Showing 33001 words to 36000 words out of 72718 words

Chapter 12 - RABO AJALI COMPLETE DOCUMENT BY Aisha Ya'u kura.txt

16 Dec 2024

2290

wadanda suka riketa tana fadin a dawo dashi ko ya mutu a bar mata gawarshi,
suna shashi a mota Afeeyah ta saki wani gigitaccen ihu ta faďi kasa sumammiya....


Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣3⃣ By Aysha Ya'u Kurah


A hankali ta fara buďe idonta da yayi mata nauyi sosai,
dishi2 take gani tayi saurin mayar dasu ta runtsesu tana fitar da wani irin wahalallen numfashi,
muryar Anty Asiya ce yasa ta kara bude su ta kalleta,
anty Asiya ta shafa kanta idonta cike da kwalla tace sannu Afeeyah, babu inda yake miki ciwo,
ta lumshe idonta tana girgiza kai hawaye na zuba a gefen idonta, anty Asiya ta fara yi mata nasihar da daga ji itama na karfin hali ne,
saida ta daďe tana mata nasiha sannan ta tashi ta fita,
da sauri safnah ta dawo gefenta ta rike hannunta tana zubar da hawaye tace Afee,
Afeeyah ta kara runtse idonta hawaye na gangarorowa cikinsu kamar an saki ruwan pampo,
Safnah ta kwanta a jikinta cikin muryar kuka tace don't stop dis tears Afee let it flow nasan yadda kikeji, cry as much as u can,
Afeeyah ta kara fashewa da kuka, suka dinga yi ita da safnah dake jin mutuwar ta ko ina a cikin jikinta,
sun daďe suna kuka kafin safnah tayi shuru ta mike tana kallon Afee,
safnah tace Afee tashi kiyi sallah kinsan fa bakiyi azhar ba gashi har la'asar ta wuce, dakyar Afeeyah ta gyaďa mata kai tace shikenan safnah sun kaishi sun birne min shi ko,
shikenan ni yanzu bani da wani sauran gata a duniya ko, dan Allah safnah ki roka min Allah in mutu in bi shi dan wallhy bazan iya rayuwa ba,
Goggon daura ce ta shigo cikin dakin ta zauna gefensu tace zaki iya rayuwa Afeeyah,
wannan kukan da kikeyi babu wanda zai hanaki yinshi domin shine kadai ne zai rage miki raďađin da kikeji, ki sani jabeer yayi mutuwar da ko wane musulmi zaiso yayita, ya mutu a daren alhamis aka kaishi ranar jumma,a, ya mutu a hanyarshi ta ziyara kuma da kyakykyawar niyya a zuciyarshi,
ko wannan muka tuna ya isa yasa mu ji dadi saboda yayi mutuwar da akeso,
tashi maza kije kiyi sallah ki karfafa zuciyarki kiyi mishi adduar samun rahama wannan ita kaďai ce hanyar da zaki nuna tsantsar soyayyarki gareshi yanzu,
Afeeyah ta gyaďa kanta ta mike dakyar ta shiga bayi..


Karfe biyu saura motar oyizah tayi parking a cikin gida,
tayi mamakin rashin ganin "saunanta" a waje yazo tararta kamar yadda ya saba, ciki ta wuce cikin farin ciki tana kwala kiran sunan Affan,
salma da farida ta tarar a parlor suka yi mata sannu da zuwa, ta amsa haďe da zama tace ina "rakumi na" yau banga yazo yi min oyoyo ba,
salma ta tabe baki tace yana can gidan rasuwa kinsan Abokinshi dan girman kan nan ya wullah,, oyizah cikin tashin hankali ta mike tace how comes ya fita daga gidan nan,
farida tace nayi mamaki nima mummy, Alhj basheer yayi gyaran murya ya fito daga ďaki,
oyizah ta boye tashin hankalinta tace sannu da gida "ya hajj" yace yauwa safiya kin dawo lafiya, tace lfy lau,
ya kalli salma yace kun shiga gidan gaisuwan kuwa,
suka turo baki suka ce yanzu zamu shiga da mummy,
alhj basheer yace ya kamata bari in koma gurin zaman makoki,
oyizah ta matso kusa dashi cikin kissa tace alhj ina ďana yake,
alhj basheer yayi murmushi yace kice dan rigima, yana can wai shi bazai dawo gidannan ba sai an dawo mishi da abokinshi,
oyizah bata san sanda tace to waye ya fitar dashi daga gidannan,
alhj basheer cikin rashin fahimta yace ban gane ba,
tayi dan murmushi tace naga ya ďade bai fita bane bana son ya fita shi kaďai wani abun ya sameshi,
alhj basheer yace Ayya, baba ado mai gadi na fara turowa ya taho dashi saboda yazo yayi sallama da abokinshi duk da ba wani hankali gareshi ba,
sai baba ado ya dawo yace wai yaki zuwa daga sunzo bakin gate sai ya juya a guje,
shine naje da kaina na ďaukoshi dakyar yana ihu ya iya fitowa daga cikin gidannan,
saida muka shiga gidan alhj bara'u sannan ya iya buďe idonshi, kuma kinsan ya gama tsorata da gidannan dan kiran namun daji kawai yakeyi wai gasu nan zasu cinyeshi a bakin gate,
oyizah da gumi ya tsatsafo mata tace ayya my baby ni na faďa mishi in ya fita akwai animals da zasu cinyeshi saboda ina tsoron ya fita yaje wani abu ya sameshi,
alhj basheer yace aiko ya tsorata sosai dan yace shi acan gidan alhj bara'u zai zauna nan gidan akwai lions da sauransu,,
oyizah ta haďiye miyau tace yanzu zanje gidan ay sai mu dawo gida,
alhj basheer ya ďaga kafaďa yace sai kinzo,, sama oyizah ta wuce tana huci, a zuciyarta tace alhj ya fara bata mata aiki, shikenan ya karya wannan kafin da ta daďe da yinshi, wanka tayi sauri tayi ta shirya suka wuce gidan rasuwa...


Tun a kofar gida inda maza sukayi dafifi ana karbar gaisuwa gaban oyizah ya faďi saboda haďa ido da tayi da wani tsoho mai matsanancin kama da jabeer,
saidai shi ya tsufa sosai, maida kanta tayi gurin Affan da ya lafe jikin tsohon yana tsotson hannu idonshi a lumshe,
dakyar ta iya gaisar da mutanen gurin saboda irin kallon da tsohon nan ke mata,
cikin gida suka shige ita da yayanta sai a sannan hankalinta ya kwanta,
bayan tayi gaisuwa sama2 sai suka fito ta tsaya daga ciki ta aika farida ta kira mata Affan,
farida ta wuce ta keta gurin mazan saboda rashin kunya tasa hannu zata fara bubbuga affan,
da sauri tsohon nan ya tare hannunta yace ke lafiyarki,
ta tsaya kerere tace mummy ce tace in kirashi mu tafi gida,
ya kalleta sosai yace kice wai bacci yakeyi,
farida ta turo baki ta juya taje ta faďa ma oyizah sakon wannan tsohon,
hankalin oyizah ya kara tashi tace kuzo muje, suka fito, har ta fara tahowa gurin da suke sai ta canza hanya,
farida tace mummy gasu can fa,
oyizah tace kuzo mu tafi anjima zan sa a kirashi,
sai a lokacin kaka liman ya ganeta, a zuciyarshi yace tabbas bazaki iya hada ido dani ba dan mugu na tsoron kwayar idona, ya shafa kan Affan a zuciyarshi yana kitsa abubuwan da zaiyi ta karkashin kasa ba tare da wani ya sani ba bare ta kara ajalinshi....


Oyizah na shiga gida ta fara safah da marwah tana sake2 a zuciyarta,
fitar Affan daga cikin gidannan ba karamin tashin hankali bane a gareta,
to wani tsoho ne wannan da ya firgita ganinta kamar wani aljani, yanzu shikenan Affan yana can gurin dubban mutane kuma tasan dole wasu zasuyi mishi addu'a,
Noooo bazai yiwu ba ta fadi da karfi haďe da tashi ta kara fita daga gidan....


Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:34] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣4⃣ By Aysha Ya'u Kurah


Tun kafin ta karasa take kiran wayar alhj basheer bai ďauka ba saboda suna addu'a a gurin zaman makoki, tana karasawa taga maza sun kara yawa a gurin ta kalli gurin da tsoho da Affan suke bata gansu ba,
cikin tashin hankali ta wuce cikin gidan kamar zata rusa ihu,
a waje ta tarar da Amirah ta rako yan makarantarsu tace "ke" ina Affan yake,
Amirah ta fara waige2 sannan ta juyo ta cigaba da magana da kawayenta,
oyizah ta hassala tace ba da ke nake magana ba Amirah,
Amirah tace ay bansan dani kike ba naji kamar "ke" kikace, yana ďakin yaya jabeer,
oyizah ta harareta a hankali tace mara kunyar banza, ta wuce dakin jabeer,


Kwance ta sameshi ya kura wa makeken hoton jabeer ido baya ko kiftawa,
cikin fushi tasa hannu ta make kanshi da karfi,
a zabure ya mike yana kallonta,
hararshi tayi tace wuce muje gida, bai ďauke idonshi a kanta ba ya girgiza mata kai alamar baza shi ba,
oyizah hassala matuka tace ni kake ma musu Affan,
ya kara marairaicewa yace ni abokina nake jira,
ta damko hannunshi tace dan ubanka wa ya faďa maka wanda ya mutu yana dawowa, wuce muje kafin in ji maka ciwo,
ya noke wuya yace ni bazan tafi ko ina ba,
ta janyoshi da karfi ta hankaďo shi waje,
wani irin ihu ya saka ya ruga bayan Asiya da ke tahowa gurin,
Asiya ta rikeshi tace me ya sameka Affan, Affan ya shige bayanta yana nuna mummy da ta taho tana huci kamar kumurci, tana karasowa ta kai hannu zata kara rikeshi ya kara sa ihun da ya maido da hankalin mutane da yawa gurinsu,
Asiya tace me yayi miki ne wai,
oyizah ta harareta zata kara rikeshi Asiyah ta rike hannunta tace wai me yake faruwa ne, ki kyaleshi mana ko dole ne,
oyizah ta shaka sosai ta kalli yawan mutanen dake gurin zuciyarta na zafi saboda ganin Affan ya fara mata musu,
ta kalli Affan fuskar nan babu annuri tace ka wuce muje gida, Affan ya noke wuya yace ni babu inda zani,
Abida da rabon da tasa Affan a idonta tun kafin ya fara ciwo ta fito ta riko hannunshi tace zo muje ciki,, kaci abinci ko,?
ya gyada kanshi tace to zo muje anjima abokinka zai dawo sai ya rakaka gida kaji,
ya kara gyaďa kanshi cikin murna suka fara tafiya,
da sauri oyizah tasha gaban Abida tace sakeshi tunda babu abinda kika haďa dashi,
Abida tayi mata kallon banza tabi ta gefenta ta tura Affan gaba suka wuce yana waigen mummy dake mishi wani irin kallo, masifa ta fara yi tana zage2 kamar tababbiya dan gani takeyi zasu bawa Affan maganin da zai maido mishi da hankalinshi ya tona mata asiri, dakyar suwaiba ta rarrasheta suka wuce gida suna kulla munafurcinsu..


Kuka sosai oyizah keyi a gaban alhj basheer akan ita a dawo mata da ďanta,
ta share hawayenta tace shekara uku kenan ina wahala dashi sai yanzu zaka barshi can wani guri kace ya kwana,
wallhy alhj bazan iya yin bacci ba yau in affan bai dawo gida ba,
alhj basheer ya juyo yace haba safiya, na yau dai kaďai sai kace wanda zai zauna a can dindindin,
ta harzuka tace kasan abinda zasu bashi yau ďin,
yace kamar yaya abinda zasu bashi, me zasu bashi kuwa, oyizah ta saita kanta tace ina nufin kasan baya cin komai in ba ni na bashi da kaina ba, ta kara fashewa da kuka tace yanzu Allah kaďai yasan yunwar da yakeji,
alhj basheer cikin jin dadin kulawarta ga danshi yace karki damu safiya Affan na can cikin koshin lafiya kuma yaci abinci sosai dan abin har mamaki ya bani,
kuma kinsan ďan zaman nan da yayi a gurin makoki yau har sallah yayi da kanshi saboda ganin mutane nayi,
oyizah ta mike cikin kidima tace alhj kana yi wa Allah kaje ka dawo min da ďana,
alhj basheer yace wai bakiji abinda nace miki bane, ki bari zuwa gobe mana,
ta girgiza kanta ta wuce ciki tana kuka tana faďin dan kaga na damu dashi ne shiyasa kake nuna min ba ni na haifeshi ba,
alhj basheer yayi murmushi a zuciyarshi yana kara jin son oyizah saboda yadda take nuna kulawarta ga Affan. ..


Oyizah taci kuka a wannan daren dan ta hakikance wasu daga cikin abubuwan da tayi ma Affan sun warware, tunda har Affan ke iya mata musu kuma har yayi sallah,
wani irin ihun takaici tayi da ta kara tuno da Affan na can gidansu jabeer kuma Allah kaďai yasan abinda zasu bashi.....


Mrs tijjani shattima....
[15/12 09:37] Anty aisha ya'u kura: ◆◆ RABO AJALI ◆◆ 3⃣5⃣ By Aysha Ya'u Kurah


Washe gari tun asuba oyizah taje gurin alhj basheer ido luhu2 saboda kuka da rashin bacci,
gaba ďaya ta rasa abinda zata yi a wannan daren saboda bata san ta inda zata fara ba tunda Affan baya gabanta,
alhj basheer ya ďago ya kalleta cikin bacci yace safiya lafiya, tace alhj naga kai baccinka ma kakeyi baka damu da yaron nan ba, ko bacci banyi ba saboda nasan da kyar in ya iya yin bacci,
alhj basheer yayi mika haďe da salati yace lafiyarshi kalau safiya yau a masallaci ma na samesu tare da kaka mahaifin alhj bara'u, rike ciki oyizah tayi hankali tashe tace a masallacin suka kwana?
Alhj basheer yace a'a sallahr asuba suka je, oyizah ta zauna dabass a kan gadon ta marairaice tace alhj inda zaka san irin missing din Affan da nakeyi da baka barshi ya kwana a wani guri ba, wallhy jiya banyi bacci ba dan daga na rufe ido shi kaďai nake gani,
kasan yadda na shaku dashi kuma nake jin tausayinshi, dan Allah ka tashi kaje ka dawo min dashi,
alhj basheer ya tausaya mata dan yasan tana iya kokarinta akanshi yace to bari in yi wanka zanje in dawo miki dashi,
ta saki wata dariyar murna tace nagode alhj bari in je in shirya mishi favourite break dinshi,
alhj basheer yayi dariya ya koma ya kwanta,


Daki oyizah ta koma cikin murna tace wannan karan mai gaba ďaya zanyi akan yaronnan dan bazai yiwu su dinga daga min hankali ba, gara in kashe shi ya bi abokinshi in huta da zulumi,
wata zuciyar ta haneta da sauri tace in kika kasheshi yanzu tayaya zaki samu dukiyoyin da alhj ya mallaka mishi, sannan in kika kasheshi hankalin mutane zai dawo kanki su zarge ki, gara kibi komai a hankali ki kara tsaurarawa akanshi ki maida shi mara amfani,
da wannan tunanin tayi yan tsaface tsafacenta na gaďo sannan ta wuce kitchen shiryawa Affan break...


Karfe 9 da kwata alhj basheer ya iso gidan rasuwar,
zaune ya samesu a cikin parlor sunyi shuru sai muryar Affan kadai akeji yana ma kaka liman hirar shirme,
dariya kawai kaka liman keyi yana tausayawa halin da Affan ke ciki,
da sallama alhj basheer ya shigo parlon ya tsuguna ya gaida kaka liman sannan suka gaisa da alhj bara'u,
alhj basheer ya kalli Affan yace ka tashi lafy,
Affan ya gyaďa mishi kai yace sosai ma tare da kaka mukayi bacci shi ya tashe ni yasa nayi wanka ya bani abinci ko kaka?,
kaka liman yayi murmushi yace kwarai dan kaka,
alhj basheer yace kace yau kai ďan gata ne, to tashi mu tafi gida mummynka na can tana missing dinka,
Affan ya noke wuya yace ni bazan je gida ba, alhj basheer yayi murmushi yace meyasa? Affan yace saboda har yanzu abokina bai dawo ba,
alhj basheer yace ay yana can gida yana jiranka kuyi wasa, Affan ya waro ido waje yace dagaske daddy, alhj basheer ya gyaďa kanshi yace dagaske nake,
Affan ya kalli kaka liman yace wai haka kaka, kaka liman yayi dariya yace haka ne,
Affan ya tashi da sauri yace muje daddy,
alhj basheer ya mike ya rike hannunshi yayi sallama da su kaka liman suka fito tare da alhj bara'u,
a bakin gate suka haďu da hajja rike da katuwar kular abincin sadaka,
da gudu Affan yaje gurin ta yana kokarin karbar kular hannunta, kauda kular tayi tana dariya tace bazaka iya ba Affan,
su alhj basheer suna dariya suka tsuguna suka gaisheta ta amsa haďe da kara yi musu gaisuwa,
alhj Bara'u yace ina Afeeyah dafatan jikin nata da sauki,
Hajja tace hmm sai dai addu'a tana can tun jiya take abu ďaya yanzu na baro mahaifinta yana mata rubutu,
alhj basheer yace kuka fa dole ne hajja shakuwar zaku duba, kai mutuwa, mutuwa mai yankan kauna,
Affan yace daddy Afeeyah ce ke kuka, alhj basheer ya gyada mishi kai,
Affan ya bata rai kamar zaiyi kuka yace daddy tun jiya fa take kuka kaje ka rarrasheta kace tazo muje gidanmu taga abokina muyi wasa tare,
alhj basheer yace to yanzu dai muje gida anjima zan je in rarrasheta sai in kawo maka ita gidan kaji,
Affan yayi dariya sosai yace gaba daya zata dawo gidan mu ko?, dama jabeer yace zai bani ita in ya aureta kuma kaima kace zaka aura min ita ay ko,?
sukayi dariya dukkansu alhj basheer yace eh zan aura maka ita wuce muje, ya fita yana tsallen murna,
sun kusa karasawa gidan ya rungume daddy yace daddy ka goyani kar inga lions, alhj basheer yace babu abinda zaka gani buďe idonka nasa an cire su, a hankali ya buďe idon yaga babu abubuwan da ya saba gani a kofar gidan, a tsorace ya shiga gidan yana zazzare ido,


jiki na rawa oyizah ta fito ta rungumeshi tana faďin oyoyo Affan ďina, nayi missing dinka ďana,
alhj basheer yayi dariya yace ai da kyar ya yarda ya biyo ni saida na ce mishi jabeer na nan gidan sannan,
oyizah tayi murmurshin mugunta tace muje ciki kaci abinci sai in nuna maka abokin naka, Affan yayi dariya ya bita suka shiga ciki,


Special break ta haďa mishi wanda yaji magunguna,
zaunar dashi tayi ta cika gabanshi da abinci ta diba a cokali zata fara bashi ya kauda kanshi yana rike ciki yace mummy munci abinci sosai tare da kaka har da kosai ma mai dadi, oyizah ta ajiye cokalin ta saci kallon alhj basheer da hankalinshi ke kan TV sannan ta kalli Affan tace haba baby na, baka so kaga abokin naka kenan Affan da sauri yace inaso mummy, tace oya open ur mouth kayi ko 1bs ne,
ya buďe bakinshi ta ďebo zata zuba mishi ya kara kauda kanshi da sauri yace ina zuwa mummy kaka liman yace in zanci abinci in dinga yin bismillah, da karfi yace "bismillah", oyizah ta buge bakinshi da karfi ba tare da tasan tayi ba,
washhhh Affan ya faďi da karfi yana kallonta idonshi ya fara kawo ruwa yace mummy me na miki,
ta dafe kanta tace Affan wadannan mutanen sun koya maka abubuwan da zai kasheka,
Affan ya fito da ido waje yace "kasheni" mummy?
Ta rage murya tace yess,
kaga wannan bismillahr da yace kayi, to daga ka kuma yinta zaka mutu,
Affan yace to ai jiya munyi sosai harda wani karatu ma duk munyi kuma ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login