Showing 21001 words to 24000 words out of 72718 words

Chapter 8 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt

16 Dec 2024

2291

lokacin fuskarshi dauke da damuwa yace safiya ya akayi Affan ya faďo daga wannan saman mai nisa,
sannan me ya faru a gidannan da har ya haddasa tabuwar kwakwalwarshi,
oyizah ta fara share hawayen karya tace alhj nima ban sani ba, kowa na bangarenshi ya za'ayi insan abinda ya faru,
Allah sarki Affan yanzu brain dinshi ya samu matsala,
murya a dashe alhj basheer yace eh safiya, kuma bawai fadowar da yayi bane ya taba brain dinshi, hankali tashe kamar gaske tace to me ya sameshi,
nan ya kwashe abinda doctor ya faďa mishi ya fada mata,
wani irin kuka ta fashe dashi harda zama a dirshan a kasa tana faďin mun shiga uku, yanzu shikenan Affan ya haukace,
alhj basheer ya shiga rarrashinta yana faďin addu'a zamuyi mishi safiya,
dakyar oyizah tayi shuru tace ni alhj babban tashin hankalina shine rashin ganin zeenatu,
Allah yasa ba wasu mugayen bane suka saceta suka wurgo Affan daga sama, hankalin alhj basheer ya tashi da jin furucin oyiza,
ya kalleta yace da zeenatu tayi musu me zasu saceta,
oyizah tace Alhj ka manta muna cikin zamanin da ba sai kayi ma wani komai ba zai maka mugun illah, nidai gobe kabi jirgin safe kabar kulawar Affan a gurina kaje can cameroon ka dubata dan wannan abun yafi karfin waya,
alhj basheer ya share zufar goshinshi yace kin kawo shawara mai kyau safiya, amma--- ta katseshi da sauri tace na fada maka zan kula da Affan fiye da yadda zaka kula dashi, kai dai ka tafi nemanta dan hakkinta na wuyanka,
cikin jindadin tsararrun kalaman oyizah alhj basheer yace nagode sosai safiya, Allah ya kaimu goben, tace ameen yanzu kaje ka kwanta ni zan tafi gurin Affan din in ta kama ma sai in kwana, alhj basheer yaji dadi sosai a ranshi ya dinga shi mata albarka..


Ďaki oyiza ta wuce zuciyarta wasai yanzu gida zai dawo karkashin ikonta,
wani kulli mai kyalli ta kwance ta fito da babyn "Mutum mutumi" an soke kanshi da mashi, Kallon babyn tayi hade da kwashewa da dariya tace Affan kai da warkewa har abada, haka zaka dawwama cikin hauka har ka mutu kamar yadda babyn nan take haka zaka kasance sai yadda nayi dakai,
ta mike ta daga karkashin gadonta inda ta dade da haka wani ramin sihiri ta kara tona gefen ramin ta kira sunan Affan sau uku sannan ta tura babyn ciki tana dariyar mugunta,
ta kalli wata laya ta kara saka wata dariyar tace wannan naki ne zeenatu, ba yanzu zanyi aikin ba sai an gaji da nemanki, ta mayar da layar cikin daurinta sannan ta loda magunguna hade da turarukan tsafi a jakarta ta shirya wucewa asibitin..


Tun asuba jabeer ke neman wayar Affan ba'a dauka ba,
daga karshe ma jin wayar yayi akashe,
gurin karfe 8 yaso shiga ya dubashi sai wani muhimmin aiki ya taso mishi a office ya wuce,
bai dawo gida ba sai bayan magriba, saida ya fara shiga gurin Afeeyah suka dan taba hirah sama2 sukaci abinci tare kamar yadda suka saba sannan ya mike jikinshi a sanyaye saboda rashin jin muryar amininshi yau tru out,
abinda bai taba faruwa ba tun tasowarsu dan ko tafiya daya yayi to suna manne a waya, sallama yayi ma hajja da afeeyah ya fita ya isa kofar gidan su Affan,
tun a gate mai gadi ya sanar dashi abinda yake faruwa,
kiriss ya rage jabeer ya faďi saboda tashin hankali, da kyar ya daidaita kanshi ya karasa cikin gidan, babu wanda ya samu a ciki sai farida dake waya tana kyakyata dariya,
murya na rawa yace Fa-re-da- wani asibiti aka kwantar da Affan, sai da ta kalleshi sama da kasa sannan ta ajiye wayarta, cikin masifa tace haddar sunan asibitoci aka kawo ni yi duniya,
cikin bacin rai jabeer yace "oops" na manta fa da'kikiya kamarki wacce bazata iya haddar sunanta ba bare asibitin da aka rubuta shi da turanci saboda masu ilimi su gane, farida ta mike a fusace zata fara bala'i karar bugun kofa ya hanata,
jabeer ya kalli daddy suka gaisa sama2 yace daddy wani asibiti affan yake, daddy yace muje jabeer nima can zanje nan "Arewa surgery" ne,
jabeer ya harari fareeda ta gefen ido yayi kwafa ya bi bayan daddy....


Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣3⃣ By Aysha Ya'u Kurah


Kuka sosai jabeer yayi da yaga yadda Affan ya koma,
zama yayi gefenshi yasa hannunshi cikin nashi yana karanto adduo'i yana tofa mishi,
oyizah ta harareshi tace dan Allah malam ya isa haka kar miyan ka ya jikashi ya farka lokacin farkawarshi baiyi ba,
daddy yace addu'a fa yake mishi safiya,
oyizah ta marairaice tace doctors ne suka hana alhj nima dazu ina mishi addu'a suka hana ni,
jabeer ya waigo ya kalli daddy idonshi a kumbure yace daddy ina umma,?
alhj basheer yayi jugum sannan ya fada ma jabeer komai game da zeenatu,
a rude jabeer ya mike yace daddy shine ba'a dauki mataki ba tun dazu,
innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
alhj basheer yace nasan bazata wuce gida ba gobe da sassafe zan tafi,
jabeer yace da nan ya kamata a fara daddy, in har bata nan sai a tafi can,
oyizah ta harareshi ta wutsiyar ido sannan tace hakane alhj kai kaje cameroon din mu sai mu fara nemanta anan ko jabeer,
jabeer bai kalleta ba yasa kai ya fita zuciyarshi kamar zata buga saboda tashin hankali..


Washe gari tun asuba jabeer ya bar asibitin ya isa gida,
nan suka shiga binciken duk gidajen aminansu na kusa da na nesa shi da Abida da tun jiya bata runtsa ba da jabeer ya faďa mata wannan mummunan labarin,
babu inda basu shiga ba amma babu labari,
jabeer ya zarce gurin yan sanda ya sanar musu sannan ya koma asibiti,,


yana shiga ya tarar da oyizah zaune gefen Affan tana shaka mishi turare a hancinshi, tana ganin jabeer ta mike da sauri tace jabeer ka dawo,
kaga turare ne aka bani ance yana healing ciwon kwakwalwa in ana shakawa mutum shine nake gwada mishi,
jabeer yace uhum kawai ya zauna gefenshi yana kallonshi yana mishi addu'ar da oyizah ta tsani ganin ana mishi,
a zuciyarta tace tabbas in bata katange Affan daga adduo'in mutane ba wata rana tana zaune adduar zatayi tasiri akanshi,, ta kalli Affan tayi kwafa ta maida turaren jaka ta fita daga asibitin..


A can cameroon kuwa tashin hankalin da suka shiga bazai misaltu ba,
dan kuka sunci shi da aka gama duba guraren dangi ba'a sameta ba,
alhj basheer kanshi kasa tsayar da kukanshi yayi yanata kiran sunanta kamar zautacce yana fađin ina kika shiga ne zeenatu,
da kyar Baffan zeenatu ya rarrasheshi da bashi baki akan suyi ta addu'a, ko gawarta ne Allah ya bayyana,


Washe gari tare da su yadikko aka taho duba Affan,
sun jima tsaye akanshi cikin tausayawa amma fa babu wanda a cikinsu ya iya budar baki yayi mishi addu'a,
"saidai kawai suce sannu Affan cuta ba mutuwa bane, wata rana sai labari sai kuga kamar baiyi ciwon ba,"
wadannan kalmomin su kadai duk wanda yaji Affan baida lafiya yake iya faďi,
JABEER BARA'U DAURA shi kaďaine yake yin addu'a sosai akan Affan,
hakan ba karamin ďaga hankalin oyizah yakeyi ba dan tayi duk wani abun da zatayi na tsafi akan jabeer amma ta kasa,
tabbas tasan jinin jabeer ya fi karfinta dan haka ta kudira a ranta Affan na komawa gida zata hana duk wani mahaluki zuwa dubashi bare har ya samu damar yi mishi addu'a,
sannan shima Affan din zata san yadda zatayi ta daure kafarshi a cikin gida ya zamana ko wajen gate bazai iya taka kafarshi ba,
da wannan tunanin oyizah ta ďan samu relief...


Sati biyu suka wuce babu zeenatu babu labarinta,
haka Affan bai farfaďo ba kullum yana kwance cikin oxygen,


Oyizah ta kalli alhj basheer da yake cikin damuwa har yanxu, tace ranka ya ďade ya kamata ka cire duk wata damuwa aranka, duk inda zeenatu take--- yayi saurin katseta yace na manta da batun zeenatu a wayewar garin yau saboda zeenatu ba yarinya bace duk inda take zata iya kula da kanta koda kuwa saceta akayi,
ni yanzu ciwon Affan ne kaďai ke damuna day nd nyt,
oyizah tayi murmushi a zuciyarta tace aiki yayi, ta tuno sanda zata tura layar cikin bakin gawar "Damo" saida ta tsorata taso ta bar aikin, ashe nasara ne ya hanata barinshi,,
ta kalli alhj basheer idonta ya ciko da kwalla, tace karka damu alhj Affan zai samu sauki tunda yana karkashin kulawar likitoci, zeenatu fa babu wanda yasan inda take,
tsawa mai karfi ya daka mata yace nace ki daina kawo min maganar zeenatu nan gurin,
oyizah ta mike sum2 ta wuce ďaki tana kukan munafurci..


Tsalle ta dingayi da ta shiga ďaki murna kamar zai kasheta, yanzu abinda ya rage mata shine tasan inda Affan ya ajiye kadarorin da alhj ya mallaka mishi....


Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣4⃣ By Aysha Ya'u Kurah


Ranar wata jumma'a bayan an sauko daga sallah jabeer asibiti ya wuce saboda nan ne gurin zama da kwananshi,
duk da irin kyarar da oyizah ke mishi hakan bai hanashi zuwa ba,, addu'a sosai yayi ma Affan a masallaci,
yana shiga cikin asibitin ya tarar babu kowa gurinshi kuma yaga kamar bakinshi na motsawa,
da sauri jabeer ya naďe carbin hannunshi ya karasa kusa dashi, ya rike hannunshi yasa kunnenshi saitin bakinshi,
R-u-w-a yaji yana fada muryarshi na rawa,
jabeer ya mike da azama yaje ya kira doctor suka shigo tare da sauri,
doctor ya gama duba Affan sannan ya kalli jabeer yace dan bashi ruwa kaďan,
jabeer jiki na rawa ya balle murfin Faro ya tsiyaya kadan a ciki saida yayi addu'a sosai a cikin ruwan sannan ya matsa kusa da Affan da har lokacin bai bude ido ba sai kiran ruwa da yakeyi, buďe bakinshi yayi zai fara zuba ruwan aciki oyizah ta shigo da sauri ta kabe glass cup din ya fadi ya fashe,
cikin masifa tace baka da hankali ne zaka bashi wannan ruwan daga cewa a bashi,
doctr musah yace hajiya ruwan is pure ni nace ya bashi,
oyizah ta fito da wani ruwa a cikin gora tace wannan ruwan alhj ya bani kafin ya tafi yace duk sanda ya farfaďo a tabbatar shi ya fara sha saboda ruwan addu'a ne da ya amsoshi daga cameroon,
jabeer da ya cika yayi famm yaja dogon tsaki ya fita ya bar asibitin gaba ďaya,
doctr musa ya ba oyizah da ke sharar kwallar munafurci hakuri yace bamu san akwai adduar da za'a bashi bane da bamuyi gangancin bashi ruwa ba,
tace babu komai doctor, yanzu zan iya bashi kenan,
doctr musah yace eh hajiya, nan oyizah tayi murmushi ta gefe ta zauna ta bude bakin Affan ta tsirara mishi ruwan da yasa shi sakin razananen ihu, da sauri ta mike da ta tabbatar da ya hadiye ta matsa baya tana kuka tana fadin doctr dubashi,
da kyar doctor musah ya samu yayi mishi allurar da tasashi bacci ihun ya lafa,
ya waigo ya kalli oyizah yace hajiya I think ruwan adduar nan yasashi ya farfado gaba daya saidai kuma yanzu ne za'a fara jinyar, yasa kai ya fita..


Oyizah tayi dariya sosai tace ba dole ya farfado ba, na daďe ina jiran wannan ranar, ta kalli ruwan sosai tace nasan har yakai inda nakeso yakai,
ta harari affan ta fara shafa mishi ruwan a fuska tace kai da samun sauki har abada Affan..


Tun daga ranar ciwo ya dawo sabo, saboda kullum da ihu yake farkawa sai an mishi allurah ake samun saukin abun,
ciwon kanshi kuwa ya fara warkewa, dan gurin da yayi rami ya ciko sosai,
saida yayi sati ďaya kullum ya farka da ihu yake farkawa, daga ya farka kafin ayi mishi allura oyizah zata bashi maganin da tace ruwan addu'a ne,


Watanshi ďaya a asibiti ana fama da lalura ďaya,
saidai a kawo babban likitan mahaukata gurinshi ya dinga mishi treatment saboda ciwon da ke kanshi,
yanzu kam ciwon yayi sauki sosai dan haka doctor musa ya bada shawarar a kaishi "psychiatric" alhj basheer sam yaki yarda yace saidai ya fita dashi waje,
doctor musah yace hakan ma zaifi Alhj, gara ka kaishi wajen, akwai wani asibiti a "New Toronto, Canada" sunanshi "LAKESHORE PSYCHIATRIC HOSPITAL" asibitin sun kware sosai alhj, in dai waje zaka fita dashi gara ka kaishi can,
kuma anan nigeria ma fa akwai psychiatric masu kyau kuma ana kula sosai, kamar su "FEDERAL NEURO PSYCHIATRIC" dake kaduna da kuma na Lagos, da ma sauransu, amma tunda hankalinka yafi ga fita dashi din gara ka fita dashi, mudai fatanmu a koda yaushe shine ya samu lfy,
, alhj basheer yace hakane doctor, nagode sosai in shaa Allah gobe zamu fara processing tafiyar,, doctor musah yace to Allah ya kaimu alhj shi kuma Allah ya------- doctor musa ya kasa karasawa saboda datse harshenshi da yayi, ya kalli alhj basheer ya mika mishi takardun sallama da reports din ciwon Affan tare da magunguna...


Watan Affan biyu a canada, oyizah ke zaune dashi saboda yawan tafiye tafiyen da alhj basheer keyi, jikinshi yayi kyau sosai saidai duk wanda ya ganshi yaga mai tabin hankali, komai na yara yakeyi, ga yawan son wasa, kallon ruwa da kifaye da sauransu,
a cikin wata biyun nan oyizah ta mallake Affan sai abinda tace yayi, sam bata nuna mishi hanyar kwarai saidai ta nuna mishi mara billewa, magungunan tsafi kuwa su ke ďawainiya dashi tun zuwansu canada,
doctors sunyi mamakin yadda akayi magungunan da suke bawa Affan bai mishi aiki ba,
sudai sunsan larura indai ta haukace to wacce tafi ta affan ma sun warkar bare tashi da suke ganinta minor, basu san duk magungunan da suke zuwa bashi oyizah ta karba tace zata bashi zubar dasu takeyi ba,
wani lokacin ne ma take bashi ba bisa ka'ida ba,


A ranar da suka cika wata biyu da sati biyu aka sallamesu saboda haukar affan ba ta barna bace kuma sunga in oyizah tace ya zauna nan to bazai tashi ba har sai tace ya tashi,
wannan dalilin yasa suke ganin kamar in suka basu isassun magunguna nan da wasu yan watanni zai samu sauki..


Ranar oyizah tayi murna saboda dama ta kosa ta koma gida,
yawo ta fita da Affan tayi mishi siyayyar kayan wasa da uban yawa tana zaba tana mishi dariyar mugunta shi kuwa banda murna da tsalle babu abinda yakeyi,
a daren ranar suka hawo jirgi tare da alhj basheer sai kasar mu ta gado...


Cikin dare suka iso gida a gajiye, kowanne daki yaje ya kwanta banda Affan da shi a gurinshi ma safiya ce,
zama yayi a parlor yana wasa sosai gaba daya ya hargitsa parlon,
in ya kalli hanyar dakin zeenatu sai ya runtse idonshi wasu abubuwa su dinga gifta mishi kamar rayuwar cartoon,
kuma sai yaga kamar harda shi a cikin cartoon din,
tashi yayi yana kokarin zuwa kofar dakin yaji muryar oyizah ta daka mishi tsawa,
da sauri ya dawo bayanta ya tsaya yace mummy wannan kofar wanene,
kamar na taba zama a ďakin, kin gani kofar ma kamar ta drawing ko,
oyizah ta shafa kanshi tace my baby kasan meye a kofar nan, ya girgiza mata kai, ta ja hannunshi ta fara nuna mishi kofar har zuwa hanyar steps din can saman da ya faďo tace duk nan gurin zaman macizai, da namun daji ne, kana son su cinye ka, ya noke wuyanshi ya make a bayanta,
tace to karka kara zuwa arean gurin kaji, yace to mummy,
ta kama hannunshi ta wuce side dinta dashi ta sashi a wani daki ta rufe tana kyakyata dariyar mugunta da jindadi..


Tun karfe 12 jabeer keta fama da masu gadin gidan akan su bude mishi kofa sunki, dan oyizah tace kar a kara barin kowa ya shigo saida izininta, ran jabeer ya baci sosai idonshi yayi jawur,
yace yanzu Halilu har ni ma sai ku hana shiga in an saku,
halilu yace kwarai kuwa saboda ina mutunta aikina,
jabeer yayi kwafa kamar zai juya sai ya dawo da karfinshi ya tura halilu ya ruga ciki da gudu suna binshi a baya,
da sauri alhj basheer ya fito jin hayaniyar tayi yawa,
tsawa ya daka ma su halilu yace lafiya kuke binshi kamar wani barawo,
halilu yace ranka ya dade madam ce tace kar abar kowa ya shigo,
alhj basheer yace jabeer ne kowa, baku san matsayinshi a gidannan bane,
oyizah ta fito da sauri tace yi hakuri alhj mantawa nayi in ce musu kar su hana jabeer shigowa,
alhj basheer yace to su sauran mutanen kuma fa meye dalilin hanasu shigowa,
ta fara matsar kwallah tace bana son a shigo a dinga yi ma affan dariya na fi son sai ya warke mutane su ganshi,
alhj basheer ya jinjina kai cikin damuwa yace na gamsu da bayananki, share hawayenki Allah yayi miki abinda kikayi mana na alkhairi, tace ameen haďe da hararar jabeer,
alhj basheer yace jabeer ka shiga ciki mana abokin naka yana ciki ai,
jabeer yasa kai ya shiga cikin parlon da sallama,


Zaune ya tarar da Affan da wasu kayan wasa a hannunshi, wuyanshi yasha hoda idonshi kuma kwalli, kallon jabeer yakeyi sosai wasu abubuwa na mishi yawo a kwakwalwarshi,
sai da yayi minti biyar yana kallonshi sannan ya zubar da kayan wasan ya rungumeshi yace daddy wannan abokina ne sosai tare muke wasa dashi, kaga fuskarshi ma shima drawing dinshi akayi kamar waccan kofar,
Salma da fareeda suka kwashe da dariya harda rike ciki, yayin da jabeer ya fashe da kuka haďe da kankameshi......


Mrs tijjani shattima...
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 2⃣5⃣ By Aysha Ya'u Kurah


A hankali Affan ya saki jabeer yana mishi wani irin kallo,
fuskarshi ya fara shafawa yana share mishi hawaye yace naji maka ciwo ne, ya ďaura hannunshi a kan jabeer yace yi hakuri kadaina kuka zo muje kaga kayan wasa na, kaima kana so ko?
jabeer ya gyada mishi kai hawaye na fita a idonshi,
Affan ya ďan bata fuska yace to ka daina kuka zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login