Showing 96001 words to 99000 words out of 126031 words

Chapter 33 - Aalimah Complete 1,2,3,4 Free Book by Takori .txt

ta ce,


“Malam ga shi Inna Bintou ta ce a kawoâ€.
Hannu biyu ya sa ya karba ya ce, “Madalla da Bintou da jikanyar ta, an gaishe ku, madallahâ€.
Ta juya za ta fita, sai kuma ta dawo ta tsuguna.
“Malam Aunty Gumsu-Moiram ta yi min waya dazu tace in je in mata kwana biyu, na ce mata sai na tambaye ka tukunnaâ€.
Ya ce, “Ba yanzu ba Moiram ta yi hakkuri, bana so ki je ko’ina sai kin warware dukkanki, har yanzu ban ganki kamar yadda nasan ki ba, a bai wa Gumsu hakkuri inji niâ€.
Fuska a sake ta ce, “toh Malamâ€.
Ta juya ga Daddy ta gaishe shi cikin nutsuwa da sanyin muryarta.
Ya ce, “Anya Aalimah? Haka dan Adam zai rayu da damuwa bayan ba abin da za ta sa, ba abin da za ta hana? Dubi kasusuwan wuyanki, dubi idanunki yadda suka zuzzurma ciki. Don Allah don Annabi Aalimah ni Baban ABOULKHAIR ina mai cewa a karo na sau ba adadi, ki yi hakuri. Ki yi hakuri! Ki yi hakuri…â€.
Ko kafin ya kai karshe ya fahimci hawaye sun gangaro daga idanunta. Muryarta ba ta fita sosai. A sanda take cewa.
“Na yi hakuri Daddy, na dade da yin hakuri. Zuciyata ce ta ki daukar reality, ce min ta ke ba shi ne ya mutu ba, zai dawo. Don Allah Daddy da gaske ne??â€
Malam Raazee da Daddy Ishaq suka juyar da kai don share nasu hawayen.
Daddy ya ce, “Aalimah, wanda ya mutu ba ya dawowa. Ki yarda da ayar Ubangiji subhanahu wata’ala, kullu nafsin za’ikatul maut. Aboulkhair ba zai taba dawowa ba har abada. Ki bai wa rayuwarki da ke gaba kofa ko ya ya ne ta samu farin ciki kin ji Aalimah?â€
Daga kai kawai ta yi, don ba ta da abin da za ta yi bayan daga kan, ko ta yarda ko ba ta yarda ba, ya ce,
“Tashi je ki cikin ‘yan uwanki, Allah ya yi miki albarkaâ€.
Jiki babu lakka ta mike ta wuce cikin gida.
Bayan wucewarta da minti biyar daga Malam har dansa Ishaq babu wanda ya kara yin magana. Daga bisani Malam din yayi gyaran murya ya ce,
“Ni sai inyi ta wani tunani, a duk sanda Aalimah ta zo gabanaâ€.
Daddy ya ce,
“Tunanin mene ne Malam?â€
Malam ya girgiza kai, har da daga hannaye sama ya ce, “Uhum-um-umh-uhm, a bar kazar ‘yan boko cikin gashinta, yanzu in aka yi kokarin fige ta sai kun dawo da George Bush da Mungo Park gidan nan sabida kawo nassi na bijirewa da nuna kin amincewaâ€.
Murmushi Daddy ya yi, shi ma zuciyarsa ta yi nauyi. Babu mamaki idan ba irin tunaninsa Malam Raazee ke yi ba. Bai ja zancen da nisa ba ya yi wa Malam din sallama ya mike ya kwashi takalmansa ya fice don tafiya gidansa, wanda ba shi da nisa da gidan iyayensa trackable distance ne.
7/5/21, 11:40 AM - Buhainat: HAULATU66






Aalimah ta yi sallama a shigifar kakansu. Daga shi sai Daddy 2 ta tarar a dakin, babu kowa. Ta samu gefen Malam ta zauna. Malam ya dube ta cikin kulawa, ya ce,
“Uwata me ya faru ne?â€
Ta saci kallon Daddy 2 wanda kallon fuskarsa kawai ta yi ta ji ya ba ta tausayi, da alama cikin damuwa mai tsanani yake. Ta ce, “Malam wai Daddy ne ya ce zai min aureâ€.
Yayi murmushi.
“Ke kuma ba kya so ko?â€
Ta ce, “Malam ba zan iya mantawa da Aboulkhair ba, balle in hada rayuwa da wani a bayansa, kullum ji nake a jikina zai dawo. Idan ya dawo ya same ni da aure, na ci amanarsaâ€.
Murmushi Malam ya yi kafin ya ce, “Ko da a ce MU’AZZAM ki ka aura ba za ki manta da shi ba?â€
Idanunta suka kara girma, at the same time suka kankance suka firfito waje, cikin sanyin murya tace.
“Malam, wanne Mu’azzam din?â€
“Mu’azzam Raazee Yayan Aboulkhairâ€.
Wannan karon Daddynta ne ya ba ta amsa, with every affirmation a cikin muryarsa.


Sai Aalimah ta gurfana a gaban mahaifinta a kan gwiwoyinta. Rokonsa ta ke idan wasa yake yi tana mai rokonsa da girman Allah da darajar zatinsa da ya bari, Mu’azzam tamkar uba yake a gare su daga ita har Aboulkhair. Gara ya aura mata mazan duniya bakidaya ta amince, a kan ya aikata wannan babban zunubin a gare ta.
Kamata ya yi ya tasar da ita daga durkuson da ta yi a gabansa kamar mai neman gafara. Idanunsa sun kada sun yi jajir da tausayin ta. Sai dai ko sama da kasa za ta hade ba ya jin akwai abin da zai sa shi fasa hada wannan aure, muddin yana raye ita ma Aalimah tana numfashi.
Ya ce, “Ki nutsu Aalimah ki fuskance ni, Mu’azzam shi na so tun farko ki aura Allah bai cika min wannan burin ba. Idan har da gaske kina kaunar Aboulkhair ba abin da za ki yi ki nuna masa wannan kaunar a lokacin da kasa ta rufe masa ido, banda tallafar rayuwar Mu’azzam. Kin sani Aboulkhair ba shi da wani buri da ya wuce Mu’azzam da lafiyarsa. Aalimah ba kya tausayin Yaya Ishaq? Mutumin da ya dauke ki babu bambanci da ‘ya’yan cikinsa ya karrama rayuwarki? Kina sane da cewa ba shi da buri a yanzu da ya wuce lafiyar Mu’azzam da cikar rayuwarsa. Ba za ki kasance mai rama alheri da sadaukarwa ba?â€
Aalimah cikin gunjin kuka ta ce, “Daddy, bana gudun Mu’azzam don rashin lafiyarsa. Ko kadan. Ina gudun aurensa ne kasancewar sa wanda ya fi kowa kusanci da Aboulkhair, ina matukar ganin girmansa, aurensa shi ne babban cin amanar da zan yi wa Aboulkhair a lokacin da babu shi…â€.
Wannan karon malam ne ya tare ta, “Uwata, shi ne babban farin cikin da za ki sanya shi. Shi ne babban gatan da za ki yi masa. Shi ne kauna ta hakika da za ki nuna masa. Hakkin ki ne mu ba ki dama wannan karon ki zabi mijin aure, shi ya sa har muka zaunar da ke a nan muna neman yardar ki da amincewar ki, ba don haka ba da ba za ma ki san an yi ba sai bayan an yi.
Ni na san uwata mai biyayya ce ga umarnin mu, mai farin ciki da farin cikin iyayenta. Kin zauna da Mu’azzam ko da ba gida daya ba a kalla za ki iya bada shaida a kan WANE NE SHI? Kuma kin ga yadda dan uwansa ke kula da shi, akalla muna da kyakkyawan zaton za ki iya taimakawa rayuwarsa a matsayinku na shakikan juna, ku taru ku rufa wa juna asiriâ€.
Aalimah ta rasa abin cewa, ta rasa hujjar kare kanta wajen Daddy da Malam, ban da ta zuba musu ido, sun riga sunyi nisa akan kudirinsu, kome zata ce bazasu gane ba, bazasu saurareta ba, tana mai jin abin da suke fadi kamar almara a cikin kanta. Tana mai kallon fuskokinsu na wulgawa kamar a majigi, tana ganin wasu abubuwa masu kama da taurari cikin idanunta suna ratsa fuskokinsu cikin idonta. Daga haka ba ta kara gane me suke cewa ba, kuma ba ta kara samun kalmar furta musu ba.
******




Ta farfado ne daga shidewarta ta ganta a cinyar Gumsu- Moiram, tana mata firfita da maficin kaba, Gumsu ta sa hannu ta debi ruwa tana shafa mata a kan farar fuskarta wadda ta cure ta yi jajir. Mikewa ta yi daga kwanciyar ta tashi zaune. Idanunta ta ke rarrabawa a dakin kafin ta fahimci a dakin Inna Kasisi suke. Ga Innar a gefe ta hada tagumi, bayan su babu kowa a dakin sai ita cikon ta uku.
Inna ta ce, “Gumsu, ki tafi da ita gabanki ta kwana biyu in ji Malam. Ki ci gaba da nuna mata gaskiya na tabbata za ta fahimci iyayenta, kuma za ta fahimci abin da suke so ta fahimtaâ€.
Zumbur Aalimah ta mike zaune, “Ba abin da zan fahimta in dai aure da Mu’azzam ne Inna, ba zai taba bani irin rayuwar da dan Uwansa ya ba ni ba, bayan ciwo da ke aiki a jikinsa har da hali. Halinsa ba irin na mutane ba ne. Na ce na yarda a aura min mazan duniya dukkansu, amma ban da Mu’azzam Inna…â€.
“Me ya sa ba ki gaya wa ubanki ba? Ni me ye nawa ne a ciki?â€
Inna kasisi ta katse ta cikin gatsali, kasan ranta cike da jin zafin kalaman Aalimah, duk wanda zai aibata Mu’azzam ko ba ta gaya masa ba, za ta ji zafinsa a kasan zuciyarta. Shi ne ya dauke su mutane masu daraja a lokacin da Zulaiha da Ishaq suka watsar da su. Shi ne ya fara kai ta dakin Allah kafin kowa ya kai ta. Shi ne ya dauki danginta da muhimmanci yake agaza musu fiye da kowa cikin ‘ya’ya da jikokinta. Shi ne ya dauke su mutane fiye da ubansa! Kaunar da ta ke masa ba ‘yar kadan ba ce, ba za ta juri ana aibata shi a kan idanunta ba.
“Gumsu na ba ki minti uku ki tattara Aalimah da kayanta ku tafi gidan ki. Zan iya hambare ta idan ta kai ni bangoâ€.
Gumsu ta kama hannun Aalimah suka mike, da ma tuni ta dibar mata kaya kala biyu ta zuba a babbar leda. Za su iya tafiya a kasa daga nan babban gida zuwa gidanta, amma a motar Daddy Gumsu ta jefa ledar kayan Aalimah, ta bude mata kofa ta shiga ta rufe, sannan ta zagaya mazaunin direba ita ma ta shiga ta ja su zuwa gidan, ga tsohon ciki a jikinta kusan watanni bakwai.
A gidan ma aiki daya Gumsu ta ke ta yi, wato lallashi, ban baki da jan hankali. Tana nuna mata illar ja da iyaye da yin fito na fito ga umarninsu. Ta ce,
“Aalimah, idan na fahimce ki Mu’azzam ne ba kya so, ba auren ne ba kya so ba?â€
Da sauri ta daga mata kai.
Gumsu ta yi murmushi, ta ce,
“In aka janye maganar Mu’azzam aka kawo wani za ki yarda ki yi aure ke nan?â€
Da sauri Aalimah ta gyada kai, ta kara da cewa, “Ko waye Aunty Moiram ku kawo, ban da Mu’azzamâ€.
Gumsu ta kama baki, ta ce, “Ko kunyar idona ba kya ji Aalimah? To kuwa sai dai bakin ciki ya kashe ki mu ci gumba! Mu kuma ba damuwa muka yi ki yi aure ba, ki auri Mu’azzam ki zauna da shi cikin rufa wa juna asiri shi ne abin da ya dame muâ€.


Kwana biyu kullum suna tirzawa, duk ta inda Gumsu ta billo sai Aalimah ta goce. Rashin kunya sosai take zubawa Gumsu son ranta. Gumsu bata taba sanin Aalimah nada baki ba sai a wannan lokacin. Itama bata raga mata, haushi take cusa mata ko ta ina, mai nuna soyayyar ta ga wannan hadin auren data fahimci lallashin bata lokacin ta take yi. Aalimah ta shirya ja da kowa don kubutar da kanta daga auren Mu’azzam. Daga baya ta je ta samu Inna Kasisi tace zata dawo da Aalimah gida, zuciyarta ta kasa jurewa, don kwarai Gumsu ke son Mu’azzam itama duk da ba wani sabo ne mai yawa a tsakanin su ba. Zuciyarta na matukar sonsa.
Ta kasa jure kiyayyar da Aalimah ke nunawa auren sa kiri-kiri bata shakkar kowa. Gata a cikin gidan ubansa. Amma duk abinda yazo bakinta shi take fada. Abubuwa da yawa akan kunnen Daddy take yin su. Ita kuma Inna Kasisi ta kwashe komai ta gayawa Dr. Mansour. Sai ya ga bari kawai ya kawo karshen komai, kowa ya huta, dama sun bata lokaci ne ko zata lallasu ta karbi auren da dadin rai. Amma tunda abin nata ba mai karewa bane bari ya karar da shi.
Ranar ta kama juma’a, bayan saukowa daga masallaci suka ga Daddy ya fito cikin shirin babbar shiga ta shadda Wagambari, babbar riga da hula sai kamshi yake yi.
Ya ce, “Gumsu, kira min Aalimahâ€.
A ladabce ta zo ta tsugunna a gabansa, ya kalleta cike da tausayin yadda ta rame ta fita hayyacin ta cikin sati guda kacal da yin maganar auren ta da Mu’azzam. Ya sassauta murya yace.
“Malam ne ya ce in tambaye ki, kin amince ki auri dan uwanki Mu’azzam?â€
Aalimah ta samu kanta cikin rudu. A rasa wanda za a turo ya tambaye ta sai UBAN MU’AZZAM? Wannan ma ai wayo ne da son cutar da mutum, tunda ko giya ta ke sha ba za ta iya duban tsabar idon Daddy Ishaq ta ce ba ta son Mu’azzam ba.
Ta shiga tunano tarin alhairorin Daddy Ishaq gareta a Boston…. Da lokacin da take auren dan sa Aboulkhair….hawaye suka wanke mata fuska.
Ya ce, “Ke nake sauraro Aalimah, mutane suna jira naâ€.
Ta samu kanta da cewa, “Na amince’’ (without a second thought). Tare da zubowar tawagar hawaye a kan kundukukinta.
Albarka Daddy ya shiga sanya mata, sannan ya kama hannayenta ya mikar da ita daga tsugunnon da ta yi, ya ce,
“Insha Allahu ba za ki yi nadamar auren dan uwanki ba, kuma rashin lafiyarsa ba zai zamo kalubale ga rayuwar aurenku baâ€.
Ya hada hannayenta da na Gumsu wuri guda, sannan ya fice.


Kuka Aalimah ta fashe da shi, ta zare hannunta daga na Gumsu ta shige bedroom din ta, tana mai tambayar kanta,


“wanne irin hukunci kunya tasa ta yanke wa rayuwar ta haka?â€


Ba jimawa aka soma shigo musu da huhun goro da alewa, Balkissa ta shigo tana guda, kamar wata marokiya, tana gaya musu an daura auren Yaya Mu’azzam da Aalimah.


******


“Kana ina Mu’azzam?â€
“Daddy I’m at San Francisco, na zo Seminar ta kwanaki uku da Valero Corporation sai jibi zan koma Vegasâ€.
“O.K, in ka koma masaukinka, ka samu nutsuwa, ka kira ni don Allahâ€.
Da haka suka yi sallama.


Mu’azzam na komawa hotel din da ya yi masauki wanka kawai ya yi da sallahr isha, sannan ya kira mahaifinsa.
“Wato kana ji ko Mu’azzam? Gyara nake so ka yi wa gidanka, gyara na sosai, in nace sosai ina nufin sosai, ya koma sabo kal!â€
Murmushi Mu’azzam ya yi, a very gentle smile irin nasa. Wanda ba kasafai yake yin sa ba sai abu ya bashi dariya sosai. Banda abun Daddy shi kullum gidansa kamar sabo yake, ko’ina kal-kal yake yana sheki da daukar ido sabida kwarewar Jacob a gyaran gida, tare da fesar da kamshi mai sanyi, wanda ke fitowa daga furannin gidan da room fresheners masu kyau da Harrison ke fesawa akai-akai, ko su Mummy da ke wuni dafe-dafen da ba ya so ba su da bata wuri, suna tsaftace inda suka bata sosai. Ya ce,
“Daddy ai kullum gidan cikin gyara yakeâ€.
Daddy ya ce, “Duk da haka, a fidda dakin nan dake rufe na kusa da naka, a yi masa gyara na musamman. A yi furnishing dinsa da furnitures masu kyau. Wannan dakin dake rufe na kusa da bedroom dinkaâ€.
Cikin shanye mamaki Mu’azzam yace.
“Ok Daddy, za’ayi yadda kake so, yanzu dai bana gari amma ba abin da zai gagara insha Allah. Amma Daddy tukunna me za’a yi da dakin?â€
Maimakon ya amsa masa tambayar da yayi masa sai cewa yayi.
“Zan turo maka kudin da suka saura min ka kara, kai dai ka yi yadda na ce, in an gama ka sanar da ni. Allah ya yi muku albarkaâ€.
Bai bashi damar cewa komai ba ya kashe wayarsa. Daddy kullum mantawa yake da cewa shi din ma’aikacin Chevron ne. Chevron din da itace lamba daya kan petroleum a Amurka.
Mu’azzam ya jima rike da wayar sa, yana tambayar kansa ko sai yaushe su Daddy zasu daina wahalar bashi kudi daga shi har Mummy, su yarda shi din yanzu Engnr. Ne na man petir wanda ya tsaya da dugadugansa baya bukatar tallafin su a komai? Tsakanin Daddy da Mummy bai san wa ya fi son sa da tausayin sa ba.
Ajiyar zuciya yayi. Ya rasa wanda yafi wani tausayinsa da son samar da kykkyawar rayuwa a gare shi tsakaninsu. Domin daga baya Daddy ya gaya masa komai da ya faru tsakaninsa da Mummy da har ya kai ga saki, lokacin da ya fahimci su Mummy basu da niyyar barin gidansa. Wannan sacrifice da mahaifiyarsa tayi a kansa yasa shima ya cizge duk wata damuwa da zamansu ke jaza masa, yayi dammarar cigaba da zama tare da mahaifiyarsa cikin so da kauna tare da bata dukkan kulawa har karshen rayuwarsa.
Ta wani fannin tausayin mahaifinsa ya kamashi, tunda ya haife shi yake wahala da shi har gobe bai huta ba! A yanzun kuma da ya kamata ya hutan, ya ki yarda ya huta. Kullum kallon karamin yaro mai bukatar kulawar iyaye yake masa. A wani bangaren, ya fada tunanin abin da Daddy zai yi da daki a gidansa. Kuma ma kusa da dakinsa, saidai ko kusa tunaninsa bai kawo masa aure ba, don shine abu na karshe da ba zai zo cikin tunanin sa ba, daga karshe ya soma kiraye-kirayen waya yana bada order kan cika umarnin Daddy.


Kafin ya dawo an gama komai. Gidansa ya zama sabo kal daga sama har kasa. An zuba wasu gogaggun furnitures farare sol ‘yan kasar Italy an lullube shi da curtains ruwan madara. Dakin sai wani kamshin sabunta yake yi mai dadi. Haka gidan bakidaya an pente shi da wani irin fenti fari kal mai santsi da sheki. Alamu ne na cewa (white) is the favourite colour na mamallakin gidan. Har kitchen ba’a bari ba shima ya sha gyara ta ko’ina da sababbin kitchen cabinets sai daukar ido yake.
Yana shigowa gida daga tafiyar da yayi Mummy da jin motsinsa da sallamar sa ta fito daga daki da sauri har tana tuntube, zaninta na kuncewa. A dugunzume ta tare shi da tambaya ko bari ya huta bata yi ba daga gajiyar zaman jirgin kasan da ya kwaso tun daga SanFrancisco har Las Vegas.


“Mu’az, aure ka yi ne babu labari?â€


Ya lalubi kujera guda cikin tausasan leathers din da ke falon, ya zauna cikin nutsuwa, a lokaci guda yana mai loosing neck tie din wuyanshi shi yadda zai ji dadin zaman. A gajiye yake matuka.
Dariya Mummy ta bashi sosai, ya yi murmushi, ya ce.
“Sai dai in ke ki ka sake yi min babu labariâ€.
Ta daure fuska ta ce, “Ka bar zancen wasa, tsakani da Allah aure za ka yi?â€
Sai a lokacin ya ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login