Showing 75001 words to 78000 words out of 126031 words
Chapter 26 - Aalimah Complete 1,2,3,4 Free Book by Takori .txt
direban karamar motar ya yi tunanin abin yi, ya yi mugun taho-mu-gama da bakar Jeep din wanda hakan ya sanya duka motocin biyu fara katantanwa a tsakiyar babban titin kafin a karshe su duka biyun su hantsila wani katon rami a gefen titin. Ba ka jin komai sai hailala da salatin mutanen da ke cikin motocin cikin mika wuya ga hukuncin mahaliccinsu.
******
Da asubahin ranar Hassana da Hussaina suka ci gaba da ruda gidan da kuka, wanda suka kwana suna yi suna hutawa. Tun daren jiya sun ki karbar nono. Daga Basma har Aalimah babu wacce ta runtsa, suna fama da yaran nan saboda mama na can dakinta kwance babu lafiya, ta ce kuma takamaimai ba ta san inda ke mata ciwo ba, amma ko hannunta ta kasa motsawa balle ta zo ta taimaka musu. Daga kwance ta ce su dinga yin addu’a suna tofa musu.
Basma gefe ta koma ta zuba tagumi, nonuwa sun mata suntum suna ta sukarta suna kuma diga, duk sun jika gaban rigarta. Aalimah na so ta yi sallar asubah don har masallacin kusa da su sun idar, yaran duka biyu suna hannunta tana jijjaga su, ta san in ta ajiye su Basma ko taba su ba za ta yi ba. ta zama dumm! Kamar wadda ta samu ciwon kurumta na lokaci mai tsawo.
Aalimah ta ajiye daya ta goya daya. Rabonta da goyo tun haihuwar Aunty Gumsu. Tunda aka sallamo Basma Mama ke goya su, ta zura hijabi ta tada sallah zuciyarta na harbawa da kukan da yarinyar ke zubawa a bayanta. Ga wadda ta ajiye ita ma ba ta fasa ba. Kawai ita ma sai ta soma kukan tausayin Basma, ta san tsananin damuwa ne ya sa ta daina tabuka komai a kansu. Allah-Allah ta ke ta idar su tafi asibiti, tukin motar da Aboulkhair ya nace ya koya mata duk da ba ta so yau zai yi mata amfani. Da safe ma ita ta kai su asibiti aka duba yarinyar aka ce mura ce kawai, suka sayo magani suka dawo.
Nan Mama ke gaya musu tafiyar su Daddy a mota sakamakon rashin jirgi. Duka addu’ar sauka lafiya suka yi musu, suka ci gaba da hidimar yaran.
Tun bayan maghriba kuma suka bude makogaro suke zunduma kuka. Wanda shi ne har yanzu suke fama. Tana idarwa ta fito goye da Husainar ta je dakin su Sabrina ta rufe su da duka suna barci. A tsorace duk suka tashi suna tambayarta me ya faru? Kuka ta hau yi a gabansu tana fadin, sai barcinsu na tsiya ya jawo musu masifa, uwarsu na kwance babu inda ta ke iya motsawa tun dare suna nan suna barcin asara, duk kukan da ‘yan biyu ke yi ba su san ana yi ba ko me? Rantsuwa suka hau yi mata suna dirgowa daga gado suna fadin, wallahi ba su sani ba, kuma su ba su ji kuka ba. Ta ce su je su kula da Mama ita da Basma za su je asibiti a duba yaran.
Wata na ture wata haka suka fita a gigice, ta bi su da harara da idanunta da suka yi jawur. Lokaci-lokaci gabanta na tsinkewa ya fadi, har sai ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta ta ambaci sunan Allah. Dan cikinta sai wani irin juyi yake kamar ya wuce watanninsa. Ta dawo tana rarrashin Basma, ta canza riga su tafi asibiti, amma ta yi gumm! Kamar ba da ita ta ke ba, gani kawai ta ke rasa yaran za ta yi, don haka ba ta ga amfanin su je wani asibiti ba. ga Aboubacar tun kafin azahar rabonsa da kiranta, ita kuma in ta kira shi wayar ba ta shiga. Dalilin damuwarta kenan.
Aalimah ta yi rarrashin duniyar nan, Basma ta ki tashi, kawai sai ta fashe da kuka mai karfi.
Ta ce, “Basma, ya ki ke so in yi da raina? Kina so na zauce? Ga Mama can ba ta san wanda ke kanta ba, ni ma zuciyata tsinkewa ta ke yi, karfin hali kawai nake yi, su kuma da gani akwai abin da ke damunsu. Jarirai su kwana ba su sha nono ba ki ce haka za mu ci gaba da zama da su muna kallonsu?â€
Basma ko gezau! Sai ta rabu da ita ta sanya hijab din sallarta ta dauki mukullin motar Aboubacar da ya bar musu don irin hakan, kamar ya san za su bukace ta. Ta nade Hassanar a shawul mai kauri, ta dauki katinansu na asibiti ta tafi, Suhaima ta biyo ta da gudu ta karbi ta hannunta tana fadin, “Muje na raka ki in ji Mamaâ€.
Da suka je asibitin a sashen sababbin haihuwa aka karbi jariran (Day old), likitoci suka hau bincikarsu. Suka samu wuri ita da Suhaima suka zauna. Sai a lokacin nutsuwa ta soma dawo mata jin ta daina jiyo kukansu. Tunanin Aboulkhair ya fado mata. Ta kira shi bayan sun dawo daga asibiti da safe ya ce mata suna Katsina, “in mun shiga Niger I will call you. Take care of yourself and my baby for me MON AMOUR!â€.
Kiran da har yanzu ko kyallinsa ba ta gani ba. Tsabar jiran kiran wuni ta yi rike da wayar a hannunta, in sallah za ta yi a cikinta ta ke soke ta. Da ta gaji da jiran ta yi ta gwadawa ita ya ki shiga. Ta yi tunanin sun shiga sahara sun rasa network, amma har twins suka fara jiniyarsu babu kiran Aboulkhair ko na Aboubacar. Mama ta ce, Daddy ma bai kira ba. A lokacin ya isa a ce ma sun shiga Niamey. To balle yanzu da za a iya cewa sun kwana sun hantse, tunda har ga shi alfijir ya keto.
Ba ta kawo wani mummunan tunani a ranta ba, duk da ta san Aboulkhair yana da layin Niger. Ta sa a ranta bai samu sukunin kiran nata ba ne saboda gajiya duba da cewa, shi ya tuka motar tun daga Nigeria har Niger, har kuma babban birni Niamey. Sai dai wannan tsinkewar na zuciyarta shi yake damunta, saboda ba a son faduwar gaba ga mai ciki. A matsayinta na medical personnel ta san hatsarin hakan, don haka ta koma hailala da salatin Annabi cikin zuciyarta.
Daidai lokacin likitan da ya karbi yaran ya fito. Tambayarta ya yi, ina uwarsu? Ta ce tana gida.
Da mamaki ya dube ta, sai kuma ya basar ya
ce ta je ta zo da ita za a debi nonon a ba su ta hancinsu, masassara ce ta cika musu makogaro.
Ta ce da Suhaima ta zauna ta je ta zo da Basma, ba za ta jima ba. Har Mama za ta dauko.
Tun daga nesa ta hangi bakar motar ‘yansanda fake a kofar gidansu. Tsinkewar da gabanta ke yi ya fadi da ta samu ya lafa sabida karfin hailala ne ya sake faruwa da ita. ‘Yansanda biyu na tsaye tare da maigadinsu Bilyaminu.
A hankali ta ke rage gudun motar ta wuce su ta nufi gate tana danna wa Bilyaminu horn da nufin ya zo ya bude mata ta shige.
Bilyaminu ya karaso da sauri, maimakon ya bude mata sai ya tsaya yi mata bayanin wai ‘yansandan gidan suka zo. Wani babba a gidan suke son gani. Ba halinta ba ne raina babba ko na kasa da ita, amma ba ta san sanda ta sakar wa Bilyaminu harara ba, “Amma dai ka san daga Daddy har Yaya Aboubacar ba sa nan ko? Don me ba za ka gaya musu ba da za ka tare ni kana gaya min? Ka san uzurin da ke gabana? Tunda ka ga na fita da asubah na dawo yanzu ba sai ka bude min kofa ba ka san ya zaka yi da su ba, tunda ba sata na yi ba?â€
Daya daga cikin ‘yan sandan ya karaso ganin ta ki kula su, kuma ta rufe dattijon da fada, “Excuse me Madam!†Ya fada da kyakkyawar siga.
Dole ta yi shiru ta bi shi da ido.
“Muna neman gidan Dr. Mansour Raazee, lecturer a jami’ar Bayero, tsangayar Mass Communication, da gidan Aboubacar Raazee, accounter GTBank Hotoro Branchâ€. Ya fada cikin harshen turanci.
A sanyaye ta ce, “Nan ne!â€.
“Ko za ki turo mana namiji ya bi mu ofishinmu? Akwai bayani a kansuâ€.
Girgiza kai ta yi, abin gwanin ban tausayi ta ce, “Ni ce babba a gidan, babu namiji bayan su, uwata kuma ba ta da lafiyaâ€.
Tsayawa ya yi yana tunani, bai kamata ya tafi da ita ba ya gaya mata al’amarin da ke tafe da shi, ga ciki yana gani tare da ita, kuma ga dukkan alamu dukkaninsu ‘yan uwanta ne. A hotunan da aka turo musu babu wanda bai yi kama da ita ba.
“Madam, daure ki turo min namiji ko makocinku ne, zan fi son magana da shi a kankiâ€.
“Ka yi hakuri Officer, ni ma bakuwa ce a unguwar ban san kowa ba. Ka yi hakuri ka bar ni in wuce in ba za ka hanzarta fadar uzurinka ba. Na baro jarirai a asibitiâ€.
Kawai sai ta soma hawaye a gabansu, zuciyarta ce ta tsinke, jikinta ya gama ba ta wani tafiyayyen labari ne suke tafe da shi, wanda zai kawo karshen duk wani farin cikin rayuwarta. Wanda suke shakkar tattauna shi da ita, ganinta mace, kuma mai ciki.
“Ok, since you insist (tunda kin dage), za ki iya biyo mu ofishinmu?â€
Ta zuki numfashi da kyar, amma ta kasa furzo shi waje. Yau ita ce a ofishin ‘yan sanda a kan laifin da ba ta sani ba! Kodayake sun ce abin da suke tafe da shi din ya shafi babanta da yayanta ne. To ko laifi suka yi? Ko kama su aka yi a hanyar Niger din? To su kuma sauran da ba’a ambata ba ina suke?
Ba ta da amsa ko daya, don haka ta share hawayen da suka cika mata fuska ta ce su ba ta minti goma ta fada a gida, ta dauko ‘yar uwarta ta kai ta asibiti, sai ta same su a inda suka ce.
Tana shiga gida ta tarar da wani tashin hankalin. Basma ce a sume, su Sabrina na ta sheka mata ruwa. Duk tsananin da Mama ke ciki ta sa sun tayar da ita sun jinginar a jikin filo. Sabrina ke gaya mata tunda aka yo mata waya daga Niger aka ce su Daddy ba su isa ba tun jiya kuma an kasa samun kowannensu a waya ta ke suma tana farfadowa. Ta dubi Mama a firgice sai Mama ta lumshe ido, ta ce, “Ku hada karfi ku sa ta a mota, ki kai ta asibitiâ€.
Jikinta na rawa ta ce, “Mama har ke zan kai, wallahi ba zan barki a gida ba. Kuma yanzu zan yi wa Mummy waya har Niger din in gaya mata ga halin da ku ke ciki dukkanku, ni kadai ba zan iya ba, kwakwalwata kamar ta zauce. Yanzu haka ‘yan sanda ne a bakin gate sun zo tafiya da ni. Ba su je Niger ba, ina suka je? Na shiga uku ni Aalimah, ko dai ‘yan fashi ne suka tare su?â€
Dukkansu babu wanda ya kawo wani abu a zuciyarsa bayan wannan, Mama ta ce ba za ta iya fita zuwa mota ba. Aalimah na kuka ta ce, “Ko a goye ne sai na kai ki asibitiâ€.
Ita da kannenta biyu suka ciccibi Mama, rabi kuma da kafarta suke janta a kasa zuwa mota. Suna fitowa harabar gidan Tabawa da Sabira suna shigowa (masu aikin Mama), wadanda ba aikin kwana suke yi ba.
Wata ajiyar zuciya Aalimah ta yi, da hanzari suka taimaka mata ta sa Mama a mota, ta gaya musu saura Basma, Tabawa ita kadai ta ciccibo Basma sabida kakkarfa ce. Gabadayansu suka duru a motar har su Sabrina, su biyu a gaba, ta ja su zuwa asibitin da ta kai su Hassana da Hussaina.
Dukkansu an karbe su ba bata lokaci, da yake asibitin na kudi ne, international. Ta gaya wa Mama za ta je ofishin ‘yan sandan ta dawo, Mama na daga kwance ta ce ba ta yarda ba. Ta kara gwada layin Aboulkhair, in har yanzu ba ta same shi ba, ta kira Uncle Oussama ta gaya masa, ko kofar asibitin ba ta yarda ta taka ba.
Hakan kuwa ta yi, duk da cewa ta so Mama ta barta ta je, don idan reality bai kassara ta ba, fargaba da zullumi dake zuciyarta za su haifar mata da hauhawar jini, wanda shi ma ba’a sonsa ga mai ciki.
Jiya-i-yau. Ba ta samu Aboubacar ko Aboulkhair ko Daddy ba. Don haka tana kuka ta kira Oncle Oussama wadanda ke can zugum-zugum sun kasa daura aure bayan sun tara jama’a makil daga birni da kauye, tunda babu labarin iyayen yaran bayan kowa ya tabbatar da tahowarsu tun jiya.
Kukan da ta ke yi bai hana shi gane me ta ke cewa ba. Duk halin da suke ciki tun jiya ta warware masa. ta gaya amsa yanzu haka duk an ba su gado daga su har jariran kuma Mama ta hana ta zuwa police station din.
“Za mu zo a yau, kada ki sake kije police station dinnanâ€. Abin da ya ce mata kawai kenan yana mai jin wani irin tsoro da tashin hankali na shigarsa.
Ango Hamoud da ya yi zugum a gefe, da Mu’azzam da ya iso tun jiya ya ja gefe ya ce su je su nema musu ticket yanzu-yanzu mai zuwa Abuja, shi da Edrissa da Mu’azzam da angon da Malam kansa. Bayan wannan bai kara musu bayanin komai ba. Ya karbi sadaki daga hannun kaninsa babban dan Inna Bintou ya daura auren Khaleesat da Hamoud ba cikin dadin rai ba, sai don ba yadda za su yi da jama’ar da suka tara. Tun ba a gama watsewa ba ya ja Malam gefe ya gaya masa duk bayanin da Aalimah ta yi masa a waya, ya kara da cewa, yana tsammanin suna hannun ‘yan sandan da suka je neman wani nasun, ko dai sun yi wani laifin ne an kama su, ko ‘yan fashi ko hadari. Abin da yake zato kenan.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’unâ€. Shi ne abin da Malam Ibraheem Raazee ke ambato, babu kakkautawa. Zufa na keto masa ta ko’ina a jikinsa a lokacin da ya daga kai ya hangi Mu’azzam na fitowa daga mota.
Su waye suka mutu su waye zasu rayu? Kun yarda rayuwa bata da tabbas? Kun yarda ba abinda yake dorewa banda ikon Allah? Idan kun yarda da hakan to yanzu muka fara labarin Aalimah.!SumayyahAbdulkadir na tafe da cigaban labarin nan ba da jimawa ba!!!
7/2/21, 8:24 AM - Buhainat: ADAMU DANKOLI
A bakin gate ta tadda Mu’azzam din don already Oncle Oussama yayi masa waya ya gaya masa ga Aalimah nan zata zo ta dauke shi zuwa airport, Mu’azzam cikin kokarin controlling damuwarsa da boye bacin ransa na wannan kumbiya-kumbiya da Iyayen nasu ke ta yi masa ya tambayi Oncle Oussama su Daddy din fa? Sun same su? Amma sai Oncle Oussama yace ai suna tare, da su zasu wuce Niamey gabadaya, sun dan samu hatsari ne ashe, amma da sauki sosai.
Ya kara da cewa sun dauko su daga asibiti Ambulance ta taho dasu filin jirgin shi kadai suke jira, har an sa su a jirgi karkashin kulawar likitoci. Hamoud da Oncle Eidrissa zasu biyo su daga baya sabida kada a bar su Aalimah babu babba tare da su.
Ba don ya gamsu da wannan bayanin ba sai don bai isa ya musawa Kawun nasu ba, ko ba komai ya san bazai gaya masa karya ba, kuma koma me suke boyewar daga karshe dole zai sani ai. Tunda yace suna raye kuma sun gansu suna tare dasu to alhamdulillah.
Sanda Aalimah ta iso get din gidan yana waya ne da Oncle Oussama, saida ta jira ya gama. Ta bude masa kofar gaban motar da nufin ya shiga amma sai yace ta fito ta koma gaban shi ya tuka motar, ya fadi hakan ne ba tareda ya kalli direction din da take ba, yace in ya so ta dinga nuna masa hanya. Bazai iya ganin mace da ciki tana tuki ba. Dazu ba karamin tashi hankalin sa yayi ba jin cewa ita zata tuka su Malam. Haka suka dauki hanyar airport babu mai magana a cikin su, babu mai kallon dan uwansa, sai zukatansu dake cike da zullumi iri daya; (tunanin halin da Aboulkhair da iyayensu ke ciki), sai nuna masa hanya data ke yi lokaci-lokaci har suka shiga cikin filin jirgin.
Ta nuna masa inda ya kamata yayi parking ya kashe motar Suka fito a lokaci daya.
Passengers har sun fara shiga jirgin wanda zai tashi dasu zuwa Birnin Tarayyah, don haka suna hango su su Malam dake zaune a reception suka mike suka tadda su. Malam ya kama hannun ta, ya kuma dafa kanta ya sanya mata albarka, tare da yi mata fatan sauka lafiya. Tana tsaye a inda suka barta suka wuce zuwa cikin jirgi. Mu’azzam shine karshen shiga jirgin bai san me yasa baya ko waiwaye ba.
Tana tsaye inda suka barta ta yi folding hannuwanta a saman kirjinta, tana kallon su suna shiga a hankali babu mai walwala a cikin su. A rashin sanin ta tare da farin cikin rayuwarta zasu tashi, wanda yau ya ke kwance a karkashin fukafukan jirgi. Instead of first class seats da ya saba hawa a duk lokacin da zai hau jirgi. Kullum yana gaya mata shi baya son economy class ko da zai tatike account din sa. Yau gashi a karkashin fukafukan jirgi. Da gaske rayuwa mai iya canzawa ce a kowanne lokaci ba tare da dan adam ya shirya ba. Shi yasa ake so a kowanne lokaci dan adam ya zamo cikin shirin haduwa da Ubangijin sa. Wannan shi zai sanya ya zamo koyaushe cikin aikata kyakkyawan aiki. Ta dade a tsaye don har sai da jirgin ya soma barin kasa sannan ta juya ta koma gida, tana mai jin duniyar bakidaya na yi mata wani irin kunci ta kowanne bangare wanda bata san dalilin sa ba.
A Abuja ne dai sai da aka bata musu lokaci wajen bincike da cike-ciken takardu kafin aka amince musu suka wuce da gawar zuwa Niamey.
Tun a cikin jirgin farko Mu’azzam ya soma shan jinin jikin sa, sabida bai ga majinyatan cikin jirgi tare da su kamar yadda Oncle Oussama yace ba. Daga Malam har Oncle din