murmushi ta yi, ta ce, “Ka ajiye a wajenka, ni ba abin da zan saya, beside komai nake so zan iya gaya makaâ€.
Haka suka yi ta musu, ta dage ba za ta karba a hannunta ba, ya dage nata ne shi ba zai mata ajiyar kudi ba, in Mu’azzam ya gani a hannunsa ba zai ji dadi ba. In ba abin da za ta yi da su din, ta kwashe ta tura wa Kawu Mansour ko mama Asi. Ta yarda da wannan shawarar.
Har suka zo gida Aalimah is very curious and questioning Aboulkhair a kan rayuwar Mu’azzam saboda al’amuransa bakidaya sun kara rikitata. Sun kara daure mata kai, mutum kamarsa mai cikar mutunci da kamala, ga rayuwar duniya Allah ya ba shi daidai misali, amma babu iyali, babu ranar zancensu? Kallon da ta ke masa daga nesa-nesa da ta zo kusa da shi ta ga ba haka ba ne. ba ta ga annoyance din a tare da shi ba banda ganewa da ta yi shi din is a very serious person, mai matukar tsantseni da lokacinsa. Mai girmama bako, mai tarin al’amuran yi fal a gabansa. Tambayoyin da ta ke yi wa Aboulkhair har ya rasa wanne zai fara amsa mata.
Tambayarta ta karshe ita ce, “Wane magani yake cewa za mu cika masa gida da shi? Maganin me yake cewa zai je ya sha ya kwanta?â€
Aboulkhair ya sanya hannayensa biyu ya toshe kunnuwansa bayan ya kashe motar a ma’adaninta, ya ce, “Baby, ina da nawa matsalolin ki taimaka min in warware su. Sannan in waiwayi naki matsalolin which is MU’AZZAM. Na daya, hundred kiss at mouth, fifty at my nose, seventy at my tongue, eigthty at my eyes and two hundred at my neck. In kin gama wannan ki zo na yi miki alkawarin warware miki rayuwar Mu’azzam bakidaya, tun daga kuruciya har girma. Amma ko daya ki ka tsallake ina kirge da abuna, kin tsallake chapter daya cikin labarin Mu’azzamâ€.
Aalimah ta dora hannayenta biyu a ka tana fadin, “Na shiga uku! Mon Amour ka yi min sassauci, ba zan iya ba, and I really-really want to hear his story, amma haka zan ta binka ina sumbata kamar zan cinye ka? A tarihin gidanmu babu mayeâ€.
Ya hadiye dariyar da ta ba shi, ya yi gaba yana fadin, “Za ki ga maita! Sai ki zaba ko maita ko labarin Mu’azzamâ€.
Ta ciji yatsa ta bi shi da gudu, suka shige gidan nasu. Ta riko hannunsa zai shige dakinsa, “Mon Amour ka saurare ni. Zan yi maka tausa dai kadai, Allah ba zan iya ba ina jin kunyarkaâ€. Ta fada kamar za ta yi kuka.
Kwacewa ya yi ya shige yana fadin, “Ni fa na gama magana, ai it is an option, not a choice, ban ce dole ba, ki rike tausarki, in ita ce ina da injin da zai yi min. I just want to confirm I’m married to Aalimah Mansour, (kawai ina so in tabbatarwa kaina ina auren Aalimah Mansour) saboda har gobe ji nake kamar a mafarki… kamar za ki kubuce min Aalimah… kamar har gobe ban gama mallakarki ba. Kamar akwai wasu sauran gurabe cikin zuciyarki da ban kai ga isa baâ€.
Intonation din da yake maganar da shi, da yanayin da ta gani cikin kwayar idanunsa su suka taru suka sukurkutata, suka rikitata, suka sa ta jin wani irin tsoro na ratsa ta. Sanda ta kankame shi ba ta sani ba… sanda ta soma rufe shi da sumbar a guraben da ya bukata da ma in da bai bukata ba, ba ta yi shawara da zuciyarta ba. Ba ta tuna akwai wata aba wai ita kunya cikin idanunta ba. Tun yana fadin, “Niceâ€. Ya koma, “Sweetâ€. Ya koma, “Splendidâ€.
Al’amarin da bai tuke a ko’ina ba sai a gadon barcinsu. Wata irin soyayya mai zafi da tsanani wadda a yau ba ta Aboulkhair ba ce shi kadai, 80% ta Aalimah ce da hobbasarta. Aboulkhair ya yaba, ya yi tukuici yadda ya kamata. Saida suka dawo hayyacinsu ya soma kyalkyala mata dariya. Ya ce ba wuya za a sayar da kanta a Las vegas. Shi duk abin da ya fada don ta yi masa abin da yake so ne, kuma ga shi ta yi.
“Ban da rashin wayo irin naki, wane gurbin ne ban kai ga isa ba? Yana ina? Nuna min shiâ€.
Hannayenta biyu ta kai ta rufe fuskarta, ya rungume ta tsantsan, ya ce, “Aalimah, Allah ya yi miki albarka, ya albarkaci rayuwarmu da ‘ya’ya masu irin tarbiyyarki, ba wata kubucewa da na yi tunanin za ki yi min banda ina so in koyar da ke yadda za ki tafiyar da ni. Kunyarki is too much… Ni kuma… ni kuma…â€. Ya soma zagaye dan bakinta da yatsansa ibham, “…Ina so kullum in ji sulbinshi da sanyinshi da taushinshi kan fatar jikina. In ki ka yi min wannan kin gama min komai, kin kauda hankalina daga kowacce diya mace. Kin zama ni na zama ke, mun zama sirrin juna. Bude kunnuwanki in gaya miki ko wane ne MU’AZZAM???
LABARIN MU’AZZAM.
Wato tunda muka taso daga shekaru biyar a duniya zuwa sama, mahaifiyarmu ta dora mu a kan turbar duk abin da muke so sai mun same shi, kuma za ta iya samar da shi gare mu ta kowacce hanya in har hakan zai sa mu farin ciki. Tun muna kanana Mummy ta lalata mu da kashe kudi, a kullum tana gaya mana don mu ta ke aiki, burinta mu samu duk abin da muke so a rayuwa mu ji dadi a kasar da muke zaune, mu zama daya da ‘ya’yan turawa, mu manta da ‘yan kauyen dangin Daddy don ba kaunarmu suke yi ba. A cewar ta da ba su bar Nijar ba, da tuni sun raba ta da Daddy, saboda rashin son da suke mata. In za mu tafi makaranta haka ta ke damtso kudi ta ba mu, ta ce mu kashe duk da ga lafiyayyen abinci da abin sha ta cika mana lunch box da shi. Mu kuwa mu yi ta bushasha da abokanmu.
Duk kokarinta na hana mu yin abokai tana cewa, mu zama abokan junanmu kadai, abokai suna cutar da yaro ne kawai su canza masa tarbiyya. Wannan tsoratarwa ta Mummy ba ta yi wani tasiri sosai a kanmu ba, saboda muna neman wadanda za su taya mu cinye tulin kudin da ta ke ba mu ne, ba mu kuma san ya za mu yi da su ba. Abinki da makarantu na nasara masu tsananin kula da sanya ido, ba a dade ba school authority ta fahimci irin kashe kudin da muke yi a sayi banza sayi wofi, da irin abubuwan almubazzarancin da muke zuwa da su, ta yi wa Daddy magana. Ya kuma bincike mu kan inda muke samun kudi, inda ba tare da bata lokaci ba muka gaya masa Mummy ce ta ke ba mu. Don haka ya yi mata magana, ya kuma gaya mata tsawatarwar hukumar makaranta. Sabida haka